x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - MAZAN JIYA 4

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 68055 words

Category: Adventure Stories

Views 178

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
babu damar hakan sai
mu rungumi kaddara: Ta shi muje mu kwana
domin kuwa dare ya raba sosai: Yana da kyau
mu sami barci a wannan dare sbda gagarumin
aikin dake gabanmu a gobe

mulaifa ta mike tsaye tace zanje dai na kwanta
amma tun nayi barci ba zan iya ba tunda ina
cikin fargaba da zullumi bisa abinda ka iya

72

TASKARNOVELS.COM.NG
faruwa gobe: Hatta kai da sarki duk nasan cewa
baza ku iya rintsawa ba a wannan dare

inmal yayi murmushi karfin hali yace hakika
maganarki gaskiyace. Koda gama fadin haka
sai ya kama gannun mulaifa yaja ta izuwa ga
tantin sarki

: Koda suka iso kafar tanti sai ta dubeshi tace
inason na karar da wannan dare tare dakai
gaba dayansa tund babu mamaki daga yau ba
zamu sake samun damar jin muryar juna ba da
ganin fuskokinmu. Koda jin haka sai inmal ya
girgiza kai ya ce ai duk wuya duk dadi komai
RINTSI DA TSANANI ina san ran cewa bazamu
rabu ba kumma muna tare. Ki sani cewa
mahafinki ya gaya mini cewa bisa binciken da
yayi a hallarar tsafinsa lallai mutum hudu zasu
tsira da rayuwarsu a wannan sansanin yaki:
Kuma mutum biyu daga bangare abkan
gabarmu ne ragowar mutum biyu kuma daga
namu ban garen: Ina ji a jikina cewar kina daya
daga cikin mutane biyun : koda inmal yazo nan
73

TASKARNOVELS.COM.NG
a zancensa sai idnsa suka ciko da kwallah har
hawaye yazubo masa : Al amarin da ya
dugunzuma hankali mulaifa kenan ta rungume
inmal tana mai cewa yakai abin kaunata ina
dalilin zubar wannan hawaye naka? Inmal yace
ba komai ne yasani wannan kuka ba face
tunanin cewa zan iya rasa babban masoyina na
biyu a wannan yaki wanda na tabbatar da cewa
yana sona kamar yadda mahafina marigayi
yake sona. Dajin wannan batu sai hawauye
yazuvowa wa mulaifat tace Tabbas na san ba
wani kake nufi ba face mahaifina

Koda jin haka sai inmal ya dada kankame
mulaifa a kirjinta yana mai sake fashewa da
sabon kuka: itama ta tayashi da kukan

A haka dai suka karasa cikin tantin na ta suka
zauna suka cigaba da hira maimakon su kwnta
su yi barci basu gushe ba suna hira har sai da
Alfijir ya keto a sannan ne mai sacewa ya
sacesu basu sani ba suka kama gyangyandi
74

TASKARNOVELS.COM.NG

: Sai da gari ya waye sosai har rana ta hudo
bayan kowanne bangare na mayanka sun
kimtsa sannan aka yiyo gayya aka taho filin
daga

azuvowa wa mulaifat tace Tabbas na san ba
wani kake nufi ba face mahaifina

Koda jin haka sai inmal ya dada kankame
mulaifa a kirjinta yana mai sake fashewa da
sabon kuka: itama ta tayashi da kukan
A haka dai suka karasa cikin tantin na ta suka
zauna suka cigaba da hira maimakon su kwnta
su yi barci basu gushe ba suna hira har sai da
Alfijir ya keto a sannan ne mai sacewa ya
sacesu basu sani ba suka kama gyangyandi

: Sai da gari ya waye sosai har rana ta hudo
bayan kowanne bangare na mayanka sun
75

TASKARNOVELS.COM.NG
kimtsa sannan aka yiyo gayya aka taho filin
daga. * * * Sarki Dujalu akan gaba tare da
zakwakuran dakarunsa cikin gagarumar shigar
yaki mai tsananin kwarjini fiye da wadda suka yi
a yakin daya gabata: * * * A bangaren su sarki
maharaz kuwa inmal ne akan gaba shima tare
da nasu zakwakuran mayakan ababan dogaro:
A kowanne bangaree kuma a sararin samaniya
aljanu ne ke shawagi rike da muggan makai na
KARE DANGI

Kawai jira suke a basu umarni su afkawa abkan
gaba. Sarki maharaz ma sai gashi akan gaba
kusa da inmal rike da takobi da garkuwa: Al
amarin da yai matukar baiwa inmal mamaki ke
nan kuma ya firgitashi ya dubi sarki maharaz
cikin tsananin damuwa yace Ya Shugabana
mene ne ya kawoka nan gaba alhalinka san
cewa kai ba gawurtaccen ma yaki bane kuma
gashi ba za ayi amfani da karfin sihiri ba a
wannan yaki face tsagwaron karfin dantse
kwarewa da sanin makama: Sa adda sarki
maharaz ya ji wannan tambaya ta inmal sai yayi
guntun murmushi cikin yake yace ya kai dana
76

TASKARNOVELS.COM.NG
kayi sani cewa ni yanzu komai na duniya yafita
daga raina koda mun sami nasarar wannan yaki
kuma mun sami nasarar dauko Takobin SAIFUL
LUJARA bani da sauran bukatar na mulki
duniyar tunda abkan jin dadin mulkin nawa bbu
shi a lokacin da burin nawa ya cika na mallaki
kayan yakin maxan jiya a sannan ne zan biya
abkina Hibru wahalar bautar daya yi mini da
kua hkrin da yayi dani na tsawon shekaru ina
wulakantashi da rashin jansa a jikina

ina so kasani cewa yau ne ranar farki da zanyi
yaki a cikin fishin da ban taba yi ba sbda haka
lallao zan baka mamaki a wannan yaki

Zan yi gagarumar jarumtaka irin wacce ban
taba yi ba kuma zan ragargaji abkan gaba da
yawan gaske. Sa'adda sarki maharaz ke
wannan jawabi sai ya hango gimbiya mulaifa a
can bayan mayakansa a tsaye bisa kan wani
dutse mai tudu tana hango abin da ke faruwa:
koda ganinta sai idanun sarki maharaz suka
ciko da kwallah ya dubi innal yace yakai dana
77

TASKARNOVELS.COM.NG
kayi sani cewa a bayan wannan yaki ne uwa da
uba a waken mulaifa sbda haka na damka
amanarta agareka: Ina mai farin ciki daya
zamana cewa yata ta kamu da tsaananin
kaunarka ko ba komai na san cewa ba zan
mutu na barta a matsayin marainiya ba mara
kowa ko masoyi ba na san tana da kai. Zan ci
gaba.
MAZAN JIYA
Littafi na Hudu 4
Part H
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
* * * A dai dai wannan lokaci ne sarki dujalu
ya zare takobinsa da hannunsa na hagu daya
dungulmin nasa na dama kuwa na boye acikin
rigar da ke jikinsa

yana zare takobin tasa kuwa sai yadubi inmal
ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa
78

TASKARNOVELS.COM.NG
mai amsa kuwwa hari sai da kasa takama
girgiza kamar zata tsage komai ya rufta cikinta
sannan yace ya kai da mai kamar ubansa kayi
sani cewa yakin da zamu yi yau ba irin wanda
muka yi bane a karon farko kuma ba irin na karo
na biyu bane: Yanzu zamu kaure ne da yaki
kwanmu da kwaekatarmu: Ma ana mu cakude
mutanenmu da aljaninmu kuma ba yaro ba
babba babu tsoho ko tsohuwa bare mace ko
namiki: babu sani kuma bbu sabo Zamu yi ta yi
har sai mai nisan kwana a cikinmu ya tsira da
rayuwarsa: Amma bisa sharadin nan dai na
farko wato babu batun amfani da karfin sihiri
sai tsagwaron karfin dantse: Kafin inmal ko
sarki maharaz daya daga cikinsu ya budi baki
yace wani abu tuni sarki dujalu yayi nuni da
takobinsa izuwa ga rundunar su sarki Maharaz.
Wohoho! Ai kuwa nan take gaba dayan
dakarunsa mutane da aljanu suka kama zare
makaman: Karar zare makaman ta cika dodon
kunne da dajin gaba daya tamkar ana aiki da
dukkan makerun duniya: Ai kuwa suma
rundunar tasu sarki maharaz sai suka
zazzarenasu makaman: A lokacin guda
kowannen bangare suka rugo da gudu suna ihu
79

TASKARNOVELS.COM.NG
da kururuwa domin a gwamutse: Wohoho Inda
ace mutum na tsaye a gefe daya yana kallon
wannan sansanin yaki daga nesa kadan to da
nan take zai tsure da gudawa sbda tsananin
tsoro da fargabar abinda zai faru, kai hatta kasa
sai mutum ya tausaya mata sbda girgiza ta
kama yi kamar zata rufta da duk abinda ke
samanra sbda tsabar dudufniyar kafafuwan bil
adama dana aljanu sararin samaniya kuwa sai
yauo bakikkinri sbda ha yakin bala in dake fita
daga cikin bakunan aljanu gami da sautin
ihunsu mai haddasa tsawa da walkiya ai kuwa
rundunonin biyu na haduwa aka ruguntsu me
da masifaffen bala in yaki wanda yafi gaban
bayani mai bayani: fasaltawar mai basira ko
labarin mai labari kawai sai dai abinda ido ya
iya tantancewa: tartsatsin wuta ya tinka fallatsi
a sararin sama yana zuvowa kasa yana
haddasa gobara. KAICO! WANDA BAI SAN YAKI
DA MASIFA BA SHINE YAKE FATAN SU: A
wannan rana duniyar gaba dayanta sai da ta yi
girgiza tamkar zata nutse i zuwa cikin karkashin
kasa: Duk wani abudaya kasance mai rai walau
mutum aljan dabba tsuntsu ko kwaro sai daya
firgice yayi nadamar zuwn wannnan rana: Nan
80

TASKARNOVELS.COM.NG
fa filin yakin ya ruguntsume gami da
hautsinewa da dumulmulewa aka shiga cin
kasuwar daukar rayuka: jini kuwa daya soma
fallatsi da malala gami da tsartuwa a sama da
kasa sai da kalar bishiyoyi mutane da aljanu
suka koma jajaye suka rine da jini babu kyan
gani: Sai da takai ta kawo cewa aljanu nasa
shaida yan uwansu aljanu mutane basa gane
yan uwansu mutane; banda sara da suka babu
abinda ake ji: Sassan jikin bil ada;a kuwa suka
rinka shawagi a sararin sama suna zubowa
kasa tamkar ruwan samansu akeyi

* * * Wohoho! JARUMTAKA KYAUTA DAGA
ALLAH: WANDA DUK ALLAH YABASHI
SADAUKANTAKA GAMI DA JURIYA DA NACI TO
FA SAI DAI AZUBA MASA NA MUJIYA KO KUA
AYI MASA ALLAH YA ISA! DOMIN YAZAMA
ALAKAKAI KO KUMA ACE KADANGAREN BAKIN
TULUA KARSHI A KAR TULU A BARSHI YAYI
BARNA. Duk inda sarki dujalu da jarui inmal
suka sa gabansu sai dai kaga mazaje na
zubowa kasa tamkar ana sassabe a gona: Sai
da aka shafe sa a bakwai ana asarar miliyoyin
81

TASKARNOVELS.COM.NG
rayuka amma duk bala in da ake yi inmal da
sarki dujalu suna ta laluben juna amma sun
kasa haduwa sbda bala in yaki gami da
cakudewarsa
Al amarin sarki maharaz Kuwa a wannan rana
yayi shammace kuma yayi matukar bada
mamaki domin shima sai yazamo gagarumin
FASA TARO mai TARWATSA MAZA: domin duk
inda ya durfafa sai dai kaga ana zubewa tamkar
ana karkada bishiyar busassun ganyaye:
Takobinsa ma gaba daya rinewa tayi tazama
jajawur kamar yadda dukkkanin jikinsa yayi: Kai
a wannan rana zufar jini ceta lullube fuskokin
mutane aljanu har sai sun goge jinin dake
fuskokinsu sanan suke iya gani: kai sbda
tsananin bala i da masifar wannan yaki sai gaba
dayan nahiyar da ake wannan mugun yaki sai
da tayi bakikkirin tayi duhi dundum Tartsatsin
wutar da ke tashi sakamakon haduwar makaan
yaki kawai ya rinka haskawa har ake iya gane
juna: Ana cikin wannan bakin gumurzu ne sarki
maharaz ya ga wani bakon jarumi a cikin jama
arsa yana ta ragargaza abkan gaba: Jarumin ya
rufe fuskarsa da jakinsa gaba daya yaddda an
kasa shida namiji ne ma ko mace: Yana rike da
82

TASKARNOVELS.COM.NG
takubba guda biyu kuma shima duk inda sarki
maharaz ya dauke kafarsa anan yake sa tasa.
Duk sa adda aka kai wa sarki maharaz wani
mummunan hari sai kaga wannan bakom
jarumi ya kareshi: Babu abinda ya daurewa
sarki maharaz kai face tsananin zafin naman
jarumin jarui da tsananin jarumtakarsa tamkar
ta inmal: Burin sarki maharaz shi ne yaga fuskar
wannan bakon jarumi amma abu ya gagara: Ai
kuwa shima inmal sai ya hango wannan bakon
jarumi koda yaga irin gagarumin aikin da yake yi
gami da kare rayuwar sarki maharaz sai ya cika
da dumbin farin ciki: ya sami dadin kwarin
guiwa da kuzari ya ci gaba da tagargazar maza:
KAICO MUTUWA RIGAR KOW: BALA I BA A SA
MAKA RANA: MUGUN JI DA MUGUN GANI BA
SHI DA DADI: TSAUTSAYI DA ASARA BASA JIN
BIRKI IN SUKA TAHO TAMKAR KUMALLO SUKE
BABU MAI IYA TSAIDA SU
KAICO MUTUWA RIGAR KOWA, BALA I BA A SA
MAKA RANA: MUGUN JI DA MUGUN GANI BA
SHI DA DADI: TSAUTSAYI DA ASARA BASA JIN
BIRKI IN SUKA TAHO TAMKAR KUMALLO SUKE
BABU MAI IYA TSAIDA SU
83

TASKARNOVELS.COM.NG
* * * Haka dai aka cigaba da wannan yaki
wanda tun daga farko kafuwar duniya kawo i
yanzu ba a taba yin makamancinsa ba domin
sai da aka kwana tara gami da sa a tara ana
zubar da mazaje da aljanu da mutane a kas a
sannan ne tsananin gajiya da nadama ta sa
kowane bangare yayi janyewar dole aka ja da
baya domin makogwaron kowa ya bushe sbda
tsananin kishirwa: Hanji cikin kuwa ya
kananade ya daure sbda yunwa: Shin kasan
ruwan Kogin BAHAR SUFIYA wanda ya rine ya
zama jini tafarfasa yake sbda masifar tartsatsin
wutar dake zbowa cikinsa. Da Zarar mutum ya
tsoma hannunsa a ciki domin ya debo ruwan
jinin ya sha ya kawar da kishirwa sai kaga nan
take hannun nasa ya kone tamkar a cikin wuta
ya tsomashi

** * Lokacin da kowanen bangare ya ja da
baya aka dai na sara da suka sai gaba dayan
duhun da ya mamaye sama da kasa yayaye
tamkar da can a cikin bakin dare ake gari ya
waye: A sannan ne idanun kowa suka bude
sosai aka ga irin mummunar asaran rayukan da
84

TASKARNOVELS.COM.NG
akayi: Da zazar mutum ko aljan ya dubi kas sai
yaga ashe kowa akan gawarwaki yake tamkar
da gawar aka yi kasar wajen duka sai dai kaga
gawa kan gawa; lodi ajan lodi har tana tsiri tana
ruguzowa kasa: A sannan ne mazaje suka kama
mugun haki kamar ransu zai fita daga cikin
gangar jikinsu aka fara kallon kallo aka fara iya
shaida juna: sai gashi sarki dujalu da jarumi
inmal sun yi arba da junansu ashe ma tazarar
da ke gsakaninsu bata wuce taku goma ba
amma wani iko na allah duk tsawon kwanakin
da suka shude ana wannan bakim artabu ko
sau daya basu hadu ba sun yi gaba da gaba: A
dai dai wannan lokaci ne bakon jarumin cikin
rundunar su sarki maharaz ma ya cire hular
karfen da ke kansa sai ga dogon gashi na mace
mai tsananin baki da sheki ya zubo kasa, BA
WATA BACE FACE GIMBIYA MULAIFA! Al
amarin da yai matukar girgiza kowa kenan a filin
yakin aka cika da dumbin mamaki: Sarki
maharaz dake tsaye a can gefe daya yana ta
faman haki baisan saadda ya saki takobinsa ba
ta fadi kasa ba sbda tsananin mamakin ganin
cewa ashe yarsa ce gimbiya mulaifa bakuwar
jarumar da tayi ta ragargazar abkn gaba
85

TASKARNOVELS.COM.NG

Abinda yai matukar daure masa kai shine
yaushe mulaifa ta koyi yaki haka har ta kuma
tasami wannan gagarumar jarumtakar amma
bai sani ba? Koda sarki dujalu ya hango sarki
maharaz sai ya yunkura da nufin ya ruga izuwa
gareshi domin ya gagauta hallakashi ya
kunsawa jarumi inmal bakin ciki a karo na biyu:
KwatsaM! Ba zato b tsammani sai aka ji an
busa kahon tsai da yaki daga kowannen
bangare

Cikin tsaninin bakin ciki sarki dujalu ya mai da
takobinsa cikin kufe sannan yadubi a dadin
gawarwakin jama arsa na mutane da aljanu ya
kwantantasu da nasu sarki maharaz sai ya ga
kusan kunnen doki ne amma kuma a kaso
goma na kowannen bangare An karaar da kaso
bakwai bakwai: Al amarin da yai matukar
dugunzuma hankalinsa keanan ya tabbatar da
cewa lallai RAGAS aka dada yi a cikin wannan
yaki. Kawai sai sarki dujalu ya durfafi inda sarki
maharaz ke tsaye:
86

TASKARNOVELS.COM.NG

Zan ci gaba.

MAZAN JIYA
Littafi na Hudu 4
Part I
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
Har inmal ya yunkura zai tareshi sbda tunanin
ko cutar da maharaz zai yi: sai sarki maharaz ya
dagawa inmal hannu yana mai yi masa nuni da
ya dakata: inmal ya vi umarni ya tsaya a inda
yake har sai da sarki dujalu ya iso daf da inda
sarki maharaz yake tsaye yadda har suna iya jin
numfashi juna sannan yace yakai babban abkin
gabata kayi sani ce wa hakika ka shammaceni
ainun domin ban taba zaton cewa kai da yarka
kuna da gagarumae jarumtaka haka ba: To
amma ka sani cewa idan aka dawo filin daga

87

TASKARNOVELS.COM.NG
zamuyi karo ne na karshe: Na rantse da darajar
abin bautata ba zaku tsallake masifataba

: Da wannan hannunawa guda daya sai na
dada kunsa muku bkin cikin da bazai taba
shafewa ba a cikin kundin tarihin rayuwarku

Lokacin da sarki dujalu ya yazo nan azancesa
sai sarki maharaz ya bushe da dariya lokaci
guda kuma ta turbune fuska ya dakawa sarki
dujalu tsawo ya ce yakai babban abkin gabata
kayi sani cewa mulki da daukaka ba banza
bane: Duk dan sarki dole ya gaji jarumtaka
domin ba a yin mulki a banza: na dade ina boye
jarumtakata kuma ina tandinta sbda zuwan irin
wannan rana: ina mai tabbatar maka dacewa
koda zaka cusa mana wanna bakin cikin a karo
na biyu kaar yadda ka kunsa mana na farko ka
rabau da babban masoyinmu sarki yaki Hibru
to kai a kwa sai mun kunsa maka bakin cikin da
zai bibiyeka har izuwa karshen rayuwarka.
Koda gama fadin hakan sai sarki maharaz ya
juya ya nufin sansannsu gaba dayan sauran
88

TASKARNOVELS.COM.NG
jama arsa wadanda suka yi saura mutane da
aljanu sai suka bi bayansa sai jarumi inmal da
mulaifa suka tsaya ana kallon kallo tsakaninsu
da sarki dujalu a lokacin da suma jama ar sarki
dujalu suka juya suka nufi sansaninsu: tsirarun
dakaru na kowannen bangare ne suka tsaya
suna tatara gawarwakin yan uwansu suna
tarasu a waje guda domin akonesu sbda
yawnsu yafi karfin ace za a binne

Sai da ka shafe kusan dakika dari da ashirin
ana kallon kallo gami da harara tsakanin sarki
dujalu da su inmal sannan mulaifa ta zo ta
kama hannun inmal ta janyeshi suka tafi izuwa
nasu sansannin suna waigen sarki dujalu: Har
sai da su inamal suka bacewa dujalu dagani
sannan shima ya juya a fusace ya nufi nasu
sansanin * * = bayan kowa ya huta hankalo ya
dawo jiki: wato kawar da yunwa da kishirwa:
MULAIFA da inmal na zaune a cikin tanti suna
hutawa har izuwa tsawon lokaci daynsu bai ce
uffan ba sai inmal yayi gyaran murya yana mai
dubeta yace yake abar kaunata; kiyi sani cewa
a yau ya da uba sun yi matukar shammatata
89

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma sun bani mamaki: ashe keda sarki kuna
da gagarumar jarumtaka haka amma ban taba
sani ba? To wau shin dama kuna karbar horon
yaki ne a boye batare da kowa yasani ba???
Koda jin wannan tamb&ya sai gimbiya mulaifa
tayi dariya sannan tace ni kaina ban taba sani
cewa mahaifina yana da irin wannan
gagarumar jarumtakar ba: Amma tawa
jarumtakar na sameta ne daga wajen wanda ya
ko ya maka

Koda jin wannan batu sai inmal ya sake
mamaki ya dubi mulaifa cikin alamun rashin
yarsa da batunta yace haba masoyiyata ya ya
zaki min da wani zance na rainin hankali?
Yaushe mahaifina ya kooya miki yaki amma ko
sau daya ba taba gani ba alhalin ke boyeki ma
ake yi a cikin gidan sarauta babu wanda ya isa
ya je kusa dake? Sa adda mulaifa taji wannan
batu sai ta bushe da dariya sanan tace yakai
abin kauna kayi sani cewa mahaifinka bashi da
iyaka a cikin gidanmu face daki guda daya wato
dakin da maigirma darbuza yake: Ba zan taba
mancewa da ranar da mahaifika ya fara koya
90

TASKARNOVELS.COM.NG
mini yaki na: Abun ya faru ne a wani yammaci
ina zaune a cikin farfajiyar turakata a cikin
lambu ina shakatawa cikin nishadi ina kallom
furaanni da kananan tsutsaye wadanda aka
killace acikin kanannan kejina suna ta dan
tsattsage tsattsagesu a ciki abin gwanin ban
sha awa kasancewar su kyawawan tsutsaye
masu launin jiki kala kala. Kwatsam Ina cikin
wannan hali sai na hango marigayi shi kadai ya
durfafo cikin lambun

Nan take na mike tsaye da sauri na ruga
gareshi ina mai risinawa cikin biyayya da nufin
na duka na gaishe shi amma sai yai sauri ya
kama kafaduna ya tasheni tsaye yace haba
ranki yadade a ina kika taba ganin ubangida ya
dukawa bawansa? Koda naji wannan tambaya
sai na dubeshi a cikin mamaki nace ya kai
abkin abbana hakika kabani mamaki domin
ban taba zaton cewa wannan kalma zatafito ba
daga bakimka duk da cewae nasan a halin
yanzu mahaifina baya girmamaka kuma baya
janka a jikinsa na san cewa kana da babban
matsayi a wajensa wanda yakasance boyayyen
91

TASKARNOVELS.COM.NG
al amarin: Dajin wannan batu sai shima
marigayi ya cika da tsananin mamaki ya dubeni
yace dani mahaifinki ya taba baki balarin
matsauina ne wajensa??? Da jin haka sai na
girgiza kaina nace ko kadan bai taba gayamin
ba amma naga tarihin duk alakar da ke
tsakaninku ne acikin kundin tarihin rayuwarsa
wanda ya boyeshi acikin wata akwattu da ke
karkashin gadonsa na barci

Duk duniya babu wnda ya isa ya iya bude
wannan akwati sbda an kulleta ne da karfin
wadansu dalasimai na tsafi guda saba in da
daya: Dole sai mutm ya hadasu sannan zata
budu

Tun ina da shekara shida a duniya nake jin
sarki yana karanta wadannan dalasimai na tsafi
kullum da tsakiyar dare a cikin turakarsa kuma
baya daga murya a duk sa adda zai karantasu
sai dai na jiyoshi kamar yana yiwa wani rada

92

TASKARNOVELS.COM.NG
Tun a sannan na ke
End Ads