x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - KASUWANCINA

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 176000 words

Category: Romance Story +18

Views 134

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
gayu komai kadan kadan ba dole na cinye ba.

Yau kuwa yace sai ya kure yarinyar nan mayya,ya Mike ya koma kitchen sai gashi dauke da kaza tasha hadi tana tiriri da Alama warming dinta yayi ya turo min gabana,kamar nayi kuka sabo da dadi yaushe rabon naga kaza guda a gashe sabo da murna ban san sanda na kalleshi ba nace Dan Allah ka daukeni aiki ko share share da goge ne a gidan nan,wata uwar Harara ya zabgo min ban san sanda nace yi hakuri na fara yagar kazata ba ina aikata cikina,gani yayi fa da gaske zan iya cinyewa kawai yace karta je ta barke min da Zawo a gida kawai ya taso ya fisge plate din tare da cewa Mayya.

Yana dawowa ya mika min faskekiyar wayarsa nufinsa wai nasa Number na kira gida,ban iya ba amma gudun laifi na karba haka nan take nayi kamar zan iya na zuba yatsuna guda biyu na fara birkita screen din,naga Sam ban gane ba nasa yatsuna guda hudu na fara dirzawa a fuskar wayar,na juyata na juya na dukufa kamar Idona zai zazzago sabo da yanda na zarosu ni a dole me danna waya,shi kanshi da ya kalla yayi tunanin wannan yarinyar Aljanu gareta ko mahaukaciya ce bai San tsabar rashin zaman aji ne da rashin shiga mutane daga siye sai siyarwa, gani yayi zan masa barna ya fisge abarsa tare da cewa fada min Number cikin hasala kamar zai dakeni,to mu dai a gidanmu babu waya dama akwai wani Shehu me Kanti idan wani abu ya faru shi Muke kira a waya sai ya kai gidanmu ayi magana don Number dinsa na kaina,na iya da turanci amma wai dan kar nayi mistake ya dakeni sai naji tsoro nace gwara na fada da hausa nan na fara cewa

sifili takwas sifili...wait wait ths is bull shit ban san wannan abun ba,nan nace yi hakuri bari na Canja na firgita kawai maimakon na fada da turancin sai wai dan yafi ganewa sai nace..tayar mota.. takwas..tayar mota,wai gani nayi Zero (O) yana kama da tayar mota shine dan yafi ganewa nace haka,wani mugun dariya ce ta kamashi da ya gano me nake nufi da Zero ne Tayar mota lallai wannan yarinya dakikiyace amma sai ya daure fuska yace wlh zan kwada miki mari zan miki abinda baza ki manta ba,nan take nace 080 sannan na fada masa Numbers da turanci,yace amma ke dan Iskanci zaki raina min hankali kin iya fada dai dai nonsense tare da Jan tsaki yana dialing bugu daya aka daga ya mika min wayar nace Hello...Shehu Mufeeda ce,dan Allah dan kaiwa Ammah wayar mana minti daya,nan Shehu yace to Mufeeda ya fita da sauri yayi Sallama gidan tare da gaishe da su Ammah dasu Meenat suka gaisheshi suna cikin wani Hali sunyi jirim suna jimamin Ina Mufeeda ta shiga tun safe har dare hankalinsu ya tashi,Shehu yace gashi inji Mufeeda tace za kuyi magana ai da sauri Ammah ta karba jiki na bari,Mufeeda tace Ammahna kuna lfy? Ya jikin naki? Ammah tace ba ta wannan nake ba kina Ina Mufeeda lfy iceko,dariya ni Mufeeda na kakalo tare da cewa lfy lau Ammah kin ganni a gidan wannan kawar tawa wacce kika sani Naeema yar gidan me kudin nan kin San ai da sun tafi kasar waje to sun dawo shine muka hadu a kasuwa tace muje naga gidansu,
shine ma mamanta take tambayata ke nake basu labarin cutarki da aikin da za ayi miki shine Maman tace mijinta yayi tafiya gobe ko jibi zai dawo na zauna kar na tafi na jira zai iya biya mana kudin aikin da za ayi miki,kinga ai bazan taho ba shine na zauna ina jira kuyi addua Allah sa a dace,nan take Ammah wani farin ciki ya lullubeta tace Mufeeda kin tabbatar haka zancen yake ba karya?nace tabbas Ammah ai kin San halina dai ko kin San kuma dalilin fita ta Allah watakil ya amshi adduar mu,Ammah kinga dadin da naci harda Kaza da Yogourt,kuyi addua amma yau Ni ina cikin daula ina su Meenat bani su,nan ma aka bawa Meenat suka Sha labari aka mikawa Maeeshah ma tana Anty jambaki pink ya kare ki siyo min wani,kuma takalmi na ya tsinke Sis nace to Maeeshah zan siyo bawa Ammah,nan nace Ammah aci gaba da kular min da Kasuwanci na dan Allah Meenat tayi komai,Ammah tace kin San basu iya kosan sosai ba,Nace Ammah suyi haka koma yane a tara min kudin in na dawo za muyi magana sai goben idan ya dawo me gidan zan sanar dake idan Bai dawo ba zan fada miki komai dai,Allah yasa a dace cewar Ammah ta mikawa Shehu wayarsa Mufeeda tayi masa godiya ta kashe shima ya musu sallama ya tafi,nan Ammah tace Meenat ta kulle musu gida ta rufe suka yi kwanciyarsu cikin farin ciki.

Ni kuwa ina gamawa hankalina ya kwanta nan na saki ajiyar zuciya,shi kuwa da mamaki yake kallona yanda na iya fesa karya haka,lallai suna da matsala amma ina ruwansa,ni ko dama su Ammah nake ji kuma na gyara komai,idan na koma nasan karyar da zan kara shimfidawa, baki ya tabe nan take ya fisge wayarsa tare da wucewa samansa,ni kuwa yana tafiya na koma saman 3seater na kwanta a tsorace har bacci ya saceni, tunda ya shiga bedroom ya rasa wannan mugunta zai min wacce bazan manta ba ina cikin bacci naji ya harbo ni kasa daga saman sofa,a firgice na tashi, ba Imani yace sai nayi Kamun kunne,haka nayi na Dade ina yi har sai da na saki Kuka,sannan yace nayi kneel down sannan Hands up nan ma na fara ina tayi haka yayi tafiyarsa ya barni ina ta abinda ya sani har bacci ya kwasheni na bingire a wajen,ban farka ba sai da gari yayi haske na Mike a firgice tunawa da banyi Sallah ba yasa na Mike da sauri na fada bedroom din da nayi Alwala jiya,komai na kayan wanka da amfani a kwai a toilet din masu tsadar gaske,ba bata lokaci tube kayana na kai hannuna ruwa me dumi sosai yana zubowa gwanin dadi ban san sanda na fara wanke kaina da shampoo me kamshi da tsada ba,ina gamawa na dauki liquid soap na sheka wanka sai kamshi ina ta washe baki,ina dubawa naga harda sababbin tooth brushes da toothpaste na dauka kuwa na wanke bakina tas abinka da abu me tsada hakorana suka kara haske da kyau Malam nayi wani Fresh dani,Towel nasa tare da goge jikina tas,sa nan na daura Towel na fito ina kara tsane gashina,mirror ba abinda babu na shafawa masu tsada,na dauki lotion na shafa a jikina,babu powder sai wata fara kawai na shafa abata na dauki lipgloss na shafa me kyau red,ban san jagirar waye ba na dauka na zizara a Idona sai gashi nayi kyau sosai.

Gashi na wanda ya bushe na taje na shafe shi da Maya Mayan gashi yana sheki da kamshi dama gani Allah ya bani tsayin gashi,Daure abina nayi nan take nayi acuci da gashina sannan na shafa roll on tare da turaren jiki dana gani me arnen kamshi,kayana na kwaso na saka haka ina so na wanke pant dina amma ba dama kawai na maida abina sai lokacin na tuna banyi sallar Asuba ba da sauri nayi tare da Azkhar sannan na fito Palo cikin Jin dadi na zauna,ina jin motsi na sauka kasa tare da kneel down na daga hannu sama wai dan yace a haka na kwana inayi,kallo daya ya min yasan Lallai har wanka nayi,ko kallona baiyi ba ya fita,15mnt sai gashi ya dawo tare da take away leda hudu,ya zauna a saman Sofa tare da miko min leda uku da sauri na karba dama yunwa nake ji nan na zauna daram tare da bude ledar sai ga kwai da chips tare da gashashiyar Hantar rago, haba Malam nan na zaro harshe na lashe labbana na fara dagargazar Harka yi nake ba ji ba gani,nan na kau da Leda daya na bude daya na lashe na jawo ta Ukun na cinye komai tas tare da daukan ragowar ruwana na jiya na shanye tas nace Alhmdllh tare goge hannuna da tissue din dana gani ciki.

Mamaki ya gama kashe Aayan har firgita yayi yana mamakin a ransa kuma cikinta baya lalacewa,yana kallon TV yace tashi ki gyara gidan nan kaf yayi maganar kamar bada ni yake ba,Zumbur na Mike na kayan aikin,kitchen ya nuna min da yatsa ina shiga na gansu a shirye na hado da kayan mopping,yace na biyo shi haka yasa na gyara samansa Kas Kas, ko ina yana kyalli har su toilet,abin ya bashi mamaki baiyi zaton zan iya gyara haka ba,muka dawo kasa ko ina na gyara har room din da nayi wanka da toilet,haka ya dinga nuna min wasu sashen har wajen motsa jikinsa sai da na gyara tsab,ta window na hango maza suna ta aikin gyaran compound flowers tare da goge windows ni kuma na gyara ciki, nayi matukar jigata nasha wahala,yace sai na shiga kitchen haka na shiga na wanke na goge na gyara komai neat har store,haka fridge ma ya fitar da abinda suka lalace yace na gyara ciki tare da bani wasu abin na gyaran Fridge haka na gyara fes na kara Mopping kitchen din na wanke komai na shanya su sannan na fito,ina fitowa yace naci gaba da Kamun kunne ba Hutu,inayi ina kuka,sai da na kai 1pm sannan yace naje nayi Sallah na bar masa gida,cike da Murna na Mike na gyara jikina tare da Alwala nayi Sallah ta saida na kara gyara fuskata gudun tuhuma wajen Ammah sannan na fito tare da yin hanyar waje,Keee naji muryarsa me sanyi,juyowa nayi a rude nan naga ya daga waya yana magana Hello Abbi ka tashi lfy,ta ciki naji Muryar Abbi yace zo ka bude min kofa ina son magana da kai gani a gidan ka wato ni zaka rainawa Hankali ko,nan take ya firgita amma dake namijin duniya ne sai ya maze bai kawo komai ba ya raba ta gefe na wani kamshi ya dakeni nan take jiki na ya mutu na lumshe ido,kofar ya bude kawai sai ga Abbi ya bayyana a gabana da sauri na tsorata tare da ja baya.

Salati ya saki da salallalami yace dama nasan wlh ba abin kirki kake aikatawa a wannan gidan ba shi yasa nazo da kaina,ashe baka da kunya baka da mutunci ai jiya na tambaya ina ka kwana ance ba a sani ba nasan kana nan,ashe abinda kake aikatawa kenan munafiki ka nuna Sam kai baka kaunar mata Ashe abinda kake kenan,karuwai kake kawowa gidanka,ashe shi yasa baza ka iya zama da aure ba,wannan yaro kwai tsinanne in Allah ya yarda Cutar kanjamau ce ajalinka,baza ka jawo mana abin kunya ba wlh dole yau Hajja taji zancen nan kuma aure dole kayi zaka ga abinda zai biyo baya,nan Abbi ya min kallon Banza ya fice a fusace.

Shi kuwa Aayan ko a jikinsa haka ya nuna amma yaji zafin sharrin da Abbi ya masa,ni kuwa tausayinsa naji sabo da na tuno maganganunsu farkon ganina dasu,Driver ya kira a waya sai gashi yazo umarni ya bashi jeka wannan zata gwada maka gidansu ka,ka kaita can.Nace na gode wata uwar Harara ya balla min nan take nayi mukus tare da bin bayan Driver na shiga motar sai muka bar gidan ina jin dadi na rabu da jaraba.











AsmaBaffa
[1/1, 10:59 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖

KASUWANCI NA






11-15






Official






By
AsmaBaffa







Ths page is for u MARCYCOOL.

ina matukar Godiya da jinjina fans masu Sharhi aci gaba da gashi kuna birgeni.








Allah ya taimakeni Driver na da kirki cikin mutunci ya kaini har kofar gidanmu wanda kaf mutanen unguwar mamaki sukeyi na wannan arniyar mota amma wai sai suka ga Ni Mufeeda yar Kasuwa yar talakawa fitik wai ni aka sauke a wannan mota, ai fa sai mutane suka fara guna guni ga zahiri ai karuwancina ya girmama ni kuwa Allah sarki ban san ma sunayi ba, wata kawata a makwaftan mu Nawwara itama dai Nawwara yar malam Shehu ce talakawa amma sun fimu rufin asiri ita kadai ce kawata sai kuma wata yar gidan masu kudi Na'eema amma ita yanzu sun koma Kasar waje da karatu har iyayenta suna kasar waje abinsu,

A hanya Nawwara tace Mufeeda kece a wannan zundumemiyar mota haka duk da bana zarginki ki kiyaye ko sabo da sharrin yan Unguwa,Murmushi nayi tare da cewa Allah kadai nake tsoro ni,Allah yaga zuciyata.
cike da farin ciki na shiga gida da Sallama dauke a bakina,da fara'a suna min Oyoyo sannan na wuce wajen Ammah tare da gaisar da ita,tace Mufeeda kar ki kara yin irin wannan tafiyar kinji na fada miki,wannan ya Zama na karshe da zaki tafi wani gida ki kwana ba tare da Sanina ba sai dai ki bugo waya,bazan yarda da wannan shirmen ba,karki ga na yarda dake kice zakiyi abinda kika ga dama ko dan kina ci damu etc kice zaki juya ni baki isa ba,ni ba irin iyayen nan bace masu son abin duniya akan yara ne ke ci dasu sai su zauna yaran na juya su sai abinda suka ga dama zasu yi,ki nutsu wlh akan haka gwara mu daina karbar abin hannunki bana so neman Kudi ya kaiki ga halaka ko sabawa Allah,naji matukar ciwo da sai dare ma zaki bugo ki fada min ni har ga Allah ban yarda da zancenki ba kawai dan naji lafiya kike yasa na dan samu nutsuwa,nan Ammah ta dinga fada ba ji ba gani ina bata hakuri harda kuka na,nace bazan kara ba kiyi hakuri abinda na tsaya nema ma ba a dace ba domin me gidan yayi tafiya kasar waje nan ma na kara mako karya ta na fada,aiko nasha fada wajen Ammah,ni dai hakuri nake bayarwa har ta hakura.

Bayan kwana biyu tsakani naga sana'ar tawa ta danyi kasa don haka na tattara ragowar kudin dake hannuna na siyo kajin Hausa da Akuya guda daya wai zan gwada yin kiwo ko za a samu suyi albarka,Kaji biyu yan budurwa na kawosu,akuya tana meee...mee na samu na daure ta can karshen gidanmu,lokacin wake beans yana araha kawai na auni kwano biyar na boye ina jira yayi tsada na siyar naci riba,sannan na dan siyowa su Meenat kayan kwalliya tare da kayan makaranta Uniform na dinka musu sabo idan an koma schl suma su sa sabo,haka na siyo mana Atamfa muka raba yadi biyu kala Uku akayi mana dinki me kyau na talauci domin rabi wasu yadi ne na adon Atamfa akayi mana kari dashi,sai suka ba da ma'ana,dama bamu da kudin dinka shadda daga atamfa sai materials sai kuma kayan gwanjo da muke sawa,suma dinkin atamfar na talauci duk bamu da riga da zani ko daya daga skert damamme sabo da yadinma bai isa ba bare tela ya maka mana dinki dole sai dan fitted,sai ko dogayen riguna baza ka gammu cikin Tsumma ba Sam sabo da ina yawan yi mana dinki tare da yan takalma na roba yan Dari hudu zuwa biyar muna dasu da yawa dasu muke too match,haka mayafai ma ina siya mana da hijabai zaka ga muna canja abinmu iri iri mata sai da gyara ai,bani da burin da ya wuce naga Ammah cikin farin ciki Tare da kannena duk kudin da nake nema sabo da su nake nema.

Asalinmu
Sunana Mufeeda Adam Fatima, Asalin Shuwa Arab ne Babanmu,a Borno state suke da Zama tare da Family dinsa gaba daya,Bashi da Ilmin Boko sosai sai kasuwanci da yake y,Babanmu Adam yana da dangi da yawan gaske wanda mu bamu San dasu ba Sam,Iyayensa sun Dade da rasuwa tun yana yaro domin shi kadai suka Haifa Allah ya musu rasuwa ya taso a maraya,shi yasa ma ya taso da neman Kudi har Allah ya kawoshi Kano state,yana shiga kauyuka saro kayan Noma ya kai kasuwa,Har ya shiga Kauyen Ammah wato Kauyen Rimin Gado can rigar Fulani,Nan yaga Ammah cikin halin rashin gata tana Shan wahala hannun matar uba sabo da bata da Uwa sai Uba,danginta kuma fulanin tashi ne basa Zama Sam kullum a yawon daji suke basa Zumunci,bayan Adam Abban mu ya auri Ammah da shekara daya Allah ya dauki ran Baban Ammah wato Sulaiman,Haka Abba yaci gaba da kula da Ammah suna zamansu lfy a cikin birnin kano gwale,ko sunje kauyen ma ba wasu dangi sun tafi yawon Shanunsu har Ammah ta daina zuwa ma tunda duk yan Uwanta sai wanda suke uba daya kuma basa kulata sai ta kyalesu kawai amma duk da haka tana kaimu muna zuwa itama kafin lalura ta sameta tana zuwa musu.

Mu kuwa ganin basa zuwa basu damu da mu ba ko tace muje sai muki zuwa idan munje ma basa ganinmu da daraja,Shekarar Ammah da Abba biyu da Aure ta Haifeni aka sa min suna Mufeeda kowa yana yabon kyauna,sai da na cika shekara biyu sannan aka kara haifar Meenat,itama After 3years sai aka Haifi Ma'eeshah,Lokacin Babanmu ya samu wadata sosai ya siyi gida kato cikin Rijiyar Zaki muka koma ciki yana Business sosai sannan ya zana waec da Neco ya koma makaranta yayi NCE ya gama,lokacin tuni ina zuwa Primary schl amma ta Gomnati sabo da ba masu kudi bane mu sai rufin asiri domin munfi karfin ci da Sha bare sutura,ina primary 3 aka saka Meenat da Ma'eesha suma muna zuwa nice Babba, Da yamma muje Islamiyya, ina kula dasu sosai domin tun ina yarinya Allah yasa min son iyayena da yan uwana fiye da kaina,mun taso cikin kulawa da tarbiya muna jin dadinmu har na kusa gama Primary

sai kuma muka ga Abbanmu sam ya daina kula Ammah sai wulakantata yakeyi,ba
End Ads