ya dade ko Yanlabai wayo na shirya masa wai zan masa.
Sai da na gama shirya lafiyayyan girki kala Hudu ga kayan Sha iri iri ko ina na gyara sai kamshi ke tashi,wanka na fada na tsantsara kwalliyata cikin fitted gown black and Silver,gogorona Silver na daurashi dan dagwas,sarka da abun hannu duka silver color wow ga red jambaki na saki gashi yalala.
Ina fesa turaruka naji sallamarsu suna knocking, fita nayi tare da bude musu su uku Sayyah,Mardiyya da Islaha yar gidan Wata babbar lauya, idanu suka zuba min yanda suka ganni kamar wata Queen,nan suka hau yabon kyauna Sayyah tace shegiyar kin ganki kuwa muna ganinki a Uniform muna rudewa Ashe kinfi ma haka gaskiya mijinki yayi dace ya huta,Mardiyya tace zai kwashi harkoki,dariya mukayi gaba daya nace kufa baku da mutunci,Islaha sarkin jiji da kai,bata kawa sai da me kudi,nima ganin mijin da nake aure masu kudi ne yasa ta biyo su dan ta tabbatarwa idonta,ta kuma taba ganin Aayan a TV tana sonsa sosai shine yanzu ta samu hanyar da zata ganshi face to face ko zata dace ni ko ban sani ba.
Zama mukayi a Palo suna kalle kalle duk sun Zama yan kauye suna kallon haduwa,Maeesha na kwalawa kira,yau sabo da na kara kankaro girmana bance Ma'eesha ba wai nima fa na Zama yar gayu sai da nayi zaman Hajiyoyi a kujera irin me ji da Hutu da Naira sannan na wani Kebe baki tare da cewa Angel...sai ga Ma'eesha ta fito da Headphone a kunnenta tana Jin waka cikin English wear riga da skert tayi kyau, da fara'a tare da ladabi ta gaishesu suka amsa Sayyah tace Ma'eesha ko,Marrdiyya tace gaskiya kuna da kyau Mufeeda,nace tnx Dear, Islaha kuwa sai wani cin magani take tana yanga sai danna waya take,tana kishi da bakin ciki.
Angel kawo musu ruwa,Maeesha ta cika musu gabansu da kayan abinci dana Sha iri iri,nace to ya akayi Frnds Gist me mene News?
Sayyah dama itace muke so close tace bari mu fara cin abincin Amarya muji ko kin iya,Nace ai kema kin sani yarinya,muna ta hira sosai banda Islaha,ko abincin taki ci sabo da bakin ciki,mu kuwa bamu San meke ranta ba ko ta kanta bamu bi ba.
Kamar Aayan yasan yau kankaro girma na da mutunci na nakeyi gaban Frnds,lekowa yayi ta sama tare da dafa jikin Karfen steps din sannan yace Baby ina kika sa min Envelop din nan,bana so frnds su gane min shi,amma munafuka Islaha tana Jin murya tasan shine da sauri kamar wata engine haka ta daga kai kamar kadangare tana ta faman kallonsa,wani haushinta na naji kamar na koreta daga gidana, gani nayi zai sakko kasa kuma yasha wanka da alama fita zaiyi, nace bari nazo na dauko ma,ina yauki da kisisina muka hadu dashi a steps,su Sayyah kallo kawai suke Sha,a gabansa na tsaya ina murmushi kamar zan shige jikinsa na zura hannayena na rungumo bayansa amma bamu hada jiki ba,kyakyawar fuskata yake karewa kallo da idanunsa masu kyau,hannu na zare tare da saka hannuna cikin nasa nace muje ka gani,ba musu ya Bini tare da zame gannunsa,ina gaba yana bayana ya daura hannayensa biyu a waist dina sai kare musu kallo yake har muka shiga Bedroom.
Islaha kasa kallon tayi sabo da bakin ciki,Sayyah da Mardiyya kuwa kunya suka ji lallai Ashe suna ganina yarinya ba ruwana da duniya Ashe haka nake sai kuskus sukeyi suna dariya,Islaha na zabga musu Harara.
Muna shiga yace na fasa fita ni duk ya wani birkice min,nace dan Allah? da ka kyauta dama a raina bana so ya fita su ganshi,yace amma sai dai in zaki zo mu kwanta,baki nayi kaga ai bazan kwanta suna Palo ba ka bari sai dare,to bazan zauna ni daya ba bari na fita,ba yanda zanyi dole na barshi ya fita tunda ina da bako,kallona yakeyi kamar zai hadiyeni kinyi kyau shine sai da zaki baki kika yi wannan kwalliyar su kika yiwa? Wani idan ya shigo fa ko Ameer,dadi ne ya kamani ko dai ya fara kishina,nace ai kasan dai ina yi kullum iri iri sai wannan kadai zaka ce tafi kyau?, bafa nufina kinyi wani kyau can da yawa ba,kin danyi dai kyau kadan,addini kuma ai baice kiwa wani ya gani ba sai Muharrami ba nufina wani abu ba is just tht na tunatar dake addi ne.
Murnata ta koma ciki haushi naji,kawai nace tnx na dakko masa Envelop da ya nema nayi waje abina ko saurararsa ban kara yi ba.
Ina fita muka dora hirarmu sai gashi ya fito zai fita,Sayyah tace ina wuni? Sai lokacin ya gane da mutane a palon,Amsawa yayi kawai da fara'a ya kara gaba,zumbur muka ga Islaha ta Mike wai ita gida zata tafi,Sayyah tace amma kin San haka ne yasa kika ce Muzo ki kawo mu a motarki? Sai Ku hau Napep ni na gaji tafiya zanyi,Nace ki Bari Driver na zai kaiku ga motoci a gidan nan sai kun Zaba,gaba tayi tare da cewa sai mun hadu a schl.
Sauri take ta cimma Aayan dan ta samu dama amma karaf sai suka ci karo da Ameer zai shigo part dinmu,karo sukayi da kai,dama tun asali kun San yan gidan basu da mutunci ko wanne bako ne babu me kulaka,yana dagowa yaga tayi ma gaba abinta,cikin zafin nama ya jawo rigarta baya tare da wanke ta da mari are u Mad zaki buga min wannan katon kan naki ki wuce baki da hankali,Hawaye ne ya zubo mata ba Marin ne ya dameta ba irin asarar da ya jawo mata bata ga Aayan ba sai fitar motocinsa taji.
Kyaleshi tayi ta wuce shima ya kara gaba yana takaici,Tana yin gaba ta hadu da Su Haneefa,Sajeeda tare da sauran yan matan,Gefe su Khaleel ne ke buga game,Tazo wucewa Haneefa tazo daukan Ball dinsu sai ta sata a kafa ta saita kan Islaha ta buga mata da karfi sai ga Islaha Tim a kasa nan ta saki Kuka baki ya fashe,su Khaleel da sauran suka dauki shewa da dariya,Bata kula su ba a tsorace da gudu ta fada yar karamar motarta ta bar gidan a gigice dama gidan idan rashin kunyarka bata kai karshe ba to baza ka iya shiga ka fita lafiya ba.
Bayan sallar Isha nasa Driver ya maida su tare da kudi ko wacce Dubu biyar kuma a kudin Aayan nake shiga kawai na ebo na basu tunda ni ba wasu kudi nake kashewa ba kuma ba baki nake ba yana dawowa nake fada masa na ebi kaza yace ba damuwa sabo da yasan ina da hankalina.
Aayan baya fita ya dade a waje ko wanne time daga aiki sai gida ko masallaci,Hankalina ya tashi Meenat bata dawo ba tunda ta tafi schl zana Exam,Kuma 4 zuwa 5pm take dawowa Normally amma gashi har bayan Isha bata dawo ba yau.
Ma'eesha tace Sis Meenat fa ya zamuyi Innalillahi har yau bata dawo ba,hankalinmu ya tashi sosai har na fara kuka ma ni ganin har Aayan naji shigowar motocinsa amma Meenat shuru,Kuka nake sharba ko sace Meenat akayi wayyo,Aayan yana shigowa yaga muna kuka yace lfy? Nace Meenat bata dawo ba tun safe har baki na sun tafi gashi mun kira mutane da dama har schl mate wai sunce ta taho gida,ina zata tsaya dan Allah idan ba saceta akayi ba,Aayan yace zata dawo ne ai mene na kuka bari ki gani,Aayan ya dinga bige bige waya ba labarin Meenat,Kawarta Husna na kira nace dan Allah da kuka tashi ko kinga Meenat sanda ta hau Napep ko Taxi? Husna tace wlh wani me Napep muka gani Anty yayi parking a bakin schl da yawa student sunje zasu hau yaki daukan kowa amma Meenat ganin yamma nayi taje tace ko zai kaita gida ba musu yace tazo su tafi yanzu Anty bata dawo ba? Ina kuka nace bata dawo ba wlh Husna an sace Meenat.
Shi kanshi Aayan jikinsa yayi Sanyi ya rasa me ma zaiyi,amma baya so ya nuna mana kar hankalinmu ya kara tashi sai ma lallashinmu da yakeyi,Muna haka sai ga Ameer ya shigo shima yace lfy? Nace Meenat Babu ta bata an saceta ina kuka na bashi labari,shuru yayi tare da Zama a kujera yace maybe wani tayiwa rashin kunya ya saceta,nace zata aikata gaba daya haka muke ba a taka mu muyi shuru sai mun rama bama daukan raini.
Ameer yana ta tunani sai kuma ya Mike yace Zo muje Ma'eesha mu bincika wani waje muji,da sauri ta maka Hijab ta bishi tana Hawaye, mota suka shiga ya figa da sauri,suna tafiya ya kira wayar Sameera Yar daba bugu daya ta dauka tare da cewa Hello waye? Ameer yace Driver din Rabiu Rabson ne yace na nemeki akwai Deal,Sameera ta kyakyace da dariya tare da cewa shege Rabson Ashe yasan dama ina nemansa,zo Ku dauki karamar shegiyar nan gata an kawo min ita har gida wlh sai sun gane cewa ba a ja damu,Ameer ya kara kumbura Murya ta yan daba yace kadan daga aikinki ice ko akwai kudi karfa ki mana yawa,tace ai ko nawa ne zan kashe akan wannan yarinyar yanzu ma nasa a sauya mata kamanni.
Ameer yace wanne gidan kuke yanzu?gidan karshen layin nan can dajin da ka sani na wajen gari nan Sameera ta gwada gidan,Nan take Ameer ya kashe waya ya kira wani cikin yaran Sameera ya kara tabbatar masa nan ne gidan,yan Sanda ya saita da komai suka nufi gidan.
Suna zuwa yan Sanda na labe Ma'eesha ta cika da mamakin Ameer yanda yake abu kamar babban soja ko Dan sanda,gashi da basirar gano matsalar abu har ya iya yin tunanin Sameera ce zata iya aikata haka,zauna a mota Ameer yacewa Ma'eesha shi kuma ya shiga gidan,ta kan me gadi yan Sanda suka fara Damkewa sannan suka shiga,Sameera na Zaune ta hakimce a saman kujera ga kartin Maza sun zagaye Meenat,mutum daya a ciki ne yake dukan Meenat duk ya fasa mata jiki da katuwar bulalar wire ta Wutar Nepa.
Meenat sai kuka takeyi Sameera tace sai ta bata hakuri ita kuma tace akan ta bata hakuri gwara a kasheta.
Yan Sanda tare da Ameer ne suka fado dakin, Meenat tana ganin Ameer shi kadai ta sani ta Mike da gudu ta fada jikinsa tare da kankameshi, Ameer yana tsaye kikam ya kasa komai,yan Sanda suka kama su Sameera da yaranta gaba daya aka hankada keyarsu,Sameera ta kalli Ameer tare da cewa u r smart zan dawo kanka sai na fito.
Ko kulata baiyi ba ya dauki Meenat kamar jaririya sabo da sun mata rauni da yawa zata bata masa lokaci, suna tafiya yace ki min shuru ni ko na jefar dake,Meenat da iya shege sai tayi Murmushi tana share hawaye ta kara wani kwantar da kanta a kirjinsa,yace anji jiki me laushi da kamshi dallah tashi da badan Anty Mufee ba bazan zo ba,a hankali tace Na dai gode yaron kirki,nine yaron naki? Shuru tayi,Maeesha tana mota ta hangosu ta danji haushi a ranta kishi tana son Ameer amma kuma ta tuna ai yar uwarta ce ko Ameer din take so ma zata barwa Meenat shi kuma ma ai ga jikinta da rauni taimako ne,
Sai murna takeyi ta fita da gudu,Ya sa Meenat a bayan mota sannan yaja sai asibiti,ya hana a fada min ina ta faman Kuka na Aayan yana lallashi,Anyiwa Meenat abinda suka dace a asibiti sannan suka taho gida,sai ganinsu nayi gaba daya Meenat na dingisa kafa,murna wajena da Hamdala ba a magana,Gaba daya muka zauna a Palo,Maeesha ta bamu labarin komai sai godiya mukewa Ameer har Aayan,Aayan yace ya akayi ka gane Sameera ce? Ameer yace tunda muka je Birthday party naji furucinta nasan sai ta aikata,ina jin ba Meenat nayi tunanin itace sabo da sunyi fada a wurin party Aayan yace sunyi ma da Wannan marar jin ya furta yana dungure min keya.
Na dinga tsinewa Sameera kuwa,Meenat tace to sarkin Mita yau kwana za ayi ba bacci kina nanata zancen nan,ai kuwa Ameer har ya tafi idan na tuno sai nace Ohhh ke duniya Allah dai ya tsinewa Sameera,Aayan yace addua zaki mata,bazan bata bakina ba nace,Meenat sun kwanta nima munyi shirin bacci ina kusa da Aayan yana zaune Saman Bed yana danna waya, nace Hmm Amma Sameera Allah ya wadaran Halinta,kallona yayi yamin shuru har ya gama abinda yake yace kwanta ki daina damuna da wata Sameera,nace Allah ai Sameerance yar Iska ta bani haushi na kwanta a jikinsa,munyi shuru har bacci ya fara tafiya dani na tuna nace Wai Sameera tana da iyaye,tsaki yaja ya juya min baya,juyowa ya sakeyi tare da rungumeni ya fara Romancing dina na zare hannunsa daga jikina tare da cewa kyaleni naji da jimamin abinda ya Dameni Sameera Allah ya kwaso jarabar duniya data lahira ya.....bakinsa baji cikin nawa,Na kwace baki na nace inba sai naci uban Sameera ba Allah ya....Ni ba Uban Sameera ba dai cewar Aayan,sai na tuna me yake nufi nayi shuru duk yanda yaso na bashi dama mu Sha murje murjenmu naki yarda ni jimami nakeyi,muryarsa naji cike da haushi yace Allah ya isa tsakanina da Sameera tazo kawai ta Rusa min Harka,Dariya nayi tare da cewa kaima ka dawo hanya ke nan? Yace yau kwana zanyi ina kwashewa Sameera Albarka ta cuceni.
Zancen muka Dena amma ya hanani sakewa da tabe tabe ban san sanda na mika wuya ba muka Sha romancing dinmu cikin nishadi da jin dadi.
Kwana biyar tsakani yaune kuma Hajja ta tasa keyar Ameer suka tafi karbo magani dole ba yanda zaiyi gudun kar ta gane ya bita sai da suka gama zagayensu dama duk ta sanar musu a waya an hada komai, duk wajen Malamin da suka je sai Ameer yace Malam to kuma me zamuyi wannan magani ya karye ko munyi aiki dashi bazai ci ba?ya dace mu sani gudun kar mu bata rawar mu da tsalle,Hajja har murna take Ameer me kaifin basira ne,bata San so yake duk ya karya maganin ya watsar dasu ba,bai so ya kona kar azo wani abu kuma ya samu Su Mufee,gwara komai da ilmi.
sai da suka huce gajiyar Hanya tace to Ameer gasu ka tafi dasu duk nayi ma bayani yanda zakayi amfani dasu,dana abinci,dana sawa a cikin pillow,kasan gado,da wanda zaka samu ka yafa mata a jiki ba tare da ta gane ba,Ameer yace an gama ya wuce da magunguna,cikin dare duka ya fito dasu wani Malamin yace ana musu fitsari sun karye,nan Ameer ya fada toilet ya tsula musu fitsari ,wasu Kuma akace idan aka kona etc duk yabi yayi musu yanda Malam yace in anyi baza suyi amfani ba sun karye, sannan ya juye komai a toilet yayi Flowshing gaba daya suka tafi.
Kwana biyu tsakani ya samu Hajja yana murna yace aiki ya kammala na gama komai sai saurare,Hajja tace badai su kamaka ba ko?yace haba ai na girmi tunaninsu.
Kusan kullum sai na je na gaisar da Daddy haka Su Meenat ma, yau ma na shiga Bedroom din Aayan domin mu kwanta na tadda suna waya da Yarima,Aayan yana dariya da gani a raina nace ta mugunta ce wannan, sai naji yace Saura kadan da kanta zata San inda ta nufa ai komai ya tabbata na gane ta gama fadawa sai kuma yanda zan tarwatsa komai,baki na bude a boye na kara danne kirjina sabo da tsorata da nayi ba Shakka ni suke nufi, wani kuka yazo min a raina nace sai an sakeni,yana gama wayar kamar me Aljanu na fada kansa Saman Bed ina kuka sosai na fara cizonsa da yakushi ina kuka nace sai an sakeni wlh bazan zauna ba,yana kokarin cireni a jikinsa ya kasa,Mari ya kwada min har biyu wanda yasa nan take na dawo haayyacina amma ban daina kukan ba,kallo na kawai yakeyi da mamaki bai San me ke damuna ba,shi yasan bai min komai ba,ni kuwa kukana nakeyi,ya kasa cewa komai duk nasa fatarsa tayi jajir inda na yakusa da cizo,jikina yayi Sanyi kuma naga ban kyauta ba,da alama na bata masa rai matuka Allah sarki ina son mijina ni dai Bana fata a sakeni bacin Raine kawai da zuciyar banza me kai mutum ta baro sai an aikata ayi dana sani marar amfani,Shesheka nakeyi naga ya Mike tare da cewa miko biro da takarda a fusace,Nan take jikina ya fara bari ina addua kar ya sakeni,a hankali na kalleshi shima ni yake kallo,nace Dan Allah karka sakeni kaji? Tsaki yaja yace kawo min nace ko,nace dan Allah ni dai dan Allah pls na fasa wlh kuskurene ina son Aurena,Yace ni ance miki mahaukacine ko yaro ne irinki da zakice nayi abu ba tunani nayi,dakko min biro nace ko ya daka min tsawa,jiki na bari nace gashi na dakko na mika masa kuma na rungumeshi tare da dabaibayeshi ta ko ina,a hankali nace in dai akan na yakushe ka ne kayi hakuri bari na biyaka fatarka,Toilet na nufa ya Bini da kallo kawai,ruwa me Zafi a bowl tare da dan towel karami fari na dakko,ban kulashi ba na cire masa riga tare da kwantar dashi tunda yana daga Zaune, yana kallon ikon Allah na gasa masa jiki,yace kin gama?nace ae,yace to kawo min takardar da biron a rude na fara ina ina da soshe soshe na kashe light duf na cire kayana duka na shige masa jikinsa gaba daya na sukurkutashi,yace ba abinda kike nufi zan rubuta ba fa abu zanyi Jotting na Office nace ni gobe kayi banda yau,Sai salo nake masa,yace fada min me yake damunki?idan baza ki fada ba kuma fitar min a room,cike da shagwaba na sanar masa komai da na naji suna fada,Dariya ya