x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 17 - MAZAN JIYA 4

  • 48001 words
  • 51000 words
  • Out of 68055 words

Category: Adventure Stories

Views 191

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
baya jin sara d suka amman
yana fahimci yana jin bugu sai ya fara yi masa
lugudun naushi a fuska, nan da nan ya hada
masa jini da majina sai ga idanun Dujalu sun
kunbura sunyi suntum har ma ya fara gani dishidishi. Kaico! Hakika tsananin wuya da wahala
ita kw sa yaro ya gudu da kafarsa, ganin cewa
zai iya rasa ranshi ne yasa sarki Dujalu ya juya
baya da gudu ya taso izuwa saman tekun yana
haki kamar ransa zai fita, a sannan ne yayi arba
da aljani Darzuba tare da jarumi Hasnalu suna
kafsa mummunan yaki a karo na biyu. A
wannan karon kowannensu yana iya kare harin
kowa gami da mayar da martani cikin tsananin
zafin nama na gaban kwatance, saboda
wannan bala'in gami da masifa ne yasa dajin ya
290

TASKARNOVELS.COM.NG
rikece ya kama girgiza a duk sa'ad da jelar aljani
Darzuba ta daki kasa, da kum irin wutar da yake
fesowa waje daga cikin bakinsa, sarki Dujalu
yayi tunani a cikin zuciyarsa yace Tabdijan
yanzu wai nan aljani darzuba ne yake son ya
kashe jarumi Hasnalu domin ya samu damar
dauko wannan takobi, ni gashi har na samu
damar shiga karkashin wannan teku kuma na
gano inda takobin take, aiko ya zamar mani dole
nayi duk yadda zanyi naga n dauko wannan
takobi tun kafin aljani Darzuba ya samu nasarar
kashe wannan yaro Hasnalu, koda ya zo nan a
zancen zucinsa sai ya sake yin nutso a karo n
biyu izuwa karkashin tekun ya nufi inda wannan
mugayen ljanun suke a guje cikin tafiya ta
yanayin tafiyar kifi, koda aljanun suka sake
ganinshi ya durfafosu sai daya daga cikinsu ya
sake tararsa, nan fa aka cigbaa da bakin
yamutsi, aikuwa sai sarki Dujalu yaji aljanin ya
rufeshi da luguden duka ta ko'ina har ma a
wannan karon ya kasa karewa, suna cikin
wannan hali ne aljanin ya gabza masa wawan
naushi a baki, Dujalu ya kurm wani uban ihu
gami da kururuwa, take hakoransa na gaba
guda uku suka yi fitar burgu daga bakin nasa
291

TASKARNOVELS.COM.NG
tare da wani gudan jini. Cikin rudewa da
dimaucewa bisa jin radadin zafi sarki ya juya da
baya a guje ya bar wajen, da kyar da sidin goshi
ya samu ya taso saman tekun, yayin da yaji
kansa ya kumbura yayi suntum gashi jini na
yoyo a bakinsa kuma numfashinsa na sarkewa,
hakika wuya bata da sabo, bisa dole sarki
Dujalu yayi ninkaya ya dawo bakin gabar tekun
ya cigaba da numfashi da kyar kamar ransa zai
fita, a lokacin ne kuma ya cigaba da zuba wa su
aljani Darzuba idanu yana kallon bakin
gumurzun da suke yi, har izuwa wannan lokaci
su jarumi Imnal suna can sama kan bishiya sum
suna hangen gumurzun da ake yi. Haka suma
su aljani Raugatul Agwanu suna nan a labe a
bayan wannan dutse suna kallo. Bayan aljani
Darzuba da Jarumi Hasnalu sun sake shafe
kimanin sa'a biyu sun wannan fafatawar sai
suka ja da baya a karo na biyu suna haki da
kallon juna saboda gajiya, nan fa kowannensu
ya fara tunanin hanyar da xai bi domin ya samu
nasara akan dan uwan gaminsa, a daidai
wannan lokacin ne jarumi Hasnalu ya fara yi wa
Allah kirari a cikin zuciyarsa yana mai cewa: Ya
Allah kaine sarki kuma mabuwayi gagara misali,
292

TASKARNOVELS.COM.NG
Allah kaine mai daukakawa da kuma
kaskantawa, kuma kaine kayi gaskiya da karya
ka tabbatar da bambancinsu, wanda duk ya
bika ya tsira wanda kuma ya kaucemaka to ya
tabe, ya Allah idan har jihadin nan da nake
dominka ne to ka gaggauta bani sa'a akan
wannan shaidanin aljani na halakashi gama
fadin hakan keda wuya sai jarumi Hasnalu yaji
wani irin gagarumin karfi ya shigeshi wanda bai
taba jin kamarsa ba a iya rayuwarsa ta duniya,
kawai sai yayi wurgi d takobin hannunsa ya
tunkari aljani Darzuba ba tare da shakkar komai
ba. Al'amarin da yayi matukar baiwa Darzuba
mamaki kenan, ya fara kyalkkyala dariyar
mugunta da kuma murna, dan haka shim sai ya
tunkareshi da nufin ya kamashi yayi filla-filla da
sassan jikinsa, aikuwa suna haduwa sai aljani
Darzuba ya kaiwa Hasnalu cafka da hannunsa
ya matse wuyansa da dukkanin karfinsa,
amman sai yaga Hasnalu kikam ko motsi
baiyiba, kamar ba bai taba shi ba. Darzuba ya
tattaro karfinsa ya gabza wa Hasnalu naushi a
fuska, take yan yatsun na Darzuba suka
kakkarye ya kwalla ihu gami da durkushewa
kasa yana mai yarfar da hannunsa cikin
293

TASKARNOVELS.COM.NG
tsananin mamaki. Cikin zafin nama Hasnalu ya
kama dayan hannun na Darzuba ya cisgeshi da
karfin tsiya daga jikin kafadarsa, aikuwa sai
Darzuba ya sake kwarara wani gagarumin ihu
fiye da na farko ya zube a kasa magashiyan, sai
ga jini irin nasu na aljanu yana bulbulowa daga
cikin dungulmin kafadarsa, Hasnalu yazo kan
aljani Darzuba ya daga hannunsa sama ya
dunkuleshi sannan ya gabza masa naushi a
gadon baya, saboda karfin naushin sai da
gadon bayan darbuza ya burme yayin da
hannun Hasnalu ya shige ciki, zaro hannun
nashi keda wuya sai ga kayan cikin aljani
Darzuba suna sulalowa kasa. Darzuwa ya
kwarara wani uban gunji wanda yasa dajin
gurgiza gabadaya, sannan ya kama shureshuren mutuwa, yan dakiku kadan jikinsa ya
sandare ya daina motsi. Koda ganin wannan
gagarumin bajinta wadda jarumi Hasnalu yayi
sai su Imnal suk sakko daga kan bishiyu da suka
hau, suna masu rugowa gareshi cikin tsananin
murna suna kuma yi masa jinjina. Nan take
Imnal, sarki Maharaz da Mulaifa suka karbi
addini musulunci, Hursiyya ta ruga da gudu
izuwa bakin gabar teku inda sarki Dujalu yake
294

TASKARNOVELS.COM.NG
kwance magashiyan, koda ta isa gareshi taga
yadda kansa ya kumbura sannan ga hakoransa
uku sun fita sannan ga jini nan male-male a kan
kirjinsa wanda ya zubo daga bakinsa kuma taga
yadda idanunsa sukayi luhu+luhu kawai sai ta
gashe da kuka tare da fadawa saman kirjinsa
suka rungume juna tana mai cewa ya kai dan
uwana shin yanzu abinda ya sameka da kuma
abin al'ajabi da ka gani da idanunka bisa
jarumtakar da Hasnalu yayi da taimakon
ubangijin musulunci basu isa hujjar da zasu sa
ka karbi addinin Musulunci ba? Sa'ad da sarki
Dujalu yaji wannan tambaya daga bakin yar
uwarsa Hursiyya sai ya janye jininsa daga jikin
nasa suka fuskanci juna sannan ya danyi
guntun murmushi irin na manyan kafirai masu
taurin zuciya ya ce haba yake yar uwata ai
haryanzu sharadinmu bai cika ba, domin kuwa
sai naga Wannan jarumin ya shig cikin wannan
taku ya dauko takobin Saiful Lujara sannan zan
bayar da gaskiya ga addininsa. Koda jin wannan
batu sai jarumi Hasnalu ya dubi sarki Dujalu ya
ce idan har ka amince zaka karbi addinina
tabbas yanzu zan shiga wannan taku na dauko
takobin daga gagareku dauko da izinin
295

TASKARNOVELS.COM.NG
ubangijina. Gama fadin hakan keda wuya sai
jarumi Hasnalu ya juy tare da fadawa cikin
wannan teku yayi nutso izuwa karkashinta yan
mai karanta addu'o'in samun sa'a da neman
tsari. Allahu Akbar yardar Allah tafi ta kowa,
wanda duk Allah ya yarda da shi tofa babu mai
iya ture shi ko yaga bayansa, sannan kuma
babu irin matsayin da bazai iya kaiwa ba, shi
kansa jarumi Hasnalu lokacin da yayi nutso
izuwa karkashin wannan teku sai ya cika da
dumbin mamaki bisa yadda yaga ya cigaba da
numfashi tamkar a bisa turba ya ke ba a
karkashin ruwa ba, sannan kuma yaji ana tafiya
da shi tamkar wani ne ke masa jagora bashine
ke sarrafa gangar jikin tasa ba, kuma gudu ake
da shi a tsaye tamkar gudun tauraruwa mai
wutsiya, cikin dakiku kadan ya hango rundunar
wannan miyagun aljanun masu gadin akwatin
zinare wacce aka sanya takobin Saiful Lujara a
cikinta. Koda wadannan aljanu suka hango
jarumi Hasnalu ya durfafosu cikin wata irin
tafiya mai ban al'ajabi, sai suka taso masa
gabadaya tare da barin akwatin ita kadai
maimakon aljani daya ya raineshi kamar yadda
suka yi wa sarki Dujalu. Aikuwa suna haduwa
296

TASKARNOVELS.COM.NG
da jarumi Hasnalu suka raina kansu, domin
kasu ya rinkayi da karfin tsiya yana kakkaryasu,
nan fa aljanun suka rinka wani irin mugun ihu
gami da ruri, hatta su jarumi Imnal da suke a
can wajen takun sai da ihun aljanun gami da
rurinsu ya dimautasu, suka ji kamar su arce da
gudu, amman sai suka tsaya suna masu toshe
kunnuwansu da hannayensu suna masu cigbaa
da kallon tekun domin suga abinda zai faru.
Aiko ba a jima b suka fara ganin sassan jikin
aljanun yana tasowa saman ruwan, kafin a jima
saman takun ta cika makil da sassan aljnun, sai
bayan kamar dakiku dari da sittin sannan suk ga
jarumi Hasnalu ya fito daga cikin tekun yana
mai rike da akwatin zinare. Koda ya iso bakin
gaba sai Hursiyya ta ruga da gudu ta tareshi
cikin tsananin farin ciki ta rungumeshi tana mai
yi masa jinjina. Sarki Maharaz, Mulaifa da Imnal
ma sai suka tareshi suka kama dariyar farin ciki,
nan take Jarumi Hasnalu yayi bismila ya kama
kwadon dake jikin akwatun ya balleshi da karfin
tuwo, take marfin ya balle, koda aka yi arba da
abinda ke ciki sai kowa ya cika da mamaki,
domin ashe ba wai iya tabokin Saiful Lujara ce
kadai a cikin wannan akwatu harda mashin
297

TASKARNOVELS.COM.NG
Galilur Haras tare da hular lamsara. Hasnalu ya
debo wannan kayan yakin guda uku ya zo gaban
sarki Dujalu ya zubesu a gabashi sannan ya
dubeshi yace ya kai wannan sarki yanzu gashi n
dauko abinda ya gagareku daukowa, saboda
haka sai ka cika alkawari ka karbi addinina.
Koda jin wannan batu sai sarki Dujalu ya
takarkare ya bushe da dariya, al'amarin da ya
baiwa kowa mamaki kenan, lokaci guda kuma
sai ya turbune fuska yake idanunsasuka ciko da
kwalla har hawaye ya fara zubo masa a lokacin
da ya kura wa yar uwarsa idanu, Dujalu ya
kauda kai ga barin kallon Hursiyya ya dubi
Hasnalu ya ce ya kai wannan gawurtaccen
jarumi kayi sani cewa hakika a yanzu addininka
shine na gaskiya, to amman fa b zan iya karbar
addinin naka ba, saboda burina shine na mutu
akan irin tafarkin da iyaye da kakannina suka
mutu a kansa,abin kunya ne a gareni ace irin
tsatson gidanmu ya kauce daga turbar gado,
babban abin bakin cikina shine zan mutu ba
amfana da kayan yakin mazan jiya ba yadda
labarina zai bazu a ko'ina a cikin wannan
duniya, har ya zamana cewa ba za a taba
mancewa da ni ba. Hursiyya ta kalli dan uwanta
298

TASKARNOVELS.COM.NG
sarki Dujalu ta ce saboda yasakake cewa
mutuwa zaka yi alhalin gaka a raye kana
magana muna sauraronka. Kayi sani cewa mu
duka mun dawo daga rakiyar tsafi gami da
aljanu, mun gano cewa duk karya ce, tunda
gashi ma munga takobin Saiful Lujara a waje
daya da hular lamsara da kuma mashin galilur
haras, alhalin an bamu labarin cewa a wajaje
daban-daban suke. Lokacin da sarkk Dujalu
yaji wannan batu sai hawaye ya sake zubo masa
a karo na biyu ya ce ya ke yar uwata kiyi sani
cewa wannan mugun duka da aljanu suka yi
mani a karkashin wannan teku sa'ad da nake
kokarin dauko takobin Saiful Lujara ba karamar
illa yayi mani ba, domin ta kai cewa sun tara
mani jini a jikina, tabbas wannan duka shine zai
zamo sanadin ajalina tabbas ba zan tashi ba.
Hakika inda nasan zan rayu tofa ba zan karbi
addinin Musulunci ba sai dai na karbi
wadannan kayan yaki na mazan jiya domin na
cika burina, shin wani ya cigaba da baki labarin
Mazan Jiya kuwa daga inda na tsaya maki ko
kuwa baki samu wanda ya baki ba? Hursiyya
tayi ajiyar numfashi sannan tace tabbas aljani
Radiyan ya cigaba da bani labarin hikayar
299

TASKARNOVELS.COM.NG
sadauki shaddadu har yazo inda ya hadu da
jaruma Ziya'ul hak sukayi gagarumin yaki wanda
takai cewa su duka sun fada cikin wani rami mai
zurfi, wanda kasansa cibiya ce ta ruwan wata
korama, a cikin koramar ne ma mashin galilur
haras ya fada ruwan ya tafi da shi. Koda
Hursiyya ta zo nan a zancenta sai sarki dujalu ya
dakatar da ita da hannunsa a lokacin da yayi tari
gudan jini ya zubo daga cikin bakinsa. Al'amarin
daya firgita Hursiyya kenan ta sake fashewa da
matsanancin kuka tana mai kankameshi a
jikinta, su kuwa su jarumi Imnal dukkaninsu sai
suka kamu da tsananin tausayi musamman da
sukaga gashi sarki dujalu yana kan gangarar
ajali, amman ga dukkan alamu bashi da rabo na
musulunta. Cikin matukar karfin hali sarki
dujalu ya janyo Hursiyya daga kan kirjinsa ya
dubeta a lokacin da hawaye ke zuba daga cikin
idanunsa ya ce ya ke yar uwata bani da wata
nadama a wannan duniya face guda daya, itace
zan tafi na barki a cikin begena, amman kuma
ina farin ciki da naga kin samu masoyi wato
wannan bakon jarumi, ko ba komai nasan zai
iya debe maki kewar rashin dan uwa da kuma
dangi, kuma zaki samu iyali a tare da shi, yanzu
300

TASKARNOVELS.COM.NG
zanyi kokari kafin rai yayi halinsa na karasa maki
labarin jarumi shaddadu inda halima na baku
labari Sadauki Hulkas na birnin Romaniya mai
hular lamsara. Game da wannan kayan yakin na
mazan jiya kuwa da kuka gansu yanzu a tare a
wannan akwatu, abin ya samo asli tunda daga
lokacin da kowanne jarumi daga cikin mazan
jiyan ya rabu da makaminsa, shidai mashin
galilur haras daga lokacin da ya fada wannan
korama sa'ar da shaddadu da Ziya'ul hak suka
yi yaki to fa bai sake ganinsa ba har izuwa
karshen rayuwarsa, kuma aljanu ne suka dauko
mashin a cikin wannan korama suka dawo da
shi nan cikin tekun bahar suffiya suka sanya shi
a cikkn akwatin da aka sanya takobin Saiful
Lujara, ya ke yar uwata anan gaba zaku ji yadda
kayi itama hular lamsara tazo tekun bahar
suffiya. Yake yar uwata yanzu sai ki saurara da
kyau domin kiji karashen hikayar sadauki
shaddadu. Sarki Dujalu ya sake yin tari hudan
jini ya zubo, al'amarin da ya sake jefashi cikin
mugun yanayi kenan kamar ma ba zai rayu ba,
amman sai ya daure ya cigaba da bayani kamar
haka: "Lokacin da karuwa yaldisa ta sunkuci
jarumi shaddadu ta sabashi a kan kafadarta ta
301

TASKARNOVELS.COM.NG
ruga da gudu izuwa cikin daji sai da ta yi tafiya
mai dan nisa dauke da shi sannan ta iso bakin
wani Kogon dutse. Kai tsaye ta kunna kai
izuwa cikin Kogon ta shimfide Shaddadu a gefe
daya sannan ta je ta karyo reshen bishiyoyi ta
hada itatuwa ta kunna wuta a cikin Kogon ta
fara kokarin dinke katon ramin da ke kan
Shadaddu sai da ta gama dinke raunin ta shafa
masa magani jini ya daina tsattsafowa sannan
ya farfado. Koda Shadaddu ya bude idanunsa
ya yi arba da Yaldisa zaune a gabansa sai ya
cika da tsananın mamaki ya kama waige-waige
da dube-dube. Nan take ya yunkura da nufin
ya mike zaune amma sai Yaldisa ta danna
kirjinsa ta mai da shi kasa kwance ta cé, Kada
ka tashi ya kai masoyina domin kuwa ba za ka
iya yin tafiya ba yanzu don na san kana jin jiri,
dole sai ka huta sannan lafiyar jikinka za ta
dawo. Cikin tsananin rudewa Shadaddu ya
dubi Yaldisa ya ce, Ina Mashina? Yaldisa ta ce,
ban tsince ka tare da Mashinka ba, kai kadai na
gani a bakin gabar koramar a cikin mugun hali
mai kama da suma ko mutuwa. Ni kaina
hankalina bai kwanta ba sai a yanzu da na ga ka
farfado daga wannan dogon suma. Koda jin
302

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan batu sai hankalin Jarumi Shadaddu ya
dugunzuma ainun fiye da ko yaushe a
rayuwarsa ya fara tunanin cewa, ya bai wa
mahaifiyarsa kunya kuma shi ke nan har abada
ba zai sami nasara ba akan abokin gabarsa
Sarki Laffaru, muddin wannan Mashi na Galilul
Haras ya koma hannun Ziya'ul Hak. Nan fa
zuciyarsa ta kama wasi-wasin inda Mashin yake
a halin yanzu domin ba shi da tabbacin cewar
yana hannun su Ziya'ul Hak. Cikin alamun
tsananin damuwa ya dubi Yaldisa ya ce, ya ke
wannan ma'abociyar karame a gare ni hakika
kin yi mini taimakon da ba zan taba mantawa da
shi ba a rayuwata don haka, na yi miki alkawarin
zan yi miki babbar sakayya a nan gaba. Koda
jin wannan batu sai Yaldisa ta murmushi ta ce,
ba na bukatar ka biya ni abin da na yi maka da
dukiya, amma ni akwai alfarmar da zan nema
nan gaba a wajenka. Shaddadu ya dubi
Yaldisa cikin mamaki ya ce, Ke kuwa wacce irin
alfarma ce wannan za ki nema a wajena?
Yaldisa ta yi murmushi ta ce, Ka yi hakuri ba zan
iya fada maka ba a yanzu sai a lokacin da za ka
biya ni ladan da ka yi niyya. Yanzu dai na san
hankalinka a tashe yake saboda rashin ganin
303

TASKARNOVELS.COM.NG
Mashinka. Abin da za a yi shi ne, zan bar ka a
nan cikin wannan Kogon dutse domin ka huta,
kuzarinka ya dawo. Ni kuma zan koma can
gidan Sarauta. A can ne zan samo labarin inda
Mashinka yake saboda na fuskanci cewar
wadannan abokan gaba naka sun hada kai da
Sarauniyarmu domin a ga bayanka. Sa'adda
Shadaddu yaji haka sai ya kamu da murna ya
ce, maza ki je ki aiwatar da hakan lallai zan
kasance mai zuba idanu don ganin dawowarki.
Yaldisa ta yi murmushi mai taushi a gare shi ta
ce, zan yi kokari na dawo da wuri kuma ka
kwantar da hankalinka babu abin da zai same
ka muddin kana cikin Kogon nan. Tana gama
fadin hakan sai ta juya ta fice da sauri ta ruga da
gudu ta nufi hanyar da za ta fitar da ita daga
cikin dajin gaba daya. ****** Al'amarin Aljani
Maruful Dauwaz sai da ya shafe kusan sa'a
guda yana neman Jaruma Ziya'ul Hak a saman
wannan korama da karkashinta sannan ya
hango ta a kwance ko alamar rai babu a tare da
ita. A dimauce ya duro kasa ya dago ta zaune
sai ya ga ashe da ranta domin tana numfashi
sama-sama, sannan ga katon rauni a kanta
wajen ya dare jini na zuba. Cikin hanzari ya
304

TASKARNOVELS.COM.NG
dinke mata wannan rauni sannan ya tofa mata
wadansu dalasimai na tsafi akan raunin amma
sai ya ga sihirin tsafin ya ki yai tasiri. Al'amarin
da ya yi matukar dugunzuma hankalinsa ke nan.
Bisa dole ya je ya samo wadansu ganyayen
bishiyoyi ya dandaka su sannan ya shafa akan
raunin. Jaruma Ziya'ul Hak ba ta farfado ba sai
bayan tsawon sa'a daya da rabi. Idanunuta na
budewa ta mike tsaye zumbur! Cikis kuzarinta
tamkar babu abin da ya same ta ta dubi gabas
da yamma, kudu da arewa ba ta ga abokin
fadanta ba sai Aljani Maruful Dauwaz. Cikis
kaduwa da damuwa ta dubi Maruful Dauwaz ta
ce, ina abokin gabar tamu yake? Maruful
Dauwaz ya yi ajiyar zuciya cikin alamun takaici
ya ce, ban gan shi ba. Ke ma ban gan ki ba sai
da na sha wahalar nemanki a cikin wannan
korama. Ya ke abar kaunata, ki yi sani cewa,
yanzu babban tashin hankalina shi ne sihirin
tsafina da na ki gaba daya sun daina tam kuma
ban san dalili ba. Ina sa ran cewa shi ma
Jarumi Shadaddu nasa sihirin tsafin ba zai yi aiki
ba amma fa idan har ya ga Mashin Galilul Haras
Shirin nasa zai dawo. Tabbas ba wani abu ba
ne ya janyo lalacewar sihirin tsafin namu ba da
305

TASKARNOVELS.COM.NG
nasa face haduwar makaman Yakinki da
Mashinsa na Galilul Haras. Koda Aljani
Maruful Dauwaz ya zo nan a zancensa sai ita
ma Jaruma Ziya'ul Hak halinta ya dugunzuma
ainun fiye da ko yaushe ta rasa abin da ke ma ta
dadi a duniya. Ziya'ul Hak ta dubi Maruful
Dauwaz cikin alamun tsananin damuwa ta ce,
to yanzu mene ne abin yi? Maruful Dauwaz ya
ce, ba mu da wani zabi wanda ya fi mu bazama
neman Jarumi Shaddadu da Mashin Galilul
Haras a cikin wannan kogi. Idan ba mu gansu
ba sai mu koma izuwa gidan Sarautar Sarauniya
Zubaina mu sake neman taimakonta tun da dai
da dan gari akan ci gari. Ita ce za ta iya sanin
duk inda za a iya zuwa a ga Shaddadu. Ni kam
ina zargin cewa akwai wanda yake taimakon
Jarumi Shaddadu a cikin garin nan! Ziya'ul Hak
ta numfasa ta ce, tabbas Biri ya yi kama da
mutum, domin in da babu wanda yake boye shi
da babu yadda za a yi mu neme shi mu rasa
haka, duk da cewar Sarauniya Zubaina tana ba
mu taimakonta. Ba tare da ɓata wani lokaci ba
Aljani Maruful Dauwaz ya rankwafa kasa Ziya'ul
Hak ta hau kansa ta zauna sannan ya bude
fuka-fukansa ya
End Ads