tunani Allah yasa ya warke ya yi maganin gaba daya.
Bayan na gama girkin daren nawa Ameer yau bai dawo da wuri ba daga ni sai Aayan muka ci,. 8pm nayi shirin bacci da komai a dakinsa shi kuma naga yana ta cin kwalliya kamar ranar daurin aurensa sai fesa turaruka yake faman yi,nace ina zaka je? Yace wajen yarinyar nan ta Us ce tazo kuma a Hotel ta sauka ba dadi Budurwa kamarta ta zauna a Hotel ai ba mutunci ko kawai zanje dakko ta ne ta zauna damu kafin ta koma.
Kamar ana zuba min ruwan zafi haka naji a zuciyata,ji nayi kamar zanyi hauka gaba daya hankalina baya jikina Sabo da tsananin kishi,nace idan an Isa Allah ya dau raina yau ba sai gobe ba, nace Wayyo Jama'a ga Kwarto,Ameer ya dawo yana kasa yana juyowa ina ta ihun Kwarto a sama,shi dai yasan Aayan yana gida Amma yace bari ya gani kar ko wani ne daban da Sauri ya karaso Saman yace Anty Mufeeda lfy waye,Aayan ne ya fito cikin shirinsa yace kyaleta jeka kuruciyarta ce ta motsa,Ameer yana dariya yace Ya Aayan kaine kenan Kwarton Aayan yace ae fa gani,Ameer ya juya yayi tafiyarsa yana dariya a ransa yace Mufeeda itama irin yan fulanin garinsu ce kenan,Ni dai ko a jikina na fara kuka yana daukan Agogo zai fita na dakko Jambaki da Sauri na bude shi na dinga shafa masa a rigar ta ko ina na jefar da jambakin na kama rigar na dirje lips dina da ita kalar pink jambaki ga wancen Red,yace kinyi ta banzan dole zanje ya bude kofa kenan na jawo rigarsa ta baya,ina ta uban nishi ina Hawaye,hakan baza ta kaini ba na tsuguna na kwaso kafafunsa Amma ko motsi baiyi ba,sai ya biye min ya tsaya don yaga me zanyi masa tunda Hannunsa nake ta ja da karfi,sai ya biyoni tunanina ni nake jansa ta karfi ina nishi na jawoshi har Jikin Bed,ya tsaya kuwa,nace kwanta to dan Allah kaji ina ta kukana,yaki kwanciya na kara mikewa na danna shi kan Bed ta karfi,nan ma gani nake ai karfi nane ya kwanta sharab,yana kokarin mikewa na fada kansa na kwanta daf daf tare da rufa mana bargo tare nace ka dubi girman Allah ka kwanta,Sabo da me? Aljanune suka ce kar na barka ka fita kana fita zaka samu matsala,a lokacin kuma da Aayan yake son fita lokacin Abbi ya barbada masa Wani garin magani a kofar fita wajen part dinmu suna jira ya taka wajen,mu harga Allah bamu san da wannan ba kishi na ne yasa na hanashi fita.
Sai da Abbi Sani ya Kira Aayan a waya wai ya fita yanzu ga abokan Daddy nan sunzo duba Daddy daga Abuja kuma karya yake burinsu kawai suga Aayan ya taka maganin kafin gari ya waye,idan har gari ya waye to ya karye maganin ko an taka bazai yi ba,shine suka rasa yanda zasuyi ya fito suka hada abin da Wai Bakin Daddy sun san yanda yake kaunar Daddy dinsa.
Ta inda Allah ya tsare Aayan sai a ransa yace bari ya tsokaneni yaji shine yace ai wajen wata zaije,ni kuma uwar kishi shine sai da nasan yanda zanyi na hana fitar ta dole,a hankali na kai bakina zan masa kiss yace karki taba ni,why? Kince Sabo da jikinki nake taba ki so na daina taba ki,to Sabo da me kake tabani? Fadi gaskiya naji? Murmushi ya saki sannan yace Do not judge a person by their looks or the things they have. You do not love some one for their appearance or their nice cloths but because of their personality, their thoughts etc u have to Understand kinji?
Shuru nayi ina jin dadi yaci gaba Sometimes people don’t tell you how they truly feel about you but they will always show you so pay attention ki gane ba sai ance kullum ana sonki ba kamar yarinya ku yan mata haka kuke.
Baki na turo tare da cewa ni dai duk da yanzu ina jin turanci kayi min da Hausa yafi shigata sosai kai turancinka na turawa kakeyi duk a harde, murmushi yayi yace Ok ku mata sai kuyi shekara yafi goma tare da mutum yana ta nuna muku yana sonku Amma wai in dai bai ce i love u ba to kawai ba sonku yake ba,wani ma sai ayi ta cewa ai kawana ne,kuma in ka sake kana gani zata auri wani ta barka,sai kace daga baya ina sonki tace me yasa baka fada min da wuri ba bayan duk abubuwan da ka nuna mata na zallar so ne.
Murmushi nayi nace uhm munfi so muji gar da gar, kumatuna yaja da dan karfi sai da nayi kara sannan yace I LOVE YOU......I DO REALLY LOVE YOU,I NEED U,I LOVE EVERYTHING ABT U,U ARE MY SOULMATE BABYNA ya karasa furtawa tare da hade bakinmu waje daya yana sha,Dadin da nake ji ya wuce a fade shi,nan take na kara kankameshi,naji yana nema ya zarce nace bari nayi fitsari,a hankali ya sakeni na shiga toilet,na kulle tare da jingina da jikin kofar ina sauke numfashi da ajiyar zuciya bakina yaki rufuwa Sabo da murna,dama Sabo da kar ya gano ni yasa na gudo toilet Sabo da nayi murnata ni kadai,harda tsalle da murna ina yarfe hannun dadi,sai da na dade ina murna sannan na hade rai na fito daga toilet irin ko a jikina bana murna, gefensa na kwanta ya kalleni tare da saka hannunsa cikin nawa Baki ce komai ba Baby, akan me fa na furta ina yanga,do u love me too? Yatsina fuska nayi tare da cewa sai nayi tunani na duba naga ko ka dace,Murmushi kawai yayi tare lumshe ido ya jawo ni jikinsa Amma Sabo da iya shege sai na ja baya kadan tare da kwace jikina.
Shima bai takura min ba ya kyaleni kawai tare da daukan wayarsa dake uban ruri sunan Abbi ne a jiki,sai yanzu ya tuna Abbi ke neman Sa yaje tarbo Bakin Daddy,amma abin mamaki baki daga Abuja su rasa lokacin zuwa sai dare kawai dai yace gani nan yanzu su jirani,Abbi yana ta masifa ka wulakanta mutane Sabo da kai ga me kudi ko to kayi gaggawar fitowa,burinsu ya fito ya taka maganinsu,Ni kawai ban yarda da fitarsa ba kishi nake ko wayo zai min macece da yace daga U.S take,nan take na fashe da kuka ganin ya mike da gaske fita zaiyi, a hankali yace mene ne? Ni..Allah ba inda zaka fita,Indai ka fita Bazan kara tayaka kwana ba kawai baka so na,mirmushinsa me tsada yayi tare da cewa kina jin yanda Abbi ke fada bakin Daddy suna jira na kiyi hakuri naje naga ko su waye mana,Yanzu wasu bakin kirki ne da Dare haka ni Dai Allah baza kaje ba na sani ko wajen budurwarka zaka je.
Hakura yayi kawai da fita Sabo da yaga da gaske tunanina yana da budurwa gudun Zargi sai yace Ok na fasa to,murna na fara yi tare da kashe wayoyinsa gaba daya na ajiye gefe,shi kuma yana zaune gefen Bed na zagayo ta bayansa tare da Zura hannayena ta cikinsa na rungumeshi gaba daya a jikina,bai san sanda ya lumshe ido ba jin yanda Albarkatun kirjina suka sauka a bayansa,Kasa jurewa yayi ya juyo tare da matsane a kirjinsa gaba daya kamar zai fasa min Kashi, gaba daya ya tafi dani ban san sanda na biye masa ba alhalin nace na daina yarda yana taba min jiki yanzu sai na bashi wahala Amma sai gashi na kasa jurewa,har mamakin kaina nakeyi yanda nake da Feeling me karfi kan Aayan bana jurewa.
Da Zafi zafi muke Sarrafa juna kowa na nuna kwarewarsa Har Aayan ya dauki Hanyar Cinma burinsa Amma sai kawai sha'awarsa ta tsaya cak ya gagara komai,ni kuwa dama gyaran jikin da nayi nace shike nan na hakura ya samu abinda yake so Sabo da son kudi na bana so nayi asarar kudin gyaran jikina gwara ko mutuwa zanyi kawai ya Mori kudinsa tunda dama danshi nayi gyaran idan ba ayi ba ai na rafka asara tare da bata lokacina.
Kallonsa nayi da tausayi sosai Sabo da yana da sha'awar abin Amma kuma bazai iya ba wannan Masifa ce,sai dai yayi ta shan wahala,shuru kawai naga yayi ya fada dogon tunani,Nace Man ya akayi ne? Har yau baka warke ba ko? Kai kawai ya daga min,da kyar yace min am so sorry na kasa baki hakkinki shi yasa bana son auren nan,amma kiyi hakuri idan kinga da matsala ko zaki shiga wani Hali tunda ban san ranar warkewa ta ba ki fada min duk da ina sonki nasan da kyar idan zan rayu babu ke zan iya hakura, Hawayen tausayinsa ne ya ziraro min nan take nayi Sauri na rufe masa baki nace karka kara ambata in Bazan iya ba zamu iya rabuwa ka daina ba kai ka daurawa kanka ba Allah ne kuma watarana zaka warke,kayi hakuri itace Kaddararmu ba shi nake so a tare da kai ba wlh ko shekara nawa zakayi a duniya zan iya hakura mu zauna tare,Allah idan har kaji ni Mufeeda nace ka sawwake min ko mu rabu ko zan bar gidan nan abu na farko da zaka min kawai ka kaini gidan malamai masu Rukiyya kawai ba kalau nake Ba ko Aljanu sun shafe ni ko an min asiri kaji na rantse.
Ka daina damuwa ko kasawa kanka tunani, na gode Baby Na gode yake ta maimaitawa I love u so much My wife,yanzu in naji kince mu rabu ko zaki barni na...da Sauri na karasa ka kaini Ruqiyya wajen Malamai kawai asiri aka yi mana,Dariya yayi kadan tare da kara kankameni a jikinsa.
Can kuwa su Abbi suna ta faman kiran Aayan a kashe ma wayar,Abbi yace iyyeeeeeee ehhh lallai yaron nan fa ya fara tsallake iyaka dan muna daga kafa ne kawai idan mukayi sake muna jiran Hajja to lokaci zai kure mana,da gani yar iskar matarsa ce ta hanashi fitowa wlh bazai wuce ita bace,Abbi Sani yace dama naga Alama yanzu sai abinda tace Gwara mu fara maganin shegiya,akwai Maganinta Hanifa ko Sajeeda zan bawa aikin su zuba mata a abinci inda da kanta zata bar gidan a nemeta a rasa taje can tayi ta garari a duniya.
Abbi yayi dariya sannan yace ai har kannenta kar a bari su dawo tunda sun tafi dangin ubansu to su zauna can ko su Bita ita Mufeedan su karata can,da banyi niyyar kulata ba Amma yau ta shiga gonarmu,Washe gari da Safe Saturday Ameer yana Bedroom muma haka na hada mana break na shirya a Dining na koma ina taya Aayan shiryawa Sajeeda ta samu yanda zatayi ta bude kofar ta shigo a hankali tare da kallon gefe da gefe ta tabbatar ba kowa a wajen sannan da Sauri ta karasa saman Dining ta bude duk kalolin abincin dana shirya ko wanne ta barbada garin maganin sannan ta rufe a hankali ta juya zata tafi duf Numfashinta ya dauke na wasu dakiku sakamakon ganin Ameer da tayi tsaye a bayanta ya harde hannaye a kirjinsa,yana mata wani wulakantaccen kallo.
Nan take jikinta ya fara mazari, ba zato taji mahaukacin Mari ta ko ina,zafi ya hada ta kamar an dosana mata wuta a fuska,Fisgo wata waya yayi ya fara tafkarta yana Ball da ita,tun tana neman agaji har ta garara,ni kuwa munji kamar hayaniya amma hankalinmu bai kawo ba,Ameer ne ya samu Kwalaba ya fasa tayi cako cako ya jawo Sajeeda kiiii har palo ya zauna saman Kujera,Fuskarta ya rike da karfi tare da dagata,tana kuka tana bashi hakuri tasan Ameer bashi da Imani zai iya yankar jikinta da Kwalaba,kamar me aski ya fara karta mata Kwalaba tun daga goshi jini na tsatsafowa,Sai yanzu muka fito nan muka hango irin muguntar da Ameer ke aikatawa,Aayan ne yayi magana da karfi Ameer me ya faru wannan wanne irin rashin Imani ne?
Gashin Sajeeda ya fisga da karfi tare da cewa confess dan uwarki,nan take Sajeeda tana kuka ta fara tonawa kanta asiri da Abinda Abbi ya sata aikatawa,Ni Mufeeda Salati na fara nace Ameer hada da kirjinta duk ka karce shege a Zane mata ko ina,Aayan yace no..Ameer kyaleta taje mun godewa Allah ma haka tunda ya nuna mana,baki na turo nace ni dai baza a barta ba sai an cire mata farcen kafa na Babban yatsa ta karfi zan tsige shi,Aayan yace ba a nan gidan ba ke tashi ki tafi,tana mikewa na damkota tare da yarda ta kasa Aiko Sajeeda ta fini karfi kawai sai ta rufeni da Duka sosai na koma neman a taimakeni,Aayan yace au Sajeeda naji tausayinki an barki shine zaki dukar min Mata to na fasa,Sajeeda da fuska duk zanen Kwalaba da jini tace ae din tare da gallawa Aayan Harara kafin ta maida idonta ya kafeta da Mari hagu da dama tare da bude kofa yayi short da ita waje ya maida kofar ya rufe,Ameer yace na fada ma basu da kunya.
Nace ai wlh sai naci ubanta idan na kamata sai na karya mata hakori sai na tsoma mata yatsa a ruwan zafi, dariya Aayan yayi yace ai tafi karfinki gashi zata ji miki rauni a banza nan nace ai kyaleta nayi kawai Amma mu fada a wajenmu harda na siyarwa dan Babanta. Kwashe abincin nayi gaba daya na juye a leda na kai Dustbin Ameer ya fita dasu waje,haka na dan dafa mana saukakakken abinci abincin mu me dadi muka karya,s ai mita nakeyi na hana kowa sakewa.
Tunda Hajja da Abbi suka ga abinda aka Yiwa Sajeeda suka shirya Tafiya can kasar Kudu cikin wani kauye wajen Babban sabon bokan da aka basu lbr anyi,
Har wanda ya basu labarin bokan gaba daya da shi aka shirya yayi musu Rakiya banda Hajja ta dai ce Abbi yayi komai.
A jirgi suka sauka a Enugu daga nan suka dauki Taxi wai ya kaisu wani daji ko a garin Enugu tsoron bin hanyar Dajin akeyi Sabo da matsafa sunyi yawa a dajin, Driver yayi ta Maza yana Tafiya dasu yana tsoro ko yan yankan kaine,yana Tafiya yana jan tsaki yana Chaiiiiii Alaji,suna jinsa har dai ya kaisu dai dai inda zasu dan shiga dajin da kafa mota ko machine basa shiga sai da kafa,Suka sauka tare da bashi kudi yace Alaji always making juju Money,go and Meet ur Malam is Better than to visit ths land wooo, u have to be very careful with ths place,ahhh see me see troble because of Money so people can do anything in ths world they can even kill them self,Abbi yace Abeg carry ur Wahala and Go stupid Taxi Man,shi dai me Taxi ya figi motarsa bayan ya gama surutunsa.
Dan cikin dajin suka shiga kadan sannan Me Rakiya yace anzo wajen,Abbi yace ya sunansa kace? Mutumin yace sunansa SHAKYLGANCY sai kace dan India cewar Abbi,ai a india ya koyi har kar nan Alhaji cewar me Rakiya.
Suna zuwa wajen anyi Ado da komai Red Abbi yace Shakylgancy.....Shakylgancy.....Sai ga Shakylgancy bugul ya bayyana kamar Aljani wani me mummunar suffa,Cikin harshen turanci Abbi ya koro baya nansa,Shakylgancy ya kece da daria sannan yace shima cikin turancinsa yace 1million Amma baza a biyashi sisi ba sai in magani yayi suka ce Shakylgancy baza mu iya dawowa nan ba karbi kudi kawai ko yayi ko baiyi ba karbi kawai zamu dinga contacting dinka a waya idan ta kama dole nayi kokari mu dawo,Shakylgancy ya washe hakoransa tare da wani hancinsa kato kamar tattasai ya karbi kudi yace suje zasu ga aiki.
Bayan su Abbi sun fito gefen titi tare da Dan Rakiya suna neman Taxi wata mota ta yan Mafiya matsafa ta shararo da gudun tsiya dan Rakiyar su Abbi shine a gefen titi motar na zuwa tayi gaba dashi ta markadeshi a titin fit kansa ya dinga gare gare kamar Ball a saman titi,su Abbi sunyi mutukar firgita shi da Abbi Sani nan suka ga fa an kashe banza motar ko slow down bata yi ba,aiko su Abbi suka take da gudu suma suka mike titi sambal suna ta yi kamar yan tseren gudu basu san sanda suka watsar da takalma tare da babbar rigarsu ba,dama Abbin Sajeeda cewa yayi suje sun wakilceshi shi tsoron zuwa kudu yake yi tunda watarana a Crossriver akasace wani a gaban sa shike nan ya firgita.
Sai da su Abbi suka yi Nisa sannan suka samu Taxi da kyar ta kaisu Har airport a Hanya suka siyi Sababbin takalma Amma Sabo da rashin Imani ko Jimamin Mutuwar abokin Rakiyar tasu basu yi ba sai Abbi da yayi karfin halin daukan hoton gawar a waya Sabo da ya nunawa iyalansu gashi wancen talaka ne shi da iyalansa Amma an mutu a shirka,nan ba aci ba can ba a ci ba,a kiyaye talaka ka lallaba kanka ka samu a Aljanna.
Yau ni kuwa shirye shirye mukeyi Su Meenat zasu dawo daga Maiduguri Ameer yafi mu Zumudi wurin Magrib sai gasu kuwa da kaya Niki Niki sun shigo sai murna lokacin Yarima yazo sun finta tare da Aayan,sai hira mukeyi muka ci muka sha,Ameer yace Duk kunfi kyau a Kauyen Rimin Gado har kumatu kuka yi,Meenat tace ai baka kyauta ba tunda ka wani gudo,yana dariya yace tab ina wani zan iya zama a wannan garin toilet ce tashin hankali ana kallonka a waje,ga wata katifa kamar ta jariri,dariya mukayi gaba daya muna haka sai ga Aayan tare da Yarima,Yarima yana ganin Ma'eesha wani sanyi ya fara ratsa shi ita kuwa Ma'eesha kunyarsa takeji kwarjini yake mata wata uwar signa ya mata da ido ai ko Nan take gaban Ma'eesha ya fadi rass Sabo da lokacin Ma'eesha ta cire Ameer dama shakuwace