x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - MAZAN JIYA 4

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 68055 words

Category: Adventure Stories

Views 186

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ke wannan Almajira tunda dai
na ga kina da kokarin yawo a garin nan sai ki
zuba ido da kyau da zarar kin ga bakon Jarumi ki
hanzarta zuwa nan inda muke zama ki zo ki
sanar dani tunda kin ga ni na fiki kwarin jiki sai
na garzaya fada na sanar da sarauniya. Na
yarda ki sam mini ladan da Sarauniya za ta
bayar ba sai mun yi raba dai-dai ba. Ni burina
kawai shi ne, a kama wannan Saurayi saboda ya
ci mutuncin garin nan kuma ya keta alkadarin
Sarauniya. Sa'ad da tsohuwar Almajirar ta ji
wannan batu sai ta numfasa ta ce. "Babu komai
lallai zan yi kamar yadda ka bukala. Amma ina
da tambaya a gare ka. Wai shin me ya sa dazu
207

TASKARNOVELS.COM.NG
ka kare ni a wajen Sarauniya har ka fadi sunan
wani kauye ka ce daga can na zo alhalin ni ban
ma taba jin sunan kauyen ba?" Koda jin
wannan tambaya sai tsohon ya numfasa ya ce.
"Ai abokin barawo, barawo ne. Inda Sarauniya
ta kama ki da wani laifi to da gabadayanmu
laifinki ya shafe mu mu duka. kin ga ke nan,
dukkaninmu 'yan uwan juna né daga yau mun
zama abokai". Koda gama fadin hakan sai
tsohon ya bushe da dariya ya mikawa tsohuwar
hannu da nufin su gaisa, amma sai tsohuwar ta
noke ta ki ta ba shi nata hannun. Kawai sai ta
mike tsaye da kyar tana dogara sandarta ta
dube shi ta ce, "Ka yi hakuri ba na taba jikin
namiji, sai mun sake saduwa". Koda gama
fadin hakan sai tsohuwar ta juya ta nausa cikin
gari rike da dan kokonta tana mai ci gaba da
bara. Shi kuwa tsohon sai ya bi ta da kallo
kawai yana mamakin wannan kalma da ta gaya
masa. Bai daina kallon tsohuwar ba har sai da
ta bace masa da gani sannan shi ma ya mike
tsaye ya kama hanya ya nufi can bayan gari.
Tohon ya ci gaba da tafiya har sai da ya shiga
daji ya iso gaban wata bishiya sannan ya rikiďe
zama Jaruma Ziya'ul Hak. A daidai wannan
208

TASKARNOVELS.COM.NG
lokaci Aljani Maruful Dauwaz ya fito daga cikin
wata duhuwa da sauri ya dubi ziya'ul Hak cikin
damuwa ya ce, Mene ne labari? Shin ba ki ga
abokin gabar tamu ba ne?" Ziya'ul Hak ta yi
ajiyar zuciya cikin alamun damuwa da takaici ta
ce, "Ai na zagaya garin nan kaf ina neman
Shaddadu amma ban gan shi ba. Kai a takaice
ma dai ita kanta Sarauniyar garin nan nemansa
take ruwa a jallo saboda ya aikata babban laifi
ya shigo gari babu izini ya ɓalla kofar garin kuma
ya yi wa Dakarunta dukan tsiya". Nan dai
Ziya'ul Hak ta ci gaba da bai wa Aljani Maruful
Dauwaz labarin duk abin da ya faru tun daga
lokacin da ta ɓatar da kamanninta ta zama
tsoho ta shiga cikin garin tana neman Shaddadu
kawo izuwa sa'adda ta je ta zauna a gefen
hanya cikin almajirai har wannan bakuwar
almajirar ta zo, da yadda suka rabu da almajirar
a karshe bayan tafiyar Sarauniya Zubaina."
Koda jin wannan labari sai Aljani Maruful
Dauwaz ya dafe kai cikin tsananin bakin ciki
kamar zai yi kuka sannan ya dubi Ziya'ul Hak ya
ce. "Kaico! Kin yi asarar babbar dama wacce
yakamata ki yi amfani da ita wajen kashe abokin
gabarki. Ai wannan tsohuwar almajirar da kika
209

TASKARNOVELS.COM.NG
taimaka ba tsohuwa ba ne face Jarumi
Shaddadu. Koda jin haka sai Ziya'ul Hak ta
zazzaro idanu ta dubi Maruful Dauwaz cikin
mamaki ta ce, "Yaya aka yi ka gane cewar
tsohuwar Shaddadu ne?" Maruful Dauwaz yai
ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ai bisa binciken da
muka yi ni da iyayenki kafin mu baro su mun
gano cewa Sharlis ta cire wa Shaddadu sha'awa
irin ta 'ya mace tun yana yaro karami, don haka
ba zai taba yarda ya taɓa jikin 'ya máce ba.
Duk da cewar kina cikin siffar namiji, kuma
tsoho, ba zai gaisa da ke ba domin shi bai yarda
da kowa ba a cikin garin. Yana daga cikin
makarin sihirinsa idan har ya taba jikin 'ya mace
da hannunsa. Wannan sandar da kika gani a
hannun tsohuwar tana dogarawa ba sanda ba
ce Mashin Galilul Haras ne wanda mahaifiyarsa
ta ba shi. In da kin shammace shi kin soke shi
da makami a wannan lokaci da take zai fadi ya
mitu saboda in dai ya batar da kamanninsa na
zahiri za ki iya yin tasiri a kansa. Koda Aljani
Maruful Dauwaz ya zo nan a zancensa sai
Jaruma Ziya'ul Hak ta yunkura da sauri a fusace
da nufin ta ruga izuwa cikin gari, amma sai
Aljani Maruful Dauwaz yai caraf ya ruko ta ya ce,
210

TASKARNOVELS.COM.NG
"Ina kuma za ki je?" Ziya'ul Hak ta ce, "Neman
Shaddadun zan tafi tunda na gane irin yanayin
da yake". Koda jin haka sai Maruful Dauwaz ya
bushe da dariya sannan ya ce, "Yaro man Kaza.
Hakika masu iya magana sun yi gaskiya da suka
ce, "Wanda ya riga ka kwana dole ne ya riga ka
tashi". Ina so ki sani cewa Shaddadu ya ri ga ki
zuwa wannan duniya tunda ya girme ki da kusan
shekaru hudu. Don haka dole ne ya fi ki wayo.
Ina mai tabbatar miki da cewa yanzu dole ne ya
sauya siffarsa don haka abu ne mawuyací ko
kun hadu ki gane shi. Kada ki manta cewa
farautar juna kuke yi kamar yadda kike
nemansa haka shi ma yake nemanki ruwa a
jallo. Ina mai dada yi miki tuni da cewar kada
ki yarda ki Yaki Shaddadu muddin yana tare da
wannan Mashi nasa na Galilul Haras. Idan kuwa
kika yi gangancin aikata hakan ta farat daya zai
sami nasarar hallaka ki." Lokacin da Aljani
Maruful Dauwaz yazo nan a zancensa sai jikin
Ziya'ul Hak ya yı sanyi ta yı shiru tana tunani,
daga can kuma sai ta dago kai ta dubi Maruful
Dauwaz ta ce, "Ya kai babban masoyi yanzu
mene ne abin yı? Ya za a yi na gane Shaddadu
da zarar na hadu da shi?" Maruful Dauwaz ya
211

TASKARNOVELS.COM.NG
numfasa ya ce, "Hanya daya ce, sai dai mu
shiga cikin garin tare ni da ke, domin ni duk irin
yanayin da zan gan shi sai na shaida shi, to
amma kuma ni ma dole ne na juye izuwa
kamannin Bil'adama. Koda jin wannan batu
sai farin ciki ya lullube Ziya'ul Hak ta ce, "Ai shi
ke nan ta kwana gidan sauki, sai ka zo mu koma
cikin garin domin mu gaggauta gabatar da abin
da ya kawo mu. Burina shi ne m, mu kashe
Shaddadu kuma mu raba shi da Mashin Galilul
Haras sannan mu tafi da iyayena can Birnin
Kufa mu kashe mahaifiyar Shaddadu domin na
kwatowa mahaifina Sarautarsa". Koda jin
wannan batu sai Aljani Maruful Dauwaz ya shiga
yi wa Ziya'ul Hak kirari yana mal cewa, "Haka
ake son 'ya ta gaji ubanta wajen ra'ayi da taurin
zuciya gami da jarumtaka". Ba tare da ɓata
lokaci ba Ziya'ul Hak ta yi girgiza ta zama
saurayi wanda bai fi shekara ashirin da biyu ba
a cikin shigar mafarauta. Shi kuma Aljani
Maruful Dauwaz sai ya yi girgiza, take shi ma ya
rikide ya zama wani kyakkyawan Kare. Nan take
saurayin ya ruga da gudu izuwa cikin gari, Karen
ya rufa masa baya suna tsala zababben gudu
tamkar za su tashi Sama. * Al'amarin Jarumi
212

TASKARNOVELS.COM.NG
Shaddadu kuwa, lokacin da ya baro wajen
Almajirai masu bara a gefen hanya ya zamana
cewa ya yi nisa da su har ya shiga wani bangare
daban inda babu mutane, sai ya rikida ya sauya
siffa ya zama tsaleliyar budurwa cikin shigar
Yaki, wannan sanda tasa kuwa sai ta rikide ta
zama garkuwa kuma ga Takobi a rataye à
kafadarsa. Budurwar na sanye da Hular karfe
idanunta kadai ake gani. Tsawon budurwar da
kaurin jikinta in daya ne sak da na Sarauniya
Zubaira, kai hatta kayan Yakin irin nata ne.
Bayan Shaddadu ya gama rikidewa izuwa cikin
wannan siffa sai ya dauko madubin tsafinsa ya
shafe shi da hannun hagu, ya shiga bincike.
Nan take ya gano cewa ai tabbas Jaruma Ziya'ul
Hak na nan a cikin wannan gari kuma ita ma
tana farautarsa kamar yadda yake farautarta
ruwa a jallo. Al'amarin da ya matukar bashi
mamaki ke nan kuma ya dugunzuma hankalinsa
domin ya fuskanci cewa shi fa yanzu ya shiga
babban tarko tunda Sarauniya Zubaina na
nemansa kuma Ziya'ul Hak na nemansa kuma
kowacce a cikinsu so take ta hallakashi.
Shaddadu ya ci gaba da bincike a cikin madubin
tsafin nasa. Koda yai nisa a cikin binciken sai ya
213

TASKARNOVELS.COM.NG
gano cewa ashe wannan tsoho da ya hadu da
shi a wajen bara ba tsoho ba ne Jaruma Ziya'ul
Hak ce. Al'amarin da yai matukar fusata shi ke
nan ya ci gaba da bincike don ya gano a inda
wannan tsoho yake a sannan amma sai
madubin tsafin nasa ya kasa nuna masa komai.
Shaddadu ya ci gaba da nacin binciken amma
abu ya gagara. Bisa dole ya hakura ya mayar da
madubin tsafin nasa cikin aljihu sannan ya
kunna kai izuwa cikin garin. Duk inda ya gifta
sai ka ga mutane na zubewa kasa suna gaishe
shi domin gani ake Sarauniya Zubaina ce.
Haka dai ya ci gaba da yawo kwararo- kwararo,
lungu-lungu, duk inda ya hadu da Dakarunsa
masu yawon farautar bakon Jarumi sai su ma su
zube kasa su gaishe shi. Shaddadu ya ci gaba
da zagayawa duk inda ya je ga Almajirai sai ya
zuba musu idanu ko zai ga wannan tsoho
wanda suka hadu a wajen bara amma bai gan
shi ba *** Fada wacce ta karatu ainun da
kayan alatu domin komai na cikinta an yi shi ne
da zallar zinare da kuma lu'u-lu'u. Sarauniya
Zubaina na zaune akan karagar mulkinta
fuskarta a murtuke, kai da gani ka san cewa
ranta a bace yake. Kawai sai ta mike tsaye ta
214

TASKARNOVELS.COM.NG
kama kai kawo cikin fishi da kunan rai. Gaba
dayan fadawanta da Bokayenta na zaune sun
sunkuyar da kasu kas cikin alamun tsoro don
kada laifin wani ya shafe su. Kawai sai ta dube
su gaba dayansu ta ce, "Amma dai taron nan
naku duk ya zama na banza. Yanzu ace mutum
daya ya shigo garin nan ya zame mana matsala.
Tun jiya ake neman wannan bakon Jarumi
amma an rasa a inda yake alhalin kun yi bincike
kun gano cewar lallai yana nan a cikin garin nan.
To ku sani cewa idan har ba ku kamo wannan
Jarumi ba a yau gaba dayanku sai na sauke ku
daga kan mukaminku." Koda jin wannan batu
sai hankalin gaba dayan 'yan majalisar ya
dugunzuma suka kama rokon Sarauniya akan ta
yi musu sassauci. Har Sarauniya ta dube su za
ta daka musu tsawa sai kawai ta hango wani
bakon saurayi a cikin shigar mafarauta tare da
wani Kare biye da shi sun shigo fadar kuma sun
tunkaro inda take kai tsaye. Har Dakaru sun
yunkura za su tare saurayin sai Sarauniya
Zubaina ta yi musu nuni da su kyale shi. Ba
tare da fargabar komai ba kuwa wannan saurayi
ya ci gaba da durfafar Sarauniya sai da zo daf da
ita sannan ya zube kasa ya kwashi gaisuwa
215

TASKARNOVELS.COM.NG
sannan ya dago kai ya dube ta ya ce, "Ya
Shugabata ni mutumin kauyen JALRIS ne, kuma
yanzun nan na shigo garin nan. Na fito daga daji
domin yin farauta sai na sami labarin cewar
wani bakon Jarumi ya shigo kuma ya karya
dokokinki amma an kasa gane shi da gano inda
yake. To ni ya Shugabata ina mai tabbatar miki
da cewa a duk irin yanayin da wannan Jarumi zai
shiga in dai zan yi arba da shi sai na gane shi
kuma zan iya jagorar tafiya farautarsa". Koda
jin wannan batu sai Sarauniya Zubaina ta kamu
da tsananin farin ciki ta dubi Mafaraucin ta ce,
"Ai kuwa idan har ka taimaka aka kamo wannan
tsageran Jarumi sai na ba ka lada mai tsoka irin
wanda ba a taɓa bai wa wani ba a masarautata.
Yanzu Dakaru nawa kake bukata wadanda zan
ba ka su yi maka rakiya izuwa farautar wannan
Jarumi?" Mafaraucin ya ce. "Ai ba na bukatar
Dakaru da yawa ko mutum arba'in kika ba ni
sun isa domin na sanar da su dokokin farautar
Jarumin su kiyaye, amma idan suna da yawa ba
za a sami nutsuwa ba" Nan take Sarauniya
Zubaina ta sa aka waro Dakaru mutum arba'in
wadanda suka kasance zakwakuran Jarumai ta
bai wa wannan mafarauci sannan ta dube shi ta
216

TASKARNOVELS.COM.NG
ce. Nan da yaushe zan jira dawowarku tare da
wannan bakon Jarumi?" Mafaraucin ya ce,
lallai kafin faduwar rana za mu zo miki da
wannan mai laifi. Zubaina ta yi murmushin
farinciki sannan ta sallame su gabadaya suka
fice daga fadar. Nan fa labari ya bazu ko ina a
cikin garin cewar an tafi farautar bakon Jarumi
kuma za a zo da shi fada kafin faduwar rana.
Bisa wannan dalili ne jama'ar gari suka yi ta
tuttuɗowa izuwa fadar saboda kowa yana son
ya ga wannan takadarin Jarumi wanda ya zo ya
gagari Sarauniya da Dakarunta. Hakika masu
iya magana sun yi gaskiya da suka ce "Kifi na
ganinka mai jar Koma". Ashe lokacin da ake ta
yada wannan labari a cikin gari cewar wani
bakon mafarauci ya je fada kuma ya tabbatarwa
da Sarauniya Zubaina cewar zai kamo mata
bakon Jarumi kafin faduwar rana har ma ta ba
shi Dakaru sun bazama nemansa Shaddadu
ya ji a daidai lokacin da ya zo zai gifta wani layi,
wadansu matan aure ne guda biyu a tsaye suna
hirar. Koda jin wannan batu sai jikin Shaddadu
ya ba shi cewar lallai Ziya'ul Hak ce ta rikide
izuwa wannan bakon mafarauci domin in ba ita
ba babu wanda zai iya cewa zai iya yin
217

TASKARNOVELS.COM.NG
farautarsa. To amma idan har za ta iya farautar
tasa me ya sa wancan karon ba ta shaida shi ba
a lokacin da suka yi ɓad-da-kama duk su biyun
suka yi siffar Almajirai? Shaddadu ya numfasa
ya ce, "Amma kuma ai idan ka ji Makaho ya ce a
yi wasan jifa, to tabbas ya taka Hoge, don haka
lallai akwai abin da ta taka." Wata zuciyar
kuma sai ta ce da shi, "To wai shin me kake
tsoro ne alhalin mahaifiyarka ta tabbatar maka
da cewa in dai kana tare da Mashin Galilul
Haras babu wani mahaluki da ya isa ya sami
nasara akanka walau mutum ko aljan. Ai
wannan wata babbar dama ce ka samu da za ka
yi arba da Ziya'ul Hak tunda dole da ita za a fito
wannan farauta. Kawai ka tsaya a yi fito-na-fito
domin a yi ta-ta- kare. Koda gama aiyana
hakan sai Shaddadu ya rikide ya zama dan
karamin kwaron nan da ake kira Malam Buda
mana littafi ya tashi sama ya tafi izuwa kan wata
bishiya da ke gefen wata babbar hanya ya sauka
ya zube kasa yana kallon kan hanyar. Ita dai
wannan hanya babu wata babbar hanya sama
da ita a duk fadin garin don haka Shaddadu ya
tabbatar da cewa dole ne su Ziya'ul Hak su biyo
ta wajen. *** Al'amarin bakon Mafarauci mai
218

TASKARNOVELS.COM.NG
Kare kuwa, lokacin da ya baro fada tare da
wadannan Dakaru mutum arba'in sai suka ruga
da gudu izuwa cikin gari. Mafaraucin ne akan
gaba da farko amma daga baya sai Dakarun
suka ga Karensa ya wuce gaba yana musu
jagora. Duk inda aka je sai Karen ya tsaya ya yi
shinshine-shinshine a kasa da sama, kudu da
arewa sanann a ci gaba da tafiya. Sai da suka
shafe kusan sa'a hudu suna yawo kwararokwararo sannan suka iso wannan babbar hanya
wacce ke dauke da wannan bishiyar wacce
Shaddadu ya sauka akanta a siffar Kwaron
Malam Buda mana littafi. Kalar jikin kwaron ta
saje da kalar ganyen bishiyar saboda haka in dai
ba kwaron ne ya yi motsi ba babu yadda za a yi
mutum ko aljan ya gane akwai wani abu akan
bishivat Tun daga nesa Jarumi Shaddadu ya
karewa wannan mafarauci kallo ya gane cewa
ba kowa bane face Ziya'ul Hak domin ya lura da
layar da ke wuyansa wacce ta kasance baka ta
sauya launi ta zama ja a daidai lokacin da yai
arba da Ziya'u Hak. Da ma mahaifiyarsa
Sharlis ta gaya masa cewa lallai in dai yai arba
da Ziya'ul Hak sai layar da ke wuyansa ta sauya
launi ta koma ja Duk da cewa Shaddadu na
219

TASKARNOVELS.COM.NG
cikin siffar kwaro sai da jar layar ta nuna alama
a jikin kwaron. Bayan Shaddadu ya gane
Ziya'ul Hak sai kuma ya lura da wannan Kare da
ke mata jagora ita da sauran Dakaru. Yana
kallon Karen ya gane cewa ba dabba ba ce
Aljani ne kuma tunda ya zo duniya bai taba
ganin Aljani mai kwarjini irinsa ba. Nan take
Shaddadu ya ji zuciyarsa ta buga da ƙarfi a
karon farko a rayuwarsa. Al'amarin da yai
matukar girgiza shi ke nan kuma ya ba shi
mamaki. Kuma hakan ba ta taba faruwa ba a
gareshi, kawai sai zuciyarsa ta ce da shi, Haba
Shaddadu, wai shin tsoron me kake yi nes?
Shin ka manta ne cewar mahaifiyarka ta gaya
maka cewar in dai kana tare da wanann Mashi
na Galilul Haras babu wani tsautsayi da zai
same ka kuma babu wanda zai yi nasara a
kanka?" Koda tuna wannan batu sai zuciyar
Shaddadu ta kekashe ya yanke shawarar kawai
a yi ta ta kare a wannan wuri.. Lokacin da
mafarauci da Karensa suka zo za su gifta ta
kasan wannan bishiya wacce Shaddadu ke
zaune a kanta cikin siffar kwaron Malam buda
mana Littafi sai Karen ya tsaya cak kuma ya ki
ya wuce gaba. Koda ganin haka sai wannan
220

TASKARNOVELS.COM.NG
mafarauci ya dakatar da Dakarun da ke
bayansa yana mai tsayar da su da hannu, suka
yi cirko-cirko sannan shi ma ya zare Takobinsa
yana mai gyara tsayuwa. Karen ya zuba idanu
akan bishiyar yana ta kallon kurilla amma sai ya
kasa ganin wannan kwaro saboda kalar jikin
nasa ta saje da kalar ganyen bishiyar iri daya
sak! Kwatsam! Ba zato ba tsämmani sai suka
ga kwaron Malam Buda mana littafi ya sauko
kasa daf da wannan Kare. Ai kuwa sai Karen ya
razana ya dawo baya a guje yazo daf da
maigidansa wannan mafarauci ya tsaya. Koda
kwaron ya sauka a kasa sai ya rikide ya zama
Jarumi Shaddadu a cikin gagarumar shigar Yaki
kuma rike da Mashin Galilul Haras. Faruwar
hakan ke da wuya sai shi ma wannan mafarauci
ya rikide ya zama Jaruma Ziya'ul Hak a cikin tata
shigar Yakin. Shi kuwa wannan Kare sai yai
girgiza ya zama Aljani Maruful Dauwaz. Koda
wadannan Dakaru mutum arba'in suka yi arba
da Aljani Maruful Dauwaz sai suka sulale kasa
sumammu gabadayansu sabo da tsananin
razana da firgita bisa ganin siffarsa. Nan fa aka
fara kallon-kallo tsakanin Jarumi Shaddadu da
Jarumi Ziya'ul Hak, kowannesu jikinsa ya kama
221

TASKARNOVELS.COM.NG
tsuma ana hararar juna. Cikin tsananin fishi
Ziya'ul Hak ta yunkura za ta afkawa Shaddadu
sai Aljani Maruful Dauwaz yai wuf ya riko ta
kuma ya yi mata rada a kunne ya ce, "Ashe har
kin manta cewa idan har Shaddadu na tare da
Mashinsa na Galilul Haras ba za ki taba samun
nasara ba a kansa. Koda jin wannan batu sai
rán Ziya'ul Hak ya ɓaci ta dubi Maruful Dauwaz
ta ce, to yanzu shi ke nan muna ji muna gani ga
abin da muka zo nema sai dai mu kyale shi?
Maruful Dauwaz ya sake yi ma ta rada a kunne a
karo na biyu ya ce, "Ke yarinya ce kin cika
gaggawa, ki tsaya mana mu jarraba dabarunmu
na manya. Ai ita Saniya sai da shafa ake tatsar
nononta. Gama fadin hakan ke da wuya sai
suka ji Jarumi Shaddadu ya tuntsure da dariya.
Lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa ya dube
su ya ce, Tabbas yau ne na yarda cewar idan
Kere na yawo, Zabo ma yana yi, wata rana dole
a hadu.Yau ramin karya ya kure babu ta inda za
a bulle. Babu zancen бuya ko sauya siffa. Kun
sani, ni ma na sani farautar juna muka fito, don
haka yanzu sai a yi ta ta kare ko ni ko ku! Koda
jin wannan batu sai Ziya'ul Hak ta tari
numfashin Shaddadu ta ce, "Kai tsohon
222

TASKARNOVELS.COM.NG
munafuki dan munafuka karyarka ta sha karya.
A yau din nan zan yanke burin mahaifiyarka
wanda ta dade tana tanadinsa shekara da
shekaru. Yau zan kwatowa mabaifina
'yancinsa
End Ads