x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - KASUWANCINA

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 176000 words

Category: Romance Story +18

Views 149

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
Abbi na zugata dan a bangarensu take,lokacin Hajja ta matsa min ita Kano take so mu koma da zama Abuja ba dadi,haka na zabi unguwa mafi kyau na tsantsara mana wannan gidan da muke ciki wanda duk shekara sai an canja masa fasali, Sabo da bacin Rai Aayan ya tafi yin karatun masters dinsa na Electrical engeneering,Nafisa tana nan tana sheka rashin mutunci har da ni,yana gama Masters a london ya dawo ya mata mugun duka ya saketa sakamakon zagina da yaji tayi.

Suka kara nemo masa mata wata Rukayya ana ce mata Ruky lokacin Aayan bai warke ba na dage masa da addua Allah ya taimake mu ya warke don baya boye min komai nima bana boye masa yace min yanzu yana jin Sha'awa, Ruky da Farko tazo da mutunci tasha wahala hannun Hajja duk cikin Matan da suka aurawa Aayan Hajja bata son Ruky Sabo da taga kamar tana Son Aayan,shi kuma Aayan bai son Ruky ya dade da ganowa Ruky Makaryaciya ce gata kawai sha'awarsa takeyi dama tuni tasan Maza tun a waje,amma duk da haka nace yayi hakuri ya bata hakkinta,yaje mata da niyya kawai sai kuma ya kasa aikata komai gashi yana sha'awa Normal Amma ya kasa aikata komai,Ruky dai taga no way itama tace a saketa,wannan da yake Hajja bata sonta sai da tasa wasu suka Zane Ruky tas wai ta ci kudinsu a banza bata yi zaman aure ba,Da kanta Ruky tace a saketa,na bata hakuri Amma tace ina sam Allah ya karta baza ta zauna ba,Aayan yace taje itama,daga sannan kawai yace wa su Abbi bashi da lfy bazai taba haihuwa ba,an gwada shi hasali ma bazai iya Yiwa mace komai ba,sannnan ya kara daurawa kansa cuta yace ai ciwon sugar da Hawan jini ne dashi wai duk dan su kyaleshi haka ya huta don ya rantse bazai kara auren matar da zasu zabo masa ba ko me za ayi.

Muna rayuwa haka kullum kiyayyarsu Karuwa takeyi akanmu musamman Aayan sunfi takura masa har Hajja cikin jikokinta bata son Aayan,Shi kuma baya shiga harkarsu baiyi rayuwa dasu bama bai taso dasu ba sam basu saba da juna ba,Sabo da basa sona da Dana nace Abbi ko kannensa su bawa Aayan auren Yarsu daya ayi yar gida sukace sam basu yarda ba Sabo da a zuciyarsu suna da manufa a kanmu.
Muna ta rayuwa kwatsam Aayan ya birkice min shi Barin kasar zaiyi bai son gidan nan,aikinsa ma Shi bari zaiyi ya daina komai,na rude muna ta addua watarana ya fita shike nan bai dawo ba,Kowa har Securities basu ganshi ba,sati daya,biyu,uku,wata daya har wata Uku,babu nema cigiya har kasashe ba a ganshi ba,addua sosai har masallatai na raba,ana ta yi sai aka ganshi can wani kauye a gindin bishiya ya dawo hayyacinsa,ashe su Abbi ne suka masa kucciya,ganin haka nace dole mu Barsu,ai kuwa Hajja tace idan na tafi bata yafe ba ta tsine min,Aayan yace mu zauna kawai Amma shi zai koma Abuja da zama shine Aayan ya koma rayuwa a Abuja lafiya yana min aikace aikace na Business tare da fita kasashe,yana yawan zuwa Umrah Sabo da addua ko yaushe zaki ji ya tafi idan ya Zama less busy.

To Daddy wannan cutar taka fa? Ai yau kimanin shekara daya da rabi kenan ina haka har na saba ma,shima sati daya ina dan jin jikina ba dadi nazo wucewa Naji yan uwana su Abbi suna shawarar yanda zasu kashe Aayan mijinki Sabo da su gaji dukiyata su da yaransu,har yanzu a wannan kudirin suke,kuma duk yaransu sun san da wannan,dalilin haka na yanke jiki na fadi shike nan komai ya daina motsi shima ba kasar da ba aje ba har na gargajiya da addini anyi,masu irin cutata da yawa suna tashi suna warkewa Amma ni tun muna yi har mun gaji ma na hakura na barwa Allah.
Aayan yace bai hakura ba na hanashi har haushina yake ji yaki zuwa gaisheni Sabo da naki yarda mu ci gaba da neman magani,kin san mijin naki ba dama.
To Daddy ni kuma me yasa ya aureni? Nine nasa aka auroki yata ke zabina ce,watarana kafin kuyi aure yazo nan yana ta fushi da masifa wai daga ya kwanta a kasa wata tazo ta haye masa jiki Kazama,watarana ya kara zuwa yana fushi wai wannan ce ta zageshi wlh sai ya halakata,da kyar na lallashe shi,watarana kuma yazo yana dariya yace min kece dai ya kara ganin ki son kudi ya kaiki wani gida ko wani ya biyoki ko me kina dai ta sheka gudu kika kasa tsayawa da kanki sai da kika bigi bishiya,wata rana kuma yazo nan yace min Daddy naga mayyar nan nace wace mayya yace me son kudi taje Maula gidan Yarima tana ta shan fura a leda a gaban Maza.
Shine na bashi Umarni nace lallai lallai dole ne yaje ya aureki,sabo da ina so ko Allah zai sa yayi dacen mata ko ma ya samu haihuwa ya tara zuri'a.idona na rufe gaban Daddy sabo da kunya,yace min ke yarinya ce,nace ae a hakan,ba fushin da baiyi ba shi baya Sonki bazai aureki ba nace dole ya aureki duk yanda zaiyi ma ya aureki amma nace zai iya aurenki na Kasuwanci zuwa dan wani lokaci sai ku rabu idan zaman bai yuwu ba,bana son a cuci wani,lokacin yace indai dan na wani lokaci ne ya yarda zai biyaki kudi ya aureki tunda ina son yayi aure,ko yaushe kike so kasuwancinku ya kare ki fada masa zai rabu dake yata baza a cuceki ba,bazan miki dole ba,nasan aure a haka bazai yuwu ba,shima na fada masa.

Ya akayi su Abbi suka yarda? Sai da muka biyasu kudi me yawa sannan suka sa Hajja ta yarda suma suka yarda suka Zama maneman aurenki,kudi aka biyasu in ba haka ba sai sun zuga Hajja tazo tace bata yarda ba, ko auren da basu zuga Hajja tayi masa ba shima Contract sukayi Deal aka biyasu kudi suka kyale zancen,sun san kuma zamu iya kwace kudinmu tunda a tafin hannunmu suke,sabo da sun San baza su iya sawa a sakeki ba an rigada an biya shi yasa suka zuga Hajja tace ki dawo gidan nan da Zama,wannan securities din ma duk Aayan ne yasa suke tsaro na sabo da makircinsu,to Daddy dukiyar taka fa? Tana hannun dana Aayan na bar masa komai tuntuni shine me kudin shi yake komai kawai taimaka masa nake da shawara,mijinki young millonier ne da an San abinda yake dashi a duniya to da duk duniya sun San da zamansa,amma duk da haka da dama sun sani kasashe nayi suna shima haka.

Yarima Bobo fa Daddy?shi kadai ne abokinsa dan Nigeria da sukayi karatu tare kuma ya yarda dashi sun aminta da juna,ranar danaga ya Zane su Haneefa fa? Waya tayiwa Abbi kuma yasan ba mai iya taka musu birki sai shi shi yasa yace yaje ya Zane masa su.babu wanda suka tsana yanzu sama da mijinki da kuma wanda suke tare da shi,suna nan akan bakansu karki ga suna miki dariya ko sunyi luf kice sun shiryu wlh wani kullin suke kullawa,da bana raye da tuni Aayan ya bar kasar nan tunda ko tayi masa baki bazai bishi ba to amma ina raye ni zata yiwa kinga akwai matsala,ki nutsu yata shi yasa na baki labari ki san yanda zaki zauna dasu da basira tare da gogewa,fada da zage zage ko duka ba shi bane use ur Upper ki kwaci yancinki da na mijinki, idan kuma Kun shirya rabuwa baku da matsala Ku kuke zaune sa juna ba ni ba,yanda kukayi dai dai ne,a takaice na baki labari dan na yaba da tarbiyarki,nasan Aayan bazai fada miki ba shi yasa na sanar dake,idan kin zabi business za a biyaki ko nawa ne karki damu tashi kije a sannu kuma zaki ci gaba da gano halayensu daya bayan daya,abinda da ma ban sanar dake ba duk zaki gane nan gaba,a takaice na sanar dake.

a raina naji tausayinsu sosai har kwalla nayi sannan sai naji tausayin kaina da yan uwana,garin neman gira zan rasa ido,haka kawai son kudin jaraba ya kawoni inda za a ruguza mana rayuwa,yanzu ya zanyi?Me zanyi,lallai fada da masifa ba shine kadai zai kwace mu ba,ashe Aayan yana da gaskiya da baya saurarsu yake cewa na sharesu kawai,irin wannan kiyayya haka wacce zuciya ce dasu,ba a saduda ba dana sani tun tuni kayi ta abu daya akan wani,har Aayan suka batar dashi lallai,to tunda suka Yiwa yan Uwa haka ai nasan ma wajen Kudus zasu cilla ni shike nan zan bace ko a halakani,a raina nace ni na fasa auren na hakura da Kasuwancin kawai bari ya dawo ya sake ni kawai mu tafi,bazan iya wannan rayuwa ba wannan gidan ai sai su ni kam yafi karfi na.

Muryar Daddy naji yace tunanin Me kikeyi yata?nace ba komai kawai mamaki nake yanda kuka iya Hausa haka bayan ba anan kuke ba,yace lokacin Hajja bata wani jin turanci da Hausa muke magana har na kai 5yrs daga nan ina son yaren akwai wani bahaushe abokinsa yaci gaba da koyamin na iya sosai,Aayan ma na koyawa Mamansa duk da bata wani iya ba haka muke masa Hausa ya tashi da yare biyu,da ya dawo nan kuma sai ya kara gogewa da yaren.

Me kike so kiyi da kudi yata idan kin samu da har kika amince da wannan aure ba tare da bincike ba duk da cewa Aayan ya min bayanin halin da kuke ciki? Daddy Sabo da muyi Karatu Meenat ta zama Likita,Maeesha ta zama lauya,sannan nayi mana gida me kyau,mu dinga cin kayan dadi,sannan idan munyi aure mu dankara kayan daki masu kyau shike nan,Murmushi yayi yace to wannan tunanine me kyau,me yasa kike son Kanwarki tayi likitanci ke kuma fa? Nace ni abinda yake birgeni da Likita Daddy naga sun gwalewa mutum ido sai ayi zuruuu ana kallo sai ace yana da cuta Kaza hhhh na karashe ina dariya shi kanshi Daddy yaji kuruciyar tayi yawa sai dariya yakeyi.

Yace Allah me iko to Lauya fa? Shi Lauya Daddy Allah hular nan da suke sawa wata tum tum kamar gashin tinkiya itace take bani dariya,kuma da glass dinsu yana birgeni,sannan idan suka tsaya suna zuba karya gaban alkali sai ka rantse gaske ne,shine suke birgeni sun iya sheko ta,Daddy yayi dariya to ai ba kowa ke yin karyar ba a cikinsu,amma dai sunayi ga shedar zuuur a karbi kudin mutum,Yace Allah ya shirya su,ke kuma fa me kike so ki zama ?nace ai ni nawa yafi nasu dadi malamar Makarantar primary na dinga shiga aji gaba daya a mike ace Good morning Aunty,nace morning student How are u,suce we are fine thnk u Ma,sannnan ni kuma ina bata rai ina yanga tare da tsawa nace Sit down,kuma na dinga koya musu A babba a karama,Baba ya tafi Gona,malam yana karatu,Inna tana Girki.Daddy ya dinga dariya yace ah lallai naki yafi dadi,tashi ki tafi Yata gashi 4pm tayi Sallah zanyi, 8pm Aayan zai dawo yau daga Umrah,cikin Kasuwancin naku da kukeyi ki dafa masa abincin gargajiya yana son wainar shinkafa da miya.

Na mike nayi masa sallama zan tafi yace Yata yau kin sani nishadin da na dade ban samu ba shekarunki nawa ne haka? Tunda kaine Daddy na gaskiya zan fada ma 16 nake saura wata biyu na shiga 17yrs Amma karka fadawa kowa Sabo da har Aayan 17 nace masa bana so a dinga min kallon yar yarinya.
To Bazan fada ba sai kin sake zuwa yata nace to Daddy Allah kara lfy na fito na dawo part dinmu.

Sallah nayi na fada kitchen na fara hadin wainar shinkafa da Miya,Su Meenat sun tafi karbo mana dinkunan da muka kai wurin tela, bani na gama Wainar ba sai wurin 7:30, ina kitchen su Meenat sun dawo tare da Driver duk na zuba musu sunci har Driver,Ni kuwa ina kitchen a kaskon ma naci na koshi da naga na soya wata tayi min kyau sai nace wannan tawa ce ni zan cinye ta,saai na jefata a plate na zuba Miyar taushen na cinye ina yarfe hannu,ga zafi ga Dadi,miyar tayi dadi harda naman Rago,ina gamawa na masa kunun gyada,na yanka masa Fruits a wani glass Bowl me kyan gaske nasa a fridge,Meenat da Ma'eesha ne suka wanke abubuwan dana bata tare da gyara kitchen fes bayan sun gyara ko ina na gidan sosai yana kyalli ko ina kamshi ke tashi,Dakin Aayan na kara gyarawa duk da cewa sun gyara sai da na kara tisawa na kunna Ac ga sanyi ga kamshi,na kulle,nayi Sauri na shiga wanka,na fito yau Salo zan canja a gidan nan.

Meenat ce ta gyara min gashi da mayuka,na shafa lotion me kyau da kamshi,dama gashi na kara haske abinka da fara dama ta samu waje, yar kiba da kyau nayi Sabo da ina ci ina koshi a kan lokaci,Cikin dinkunan na zabi wani Lace me kyau pupple and Brown riga da skert nasa,yanda na fito a dinkin ba a cewa komai,mazaune sun cika fam dinkin das a jikina,Meenat ta shafa min powder sama sama ban son kwalliyar nan me yawa ni,maroon jambaki ta sa min sai kwalli tare da samin eyeliner a saman ido harda nayi tsananin kyau,gira kuwa na hana tayi min da brush na taje na gyarata ba tare da na kara komai ba Sabo da girarta baka ga yawa,tace saura sarka aka Sa min wata yar karama pupple da dankunnenta,nasa agogo na wani me kyau na yan gayu da muka siyo Brown,Meenat tace sai na Sa zobe ma yana kara kyau a hannu,haka nasa wani me kyau,ta zauna ta tsantsara min dauri tare da sakin gashina ta baya kyau ba a magana ni kaina sai yanzu na kara son kaina,naji kamar na lashe kaina Sabo da yanda na hadu,nace kai ashe nakai haka kyau,Meenat tace bakya fito da kyan naki ne ai ke kullum ke kike maida kanki baya.

Nace a haka dai duk kwalliyar taki aka hadu da Kwaja kuma,Dukana tayi a baya da wasa muna dariya,tace Allah sai na kai kararki,nace yawwa gobe zan kaiku ku gaisar da Baban Aayan,Allah ya kaimu.
Nace bari nasa takalmi ko?tace ae kisa me tsini ki Bada mamaki yau,ai ko na dakko cikin sabbabinmi wani Brown me tsini wow wow na gama birgewa yau ko uban waye ya ganni yau sai yawunsa ya tsinke indai Namiji ne.

Ina cikin gwada yanda zanyi Tafiya Meenat tana gyara mana dakin muka ji Karar motoci,nan take na zaro Hijab Meenat ta fisge ke wai mene haka bayan kin gama kwaye cinya ya gani dan Allah muje palo,duk sunyi kwalliya Meenat cikin Doguwar rigar arab,Maeesha English wear tasa riga da Wando suma sababbi sun sha kyau,mun baza turaruka,ni kuwa kamshin nawa daban ne da nasu.
Knocking muka ji nace wayyo kunya nakeji gashi nan zai ce sonsa nake,Meenat taja tsaki tace tonawa kanki asiri ki huta,Maeesha ce ta bude kofa ni kuma na hakimce a kujera na maze ina danna yar nokia ta ka rantse wata shegiyar waya ce nake chat ko wani abu.

Wow wani Balarabe ne ya shigo Aayan sanye da farar fitted jallabiya yasha kyau kamar me don ya canja style din gyaran gashi na ala tsine uwar me karya.

Kamshi ya cika gidan,cikin Securities wani ya taho zai shigo masa da akwatuna sai muka ga ya juya da Sauri ya bude kofar yace jeka daga nan ma is ok,da kansa ya shigo da akwatuna har Uku masu kyau na gaske.
Sallama muka amsa Meenat ta kifta min ido na mike jin karar takalmina ya kalleni muka hada ido,na tafi da shi Amma sai muka ga ya tamke fuska,naje har gabansa na makale murya can kasa nace sannu da zuwa Aayan.

Bina yayi da kallo yanda na sheka kyau ba a cewa komai,akwati daya na karba,Meenat ma tazo tace Sannu da zuwa yaya,da fara'a ya amsawa Meenat yace ya gida ya schl,tace lfy,Maeesha kuwa hannu ya bata suka tafa har suna dariya,tace yaya dama tuntuni Meenat take nemanka zata kawo ma karar Sis Mufee wani me Katon ciki ne cikinsa kamar Randar Ammah yake zuwa wajen Meenat wuyansa Allah kamar bulalar malaminmu,shine Sis take ta tsokanarta tana mata dariya.da gaske ya tambaya yana kallon Meenat da yake duk yarane da Sauri Meenat tace ae wlh tun rannan kullum sai ta min dariya har da dare dan Allah yaya ka koreshi in yazo,ba damuwa in yazo ki fada min yace tare da Haurawa Sama,daya bayan daya na dinga kai masa akwatunan har Bedroom,ya shiga wanka lokacin na sakko kasa naji ana buga mana kofa nasan bazai wuce jarabar yan gidan ba,ina lekawa na hangosu kuwa mata da maza manya da yara na bude tare da cewa lfy? Basu gane ni ba sabo da kyau,Ke dalla matsa gidan ubanki ne? Juyawa nayi dan su kara ganin yanda na hadu,gaba dayansu da kyar suka gane ai nice, da mamaki sukace wajen dan Uwanmu muka zo ko kina da gado ne a gidan nan? Na yatsina fuska nace ku koma sai gobe da Safe a halin yanzu Bazan iya Barin me gidana yaga kowa ba dan karma a bata mana Mood, yanzu na boye abina na Adana mijina,na killaceshi baza kuzo ku Sa masa tention ba aikin banza sai roko da san abin duniya duk abinda ake muku bakwa gani sai kun shiga hakkin iyali ba dama mu gabatar da Sunna cikin kwanciyar hankali Naja tsaki kafin suce komai na banke kofa na kulle nasa lock nayi tafiyata.









AsmaBaffa
[1/13, 12:33 AM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA






51-55






Official






By
AsmaBaffa








Ina matukar baku hakuri fans
End Ads