x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 26 - KASUWANCINA

  • 75001 words
  • 78000 words
  • Out of 176000 words

Category: Romance Story +18

Views 157

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
Door zan bude, muryar Aayan naji a hankali yace kuma a haka zaki fita again? Da sauri na koma daki na saka Katon Hijab sannan na fito na bude kofar,Ameer yasha wanka gaskiya ba karya yayi kyau cikin kana nan kaya,Murmushi yayi min na bashi hanya ya shugo,Aayan tunda yaga shine ya kara hade rai da kyar ya amsa masa gaisuwar tasa,Yau Ameer harda ce min Aunty ya gida,ganin da mutunci yazo da fara'a na amsa masa nima sannan na koma kusa da kafafun Aayan inda yake kwance na fara masa tafiyar tsutsa a kafafu ina wasa da yatsunsa,Ameer yana satar kallonmu ransa ya baci sai kishi yake taso masa Amma ya danne, Aayan yana kallon yanayin Ameer shi bai yarda dashi ba sam yayi kicin kicin.

Cike da shagwaba nace Yanlabai Abincin pls,wani shock yaji a jikinsa yanda nayi maganar shi kanshi Ameer sai da yasha mamakina a haka yar yarinya dani sai iya shege fal ciki,Ameer a ransa cewa yake ina ma nine Aayan gaskiya ya dace wlh irin wannan kulawa haka ga shagwaba kai da sake,a fili kuwa kamar baya jinmu danna wayarsa yake ya hakimce a kujera,Damun Aayan nayi da pls kajiii har sai da ya gaji ya mike zaune tare da ajiye wayar gefe can yace Bani zanci,da murna na zuba masa tare da mika masa,kin karba yayi yace hannunki aikin me yake? Da Sauri na gyara zama kusa dashi,yace ba fa a dining bane bazanji dadin ci ba,Nace ya zanyi to? Ke kika damu naci ai sai kiyi yanda kika ga dama ya fada cike da gadara, cinyarsa kawai na zauna samanta sosai bai ce komai ba sai lumshe ido da yayi ma,

na fara bashi a baki da hannuna idan na bashi bazai ko hadiye ko taunawa ba sai nace to ka ci mana sannan zai fara taunawa yana yanga yana kumbura wai fushi yakeyi shi fa,Ameer Kamar Tv yake kallonmu ya wuce gaban a share abin,yanzu ma waya Aayan yake dannawa yaki dago kansa bare na bashi abinci nayi nayi lallashin ya dago yakiya,sai ma ya kara yin can gefe da kansa ina binsa da kyar na rike kan da hannu na biyu na saitashi nan kuma ya tsaya Kikam a haka yaki bude bakin,Sai da nasa daya hannuna na bude masa lips sai ya datse hakoran nasa kuma suma,Yatsu nasa na ware su da kyar ya hangame dan mitsilin bakin nasa ya barshi haka,Ai Ameer tagumi ya rafka tare da Sa mu gaba kamar Tv yana ta dariya, na Sa masa abincin yaki kulle bakin bare ya hadiye nan ma Hannu nasa na rufe na matse bakin sannan ya cinye, haka yake ta bani wahala idan nayi wannan sai nayi wancan duk ya gajiyar dani ni kuma kamar dole sai yaci.
Ameer ganin gatan Aayan yayi yawa ma haushi da kishi ya dameshi gashi wani abin yana sashi dariya ma watarana Amma kishi ji yake kamar ya mutu ko Ya batar da Aayan ace yau shine ake masa haka ai da yafi.

Muna zaune na zubawa Ameer nace gashi Ameer kana shan kunun Gyada na sani ko? Ga abinci ma ka zuba ai ko ba ya sha sai ya sha yau tunda ni nayi girkin kuma daga hannuna ya fito, ya karba yana sha ko kallon Aayan baya yi Sabo da haushinsa yake ji ya aure masa Mufee Amma ta wani fannin yana godewa Aayan dan ta silarsa ya sanni kuma zai kwace ni nan gaba.

Muna zaune sai ga Meenat da Ma'eesha sun dau wankan Material dinsu na ankon Birthday da zasu je yanda suka sha kyau ba a magana,Kamar yanda nace haka suka zo gaban Aayan tare da durkusawa suka gaisheshi cike da Ladabi sannan sukace Yaya Zamuje Birthday din kawarmu ta schl a gidansu akeyi idan ka Amince,mamaki yayi sannan kuma yaji dadi ga Sis dinsu basu nemi izininta ba sai shi gaskiya suna da tarbiya sun san me sukeyi,da murmushi dauke a fuskarsa yace shine kuka sha kyau haka salon a dinga kalkemin matana gaskiya am gealous dariya mukayi gaba daya har Ameer,Ameer yace Wannan Ma'eesha ai tafi kyau ma wannan Meenat ta fiye iyayin tsiya wai ita me kwalliya shi yasa bana kulata ni,Dariya nayi nace Wannan ai tsokanace Ameer kana ganin Yan mata an hadu,Ameer ya tabe baki tare da cewa masifaffiya dai ta fasawa Khaleel kai rannan wannan ai Dukan mijinta zata yi watarana, shi yasa ma bata da saurayin kirki sai irin su Kwaja da Nasuru Opera,Aayan ya sheke da dariya Kai Ameer wanne Nasuru Ópera din kake nufi? Ameer yana dariya yace Opera daka sani wanda su Haneefa suke aikensa Sa ido wajen wanda suke fada ai Camera suke bawa Opera Sabo da shige shigensa ake ce masa Opera kaga ko ina ka shiga ta Opera kayi Searching,Dariya muka dinga yi banda Meenat da take son yin Kuka.

Ma'eesha tace wlh mantawa nayi Sis ban fada muku ba rannan ma a hanyar schl wani ya dinga bin Meenat yace sunansa FELA me GALA wai shi dan rawar gala ne a kasuwannin kauye baku ganshi ba kafafunsa kamar na sauro yasha wandonsa Fela kato sai uwar Kafada kamar ansa riga a hanger ,Ameer yana dariya yace baki da sa'a Meenat Allah yayi a cikinsu zaki samu miji wai ya akayi ke duk wankan naki da iyayinki kike karewa a yaran su Sajeeda,Nima nace dama Yaran su Haneefa ne? Ameer yace sosai ma ai Fela Gala shike sanar musu duk wani wajen chasu idan za ayi show Saturday sunday irin su Haneefa ai duk basa muamula da manyan Yara,ki kula ki gani duk wata yar duniya me ji da kanta zaki ga mace har mace ga kudi ga kyau Amma indai lalatacciya ce bata taba kula mazan kirki sai daí ki gansu da maza kazamai,garori,munana, tabbas zancen Ameer hakane na fada a raina duk haka yan bariki suke kuma mace na ji da kanta Amma in kaga wanda take kulawa suna harka sai ka kusa kuka.

Aayan yana dariya ya kalli Meenat da ta hade kamar yar Minister ya kasa rike dariyarsa duk ya san yaran nasu Sajeeda,karku damar min mata Kunji na fada muku kai Ameer tashi ka kai min su Driver dinsu dama baya nan kaga kaima kaci wanka kuje ko zaka samu wata Operiya a can kaima, wannan yarinyar da bata da kunya zaka ce na kaisu,Magana nayi nace haba Ameer ka kaisu mana kuje ku dawo yanzu ko dan ni ka taimaka,Ameer yace a ransa dole na kai tunda Umarninki ne Queen Mufee ta,Tunda zan faranta miki ai zan kaisu dole,A fili yace Sunci darajar Ya Aayan da ke kuzo mu tafi kuma ku tabbatar takalminku fes yake kar a bata min mota,Meenat sai Harara take zuba masa har suka fita tare gaba daya,da Sauri ya wuce wajen Hajja yace ku je jikin mota ina zuwa,

yana Zuwa wajen Hajja tana ta faman kurbar kunu yace Hajja Albishirinki na samo babbar hanyar maganin matsiyatan nan,Hajja tace mene abinda ka samo fada min Dan Albarka, yace yanzu zan shiga jikinsu sosai zaku ga muna mutunci dasu sosai,zan kwantar da kaina a wajensu yanda zasu yarda dani kinga kafin mu karbo maganin da zamu Sa musu na kulla alaka dasu me karfi ni sai na shige na aikata komai da Komai ko Ya kika ce,amma in ba haka ba za a samu matsala wajen aikata abinda malamai suke so a kansu tunda basu yarda damu ba,don haka yanzu zan fara kullum zaki dinga ganina a part dinsu zamu dinga mu'amula har su yarda dani cikin kankanin lokaci sai kawai mu gama dasu,Wani farin ciki ya kama Hajja,tace haka za ayi yanzu ka kawo magana me kyau,amma da ubanka yazo min da maganar banza ba basira ba wayo a ciki,to Amma kana ganin zasu yarda ka shige musu jiki har su yarda dakai? Ameer yace har nayi nisa ma yanzu ma sun yarda dani gashi nan sunce na kai mata kannenta wani party na dawo dasu,Hajja ta mike tsaye da murna dan Manzon Allah fa? Ko wasa kake?Yace da gaske leka ta window zaki gansu shi yasa nazo na sanar miki kar a kawo miki gulmata ki yarda kin san muna tare ke nakewa aiki,Hajja tace yo wa Isa ya kawo min gulmarka dan Albarka ai kasan bana yarda da maganar su a kanka,dariya Ameer yayi a ransa yace tsohuwa kenan nima kaina nake gyarawa hanyar samun Mufeeda na aureta ina ruwana da wani kudirinku ke dasu Abbi can da yawarku,a fili yace Hajja me zan siyo miki? Hajja tace abinda ka saba siyo min kullum dan Albarka,Ameer yace ai yau ba Hantar Rago kadai zaki ci ba harda yan shila idan ma dawisu kike so shi zan kawo,Dariya Hajja ta saki tace Ko mene ma duk ina so tunda kaine dan Aljanna.Ameer ya fito ransa fes ya tsara Hajja Sabo da yasan ana ganinsa tare da Su Meenat za a kai gulmarsa wajen Hajja ta daina yarda dashi,yanzu kuwa ya kashe bakin tsanya.

Yana fitowa ya harari Meenat ke zaki shiga baya Ma'eesha ta ce zata shiga gaba tafi kyau baza a ganni da mummana a gaban mota ba,Meenat tayi banza dashi ta shiga bayan felleliyar motar Ameer, Ma'eesha a gaba,Ameer shi irin yan Tsabtar nan ne da shegen iyayi shi a dole Saurayi wankan ma da yake irin na mawakan turai matasa irin su Justin Bieber etc kowa yaga Ameer zaiyi tunanin kwallon dan iska ne ko ta askinsa kawai ba sai an tambaya ba,wandunansa kansu na zamani samari masu ji da kansu,Duk da cewa duk matasan yan wanka ne a gidan su Ameer Amma Ameer shi mata ma rubibinsa suke gashi da wanka Tsabta ga kamshi kuma yana da kyau wanda ke jan yan mata Uwa Uba ga diri me kyau.

Aayan ne kadai bazai já dashi ba dan Aayan shi halittarsa ce ba kakalowa yayi ba haka yake komai in yayi me kyau ne,shiga kuwa dama shi a turai yake kana gani komai a jikinsa yake ba wasu yan dabaru akayi ba zallar baiwa ce,Shi kuwa Ameer tsabar kakale kakale ne da jarabar son iyayi ace Babban yaro sai da ya tsatso kyansa ya fito fili,Su Mujaheed ma haka suke shegun duniya ne wajen gayu,Suna Tafiya a hanya Ameer ya daga waya wata cikin yan matansa ta kirashi yanda ya kanannade murya kamar Sardaunan Ramlat yana Rapping English kamar wani Dj khaleed,Baki Meenat ta tabe tana jin iyayin da yake faman Digawa,aranta tace wannan wlh irin mijin Sis ne har kusan Halinsu ma sai daí Aayan karshe ne a komai,bayan ya gama wayar ya wani rare kidan Nija kawai tashi yake kamar zai fasa mana kunne,Maeesha ce mayyar rawa har ta fara yi a motar tana ihu uhhhh tare da dage hannaye sama,Shi kuwa idan kida yayi kida sai daí kaga ya bugu sitiyarin yana juya kan mota komar ma motar yakewa rawar,yanayi da kansa gashi duk Baiti ya iya abinda suke cewa kamar shi ya rerata, dama ga motar tasha tint ta samarin zamani,Maeesha yin abinta take wata tana shigowa me dadi tace ohhh yeee taci gaba da yi tana bi itama shi kanshi Ameer ta bashi dariya,ya kalleta yace ashe dai ke yar gari ce kin waye,duk kin san wakokin nan haka Amma kin iya rawa? Ma'eesha tace sosai ma ai wayar Sis Mufee nake sacewa naje schl da ita na turo latest a wayoyin classmate dina,duk wacce ta shigo bata wuceni har rawar,Ameer ya mika mata hannu suka tafa yace kin birgeni ta gidana,ai kawai a Shana,tace tunin ma ai Baza a barmu a baya ba ina jss3 fa going to ss1 ai dole aje damu,Ameer yace yessooooo Baby,

Meenat tana jinsu suna tayi sun cika motar ga kida ga surutu suna ta yi da baki gashi ana jin wakar ana bi kuma da baki ga rawa anayi a zaune gaba daya sun gigita motar.
Meenat kuwa wayarta take latsawa wacce Aayan ya siya mana tare katuwar gaske.
a wani karamin hole akeyi Amma ya tsaru sosai wajen sabo da yarinyar dangin masu kudi ne shi yasa aka tsara abin,ashe yarinyar Cousin din Sameera me yan daba ce,itama Sameera tana wajen itace ma ta hada mata Birthday party din,Yan mata irin su Meenat duk sune a wajen ansha wanka da samari na schl Yara tare da wasu kuma manya sai yan Uwa,Yarinyar Husna tasha wanka ana ta pics wasu na rawa,su Meenat ma suka Parker a wajen,Ameer yace ki bari yarinya na kankaro miki girma yanzu,Harara Meenat ta watsa masa,yace ni da zan taimaka miki nayi featuring dinki a wajen,Maeesha tace muje tare Yaya Ameer ni kayi ft dina ko a pics din da za muyi,kina ja Baby kanki na kawo light muje,ya rikewa Ma'eeshah hannu Meenat na gabansu duk inda suka wuce sai an kallesu,abinda Meenat bata sani ba an san Ameer sosai shima yanda yake nuna kudi da kalar Naira yana karyar arziki,kusan dama Daddy na Aayan ya makalewa lokacin Aayan bai dawo Nigeria ba,Ameer yake likewa Daddy sai da yayi suna sosai,ko a Tv za a nuna Daddy zai bude Abu sai kaga Ameer a wajen tun yana karami yake son ace shi wani ne yayi suna duniya ta sanshi shi yasa da farko bashi da Kamar Daddy shi yake masa labadi,ganin haka su Abbi suka juyawa Ameer hankali da ya girma sosai sai ya daina Saurarar Daddy gaba daya yake bin iyayensa.

Ai kuwa Meenat tasha mamaki yanda taga ana ta kallon Ameer ana girmamashi ,mata na rubibinsa,Har uwar gayya Sameera tazo wajensa suka gaisa tace Ina Aayan?Yace yana gida,ka gaisa min shi,wannan yaran fa?ta furta tana mana wani kallon Banza,tana ta kallonmu tace Amma wannan sunyi min kama da wata sosai,yawwa yarinyar da Aayan ke aure,Ameer yace kannenta ne,Sameera tace kai Amma yarinyar bata da kunya ko kadan ina nan zan gyarata soon,nan take Ameer ya canja fuska yace ban gane ba? Tace kwarai tayi min laifi wanda ni kuma sai na nuna mata duniya ba kowa ake tabawa a kwana lfy ba,Ameer ya fusata yace lallai kema kuwa da kin tabbata wani in ya tabaka ya taba banza kuma ba kowa ake tabawa ace za a iya ramawa ba,wani in ya taba har abada ba a iya daukan fansa a kansa,Sameera tayi murmushi tace ba irinmu ba wlh,Meenat ma tace to ke har wace da baza a miki ki hakura ba wata tsohuwa ma dake,Sameera tace duk sai kun maimaita abinda kuka ce,Ameer yace Sameera kin san Halina ke a yan daban naki kanana ne kawai kallonki ake ana tunanin kin wuce haka Amma baki kai ba,wlh wlh kika sake wani abu ya samu Mufeeda ki fara irga kanki cikin wanda suka sheka lahira kin san mu kin san Halina try me.Dariya Sameera tayi tace Ameer kenan ko Aayan da take matarsa bai ce min komai ba sai kai? Husna ce tazo ta janye su gaba daya tana kuzo muyi pics nan fa suka dinga daukan hotuna Har Ameer dan shishigi cewar Meenat,yan mata kuwa jikin Ameer suke faman mannewa ana daukansu,anyiwa Ameer ma haka inaga Aayan uban kyawawa da daukan wanka Meenat ta fada a ranta.

Tunda su Meenat suka tafi naci gaba da bawa Aayan abinci yana min yanga,Yana karba da kyar har na gaji na mike na barshi a nan yana fushinsa,Kwashe komai nayi na gyara ko ina aiki yana kallona har Magrib tayi na shiga kitchen zan mana Dinner,Ban san sanda yaje masallaci ba kuma bai dawo ba har bayan Isha sosai,

Su Meenat Suna gamawa Ameer ya dawo dasu gida sai da ya tsaya ya siyo musu ice cream sai yace banda Meenat bata da biyayya nawa dana Ma'eesha ne,Meenat tace sanda zansha ma ka sani ne,kuma sai na sha sai dai ka mutu.
Ina gama girkin na gyara komai na gidan nayi wanka nasa rigar bacci ta da turare na kaiwa Aayan abincinsa yana dakinsa ya dawo ina ajiyewa na juya na bar dakin,Bedroom naje tare muka ci abincin mu dasu Meenat muka koshi bayan ina dafawa naci wani kitchen Sabo da tsaro ko Aayan zai ce muci tare sai yaga ina cin kadan irin yar gayu ni.
Muna gamawa mukayi Brush muka kwanta tare dasu kamar yanda mukeyi da,Meenat tace to yau kuma baza aje hirar ba?Nace ina ruwanki Sa ido,Meenat tana dariya tace a'a maida wukar bani na kar zomon ba,Sis yau ba jin dadi?Dan Allah da zafi ko dadi ne dashi nasan yanzu an gama kwashe ki,Dukan wasa na kai mata ina dariya nace zan ci uwarki wlh uban kwasheni akayi ki bari idan kinyi auren kyaji naki kalar, kwana nan zan fara zuwa gyaran jiki idan munyi hutun schl zan karbi kudi wajen Aayan Amma bazance gyaran jiki zanyi ba kar ma yayi tunanin shi zanwa ko sonsa nake,Meenat ta dinga dariya tace Sis wa zakiwa gyaran jikin to? Kyaji dashi can sai kizo nan ki tamana zancen da bashi kenan Ba can kuma da kinje ki zage ku sha love,oh karya nake miki kenan? Meenat tace to mu dai kiyi bacci dan Allah mun gaji da labarinki ke Sis sai za ayi bacci kice zaki bamu labari,ko tsakar dare ki tashe mu,

Nace Meenat kinfa rainani wlh tam,ai kuwa sunyi Baccinsu wurin 12 na kasa bacci sabo da tunanin Aayan Yamin yawa sai juyi nake ina tunano yanda muke murza juna ina murmushi ni kadai, na tuna da abinda nake so muyi shawara da Meenat Aiko ba bata lokaci na juya jikin Meenat dake shakar bacci nace Meenat ina girgizata tsaki ta ja tana sosa gefen kunne,nace Meenat ki tashi mana na daka mata duka ta mike a firgice, nace mantawa nayi ban fada miki ba wai don Allah rannan kika ce kinga alamar Aayan kamar yana so na?

Wani takaici ya
End Ads