muka ji wani irin gurnani mai
tsananin ban tsoro a bayanmu. Cikin tsananin
firgita ni da mahaifiyata muka waiga baya ai
kuwa sai muka yi arba da aljani Raugatul
Aguwanu: Nan takemuka razana ainun:
Faruwar hakan ce tasa nayi tuntube na fadu
kasa: ina faduwa sai wannan dutse dake tafin
hannuna ya subuce ya gangare kasa can
gabana: kafin na mike ba ruga inda dutsen yake
sai kawai naji an figeni anyi sama dani ana ta
kyalkyala wata dariya mugunta: Abinda
idanuna kawai suka iya hangowa sa adda na
kallo kasa shine: Haukacewar mahaifiyata tana
135
TASKARNOVELS.COM.NG
ihu tana cisge gashin kanta kuma tana
sambatu. Daga nan sai jinayi an lulaka dani
izuwa can kololuwar samaniya a sannan ne jiri
ya debeni: Lokacin fa na farka na bude idanuna
sai na tsinci kaina a cikin wannan dan karamin
keji da ke rataye a saman kogon aljani
RAUGATUL AGAWANU: a firgice na mike tsaye
na kama kai kawo cikin kejin: a sanan ne na
gane cewa an asirceni na zama yar mitsitsiya:
Nan take na kwarara uban ihu kuma na fashe
da matsanaicin kuka: lokacin da Gimbiya
Shalbirat ta zonan a Labarinta sai hawaye ya
zubo mata ta dubi sadusa Halyal tace wannan
shine labarina don haka ni na sancewa anan
dajin zan gama rayuwata tunda ba zaku iya
kubutar dani ba daga hannun wanan azzalumin
aljani kuma ko dama kin kubutar dani bani da
sauran sha awar cigaba da rayuwa tuda bani da
sauran masoyi a doron kasa: Koda jin wannan
batu sai tausayin shalbirat takama boka
sadusa da dansa halyal har idanun su suka
ciko da kwallah: kawai sai halyal ya dube
shalbiyat yace yake wannan ma abociyar
kyawu kayi sani cewa baki databbacin cewa
mahaifiyarki tana raye ko ta mutu? Saboda
136
TASKARNOVELS.COM.NG
haka bai kamata ki cire sha awar ci gaba da
rayiwa b a doron kasa, bayan haka ina mai
tabbatar miki dacewa mahaifina da muke tare
da shi a yanzu zai iya kubutar dake daga
hannun wannan aljani kua na yi miki alkwari
komai dadewa sai na rakaki har izuwa birninku
kin sadu da mahaifiyarki muddin tana raye:
Haka kuma indai juzairat na nan a raye sai kin
dauki fansa akanta: Sa adda Gimbiya
Shalbiraat taji wannan bau sai ta girgiza kai
tace wannan albishir naka daidai yake da
tatsuniya a cikin kunnena ko kumma na kirashi
da mafaarki da va zai taba zama gaskiya ba:
Koda jin haka sai boka sadusa yayi dariya
sannan ya dubi shalbirat yace ke yarinya
abinda dana yafada miki gaskiyane amma bari
na fara nuna miki karfin aikina tun daga yanzu
Gama fadin hakan ke da wuya sai sadusa ya
karanta wadansu dalasiman tsafi guda bakwai
ya tofa akan tafin hannunsa na hagu sannan ya
dafa kan shalbirat
137
TASKARNOVELS.COM.NG
Nan take Shalbirat ta dawo cikakkiyar surarta
ta budurwa mai tsananin kyauwun diri da sura
maimakon yadda ta kasance a da yar mitsitsiya:
Shi kansa sadusa sai daya dimauce bisa ganin
tsananin kyawun nata: Yayin da shalbirat taga
ta dawo izuwa chakkiyar surarta ta mutum sai
ta cika da tsananin farin ciki ta kama kyakyal
dariya kamar bazata daina ba, sai daga can ta
nutsu ta dubi boka sadusa ta durkusa har kasa
bisa guiwoyinta takama yi masa gdya shi kuma
sai ya kama kafadunta ya yasheta tsaye suka
fuskacin juna yana mai yi mata murmushi yace
wannan taimako dana yi miki ba komai bane
face taimakon kaina domin kema akwai
muhimmiyar rawa da zaki taka nan gaba bisa
bukatar da ta fito damu daga birninmu
A gobe ne zan rabaki da wannnan daji kuma
idan mun isa can bakin kogin bahar sufiya za ki
rabu da wannan azzalumin aljani har abada:
yanzu sai kuzo mu cigaba da yawatawa a cikin
wannan daji har izuwa lokacin da aljani
Raugatul Aguwanu ya bukata: Koda gama fadin
haka sai boka sadusa ya kunna kai izuwa cikin
138
TASKARNOVELS.COM.NG
dajin cikin sauri shalbirat ta kama hannun
Halyal suka taja shi suka bi bayan boka sadusa
Haka dai su boka sadusa suka yi ta yawo a
cikin dajin Darul HusHushul Maut; Shalbirat ta
wucce gaba tana yi musu jagora har suna
mamaki yadda ta lakanci hanyoyin dajin: Ai
kuwa sai suka yi ta ganin abubuwan al ajabi
wanda basu taba tsamamanin zasu gani ba:
Abinda suka gani kuwa shi ne gaba daya
bishiyoyin dajin na yan yan itatuwa ne iri iri
sannan kuma bishiyoyin da ruwa ke zuba daga
cikinsu mai haske da dadin dandano, gaba daya
dajin a cikin ni ima yake kuma kowanne wuri
irin tasa ni imar dabam data gaba: Duk inda
mutum ya shiga ba zai ji zafi ba kuma ba zai ji
sanyi ba sannan a duk inda zaka kwanta wata
irin ciyawa ce a lullbe mai tsananin laushi
kuma hankalo kwance mutum zai yi
kwanciyarsa babu tunanin wani kwaro zai
cijeshi ko kuma wata muguwar dabba zata
kawo masa hari
139
TASKARNOVELS.COM.NG
Nan take sadusa Halyal da shabirat suka
tsinko yayan itatuwa kala kala masu dadi suka
sami wuri suka zauna suka kama ci suna hira
har sai da suka koshi sannan suka mike suka
cigaba da yawo abinsu: Shalbirat Dai a
wannan rana ji ta yi taamkar an tsamota daga
cikin gagarumar wuta an sanyata a cikin ruwan
sanyi sbd farin ciki
Haka dai suka wanzu suna yawo har suka gaji
suka kwanta suka kama barci: Al amarin aljani
Raugatul Aguwanu kuwa tunda ya sha wannan
giya yayi tatul kama barci bai farka ba sai da
dare ya raba: A firgice ya farka zuciyarsa na
dukan uku uku: Cikin hanzari ya mike tsaye ya
dauko madubinsa na tsafi ya shafeshi: Nan
take yaga Hoton Shalbirat Sadusa da Halyal a
cikin dajin a kwance suna ta shara barci. koda
yaga Shalbirat a cikin cikakkiyar surarta: ta
mutum sai ya razana ainun ya kuma tabbatar
da cewa lallai boka sadusa ya cika hatsabibi
domin shi a tunaninsa baza a taba samun
bokan da zai iya karya wannan asirin ba: Nan
dai zuciyarsa ta kama sake saketana mai gaya
140
TASKARNOVELS.COM.NG
masa cewa: AI KAWAI YANZU TUNDA SU BOKA
SADUSA BARCI SUKEYI YAJE YA KASHESU YA
DAUKE SHALBIRAT YA SAKE MAI DA ITA YAR
MITSITSIYA YA SATA A CKIN KEJINTA: wata
zuciyar kuma sai ta ce da shi
TO IDAN KUMA KA KASHE WANNAN BOKA
WAYE ZAI TSERAR DA KAI DAGA SHARRIN
SARKI DA ZAI MALLAKI KAYAN YAKIN MAZAN
JIYA? TABBAS IDAN KA BIYEWA SON
ZUCIYARKA ZAKA YI CIN DARE DAYA NE
KUMBURIN CIKI: ZAI FI KYAU KA TSAYA KA GA
IYA KOKARIN DA WANNAN HATSABIBIN BOKA
ZAI YI MAKA. haka dai aljani Raugatul Aguwanu
yayi ta wasi wasi acikin zuciyarsa har dai daga
karshe ya yanke shawarar ya jira abinda zai faru
a gaba: Kashe gari da sassafe su boka sadusa
suka farka daga barci kawai sai suka ga aljani
Raugatul Aguwanu zaune a can gefe daya ya
zura masu idanu: koda suka tashi zaune sai
Raugatul Aguwanu ya risina ga boka sadusa yai
gaisuwa sannan ya dubi shalbirat ya sake
duban sadusa yace ya shugabana anya kuwa
bakayi mini gaggawa ba? Ai ina ganin cewa bai
141
TASKARNOVELS.COM.NG
kamata ka ai da shalbirat izuwa ainahin siffata
ba tun yanzu tunda ban gamsu da cewar za ka
iya warware mini matsalata ba
Koda jin wannan batu sai boka sadusa ya
murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa ya dakawa Raugatul Aguwanu harara
yace shin kaine ka fini sani abinda yafi dacewa
muyi ko kuwa nine? Raugatul Aguwanu ya
sunkui da kansa kas ya ce ka gafarceni ya
shugabana mantawa nayi
boka sadusa yai murmushi yace yanzu nake
son ka daukemu mu ukun nan domin mu tafi
izuwa can sansani yaki wato can baki kogin
bahar sufiya : koda jin haka sai idanun Raugatul
Aguwanu suka zazzaro ya kamu da tsananin
tsoro yace haba ya shugabana ya ya zaka ce na
kaimu izuwa inda ajali yake? Ina mai tabbar
maka dacewa masifar da ke bakin kogin bahar
sufiya a yanzu babu kamarta a ko ina a cikin
duniya
142
TASKARNOVELS.COM.NG
koda jin haka sai boka sadusa yayi murmushi
sannan yace ai ba wai ina nufin muje har inda
ake yakin bane zaka sauke mu ne acan bayan
kogin bahar sufiya nesa da inda ake fafata yakin
sannan kaje kayi mana leken asiri bisa abinda
ke faruwa
abinfa nake bukata kawai shine nagane
bangaren da suke samun nasara: Da zarar na
gano hakan akwai a sihirin da zanyi daga inda
muke mu dauko Takobin SAIFUL LUJA RA a
karkashin kogin ba tare da su sarki dujalu sun
sani ba mu bace daga wajen
kaga kenan sun sha wahalar banza kuma sun
kashe junansu a banza wato kura da shan bugu
gardi da kwashe kudi
koda boka sadusa yazo nan a zancesa sai
aljani Raugatul Aguwanu ya kura masa idanu
143
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin alamun rashin yarda yai shiru yana tunani
da nazari. Daga can sai ya ce kai boka nifa ina
ganin cewa kazo mini da zance na rainin hakali:
Yaza ai kace zaka iya dauko takobin saiful
lujara da karfin sihirinka alhalin wadanda suka
fika karfin sihirin nesa ba kusaba sarki dujalu
da sarki maharaz tuntuni sun kasa daukota?
Koda ma dayansu ya sami nasarar wannan yaki
sai ya sha bakar wahala kafin yagano inda
takobin take acikin karkashin tekun: Kai ni ga
yadda mana sami tarihi cewa aka yi tsaron
dake inda takobin take yafi gaban hasashen
mai hasashe sai dai abinda ido ya gani kawai.
Zan ci gaba. Da fatan an tashi lafiya, sannan
duk wanda yake son complete zai iya tuntubata
ta wannan number 08138873799 kira ko
whatsapp. MAZAN JIYA Littafi na Hudu (4)
Part M Na Abdulaziz Sani m gini Typing
Abubakar Saleh AlQuyraemey Koda ma
dayansu ya sami nasarar wannan yaki sai ya
sha bakar wahala kafin yagano inda takobin
take acikin karkashin tekun. Kai ni ga yadda
mana sami tarihi cewa aka yi tsaron dake inda
takobin take yafi gaban hasashen mai hasashe
sai dai abinda ido ya gani kawai. koda jin
144
TASKARNOVELS.COM.NG
wannan batu sai boka sadusa ya murtuke
fuskarsa yace to shikeanan idan har baka
aminta da abin danake gaya maka ba sai ka
yankewa kanka hukunci. kofa dai yanzu my yaki
juna ni dakai wandaya kashe dayan yayi abinda
yaso: ko kuma murabu salin alin kowa ya kama
gabansa: amma kasani dace idan muka rabu
salin alin har abada ka rabuda Gimbiya
Shalbirat kenan baza kasake mallakarta ba:
lokacin da boka sadusa yazo nan a zancesa sai
hankali aljani Raugatul Aguwanu ya
dugunzuma ainun fiye da ko yaushe yarasa
abinda ke masa dadi a duniya, nan fa ya kasa
zaune ko tsaye ya rinka kai kawo. daga can sai
ya dubi sadusa yace ka bani sa a uku na koma
can kogona nayi bincike. da tunani tukkunna:
sadusa yai murmushi yace jeka nabaka tsawon
sa a biyar ma: nan take aljani Raugatul
Aguwanu ya bace bat tamkar kiftawar ido: A
Sannan ne shalbirat ta dubi boka sadusa cikin
alamun tsoro tace yakai abul halyal anya kuwa
kana ganin cewa Raugatul Aguwanu zai amince
ya daukemu yakaimu bakin kogin bahar sufiya?
To wai shin ma meye hikimarka ta zuwanmu
can din alhalin kasan cewa sansani ne na
145
TASKARNOVELS.COM.NG
mutuwa? Sadusa yai ajiyar zuciya sannan yace
kiyi hakuri yake wannan yar sarki: Ki tuna cewa
mu bamu baki labarin mu ba kamar yadda kika
ban mu naki sakamakon cewar babi isashen
lokaci na yin haka: Ni dai kawai abinda na sani
shine sau tari sai ka tari aradu da ka sannan
kake fita daga cikin wata masifar: akwai abin
da ya baromu da kasarmu kuma bukatarmu ba
zata biya ba face mun dangana da bakin tekun
bahar Sufiya inda ake yin wannan yakin: kuma
ki rungumi kaddara har izuwa sa adda zamuje
can dinko bakomai dai gwara ki mutu acan
sansanin yakin da dai ki mutu a hannun
wannan azzalumai alajni: kodajin wannan batu
sai shalbirat ta jinjina kai tayi shiru bata kara
cewa komai ba
* * *: BIRNIN SARKI DUJALU: ACAN gidan
sarautar sarki dujalu kuwa tundaga ranar da
kunyaga lazimat ta tafi neman hanyar da
Gimbiya Hursiya zata sami damar komawa
sansanin yaki a cikin kwanki kadan bata dawo
ba har kwanaki biyu da aka dirba mata suka
cika: A dare kwana na biyun ne hankalin
146
TASKARNOVELS.COM.NG
Gimbiya Hursiya ya dugunzuma ainun ta kasa
zaune ko tsaye: fara zubar da hawaye domin ta
saddakar da cewar har abada baza ta sake
ganin dan uwanta ba sarki dujalu ba, babu
abinda yake kara fusatata facw a duk sa adda
ta leka wajen turakarta ta cikin taga sai ta
hango aljani barzaru yana shawagi a saman
turakae yana kewayeta don tabbatar da tsaro
wato dai ta san cewa gadinta yake yi babu
yadda za ayi wani ya iya zuwa yatafi da ita
batare da yagani ba: Gimbiya Hursiya na cikin
wannan hali ne ta jiyo alamar takun sawu an
nufo kofar turakar Ta kawai sai ta zuba idanu
akan kofar shigowar: abinda ta sani shine
koma wanane ya taho in dai bai kasance daya
daga cikin kuyangitaba ko bayinta aljani
barzaru ba zai barshi ya shigo ba: Ashe ba wani
bane ya durfafo turakar ta ba face kuyanga
lazimat rike da wani jan fure mai kamshin gaske
fisa faranti: yayin daya rage bai fi saura taku
biyar ba tsakanin kuyaga lazimat da kofar
turakar gimbiya sai kawai taga aljani barzaru ya
fado juf a gabanta; ko Gezau batayi ba ta
dubeshi a fusace yace meye haka zaka sha
gabana alhalin kasanni na sanka ko kuwa ni
147
TASKARNOVELS.COM.NG
bakuwa ce a gidannan? Aljani barzaru ya daka
mata tsawa wacce tasa hanjin cikinta ya kada
hannunta yakama karkaewa har farantin dake
hannunta ya fadi kasa tayi sauri daukeshi:
Barzaru yadubi wannan fure dake kab faranti da
kyau sannan ya dubi kwayar idanun lazimat ko
zai ga alamun rashin gaskiya a tare da ita sanna
ya ce: ke tsohuwar makira: ni fa ban yarda dake
ba ina kyautata zaton cewa akwai wani kullin
boye da kuke shiryawa ke da gimbiya. shin
baku san cewa ina lura da dukkan motsi ku ba?
Yau kwanaki biyu kenan rabonki da turakar
gimbiya alhalin kullum kuna tare baku taba
rabuwa ba sai sa adda sarki ya tafi da gimbiya
bakin tekun bahar sufiya: lallai akwai alamar
cewa ta turaki ne kiyi mata aikin ne don haka
ban yarda da wannan furen da kika kawo mata
ba: bani shi na koneshi: Har aljani Barzaru ya
yunkura zai dauke fure sai ya jiyo muryar
gimbiya Hursiya tana mai daka masa tsawa; ba
shiri ya janye hannunsa: nan take Hursiya ta
dako kofar turakarta ta fito waje cikin tsananin
fusata ta dubi aljani barzaru tace au sbda
samun dama shine zaka wuce gona da iri a
cikin aikin naka na gadinna? Shin ka manta ne
148
TASKARNOVELS.COM.NG
cewar tun ina yarinya karama babu abinda
nakeso sama da jan fure? Ka sani cewa labari
ne yazo mini cewa an sami sabon samfarin jan
fure a can birnin zandal shi ne na aikata taje ta
siyo mini shi kuma ka san cewa dole ne mutum
ya shafe kwana biyu kafin yake birnin zandal ya
dawo
ka dubi wannan fure da kyau kaga ni zaka ga
cewa yasha bamban da irin sauran janjayen
furen da ake kawomini: Koda jin haka sai aljani
barzaru ya kurawa wannan fure idanu nan take
kuwa ya ga lallai fure ne dabam domin bai
kasance ja zallah ba akwai ratsin ruwan dorawa
a jikinsa: koda ganin hakan sai ya zube kasa a
gaban Gimbiya ya kama tuba; ko kallinsa
Gimbiya batayi ba ta kama hannin kuyanga
lazimat taja izuwa cikin turakar suka rufe kofa
suka kulle: A sannan ne aljani barzaru ya mike
tsaye ta bude fuka fukansa yai sama yana mai
cigaba da shawagi yana kewaya saman turakar
ta gimbiya don tabbatar da tsaro: ABINDA BAI
SANI BA SHINE AN KULLE KOFA DA BARAWO
KUMA BAWANI BANE BARAWON FACE
149
TASKARNOVELS.COM.NG
WANNAN JAN FURE WANDA KUYAGA LAZIMAT
TA SHIGA DA SHI CIKIN TURAKAR GIMBIYA:
Lokacin da Gimbiya Hursiya ta ja kuyanga
lazimat izuwa cikin turakarta sai suka shige har
can cikin daki barcinta: Suna shiga sai lazimat
ta rufe dakin gami da tagogi sannan ta fiddo
wani turare wuta na tsafi daga cikinAljihun
rigarta: take turarren wuta ya kunna kansa
hakinsa ya cika dakin gaba daya tamkar hazo
ne ya shigo dakin: faruwar hakan ke da wuya
sai wannan jan fure da ke kan faranti wanda
lazimat taxo dashi ya rikide ya zama wani dan
wadan aljani mai kwalelen kai wanda tsawonsa
bai wucce kamu biyu ba. Tunda gimbiya
Hursiya ta zo duniya bata taba ganin mitsitsin
wada kamar saba sai kace yar tsana: yana da
kwala kwala idanu kamar na mujiya hancinsa
kuwa wakakeke ne kamar na a zura kwai a ciki:
yana da dan mitstsin baki tamkar kwallon
dabino bazai iya shigewa ba: kafafuwansa
kuwa yan dugul dugul ne kaman na agawagi:
koda bayyaynar wannan aljani sai gimbiya
Hursiya ta fadawa kainun taja da baya cikin
sauri tana mai fadawa kan gadonta kamar za ta
kwalla ihu: cikin tsananin razana ta dubi
150
TASKARNOVELS.COM.NG
kuyanga lazimat tace sabda me zaki jeki nemo
mini wannan aljani n mai ban tsoro haka? Koda
jin ewannan tambaya sai kuyanga lazimata tayi
murmushi sannan tace ya shugabata wannan
aljani ba mai cutarwa bane kawai dai halittarsa
ce haka: nantake dan wadan yadaka tsalee
daga fartanti dayake ya dure kasa daf da gadon
Gimbiya yai sujadda agareta yace sunana boka
RADIYAL IBN ZAILUR: INA zaune a can nahiyar
da ke kudanci taku ne sako ya riskeni cewar
kina neman wanda zai kaiki can sansanin yaki
na teku bahar sufiya shiyasa na taso da kaina
nazo domin na biya miki wannan bukata amma
bisa sharadi guda?? ANAN ZANDAKATA SAI
KUMA IN ALLAH YAKAIMU GOBE DASAFE
DAFATAN ZAN IMIN AFUWA NA KWANA BIYU
DA AKAJENI. Da fatan an tashi lafiya, sannan
duk wanda yake son complete zai iya tuntubata
ta wannan number 08138873799 kira ko
whatsapp. INA zaune a can nahiyar da ke
kudanci taku ne sako ya riskeni cewar kina
neman wanda zai kaiki can sansanin yaki na
teku bahar sufiya shiyasa na taso da kaina nazo
domin na biya miki wannan bukata amma bisa
sharadi guda:?? Cigaba: Page 125 Koda jin
151
TASKARNOVELS.COM.NG
wannan jawabi sai Gimbiya Hursiya ta tashi
zaune tana ;mai gyara zama sannan ta dubi
boka Radiyan ciki murmushi tace ina
sauraronka ya kai wannan babban boka:
Radiyan yayi gyaran murya sannan yace a halin
yanzu nayi bincike na gano cewa a duk fadin
duniya babu wani aljani dazai iya zuwa bakin
kogin bahar sufiya a cikin yan kwanaki kadan
kafin a gaa gagarumin yaki da ake fafatawa
acan face aljani daya wanda ake kira da suna
Raugatul aguwanu wanda ke zaune a cn dajin
darul Hushshul maut: Dajin ne wanda sama da
shekaru bakwai baya mutane aljanu dabbobi
da tsuntsaye da kwari suka daina shiga ko
wanzuwa a cikinsa amma a halin yanzu wani
takadarin boka dake nan garin mai suna
sadusa ya karya kofin da ke dajin ya shiga har
ya sadu da aljani Raugatul aguwanu zai
daukeshi a gobe su tafi izuwa bakin kogin na
bahar sufiya: zan iya kaiki can dajin Darul
Hishushul maut a yau dinnan acikin abinda
wuce sa a biyar ba kuma zamy shiga ne a
sirrance ba tare da mun bari su aljani Raugatul
aguwanu sun ganmu ba ko suji motsinmu ba:
Nida ke zamu shiga cikin kunnen aljani
152
TASKARNOVELS.COM.NG
Raugatul aguwanu ne muyi zamanmu a ciki a
lokacin da yake barci: Ba zai taba sanin da
zamanmu ba a cikin kunnen nasa muddin
zamu jure yi masa susar kunne domin a duniya
babu abinda yake sa shi yamanta da koai face
susar kunne: Page 126 zidane kd
A haka za a tadi dau izuwa bakin tekun bahar
sufiya ba a sani ba: Sharadin dake tsakanina
dake shi ne ba zan yarda na kaiki inda aljani
Raugatul aguwanu yake ba face kinyi alkawari
cewar idan dan uwakinki sarki dujalu ya sami
nasarar cin yaki kuma ya dauko takobin Saiful
Lujara zaki sa ya maisheni daya daga cikin
manya fadawansa na hannun dama: lokacin
da boka radinya yazo nan a jawabinsa sai
hankalin gimbiya Hursiya ya dugunzuma tayi
shiru tana tunani da nazari al amarin ta rasa
abinda zatace: daga can sai ta dago kai ta dubi
boka radiyan tace yakai wannan boka kayi sani
cewa ina da wadansu yan tambayoyi a gareka
kafi na aminta dakai: da farko dai ina son kaga
mini dalilin da yasa boka sadusa yaje ya hada
kai da aljani Raugatul aguwanu domin yaje
153
TASKARNOVELS.COM.NG
sansanin yaki? Tambaya ta biyu itace ta ya kake
tunanin zaka iya fitae dani daga cikin gidan
sarautae nan har ka kaini dajin darul hushushul
maut alhalin aljani barzaru na shawagi a saan
turakata yana gadina? Tambaya ta uku wacce
itace ta karshe yaza ayi muyiwa aljani