x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - MAZAN JIYA 4

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 68055 words

Category: Adventure Stories

Views 196

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
kin huta domin mu rigasu zuwa sansanin
yakin, tunda naji sunce su sai nan da sa'a
bakwai sannan zasu cigaba da tafiya. Ba tare
da gardamar komai ba Hursiyya ta mike tsaye ta
fara harhada kayanta cikin murna domin bata
da wani buri d ya wuce ta isa bakin kogin Bahar
Suffiya ta sake saduwa da danuwanta sarki
239

TASKARNOVELS.COM.NG
dujalu kafin mai rabawa ta rabasu. Nan da nan
kuwa ta nade shimfidarta, aljani Radiyan ya
shige gaba tana biye da shi suka cigba da tafiya,
haka dai suka cigaba da ratsa wannan
kyakkyawan daji mai dauke da ni'imar
kyawawan bishiyu, duwatsu da koramai, babu
abinda da yake baiwa Gimbiya Hursiyya haushi
face idan ta kalli aljani Radiyan ta ganshi dan
mitsitsi a gabanta bai fi ta sa kafa ta shureshi
ba, sai wasu siraran kahuhuna a kansa, sannan
ga shi bakikkirin hade da jajayen kwalakwalan
idanu, yana tafiya shafal-shafal kamar iska zata
daukeshi, babu damar ya goyata bayanshi su
tashi sama suyi wannan tafiyar cikin kankanin
lokaci saboda kankantarsa da rashin karfinsa.
Haka dai suk cigaba da tafiya har tsawon rabin
sa'a a cikin wannan daji b tare da sun hadu da
wani mugun abu ba face face tsuntsaye da
suketa shawagi a sama, sai kuma kananun
dabbobin daji da kwari da ke kai kawo.
Kwatsam! Sai suka hango wani mutum daga
can gabansu a zaune bisa buzu ya fuskanci
gabas yana wani irin aiki mai kama da bauta,
Mutumin yana sanye da fararen tufafi wadanda
suka rufe jikinsa gabadaya, a gefe daya kuwa
240

TASKARNOVELS.COM.NG
takobinsa ce a ajiye da jakar guzurinsa, da yake
ya juya masu baya ne basa iya hangonsa balle
su gane cewa tsohone ko yaro ne. Koda su
Hursiyya suka hango wannan mutumin acan
nesa da su sai suka firgita ainun, aljani Radiyan
yayi maza ya kama hannu Hursiyya ya jata zuwa
bayan wani dutse suka buya suna leken
wannan mutum. A lokacin ne Hursiyya ta dubi
aljani Radiyan cikin tsananin mamaki tace haba
ya kai Radiyan yaya kana matsayin aljani
amman ka dinga shakkar biladama, duk ina
hatsabibancinka? Sa'ad da aljani Radiyan ya ji
wannan tambaya sai yayi ajiyar zuciya sannan
ya dubi Hursiyya cikin alamun karayar zuciya ya
ce ai duk mahalukin da kika gani a cikin wannan
daji to babu shakka hatsabibancinsa yafi gaban
tunani, dan abubuwan hatsarin daya wuce sunfi
gaban tunani, ke yadda aka yi ma yazo har nan
dinma shine babban abin al'ajabi, saboda fiye
da shekaru dubu arba'in ba'a taba samun wani
mahaluki daya keta dazuzzukan wannan nahiya
ba har ya isa bakin tekun Bahar sufiya ba sai a
wannan shekara da aka zo neman kayan yakin
mazan jiya, ni abinda nake so ki gane shine ban
yarda da cewar wancan mutum ne ba, babu
241

TASKARNOVELS.COM.NG
mamaki day daga cikin aljanun da suka zo
wannan yaki ne ya zo nan dan yayi leken asirin
abokan gaba dan kada a karo gudunmawar
dakarun yaki. Koda jin wannan btu sai gimbiya
Hursiyya ta yi tsaki sannan ta ce ai wannan
zancen banza nema kake yi, ta yaya wani aljani
zai baro can sansanin wannan azababben yaki
har ya zo nan alhali nasan ana can ana cikin
bala'i da masifar da mutum bai isa ya gudu ba,
tunda kai tsoro kake ji ni bari inje inga ko waye.
Kafin aljani Radiyan ya kara cewa wani abu tuni
gimbiya tabfito daga bayan dutsen da suke boye
ta durfafi inda wannan mutumin ke zaune, nan
fa tsoro ya sake baibaye aljani Radiyan ya kasa
biyota bare ya dawo da ita, dan haka sai ya
cigaba da buya a bayan wannan dutse yana
mai.leken abinda zai faru. Hursiyya ta cigaba
da tunkarar inda wannan mutum yake har yya
zamana cewa tazarar dake tsakaninsu bata
wuce taku goma ba, kuma gashi takun sawun
Hursiyya ya cika dajin gabadaya, saboda
kasancewar tana taka busassun ganyayyakin
da suka zubo kasa, amman abin mamaki shine
ko motsawa wannan mutumi bai yi ba bare ma
ya waigo yaga mai ke tahowa. Kawai sai ya
242

TASKARNOVELS.COM.NG
tsaida hankalinsa akan bautar da yake yi yana
mai cigaba da fuskantar alkibla, al'amarin da
yayi matukar baiwa Gimbiya Hursiyya mamaki
kenan har ziciyarta ta buga da karfi, a lokacin da
tsoro ya baibayeta ta fara tunanin to ko abinda
aljani Radiyan ya fada mata gaskiya ne, na
cewar wannan ba mutum bane aljani ne, kawai
sai ta yi kundunbala ta cigaba da tafiyar har sai
da ta isa daf da mutumin ta kuibin damansa,
take tayi arba da fuskarsa, aiko nan take
gimbiya ta dimauce ta kuma cika da dimbin
mamaki, har bata san sa'adda ta durkushe kasa
ba bisa gwiywoyinta tana mai kura ma wannan
mutumi idanu ko kiftawa bata yi, ba wani abune
ya ja dimauta gimbiya Hursiyya ba har ta kamu
da tsananin mamaki ba face tsananin kyawun
wannan mutum, domin ya kasance kyakkyawan
saurayi wanda shekarunsa baza su wuce
ashirin da biyar ba, duk irin tsananin kyawun
gimbiya Hursiyya kuma duk da kasancewarta ya
mace da tayi arba da wannan saurayi sai nan
take ta ji ta raina kanta domin gani tayi ta zama
mummuna akan wannnan saurayi. Sai da
saurayin ya gama ibadarsa ya juyo da nufin ya
mike tsaye sannan ne yayi arba da Hursiyya.
243

TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin mamaki y ce mutum ko aljan? Koda jin
wannan tambaya sai ta kamu da tsananin
mamaki da wani irin kallo mai dauke da alamar
tambaya ta ce ai nice ya kamata nayi mkaa
wannan tambaya, tunda babu wani mahaluki da
ya isa ya kawo kansa nan face ya cika hatsabibi.
Koda jin haka sai saurayin yayi guntun
murmushi wanda hakan yasa kyawunsa ya karu
ainun, nan fa Hursiyya ta dada rudewa taji
kamar ta rungumeshi, amman sai ta dake ta
cigaba da kura masa idanu. A lokacin ya cigaba
da magana d cewa ni ba hatsabibi bane, kuma
ban dogara da komai ba face Ubangijina,
sunana Hasnalu Ibn Bashriyya ni ma'abocin
addinin Musulunci kuma ba wani abu ya kawo
nan ba face neman mahaifina wnada ya baro
can nahiyarmu kimanin shekaru ashirin da suka
wuce tun ban fi shekara biyar ba a duniya domin
ya zo y yada Addininmu na Musulunci a
nahiyoyin dake wannan bangare, tunda
mahaifin nawa ya baro gida awancan lokacin
kawo izuwa yanzu bai koma ba kuma ba a sake
jin duriyarsa ba, ni burina kawai sjine na sani ko
yana raye ko kuma ya mutu, idan ma ya mutu
zan so ace koda kabarinsa ne na gani. Na sami
244

TASKARNOVELS.COM.NG
labari cewa gaba daya mutanen dake wannan
nahiyoyi sun tsani addinin Musulunci kuma
sunyi imani da tsafi gami da bautar gumaka,
dan haka ana sa ran lallai sune zasu kashe
mahaifina. Tun da na taso na fara wayo
mahaifiyata take bani wannan labari, ni kuma
tun a sannan n kudiri aniyar sai na zo wannan
nahiya na sauya wa mutane addininsu da ma
rayuwarasu akan tafarkin gaskiya domin duk
addinin da suke yi addini ne na karya, tsafin da
suke yarda da shi shirka ce kuma bata ne
mabayyani, domin Ubangijine wanda yafi
cancanta da a bauta ma wa, shine wanda ya
halicci sammai da kassai kuma shine ya halicci
mutum da aljan badan komai ba face su bauta
masa a doron kasa, amman sai wasunsu suka
bijire masa suka bautar waninsa suna aikata
kafirci da alfasha a bayan kasa. Lokacin da
Jarumi Hasnalu Ibn Bashriyya ya zo nan a
zancensa sai gimbiya Hursiyya ta cika da
tsananin mamaki fiye da koyaushe ta dubeshi
ta ce yanzu kai ta yaya zaka iya aiwatar da
abinda ya gagari mahaifinka? Koda jin wannan
tambaya sai Hasnalu yayi murmushi ttare da
cewa ai daman na fada maki tun farko ni da
245

TASKARNOVELS.COM.NG
ubangijina na dogara, tunda kika ga mahaifina
ya kasa jaddada addinin Allah a wannan
nahiyoyi naku to Allah ne bai nufeshi da dacewa
ba, amman ni ina sa ron dacewar. Hursiyya ta yi
shiru tana tunani gami da nazari al'amari a cikin
zuciyarta, daga can kuma ta dago kai ta dubeshi
ta ce yanzu yaya za a yi na gamsu cewar
wannan addini naka shine na gaskiya akan
namu, kuma ya za a yi nasan cewa Ubangijinka
shine mafifici akan dukkanin wani Ubangiji?
Hasnalu ya sake yin murmushi a karo na uku
sannan ya ce ai ni indai muna tare d ke, to da
sannu zaki gaskata hakan. Hursiyya tace ni
kuwa idan har na fahimci addininka shine na
gaskiya, to zan kaika inda zaka sa gaba daya
mutanen dake wannan nahiya su karbi
addininka kuma nayi maka alkawarin zan sa a
bincika labarin mahaifinka, idan ma yana raye
zan sa a nemoshi a duk inda yake. Koda jin
wannan batu sai Hasnalu ya cika da mamaki
gami fa murna ya dubi Hursiyya ya ce ke kuma
wace ce awannan nahiya da har kike tunanin
zaki iya yi mani wannan taimako? Hursiyya ta
kalleshi sannan ta yi murmushi kana daga
bisnai ta ce da shi suna na gimbiya Hursiyya,
246

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma na kasance kanwa ga sarki Dujalu, sarkin
da gabadaya nahiyoyin nan babu kamarsa a
karfin tsafi, mulki, jarumtaka gami da arziki face
wani sarki d ake kira Maharaz. A yanzu haka
dakarun sarki Dujalu dana Maharaz suna can a
bakin wani teku da ake kira bahar sufiya suna ta
gabza yaki a tsakaninsu... Nan dai Hursiyya ta
zayyane wa jarumi Hasnalu dukkanin abinda ke
faruwa har da makasudin wannan yaki, wato
akan dauko kayan yakin mazan jiya saboda
kowanne sarki yana da burin mallakar kayan
yakin dan kawai ya samu damar mulkar
mutanen duniya gaba daya. Yayin da Hursiyya
ta gama baiwa Jarumi Hasnalu wannan labari,
sai ya cika da tsananin mamaki bis yadda
mutane suka yi imani da karya da tsafi, sannan
kuma sai ya kamu da farin ciki dan yana ganin
cewa ya samu hanyar da zai jaddada addinin
Allah a wannan nahiyoyi. Hursiyya ta dubi
Hasnalu cikin nutsuwa ta kare masa kallo sai
taga bai kasance wani katon mutum ba mai
kirar Sadaukai kuma gashi ya ce shi baya tsafi,
dan haka sai fara tunani a ranta cewar ta yaya
zai iya nuna wani abin jarumtaka wanda har zai
sa mutane su amince da shi su karbi addininsa,
247

TASKARNOVELS.COM.NG
tabbas indai zai je bakin tekun bahar sufiya ya
dauko takobin Saiful Lujara a karkashin takun
kowa ya gani to da ya tsaida yakin gabadaya
kuma dole ne a gaskata ubangijin nasa. Tana
cikin wannan tunani ne suka hango aljani
Radiyan ya taho da gudu dugul-dugul kamar zai
kife kasa saboda gajarta, har jarumi Hasnalu ya
zare takobinsa zai afka masa, sai Hursiyya ta
sha gabansa ta dube shi cikin murmushi tace
mayar da takobinka ai wannan abokin tafiyata
ne, in ba don shi ba da ban zo nan ba, har ma na
sadu da kai, nan take aljani Radiyan ya ja
Hursiyya gefe suka kama kuskus, ya dubeta
cikin alamun tsoro kamat ace ket ya fita da
gudu, jikinsa na tsuma yace shin kin tabbatar da
mutum ne wannan ba aljani ba? Hursiyya ta
kyalkkyale da dariya sannan ta ce na tabbar
mutum ne. Nan take ta kwashe labarin dukkan
abinda ya faru tsakaninta da jarumi Hasnalu ta
zayyane masa. Koda jin haka sai boka Radiyan
ya murtuke fuska ya dubeta cikin fushi ya ce
saboda me zaki gaskata zancen ma'abota
addinin Musulunci, mutanen da suka kasance
abokan gabarmu tun iyaye da kakanni, to ki sani
cewa bamu da makiya sama da wadannan
248

TASKARNOVELS.COM.NG
mutane, kuma duk abinda ya fada maki zancen
banza ne babu gaskiya a cikinsa, kada kyawun
wannan saurayi ya rudeki kizo ki aikata abinda
zaki jefamu a cikin danasani. Sa'ad da gimbiya
Hursiyya ta ji wannan batu sai ta yi ajiyar zuciya
kuma ta yi shiru tana tunani har izuwa tsawon
yan dakiku, sannan ta dubi ljani Radiyan tace
dole ne na jaraba wannan saurayi domin na
tabbatar da gaskiyarsa ko rashinta kafin na ki
bashi yarda ta, ai masu iya magama sunce
ranar wanka ba a boyon cibi, kuma sunce
sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba a je ba,
kawai mu cigaba da wannan tafiya tare da shi
har mu kure karyarsa. Koda ta zo nan a
zancenta sai Hursiyya ta rabu da aljani Radiyan
taje gun Hasnalu ta dubeshi cikin murmushi ta
ce ni da abokin tafiyata mun amince mu tafi
tare da kai har ixuwa filin daga inda ake fafata
yaki, amman bisa sharadi guda, sharadin kuwa
shine dole ne kayi abubuwan al'ajabi guda uku
wadanda zasu nuna mana cewa ka cika jarumi,
kuma ubangijinka shine ubangijin gaskiya.
Sa'ad da jarumi Hasnalu ya ji wannan batu sai
yayi murmushi shima y ce nayi imani da
ubangijina dari bisa dari, dan haka nasan cewa
249

TASKARNOVELS.COM.NG
zai bani ikon hayewa wannna sharadi da kuka
gindaya mani, nima kuma bisa sharadin muddin
na yi wadannan abubuwa da kika shardanta
mani to zaki karbi addini na. Hursiyya ta yi
murmushi sannan t ce na amince zan karbi
addininka matukar kayi abubuwan dana
sharadanta maka, muje zuwa mahaukaci ya
hau kura. Koda ta zo nan a zancenta sai jarumi
Hasnalu ya mayar da takobinsa a cikin kubenta,
kuma ya nannade buzunsa ya sabashi a
bayansa ya daure sannan ya dubi aljani Radiyan
ya ce wace hanya zamu bi ta kaimu zuwa bakin
kogin na bahar sufiya inda ake yakin? Aljani
Radiyan yayi nuni da hannunsa izuwa yamma
yana mai cewa nan zamu bi. Nan take Hasnalu
ya wuce gaba yan mai karanta wasu Addu'o'i na
musamman a zuciyarsa, Hursiyya na biye fa shi
daf da daf, sannan sai aljani Radiyan a bayansu.
Nan fa suk cigaba da kutsawa cikin sarkakiya,
duhuwoyi, koramu d kwazazzabai, haka suka
cigaba da tafiya tamkar ba zasu daina ba, wani
lokacin sukan jiyo kukan manyan dabbobin daji
acn nesa da su, wani lokacin ma sai suji tamkar
a gabansu dabbobin suke kuka, amman wani
iko na Allah har sai da suka shafe rabin sa'a sun
250

TASKARNOVELS.COM.NG
tafiyar basu yi arba da muguwar dabba ko guda
daya ba, banda kukan dabbobima sukan jiyo
gurnani irin na dodanni da aljanu wanda hakan
yasa aljani Radiyan da Hursiyya suka tsorata
ainun jikinsu ya kama tsuma, amman sai suk ga
shi jarumi Hasnalu ko gezau beyi ba, kawai sai
cigaba yake ma da tafiyarsa tamkar a cikin gari
yake ba a daji ba. Kwatsam sai kawai suka ga
sun shigo cikin wani wuri mai wani irin yanayi na
ban tsoro, wajen yana dauke da wasu irin
dogayen bishiyu masu tarin dogayen jijiyoyi da
suka zubo kasa tun daga sama, sannan akwai
ruwan wata korama a wajen da ke kwararowa
daga kan duwatsu, bugu da kari kuma sai suka
ga bishiyoyin ayaba da yawa a wajen kuma g shi
an tsittsinki ayabar, anci wata an kuma zubar da
wata a kasa gata nan a ko'ina birjit. Koda suka
yi arba da wannan wuri sai jarumi Hasnalu ya
tsaya cak, kum ya juyo yayi w su Hursiyya da
suma su tsaya kuma suyi shiru. Nan take kuwa
suka bi umarninsa, Hasnalu ya zaro takobinsa
daga cikin kubenta a hankali dan kada aji sautin
zaretan, sannan ya fara kallon gabas da
yamma, kudu da arewa yana nazarin hanyar da
ya kamata su bi, domin su cigaba da tafiya,
251

TASKARNOVELS.COM.NG
amman sai yaga hanya daya ce jal dole ne sai
sunbi ta wani katon kogon dutse mai duhun
gaske. Nan fa Hasnalu ya ji a jikinsa cewa lallai
baza a rasa wani mugun abu ba a cikin kogon,
kuma gashi duhune dundum a ciki, suna shiga
abinda ke ciki zai iya cutar da su ba tare da sun
ganshi ba, nan fa Hasnalu ya fara tunanin
dabarar da zai yi yasa duk abinda ke cikin kogon
ya fito waje ayi gaba da gaba. Nan take kuwa
dabara ta fado masa ya daga kansa sama yana
mai wangame bakinsa ya kwala kabbara da
karfi, aikuwa take dajin ya kama amsa kuwwa,
duk wani abu dake wannan daji sai da ya razana
tsuntsaye suka kama tashi sama suna sauya
sheka, dabbobin dake wannan daji suka kama
fitowa suna karo da masu kokarin shiga saboda
rudewar da suk yi, aikuwa a sannan ne suka ji
cikin wannan kogon dutsen ya rude da wani irin
gurnani mai yawa da karfin gaske, al'amarin da
yayi matukar razana aljani Radiyan da Hursiyya
kenan, kafin kiftawar ido sun ruga da baya
izuwa cikin duhuwar bishiyoyi suna masu leken
jarumi Hasnalu domin suga abinda zai faru
gareshi. Shikuwa Hasnalu sai ya kara rike
takobinsa da hannu biyu yana mai gyara
252

TASKARNOVELS.COM.NG
tsayuwarsa alokacin da wannan mugun
gurnanin yake dada karuwa, gami da wani irin
takun sawaye tamkar giwaye ne ke shirin fitowa
daga cikin kogon dutsen wanda har sai da ya
fara haifar da yar karamar girgizar kasa. Sai dai
hakan bai sa jarumi Hasnalu ya razana ba ko
kuma yayi yunkurin ja da baya ba, kwatsam sai
ga rundunar wasu burirrika manya manya masu
tsananin tsawo da kaurin gaske gami da
tsananin muni, su dai wadannan burirrikan
adadinsu ya kai kusan dari, suna da zara-zaran
farata a hannunsu, masu kaifi da tsini kamar
wukake, duk da cewar jarumi Hasnalu yana da
dakakkiyar zuciya amman sai da zuciyarshi tayi
rawa yayi tunanin cewa lallai fa yau ya gamu da
gamonsa. Al'amarin su Hursiyya da aljani
Radiyan kuwa lokacin da suka hango wadannan
burirrika a take suka firgice suka kwanta a kas
cikin duhuwar ciyawa, kuma suka dauke
numfashinsu tamkar marasa rai. Lokacin da
wadannan munanan burirrikan sukaga
biladama guda daya jal a gabansu yana rike da
makami, sannan babu alamar tsoro a tare da
shi sai suma suka tsaya cak suna kallonshi cike
da tsantsar mamaki, ba wani abu ne yasa suke
253

TASKARNOVELS.COM.NG
mamaki ba face shine kadai mutum na farko
daya taba yin arba da su ba tare da ya sume ko
kuma ya haukace ba. Nan fa aka fara kallon
kallo tsakanin burirrikan da jarumi Hasnalu har
izuwa tsawon yan dakiku, a duk sa'ad da yayi
arba da jajayen idanun burirrikan masu ban
tsoro da tsananin ja tamkar an gasa dan bida a
cikin wuta sai yaji kamar jiri na dibarsa. Nan
take Hasnalu ya fara karanto addu'o'i na neman
tsari domin ya fuskanci cewar burirrikan suna
da kofi a tare da su. Sannu a hankali burirrikan
suka fara rarrabuwa suna yiwa Hasnalu
kawanya, shi kuwa sai ya cigaba da tsayuwa a
inda yake ba tare da ya motsa ba, kawai kuma
sai ya rufe idanunsa tare da daga takobinsa
sama sosai tsininta na kallon sararin samaniya.
Al'amarin da ya dan tsorata burirrikan kenan
yasa suka kasa afka masa farat daya, suka rinka
kusantarsa da kadan kadan. Hursiyya da aljani
Radiyan dake boye suna ganin dukkanin abinda
ke faruwa, kawai sai suka sake cika da dumbin
mamaki musamman ganin dakewar zuciya irin
ta jarumi Hasnalu, kuma suka cigaba da zuba
ido dan suga irin gumurzun da xai yi tsakaninsa
da wadannan birirrikan. Kamar hadin baki sai
254

TASKARNOVELS.COM.NG
kawai birirrikan suka yunkura gaba dayansu tare
da afka masa a lokacin guda da nufin suyi
gutsu-gutsun da sassan jikinsa kowa ya ja
rabonsa, aikuwa sai suka kaiwa isk sara da suka
domin kuwa tuni Hasnalu ya daka tsalle sama
tamkar daga cikin baka aka harba shi, kafin su
dga kawunasu sama yayi alkafira a saman
kawunasu ya dawo kasa hannunsa na rike da
takobinsa, a sannan ne ya shiga gididdiba su
yana sare masu kawuna, koda ya dira kasa
kuwa sai ya cigaba da daukar rayukansu cikin
bakin zafin nama irin wanda dan adam bai taba
gani ba, yana saransu da sukansu yana hadawa
da kabbara, sai dai kaga sassan jikin birirrikan
na shawagi a sama ko kuma kaga hanjin cikinsu
na bullutsowa waje suna faduwa kasa matattu.
Koda birirrikan suka ga Hasnalu yayi masu
mummunar barna kuma ga shi a tsakiyatsu
amman sun kasa koda warzanar jikinsa sai suka
fusata ainun kuma suka haukace suka rinka
jijjigo bishiyoyi daga karkashin kasa suna masu
kai masa duka ta ko ina, a hakan ne daya daga
cikinsu ya samu nasarar kwada masa bishiya a
kirji, saboda karfin dukan sai da Hasnalu yayi
sama bayansa ya gwaru da jikin wata bishiya
255

TASKARNOVELS.COM.NG
take yayi aman jini, kuma tsinin reshen bishiyar
ya sokeshi a gefen hakarkarinsa na hadu, nan fa
Hasnalu ya kwala kabbara a lokacin da ya
subuto sakamakon tsananin zafi da zugin da ya
ji, a matukar galabaice ya fado kasa aikuwa sai
birirrikan suka yo masa ca domin su cinye
namansa danye, a lokacin ne hankalin gimbiya
Hursiyya ya dugunzuma ainun bisa mamaki sai
kawai ta ji hawaye ya subuto mata dan ganin
Hasnalu zai hallaka. Ba zato ba tsammani sai
kawai taga Hasnalu ya mike tsaye zumbur ya na
mai cigaba da yakar burirrikan yana gididdibasu
da takobinsa yana mai cigaba da yin kabbara,
End Ads