Raugatul
aguwanu susa a kunnensa ba tare da yagane
cewa akwai baki hallitu a cikin kunnen nasaba?
Page 127 zidane kd: Sa adda boka radiyan yaji
wanna tambaya sai ya bushe da dariya lokaci
guda kuma ya hade rai ya ce yake wannan yar
saki kiyi sani cewa hakika aiki sai mai shi:
Dangane da tambayarki ta farko am . Sarta
itace fadawan dan uwanki suna son su gaje
karagar mulkinsa idan har yazamana cewa bai
sami nasarar yaki ba a bakin tekun bahar sufiya
domin su ke suga halin da ake cikin a sansanin
yaki ne boka sadusa ya nemi hadin kan aljani
Raugatul aguwanu tunda shi kadaine xai iya
zuwa can din: dangane da tambayarki ta biyu
kuwa itace sa adda na shigo gidan nan ba tare
da aljani barzaru ya ganni ba taha kema zaki
fita : sai tambayarki ta uku wacce itace ta
karshe amsarta itace duk jikin aljani Raugatul
aguwanu babu inda yafi girma da nauyi sama
154
TASKARNOVELS.COM.NG
da kunnunwansa guda biyu don haka idan
muka shiga cikinsu tamkar a dauki yar karamar
tsakuwa ne a jefa cikin RIJIYA GABA DUBU:
bazai ji sa adda zamu shigaba kuma dazarar
mun fara yimasa susa zai sami cikakkiyar
nutsuwa da zai yi azabbaben gudu a sararin
samaniya har mu isa bakin kogin bahr sufiya
cikin sa o i kadan: Yanzu dai kin shirya zamu
tafi cikin murna Gimbiya Hursiya tace aini bani
da wani shiri sai naka: page 128: kafin ta gaa
rufe bakinta tuni boka radiya yayi nuni da
hannunsa na hagu gareta: lokacin guda shi da
ita suka rikide suka zama wannan jan fure guda
daya kawai sau kuyanga lazimat ta sunkuya ta
dauki wannan fure ta dorashi akan farantin ta
fita daga cikin turakar gimbiya Hursiya rike da
faranti: Tana fitawa sai taga aljani barzaru
tsullu agabanta fuskarsa a murtuke babu
alamar annuri nan take ya daka mata tsaya ta
firgita ainun har ta saki fitsari a tsaye bata sani
ba: hunnunta yakama karkawa farantin dake
hannunta ya rinka jujjuyawa kamar zata
sakeshi ya fadi
155
TASKARNOVELS.COM.NG
aljani barzaru yadubi wannan jan fure da ke
hannunta sannan ya dubeta cikin alamun
rashin yarda yace ina ma anar fitowa da
wannan jan fure yanzu alhalin dazu nan kika
shiga dashi? Kuyanga lazimat ta budi baki
muryata na rawa tace ai gimbiya ce tace
batason wannan kalar sai dai mai dashi na
canjo da irin wanda aka saba kawo mata: page
129: barzaru ya ce tome yasa kuke gudanar da
wannan al amari yanzu a cikin wannan dare
maimakon ku zarta dashi da safe? Lazimat tace
ai ka sani cewa yanzu duk abinda gimbiya
takeso shi takeyi tunda sarki baya nan: Duk
umarnin da ta bayar shi akebi a gidannan :
kodajin haka sai alajni barzaru ya gyada kai
yace Tabbas kiyi gaskiya amma dai ni yanzu
ban zan amince da keba facce mun koma tare
dake cikin turakar gimbiya na ganta da
idanuna: koda jin wannan batu sai hankalin
kiuyanga lazimat ya dugunzuma ainun fiye da
ko yaushe alamomin tsoro da rashin gaskiya
suka bayyana kururu akan fuskarta: koda ganin
haka sai aljani barzaru ya tukuda keyarta suka
koma cikin turakar gimbiya suka wuce kai tsaye
izuwa cikin dakin barcinta: zidane kd
156
TASKARNOVELS.COM.NG
WHATSAPP 09064179602 koda suka tura
kofar sai suka ui arba da gimbiya hursiya
kwance akan gadonta tana ta shara barci: al
amarin da yai matukar daurewa aljani barzaru
kai kenan yacika da tsananin mamaki: ita kuwa
kuyanga lazimat sai ta sami nutsuwa takama
murmushi; Nan take suka juyo da baya kafin su
fice daga cikin dakin tuni gimbiya hursiya
wacce ke kwance a kan gado tanaBarci ta
rikide ta zama ha yaki yashige cikin wannan jan
fure dake hannun lazimat ba tare da aljani
barzaru ya lura ba: PAGE 130 ZIDANE KD:
WANNAN SHINE ABINDA YAFARU A BIRNIN
SARKI DUJALU BAYAN GIMBIYA HURSIYA TA
SAMI HANYAR DA ZATA SAKE KOMAWA CAN
SANSANIN YAKI DOMIN TA SADUWA DA DAN
UWANTA SARKI DUJALU : * * * ACAN
sansanin yaki kuwa ba a sake fitowa filin daga
ba sai bayan cikar kwanaki uku: Da sassafe
kowane bangare suka fito alaui sahu sahu ana
fuskantar huna aka baiwa tekun bahar sufiya
baya
157
TASKARNOVELS.COM.NG
: NIMA SULEIMAN ZIDANE SAI NABAWA TEKUN
BAHAR SUFIYA BAYA: DOMIN SAMUN
LITTAFAN YAKI NA SOYAYYA E:BOOK KAI HAR
DAMA AUDIO MP3 ZAKA IYA MANA MAGANA TA
WATSAPP TA WANNAN NUMBER KAMAN HAKA
09064179602: TURAMAKA KUMA MUSAKA A
GROUP DINMU NA WHATSAPP: NAKU HAR
KULLU SULEIMAN ZIDANE KD NAKE CEWA
ALLAH YANUNA MANA GOBE LAPIYA
MAZAN JIYA 4 Littafe Na Hudu Part 23 Na
abdul aziz Sani: Typing: Suleiman Zidane Kd:
: Da sassafe kowane bangare suka fito alaui
sahu sahu ana fuskantar huna aka baiwa tekun
bahar sufiya baya
: wannan karon sai gashi su magaba daya
dakarun aljanu ma sun sauko kasa bisa turba
fuskanci junansu: Rundunar sarki maharaz na
158
TASKARNOVELS.COM.NG
kallon gabas su kuma rudunar sarki dujalu sun
bawa yamma baya kowa sai muzurai yake:
Gurnani da hucin dakarun aljanu kadai ya isa ya
firgita mutu ya tsure da gudawa bare kuma idan
yaga tsananin yawansu da kwarjininsu:
Abangare bil adama kuwa dakarun kowane
bangaren sun yi sabuwar shiga Yaki fiye da
wadda suka yi a karon farko da karu na biyu a
Yakin kuma kowacce runduna ta fito ne a
fusace da nufin ayi ta ta kare a yau wadanfa ke
da sa a su sami nasara:Page: 131 Batare da
shakkar komai ba Jarumi Inmal ya fuskacin
wani babban jarumi mayaki na sarki dujalu
wanda yafi kowa kokari a wancan karo na biyu
da aka fafata: Sarki ya dubi inmal a wulakance
cikin raini sannan ya dubi sarki Maharaz ya
bushe da mahaukaciyar dariya yace yau zan
kashe da a gaban ubansa: Sannan nayiwa
uban mugun kisan gilla irin wanda ba a taba
yiwa wani mahaluki ba: Kafin sarki dujalu ya
gama rufe bakinsa tuni jarumi inmal yatari
numfashinsa cikin daga murya ya daka masa
tsawa yace kai tsohon azzalumi karyarka ta sha
karya: Na rantse da kaunar da nake yiwa
mahaifina marigayi yau sai na kasheka da
159
TASKARNOVELS.COM.NG
Hannuna kamar yadda ka kashe min mahaifina
domin na rushe mugun nufinka na son ka
mallaki kayan yakin MAZAN JIYA domin ka
cigaba da mulki zalunci a doron kasa: koda jin
haka sai dujalu ya sake tuntsurewa da dariyar
mugunta a karo nabiyu sannan yace ai shi
kenan inda babu kasa anan ake gardamar
kokawa kuma ga filo ga mai doki sai akasa
tseren mugani: Yau fa ba gudu ba ja da baya:
Ba za a busa kahon tsaida yaki ba har sai dole
bangare guda ya sami nasarar murkushe daya
bangare a yau babu batun mutum da mutu ko
aljani da aljan babu batun da tsafi ko babu
tsafi: Duk abin mutu yake takama dashi to yayi
amfani da shi tunda yau ne karo na karshe:
Page 132 Suleiman zidane kd: whatsapp
09064179602: Dajin wannan wajabi sai sarki
maharaz ya yi murmushi murna yace abin
nema yasamu tunda matar falke ta haifi jaki:
Tunda ka zaba hakan nima na amince muje
zuwa mahaukaci ya hau kura: Nan take wani
Shirgegen aljani mai siffan batoyi daga
bangaren dakarun Sarki Dujalu ya daga wani
narkeken kaho ya busa karar bushin kahon ta
cika dajin gaba daya amsa kuwa har ruwan
160
TASKARNOVELS.COM.NG
tekun yakaa tamba tambal kamar zai yi
ambaliya ya cinye duk abinda ke wajen:; KAI
HATTA NI ZIDANE SAI DA NA TOSHEN
KUNNUWA NA SABDA TSABAGEN KARAR DA
YA ADDA BINI
koda mayaka suka ji sautin wannan kaho sai
aka zabura aka ruga dagu daga kowawane
bangare
Wahoho ! Karar sawayen Mutane da aljanu
cika kunnuwa sbda dudufniya kuma ya
haddasa karamar girgizar kasa: Ihun mazaje
kuwa da karajin aljanu ya haifar da rudewar
duk wata hallita dake dajin gaba daya rudewar
duk wata hallitar dake dajin gaba daya har da
wacce take cikin karkashin tekun bahar sufiya:
Page 133 lokacin da rundunoni biyu suka
gwamutse kuwa sai aka ruguntsume da
azababben yaki na gaban tashin hankali; domin
nan take kasuwar diban rayuka ta kama ci: sai
dai kaga aljani ya daga kafa ya talitse bil adama
hamsin a lokacin guda: WANNAN WANA KALAR
161
TASKARNOVELS.COM.NG
BALA KI NE ZIDANE KD: Koda sarki maharaz da
sarki dujalu suka ga anfara asarar rayunka bil
ada;a daga kowane bangare sai kowannensu ya
fara amfani da karfin sihirinsa na kone aljanun
abokan gaba: Waiyo! Nan fa gaba dayan
aljanun da ke sansanin suka raina
jarumtakarsu gami da karfin sihirinsu domin
duk ya tashi a banza sai dai kaga aljani ya kama
da wuta yana ihu yana gudu domin ya fada cikin
tekun bahar sufiya amma kafin ya kai bakin
tekun tuni ya kone kurmus Hatta kasusuwan
jakinsa sai sun ruburbushe sun zama toka:
Babu abinda zai baiwa mutum tausayi face
yanayin mutuwar da suke yi domin da farko dai
sai sun fara kumbura sun yi suntum Ya yin da
wutar ta fara cin jikinsu sannan sai kaga
idanunwansu suna bullutsowa su fado kasa
daga nan kua sai cikin ya fashe kayan cikinsu
su zubo: da sun fara kokarin gudu kuwa sai
kaga sassan jikinsu na guntulewa yana faduwa
kasa a haka har sai sun narke gaba dayan su
zama toka
162
TASKARNOVELS.COM.NG
Page 134 zidane kd: Sai da aka shafe sa a
bakwai ana wannan bakin gumurzu suma
mutane suna nasu yakin: kuma kowanen
bangare suna asarar rayuka: Duk inda jarumi
inmal ya kutsa a cikin rudunar sarki dujalu ta bil
adama sai dai kaga mazaje na zubewa kasa
ramkar ana sassabe a gona sbda inmal ya fito
da wanannan yaki ne a fusace da takobi biyu
yake amfani don haka nan da nan jikinsa gaba
daya ya rune da jini: Koda sa a bakwai ta cika
sai ya zamana cewa gaba dayan dakarun
aljanun sun kare babu ko guda daya a wajen:
Don haka sai aka daiana jin karajinsu: hakan
cetasa kowanne bangare suka janye aka ja da
baya akayi cirko cirko ana haki da kallon juna: A
sannan ne kowane bangare ya gano irin
mummunar barnar da akayi masa: Su kansu
dakarun bil adama na kowane banagare an
kashe kimanin kaso saba in daga ciki dari
Tarin gawarwakin da ke zube a kasa kuwa
wasu kan wasu har suna tisra a sama gar ya
ninka na wancan karon: koda sarki dujalu ya
dubi gaba day gawarwakin dake zube a kasa
163
TASKARNOVELS.COM.NG
kuwa wasu kan wasu har suna tsira a sama har
ya ninka na wancan karo; koda sarki dujalu ya
dubi gaba dayan gawarwakin da ke kwance a
kas kuma ya dubi ragowar dakarun bil adaman
da suka rage a tsaye ya fahimce cewar RAGAS
ake yi a wannan yaki: sai rabsa ya baci
zuciyarsa taka ma tafarfasa kaan zata kone:
Page 135: zidane kd: kawai sai ya takarkare ya
kwarara uban ihu sannan ya wangame bakinsa
wata irin gagarumar guguwa ta rinka fitowa
daga cikin bakinsa ta durfafo inda abkan gaba
suke zata hallakasu gaba daya: koda sarki
maharaz yaga wannan guguwa ta durfafo
rundunarsa sai shia ya wangame bakinsa irin
wannan guguwa ta rinka fita da gudu taje ta
tare guguwar dujalu: Ai kuwa suna haduwa sai
suka haifar da tsawa tartsatsin wuta gai da
walkiDa kumma girgizar kasa: tsawon yan
dakiku ana cikin wannan masifa gami da tashin
hankalo amma an rasa wanda zai iya cutar da
wani: Al amarin daya fusata sarki maharaz da
sarki dujalu kenan suka ci gaba da jarraba
sirrinkan tsafin su kenan har sai da kowannen
yayi amfani da sihiri guda dari da tara da casa
in da tara; a Lokacin be duk su biyun suka jigata
164
TASKARNOVELS.COM.NG
ainun kuma suka jike sharkaf da gumi suka
zube kasa a cikin matukar galabaice suna
numfashi sama sama: kamar ransu zai fita: A
wannan lokaci jama ar kowannensu sun yi cirko
cirko suna kallon abin al ajabi: baan sarki
dujalu da sark maharaz sun dawo cikin
hayyacinsu sai suka mike tsaye a tare kamar
hadin baki suka tako kafafuwansu suka durfafi
juna: Page 137 Cikin Alamun tsoro inmal ya
yunkura zai kaiwa sarki maharaz dauki don
gudun kada dujalu ya cutar da shi kawai yaji
anrukoshi ta baya yana waigawa ya ga ashe
Gimbiya mulaifa ce kawai sai ta dubeshi tace
kwantar da hankalinka ya masoyina sarki
dujalu ba zai iya cutar da mahaifina ba sbda
karfinsu yazo daya kuma kasani cewa babu
yaudara ko ha inci a wannan yaki bisa
alkawarin da aka dauka da farko sai gaskiya da
gaskiya: kai ga ke nan ko yar kashi zasu gwada
kafin ya cutar da shi zamu iya kai masa dauki a
sake ruguntsumewa da yakin gaba daya: kuma
ni ina ganin cewa tunda yanzu sarki dujalu
yasami nakasa hannu daya gareshi sarki zai iya
saun galaba akansa: inmal ya girguza kansa
yace bahaka bane duk yadda kike zato sarki
165
TASKARNOVELS.COM.NG
dujalu ya wucce nan wannan rashin hannun
dayan da yayi ba zai rage masa komai ba face a
yakara masa tsananin kafin zuciya da taurin
domin ya gaya dauki fansa: Ni yanzu kawai
abinda nake tsoro shi ne rashin sanin mutane
hudun da aka ce sune kadai zasu rayu a
wannan Yaki; ni kaina bana sa kaina a cikin
wadanda zasu tsiran: Page 137 koda jin haka
sai mulaifa ta girgiza ka tace idan har kayi imani
da cewa akawi wani addini wanda yafi dukkan
addininmu gaskiya to bai kamata yanzu karinka
amfani da abinda tsafinmu ko tsafin sarki
dujalu ya fadi ba: Ka yi sani cewa tun da ka bani
labarin ma abota addinin MUSULUNCI sai
tunanina ya sauya akan komai kuma naji cewar
na gamsu da addini don haka kaia yanzu ina
sonka sauya tunaninka daga kan komai ya
koma ya izuwa ga yarda da wannan sabon
addini na Musulunci: Sa adda jarumi inmal yaji
wannan batu sai yayi ajiyar zuciyar sannan yace
hakika kin yi Gaskiya ya masoyiyyata tabbas
yanzu bani da tabbacin abin da zai faru a
karshen wannan yaki: Yanzu dai bari muzuba
ido muga abinda zai faru a tsakanin manya
Giwayen biyu: Gama fadin hakan ke da wuya
166
TASKARNOVELS.COM.NG
sarki maharaz da sarki dujalu suka hada
yazamana cewa tazarar da ke tsakaninsu bata
wucce ta ku uku ba: sarki dujalu ya dubi
maharaz ya kyalkyale da dariya ai kuwa shima
sarki maharaz ya bushe da dariyar suka zama
kamar wadanda suka sami tabin hankali:
lokacin guda kuma suka tsuke bakunansu koda
ya murtuke fuska sannan dujalu ya dubeshi
yace Hakika nayi maka jinjina yakai abkin gaba:
domin haka akeson namijin kwarai ya zamo mai
taurin rai da rashin Karayar zuciya: gashi dai
fiye da rabin dakarunmu na yaki sun shude
amma baka sare ba kuma gashi na kashe
babban amininka abokinka kuma masoyinka
na kwaria wanda ya kasance dirka birninka
amma ba ka razana ba: to fa ka sani cewa
yanzy ne zan a rufe babin wannan yaki tunda ni
da kai duk mun yi amfani da karfin sihirinmu
har guda daru tara da casa in da tara saura
guda dai dai yarage mana kuma kasani idan
mukayi amfani da cikon na dubun dayan mu
bai sami nasara ba shi ne har abada tsafinmu
ya daina tasiri
ANAN ZANDAKATA SAI KUMA GOBE IN ALLAH
YAKAIMU :SULEIMAN ZIDANE KD: DOMIN
167
TASKARNOVELS.COM.NG
SAMUN LITTAFAN YAKI NA SOYAYYA E:BOOK
KAI HAR DAMA AUDIO MP3 ZAKA IYA MANA
MAGANA TA WATSAPP TA WANNAN NUMBER
KAMAN HAKA 09064179602: TURAMAKA KUMA
MUSAKA A GROUP DINMU NA WHATSAPP:
NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD NAKE
CEWA ALLAH YANUNA MANA GOBE LAPIYA
Pls kuringa comment inbakwayi zan dana post
gaskiya nafara gajiya MAZAN JIYA 4 Littafe Na
Hudu Part 24 Na abdul aziz Sani: Typing:
Suleiman Zidane Kd:
: sihirinmu har guda daru tara da casa in da tara
saura guda dai dai yarage mana kuma kasani
idan mukayi amfani da cikon na dubun dayan
mu bai sami nasara ba shi ne har abada
tsafinmu ya daina tasiri
Sa adda sarki maharaz yaji wannan batu sai ya
bushe dariya al amarin da yai matukar baiwa
sarki dujalu mamaki kenan: Maharaz ya dubi
dujalu a fusace yace ai ni ban ga amfanin
sihirin tsafi ba a wajenmu yanzu tunda gashi
yanzu dayanu bai cinye wannan Yaki ba sbd
168
TASKARNOVELS.COM.NG
haka in ka shirya ga cikon sihirin tsafi nan na
dubu gareka: Kafin sarki dujalu ya budi baki
yace wani abu tuni sarki maharaz yayi nuni da
Hannunsa izuwa kan dujalu: Nan take wata irin
farar wuta ta tafi izuwa kansa zata koneshi:
bisa dole ba don a son ransa ba yana kuka da
ihu gami da takaici sarki dujalu ya tare wannan
farar wuta da nasa tafin hannun sai gashi
shima tasa farar wuta ta taho da gudu ta tari ta
Sarki maharaz: Wutar biyu na haduwa sai suka
yi bindiga tamkar dutsen wuta ne ya fashe har
sai da dajin gaba daya ya yi girgiza: Sarki dujalu
da Sarki maharaz kuwa sai gani aka yi sun
sulale kasa sumammu: A guje kowane bangare
suka je suka dauko sarkinsu Sai da aka
yayyafawa su sarki maharaz ruwa sannan suka
farfado: Koda kowannensu ya bude idanu sai
suka mike tsaye zumbur a fusace: Nan take
kowannensu ya zare takobinsa ya daga ta
sama: Page 139: cikin hadin baki kowanensy ta
kwarara uban ihu yana mai ba da umarnin a
afkawa abkan gaba: Nan take kuwa kowacce
runduna ta zare makamanta aka ruga da
azababben gudu cikin mugun nufi ana ihu da
kururuwa: Ana haduwa a tsakiya sai aka
169
TASKARNOVELS.COM.NG
gwamutse kuma aka ruguntume da masifaffen
yaki: karar karafa ta cika dodon kunne aka
shiga gididdibar sassan jiki jii ya rinka fallatsi da
fauntsama asama yana yiwa mutane da kasa
ado: Ihun mazaje ya yawaita bisa sa kuwa sai
sarki dujalu da inmal suka yi karo da juna: Sarki
maharaz da babban sadaukin nan na dakarun
dujalu ma suka yi karo; NIKUMA ZIDANE SAI
NAYI KARO DA WADANDA BASU SAN YI MANA
COMMMENT: PAGE 139 Nan fa aka kacame da
azababben yaki ya zamana cewa jaruman hudu
suna kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin
zafin nama juriya da bajinta : CAIKO HAKIKA
MASU KARIN MAGANA SUYI GASKIYA DA SUKA
CE TASHIN HANKALI BA A SAMASA RANA
KUMA WANDA BAI SAN YAKI BA SHI NE YAKE
CEWA ALLAH YA KAWOSHI DOMIN MASIFARSA
TA WACCE TUNANIN MAI TUNANI: IN BA YAKI
BA MENENE YAKE KAWO FATARA DA TALAUCI
FARAT DAYA? YAKI NE YAKE HADDASA YUNWA
DA KISHIRWA KUMA SHI NE YAKE HADDASA
CUTUTTAKA MARASA ADADI: YAKI NE YAKE
KONE ALBARKATUN KASA KUMA YA
GURBATAR DA RUWAN SHA: Kai jama;a wanan
rana ita kanta masifa sai da tasan cewa ta
170
TASKARNOVELS.COM.NG
jangwalo masifa domin sai da maza suka raina
kansu domin sun san cewa suna karo da maza
yan uwansu: anfara wannan yaki Gumurzu
tsakanin sarki dujalu da jarumi inmal duk su
biyun suka gano cewa shayi ruwa ne ba abinci
mai nauyi ba domin karfin yazo daya duk da
cewa kuwa Sarki dujalu da hannun daya yake
yakin amma sai gashi yazamewa inmal
alakakai: Shi dai sarki dujalu yana amfani da
kwarewarsa gami da sanin makama kuma da
tsohon kashi: Page 141 zidane kd: Shi kuwa
inmal yana amfani ne da tsananin juriyarsa da
nacinsa inbadon hakan ba datuni ssarki dujalu
ya gama da shi
Gashi dai karfin dantsensu yazo daua gami da
zafin namansu domin kowanensu yana iya kare
harin kowa kuma yamai da martani to amma
dai kowanensu hankalinsa a tashe yake, domin
sun san cewa idan aka jima anan wannan
gumurzu a haaka komai zai iya faruwa: Irin
wannan matsala da Sarki dujalu da inmal suka
fuskanta ce ta sami sarki maharaz da sadauki
Himalu na bangare sarki dujalu, don haka
171
TASKARNOVELS.COM.NG
tsanani yakai tsanani, tura takai tura kowa ya
kuntata mafita kawai ake nema ta kowanen
hali. WANNAN SHINE ABINDA YAFARU A BAKIN
TEKUN BAHAR SUFIYA A LOKACIN DA YAKIN
KARSHE YA KACAME TSAKANIN RUDUNAR
SARKI DUJALU DA RUNDUNAR SARKI
MAHARAZ, DUK SABODA KAYAN YAKIN MAZAN
JIYA WADANDA SUKE KARKASHIN KOGIN
BAHAR SUFIYA KUMA BABU WANDA YA SAN A
INDA KAYAN YAKIN SUKE FACE WADANSU
MUGAYEN AZZALUMAN ALJANU MASU
TSANANIN KARFIN DANTSE MAZAUNA
KARKASHIN TEKUN WA DANDA SUNE MASU
GADINSU. ADADIN ALJANUN YA NINKA
ADADIN DAKARUN DA SUKA YI YAKIN A BAKIN
TEKUN SAU ARBAlN, DON HAKA SUN ZUBA
IDO SUGA WANNAN ZAI IYA SHIGOWA CIKIN
KARKASHIN TEKUN YA HALLAKASU GABA
DAYANSU YA IYA DAUKAR TAKOBIN SAIFUL
LUJARA: Page 141 zidane kd: page 142 ANAN
ZANDAKATA SAIKUMA IN ALLAH YA NUNA
MANA GOBE KUYI HKR BAYAWA YAU DAN
ALLAH COMMENT
172
TASKARNOVELS.COM.NG
: DOMIN SAMUN LITTAFAN YAKI NA SOYAYYA
E:BOOK KAI HAR DAMA AUDIO MP3 ZAKA IYA
MANA MAGANA TA WATSAPP TA WANNAN
NUMBER KAMAN HAKA 09064179602:
TURAMAKA KUMA MUSAKA A GROUP DINMU
NA WHATSAPP: NAKU HAR KULLU SULEIMAN
ZIDANE KD NAKE CEWA ALLAH YANUNA MANA
GOBE LAPIYA
MAzAN JIYa 4 Littafe na hudu Part
25 Typing
Suleiman zidane kd: whatsapp 09064179602:
DON HAKA SUN ZUBA IDO SUGA WANNAN
ZAI IYA SHIGOWA CIKIN KARKASHIN TEKUN YA
HALLAKASU GABA DAYANSU YA IYA DAUKAR
TAKOBIN SAIFUL