sam Bazan iya fita dake ba bari muje da kyawawana su Meenat,dama haushinshi nakeji ya bata min kwalliya kuma baice ina da kyau ba yanzu kuma wai ya fasa zuwa dani,ban san sanda na fashe da kuka ba me karfi, ba shiri yace taso taso mene haka wannan uban kuka zaki fasa min kunne,gyalena na dauka ina share Hawaye yace Sa Hijab na kara sakin kuka yace to yafa gyalen haka muje wannan masifa haka,ina dariya na yafa haka nabi bayansa,sai da na kara tsayawa a bayansa na zaro Powder a jakata muna tafiya bai San ina ta shafawa ba,na gama nasa jambakina red,kafin mu karasa mota har na gyara ribbom din gashina nayi acuci sosai na gyara mayafin aiko na dau kyau kowa ya ganni yaga yar gayu,nasa glass dina dan Brown nayi kyau ba a magana,yana juyowa sai da ya firgita kamar aljana kafin aje mota har na sake kwalliya yace zanyi maganinki a ransa tunda bakya jin magana dai dai nake dake.
Gaba na shiga Meenat da Ma'eesha suna baya shike Driving yau,katafaren store muka tsaya Meenat sai jin dadi muke muma mun Zama yan gayu,sabo da neman suna sai da na karasa tare da rike Hannunsa muka jera sabo da naga Yan mata sai shige da fice suke a wajen ko wacce ta Sha wanka, hannuna ya rike yana murzasu muna tafiya duk inda muka keta sai an kallemu,Kayan sawa iri iri yace mu zaba,dana tashi sabo da tausayin kudi abinka da ba a saba ba kawai sai na zabo atamfofi dasu laces materials dasu Ready made duk ba na sama da Dubu biyar daka biyar sai kasa,gani nake na gama kure karyar kudi, yana duba kudin yace a maida su wannan ai wanke kudinka ne Hajiya,da kansa ya dinga jidar mana kaya masu matukar tsadar gaske komai latest,haka takalma ma,bags ma ba a magana,har su cosmetics yana zabo me tsada muma muna daukan wanda muke so,har jewelries, muka je bangaren Inner wears yace su Meenat su zabi nasu aiko suka jida masu kyau iri iri,ya jani wani bangaren can daban na inner wears yace zabi size naki naga ko Bra kuwa kina sawa? kullum daga an dage miki riga direct ake tafiya can,Kunya naji na rufe ido nace Ina sawa mana amma a boye nake sawa na wanke a boye bana so ace kamata ina sa Bra,to mene a ciki dan kinsa yaja tsaki tare da cewa anya kuwa jinin birni ce ke? Nace a'a daga garinku nazo murmushi ya saki sannan yace mu bamu da dangi a Rimin Gado mu gaba da baya dan birni ne ni,muna ta Zaba iri iri masu kyau ya dauko min wata yar karama yace ga wata me kyau,Hararar wasa na masa nace kaima kasan sunfi haka wuce nan sai kace yarinya,muna dariya sai ga wata yar gayu tana kwas kwas da takalmi ga kamshi tana zubawa muryarta muka ji tace Aayan kaine a nan we finally meet here ohh,Dagowa yayi tare da zuba mata idonsa me matukar kyau ya danyi murmushi kadan sannan yace Sameera kece How u?longest time,tace am great ina ta so mu hadu wlh amma ba dama tun aurenka na farko fa gaskiya mun dade.
Wani kishi da bacin rai ya taso min na bata rai nayi kicin kicin na tashi hankalina gaba daya ina Harare harare,itace second wife din naka? Ina Yarima yana dariya yace yana lfy yar duniya kin buya amma dai kin sake aure yanzu ko? a'a aure ai sai na huta ina aiki ina samun kudina matsalar maza ta isheni baku da kirki Sam ni sai na huta zan yi Insha'allah,Jin bata da aure yasa na kara fusata na daure fuska na dawo gaban Aayan na juya bayana tare da kwantar da jikina a jikinsa muna facing juna da Sameera sai kallon Banza nake mata,Hannunsa na jawo guda biyun na sakalosu ta kafaduna ina wasa da yatsunsa,Murmushi Sameera tayi tare da cewa am sorry to say Aayan kasan bana boye abinda ke raina amma wannan tayi maka yarinya da yawa Aayan kamarka da auren kamar wannan da gani ma baza ta wuce 15yrs ba,ga mata a gari zunduma zunduma da ka fada mana ai da mun zabo maka manyan yara amma irin wannan ai kuruciya zaka sha baza kaji dadinsu ba.
Dariya sukayi gaba daya tare da wani tafawa abinda ya bani haushi kenan ya kara kuleni mene nasa na tafawa da mace,nan take naga fa ta fada min baka zata barni da takaici ban san sanda nace uhm Allah sarki kuma a hakan bashi da kamata dan ina masa abinda Babba bata isa tayi masa ba,tunda tsab nake daukeshi wanda nasan ko uwarki yafi karfin.....kafin na karasa yasa tafin hannunsa ya rufe min baki da karfi dan yasan sai na karasa ko za a mutu sai na rama,ina so na kwace baki na amma yaki Sakina ya toshe min da tafin hannunsa yana fada min a kunne kina magana wlh yau na lahira sai ya fiki jin dadi bakya jin magana ko ke ba a isa an miki abu kin hakura ba sai kice sai kin rama wannan wacce magana ce ta marasa kunya uwarta fa kika ce,Sameera ta kalleni sosai tace da Sameera kike zance yarinya zaki san kin zagi uwata,wlh sai kin San wa kika cewa haka,Allah ya taimakeki yanzu Kinci darajar Mijinki amma a sannu zan goge miki abinda ke kanki,Bakina na kwace nace Ba Sameera ba Allah yasa kece Sameeran Gayaπ€£ wlh nafi karfinki kina magana kina cijewa ke ga yar daba karewar Daba munga Amana ta Alim maπ Sameera dama irin Masu takama da yan daba ne har yara ne da ita yan daba,bata da kunya duk abinda taga dama haka zata fadawa mutum shi yasa ko zaman aure bata iya yi,sabo da ko yaushe a shirin daba take kana mata zata sa yara yan daba suyi ma kaca kaca tana takama da kudi sabo da ubanta ita kadai ya haifa ya rasu ya bar mata dukiya me tarin yawa,Tun kafin ya mutu ya raba gado yaba yan uwansa ya barwa yarsa komai,shi yasa take abinda taga dama,kuma bata San mutunci ba duk inda take da kai zata iya ci ma mutunci ta ko wanne hanya,Aayan kuwa Business ne ya hadasu tsakanin Company nata da nasa tun da dadewa.
Ni kuwa nace komai dabancinki baza ki bude min ido ba kiyi duk abinda zakiyi nima baki San ko ni wace ba shi yasa har kike magana dani haka ina kyaleki,ki Bari watarana Business ya hadamu anan zaki gane true color dina,Tsaki taja ta bar wajen a fusace,Aayan yana ta kallon yanda nake tsiwa yar ficika dani gaban sangamemiya irin Sameera ko tsoro bana ji,na kalleshi nace girma ya fadi wlh ka ba dani ina ma kallon Ustaz har wani hannu kake hadawa da yan tasha,da gani wannan yar tasha ce gaka da fyallelliyar budurwa me zaka ji a hannun wannan me suffar mazan, kayi dacen mata amma baka godewa Allah kana wani rikewa wata hannu bayan ga hannun da zaka samu lada Allah kyauta ka daina irin wannan a gabana dan wlh ni bazan dauki a wulakantani ba dan baka darajani ba Sam,ka zubar min da mutunci ace Namiji yana da kamata yana rike hannun wata banza,wannan babban matsalace dole na tuntubi kaina Ashe ma ban kai mace ba.
Yana jina ina ta masifa kamar uwarsa yana dariya a ransa,yace to yi hakuri masifaffiya tunda bakya so na daina,wai nice budurwa shi baya daukana a budurwa Sam,yace wai ke nan budurwa ce? Bacin rai ya kamani sai na danne a fili nace a'a kwaila ce,a na dinga masa masifa ina zan rama zaka San ba budurwa bace ni daga yau na Canja salo again na fasa wannan Business din da mukace za muyi wani zanyi daban sai na sa kayi nadama har ni za a wulakanta dan anga ina biyayya ina cusa kaina ina kokari naga an zauna lfy shike nan za a gani,dariya yayi yace a'a dan Allah tsokanarki nakeyi fa muyi Business dinmu zan biya kudin,nace anki din sai na rama nima.
Mun gama siyayyar komai yasa aka kai boot din mota ya biya muka fito kenan sai ga Ameer da Khaleel tare da wasu yan mata masu suffar karuwai sai chewgum suke taunawa su a dole manyan yara,na kalli Aayan na bata rai nace kalli Meenat a gabanmu tsaya kaga abinda sukeyi kalli,ya kuwa kalla sosai ni kuwa wai dan kar ya kalli yan mata nayi masa wayo,Muna zuwa Ameer sai kallona yakeyi zasu shiga mu kuma zamu fito na bi ta tsakiyar yan matan nan a hankali yanda zasu ji nace yan iska sun dauko yan iska su a dole yan mata ana yaye baki a titi na wuce fit na koma kusa da Aayan,Khaleel ya fusata kwarai da maganata haka yan matan ma,Ameer kuwa so yasa baya ganin laifina sai dai ma birgeshi da nakeyi aransa ma cewa yayi wannan gaskiya kika fada Mufeedata tabbas yan iska ne suka dauko yan iska Allah ya baki basira tare da saurin ganewaπ€£
Yan matan zasu zageni Ameer yace wlh duk wacce ta fadi ko bakar magana a kaina sai ya mata illa har fada suka so yi da Khaleel..
Muna shiga mota na tuna zanyi girki kuma kayan miyarmu ya kare nace Aayan kayan miya na manta,Yace to mu koma store din nace a'a danyi gaba wajen yar kasuwar can zamu samu.
Muna zuwa yayi parking nace sai ya fito munje tare,yace a'a nifa ban taba siyan abu a kasuwa ko gefen hanya ba a store nake siya,Na fara rokonsa dole haka ya fito muka karasa wajensu,sabo da tattalina da son kudi nace Malam kwano nawa nawa? Aayan yace nidai a zuba kawai mu tafi,nace a'a so kake ayi mana tsada bazai yuwu ba yo ni akan barkono kwano daya idan nazo sarowa Basai na yini a wajen ba ana ciniki ba kuma karshe kaga na siya arahar banza,Dariya Aayan yayi yace yini guda fa? Nace Cass ma kuwa, Agogon Dubu biyu ina siyoshi a Dari biyu da hamsim ni highest Dari biyar zan siyi shege,ka dinga zuwa dani siyayya kaga araha,Aayan kallona kawai yake yana dariya,Nace kai me kayan miya kwanon tattasan ne dari biyar a garin gaba gaba muke da zan siya haka,yace gaskiyar magana Dari hudu da hamsim baya tsada bana nawa kike so a siyar miki,Nace to ka rage,nafa San kan kasuwar nan,Aayan yace Haba Ke kuwa har kwano guda Dari hudu da hamsim kacal a kasa siya mene na tsada a nan? Harara na watsa masa tare da dan zungurinsa nayi masa magana a hankali bana son haka ba a yiwa yan kasuwa haka,zaka kashe min ciniki idan kasan haka zaka min ka koma mota yanzu duk ragi ai ragi ne,Aayan yace Malam zuba mana kwano biyar ga kudin ya zaro kudi ya mika,na fara rigima na cumimiye a jikinsa baza a biya ba kwano har Dari biyar gwara Ku tafi gida ni Ku barni a nan nayi cinikin ko Dari hudu na siya sai na samu Dari Dari ta Zama tawa,na dawo a taxi, ko kulani baiyi ba yace to tumatir fa,nace a tsaya ni zan Zaba da kaina,me kayan miya yana ta dariya yace kudi kudi ne ga gwalagwaje wanda ya gama lugwiguwicewa daf yake da rubewa kudinsa daban,ga masu kyau manya da kanana,nayi layin marar kyau gwalagwajen nace duk tumatir tumatir ne tunda dafashi za ayi mu sharbe miya Malam ga me sauki ba sai anyi asarar kudin ba a bamu wannan,Aayan dariya ta kamashi ta gaske ya dinga yi yace wlh baki isa ba gwara da Allah ya kawoni na gani dama abinda kike sawa muna ci kenan? Nace to sau nawa ka shanye miyar sa kana Santi ai ni in kaga lafiyayyan tumatir a fridge to na cin salat ne,ai ko harda kwalla Aayan yake dariya ni kuwa ko a jikina,yace Allah na gode ma da na gani da Ido na shi yasa Ashe ba kya yarda a bawa kowa yayi cefane sai ke Ashe Guba kike bamu muna ci.
Aayan yace Malam me kyau wanda yafi kowanne tsada zaka zuba, na hangame baki ina jimami shike nan za a ci kudinmu a banza,akan dan tumatir har yan Dubu Dubu na fitowa naji kamar na fisge kudin,na bata rai ina ta fushi nace ai gwara ni ka bani na dinga tara ma kudin watarana sai mu dakko a siyi abu me amfani dasu amma wlh wannan Almubazzaranci ne, mukaje layin Albasa nan ma dan yaga yanda zanyi yace zabi da hannunki one by one ki dinga zubawa a ledar mu gani,me Albasa yace ai kwano kwano muke saida wa,Aayan yace bari ta Zaba sai a auna zan biya ko nawa ne,aiko na fara Zaba sai na duba wacce ta tsage ko ta kusa lalacewa ko marar kyau sai na dauka na nunawa me kayan miya nace kaga dai wannan araha zata yi ehe,wannan ma ba me tsada bace,Aayan yana murmushi yace pick the nice one mana,na kai hannuna kan me kyau sai na koma na faki idonsa na jefa marar kyan a leda yana kallona yana dariya har na gama sannan yace to Malam juye wacce ta bari bata Zaba ba su zamu siya,haka aka auna ina gani kamar na fashe sabo da ni kudin da aka kashe kawai nake jin haushi da an tattala su ai sai a moresu watarana Rayuwar Manage na iya a haka na taso da ita na saba.
Na dauko shima ya dauki wasu muka zuba a mota ina ta harararsa yana kallona ta gefen Ido yace daga yau tsinke baza ki kara siyowa da kanki ba da kaina zan siyo ko na bayar a siyo,nace girkin ma ba sai kayi abinka ba,wlh ya kamata ka koyi adani sabo da rayuwa ni gaskiya nake fada ma.Maeesha dama suna gani sun San halina sun San yanda nakeyi a kasuwa dariya suma sukeyi Meenat tace Yaya Aayan ya kaga mutuniyar taka ta iya Zabe ko?
Dama kadan yake jira ya dinga dariya yace ai naga Zahiri yau Meenat,haka takeyi ko a gida Ammah ta dinga ta mata fada amma baza ta ji ba cewar Ma'eesha.
Meenat tace ai baka San abin haushi bama shi yasa bama Rakata kasuwa watarana akan egusi da zamu siya wlh sai da muka yini a table din me egusi har fada sukayi ya koremu gaba daya,kai ai kadan ka sani, turmi ma ba a cin arziki a gidanmu ko daka wasu sukayi a ciki sai ka biya ashirin, haka gugan Rijiya ma ko kurar Ciro guga duk na haya ne hhhhh Aayan ya dinga dariya Meenat suna ta bashi labari suna min dariya,sai da na saki Kuka sannan sukayi shuru.
Haka ma Ya Aayan watarana ta siyo min jakar makaranta me kyau ina ta murna wata kawarta Nawwara tace gaskiya jakar tayi kyau nima zan siyo aiko Mufee na jin haka tace Dari uku na siyo ta bani Uku da hamsim na siyar miki,ina kuka haka ta siyar da jakar nan taci ribar Hamsim,Aayan yana driving yana dariya.
Malamin Hajja ya hado mata muggunan da za a sa min tare da Aayan a abinci,da sauran wasu iri iri na wajen Malamai shi yasa yanzu ta saka rigima wai Daddy ya fadawa Aayan a dawo damu ai muma jikokinta ne taga abinda tayi bai dace ba bata kyauta ba
Daddy yasan ba gaskiya bane amma yasan Allah na nan ba matsala ya Sanarwa Aayan.
Godiya gareku House of Hausa Noveld kun iya Sharhi.
Bayan yayi parking a cikin gidan fitowa mukayi tare da jidar kayan muna kaiwa muna dawowa har muka kwashe komai ya rufe motar take away na abinci da ya siya mana na karba ina ta masa godiya da addua ya wuce abinsa nima na shiga Bedroom dinmu, Bayan munci mun koshi wanka nayi na shirya cikin sabuwar Nighty dina iya cinya me siririn hannu peach color na fito fes ina kamshi Meent ce ta shigo Sis kije inji Ya Aayan amma fa yana compound jikin motarsa da alama fita zaiyi,Hijab nasa har kasa kamar zai ja kasa na fita lokacin tuni munyi sallar Isha,saman Motar na ganshi a zaune cikin kana nan kaya ba karamin kyau yayi ba,wani abu ya tsirga min na tsinci kaina cikin wani yanayi na shauki wanda bazai misaltu ba wani dadi yana ratsani, kallona yake cike da tsantsan nishadi kwance a fuskarsa zuciyarsa cike take da farin ciki wani Sanyi na ratsashi.
Ina murmushi na karasa tare da cewa au akace fita zakayi kuma naga ka zauna saman bayan mota,yana murmushi yace zance fa nazo kinyi sabon saurayi kuma kina wani cewa fita dariya nayi nace kaima dai baka rabo da tsokana a haka zubin mugaye gareka, am serious ni fa zance nazo dama gori kike min kece kullum kike zuwa zance,Dariya nayi nace to nan gaba idan zaka zo ka dinga bugo waya sabo da ai banyi kwalliyar zuwa wajen saurayi ba na fada kamar gaske, muryarsa naji yace duk fa cikin business ne ki daina tunanin da gaske ne kudi za a biya ki wannan fitowar ma da kikayi kin ci kudade masu yawa,dadi ya kamani nace an gama ko kalma daya ce duk kudi ne? Yace of course, murmushi nayi tare da gyara tsaiwata yana sama na matsa jikin kafafunsa, yace yan mata suna na Aayan duk da cewa baki tambaya ba,ban san lokacin dana fara dariya ba ni abin ma kunya ya bani amma na daure nace ai yanzu gashi ka