x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 55 - KASUWANCINA

  • 162001 words
  • 165000 words
  • Out of 176000 words

Category: Romance Story +18

Views 184

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
samo Kasa a dan karamin Kwano na dawo na tankade abata luwai na dan kwabata da ruwa ina dan ebowa da cokali ina shanyewa,a kitchen ya sameni tunaninsa wani abin nake Sha me dadi,tsoro ne ya kamashi ya kwace kwanon ya zubawa kasar ruwa ya wanke dan Plate din, mene haka dan Allah?karki kara sha ko bana gidan nan kashe min jaririn zakiyi da kasa,idan ta tsotse miki jini fa ko ta miki illa ko akwai kwayoyin cuta ke kika ci fa,Kuka nasa masa nace Ni ba a sona sai jariri tun bai zo duniya ba tunda haka zaka dinga nuna banbanci to indai ciki ne zubarwa zanyi,Wasa nake miki Baby haba ni na isa ai kinfi Jariri shin din Banza,ya isa ina ruwana dashi,sai lokacin to in dai ka kara nuna ya fini wlh sai nayi ta Shan kasa da kanwa ko nasha gayyen darbejiya daci yasa cikin ya zube idan shine kawai wani yazo sama ta kai a nuna ya fini,Aayan yace ni ai ban isa wani fiki ba,waye ma ya isa na daina sonsa tuni yaje yasha zamansa,Hannunsa na rike nace wayyo..yace Mene Allah jiya naji ana min Usha Usha a cikina,ka gani yanzu ma,dariya Aayan yayi yanda nake gwadawa da Hannu kamar Yar China,cikina na rike nace wash..wash..Allah na Yau Kungfu ne ake min idan kuwa jariri ne wannan to dan kasar China ne zan Haifo shi a nan kasar.
Aayan yace shine ma yasa kansa a gefen cikina yace kai jariri ka daina kuka kana wutsil wutsil bazan taba sonka kamar matata ba,nafi sonta itace gaba da kai,Dariyar jin dadi nayi na zauna tare da cewa woo...ba a sonsa,Aayan dariya yake sha abinda nakeyi na kuruciya.

Meenat ce ta bude idonta daga baccin wahala da takeyi While Ameer yake shakar na dadi abinsa,a hankali ta zare jikinta a nasa ta fada Toilet,wanka da duk abinda ya dace tayi ta fito sosai ta gasa jikinta,Sallah ta gabatar tare da azkhar sannan ta shirya sama sama ta canja New night Gown me dan sauki saukin tsaraici ta kwanta a gefensa again kwanciyar da tayi ne ta tashi Ameer,da sauri Meenat ta rufe idonta amma ya rigada ya ganta,yaga alamar tayi kokarin yin wanka ta shirya kanta Jarumace Meenat,shima toilet ya fada ya gama komai ya fito ya gabatar da Sallar asubah tare da azkhar daga shi sai boxers ya koma Bed din tare da shigar da Meenat jikinsa sosai yana kissing dinta a wuya da gashinta zuwa gashin kanta dake kamshi baccinta takeyi kawai abinta.

Bacci suka ci gaba da yi ba su suka tashi ba sai wurin 11am hakan ma shi ya takura sabo da bata ci,Ameer waya ya buga min lokacin zanyi shirin zuwa schl sabo da muna shirye shiryen fara Waec da Neco, Sister Mufee dan Allah do me a Favour Meenat Bata da lfy ne abinci muke so,Ok zan bawa Driver ya kawo muku,kitchen na kara shiga na dan musu masu sauki,Dama nayi farfesu sai kawai na soya Chips da kwai tare da ruwan tea na shirya komai sharp sharp na bawa Driver ya kai musu,Meenat ya matsawa dole sai ta tashi taci abinci, Da kansa ya kaita ta kuskure bakinta sannan ya zuba musu abinci a Bedroom din ya dinga ciyar da ita shima yana ci har suka koshi,duk abinda yakeyi Meenat taki bude idonta bare ta masa magana wai kunya takeji ita har suka gama cin abincin ya bata Mouthfreshner ta kuskure bakinta shima haka,zata koma ta kwanta ya riketa tare da cewa dan zauna kadan ba kyau ana gama cin abinci a kwanta,Kayan da suka bata ya maida kitchen ya gyara Bedroom din sannan ya hau Saman Bed din tare da cewa kwanta Sweetlove ya sata cikin jikinsa suka kwanta ya fara kokarin cire mata yar rigarta,da sauri ta bude idonta cike da muryar kuka tace shike nan tunda kashe ni kake son yi sai ka dauki raina,Murmushi yayi tare da cewa ba abinda zan miki nafi so kawai najiki a jikina ba kaya kiyi hakuri My Meenat,Kai kawai ta daga mishi yana lashe mata hawaye da harshensa,tana shesheka tace ka..ka..kira min Ammah na gaisheta dasu Sisters kwana biyu bamuyi waya ba,Jiya fa ne kawai bakuyi magana ba Babyna amma bari na kira Sis Mufee,Yana Dialing Number din Mufee Aayan ne ya dauka yace tana schl sai anjima zan dakko ta ya akayi? Ameer yace kai ya Aayan wayar ma Tata idan tana schl tana hannunka kamar wani P.A,idan ta dawo kace ta kira Meenat back,ok cewar Aayan ya datse kiran,Ameer kuma ya Kira Ma'eesha wacce yanzu ta dan saba da harkar Yarima da sukeyi tana jin dadi kadan,Suna murza juna Kiran Ameer ya shigo Amma Yarima yace baza a daga yanzu ba sai sun gama tukun zasu kira back,Ammah kadai aka samu a waya sukayi Hira ba tare da ta gane komai ba,suna gamawa Meenat ta makale a jikin Ameer tana masa magana kasa kasa Allah ka bani wahala Honey jiya ko tausayina baka jiba,Am so sorry My love Bazan kara ba kinji yana lallashinta tana shagwaba .

Alhmdllh Daddy ya yaje Dangin Ammah Sati daya aka daura auren Ammah da Daddy ko su Aayan basu sani ba Hajja kawai ya fadawa tana asibiti har yau ba a sallameta ba, ina fitowa daga class an tashi naga Ma'eesha tana daga min hannu ita ta tafi Yarima yazo daukanta,ina daga mata hannu kawai naji an daga ni sama nasan Aayan ne ina jin kamshinsa,ana kallonmu fa zaka Sa ace bani da kunya,thts y nake so ai mu koma Abuja dagani sai ke babu me Sa mana Ido jira nakeyi ku gama zana last Exam ta Neco,Murmushin dake kara min kyai nayi tare da rike Hannunsa nace Muje Mijina,Office dina zamuje ki jirani na gama sai mu wuce gida ko,amma fa kasan bani da wata lfy kasala,ga saurin jin yunwa kuma ina tashin zuciya kaga kuwa akwai Matsala kar nayi maka Amai a Office,ba damuwa muje haka gobe baku da schl asibiti zamu je kar Babyna ya girma ba a fara dura masa kwayoyi ba,biyu da Safe biyu da dare,dariya na farayi shima haka nace kamar kasan yaran yanzu duk yan kwaya ake haifowa,sabo da tun a ciki ake dura musu kwayoyi.
Muna ta hirarmu har ya bude min mota na shiga shima ya shige Driver tare da escort suka ja sai Office katafaren building.

Tun a hanya nace a tsaya a siya min Doya da kwai haka yasa aka siya min,ya kwanto dani jikinsa yana tambayata sai me kike so Babyna?Nace Coconut da Alkubus,Ina zan samo Wani Alkubus ni kiyi hakuri na fadawa Ammah tayi miki idan zamu tafi gida sai mu biya mu karbo,banyi musu ba nace masa to Allah ya kaimu yace Ameen Sweetyna, ina jikinsa muka karasa Office yana signing da Sauran ayyuka ni kuma ina saman Cinyarsa a zaune kamar yarinya karama motsi kadan idan nayi sai yace min ya akayi ina ta ciye ciye na hankali Kwance,Duk abinda nace ina son ci da Sauri yake Bada Umarni lallai a kawo min naci rashin kunyar da yake zubawa kuwa na caring sai dai idan baza ka kallemu ba ka tafi.

Yau kwana Uku da Angwancewar Ameer jinya yakeyi har yau Meenat taki ta daina lango kullum tace bata warke ba ta wani narke zatayi kuka,amma a fagen Romancing itace kan gaba, 9pm Meenat taci uwar kwalliya sanye take cikin English Gown iya rabin cinya light blue and White sai kamshi takeyi gashinta yasha gyaran gaske kamshi ke tashi kawai ta ko ina,palon Angonta Ameer ta nufa tana Tafiya cikin nutsuwa tare da jan Hankali yana Palonsa sai chat yakeyi a waya yana Jin kamshin ta da Sauri ya fita daga WhatsApp din ashe Meenat ta gane me yayi,cikin takunta na kasaita ta karaso inda yake zaune Saman 3seater kafin ta zauna ya jawota jikinsa saman cinyarsa ta zauna yana shafa mata wuyanta da kafadunta ta baya,cikin muryar da ba a san Meenat da ita ba tace Ashe da ka shirya nan ka dawo? Yeah Princess ya furta yana Jan zip din rigarta kasa baya har yayi Zipping dinsa, Bra ya balle mata tare da janye rigar ya jata kasa ta koma kasan cikinta,Dukiyar Fulaninta masu matukar kyau da sheki suka bayyana juyowa tayi gaba daya a jikinsa ta kwanta Saman kirjinsa tare da rungumeshi tana rufe ido wai Kunya,Na shanunta ya shiga wasa dasu tana masa shagwaba,a shagwabe tace Husband ya amsa da Naam cikin dishewar murya,nuna min Chat dinka na WhatsApp na gani,Murmushi yayi tare da cewa gaskiya sai dai kiyi hakuri bazan iya nuna miki ko Contact dina ba, Ni Din?tana kallonsa kamar zatayi kuka,yace to me zaki gani in ba neman rigima ba,ni...Ni...Allah sai ka nuna min,am sorry to say gaskiya bazan iya ba,Fushi tayi a fusace ta kwace jikinta tare da maida Bra da rigarta tana niyyar tashi ga Kwalla na shirin kwararo mata,Ba shiri ya fisgota ta fado jikinsa me laushi da kamshi nan take ya mika mata wayar gashi kalla kuma nima sai naga naki murmushi tayi kyawunta ya kara bayyana ta karba tana me dauke da murmushi a fuskarta ta fara duba Contact,tana tambayarsa kowa taga Number din mace,haka WhatsApp nasa ma sai da ta bincika tas taga babu mace da suke chat,farin ciki ta shiga yi mijinta baya kula wata,Shi kuwa ko duba nata baiyi ba don baya zargin Meenat da komai.da kanta ta ja Hannunsa zuwa Bedroom dinsa sabo da tasan tayi masa laifi wajen danne masa hakki yayi hakuri da ita har ta fara Jin kunyar Ameer din nata,Rigarsa armless ta zare masa a hankali itama sannan ta kashe Light duf duhu ya gauraye dakin sai karar ac da kamshi kawai ke tashi,Bai ma san ta cire kayan ta gaba daya ba sai jinta yayi a jikinsa ta rungumeshi sosai Albarkatun kirjinta suka sashi ya saki ajiyar zuciyar ba tare da ya shirya ba ya dauki Meenat zuwa saman Bed,a nutse cike da wayewa suke gudanar da harkarsu har ya samu abinda yake so ba tare da tasha wahala ba,Gaskiya Ameer karshe ne hakan Meenat ke ayyanawa a ranta tana Jin dadi,bangaren Ameer ma hakan yake ji a ransa tana manne cikin jikinsa suna hira Sama sama har sukayi bacci abinsu.

Kwanci tashi yau Sati Uku kenan da auren Su Ma'eesha Sameera Yar daba taji sauki Sosai ta warke inda ta fitar da Alhajinta me kudi zatayi aure itama ta saduda da al'amarin duniya,an sallami Hajja daga Hospital Ta samu Lfy amma matan su Abbi basu canja ba,su Khaleel ne ma watarana suke dan tarewa Hajja sabo da su Abbi sun koma abin tausayi sun koma rakumi da Akala,Kullum Hajja kuka take sharba musamman idan taga danta Abbi Mustapha yana wanke wanke da shara yayi duhu ya rame,yau kamar kullum matar Abbi Sani ta sashi wankin kayanta sai zufa yake hadawa,Hajja ta fita tana dingisa kafarta da bata gama warkewa ba,tana fada kan ya daina wankin haka ya isa,suna haka sai ga matar ta fito babu bata lokaci ta shiga Zagin Hajja Munafuka,Karuwa sannan ta ture Hajja ta fadi rim again akan kafar data karye nan take kafa ta kara samun matsala dama bata gama warkewa ba aiki ya lalace ya dawo baya,Hajja yau tayi kukan da bata taba yi ba,ba shiri ta fara Allah na tuba ka yafeni,Na jawowa kaina,na cuci kaina da yarana na ruguza farin cikina na tarwatsa kan yarana,Hajja tana ta tuba tana tona asirinta,Khaleel da Mujaheed ne suka hango me ke faruwa da Sauri suka karasa kan Hajja suka sata a mota sai asibiti tare da sanarwa Daddy,Aayan da Ameer abinda ke faruwa,Ameer bakin ciki ya kamashi Key din mota ya dauka kawai Meenat lokacin tana kitchen ya leka da Sauri yace na fita ana kira na Babyna yanzu zan dawo har ya tafi ya dawo da Sauri ya rungume Meenat tare da kissing dinta a lips yace take care of ur self for me Wifedina,same too u Darling banda tukin ganganci kaji mijina,ya fita yana daga mata hannu ta kwalla da karfi am gonna Miss u Sweetheart kar ka bari a kalle min kai,shima da dan karfi yace Already started Missing u SweetMeenat ya fice dauke da murmushi ya manta ma da fushin da yakeyi Meenat ma murmushi take bazawa kawai.

Bai zarce ko ina ba sai gida wajen Su Abbi,yana zuwa a fusace Ameer bai kula kowa ba ya fara shigewa Bedroom din Abbi Mustapha Baban Ameer kenan ya fara watso kayan matar anci sa'a Abbi yana bayi yana wanka,kasan Bed din ya dage katifar sai ga Wata yar tukunya dauke da tarkacen tsafi a ciki tare da ruwan rubutu,Ameer bai jira ba ya fito ya jefota ta saman Bene tukunyar tsafi ta ragargaje,haka ya fita ya shige dakin Matar Abbi tana cikin gyara kaya taga Ameer ya fado da zureriyar Sandarsa tunaninta dukanta zaiyi ko Ya haukace sai ta fita da gudun tsiya,Abbi na ganin haka ya rufa mata baya dama sai abinda tace Kan tace ne kafin tace ya aikata,nan Ameer ya kulle dakin da key ya shiga bincike a dakin ya dinga samo guru,laya,ruwan rubutu,ya duba kasan bed din ba komai cikin pillow ya duba tare da Sa wuka ya tsarge pillow din ta ko ina ya fito da soson da suke ciki sai ga layu iri iri a Cikin pillow an hada dashi an dinke pillow tsab baza ka taba ganewa ba,yanzu mata abinda sukeyi kenan za a kai Amarya kafin a kaita sai an yanka pillow da razor a tura kulunboto sannan a mayar a dinke yanda ba Uban wanda zai gani sai kaga pillow normal ashe da tarkacen tsafi a ciki,miji yana ta kwanciya a kai,wasu har katifa ake yankawa asa sai a Sa zare da allura a dinke ba me ganewa Allah ka shirya mu.

Ameer yana fitowa ya fada dakin Abbin Yara Duk ya fita a hayyacinsa matar ta sashi sai ya goyata ya dinga zaga Bedroom da ita,gata wata me kiba katuwar gaske suna ganin Ameer da shegiyar wuka suka saki ihu ta fisgi Hannun mijinta suka gudu nan ma haka ya dinga kwakwulo kayan tsafi,sabo da Ameer duk irin wannan harkar ta malamai ya santa tunda suna zuwa da Hajja kafin Allah ya shiryeshi sannan Hajja tana sasu suna yin irin wannan abun wajen iyayensu mata,haka ma da Matar Daddy da kuma Matan Aayan duk irin wannan yasan su shi yasa yake da saurin gane irin wannan harkar,a leda ya kwaso komai ya fito dasu yabi ta baya duk ya warware layun sannan ya yayyaga komai da almakashi into pieces ya konesu tas,Sai ga su Abbi nan take sun dawo hayyacinsu,Hajja kawai suke nema da yaransu,Matar Abbi Mustapha kuwa taci duka hannun Abbi kamar jaka wai ta rabashi da Uwarsa,a wajen duk suka rubuta musu saki dai dai na musulunci Ameer da kansa yasa Securities sukayi waje dasu suna kuka tare da nadamar halayensu.

Da su Abbi tare da Sauran Yara suka dunguma zuwa asibiti wurin Hajja da take fadawa su Khaleel ku taimakawa iyayenku da addua su dawo cikin hankalinsu su dawo da iyayenku mata yan albarka masu biyayya,ni na jawo da nace sai sun sake aure,banyi adalci ba ko a baro sai an turani naje har gida na basu hakuri da kaina zanyi bikonsu ko da kafar katako ce,Mufeeda tare da kannenta suma zan nemi gafararsu,Daddy ne ya shigo a birkice nan Hajja ta damki hannunsa tana bashi hakuri tana kuka ka yafe min ni na jawo nice....Hajja na yafe tuntuni ni dama ban rikeki ba kuma aike Mahaifiya ta ce ba komai ya wuce ki bari kiji sauki ko na fitar dake kasar waje?Hajja tana goge Hawaye tana Allah ya maka albarka Ka yafe min dana,na maka abubuwa suna haka sai ga Aayan da Mufee duk ta kara wani fari tayi kiba da kyau Sabo da cikin dake jikinta,Hajja ta shiga bawa Aayan Hakuri da Mufee,Aayan yace shi ya hakura ta ma daina bata bakinta,Su Abbi su Ukun tare da Ameer suka shugo suma nanfa Hajja bata boye ba tace da kanta ta lalata zumuncin yaranta,To Allah yasa su Abbi sunyi Nadama nan suka shiga Yiwa Hajja fada da nasiha sannan sukace duk itace ta cucesu Amma tun da Allah ya ganar dasu sun yafe suma a yafe musu,a asibitin aka shiga yafewa juna anyi wa'azi tare da Nasiha wa juna an tunatar sosai dama wasu Iyayen da kansu suke bata zumuncin yaransu suna raba kan yaransu,a karshe Hajja tace da kanta zata je bikon iyayen su Ameer babu wanda ya kai su Abbi Murna za a dawo musu da matayensu yan kirki

Su Abbi sai gafarar Daddy suke ta faman roka sai lokacin ya fada musu ya auri Ammah kuma a satin nan zata tare a sabon gidansa daya tsantsara na fitar hankali,sun tayashi murna sosai har Abbi Mustapha na tsokanarsa an samu dangin kyau,Hajja kuwa Allura akayi mata anci sa'a ashe bata kara karyewa ba ta dan bugu dai a wajen Amma Dorin bai lalace ba,Aayan sai murna yakeyi shi da Mufee ashe Daddy ya auri Ammah basu sani ba,nan Mufeeda ta fita waje ta kira Meenat da Ma'eesha ta sanar musu Ammah ta auri Daddy ta labarta musu yanda Daddy ya basu labarin har yanda aka daura aure,Sunyi farin ciki Ammah ta samu me kula da ita,Meenat tace Sis kicewa Darling yataho gida haka na gaji da jiransa,Dariya Mufeeda tayi tace idan yazo me zai miki sarkin jaraba Bazan fada masa ba,dan Allah Mufeen Ammah ki fadawa Ameer dina na kira wayarsa a kashe,tana cikin haka sai ga Ameer ya fito, na mika masa waya nace ga Meenat tana magana,da Sauri ya karbi wayar yana murmushi yace Hello...tuba nake ranki ya dade kaina bisa wuya gani nan yanzu ki bani 15mnt Insha'allah ,Meenat sai Kukan shagwaba take masa ita yayi Sauri ya barta ita kadai.

Documents from AIHAUSANOVELS

Always visit Aihausanovels.com.ng For downloading free hausa novels

Like our Facebook page Fb.me/aihausanovels


End Ads