x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - KASUWANCINA

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 176000 words

Category: Romance Story +18

Views 150

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
na rude na rasa yanda zanyi jikina yana rawa na ja baya tare da cewa ni dai sai dai ka bani da kanka, ba yanda baiyi dani ba kan na dauka Amma na kasa sai ma shagwabewa danayi zanyi Kuka kudin sun tsoratani,mikewa yayi tare da kwaso Bundles goma yan dubu dubu ya zube min a gabana yace jeki dasu ai sai na fashe da kuka nace bana so ni,kamar naga wani Dodo na dinga ja da baya,yana dariya a ransa a fili yace kefa kike son kudi,nace ni ba irin wannan nake so ba,tunda kace sai na Eba da yawa to bani dubu ashirin sun ishemu komai da Komai,yace naga ai an baki kudin Sadaki har dubu dari Uku ya kikayi dasu?lokacin ai bana cikin hankalina Sabo da rashin lfyar Ammah da rasuwarta duk a nan suka kare.

Bundle guda ya bani na yan dubu da kyar na karba na tsaya ina tunani,kafaduna biyu ya rike tare da bude kofa ya jefa ni waje tare da rufe kofarsa,Bedroom dinmu naje da murna na nunawa Meenat tace gaskiya Sis tsakani da Allah kin damemu a wannan tsakiyar dare 3am ta wuce kinki bacci sai labarin mijinki kike mana ki kwanta mana ki huta,ni dama idan labari na Cina to komai dare sai na tashi mutum na fada masa,bayan na shirya kaina duk sun koma bacci har na kwanta nima na tuna ban fadawa Meenat labarin Daddy Baban Aayan ba.

Tashinta na fara yi Meenat Meenat ku tashi kuji banza suka min nace wai ina magana kun rainani ko,muna ji ki fada mu wlh bacci muke ji ke bakiyi ba kin hana kowa yi,ina basu labari suna uhm..eh...to...har bacci ya kwashe mu,kafin asuba wayata tayi kara ta tasheni ban dauka ba Amma sai na tashi Meenat,kawai sai ta fashe da kuka wai na hanata bacci,nace to yi shuru kwanta jaraba bakwa jin maganar Ammah tace kuyi min biyayya Amma bakwa yi,Maeesha ta farka itama tayo fitsari muka koma bacci,ni dai banyi wani baccin kirki ba sai na dinga tunanin Mijin Kasuwanci na.

Washe gari da Safe lafiyayye tea na hada mana Sai kwai na hadashi murtuk dashi naga banza ta fadi irin muci rabonmu kafin yasa a kwashe mu koma Koko,sun sha Uniform dinsu ni kuma doguwar riga da dan hijab karami,tun Safe yan gidan suke ta buga mana kofa ina ji naki budewa,bugun duniya naki budewa sai ma kara Sa lock da nayi,Ina jin Abbi yana zunduma mana ashar akan naki budewa yaransa kofa,wai nice ma zan musu breakfast kuma abinda suke so haka kowa zai fada na dafa musu,ai kuwa bugun duniya muka ki bude kofa gashi suna jin motsinmu,Abbi na gani ta jikin window ya leko yace sai kun bar gidan nan wlh tunda ba yar arziki bace ke,yar Iska,guntuwar shegiya haka ya dinga zagina ta window,na kalleshi ido da ido tare da Galla masa harara na murguda masa baki,yace zaki ci ubanki wlh sai naga waye ubanki a kasar nan,tafi nayi da hannuna na kara Harararsa ina gatsina masa goshi da gira,ni dai bance komai ba,yana ta zagina,ke yarinya ki shiga hankalinki,a nan nayi magana nace Yarinya tana bayan Uwarta ni dama haka nake idan naji haushi bani da mutunci ba kowa nake iya dagawa kafa ba ko za a kasheni,Meenat tana ta dariya Abbi ya kara kulewa,ya bar wajen a fusace yana baza babbar riga.

Aayan ne yake saukowa yasha wankan gaske cikin kana nan kaya,kamshi na tashi,Meenat tace ina kwana suka gaisa,Maeesha ya rikewa hannu tare da cewa ba gaisuwa yau?tace ina kwana tana dariya,tace kayi kyau Yaya,tnx yace sannan ya kalleni tare da cewa Abincina fa? Ai ban san zaka ci ba bari na hada ma tea,yace a'a Kunun gyada nake so ko Koko ni,idan babu kuma sai ki bani Tea,ai dole nayi maka,yo Allah na tuba ko ba gasara ai dole a nemota kamar Dan Daddy guda yana so akanta ba sai ayi yaki ba a gidan nan,Dariya na bashi sosai yanda nake maganar cike da girmamawa kamar Ina gaban Sarki,kun san wasu mazan akwai son a yabesu ko a girmamasu,wasu kuma suna so a daraja musu iyaye ya dace mata su dinga fahimtar mazajensu.

Shi Aayan a ransa yace zan gama kure wayonki yarinya har yaushe aka haifeki,Kitchen na shiga dama jiya na tace mana markaden koko,sharp sharp nayi masa tare da soya masa Chips tunda ba time din yi masa kosai,a Dining na ajiye masa sannan na dawo palo wajensa nace Ranka ya dade an gama,a ransa yace zanyi maganinki soon wai ke me wayo.

Ni na zuba masa da kaina,yana shan abinsa yayi nisa nace da sha nace Dan Allah ina neman wata Alfarma idan da hali ba damuwa kuma ban takura maka ba,yace ina jinki,nace so nake ka bani Driver daya da mota za a kaini unguwa zanje shopping sannan zamu je schl din da zan shiga,waya naga ya dauka tare da danna kira Malam Garba shugo ina son ganinka,minti kadan sai ga Malam Garba Driver yazo,Key din mota ya miko min na karba,yace gasu nan daga yau in zasu je unguwa zasu dinga kiranka kana kaisu inda suke so,ga key din mota nan a hannunta idan zaku fita ka karba idan kun dawo ka bata key din a hannunta,har schl zaka na kaisu,Malam Garba yace an gama Alhaji,nace ga key din ka kaimin su Meenat schl da yamma kuma zamu fita na fada ina wani mazewa irin matar Alhaji,Aayan yana kallona duk abinda nakeyi.
Yana gamawa ya mike tare da kara ajiye min Bundle guda na yan dubu yace gashi ki biya kudin schl din ragowar ku kara a shopping karki dawo da kwandala gidan nan duk ki tabbatar kin karar dasu a shopping,nace da gaske mu kashe duka zaka kara mana na cefane?Yace yes.

Yana fita na dinga tsalle da ihu tare da su Meenat,nace ai na fada muku ni ba a ja dani duk jarabarka sai na ma wayo,gashi dai kwana biyu har na samu abinda nake so,Meenat tace to bari mu dawo muje shopping wlh za a buga damu har mota ya bayar ana kaimu unguwa fa,Meenat tace Sis yau sai munje tsohuwar Unguwarmu a motar munyi musu birga,nace ke banza ce ba yanzu ba sai mun siyi kaya masu tsada mun koma yan gayu sai muje a gaisa ayi zumunci
Muje na rakaku mota daga nan mu ganta,gaba daya muka fita har inda Aayan ke ajiye Cars nasa,Malam Garba muka hango a wata shegiyar Benz yar gaske sabuwa dal wai itace zamu dinga hawa,su Meenat suka gaisheshi ya amsa yana me fara'a don gidan kaf babu wanda ke Saurarar dan aiki bare a gaisar dashi komai girmanka.

Meenat suka kame a gidan Baya,sai ga yan matan nan sun fito zasu tafi schl suma ina ganinsu nace pls Baba Driver ka kular min da motata ,ido suka zaro yaushe na samu matsayi har Aayan ya bani mota.da Sauri naga Hanifa ta koma ciki tana zuwa ta zayyanewa kakarsu dasu Abbi.
Ina ciki ina aiki naji bugun kofa na leka ta yar kafa na hango su Aiko naki budewa bugun duniya naki aikina kawai nakeyi.
Aayan na gani ya dawo yace na bude ina budewa Hajja kakarsu ta wankeni da Mari,ga hannunta kamar jikin bishiya Sabo da fatar duk ta tsofe ta bushe.
Zata kara min na goce,nayi niyyar magana haka nayi shuru ganin Aayan na kusa.

Abbi da Maza da mata sun kai su goma kowa da kalar zagin da yake min,Aayan na gefe ya kalleni na kalleshi,matar Abbi tace ke har kin Isa matsiyaciya daga kawoki cin arziki,na kalleta idona a bushe nace yo ai bake kika auroni ba,kema ai ba gidanku bane aure ne ya kawoki,kuma wlh Bazan ragawa kowa ba tunda ba aurenku nakeyi ba,Hajja tace iyye au Iskancin naki ya girma haka ina magana kina magana kin san dawa kike magana,nima ai baku san wace ba,Aayan ta kalla tace kai saketa yanzu na bada Umarni,maza rubuta mata saki,nace ku kuke tsoron saki idan an sakeni sai me rayuwa zan fasa ko me,Kaka tsohuwa Hajja ta rike baki dan tunda take babu wanda ya taba mata ko musu Amma gashi ni tana fada ina fada,tace saketa nace,Aayan yace baku kuka Sa na aureta ba ni ne naga dama kuma da dalilina Bazan saketa ba ya juya yayi ficewarsa tare da cewa idan kin gama ki kira Malam Garba a waya na ajiye miki Number dinsa a Dining,nace to Ranka ya dade a dawo lfy Allah ya tsare min kai,yace Ameen,nace Million dayar daka bani sunyi kadan Yanlabai,yace kin san inda suke kije ki kara yanda zasuyi,na Gode Allah ya kara budi,yayi gaba na kalli Matar Abbi Hajiya Karima nace kiji dan Allah Baby bashi da dama wlh common shopping a baka yafi million ga kyautar gida ga mota yau da Safe,tsaki naji sunja Hajja tace a sannu zan shayar dake mamaki wlh sai na canja miki kamanni ba a takani da yarana a zauna lfy.

Na kalleta nace aiki ya ganki ga tsufa ga shiga rayuwar wani Allah ya taimaka,wlh dan ina ganin girmanki ne ko ba komai zaki ci darajar tsufa da kuma matsayinki na Mahaifiyar surikina kakar Mijina idan da mutunci ke kakata ce Amma baku san haka ba,ku tambayi wace Mufeeda a Unguwarmu kowa yasan yarinyar kirki ce kuma ta wanni fannin bani da mutunci wlh da ace haka kawai ne da kun san wace ni Amma kunci darajar Mijina,ba tabani a zauna lfy dan ma ba akan kudi bane,bana yarda a taba lafiyar hanyar cin Abincina akan wannan bana dagawa kowa kafa.

Matar Abbi ce ta fisgoni suka hadu da Sauran matan suka fara dukana,sai da suka fasa min gefen bakina kadan hakan ma dan na gudu ne da Allah yasan irin Illar da zasuyi min.

Daki na fada na kulle nayi Kukana boye a fili nace wlh kun jawowa kanku dan ni indai ba lallabani akayi ba to kara lalacewa nakeyi, musamman akan kasuwancina dan yanzu auren nan ta hanyarsa muke ci muna sha shine kasuwancina kuma kowa yasanni akan Business ba mutunci zan iya ja da kowa.










AsmaBaffa
[1/9, 4:55 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA





41-45






Official







By
AsmaBaffa




Documents from AIHAUSANOVELS

Always visit Aihausanovels.com.ng For downloading free hausa novels

Like our Facebook page Fb.me/aihausanovels





MMN BASMA,SALMAT BASHEER,SUBYUSMAN ga page na baku Sabo da kauna ina Godiya.

Gaisuwa cikin Trailer zuwa ga
HAFSAT KHAIRAN
OUM FAROUG
MUM SUHAIL
MAMAN HAIDAR
HAJIYA JAMILA
MAIMOUNA MATER ta NIGER.

Kuna Raina
MEENAL SIDI
YA SALAM
DJU LUV
NANA KHADIJAH
OUM SALM@
Ina jinjina muku da Sharhi na gode.






Bayan na gama gyara gidan kaf ko ina yana sheki da kamshi,tuwon danyar shinkafa nayi tare da miyar egusi harda naman Kaza Sabo da a kwai a fridge,a dining na shirya mana komai cikin Food flask masu shegen kyau,wanka nayi na shirya cikin material cotton riga da skert nayi kyau sai ka rantse me tsada ne,dan Mayafi kawai na Sa a saman kaina wanda yasha gyara,1:30pm Sabo da a motar gida ne ba bata lokaci sai ga su Meenat sun dawo suna kwala min kira,Ku karaso mana ina ciki kuma sai kirana kukeyi,Sis yanzu muka ga Yaya Aayan a Compound su Abbi sun sashi a tsakiya tare da tsohuwar nan kakarsu sai masifa suke masa,ko saurararsu baiyi ba kawai jinsu yakeyi,Baki na tabe nace saji dashi can kuje kuyi shirin Islamiyya ga abinci nan a Dining,Bari na kira Malam Garba ya karbi abinci yaci sai muje unguwa, a waya na kirashi ya shugo na bashi abinci a flask dama na ware masa nasa daban Aiko yaji dadi sai murna da godiya yakeyi don ba a basu abincin gidan yan aiki suke burkuta musu ko wanne kwamacala ko dadi babu,fita yayi yaci ya koshi sannan ya kawo min flask din,nace in ba damuwa mu fita ka kaini unguwa,yace ai ba matsala,kudi na zuba a jakata na yafa gyale na me dan girma kalar kayana,can na hango dandazon Family ana meeting akaina irin yanda za a dauki mataki a kaina,Aayan yana zaune gefe yana latsa waya,kamar ance ya dago muka hada ido dashi, hannu kawai na daga masa irin na fita,baki ya tabe irin ina ruwansa,bayan tsadajjiyar motarmu na shiga na wani lafe a kujera ina game da yar Nokia ta wacce dan gidan Comissionar ya bani ,wata Aisha College nace ya kaini kana na Yiwa Malam Garba bayanin ya Zama wakilina a matsayin Babana ya kawo ni schl nan na tsara masa komai,yace ba damuwa yata.

Schl din 2 to 5 pm ce yare biyu akeyi Arabic da boko,Kafin ka gamata ka kware wajen Turanci da larabci tare da Sauran karatun addini dana boko,tana da kyau sosai,bayan munje wajen Pc mun masa bayani yace kinci Sa'a saura kwana Uku mu rufe daukan student na wannan shekarar,da kansa Yamin tambayoyi a lokacin na nutsu na Bada amsar wasu wasu na fadi,yace Ss1 zai sani nace to na gode,haka na biya 15k kudin schl fees,na Bada kudin Uniform har kala Hudu,sai kudin littatafai,nace Ina da aure ayi min Hijab me dan girma,haka aka gwada Size dina da komai na mikawa Malam Garba kudin ya biya a matsayin shine Ubana,aka Sa min sunana Mufeeda Adam Fatima yanda muke amfani dashi.

Bamu zarce ko ina ba sai inda ake siyar da schl bags da su Sandals na siya kala Hudu hudu suma tare da Sauran kayan karatu da komai,komai me kyau me tsada na siya,muna Tafiya a mota naga masu saida Glass na fuska,nace ya tsaya na siya,haka na zabi maka makan glass na yan gayu na gwada sunmin masifar kyau,da baki,da Brown sai farare biyu wanda ake yayi na zamani latest,yanda suka min kyau ba a magana,tun a motar na kara gyara fuskata na sa bakin nan faskeke kowa ya kalleni sai ya kara ya min kyau gashi kuma No respect.

Yanda na fita na barsu haka na dawo na samesu ana ta maganganu an hana kowa tafiya tsohuwar banza tana ta isa da Mulki ita ke magana har da wata jaka ta yan mata a gabanta wai itama fa bata tsufa ba,ganin suna wajen koda mukayi parking ban fito da wuri ba sai da na dauki lokaci yanda naga Aayan yana yi,sannan na zuro kafa daya da sabon cokeken takalmina me tsada dana siyo a wajen masu takalma na ganshi ya birgeni Dubu Bakwai na siya da jakarsa me kyau,irin zanen dake jikin material din Golden,ba wani iya tafiya nayi da me tsini ba amma karfin Hali yasa nace ai dole a je damu muma,ina fitowa sai da kowa ya Bini da kallon kurilla,yanda naci uban acuci da gashina kuma ba dankwali na daura ba kawai gyalen me dan girma da dan kaurinsa na mutunci na yafa a kaina sannan ga glass dina,Malam Garba ne ya kwaso min kayan a ledojin store din dana je,karba nayi nace na gode kaje kawai Baba sai zuwa bayan Magrib zamu fita again sabo da zamuje shopping da kannena na,yace ba matsala Allah ya kaimu,nace Ameen sannan na bashi Dubu Dubu biyu nace a saiwa iyali Alawa,ya dinga godiya nace No Need Baba Ai ba komai.

Su kuma dangin Aayan tunaninsu wasu kudi Aayan ya fara sakar min yanzu,nan take bakin ciki ya rufe su,musamman yan matan nan yau daya sunga na fara komawa wata Baturiya, Aayan yana ganin irin tafiyar da nakeyi ni ga yan mata,kwas kwas na cuno lips gaba irin yar gayun nan,nazo ta gabansu na makale Murya tare da Sallama ba wanda ya amsa nima ban damu ba dama na sani,na matsa kusa da Aayan yana zaune na sunkuya tare da rada masa taso Kaci abinci tuwo ne nasan kana ci ko? Yace zanzo kije yanzu magana akeyi min na Family,nace wanne family? anan tashi mu tafi ni dan Allah wannan har wasu dangin kirki ne,Yana so ya Harareni ko ya min rashin mutunci amma ba Hali sabo da Idan ya min haka zasu gano gaskiya sannan zasu kara wulakanta mu.ganin yaki tashi still ina tsugunne a gabansa nace ko tsoro kakeji? Naga Alama wlh tsoronsu kakeji muje ni zan tare ma fadan ko me za suyi ma zan amshe ma,tsaki yaja kadan tare da mikewa yace muje naga kin fara rainani dan kinga ina sakar miki fuska,ko kallonsu baiyi ba suka ga na janyeshi munyi tafiyarmu,Hajja makirar Tsohuwa tace kar kowa ya masa magana Ku kyaleshi ai Ubansa ya isa dashi zan yi maganinsu,kowa yaje yasha sha'aninsa zan nemeku,

Haneefa tace wannan kwai tsinanniyar Yarinya wlh,Allah ya dau ran shegiya a huta da yar Iska,Dayar a ciki tace shike nan na kasa cika burina sai da nace wa Abbi yasa Aayan ya Aureni yace baya so naje na fada sonsa na kasa cika masa burinsa,Sauran yan matan suka ce ke dai bari ai Allah ya yarda sai an saki yarinyar nan shegiya ko Nono bata dashi bata fi 16yrs ba fa,Ameer yace 17yrs take amma wlh ta iya girki dan baku jiba ne gata me kyau da tsafta inama ni na aureta,ai ni wannan ko Haihuwa nawa tayi burina Aayan ya saketa ko ta halin yaya sai na aureta,Dariya sukayi dukkansu suka tafa da yan matan,Khaleel yace mayen mata yaga kayan Dadi kana jin Aayan zai kyale yarinyar nan ko Sufi ne shi? Ameer yace ina ai wlh ko abarshi bata motsi indai bata motsa akan yarinyar nan ba to ina tabbatar ma har abada babu kuma macen da zata gani ta motsa a kanta,Dariya suka kara shekewa da ita su Haneefa harda shewa,Mujaheed yace ka manta Aayan din yanzu ne fa dan bashi da lfy ya rage amma sha'awarsa ta kai karshe,jarababbe ne na karshe kullum cikin chargi yake baya Free dan bura uba
End Ads