ta Kudurce a
ranta cewa har abada ba za ta taba mancewa
da wannan hawaye ba na farin cıkı. ko iya shi ta
samu a wajen Shaddadu ta san za ta tabu da shi
a cikin farin cikın ya tausaya mata a rayuwa ko
kuma ya so ta. Bayan Jarumi Shaddadu ya yi
dan dogon tunani da nazari a cıkın zuciyarsa sai
ya dubi Yaldisa ya ce, ya ke wannan
ma'abocıyar kyau da karamci ki yi sani cewa,
322
TASKARNOVELS.COM.NG
kin yı mını taimako a rayuwa irin wanda ni ma
har abada ba zan taba mantawa da shi ba kuma
kin nuna mini Kauna kwatankwacin irin wadda
babu wanda ya taba nuna mini face mahaifiya
ta. Ina fatan na saka miki da abın da ba za ki
taba mantawa da shi ba. Tabbas na tausaya
mikı matuka bisa yadda rayuwarki ta kasance
kuma na gamsu cewar kaddara ce ta salwantar
da rayuwarki. Hakika ba ki da wani abokin
gaba a doron Kasa wanda ya fi Sarauniya
Zubaina. Ina so ki sani cewa, matsoraci ba zai
taba zama gwani ba. Na fuskanci cewa ke ma
kina da jarumtaka gami da taurin zuciya daidai
gwargwadon irin ta ki, saboda haka, ina so ki zo
mu hada karfi da karfe mu tunkari gıdan
Sarauniya Zubaina yanzu mu yake ta ita da
abokiyar gaba ta, a yi ta ta kare, ko mu ko su. Ni
na san cewa zan ıya yakarsu da tsagwaron
jarumtaka ta domin na samı cıkakken horon
Yaki a Wajen maharfiyata. Tabbas ba ni da
burin da ya fi na daukı fansa a kan Ziya'ul Hak
bisa abin da mahaifinta ya yi wa mahaifiyata, ya
kashe dukkan zuri'arta kuma ya yi ma ta fyade
aka samı cıkına. Wani lokacın idan na tuna
cewa ina farautar rayuwar mahaifina da
323
TASKARNOVELS.COM.NG
kanwata ne sai na ji na kamu da tsananın bakin
ciki. Amma kuma idan na tuna da irin
wulakancin da aka yi wa mahaifiyata gami da
bakin cikin da aka cusa mata sai na ji na tsani
Mahaifin nawa da yar uwata Ziya'ul Hak. Koda
Jarumi Shaddadu ya zo nan a zancensa sat ya
fashe da kuka. Alamarın da ya karya zuciyar
Yaldisa ke nan ta kamu da tananın tausayinsa
ba ta san sa'adda ta rungume shi ba ita ma ta
fashe da kukan. Jim kadan sai ta janye jikinta
daga cikin nasa suka fuskanci juna ta ce, yanzu
idan muka yi kundunbala muka je muka tari su
Sarauniya Zubaina da yaki to mene ne makomar
Mashinka wanda ya fada cikin wannan korama?
Shin ba ka zaton cewa zai iya fadawa hannun
abokan gabarmu? Sa'adda Jarumi Shaddadu
ya ji waďannan tambayoyi guda biyu sai ya yi
ajiyar zuciya sannan ya ce, tabbas irin neman
da na yiwa wannan Mashi nawa a cikin wannan
korama inda yana cikinta da tuni na gan shi.
Haka kuma idan Mashin ya fada hannun abokan
gabata da tuni sun gano inda nake sun zo sun
hallaka ni. A cikin biyu dole ne ya zamo daya,
wato ko dai ruwa ya tafi da Mashin ya nutse a
cikin Teku, ko kuma wadansu aljanun masu
324
TASKARNOVELS.COM.NG
tsananin rabo sun tsince shi. Ni a ganina abin
kunya ne na koma gida wajen mahaifiyata na
sanar da ita cewar wannan Mashi ya salwanta a
hannuna bayan tun ina yaro karami take horar
da ni Yaki da jarumta domin na kare kaina da
wannan Mashi kuma na hallaka abokiyar
gabata. Masu iya magana sun ce, Sai an
gwada akan san na kwarai. Yanzu ina neman
alfarma ta karshe a wajenki da ki raka ni izuwa
gidan Sarautar Sarauniyarku a yanzu domin na
yake ta tun gabannin gari ya waye su fito yakata,
saboda an ce, Ka kashe makiyinka kafin shi ya
kasheka. Ba wai ina son ki raka ni ba ne domin
ni kadai ba zan iya ba, a'a sai don saboda ke kin
san sirrin gidan Sarautar kuma an ce, da dan
gari akan ci gari. Koda jin wannan batu sai
farin ciki ya lullube Yaldisa ta ce, ai dama na
gaya maka cewa raina da jikina duk na sallama
su a ceton taka rayuwar. Hakika ni ma yanzu na
gane cewa ba mu da wani zabi wanda ya fi mu
tunkari masifar tun gabannin ta tunkaromu.
Abu daya kawai da ma nake shakka, kuma ba
wani abu bane face karfin sihirin tsafin
Sarauniya Zubaina, to amma a yanzu haka ma
wata dabara ta fado mini zan san abin da zan yi
325
TASKARNOVELS.COM.NG
akan hakan. Ai Sarauniya Zubaina ta yi sake
Dan Zaki ya girma, domin ta raini ajalinta da
hannunta. Tun da na fara girma na yi hankali
kuma na gano cewa Sarauniya Zubaina
abokiyar gabata ce ba masoyiya ta ba na shiga
bincike akan sanin sirrinta. Ban san dukkan
sirrinta ba, amma na san wadansu da yawa.
Baya ga wannan, ina mai tabbatar maka da
cewa zan yi matukar ba ka mamaki a wannan
Yaki da za mu je mu yi a gidan Sarautar tamu.
Yanzu dai sai mu gaggauta shiryawa domin mu
san abin yi. Nan take suka fara shirya kayan
Yaki. Yaldisa ta sake komawa cikin gari a cikin
bad-da-kama ta shiga kasuwa ta siyo Kwari da
Baka gami da wadansu irin sinadarai na kayan
Yaki wadanda ita ta san abin da za ta yi da su,
sannan ta siyo wa Jarumi Shaddadu riga da
wando na karfe gami da garkuwa ta karfe, ita
ma ta siyowa kanta kayan karfen sannan ta
sake komawa can dajin cikin wannan Kogon
dutse. Shi kansa Shaddadu da ya ga irin kayan
Yakin da Yaldisa ta siyo musu sai da ya yi
matukar mamaki domin da yawa daga cikin irin
kayan Yakin ko a gidan Sarautar Birnin Kufa bai
taba ganin irin su ba tun daga yarintarsa har
326
TASKARNOVELS.COM.NG
izuwa girmansa. Sai da Yaldisa ta shafe sama
da sa'a guda tana koyawa Shaddadu yadda za
su yi amfani da wadannan sinadaran na kayan
Yaki. Bayan nan ne suka sanya wadannan
kayan Yakin na karfe a jikinsu, Shaddadu ya
rataya Takobinsa a baya kuma ya zuba wukake
a jikinsa gami da Adduna guda biyu kuma ya
goya jakar sinadarin kayan Yakin a bayansa.
Ita kuwa Yaldisa wannan Baka ta rataya a
bayanta gami da jakar Kwari wacce ke dauke da
kibiyoyi masu yawan gaske. Ita dai wannan
Baka ta Yaldisa Baka ce ta musamman wacce
ta kasance katuwar gaske kuma zaren jan ta
mai matukar tauri ne da kauri, sai kato ya cika
kato sannan zai iya tabe ta. Hakika duk wanda
ya ga Jarumi Shaddadu da Yaldisa a wannan
shiga dole ne ya razana domin shigar ta kara
musu kwarjini ainun, musamman ma shi Jarumi
Shaddadun wanda kirarsa ta kasance ta
sadaukai, kuma kirar ta sake bayyana a fili
karara. Bayan sun gama kintsawa sai suka
yanke shawarar su sauya wuri a cikin dajin su je
su nemi wani wuri mai duhuwa su biya sai dare
ya tsala Sannan su kai MAMAYAR BAZATO izuwa
gidan Sarautar. Wannan shi ne abin da ya faru
327
TASKARNOVELS.COM.NG
tsakanin Jarumi Shaddadu da karuwa Yaldisa
bayan ta ceto rayuwarsa a daji sakamakon
masifaffen Yakin da ya faru tsakaninsa da
Jaruma Ziya'ul Hak. **** Al'amarin Aljani
Maruful Dauwaz kuwa, lokacin da ya rabu da
Jaruma Ziya'ul Hak. ya ga cewa ta tafi ta ci gaba
da wanann Yaki ita kadai ba tare da taimakonsa
ba sai hankalınsa ya dugunzuma ya shiga sakesaken zuci da tunani Koda ya tuna cewa da shi
da Ziya'ul Hak yanzu duk ba su da sauran karfin
sihirin tsafi a jikinsu tunda shi ma an doke shi
da Mashin Galilul Haras har ma an balla masa
kashin kafadarsa kuma ba shi da tababcin cewa
Jarumi Shaddadu na tare da Mashinsa sai
hankalınsa ya dugunzuma kuma zuciyarsa ta
karaya da sa ran samun nasara akan Shaddadu.
Nan take ya yanke shawarar ya koma can. dajin
da suka baro Sarki Laffaru da matarsa ya sanar
da su halin da ake ciki domin idan suna da wata
dabarar da za a yi a cim ma buri su fada masa.
Ai kuwa nan take ya bude fuka-fukansa ya tashi
sama ya luluka a cikin gajimare yana mai tsala
azababben gudu na gaban kwatance domin ya
isa can dajin akan lokaci. Kash! Rashin sani ya
li dare duhu. Inda Aljanı Maruful Dauwaz ya san
328
TASKARNOVELS.COM.NG
gaibu da bai taba yin wannan ganganci ba na
komawa dajin da su Sarkı Laffaru suke domin ya
sanar da su halın da 'yarsu Ziya'ul Hak ke ciki
ba. ** A can Birnin Kufa kuwa, tun daga ranar
da Jarumi Shaddadu ya bar gida sai Sharlisa ta
rinka yin mugayen mafarkai a kansa tana yawan
ganinsa a cikin garari da tashin hankali amma a
duk sa'adda ta tuna cewa ai yana tare da
Mashin Galilul Haras sai hankalinta ya kwanta
don ta san cewa babu wani tsautsayi da zai
taba lafiyarsa ko rayuwarsa. Lokacı da ta ci
gaba da yin irin waďannan mugayen mafarkai ba
kakkautawa sai hankalinta ya dugunzuma ainun
ta rasa sukuni saboda haka sai ta dauko
madubin tsafinta ta shiga bincike. Ai kuwa nan
take ta ga duk abin da ya faru ga Shaddadu tun
daga farkon tafiyarsa kawo izuwa saukarsa a
Birnin Sarauniya Zubaina da irin bakin artabun
da ya yi da Ziya'ul Hak da kuma halin da ake ciki
na yanzu cewar, ya yi shirin Yaki shi da YALDISA
su biyu kacal! Za su je su Yaki Sarauniya
Zubaina da Ziya'ul Ilak a cikin dare. Koda gama
ganin wannan alamari sai hankalin Sharlisa ya
dugunzuma ainun, bakin ciki ya turnuke ta, nan
fa ta yanke hukuncin ta tashi ta yi shiri ta tafi
329
TASKARNOVELS.COM.NG
izuwa Birnin Sarauniya Zubaina domin ta kai wa
danta dauki. Amma babban tashin hankalin
shi ne, karfin sihirin tsafinta ba zai iya kai ta
garin ba a cikin yıni daya ba dole sai ta shafe
kwana uku tana tafiya, ke nan kafin ta je komai
zai iya faruwa, ma'ana za a iya kashe mata da a
ruguza ma ta dukkan shirinta da burinta. Nan
take ta aiyana a ranta cewar kamata ya yi ta fara
biyawa ta jejin da su Sarki Laffaru suke ta yake
su ta kashe su shi da matarsa kawai domin ta
fara rage takaici, amma kuma da ta tuna cewa
ba za ta iya shiga dajin da suke ha sai ta sake
kamuwa da tsananin bakın ciki. Babu ma abın
da ya fi daga mata hankali sama da batan
Mashin Galilul Haras. Nan take Sharlisa ta
shiga cikin dakin halwar tsafinta ta yi gagarumin
shirin Yaki da tafiya sannan ta fito ta hau kan
wani sabon Tsuntsun tsafi ya tashi da ita sama
suka luluka a cikin gajimare. *** Lokacin da
Aljani Maruful Dauwaz ya isa dajin da su Sarki
Laffaru suke, koda suka hango shi yana
saukowa kasa shi kadai babu Jaruma Ziya'ul
Hak a tare da shi sai hankalinsu ya dugunzuma
ainun nan take suka mike tsaye zumbur! daga
bakin bukkarsu suka rugo izuwa gare shi suka
330
TASKARNOVELS.COM.NG
tambaye shi ina 'yarsu take, a cikin hadin baki.
Koda jin wannan tambaya sai Aljanı Maruful
Dauwa ya sunkui da kansa kas cikin alamun
tsattanin damuwa ya kasa cewa komai.
Al'amarin da ya dugunuma hankalin Laffaru da
matarsa ke nan suka fara tunanın ko Ziya'ul Hak
ta mutu ne. Cikin fushi Sarki Laffaru ya dora
hannunsa a kan kafadar Marutul Dauwaz ya
daka masa tsawa ya ce, ya kai Sarkin Jaruman
aljanu, yaya za mu ba ka amanar yarmu amma
ka dawo ka yi mana shiru ba ka sanar da mu
halin da take ciki ba? Da jin wannan batu sau
Aljani Maruful Dauwazya dago kai ya dube su ya
ce, yarku tana nan a cikin Koshin lafiya kuma a
raye, amma tana cıkın TSAKA MAI WUYA. Ni
kaina na hadu da tashin hankali wanda ya fi
Karfina. Nan take Maruful Dauwaz ya kwashe
labarin duk abin da ya faru a can Birnin
Sarauniya Zubaina ya shaida musu, har da irin
BAKIN ARTABUN da aka yi tsakanin Jarumi
Shaddadu da Ziya'ul Hak, har aka buga masa
Mashin Galilul Haras a kafada kashınsa ya
karye ya zube kasa sumamme, kawo izuwa
lokacın da Sarauniya Zubaina da Ziya'ul' Hak
suka hada kai domin su hallaka Shaddadu
331
TASKARNOVELS.COM.NG
amma duk da haka babu tabbacin Shadaddu
yana tare da Mashinsa ko baya tare da shi.
Koda jin wannan batu sai hankalin Sarki Laflaru
da na matarsa ya kara dugunzuma fiye da ko
yaushe suka rasa abin da ke musu dadi. Nan
dai Laffaru da matarsa suka koma gefe daya
suka shiga yin shawara a tsakaninsu inda
Ramlatul Siyam ta dubi Sarki Laffaru cikin
tsananın damuwa sa'adda Kwalla ta cika
idanunta ta ce, ya kai mijina, ka yi sani cewa
idan har yarmu ta kasa hallaka wannan yaro
Shaddadu bisa taimakon Sarauniya Zubaina to
fa shi zai sami nasarar hallaka su, da zarar ya
hallaka su kuwa zai nemi duk inda muke ya zo,
kuma tunda yana tare da Mashin Gaililul haras
zai iya zuwa har nan ya yi mana kisan gilla ko
kuma ya kama mu ya kai mu har can Birnin Kufa
gaban Sarauniya Sharlis ta yi mana kisan
wulakanci. Da dai haka ta faru gare mu gwara
mu bi Aljani Maruful Dauwaz i zuwa Birnin
Sarauniya Zubaina a yi-ta-ta-kare a gaban
idanunmu. Ni kam a yanzu na sami nutsuwa
guda daya da ya zamana cewa sihirin tsafin
Shaddadu da na Ziya'ul Hak duk sun daina
tasiri. Fatana kawai shi ne ya zamana cewa
332
TASKARNOVELS.COM.NG
Shaddadu bai ga Mashinsa ba, babu mamaki
ruwa ya batar da Mashin a cikin Tekun.
Lokacin da Ramlatul Siyam ta zo nan a
zancenta sai Sarki Laffaru yai shiru yana tunani
har izuwa lokaci mai dan tsawo daga can sai ya
baro wajen Ramlatul Siyam ya je wajen Aljani
Maruful Dauwaz ya ce, to yanzu ka zo ka sanar
da mu halin da 'yarmu ke ciki kuma ka sani
cewa babu wani taimako da za mu iya yi mata
tunda har yanzu ni ba ni da karfin jikina. Na
rasa jarumtaka tun daga lokacin da Sharlis ta
sihirce ni kuma na rasa dukkan karfin sihirina na
tsafi. Kai wanne hukunci ka yanke wa kanka?
Shin ka dawo ke nan ba za ka ci gaba da tsare
lafiyar 'yata ba? Koda jin wannan tambaya sai
idanun Maruful Dauwaz suka ciko da kwalla har
hawaye ya zubo masa ya dubi Sarki Laffaru ya
ce, ya kai wannan Sarki, ka yi sani cewa muddin
ina numfashi a doron kasa ba zan iya nisantar
'yarka ba domin a dalilinta ne kadai na yarda na
ci gaba da rayuwa a doron kasa saboda tana
matukar kama da masoyiyata. Babban abin
bakin cikina wanda zan mutu da shi a cikin raina
kuma wanda shi ne burina na karshe shi ne
rashin sanin inda wasiyyar masoyiyata take.
333
TASKARNOVELS.COM.NG
Inda zan ga wannan wasiyya ta isa ta debe mini
kewar rashin masoyiyata domin zan koma
Kogon Darul Ikisina na karasa rayuwata ya
zamana cewa kullum dare da rana ba ni da wani
aiki sai karanta wasiyyar tata har izuwa ranar da
wa'adina zai cika. Tun da dai yanzu ban ga
wannan wasiyyar ba dole na ci gaba da rike
alkawarina na kare lafiyar 'yarka da rayuwarta
iyakar karfina koda a sanadın hakan ne zan
sadu da ajalina. Ina so ka sani cewa na zo ne
na sanar da ku halin da ake cíki a matsayinku na
iyayen Ziya'ul Hak don kada mu riski ajalinmu ni
da ita ba ku san abin da ya faru ba a gare mu,
sannan kuma na yi tunanin cewa ku bil'Adama
kuna da hikima da basira irin wacce mu aljanu
ba mu da ita, babu mamaki kuna da wata
dabarar wacce za ta iya tserar da mu daga
sharrin Jarumi Shaddadu. Lokacın da Aljani
Maruful Dauwaz ya yo nan a zaneensa sai Sarki
Laffaru ya sunkui da kansa kas ya shiga tunani
mai zurti har izuwa lokaci mai dan sawo daga
can sai ya dago kai ya dubi Aljani Marutul
dauwaz ya ce, Masu ya magana sun ce faduwar
gaba asarar namiji ce, sau tari idan masifa ta
tunkaro mutum to bai kamata ya zauna jiranta
334
TASKARNOVELS.COM.NG
ba gwara ya je ya tare ta domin idan ya bari ta zo
ta riske shi har inda yake za ta yi masa kwaf
daya ne. Tabhas yanzu zan yi amfani da
shawarar matata, kuma akwai wata dama guda
daya wacce idan har na same ta a cikin gıdan
Sarautar Sarauniya Zubaina to ta karfin
dantsena da na sihirina zai iya dawowa. Koda
jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Maruful
Dauwaz ya ce, yanzu kai dama ka san hanyar da
za ka iya dawo da martabarka amma ba ka bi ba
tun tuni? Sarki Laffaru ya gyada kai cikin
alamun takatci har kwalla ta zo masa sannan ya
ce, da ma Boka Muzaffar ya sanar da ni cewa
hanya biyu ce zan iya bi na sami waraka daga
sharrin Sharlis. Hanya ta farko ita ce, ta auren
Ramlatul Siyam mu haifi 'yar da za ta iya kashe
Shaddadu da mahaifiyarsa. Hanya ta biyu kuwa
ba zan taba samunta ba face a wajen
mashahuriyar Sarauniya wacce ta kasance
gagarumar matsafiya mai mulkin babban Birni
wanda ya kai Birni na Kufa. Bisa labarin da ka
ba ni na Sarauniya Zubaına na fahimci cewar
duk tana da wadannan abubuwa wadanda Boka
Muzaffar ya siffanta mini. Koda jin wannan
batu sai farinciki ya lullube Aljanı Marutul
335
TASKARNOVELS.COM.NG
Dauwaz ya ce, ai kuwa idan karfin dantsenka da
na sihirinka suka dawo shi ke nan mun tsira
daga sharrin Sharlis da danta, musamman idan
ba sa tare da Mashin Galilul Haras. Ka sanar da
ni hanyar da za ka bi ka dawo da komai naka
domin na san irin taimakon da zan iya ba ka.
Koda jin wannan batu sai Sarki Laffaru yai ajiyar
zuciya yace, ai da zarar na furtawa wani
al'amarın komai ya rushe domin ka'idar sihirin
ke nan. Yanzu dai bari mu yi shiri ni da matata
mu zo ka kai mu can Birnin Sarauniya Zubaina
domin a yi ta-ta kare. walau mu sami nasara
akan makiya ko kuma su sami nasara akanmu
kowa ya huta da fargaba. Koda gama fadin
hakan sai Sarki Laffaru ya juya ya nufi inda
Ramlatul Siyam take ya sanar da ita cewa ta
shiga cikin Bukka ta dauko musu kayansu
domin su tafi i zuwa can inda 'yarsu take. Koda
jın haka sai farinciki ya lullube Ramlatul Siyam
ta ruga i zuwa cikin Bukkar tasu ta debo musu
kayansu ta fito. Ba tare da bata wani lokacı ba
suka hau kan Aljani Maruful Dauwaz ya tashi da
su sama ya luluka a cikin gajimare yana tsala
azababben gudu. *** A can Birnin Sarauniya
Zubaina kuwa, Jarumi Shaddadu da Yaldisa na
336
TASKARNOVELS.COM.NG
labe a cikin duhuwar wadansu ciyayi da ke nesa
kadan da gidan Sarautar suna hangen Dakarun
da ke kai kawo a kofar gidan don tabbatar da
tsaro, suna tunanin hanyar da ya kamata su bi
su samı nasarar shiga cikin gidan Sarautar a
lokaci guda farat daya. Bayan sun shafe 'yan
dakiku suna tunanı sai dabara ta fado wa Jarumi
Shaddadu ya dube ta ya ce, abin da za mu yi
yanzu kawai shi ne, mu yi fitar burgu da gudu
mu afkawa wadancan Dakarun da ke bakin
kofar gidan Sarautar. Da zarar mun tarwatsa
su zan dawo da baya ki tsaya a gaban kofar
gidan Sarautar ni kuma sai na rugo da gudu, ki
hada tafin hannayenki biyu a waje guda na taka
su da kafa daya ke kuma sai ki cilla sama na
haye katangar gidan na fada ciki, ina fadawa
zan tarwatsa masu tsaron bakin kofar daga ciki
ki shigo ciki, a sannan ne za a fara wannan
gagarumin Yaki. Koda jin wannan batu sai
murna ta kama Yaldisa. Nan take su biyun suka
mike zumbur! A lokacı guda suka zare makamai
suka ruga da azababben gudu izuwa kan masu
gadin da ke kofar gıdan Sarautar. Kafin daya
daga cikin masu gadin ya dauki wata katuwar
guduma ya doka akan wani babban Bandiri tuni
337
TASKARNOVELS.COM.NG
Yaldisa ta daka tsalle sama ta doki fuskarsa da
guiwarta. Nan take yai sama ya fado Kasa
sumamme. Shi kuwa Shaddadu sai ya afkawa
sauran masu gadin wadanda adadinsu ya kai
goma sha daya a lokacin da suka yi masa
rubdugu. suna kawo masa sara da suka ta ko
ina. Maimakon shu ma ya yake su da makami
sai ya rinka kaucewa harin nasu cikin wani irin
bakın zafin nama na al'ajabi ya rinka gabza
musu naushi. Duk wanda ya