yanka
maka dukkan wannan burin naka kuma bani da
wani buri wanda yafi ya zamana cewa kaine
abkin gwamina ayanzu. Idan kowa ya dauki
tsakuwarsa domin na yi maka kisan Gilla! Koda
jin wnan batu sai sarki dujalu ya takarkare ya
bushe da dariyar mugunta sannan yace ai ni da
kai KAR TA SAN KAR ne tunda mun hada jiki ka
ji. Ni babban bakin cikina shine rashin ganin
sarki Maharaz a cikin ku ukun nan. Ko dayake
na san bai isa ya shiga wannan gumurzu ba
tunda shi jarimtakarsa ta karfin sihiri ce
17
TASKARNOVELS.COM.NG
kawai... Na so ya zama abkin gwamina na yi
masa mugun kisa a gaban yarsa da sirikinsa
domin na kunsa muku gagarumin bakin ciki.
Koda jin wanna batu sai Hibru da Inmal suka
fusata ainun suka ji kamar su zare takubbansu
su afkawa dujalu amma sai suka daure suka
tsaya suna kallonsa kawai cikin hahara jikinsu
na tsuma. Nan take sarki dujalu ya dubi Matinu
wanda ke tsye a hannun hagunsa yace. Maza
ka sa hannunka a cikin wannan kurtu ka zabo
avkin yakinka. Cikin hanzari Matinu ta cika
umarnu ai kuwa yana dauko tsakuwar sai aka
duba aka ga sunan sarkin taki barde kursham.
Matinu da kursham suka zubawa juna idanu
suna yiwa kansu kallon raini sbda kowannensu
gani yake zai iya gamawa da dayan a cikin
kankanin lokaci. ABIN DA SUKA MANTA SHINE
SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARA! sarki
dujalu ya dubi su inmal yayi murmushin
mugunta yace yanzu kuma kune zaku zaba ko
mu? Da jin haka sai inmal ya yunkura domin ya
sanya hannunsa a cikin wannan kurtu amma
sai Hibru Hibru yai sauri ya sha gabansa yace
dakata ya kai dana ai nine yakamata na zaba
yanzu kuma da izinin ubangiji garzuba sarki
18
TASKARNOVELS.COM.NG
dujalu zan zabo a matsayin abkin gwamina.
Cikin alamun firgici da tsananin tsoro inmal ya
dubi Hibru yace haba ya kai abbana ina kai ina
tarar sarki dujalu alhalin ka sancewa ya fika
jarumtaka nesa ba kusa ba? Page 18 ni kaina
da nake da kuruciya a jikina na tsorata da shi
bare kai da yanzy girma ya fara riskarka.. Yayin
da yazo nan a zancensa sai Hibru ya numfasa
yace yakai dana ai ni burina ke nan na kara da
shi domin ya kasheni ba tare da naga yadda zai
kashe kaba. Domin mutuwar tawa ta fiye mini
sauki da ganin taka. Koda sarkin yaki Hibru
yazo nan a zancensa sai Inmal yaji ya kamu da
tsananin kaunarsa gami da matukar tausayinsa
don haka bai san saadda hawaye ya subuto
masa ba. Hibru yai sauri ya kau da fuskarsa ga
barin kallon inmal don haka shima ya zubar da
hawayen kawai sai yaje inda wannan kuttu mai
tsakuwoyin yake ya zura hannunsa a cikin ya
dauko tsakuwa guda koda ya fiddo tsakuwar
aka duba sai aka ga sunan sarki dujalu ne. Nan
fa sarki dujalu ya kamu da tsananin farin ciki
yayi kururuwar murna. Shi kuwa inmal sai
yakamu da tsananin bakin ciki ya cigaba da
zubar da hawaye sbda ya sancewa lokacin
19
TASKARNOVELS.COM.NG
rabuwarsa da mahaifinsa tazo. Bayan sarki
dujalu ya gama kururwar murna gami da dariyar
faran ciki sai ya dubi Rijiju sannan ya dubi inmal
yace, ku kadai ne kuka rage baku dauki
tsakuwoyin kuba don haka dole dai baku da
sauyin abkin gwami don haka ba sai kun sa
hannun a cikin wannan kuttaba. Yanzu mu bi
ka idar wanan fafatawa domin a fara. Gama
fadin hakan ke da wuya sai sarki dujalu Matinu
da Ratinu suka hada baki suka yi rantsuwa da
Girman Gunki da suke bautawa cewar baza
suyi amfani da karfin tsafi ba ko yaudara a cikin
wannan gumurzu da za ayi face tsagwaron
karfin dantsen su da kwarewarsu ta yaki. Koda
gama fadin hakan sai suma su inmal su ka
hada baki suka yi irin rantsuwar da su dujalu
sukayi suna kammalawa ne Matinu da Barde
Kurshm na zare takubbansu suka buda suna
masu kallon juna cikin nazari sannan kuma sai
suka fara zagaya gama da dan uwansa cikin
kankanin lokaci. Lokaci guda gaba dayansu
suka yi kururuwa uku ruga kan juna suka
kacame da azababben yki suna masu kaiwa
junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama
juriya da jarumtaka kowannensu na kokarin
20
TASKARNOVELS.COM.NG
yiwa dayan farat daya. Bisa mamaki sai aka ga
duk suna amfani da da salon fada iri daya kuma
sai gashi sun kasa cutar da juna. Haka dai suka
ci gaba da fafatawa har izuwa tsawon dakika
dari uku da tamanin amma babu yanda ya sami
nasarar koda kwarzanar jikin dan uwansa.
Hatta kaifin takubbansu sai da ya fara
dusashewa sbda yawan goguwa da juna da
kansu suka ja da baya suka yi cirko cirko suna
haki kamar zakaru sbda gajiya gami da
mamakin yadda aka yi salon fadan Nasu yazo
iri daya. A bangare sauran dakarun yaki kuwa
kowannen bangare sun zuba idanu ne suna
kallo cikin fargaba gami da zakuwar sin ganin
nasu ne ya sami nasara. Bayan Matinu da
barde Kursham sun samu hutu na tsawon yan
dakiku sai kowanensu ya yar da takobin
hannunsa. Matinu ya zare wadansu gajerun
adduna guda biyu dake kuibin cinyoyinsa a
cikin kufe shi kuma Barde Kursham sai ya zare
wata sharbebiyar wuka wacce tsawonta bai
wuce kamu biyu ba amma tana da fadi gami da
tsananin kaifi sannan ya kuya ya dubi jama,ar
runfunarsa dake baya yana mai daga hannu.
Nan take wani badakare ya rugo ya kawo masa
21
TASKARNOVELS.COM.NG
garkuwa ya riketa da hannun hagu. . Yana
karba garkuwar sai ya fuskanci matinu suka
rugo da gudu izuwa kan juna. Ya yin da yarage
saura baifi taku hudu ba sai kowannensu ya
daka tsalle sama suka kaiwa juna mugun hari.
Cikin sa.a Matinu ya dankarawa barde kursham
sara a kan kafada. Shim kuma kursham ya
sokeshi da wannan wuka a tsakiyar kirjinsa har
sai da wukar ta bullo ta gadon bayansa. Duk su
biyun suka tsanfara uban ihu a lokacin da jijiyar
kafadar barde Kursgam ta tsinke jini ya kama
tsartuwa a sama. Shi kuwa matinu jini ne ya
kama bulbulowa ta cikin ramin da wukar ta yi a
kirjinsa wanda inda za a tara yar kwatarniya sai
ta cika fal da jini. Nan take du su biyun suka
kama mata gun gun a tsaye har sai dasuka
sulale kasa suka kama shure shure. Idan suka
yunkura kamar zasu iya mikewa sai kaga sun
sake bajewa. A haka dai duk su biyun suka
zama gawa. Koda ganin wanan al mari sai
kowane bangare sukakamu da tsananin bakin
ciki sakamakon RAGAS da akayi. Har sarki yaji
ya yunkura zai tari sarki dujalu sai shi sarki
dujalu ya nole yace ai ni da kai manyan giwaye
ne mu bari mu ga yadda fadan kananun giwaye
22
TASKARNOVELS.COM.NG
zai kasance sannan muyi namu a karshe...
Manyan giwaye ne mu bari mu ga yadda fadan
kananun giwaye zai kasance sannan muyi
namu a karshe... Ba tare da gardamar komai ba
Hibru ya ja da baya ya dubi inmal. Kawai sai
inmal ya tunkari abkin gwaminsa Ratiju ba tare
da ya zare takobinsa ba. Koda Ratiju ya ga
inmal ya durfafoshi babu makami sai ya cika da
tsananin farin ciki sbda tunanin cewa ya sami
babbar da mar da zai yi masa kwaf daya. Cikin
hanzari Ratiju ya zare takobinsa ya falfala da
azababben gudu izuwa kan inmal yana kwarara
ihu mai tsananin firgitarwa wanda ka iya
tarwatsa gungu dakaru a filin fama.
Zan ci gaba.
MAZAN JIYA
Littafi na hudu (4)
Part C
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
23
TASKARNOVELS.COM.NG
Ko gezau inmal bai yiba yaci gaba da tunkarasa
batare da yazare takobinsa ba daga cikin
kufeta. Ai kuwa suna haduwa sai ratiju ya
kawowa inmal wani irin mugun wawan sara a
wuya da dukkan karfinsa cikin bakin zafin nama
inamal ya sunkuya domin ya kauce saran
amma dukk da haka sai da kaifin takobin ratiju
ya shaftare saman kunne inmal ya yanke rabin
gashin kansa sai ga jini na diga daga kunnen
inmla a yayin da aka sami yar taraza a
tsakaninsu. Kofa inmal ya shafa kunnensa ya ji
jini kuma ya ga rabin gashin kansa a kas sai ya
fusata ainun zuciyarsa ta kama tarfafasa kamar
zata kone. Shi kuwa ratiju sai ya kama dariyar
keta da murna yna ganin cewa idan aka sake
gamuwa fara daya zai gama fa inmal. Batare da
inmal ya zare takobin tasa ba sai ya sake
durfafar ratiju al.amarin da yai matukar
dugunzuma hankalin sarki Maharaz ke nan.
Har Hibru ya fara kwalawa inma kira yana yi
masa tsawa akan ya zare takobinsa kafin su
hadu da ratiju. Inmal yayi kamar bai ji umarunin
Hibru ba ya ci gaba da tunkarar ratiju a hakan.
Ita kuwa Gimbiya mulaifa wacce ke tsaye acan
gefe daya tana kallon abin da faruwa tuni ta
24
TASKARNOVELS.COM.NG
fara kuka tun sa,adda ta ga an rutsure rabbin
gashin kan inmal kuma anyi masa rauni a
kunne. Sarki dujalu kuwa dariya yake ta
kyalkyalawa yana yiwa ratiju kirari gami da kara
masa kwarin guiwa. Dama sadaiki ratiju ya fi
Matinu karfin dantse da zafin nama shi kansa
sarki dujalu idan suna yar gwajin jarumtaka shi
da ratiju sai yayi da gaske yake samun nasara
akansa don haka a yanzu yana kyautata zato
cewa ratiju zai iya hallaka inmal duk da cewa
yayi yaki da inmal ya ga irin tsananin tasa
jarumtakar. Koda ratiju da inmal suka sake
haduwa a kari na biyu, sai ratiju ya kawowa
inmak muguwar suka a ciki. Kawai sai inmal ya
tare tsinin takobin da tafin hannayensa biyu.
Nan fa ratiju ya fara danno takobin da dukkan
karfinsa domin ya huda cikin inmal. Wohoho!
Mai karfi sai allah ya isa! Nan fa tsagwaron
karfin dantse ya fara amfani sai gashi duk su
biyun kwanjin jikinsu ya kumbura jijiyoyinsu
suka tashi suka yi burdin burdin. A lokacin
guda duk su biyun sai ga gumi na karyi musu.
Shi dai Ratiju ya kasa dannan tsinin takobin ta
shige izuwa cikin inmal. Shi kuma inmal ya kasa
kautar da takobin daga saitin cikinsa. Tsawon
25
TASKARNOVELS.COM.NG
komanin dakika dari da sittin suna tsaye kikam
a hakan kowannensu yana jin jiki har kaifin
takobin ta Ratiju ya fara yankar tafin hannun
inmal jimi ya fara diga. Kwatsam! Sai inmal ya
kwarara ubakjina a n.u ya daga takobin da shi
kansa ratiju sama yai wurgi da su. Tamkar an
cilla hoge sama hakan ratiju da takobin suka
luluka sama suka watse a saman. Kafin ratiju
ya fado kasa inmal ya daka tsalle sama ya
taresahi kawai sai ya kama kansa da hannu
biyu ya murde masa wuya. Sai gashi inmal ya
duro kasa bisa kan turba rungume da gawar
tatiju. Nan take yi jifa da gawar tamkar
tsummam, ya mike tsaye yana mai karkade
jurar jikinsa. Ai kuwa su sarki Maharaz basu san
saadda suka kaure da shewar farinciki ba suka
kama yiwa inmal kirari gami da jinjina bisa
wannan gagarumar jarumtaka da yayi. Shi kuwa
sarki dujalu da jama.arsa kamewa suka yi
kamar gumaka sbda mamaki da bakin ciki. Nan
take hawaye takaici ya zuvowa sarki dujalu
sbda ya san cewa yayi asarar babban
mayakinsa wanda bashi da kamarsa. Bayan
sarki dujalu ya gama alhinin mutuwar ratuju
izuwa tsawon yan dakiku sai ya tako kafafunsa
26
TASKARNOVELS.COM.NG
yazo tsakiyar filin dagar ya tsaya sannan ya xare
wadansu manyan takubba guda biyu dake soke
a gadon bayansa ya fuskanci sarki yaki Hibru.
Adaidai wannan lokacin ne hankalin inmal da
na Sarki Maharaz ya dugunzuma ainun suka ji
kamar su rike Hibru su hanashi tarar sarki
dujalu. Kawai sai suka ga shima Hibru ya zare
nasa takubban guda biyu ya yunkura zai tunkari
sarki dujalu. A guje inmal yasha gaban Hibru ya
dubeshi cikin tsananin damuwa yace yakai
abbana ka bani dama na karbeka a wannan
gumurzu ni na fafata da sarki dujalu. Koda jin
wnan batu sai Hibru ya yi murmushi yace yakai
dana kayi sani cewa ai bakin alkalami ya riga ta
bushe. Tun da har muka yi rantsuwa da girman
ubangikinmu Darbuza babu gudu kuma babu ja
da baya. Kamar yadda na zuba ido ka yina ka
gumurzu har kasami nasara hakan kaima zaka
zuba ido ka kalli nawa. YAU ne ranar da zan san
iyakar jarumtakata kuma ka sani cewa ko
kashe ni aka yi zan mutu ne a cikin alfharin kare
kasata gami da martabar sarautar abkna
aminina: alfarma daya nake nema a wajenka;
duk wuya duk rintsi karka bari gimbiya Mulaifa
ta rasa rayuwarta kuma in dai kayi tsawon rai
27
TASKARNOVELS.COM.NG
ka aureta ku koma birninmu ku karasa
rayuwarku ta duniya: koda gama fadin hakan
sai Hibru ya juya ya kalli abkinsa sarki Maharaz
wani kallo yayi masa mai kama dana bankwana
a cikin murmushi mai dugunzua hankali: Nan
take sarki Maharaz ya ji hawaye ya zubo asa
kua ya ji kamar ya ruga da gudu ya rike Hibru ya
hanashi karo da sarki dujalu: Nan take Hibru ya
durfafi Sarki Dujalu shima sarki dujalu sai ya
tunkaroshi kiwannensu ya taho a fusace acikin
mugun nufi amma a hankali suke tahowa cikin
nutsuwa ba tare da sauri ba; sai da yarege
saura baifi taku goa a tsakninsu ba sannan
suka ruga da gudu izuwa kan juna suka
ruguntsue da azababben yaki: Wohoho! Maza
maganin maza. Hakika idan jarumtaka ta hadu
da sadaukantaka gami da naci da tsantsar
juriya dole ne gumurzun ya yi dadin kallo kuma
ya zama abin tsaro: anfara wannan bakin
artabu tsakanin sarki dujalu da Hibru sai labri
ya zaa sabo: gaba dayan mutanen dake fili
babu wanda hankalinsa bai dugunzuma ba fiye
da ko yaushe sbo da ganin yadda jaruman biyu
suke kaiwa junansu mugayen hare hare na
musamman wanda babu mai iya yin irinsa face
28
TASKARNOVELS.COM.NG
tshon hannu bangaren yaki: duk dace wa sarki
dujalu yafi Hibru tsauntsar karfin dantse amma
sai gashi Hibru na iya kare hare harensa har ma
yana mai da martanin shi kansa sarki dujalu
yayi matukar mamkin yadda hakan ta kasance
domin yayi zaton cewa suna fara gumurzu zai
iya kuntatashi da karfin dantsensa cikin
kankanin lokaci amma sai gashi labari ya sha
bamban: Nan ta suka tashi hankalin kasa kura
ta turnuke filin yakin dudufniyar kafafuwansu
dakarar haduwar makamansu suka cika dodon
kunne kaai cw mutum dubu ne suka gwamuse
suke yakin: Sai da suka shafe sa:a uku cur!
Suna wannan dauki ba dadi tamkar jikinsu
bana kashi da tsoka bane face na karfe zallah
sannan suka gaji: bisa dole kowannensu ya ha
da baya suja yi cirko cirko kmar zakaru suna
haki gami da kallon juna kuma kowannensu ya
jike sharkaf da zufa kamar daga cikin kogin aka
tsamosu; Abin da ya daurewa kowannensu kai
kuma ya basu haushi shine ganin yadda suka
dade suna wannan gumurzu amma dayansu
bai sami nasar koda kwarzanar jikin daya ba:
Su kansu taron rudunonin biyu dake kallon
wannan gumurzu ji suka yi kamar da can ruwan
29
TASKARNOVELS.COM.NG
masifa ake zubowa daga sama amma da
jaruman sua daina yakin sai suka ji an dauke
ruwan masifar: Sai da sarki dujalu da Hibru
suka shefe tsawon dakika dari biyar da arba:in
suna haki da hararar juna kuma kowannensu
na tunanin irin salon da ya kaata ya sauya
domin ya sai nasara: kamar hadin baki sai aka
Ga duk su biyun sun taso da gudu a lokaci guda
sun durfafi juna: gudu ne na bala i tamkar zasu
tashi sama kuma kowannensu da dukkan
karfinsa ya taho cikin mugun nufi: maimakon
su daka tsalle sama su yi mugun gamo a kasan
kowanensu ya kaiwa dan uwansa mumunnan
hari: sai ga shi kowannensu ya wuce dan
uwansa amma sai duk suka sulale kasa bisa
guiwoyinsu suka kame kamar gumaka:
Al:amarin da ya razana kowa kenan a wajen
gashi dai dukkanninsu sun rankwafar da
kawunansu kas ama basa motsi tamka babu
mai rai acikinsu, daga can sai aka ga jini na
malalowa kasa daga jikin hannun daman sarki
dujalu kuma yana rike da hannun: shi kuwa
Hibru sai aka ga jini na malalowa ta kuibin
cikinsa: jim kadan sai hannun daan na sarki
dujalu ya gutsure ya fado kasa shima ya sulale
30
TASKARNOVELS.COM.NG
kasa sumame: shi kuwa Hibru sai ya bingire
kasa ya kaa shure shuren mutuwa; cikin
tsananin dimauta sarki maharaz da inmal suka
ruga izuwa kan Hibru: tun daga nesa suka fara
rasu ihu suka fashe da kuka: a bangare sarki
dujalu kuwa dakarunsa ne suka rugo da gudu
suka daukeshi yana cikin halin suman suka
ruga dashi izuwa can cikin sansaninsu: lokacin
da inmal da sarki Maharaz suka iso kan Hibru
yana takakarin mutuwa sai suka durkusa a
gabansa suka sake fashewa da matsanaicin
kuka sbda sun lura da raunin dake kuibin cikin
nasa sun ga yayi rami zururu babu yadda za ayi
ya rayu: hannun Hibru na karkarwa ya kamo
hannun sarki Maharaz ya dora bisa kirjinsa
suka kurawa juna idanu, cikin matukar karfin
hali Hibru ya dudi baki da kyar yace yakai abkna
yau fa ranar rabuwarmu ta zo: Tabbas mutuwa
zan yi yanzu ba zan tashi ba: ina alfahari da
wannan mutuwa tawa domin na mutu ne a filin
daga bisa kare kasata da mutuncika: sannan
ina alfahari da cewar na sarewa sarki dujalu
hannun daya har ya bar duniya ba zai taba
mantawa da niba na cusa masa bakin cikin da
zai tafi da shi har kabarinsa: koda Hibru yazo
31
TASKARNOVELS.COM.NG
nan a znacesa sai sarki Maharaz ya tasoshi
zauna ya rungumeshi yana mai fashewa da
sabon kuku yace yakai masoyina babban
amina saboda me zaka tafi kabarni a cikin
wannan duniya wacce baya da dadin zama
idan babu masoyi? Ka sani cewa in banda yata
ba mulaifa bani da kowa sai kai gashi zaka
mutu a dai dai lokacin da zan samu duniya na yi
aka sakayya bisa bautar da kayi mini a baya gai
da nuna tsantsar so da kauna: ai kuwa tun da
har tafiya zaka yi nia ina mai rokin darbuza da
ya gaggauta dauke.... Kafin sarki Maharaz ya
gama rufe bakinsa sai HIBRU yarufe asa baki da
tafin hannunsa yace idan kaima ka tafi waye zai
ga auren yayanmu kenan? Ya kai masoyina
komai RINTSI DA TSANANI Lallai ka rayu a
wannan yaki koda kuwa bamu samu nasara
mallakar Takobin Saiful Lujara ba: burina
kawai shine kai da inmal da gimbiya mulaifa ku
koma gida a raye: Saadda Hibru yazo nan a
zncensa sai sarki maharaz yasake fashewa da
kuka yace yakai masoyina kayi sani cewa bakin
alkalami ya bushe domin kafin mu baro gida
mai girma Darbuza ya tabbatar Mini dacewa
mutum hudu ne kacal zasu tsira a wannan filin
32
TASKARNOVELS.COM.NG
yaki kuma mutum biyu daga cikinmu: kaga
kenan a tsakanin ni inmal da mulaifa dole ne
dayanmu ya mutu: koda jin wannan batu Sai
Hibru ta ci gaba da kakarin mutuwa da zafi; Al
amarin da ya dimauta su inmal kenan: inmal yai
sauri ya karbi Hibru daha hannu sarki maharaz
ya rungumeshi a kirjinsa yana mai tsala ihun
bakin ciki sa;adda hawaye ke ta kwararowa
daga cikin idanunsa: a sannan ne Hibru ya dan
dawo cikin hakanlinsa ka dan ya dubi inmal
yayi masa murmushi karfin hali yace yakai dana
ka zamo mai juriya bisa rashina: ina mai fari
ciki kasancewar zan mutu akan tafin hannunka
kamar yadda mahaifin ya mutu akan tafin
hannuna kuma a filin yaki: kaima ina maka
fatan mutuwa irin ta manya mazaje a karshen
rayuwarka: ina fatan baza ka manta da
wasiyyata ba akan masoyiyarka mulaifa: a
wannan lokaci mulaifa na can nesa da su
kadan tana faman rusa kuka ta kasa karosowa
inda suke
:
33
TASKARNOVELS.COM.NG
Zan ci gaba.
MAZAN JIYA
Littafi na hudu (4)
Part D
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
hibru ya juyar da kansa ya dubi inda mulaifa
take tsaye a lokacin da idanunsa ke ganinta
dishi dishi sannan ya waigo ya dubi inmal yayi
masa kallon karshe: a hakan idanunsa suka
kafe yana yiwa inmal murmushi; kuma gaba
dayan jikinsa ya sandare: inmal bais san cewa
Hibru ya mutu ba sai daya lura da cewa
idanunsa sun daina kiftawa: koda ya fahimci
hakan sai ya tsandara uban ihu wanda ya firgita
komai da kowa ke cikin dajin: nan take shi da
sarki maharaz suka kankame gawar hibru a
jinsu suna masu fashewa da matsainincin
kuka: a sanna ne itaama gimbiya ta rugo sa
gudu ta fada kan gawar Hibru ta tayasu kukan:
34
TASKARNOVELS.COM.NG
* * * Al amarin sarki dujalu kuwa lokacin da
darunsa suka daukeshi da gudu suka tafi dashi
izuwa cikin sansaninsu sai aka wuce da shi
izuwa cikin tintinsa aka kwantar da shi akan
shimfidarsa: nan fa likitansa ya shiga aiki:
bayan ya tsaida jinin dake zuba a gundulmin
hannunsa sai ya samasa magani sannan ya
lulluceshi iya kirji da mayafi