ko ina masu kwarjini da
banTsoro amma ni dai ko gezau banyi ba na
cigaba da tunkarar inda karagar sarki take:; Su
53
TASKARNOVELS.COM.NG
kansu dakaru da zarar sun ganni sai ka ga suna
buda mini hanya ina wucewa: koda sarki dujalu
ya hangoni na durfafo inda yake zaune sai ya
kura mini ido kawai yana sauraron isowata:
kafin mutum ya isa inda aka ajiye karagar
mulkin sarki dujalu akwai wadansu dardumai
guda uku da aka shimfida kala uku: fara baka
da ja: tunda sarki dujalu ya hau kan mulki aka
shimfida wadannan dardumai amma ba a taba
ganin ranar da wani mahaluki ya taba isa inda
dardumai farko take ba wato wannan farar
darduma ya take ba bare har ya taka ta biyu da
ta ukun komai matsayin mutum komai
jarumtakarsa da karfin sihirinsa ma baya iya
zuwa ya taka wannan darduma ta farko
Kawai sai na cigaba da tafiya ina durfafar sarki
dujalu: A lokacin ne gaba dayan mutane dake
fadar suka cika da mamakina kuma suka zubo
mana idanu nida sarki dujalu domin su ga
abinda zai faru: Saboda ba a taba ganin wanda
yashigo fada ba a haka babu iso kuma babu
sallama sannan kuma gashi ya durfafi inda
54
TASKARNOVELS.COM.NG
sarki ke zaune an rasa badakare daya da zai
tsayar dani
Haka dai na cigaba da tafiya har na sami
nasarar taka durduna ta farko: Al:amarin da yai
matukar baiwa kowa mamki kenan: Shi kansa
sarki Dujalu sai da Gyara zama Yana mai Al
ajabina: Na ci gaba da tafiya sai gashi na taka
darduma na biyu
Kawai sai aka ga sarki dujalu ya mike tsaye ya
zare takobinsa jikinsa ya kama tsuma har
fuskarsa yana yi gatsine: Nima Sai na zare waya
adda wacce ta fini tsawo tana sheki gami da
wani irin walwali na tsafi
Na cigaba da tafiya da nufin na taka darduma
ta uku wacce ta kasance ja: Koda na iso
karshen darduma ta biyu sai na kasa daga
kafata na cigaba da tafiya: Nan fa na shiga
karanta wadansu dalasimai na tsafi domin na
55
TASKARNOVELS.COM.NG
wuce gaba amma sai nakasa; koda ganin
abinda ya faru sai sarki dujalu ya bushe da
dariyar farin ciki; lokacin guda kumkuma ya
turbune fuska ya dubeni yace lale marhaban
da sadusa ibn zaiyar T@bbas ban ga laifinka ba
da kake kokarin kasheni tunda nine na kashe
iyalinka danginka da duk zuri arka: A rayuwarta
ban taba zaton cewa akwai mahalukin da ya
sami sihirin tsafin dake daf da nawa ba tabbas
na san cewa kasha bakar wahala kafin ka sami
sihirin tsafin da kake da shi a yanzu samun
kmarka a doron kasa a yanzu sai an sha wuya:
Bisa wannan dalilin ba zan kashe kaba duk da
cewar ya kamata na kasheka din sbda na san
cewa ka tsaneni fiye da yadda ka tsani
mutuwarka: zan kyaleka kuma daga yau ka
zama dan majalisata amma busa sharadi guda
daya; Sharadin kuwa shine idan har kayi wani
yunkuri na cutar dani zan yi maka daurin rai da
rai a kurkuku inda zaka karasa sauran
rayuwarka ta duniya. Sa'adda tsoho Sadusa
yazo nan a lbrinsa kowa yayi ajiyar zuciya a
cikin falon sannan sadusa ya cigaba da bayani
yace yanzu abinda ya kamata mu fara yi shine
mu tabbatar da gaskiyar lbrin da gimbiya
56
TASKARNOVELS.COM.NG
Hursiya tazo mana da shi: SHIN gaskiya ne mu
muke samun nasara? Babu wata hanya da
zamu iya sanin hakan face mu tashi aljni mai
tsananin karfin gudun da zai iya zuwa bakin
kogin Bahar Sufiya koda a cikin kwana bakwai
ne yaje ya gano mana zahiri Al;amarin: Idan har
su sarki maharaz ne ke samun nasara to
tabbas akwai tuggun da zan iya shiryawa mu
yiwa sarki dujalu juyin mulki yadda ba zai taba
iya karba karagarsa bA: Amma fa idan mune
muke samun nasara a filin yakin sai dai mu
rungume kaddara mu cigaba da zaman hkri har
ixuwa sa;adda ajali sarki dujalu zaizo: yanzu
babbar matsalar ita ce gaba dayan aljanun
dake wannan nahiryar tamu sarki dujalu ya tafi
da su wannan yaki saura matansu tsofaffi da
yaransu wadanda baza su iya wanan Aki ba:
Sarauyin aljani mai tashen samartaka da kafin
gudu data be ya rage a yanxu kua ba wani bane
face aljani barzuri wanda yadawo da Gimbiya
Hursiya daga CAN bakin Tekun Bahar sufiya:
Barzaru ya kasance amintaccen sarki dujalu na
gani kasheni don haka bazai taba yarda yayi
mana wannan aiki ba sai dai maya tona mana
asiri: Ya zama wajibi nayi shiti da kaina na bar
57
TASKARNOVELS.COM.NG
wannan nahiya tamu na tafi nean aljanin dazai
yi ana wannan aiki a cikin gaggawa. Sa'ad da
sadusa yazo nan a zancensa sai hankalin kowa
ya kara dugunzuma domin suna ganin cewa ai
babu isasshen lokacin da za ayi wannan aiki:
Cikin alamun tsananin damuwa waziri ya dubi
sadusa yace yanzu a cikin kwana nawa kake
ganin za ka iya zuwa kasamo aljanin da zai yi
mana wannan aiki? Sadusa yai murmushi yace
ku bani kwana uku rak Ai Al mari ne na tsafi:
Koda jin haka sai farin ciki ya lullbe waziri da
sauran yan majalisar: Nan take suka salami
sadusa akan cewa za su jira dawowarsa nan da
cikar kwana uku: Nan dai taro ya watse kowa ya
sulale ya tafi gidabsa cikin wannan dare: * * *
AL AMARIN Gimbiya Hursiya kuwa; tun sa;adda
fada ta watse ta shige cikin gidan sarautar sai
ta wuce izuwa cikin turakarta ta zauna a gefe
gadonta ta shiga tunani mai zurfi. A dai dai
wanan lokaco ne wata kuyagarta mai suna
laziramat ta shigo cikin turakar dauke da
farantin shayi: shi dai wannan shayi na ka:ida
domin kullum sai lazimat ta dauko butar shayin
ta tsiyaya a cikin wani dan karamin kofi na lu u
lu u ta kaiwa Gimbiya Hursiya: Koda ta mikawa
58
TASKARNOVELS.COM.NG
Gimbiya kofin shayin sai ga ashe Gimbiya kuka
take yi hawaye na ta sartu kan kumatuwanta:
Al amarin da yai matukar dugunzuma hankalin
lazimat ke nan dubeta cikin tsananin damuwa
ba mai ajiye kofin shayin akan faranti ta ce ya
shugabata ki yafeni idan nayi miki wani abu
wanda ya bata miki rai: koda jin wannan batu
saI Gimbiya Hursiya ta sa hannu ta share
hawayenta sannan tace ya lazimat kiyi
sanicewa a iya zamana dake Tsawon shekaru
baki taba yi mini wani abu ba wanda ya bata
min rai
Wannan hawaye nawa dakika gayana zuba
bana komai bane face na tsananin bakin ciki
bisa karyar dana yiwa mutanen garin nan a yau
a fada: Maganar gaskiya ban san abinda ya faru
ba a filin yaki domin ana daf da fara yakin ne
sarki shammaceni yasa aljani barzaru ya sureni
yai sama da ni kafin na ankara ya luluka dani
izuwa cikin gajimare: Cikin abinda bai wucce
kwanaki tara ba muka iso nan gida, ni yanzu
babban abin bakin cikina shi ne idan sarki ya
mutu bana son na gajesgi kuma yazama duniya
59
TASKARNOVELS.COM.NG
babu wani mutum dana shaku da shi sai shi;
Mene ne amfanin naci gaba da rayuwa a duniya
bani da masoyi? Mulki daula da arziki duk shire
ne a wannan duniya idan babu masoyi:
Soyayya itace abar da take kawar da dukkan
takaici da bakin cikin rayuwa: koda Gimmbiya
Hursiya tazo nan a zanceta sai kunyaga lazimat
takamu datsananin tausayinta har itama kwalla
ya cika mata idanu ta dubeta tace ya
shugabata to yanzu ke wanne irin hukunci kika
yankewa rayuwarki? Hursiya ta ajiyar zuciya
sannan tace ni yanzu bana bukatar koai face na
koma can bakin kogin Bahar Sufiya domin naga
yadda karshen wannan yaki zai kasance idan
har sarki mutuwa zai yi to zanso na mutu tare
da shi amma bana son ace sarki ya mutu ni
nacigaba da sarauta anan sbda basan cewa
kamar yadda mutne ke kin sarki haka nima
zasukini: Nasani cewa dan uwana Azzalumi ne
tsawon shekara da shekaru mutanen dake
nahiryar nan basa jin dadi mulkinmu tun iyaye
da kakani, kin sani cewa nima bana son irin
wannan mulki da sarki ke yiwa jamaa amma
ban isa na hanashe ba don haka ciwon ido sai
hkri: Ni ina ganin cewa zai fi kyau ni da sarki duk
60
TASKARNOVELS.COM.NG
mu mutu a wajen wannan yaki domin a sami
sabo shugabanci a wannan nahiya mutane su
huta da mulkin zalunci a sami na sauyin rayuwa
mai dadi: Koda Hursiya tazo nan azancenta sai
ta fashe da kuka Al amarin da ya kara jefa
kunyaga lazimat cikin tsananin tsananin
tausayinta kenan ta rungumeta ta na mai
rarrashinta har tadaina kukan sannan ta ja
jikunta daga cikin na tata debeta tace; Ya
shugabata kiyi sani cewa a iyarayuwata ta
duniya ban taba zama da basarake mai tunani
da sani yakamata ba kamarki wanda yake da jin
kai gama son talakawansa tunda gashi kin zabi
ki mutu don kawai takawa su sami rayuwa mai
dadi:Ya shugabata kiyi sani cewa rashinki a
doron kasa ba karamar asara ba ce domin
samun mace mai kyau da kyan hali irin naki sai
an tona: Ya kamata a ce kin sami saurayi
kyakkyawa kuma mai kyawun hali irin na ki
domin yazma abkin rayuwarki ku haifawa baya
abinda zasu amfanesu; yayin da Gimbiya
Hursiya taji wannan sai murmushi ya subuce
mata tace ai niban yaba yin soyayya ba kiuma
ban zaton zanyi ta anan gaba har izuwa karshen
rayuwata ban san maye SO ba: Tun ban taba
61
TASKARNOVELS.COM.NG
kamani ba: KAUNA kawai na sani irin wacce ke
tsakanina da dan uwana sarki dujalu da kuma
mutane ire irenku wadanda nayi sabo da su
sanadiyar zamantakewa;lokacin da Gimbiya
hursiya tazo nan a zanceta sai itaa kuyanga
lazimat Tayi murmushi tace ya shugabata kada
kiyi kuri ko cika baki akan SOYAYYYA Domin
kuwa shI SO abu ne wanda baya sallama bare
ayi masa iso a duk yayin da yaga zuciya yake
nean shiga cikinta
Karfin gudunsa ya wuce na iska ko guguwa
haka kuma DAFIN SO yafi na kibiya: A duk
sa:adda ya soki mutum to fa babu wani magani
da zai warka dashi face kasancewa tare da
masoyinsa
Dajin wannan batu sai Hursiya ta bushe da
dariya sannan ta dauki wannan kofin shayi ta
kurba sau uku tace daga yau mun kulla gasa
nidake na ga wanda zai lashe gasar: Ni Hursiya
na cika miki baki cewar KIBIYAR SO ba ta isa ta
62
TASKARNOVELS.COM.NG
huda jikina ba bare ta samini dafin da zan rasa
maganinsa
Duk ranar da kika lashe wnnan gasa in dai ina
raye nayi alkawari zan yantaki kuma zan baki
dukiya mai yanwa gaske: Koda jin wannan batu
sai kuyanga lazimat ta kamu da tsananin farin
ciki tace tabbas zamu bambance tsakanin aya
da tsakuwa kuma lokacin ne zai raba wannan
gardaa dake tsakaninmu Hursiya ta yi ajiyar
dogon numfashi a lokacin data ajiye wannan
kofin shayi sannan ta kurawa lazimat idanu
tace yanzu wacce hanya kike ganin zan bina
sami damar komawa sansanin yakin nan a cikin
yan kwanaki kadan kafin yakin yakare? Zan ci
gaba.
MAZAN JIYA
Littafi na Hudu 4
Part G
Na Abdulaziz Sani m gini
63
Yayin da lazimat taji wannan tambaya sai
hankalinta ya dugunzuma tayi shiru tana
tunanun har izuwa tsawon wadansu yan dakiku
kamar ba zatace komai ba. Daga can sai ta
kawo gwauron numfashi ta aje sannan tace ya
Shuganta akan bukatarki ta biya zan iya sallaa
raina da jikina sbda kauna da aminci dake
tsakaninmu don haka ki bani kwana biyu rak
zan je na biwata hanya wucce nake gani cewa
zata kaimu ga nasara
Koda jin haka sai gimbiya Hursiya takamu da
tsananin farin ciki nan take ta bude wata farar
akwati ta debo dinare da yawa batare da sanin
adadinsa ba cikin tafin hannunta ta mikawa
lazimat tace ungo wannan ki tafi da shi sbda
nasan cewa yanzu aiki wannan zamani babu
wani wani aiki da yake tafiya ba tare da kudi ba:
Lazimat tacce haba ya shugabata ai wannan
kudn yayi yawa: Hursiya ta kada kai tace ai
girman wannan aiki da nabaki yafi wannan
64
TASKARNOVELS.COM.NG
dinare cikin turakar nan tawa duka: Hadarinsa
kuwa dai dai yake da mutum ya sayi ajalinsa
inda zan baki dukiya cikin gidan sarautar nan
gaba daya ban biyaki ladan wannan aiki ba: Ki
tashi ki tafi na sallameki sai nan da kwana biyu
ki dawo mini da jawabi mai dadi sai ki wakilta
wata daga cikin sauran kuyangina ta cigaba da
yin irin aikin da kika saba yimini
Amma lallai ki sami mai amana wacce zata iya
rike sirrina: kunyanga lazimat ta risina cikin
biyayya tace angama ya shugabata
: WANNAN SHINE ABIN DA YAFARU A BIRNIN
SARKI DUJALU BAYAN ALJANI BARZARU YA
DAWO DA GIMBIYA HURSIYA DAGA BAKIN
TEKUN BAHAR SUFIYA INDA AKE SHIRIN
FAFATA YAKI TSAKANIN RUNDUNARSU DATA
SARKI MAHARAZ
: * * * ACAN Sansanin yaki kuwa awana na
ukun da akayi ana hutun yaki kullum inmal da
sarki mahazar suna zaune a gaban kabarin
65
TASKARNOVELS.COM.NG
sarki yaki Hibru suna kuka dare da rana: Abinci
a da kyar suke cin kadan idan Gimbiya Mulaifa
ta matsa musu tana mai yi musu tuni da cewar
idan fa basu ci abinci ba to fa bazasu sami
damar cigaba da yakin ba tunda bazasu samu
kuzari ba ajikinsu
Wannan batu ne yasa suke daurewa su ci
abinci kadan bayadda zasu koshi ba: A ranar
dare na biyu ne sarki maharaaz inmal da
sauran manyan daraunsu na Yaki suka zauna
domin su tattauna akan yadda zasu bullowa
wannan yaki a wannan karo na uku domin su
sami nasara akan abokan gaba cikin kankanin
lokaci: Wani barde da ake kira shamal shine ya
fara magana yana mai duban sarki maharaz
yace ya shugabana shawara ta ta farko dazna
bayar ita ce kamata yayi ana fara wannan yaki
inmal tare da manyan jarimanmu masu
jarumtakar gaske su yiwa sarki dujalu rubdugu
domin a kashe shi da wurin tabbas idan muka
sami nasarar kashe sarki dujalu mun karya
logon abkan gabarmu tunda a bangaren
dakarunu na aljanu karfinsu yazo daidai da na
66
TASKARNOVELS.COM.NG
dakarun aljanun su: koda jin wannan batu sai
sarki maharaz ya dubi kowa yace ya ku dirkokin
birnina kun ji shawarar da shamal ya kawo:
Shin kun amince da ita ko kuwa akwai mai
korafi akanta? Gaba dayansu sai suka yi shiru
aka rasa wannan da zaice kala, sai inmal ne yai
gyaran murya sannan ya ce ai ko kadan wannan
shawarar da shamal ya kawo ba zata yi tasiri
ba: dalilina na fadin haka shine masu iya
magana sunce MASO ABINKA YAFI KA DABARA:
kada ku manta cewa shi kansa srki dujalu zai yi
irin wannan tunanin da shamal yayi don haka
dole ne ya san dabarar da zaiyi yarufe wannan
kofa: abu na biyu da nakeso da nake so ku gane
shine: Dakarun yakinsa suna da bakin naci fiye
da namu dakaru: Idan muka tattara hankalinu
akan sarki dujalu kawai zasu sai damar daza
suyiwa namu dakarun mumunar barna, kafin
inmal ya gama rufe bakinsa tuni shamal ya tarin
numfashinsa yace to wai shin kaanta ne cewar
sarki dujalu ya zama masaki mai hannu daya:
wannan lalura da ta same shi zata rage masa
karfin da zafin nama: inmal ya girgiza kai ya ce
ba haka bane ai kada mage ba yanka bane
kuma ina so ka sancewa mazanjen kwarai suna
67
TASKARNOVELS.COM.NG
yaki ne da zuciyarsu kafin jikinsu: Ma ana
taurin zuciyarsu da karfinta yafi na hannayensu
sbda haka wannan rashin hannu daya na sarki
dujalu ba zai rage shi da komai ba face ma ya
kara masa kuzari da mugun nufi akanmu: Sa
adda inmal yazo nan a jawabinsa sai jikin kowa
yayi sanyi aka yi shiru ana tunani : Jim kadan sai
wani bardw shi KIMARU ya numfasa yana mai
duban sarki maharazz yace ya Shugabana wai
shi mezai hana goben da dazar an busa kohon
ci gaba da yakin nan ka shammaci abkan gaba
ka hallakasu da karfin sihirinka? Kafin kimaru
yagama rufe bakinsa tuni sarki maharaz ya
shara masa mari sbda karfin marin sai da
kimaru ya tuntsure kasa ya mike zaune wuf,
cikin firgici yana mai sunkui da kansa kas
sauran dakarun kuwa duk sai suka firgita suka
sunkuui da kawunansu kas don kada laifin wani
ya shafesu. Sarki Maharaz ya dubi kimaru a
fusace yace shin kai kurma ne a lokacin da nayi
rantsuwa da sunan mai girma darbuza cewar
ba zan yi amfani da karfin sihiri ba tun a farkon
wannan yaki bisa yarjejiniyar da ke tsakaninmu
68
TASKARNOVELS.COM.NG
da sarki dujalu? To ka sani cewa ni da sarki
dujalu babu wandazai yi amfani da karfin sihiri
har a gama wanna yaki tunda shima yayi
rantsuwa da ubangijinu kamar yadda nayi:
yanzu dai na fuskaci cewa gaba daynku babu,
Wanda yake da wata dabara ko sabuwar hikima
wacce zamu yi amfani da ita don ganin mun
saminasara r wannan yaki. Abin da nakeso da
ku kawa shine kowa yaje yayi shirin tunkarar
wanannan yaki gobe idan aka fara yakin kowa
yayi iya kokirinsa lallai sa a tana ga mai rabo
walau garemu kukuma garesu. Koda gama
wannan jawabi sai sarki maharaz ya mike tsaye
ya tafi izuwa cikin tantinsa: a sannan ne su
bardw kimaru a suka tashi suka tafi izuwa nasu
tantunan aka bar sadauki inmal a zaune shi
kadai a lokacin da yada cikin kogin tunani: A
wannan lokaci wata irin iska mai sanyi ke
kadawa: inmal na cikin wannan tunanin ne yaji
an taba kafadarsa ta baya. Cikin dan alamun
razana inmal ya waiga da sauri don a zatonsa
aljanu ne keson tabashi, koda ya yi arba da
wanda ke tsaye abayansa sai ya cika da
mamaki ba wani bane face Gimbiya Mulaifa:
Mulaifa da inmal suka yiwa juna murmushi
69
TASKARNOVELS.COM.NG
sannan ta zauna a kusa da shi suka dubi gabas
ba tare dayansu yace kala ba har izuwa tsawo
yan dakiku. Inmal ne ya katse shirun yace
menene ya hanaki yin barci har izuwa tsawon
wannan dare? Mulaifa ta sake yin murmushi a
karo n biyu sannan tace abinda ya hanaku yin
barci kai da abbana shi ne ya hanani: Ya kai
abin kaunata kayi sani cewa bamu taba tsintar
kanmu a cikin halin bakin ciki irin na wannan
lokaci ba sakamakon mutuwar mahafinka
Sannan kuma bamu san yadda karshen
wannan yaki zai kasance ba: Ni babban abin
ma daya dugunxuma hankalina shine naga
mahaifina jikinsa yayi sanyi gaba daya akwai
alamar cewa bashi da sauran kuzari da sa ran
samun nasara a wannan yaki: Koda jin wannan
batu sai inmal yayi ajiyar zuciya ya ce ni kaina
jikina yayi sanyi ba don komai ba sai sbda ina
ginincewa karshen wannan yaki ba zai yi kyau
ba: Za a yi asarar miliyoyin rayuka ko dai ayi
ragas ko kuma ayi kare jini biri jini: Ni babban
abinda yake damuna guda biyu ne: Abu na farki
shine na tsaya nayi tunani na gano cewa damu
70
TASKARNOVELS.COM.NG
da su sarki dujalu duk muna yin wannan yaki ne
sbda son zuciya kawai kowanne bangare suna
son su mallaki kayan yakin MAZAN JIYA don
kawai su mulki duniya: Wannan duk al:amarin
ne na zalunci: Ni ka zan fi son su mallaki kayan
Yakin MAZAN JIYA don kawai su mulki duniya,
wannan duk al amarin ne na zalunci: Ni ka zan
fison na mallaki wadannan kayan yaki na
MAZAN JIYA don kawai na bar abin tarihi na
jarumtaka wanda baza ataba mantawa dani ba:
Abu na biyu da yake damuna shi ne zuciyata
tana rawa akan allolin da ake bautawa a
wadannan nahiyoyo namu sbda na fuskanci
cewar suna yin karya: Sau tari sukan fadi wani
abun suce zai faru amma kuma sai aga sabanin
haka: An ya kuwa ba kya ganin cewa akwai wani
ubangijin wanda yafi dukkanninsu wanda shine
ne mafi karfi da daukaka? Koda jin wannan
tamabaya sai mulaifa tayi ajiyar zuciya sannan
tace hakika duk abinda ka fada gaskiya ne
kuma duk mai hankali dole ne yayi tunani akan
hakan: To amma abinda nake so naki daga
gareka shi ne shin kana da wata hujja ne mai
karfi wacce tasa ka fadin hakan? Inmal yayi
shiru yana mai daga kansa sama cikin alamun
71
TASKARNOVELS.COM.NG
tunani sannan yace akwai wani lokaci a baya
da marigayi mahaifina ya gaya mini cewa akwai
wani ADDINI da ake kira ADDININ MUSULUNCI:
YA tabbatar mini da cewa bai taba ganin mai
karfinsa ba kuma yaji ajikinsa cewar shine
addinin gaskiya sbda abinda ma abotansa suka
sa a gaban koda jin wannan batu saijikin
Gimbiya mulaifa yai sanyi tayi shiru har izuwa
tsawon yan dakiku sannan tadubi inmal Inmal
tace ni kaina yanzu naji a a cikin raina na
gamsu da wannan addini domin ka karbi
addininin mu sami taimakon ubangijinsa bisa
wannan gagarumin yaki dake gabanmu: Inmal
ya ja dogon numfashi yace hakika maganarki
dutse ce amma tunda