da karagar mulkinsa a hannunku.
Take anan zan kashe ka sannan na tafi can
Birnin Kufa na kashe wannan azzalumar
mahaifiyar taka wacce ta yi kwacen karagar
mulki". Kafin Ziya'ul Hak ta gama rufe bakinta
tuni Jarumi Shaddadu ya tari num fashinta yana
mai daka ma ta tsawa ya ce, "Ke saurara 'yar
babban munafuki, Shugaban azzalumai na
duniya. Idan ba ki san tarihin waye ubanki ba to
ki koma wajensa ki nemi sani. Ina mai sanar
da ke cewa mahaifinki Laffaru a da can lokacin
da yai Sarauta a Birnin Kufa babu wani Sarki da
ya fi shi zalunci a Nahiyar gabadaya, kuma babu
wanda ya fi shi karfin dantse da jarumta.
Mahaifin ki ne ya kashe mini Kakannina da
dukkan zuri'arsu, kuma shi ne ya yi wa
mahaifiyata fyade har aka sami cikina. Kin ga ke
nan ke 'yar uwata ce amma a yau babu wadda
na tsana a doron kasa sama da ke". Koda
Shaddadu ya zo nan a zancensa sai kwallar
takaici ta cika masa idanu har hawaye ya
223
TASKARNOVELS.COM.NG
subuto masa daga cikin kwayar idanunsa bai
sani ba. Sa'adda Ziya'ul Hak ta ji wannan
jawabi sai jikinta yai sanyi ta fara tunanin cewa
hakika mahaifinta bai kyauta ba. Koda Aljani
Maruful Dauwaz ya fahimci cewar wannan batu
na Shaddadu na neman karya zuciyar Ziya'ul
Hak sai ya kira sunanta, ta waigo ta dube shi
sannan ya ce, "Ya ke abar kaunata, kada ki yi
amfani da kalmomin abokin gabarki ya yaudare
ki da su ya hallaka ki a banza. Ina mai tabbatar
miki da cewa har abada makiyi, makiyi ne ba zai
taɓa zama masoyinki ba." Maruful Dauwaz ya
dubi Shaddadu ya ce, "Kai yaro, ka yi sani cewa
abin kunya ne ni da Ziya'ul Hak mu hada karfi
mu yake ka tunda ni ba sa'anku ba ne, Ziya'ul
Hak ce daidai da kai saboda haka duk ku ajiye
sihirin tsafinku a gefe daya ku yi karon batta da
tsagwaron karfin dantsenku domin ku fid da
raini a sami daya daga cikinku ya kawar da
kishirwar gabar da ke tsakaninku tun ta iyaye."
Lokacin da Jarumi Shaddadu yaji wannan batu
sai ya tuntsure da dariya ya ce, "Kuna son ku
raina mini hankali ne. Babu wata dabara wacce
za ku zo mini da ita ko yaudara ku sami nasara a
kaina kawai kowa dabararsa ta kwace shi".
224
TASKARNOVELS.COM.NG
Kafin Aljani Maruful Dauwaz ya Rara fadin wani
abu tuni Ziya'ul Hak ta zare Takobinta ta falfala
da gudun tsiya kuma gudun tsafi izuwa kan
Shaddadu. Ai kuwa shima sai ya daga Mashin
Galilul Haras ya ruga izuwa kanta. Cikin
dimaucewa Aljani Maruful Dauwaz yai sama
izuwa kan Ziya'ul Hak domin ya sure ta don
kada ayi wannan gumurzu. A daidai wannan
lokaci ne Shaddadu ya kawo wa Ziya'ul Hak
mummunan duka aka da Mashin Galilul Haras,
ita kuma ta kai masa suka a gefen kirjinsa.
Cikin bakin zafin nama Maruful Dauwaz ya
dauke Ziya'ul Hak Mashin bai same ta ba amma
sai ya sami kafadar Maruful Dauwaz, nan take
kashin kafadar tasa ya karye, ya kwarara wani
uban ihu mai tsananin firgitarwa ya fadi kasa
sumamme. Shi kuwa wannan wawan suka da
Ziya'ul Hak ta kaiwa Shaddadu ya yi kokarin
kaucewa sukar da cikakken zafin namansa
amma duk da haka sai da kaifin Takobin ya
farka rigar jikinsa ya yanke shi a dantsen
hannunsa jini ya yi tsartuwa, ya kwalla ihu kuma
Takobin tata ta buge Mashin nasa. Ai kuwa sai
Mashin yai tsalle sama ya fada can kasan wani
rami mai tsananın zurfi da fadi wanda
225
TASKARNOVELS.COM.NG
karshensa ruwan korama ne yake gudu. Cikin
tsananin bakin ciki Jarumi Shaddadu ya yunkura
zai ruga ya fada cikin ramin don dauke
Mashinsa na Galilul Haras amma sai Ziya'ul Hak
ta daka tsalle ta sha gabansa suka sake
kacamewa da azababben Yaki a lokacin ne ya
yi wuf ya zare wadansu gajerun adduna guda
biyu suka rinka kai wa junansu sara da suka
cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta. A
daidai wannan lokaci ne wadannan Dakan guda
arba'in wadanda suka sume sakamakon Aljani
Maruful Dauwaz suka farfado. Koda suka ga
irin masifaffen Yakin da ake yi tsakanin
Shaddadu da Ziya'ul Hak sai suka cika da
tsananin al'ajabi domin ba su taɓa ganin
Jarumai masu irin wannan Jarumta ba kuma Har
i zuwa wannan lokaci Aljani Maruful Dauwaz bai
farfado ba. Nan fa su Shaddadu suka ci gaba
da BAKIN ARTABU. Duk sa'adda makamansu
suka hadu sai dai ka ga tartsatsin wuta na tashi.
Sai da suka shafe sa'a uku da rabi suna wannan
bakin gumurzu. Da kyar da sidin goshi shi ma
Shaddadu ya samu nasarar yankar Ziya'ul Hak a
cinyarta, take wajen ya dare jini yai tsartuwa ta
durkusa kasa tana mai kwalla ihu. Ba tare da ta
226
TASKARNOVELS.COM.NG
yi yunkurin tsai da jinin ba ta daka tsalle sama
cikin tsananın fushi domin ta fillewa Shaddadu
kai. Ai kuwa shi ma sai ya daka tsallen sama
suna haduwa suka gwara fuskokinsu. Take
kowannensu hancinsa da bakinsa ya fashe
suka rikito kasa a cikin wani irin mugun yanayi
mai kama da gushewar hankali, ba su san
Sa'adda suka saki makaman Yakin da ke
hannunsu ba. Ai kuwa sai makaman suka
gangara izuwa cikin wannan rami mai zurfin
gaske wanda Mashin Galilul Haras ya fada.
Lokaci guda duk su biyun suka mike zumbur
Suka tsinci kansu daf da bakin wanna rami.
Suna lekawa kasan ramin sai Shaddadu ya
hango Mashinsa akan ruwa yana tafiya. Nan
take ya daka tsalle izuwa kasan ramin ba tare
da jin tsoron zurfin ramin ba da kuma duwatsun
da ke cikinsa. lta ma Ziya'ul Hak sai ta daka
tsallen ta bi shi zuwa kasan ramin domin ta
hana shi samun damar dauko Mashin saboda ta
san cewa da zarar ya dauko Mashin take zai
sami ikon hallaka ta. Shi da ita sai suka kama
kwala ihu sakamakon razanar da suka yi bisa
ganin zurfin ramin da suka yi kudunbalar
faďawa. Tun kafin su isa kasan ramin, karamin
227
TASKARNOVELS.COM.NG
jiri ya fara dibarsu. Ai kuwa suna isowa cikin
koramar da karfi ji kake fanjam! Sai suka nutse
kasan ruwan. Ta ke duk su biyun kawunansu
ya bugu da duwatsu kowannensu ya sume,
kasancewar jikinsu ya sandare sakamakon sun
nutse izuwa ruwan sai suka taso izuwa saman
ruwa. Nan kuwa igiyar ruwa ta raba su.
Shaddadu ya yi yamma, ita kuma Ziya'ul Hak ta
yi gabas, ruwa ya yi ta tafiya da su. A daidai
wannan lokaci ne Aljani Maruful Dauwaz ya
farfado daga dogon suman da ya yi Koda ya
yunkura domin ya mike zaune sai ya ji ya kasa
sakamakon kashin kafadar tasa da ya karye.
Cikin tsananin juriya ya kama kashin da ya karye
wanda lankwashewa ya yi kasa ya dagoshi
sama yana mai tsandara uban ihu saboda
tsananin zafi da zogin da ya ji. (Maza gumbar
dutse) Wannan uban ibu da ya yi ne ya sa
wadannan Dakaru suka sake zubewa kasa
sumammu a karo na biyu saboda tsananin
dimaucewa. Aljani Maruful Dauwaz ya mike
tsaye a dimauce ya kama dube-dube da waigewaige a wajen amma bai ga gawar Ziya'ul Hak
ba ko ta Shaddadu. Al'amarin yal matukar
dugunzuma hankalinsa ke nan kuma zuciyarsa
228
TASKARNOVELS.COM.NG
ta kama tafarfasa saboda fishi Nan take ya
cika da mamakin yadda aka yi ya sume nan take
saboda an doke shi da Mashin Galilul Haras.
Haka kuma ya tuna alkawarin da ya daukarwa
iyayen Ziya'ul Hak cewar zai kare lafiyarta
amma kuma ga shi ya kasa. Maruful Dauwaz
ya tuno da irin tsananin jarumtakarsa da
tsananin karfin dantsensa amma yau duk sun
zama na banza tunda ga shi yaro karami ya yi
masa kwaf daya. Nan take takaicì ya rufe shi har
kwallar bakin yi ciki ta zubo masa. (Kamar ya
manta da tasirin mashin GALILUL HARAS)
Cikin matukar karfin hali Maruful Dauwaz ya
mike tsaye ya bude fuka-fukansa yai sama yana
leken kasa, ai kuwa sai ya hango Hular karfen
da Ziya'ul Hak ta sa akan saman ruwan wannan
korama yana tafiya da ita. Cikin gaggawa ya
sauko kasa-kasa daf da ruwan koramar ya fara
shawagi yana neman Ziya'ul Hak kuma yana
kwalla mata kira amma bai ganta ba kuma bai ji
duriyarta ba. Al'amarin da ya kara dugunzuma
hankalinsa ke nan kuma ya daďa dimaucewa,
ya sauko ya fada cikin ruwan ya yi nutso izuwa
karkashin ruwan koramar yana dube-dube ko
zai ganta. Su kuwa Dakarun Sarauniya
229
TASKARNOVELS.COM.NG
Zubaina lokacin da suka farfaďo sai suka sake
firgicewa a karo na biyu, suka dubi gabas da
yamma, kudu da arewa ba su ga Aljani Maruful
dauwaz ba sai suka mike tsaye suka cika
wandunansu da iska suka durfafi fada domin su
kai labarin abin da ya faru. **** Lokacin da
Jarumi Shaddadu ya suma a cikin wannan
ruwan korama sakamakon buguwar kansa a
dutse har ya taso sama igiyar ruwa ta tafi da shi.
sai da ruwan ya yi tafiyar kimanin sa'a daya da
rabi da shi sannan ya kawo shi daf da bakin
gaɓar wani kogi ya tunkudo shi waje. Ashe tun
lokacin da aka fito farautarsa daga fada tare da
saurayin mafarauci mai Kare labari ya riski
karuwa Yaldisa. Koda jin wannan labari sai
hankalin Yaldisa ya dugunzuma domin tun
bayan rabuwarta da Shaddadu ta kasa samun
sukuni sakamakon kamuwa da tsananin sonsa
da begensa a cikin zuciyarta. Ai kuwa tana jin
wannan labari ta fito da gudu daga cikin gidanta
ta zo kofar fada ta labe. A gaban idanunta
mafarauci mai Kare tare da Dakaru arba'in suka
fito daga cikin gidan Sarautar a guje suka nausa
cikin gari. Ai kuwa sai ta bi su da sauri tana
buya ba tare da sun sani ba har suka iso wajen
230
TASKARNOVELS.COM.NG
bishiyar nan inda Jarumi Shaddadu ya bayyana
aka kama fafatawa. Duk wannan gumurzu
akan idanunta aka yi shi tana laɓe a bayan wata
bisiya tana kallo. Koda ta ga Jarumi Shaddadu
da Jaruma Ziya'ul Hak sun fada cikin wannan
rami mai zurfin gaske sai hankalinta ya
dugunzuma ta fara kuka domin a tunaninta
Shaddadu ya mutu. Da ma a wannan lokaci
Dakarun Sarauniya Zubaina da Aljani Maruful
Dauwaz duk suna kwance a sume. Abin ka da
dan gari, koda Yaldisa ta hango Shaddadu ya
fada wannan rami sai ita ma ta juya da aya ta bi
wata hanya dabam da gudu. Tana gudun tana
kuka har ta iso cikin wata gangara mai
kwazazzaɓai da ruwa. Ta cikin ruwan ta bi da
gudu, ai kuwa sai ga shi ta bullo karshen
wannan rami mai zurfi wanda su Shaddadu
suka fado. Idonta a rufe kuma ba tare da
shakkar komai ba ta daka tsalle ta fada cikin
koramar ta kama iyo a cikinta tana neman
Shaddadu Sai da ta shafe kusan rabin sa'a a
cikin koramar har ta je bakin gaba ba ta ga
Shaddadu ba. Ga shi a wannan lokaci ta gaji
ainun tana haki da numfarfashi sama-sama
kamar ranta zai fita. Tana durkushe a gaban
231
TASKARNOVELS.COM.NG
koramar ruwa ya kado gangar jikin Shaddadu
dai-dai inda take. Koda ta yi arba da shi sai ta
kara kanta a kirjinsa. Take ta ji alamar numfashi
dan kadan. Cikin tsananin murna ta yunkura ta
mike tsaye kuma ta sunkuce shi ta dora a
kafadarta ta runtuma da gudu izuwa cikin daji.
Lokacin da aljani Radiyan ya zo nan a labarinsa
sai yayi shiru ga barin zance mai dadi saboda
gajiyar surutu. Cikin tsananin damuwa gimbiya
Hursiyya ta dubeshi tya ce haba ya kai Radiyan,
saboda me zaka katse mani wannan labari mai
dadin sauraro, mai dauke da abubuwan al'ajabi
gami da ban tsoro a daidai lokacin da dadinsa
yayi yawa kuma aka zo daidai inda za raba
gardamar gaba ta shekara da shekaru, wai shin
ma ya ya akayi kasancewa dan uwana sarki
dujalu ya soma bani wannan labari na mazan
jiya kuma har kasan daidai inda ya tsaya a
labarin nasa ka dora. Lokacin da aljani Radiyan
ya ji wadannan tambayoyi guda biyu sai ya
bushe da dariya sannan ya ce tsananin bincike
nane a hallarar tsafina yasa naga dukkanin
binda ya faru tsakaninki da dan uwanki sarki
dujalu, sannan ni yanzu na gaji da surutu ne
shiyasa na yanke maki wannan labari yanzu.
232
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin haka sai Hursiyya ta sake duban aljani
Radiyan cikin tsananin damuwa kamar zata yi
kuka tace ina mai rokonka da ka yi mani
alkawarin cewar zaka karasa mani wannan
labari har izuwa karshensa, in ya so idan muka
isa sansanin yaki na iske dan uwana sarki
dujalu a raye sai ya bani labarin Sadauki Hulkas
na Birnin Romaniya bayan an kammala yaki.
Kod jin wannan batu sai aljani Radiyan yayi
ajiyar zuciya sannan y ce Tabdijan lallai dan
adam da buri ya ke, yanzu ke har kina sa ran
cewa dan uwanki zai rayu a wannan masifaffen
yuaki da ake yi? To bari kiji ni kaina yanzu na
karamin ganganci nayi ba, dana karbi kwangilar
kawoki wannan tsubiri na kogin bahar sufiya,
abune mawuyaci duk wanda ya rabi wannan
kogi ya iya tsira d rayuwarsa. Hursiyya tayi
guntun murmushi sannan ta ce ina farin ciki zan
mutu a kusa da dan uwana sarki dujalu
maimakon na mutu a hannun makiyansa wato
fadawansa, wadanda a halin yanzu kokari suke
yi suyi masa juyin mulki. Cikin tsananin
mamaki aljani Radiyan ya dubi Hursiyya ya ce
yaya aka yi kika san wannan al'amari? Hursiyya
ta yi murmushi a karo na biyu ta ce ai kasan an
233
TASKARNOVELS.COM.NG
ce ba idone kadai yake gani ba hankali shime ke
masa jagora wajen gani. Tunda aka dawo dani
daga sansanin yaki na zuba ido akan fadawan
sarki dukkan wani motsi nasu in sane da shi,
koda ta zo nan a cikin bayaninta sai ta yi ajiyar
zuciya sannan ta cigaba da cewa ya kai wannan
boka ni a yanzu na gaji da zama a cikin wannan
wawakeken kunnnen aljanin, in bukatar na
wasa kafafafuna a bisa turba mai dauke da iska
da korayen ganyayyaki. Kafin Hursiyya ta gama
rufe bakinta sai kawai suka ji aljani Raugatul
Agwan ya saki fuka-fukansa ya sauko lasa luuu
daga can kololuwar sama, kfin cikar dakika dari
da ashirin sai gashi ya dira bisa turba. Nan take
boka sadusa haryal da shalbirat suk sauko daga
kansa suka tsinci kansu a cikin wani
kyakkyawan daji mai yawan ni'ima, domin yana
dauke da bishiyu iri-iri, da kuma koramai,
dabbobin daji ma gasu nan manyansu da
kanana. Koda muggan dabbobi sukaga su boka
sadusa sai suk tarwatse suk bar dajin gaba
daya, hatta tsuntsaye dake kan bishiyu sai da
suka yi kaura daga dajin gabadaya suka kama
guje-guje kai kace wata annoba ce ta barko
cikin dajin. Nan take aljani Raugatul Agwan ya
234
TASKARNOVELS.COM.NG
samu guri mai yalwatacciyyar ciyawa ya kwanta
domin ya dan huta. Cikin tsananin mamaki
boka sadusa ya dubeshi yace da shi kai dai ka
cika lalaci, yanzu yar wannan tafiyar da muka yi
shine sai ka kwanta ka huta? To wai shinma
wannan wane daji ne haka kazo ka ajiyemu a
cikinsa? Koda jin haka sai aljani Raugatul
Agwan ya dubi boka sadusa cikin takaici da
mamaki yace hakika ni dai a rayuwata ban taba
ganin mahaluki mai rainin wayo kamar
biladama ba, yanzu wannan tafiyar da mukayi ta
tswon kwana casa'in da uku a cikin abinda bai
wuce sa'a bakwai ba shine kake kiranta da yar
tafiya, kai fa yanzu ko yankaka za a yi ba zaka
iya kawomu nan ba a cikin shekara guda koda
kuwa da karfin sihirin tsafinka ne, to ka sani
cewa rabon da nayi doguwar tafiya ta rabin sa'a
ma yau shekara goma sh tara kenan, tinda na
sato kyakkyawa Shalbirat sa'ad dana kawota
dajina na darul hushushil maut, game da
tambayarka akan wannan dajin kuwa nima ban
san kowane daji bane tunda ban taba jin an
kirashi da wani daji ba, amman dai abinda na
sani shine daga nan zuwa kogin bahar sufiya ba
zai wuce tafiyar sa'a uku da rabi ba jal ba,in mai
235
TASKARNOVELS.COM.NG
dada yi maku tuni da cewa ni ba zan kaiku har
bakin kogin bahar sufiya ba, sai dai na ajiyeku
da tazarar zira'i dari daga tekun. Boka Sadusa
yayi dariya sannan ya ce ai mun san da haka,
amman dai kada ka manta da cewa mun taho
da kai ne domin ka yi mana leken asiri kuma ka
gano mana matsayin da yakin ke ciki. Aljani
Raugatul Agwan ya ce na san da haka amman
dai ni bazan yarda naje inda za a iya hangoni
daga can sansanin yakin ba, yanzu dai zan
kwanta bacci na tsawon sa'a bakwai kada
wanda ya tasheni har sai wannan lokaci ya cika
sannan sai na debeku na tafi da ku can din,
lallai zamu isa can a lokacin da dare ya fara,
sannan za muje a lokacin da yafi dacewa sa'ad
da duhun dare ba zai bari a hangomu ba. Koda
gama fadin haka sai aljani Raugatul Agwan ya
kishingida, kwanciyarsa keda wuya sai bacci
yayi awon gaba da shi ya kama shara uban
minshari tamkar ya kwana arba'in yana bacci. A
sannan ne Boka Sadusa, Halyal da shalbirat
suka shiga kokarin kafa tanti, bayan sun gama
kafa tantin sunyi shimfida sai suka fito da
abincin guzurinsu suka ci, abinka da gajiyayyu
nan da nan suma bacci sai ya sace su. Ashe
236
TASKARNOVELS.COM.NG
duk abinda ke faruwa Boka Radiyan da Gimbiya
Hursiyya na gani domin sun zo kofar kunnen
Raugatul Agwan suna kallonsu, koda suka ji tsit
alamar cewa suma su Boka Sadusa sunyi bacci,
sai suka fito daga cikin kunnen aljani Raugatul
Agwan uka fara kokarin sakkowa kasa, wanda a
kokarin haka ne Hursiyya bata lura ba ta tsikari
idon aljani Raugatul Agwanu da kafarta, ai kuwa
sai Raugatul Agwanu ya kai duka da hannunsa
izuwa kan idon. In ba don aljani Radiyan ya
sureta sun rikito kasa tare ba da tuni ta
ragargaje. Kawai sai sukaga aljani Raugatul
Agwanu ya muskuta ya gyara kwanciya kuma ya
cigaba da baccinsa tamkar ace mutum ne yake
bacci kuda ya dameshi ya kureshi. Nan dai
Boka Radiyan da Gimbiya Hursiyya suka mike
tsaye suka kama tafiya cikin sanda dan kada su
boka Sadusa suji motsinsu, a haka suka nausa
cikin daji. Lokacin da suka yi nisa daga inda su
aljani Raugatul Agwanu suke, ya zamana cewa
basa iya hangosu, sai suma suka tsaya tare da
zama a karkashin wata bishiya domin su huta.
Gimbiya Hursiyya ta bude jakar guzurinta ta
dauko abinci ta kama ci, sai da ta koshi sannan
ta daga battar ruwa ta sha, kawai sai aljani
237
TASKARNOVELS.COM.NG
Radiyan ya dubeta ya bushe da dariya.
Al'amarin da yayi matukar bata mamaki kenan,
ta dubeshi a fusace ta ce mene ne abin dariya
anan? Aljani Radiyan ya ce gani nayi kudai
bil'adama abu abinda yake wahalar da ku sama
da cikinku, n fuskanci cewa da yawanku idan
baku ci abinci ba sau uku a rana bakwa samun
kwanciyar hankali, sabanin mu aljanu da idan ta
kama sai muyi shekara da shekaru babu ci da
sha kuma mu rayu. Kamar yadda aljani
markahussabus ya rayu shekaru dari uku da
wani abu a cikin akwati, sa'ad da wani
mashahurin matsafin sarki ya tsare shi a cikin
wani kurkuku na karkashin kasa. Koda jin
wannan batu sai gimbiya Hursiyya ta gyara
zama tana mai tattara hankalinta gabadaya
akan aljani Radiyan tana mai cewa wane ne
kuma Aljani Markahussabus? Koda jin Wannan
tambaya sai aljani Radiyan ya sake bushewa da
dariya a karo na biyu sannan ya ce To sarkin jin
labari, ai sai dai kije ki nemi wani littafi mai suna
KUNDIN TSATSUBA a cikinsa ne zaki samu
labarin sarkin jaruman aljanu na duniya, wato
Markahussabus wanda yayi gadon jarumtaka a
wajen ubansa Larkul. Koda jin haka sai
238
TASKARNOVELS.COM.NG
Hursiyya ta murtuke fuska ta yi shiru bata ce
komai ba, a lokacin da ta dan kishingida tana
tunani. Daga can kuma sai ta dubi aljani
Radiyan ta ce wai shin yanzu da ka janyomu nan
muka yi nisa da su aljani Raugatul Agwanu idan
kuma suka tashi suka tafi bamu sani ba, ta yaya
zamu karasa can bakin kogin bahar sufiya? Da
jin wannan tambaya sai aljani Radiyan ya ce
ashe ma ke duk hirar da su aljani Raugatul
Agwanu suke yi dazu baki saurara ba, ai
Raugatul Agwanu ya ce daga wannan daji zuwa
bakin kogin bahar sufiya bai wuce tafiyar sa'a
daya da rabi ba, kinga kenan zamu iya karsawa
da kanmu, kuma idan bamu rabu da su anan ba
asirinmu zai iya tonuwa har su ganmu. Idan
kuwa suka ganmu to tabbas tamu ta kare dan
nasan cewa kashemu z su yi, yanzu dai abinda
nake so dake shine ki tashi mu cigaba da tafiya
tunda