An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
TASKARNOVELS.COM.NG
1
TASKARNOVELS.COM.NG
MAZAN JIYA
4
MAZAN JIYA
Littafi na biyu 4
Part D
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
MAZAN JIYA! (4)
Sai da sarki dujalu ya shafe sa.a shida cif yana
baiwa hursiya lbrin sadauki shaddadu na birnin
kufa, amma ba ta kosa ba da jin labarin har ya
zamana cewa dare ya raba amma ko gyangyadi
bata fara ba. Shi kuwa sarki dujalu a wannan
lokaci bakinsa ya gaji da surutu kawai so yake
yayi shiru don ya huta.
2
TASKARNOVELS.COM.NG
Dama ga tsananin gajiyar yaki gami da tsamin
jiki da radadin raunikan jikinsa sun dameshi.
Kwatsam! Sai Hursiya taji sarki dujalu yai shiru
ga barin zance..
Cikin tsanani damuwa ta dubeshi ta ce ya kai
dan uwana ina dalilin yin shirunka? Ina mai
rokonka bisa girman iyayenmu daka cigaaba da
bani wannan lbr mai dadi domin ina son naji
yadda karshensa zai kasamce kamar yadda na
ji na JARUMI HANTARU.
Koda jin wannan batu sai sarki dujalu yayi
doguwae hamma gami da murmushi sannan ya
dubi hursiyya yace haba yake yar uwata ai idan
kika ce na ci gaba da baki wannan lbr har sai na
je karshensa ba kiyi min adalci ba sbda koda
zamu kwna muna yi ba zai kare ba.
Ki sani cewa duk a cikin labaran uku babu
Hikaya mai tsawonta tunda gashi dai har yanzu
ba ta kammalu ba.
Kiyi hakuri idan mun yi tsawon rai nan gaba
bayan wanna yaki na karasa miki wannan
labari. Lallai akwai bukatar na kwanta domin na
3
TASKARNOVELS.COM.NG
sami isasshen hutu da bacci domin na sami
kuzarin domin iya ci gaba da yaki. Idan gari ya
waye.
Koda gama fadin hakan sai sarki dujalu ya
kwanta akan shimfidarsa yaja mayafi ya lulluba.
Faruwar hakan ke da wuya kuwa sai barci ya
sace shi, koda ganin hakan sai itama Hursiyya
ta kwanta akan tara shimfidar taja mayafi kuma
ta rintse idanu domin ta yi barci, amma sai
barcin ya gagara sakamakon tunani da fargabar
yadda makomar wannan gagarumin yaki zai
kasance idan anci gaba dashi a gobe ba ta sami
damar rintsawa ba sai da suba ta kusanto..
Sai da gari ya waye rana ta take amma sarki
dujalu da yar uwarsa gimbiya Hursiyya ba su
farka ba daga barci...
A wannan lokacin gaba dayan mutanen nasu
da ke sansanin tuni sun farka daga barci an yi
kalaci kuma an gama shirin ci gaba da yaki
sahun aljanu dabam da na mutane.. A wannan
lokacin manyan dakarun sarki dujalu matinu da
ratiju sun tsaya a gaban rundunar tasu suna
jiran fitowar sarki dujalu domin ya bayar da
4
TASKARNOVELS.COM.NG
umarni.... Tsakanin rundunar sun sarki dujalu
da ta su sarki Hamraz bai wucce taku dari biyu
ba sbda dama dukkaninsu abakin kogin na
bahar sufiyan suka yada sansani., kowanne
bangare suna hango abokan gabarsu...
Lokacin da matinu ta hango abokan gaba sun
gama nasu shirin tsaf kuma sarki maharaz
sadauki inmal da sadauki hibru na tsaye
agaban rudunar tasu sun zobo ido izuwa ga
nasu matinu kawai jira suke suga sarki dujalu
ya baiyana agaba,,. Cikin tsananin damuwa
matinu ya dubi dan uwansa ratiju yace ja ruga
izuwa tantin sarki ko lpya.. Kafin matinu ta
gama rufe bakinsa tuni ratiju yaruga izuwa can
tanti sarki yake.. Yana isa ya dubi dakarun da
suka Kewaye tantin don tabbatar da tsaron
yace kuyi min iso a wajen sarki. Kafin daya
daga cikinsu tace kala sai suka jiyo gyaran
,muryar sarki... Nan take sarki dujalu ya fito
daga cikin tantin a cikin gagarumar shigarsa ta
yaki kuma fuskaraa cike da annuri ya dubi
rantiju cikin murmushi yace ya kai babban
jarumi ka kwnatar da hankalinka kayi sani cewa
yau ba rana bace ta gaggawa domin kuwa a yau
ne za ayi tata kare! Ko dai muyi nasarar
5
TASKARNOVELS.COM.NG
wannan yaki ko kuma mai abonka gabar mu su
samu wata kila ayi ragas ina mai tabbar muku
da cewa yakin da muka yi jiya share fage ne ko
kuma wasan yara akan wanda za ayi yau.: (TAB
IJAM! DUK BAKAR GUMURZUN DA AKAYI KUNJI
PA WAI WASAN YARA YAKI CEWA TO KUBIYO
NI MUJI YAWANNAN NA YAU ZATA KASANCE
KENAN TIN DA YACE WANCAN WASA YARAN
NE SULEIMAN ZIDANE KD.) Yaune maza zasu
gane kurensu. Yau ne kasa da taiku zasu sha
jini suyi gyatsa, kuma a yaune tarihin jarumta
zai kafa kansa a bakin teku. Maza ka koma can
bakin filin daga ka gayawa rundunarmu cewa
gani nan tafe yanzu kuma ina zuwa za a fara
wannan yaki. A jirani zan gana da yar uwata
Hursiyya. Koda jin haka sai ratiju ya juya da
sauri kuma ya falfala da matsanaicin gdu
domin yaje ya isar da wannan sako. Tafiyarsa
ke da wuya sai sarki dujalu ya juya ya fuskanci
yar uwarsa Hursiyya suka kurawa juna idanu.
Nan take duk biyun idanunsu suka ciko da
kwlla. Hawayen sarki dujalu ne ya fara zubowa
sannan nata. Sarki dujalu ya sa hannu ya share
hawayen nasa yace yake yar uwata kiyi sani
cewa wannan hawayen nawa bai zubo ba
6
TASKARNOVELS.COM.NG
sboda tunanin zamu rabu ba. Tabbas ni na san
ba zan mutu ba a wannan yaki to amma taki
rayuwar ce bani da tabbacin zata tsira. Babu
mamaki wannan gani da nake yi miki shi ne na
karshe. Hanya daya ce nake zaton zan iya
tserar da rayuwarki wato nasa a dauke ki yanzy
a mayar da ke cikin birninmu domin ciki gaba
da tafiyar da mulkin kasata. A hakan ma bani
da tabbacin birnin nawa zai ci gaba da
wanzuwa.. Koda sarki dujalu yazo nan a
zancesa sai wani sabon hawaye yasake
gangarowa daga cikin idanu Hursiyya ta
dubeshi tace haba yakai dan uwana ashe har
ka manta da bayanin da nayi ,maka kenan a jiya
da daddare?? Nifa bazan iya rabuwa da kai ba a
yanzu sai dai a ci gabada wannan yaki a gaban
idanuna idan ma mutuwa zaka yi mu mutu tare
domin muddin bana tare da kai ba zan taba
samun sukuni da kwnaciyar hankali ba... Koda
jin hakan sai sarki dujalu ya juyawa Hursiya
baya a lokacin da shima hawayen ya sake
subuto masa ya ce ai kuwa sai dai kiyi hkr
domin rabuwarmu a yanzu ta zama dole.. Yana
gama fadin hakan yaka tafiya ya nufi inda
sansanin dakarunsa suke.. Koda ganin hakan
7
TASKARNOVELS.COM.NG
sai goimbiya Hursiyya ta yunkura da nufin ta
bishi ta gudu kawai sa taji an sureta an yi sama
da ita tamkar shaho ya dau shirwa. Wata irin
iska mai karfi taji tana busota a sama. Koda ta
dga kanta sama sau ta ga ashe wani aljanu ne
mai suna BARZARU ya dauketa wanda ya
kasance babban hadimin sarki dujalu. Koda
Hursiya taga barzaru ya juya da ita baya don
barin sansanin yakin gaba daya sai ta kwlla ihu,
ta fashe da matsanaicin kuka cikin sbda ta
gane cewa dan uwanta sarki dujalu ya
shammace ta ne ya sa a mayar da ita can gida
domin ta tsira da ga masifar wannan yaki. Haka
dai Hursiya ta ci gaba da ihu tama rusa kukan
bakin cikin har aljani barzaru ya luluka da ita a
cikin gajimare suka kule aka daina hangosu.. *
* * ACAN Sansanin yaki kuwa lokacin da sarki
dujalu ya iso filim dagar ya tsaya a tsakiyar
matinu da ratiju sai aka fara kallon kallon
tsakanin rudunar tasu da ta su sarki Maharaz.
Kowanne bangare yana da jinsin mutane da na
aljanu dukkaninsu a cikin gaagarumar shigar
yaki mai matukar kwarjini da ban tsoro. Wasu
aljanun ma ko kallomsu mutum yayi nan take
yake iya samin tabin hankali mai dakakkiyar
8
TASKARNOVELS.COM.NG
zuciya zai tsure da gudawa ya cika wandonsa
da iska. A dai dai wannan lokacin ne mulaifa ta
matso gaban inmal ta tsaya tana mai rike da
takobi, cikin tsananin mamaki inmal ta dubeta
yace yake masoyiya mene ne yakawo ki nan
filin yakin alhalin sarki ma yace ki yi zamanki a
cikin tanti har izuwa karshen Yakin? Sa.adda
mulaifa taji wannan tambayan sai tayi
murmushi tace ai idan har na zauna a cikin
tanti na bar masoyina yana fafatawa anan filin
daga kuma na bar mahaifina yana
gwagwarmaya ban cika jinin sarauta ba kuma
ban yiwa soyayya adalci ba. Idan har a wannan
yaki zaku mutu to ina fatan na mutu tare da ku.
Koda Gimbiya mulaifa tazo nan a zancenta sai
sarkin yaki hibru ya taho gareta domin ya
rarsheta ya mai da uta can baya inda tantin
sarki yake amma sai sarki Maharaz ya sha
gabansa yace ka kyaleta. Ai yana da kyau ta
nuna gadon gidansu. Cikin alamun tsananin
mamaki da fargaba Hibru ya dubi sarki Maharaz
yace haba ya kai abkna akan wane dalili za ka
bar yarka gda daya jal a duniya tayi wannan yaki
mai tsananin hadari alhalin ko sarrafa takobi
bata iyaba? Kuma bata da wani sihirin tsafi da
9
TASKARNOVELS.COM.NG
za ta iya kare kanta. Dajin wannan batu sai
sarki Maharaz yayi murmushi gami da yar
guntuwar dariya sannan ya ce abinda nakeso
da kai ya kai abkna ka zuba ido kawai zaka sha
mamaki. Sannan ina son ka gane cewa muddin
mulaifa tana tare da inmal babu abinda zai
sameta. Gama fadin hakan ke da wuya sai
sarki Maharaz ya wucce gaban rundunar da
kimanin tafiya taku goma sanan ya tsaya. Koda
ganin hakan sai shima sarki dujalu ya wucce
gaban tasa rundunar da kimanin tafiya taku
goma sannan ya tsaya.. Ya zamana cewa
tsakaninsa da sarki Maharaz bai wucce taku
arba.in ba amma sbda karfin sihirinsu
kowannesu na iya jiyo numfashin dayan. Nana
fa suka fara yin kallon kallo na yan dakiku
sannan sarki Maharaz yai ajiyar numfashi yace
ya wanan sarki kayi sani cewa yakin da muka yi
asarar Miliyoyin rayuka. A yau kuwa idan muka
cigaba zamu iya kawar da dukkkaninmu a
karshe duk mu tashi a tutar babu zamana cewa
babu wanda ya sami nasarar dauko TAKOBIN
SAIFUL LUJARA da ke karkashen wannan teku
na bahar sufiya dake gabanmu. Wai shin me
zai hana mu fito da wani tsarin dabam a
10
TASKARNOVELS.COM.NG
wannan yaki wanda zai kawo karshen rigimar
da ke tsakaninmu. Abinda nake nufi shi ne mu
ware jarumai uku uku daga cikin mu su yaki
juna. Idan nawa jaruman ne suka kashe naka
sai ka hkr ka bar mini takokobin SAIFUL
LUJARA. Idan kuma naka jarumai ne suka
kashe nawa sai na hkr na bar maka. Ba don
komai na yi wannan tunanin ba sai domin mu
rage asarar miliyoyin rayukan da za ayi anan
gaba. Sa'ad da sarki Maharaz yazo nan a
zancensa sai sarki dujalu ya tuntsure da
mahaukaciyar dariya kolacin guda kuma ya
turbure fuska tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa yace ya kai maharaz na ji duk abinda
kace kuma na aminta da shi. Amma bisa
sharadi guda biyu. Sharadi nafarko shine
jaruman uku uku da zasuyi wannan fafatawa ba
zasu yi amfani da karfin sihiri ba kuma sai kowa
ya rantse da abin bautarsa cewar ba zai yi
yaudaraba sai dai ya yi amdani da tsagwaron
karfensa da kwarewarsa ta yaki....
MAZAN JIYA
Littafi na hudu 4
11
TASKARNOVELS.COM.NG
Part B
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
Sharadi na biyu shine babu wanda zai zabi
abkin gwaminsa da kansa sai dai ayi kuria a
rubuta sunanyen jarumai shida a jikin duwatsu
a gwamutsasu a zubar a kasa kowa ya dauki
dutsen daya dauka shine abkin gwaminsa.
Yayin da sarki dujalu yazo nan a zancensa sai
sarki maharaz yai shiru yana tunani da nazari. A
wannan lokacin gaba dayan jamaar dake
sansanin yakin hakalinsu ya dugunzuma ainun
sbda sun san cewa idan har aka bi wannan
tsari wanda sarki dujalu yazo da shi dole ne ayi
asarae manyan abban dogaro na kowanen
bangare. Bayan sarki Maharaz ya gama nazari
da tunani sai ya dubi sarki dujalu yace ina
bukatar nayi shawara da mutanena.... Sarki
dujalu yayi murmushi yace na baka har tsawon
rabi sa a kaje jayi shawara bisa abinda zai
fisheju jai da jama arka... Koda gama fadin
hakan sai sarki dujalu ya juya da baya ya koma
cikin ayarin rundunarsa ya ja sadauki ratinu da
12
TASKARNOVELS.COM.NG
Matinu gefe daya domin suma su yi shawara.
Sarki Maharazya durfafi inda su Hibru ke tsaye
jikinsa a sanyaye fuskarsa cike da alamun
tsananin damuwa. Da isarsa garesu sai suka
kebe suka zauna a gefe daya suka shiga
tataunawa sarki Maharaz dubi Hibru sannan ya
dubi inmal yace me kake gani dangane da
shawarar da nazo da ita bisa rage yawan a
sarar miliyoyin rayukan da za a yi nan gaba?
Hibru da inmal suka junansu suka sunkui da
kansu kas sai ga mataimakin hibru ya taho
gareshi barde KURSHAM. Kursham ya zauna
daf da sarki maharaz ya risuna cikin
girmamawa yace ya Shugabana ka zo da
shawara mai kyau amma kuma itace mafi
hadari idan ka yi la.akari da sharuddan da sarki
dujalu ya kafa. Ka sani cewa kai kanka baka da
wani abin dogaro wanda yafi karfin sihirin tsafi
kuma gashi An ce baza ayi amfani da tsafin ba
sai dai mutun yayi amfani da tsagwaron karfin
sihirin tsafi kuma gashi ai amfani da tsagwaron
karfin dantsensa, lallai kuwa in dau hakan za
ayi to babu kai a cikin wanna fafatawan da za
ayi mutum uku uku koda jin haka sai sarki
maharaz ya dakawa barde kursham tsawa yace
13
TASKARNOVELS.COM.NG
wnann wacce irin maganar banza kake yi haka?
Ka sanin cewa yadda nake kishin jamaata da
kasata bana kishin tawa rayuwar don haka
lallai dani a cikin mutane ukun da zasu yi
wannan fafatawa. Kafin sarki maharaz ya gama
rufe bakinsa tuni sarkin yaki Hibru ya taru
numfashinsa a fusatace cikin daga murya yace
dakata ya kai abkna ka yi sani cewa wani
lokacin ran mutum daya yafi na mutane
dubunanai muhimmaci. Shin baka tunanin
cewa idan aka kasheka a farko wanna yaki
jama armu zasu sami karayar zuciya su kasa
aiwatar da komai a wanna yaki? Shin baka
tunanin cewa kai bango ne babban a filin yaki
wanda idan ya fadi bamu da kwnacin hankali a
can gida da nan waje. Kuma makiya zasu sami
karfin guiwar daza su dada zage dantse
akanmu domin ganin sun gagauta shafemu.
Abin nake so da kai shine ka amince mana mu
uku nan ni Hibru da Inmal mu wakilceka a
wannan Gumurzu da za ayi. Koda jin haka sai
sarki mahaza ya yunkura a fusace yace ba zan
taba yarda ba ayi hakan ba. Ai mutuwa tace
maza ta dada kara muku fishi da kwarin guiwa a
wannan filin daga kuci gaba da ragargaza
14
TASKARNOVELS.COM.NG
abokan gaba har ku karar dasu.. Da jin haka sai
sarki yaki Hibru ya matso gaban sarki Maharaz
ya kusanceshi ainu yadda har suna iya jin
numfashin juna yace ya kai abkina ka sani
cewa tsawon shekaru ina bauta a karkashinka
kuma ina yi maka biyyya ban taba kin bin
umarninka ba amma a yau baza ka bi umarnin
naka ba kuma zan yi maka dole akan ka hakura
da shiga wannan yaki idan kuma kaki to zan
kashe kaina. Koda gama fadin hakan sai
hawaye ya zubiwa Hibru aL.amarin da ya karya
zuciyar sarki maharaz kenan nan da nan shima
idanunsa suka ciko da kwallah ya rugunme
Hibru yana mai cewa hakika yau ka nuna mini
cewa bani da wani masoyi da ya fika a doron
kasa don haka na janye nawa nunfi. Ku tafi ku
ukun ku wakilceni a wannan yaki. Zan ci gana
da hangenku daga nan inda nake. Ubangiji
Durbuza ya baku nasara koda gama fadin
hakan sai sarki maharaz ya janye jikinsa daga
cikin na Hibru. Shi ku,ma hibru sai yadubi inmal
da barde kursham yayi musu inkiyar su bishi
izuwa can filin daga. Nan take kuwa suka bishi
da sauri suka nufi can tsakiyar filin suka tsaya.
Suleiman zidane kd) A sanna ne sarki dujalu
15
TASKARNOVELS.COM.NG
Matinu da Ratiju ma suka tunkarosu. Sai ga ya
rage saura bai fi taku goma ba a tsakaninsu
sannan suka tsaya aka yi mugun kallon kallo
yan dakiku. Nan take sarki dujalu yasa aka
kawo tsakuwoyi guda shida masu dan fadi aka
rubuta sunan kowannesu jikin tsakuwa guda
sannan aka zuba tsakuwunyi duka shidan a
cikin wani kurtu aka karkada suka hautsine a
cikin sannan aka ajiye a kasa. Sarki dujalu ya
bushe da dariya mugunta kuma ta turbune
fuska yace kowannemu daya bayan daya zai
zura hannusa ya dauko tsakuwa guda a cikin
kuttun nan. Duk tsakuwar da mutum ya daulo
to sunan wanda ke jikin tsakuwar shine abkin
gwaminsa. Suwaye zasu fara zabar tsakuwar
mu ne ko kuma kune? Sariki dujalu ya tambaya
yana mai kallon fuskar inmal. Inmal yayi dan
guntun murmushi mai nuna dakewar zuciya da
jarumta ya ce kune zaku fara zaba sanna mu.
Sarki dujalu ya bushe da dariya yace ai komai
nisan jifa kasa zai fado. Yaro yau zan kasan
cewa dujalu murucin kan dutse ne bai fito ba
sai da yashirya kuma zaku san cewa kun tabo
tsulliyar dodo. A yau ne zan karar da dukkanin
wannan runduna taku sannan na shiga cikin
16
TASKARNOVELS.COM.NG
karkashin kogin BAHAR SUFIYA na dauko
TAKOBIN SAIFUL LUJARA daga nan naje na
dauko MASHIN GALILLUL HARAS da HULAR
LAMSARA wato na hada MAKAMAN da zan
gagaru duniya gaba dayanta na zama sarkin ko
ina da ina. Ka sani cewa birninku shi ne na
farkon wanda zanje na mallakeshi. Waccan
yarinyar kuwa Gimbiya Mulaifa wacce kake
tsananin so zan masheta baiwa na wulakantata
tamkar Akuya.. Kafin sarki dujalu ya gama
wannan furuci tuni zuciyar inmal ta kufulo
jikinsa ya kama tsuma don haka sai ya daka
masa tsawa yace karyarka ta sha karsha yakai
wannan sarki. Kayisani cewa nine mai