da masoyiyata , kuma
na asa wasiyyar masoyiyata. Nan take shima
Aljani Maruful Dauwaz ya murdewa kansa wuya
ya fadi kasa matacce. A dai dai wannan lokaci
ne Sharlis ta zqre Takobinta ta yunkura zata
afkawa Sarki Laffaru sai ya dakatar da ita da
hannunsa ya dubeta yace, To yanzu idan ma kin
kasheni meye ribarki? Ni kaina yanzu duniyar ta
fita daga raina. Ki duba kigani na rasa yata,
kuma na rasa matata, kin rabani da mulkina, kin
rabani da kasata, me zan zauna nayi a duniya ,
wanne dadi ko farin ciki ne yai mini saura? Zan
tafi na bar miki duniyar in yaso keki ci gaba da
jin dadinta idan harbtana da dadin idan babu
masoyi. Kafin Sharlis ta ce wani abu tuni Sarki
laffaru ya zaro wuka a jikinsa ya kiba a cikinsa.
354
TASKARNOVELS.COM.NG
Nan take shima ya sulale kasa matacce. A dai
dai wannan lokaci ne Yaldisa tarugo wajen da
gudu tana kuka bisa hango gawar jarumi
Shaddadu. Ai kuwa itama Sharlisa sai ta
yunkura zata cakawa kanta Takobi a ciki,
ammavsaibYaldisa tadaka tsalle sama ta buge
Takobin ta fadi kasa ta dakawa Sharlis tsawa
tace, Idan kuma kika kashe kanki waye zaici gab
da mulkin Birnin kufa? Idan babu ke wa zamu
kalla mu tuna da masoyinmu? Na sami
labarinki kaf a wajen masoyina Shaddadu.
Tabbas Sarki laffaru yaci zarafinki dana danginki
amma kin wahalar da kanki akn daukar fansa
gashi ta janyo miki asarar da tafi wacce kika yi a
baya. Sau tari hakuri shine ya fi komai a
wannan rayuwa. Koda jin haka sai Sharlis ta
sake fashewa da matsanaicin kuka, ta zunguri
cikin tsuntsun tsafinta ya sauko kasa ta dira. Ita
kuwa Yaldisa sai taje ta sare kan Sarauniya
Zubaina ta dagashi sama a dai dai lokacin da
ragowarbDakarun gidan suka rugo wajen. Duk
wadanda suka karaso suka ga kan Sarauniya
Zubaina a hannun Yaldisa kuma sukaga layu da
gurayenta na tsafi sai su zube kasa suyi mata
sujjada. Nan take aka dira Yaldisa akan karagar
355
TASKARNOVELS.COM.NG
mulku, sannan aka shiga binne gawarwakin su
jarumi Shaddadu. Sai da aka kwana bakwai ana
bikin binne sun amma dare da rana Sharlis bata
da abin yi sai kuka Abincima sai Sarauniya
Yaldisa ta dura mata abaki sannan take ci.
Bayan an gama bikin binne su ne Sharlis ta yiwa
Yaldisa sallama ta hau kan tsuntsun tsafinta ya
tashi da ita sama tanabeaigen kabarurrukan su
Shaddadu tana zubar da hawaye har ta luluka a
cikin gajimare. Cikin sa'o'i kadan ta isa Birnin
kufa, inda ta zauna taci gaba da rayuwarta a
cikin mulki, amma bata gushe ba tana yin kuka
a kullum saboda tunani da begen danta
Shaddadu har ma tayi aure ta haifi yayaye ta
tsufa ainun. Kai har a ranar da ajalinta yazo da
hawaye na begen Shaddadu ta mutu. Har yau
har gobe idan mutum yaje birnin Sarauniya
Yaldisa zai ga inda aka gina kabarurruka guda
hudu, na Shaddadu, Ziya'ul Hak, Sarki Laffaru
da matarsa Ramlatul Siyam. Lokacin da Sarki
Dujalu yazo nan a cikin labarinsa sai tari ya
turnuke shi gami da aman jini, take Hursiyya ta
kankameshi tana mai fashewa da kuka ta ce ya
kai dan uwana kayi sani cewa kaima kayi rashin
dabara irin ta Sharlis tunda gashi kaima zaka
356
TASKARNOVELS.COM.NG
mutu burinka bai cika ba, duk wahalar da kasha
a baya tsawon shekara da shekaru ta zama ta
banza, inda ka karbi wannan addini na gaskiya
da tabbas sai zuciyarka ta yi sanyi ka rungumi
kaddara, kayi sani cewa wannan hawaye nawa
dake zuba ba wai na bakin cikin rabuwa da kai
bane kadai? A'a ina bakin ciki ne saboda
tausayinka gami da rashin samun babban rabo,
kaga kenan kayi biyu babu duniya bata samu ba
kuma daya can gidan ma bai samu ba. Koda jin
wannan batu sai Sarki Dujalu ya dubi Gimbiya
Hursiyya yayi mata murmushin karfin hali yace
hakika yanzu naga gaskiya kuru-kuru da idona
amman a lokacin da bazan iya karbarta ba, ina
tayaki murna da kika dace har kika karbi
wannan gaskiyar, kuma nima ina murna zan
mutu akan abinda na gada iyaye da kakanni,
albarkacin iyayenmu bazan mutu yanzu ba har
sai na kammala maki hikayar sadauki Hulkas na
birnin Romaniya domin itama hikaya ce mai
dauke da dunbin darasi wadda zata amfaneki a
rayuwarki ana gaba. Koda ya zo nan a zancensa
sai ya sake yin tari gami da aman jini har
numfashinsa ya dauke dif. Hursiyya ta fada
saman girjinsa tana mai fashewa da
357
TASKARNOVELS.COM.NG
matsanancin kuka. Ba zato kuma ba tsammani
sai kawai ta ji sarki Dujalu ya kawo gauron
numfashi yana mai bude idanunsa da kyar, nan
take ya budi baki da nufin ya cigaba da basu
labari, kawai sai sukaga wata guguwa mai
tsananin karfin gaske ta zo ta sure wadannan
kayan yaki na mazan jiya tayi sama da su, a take
kum guguwar ta rikide ta zama aljani Raugatul
Agwanu yana mai kyalkkyala mahaukaciyar
dariyar mugunta gami da farin ciki, yana mai
cewa "Shikenan na tsinci dami a kala,
gabadayanku kun sha wahalar banza ni kuma
na zo naci gajiyar wahalar taku, na samu
tsuntsu daga sama gasasse. Nan take aljani
Raugatul Agwanu ya luluka izuwa can kololuwar
sama yana mai cigaba da cewa shikenan duniya
ta zama tawa dukkan mutane da aljanu sun
dawo karkashina, kafin kiftawar ido ya bace bat
a sararin samaniyar, har ma dariyar tasa daga
baya ta gushe aka daina jinta. A dai-dai wannan
lokacin ne boka Sadusa, Halyal da Gimbiya
shalbirat ma suka fito daga inda suke boye tare
da rugowa inda su Sarki Dujalu suke, nan take
suka gabatar da kansu kuma suka bayar da
labarin abinda duk ya faru a tsakaninsu da
358
TASKARNOVELS.COM.NG
aljani Raugatul Agwanu. Boka Sadusa ne yayi
wannan bayani kuma bai boye wa Sarki Dujalu
komai ba dangane da dukkanin shirinsu shida
fadawansa na yi masa juyin mulki wanda har
takai cewa an turo shi wannan tsibiri na Bahar
sufiya domin ganin halin da ake ciki akan yakin
da sarki Dujalu ke yi. Lokacin da boka Sadusa
ya zo nan a cikin jawabinsa sai Sarki Dujalu ya
kyalkkyale da dariyar mugunta cikin karfin hali,
sannan ya dubi jarumi Hasnalu yace da shi ya
kai wannan saurayi ma'abocin kyau da
jarumtaka kuma jagoran kawo haske mai kore
duhu a wannan nahiya tamu ina mai rokonka da
ka roki Ubangijinka daya lalata sihirin wadancan
kayan yaki na mazan jiya wanda aljani Raugatul
Agwanu ya dauka, ya zamana cewa babu wani
mahaluki da zai kara amfanarsu, bawai dan na
kasa mallakarsu bane nake so a lalatasu ba, sai
domin na gane cewa duk abinda muka yi imani
da su dangane da makaman tsafine kawai,
kuma tsafi karya ne addinin musulunci shine
kadai tafarki na gaskiya. Dalili na biyu da nake
son a lalata sihirin wadannan makamai shine na
gane cewa zalunci bashi da wani amfani a
doron kasa, tunda gashi na gani da idanuna,
359
TASKARNOVELS.COM.NG
karshen ko wanne azzalumi baya kyau, sannan
yakanyi mutuwar wulakanci, kaskanci gami da
gagarumar asara. Daga can sai sarki Dujalu ya
kamo hannun yar uwarsa gimbiya Hursiyya ya
damke a lokacin da hawaye ya zubo masa ya ce
ya ke yar uwata kiyi sani cewa ko a cikin tarihin
rayuwata akwai babban darasi wanda ke nuni
da cewa hadama da dogon buri basa kai mutum
ko ina face asara gami da nadama, ki duba ki
gani ina da mulki irin wanda babu wani sarki
mai irinsa a wannan nahiya, haka kuma ina da
dukiya wacce babu wani attajiri ko mai mulkin
daya tara kamarta, hatta Sarki Maharaz kuwa.
Amman duk wannan ni'ima dana samu ban
godeWa Allah ba, gashi garin kwadayi da dogon
buri na rasa komai nawa, a karshe kuma gashi
rayuwar tawa ma zan rasata gaba daya, wannan
shine babban darasi a cikin labarina. Sarki
Dujalu ya dubi boka Sadusa ya ce kaima sai
wannan jawabi da nayi ya zama darasi a gareka,
domin na tabbatar da cewa a cikin zuciyarka
har yanzu kana da burin son mallakar
wadancan kayan yakin na mazan jiya wadanda
aljani Raugatul Agwanu ya sace ya gudu da su,
abubuwan da suka faru yanzu ya isheka ishara
360
TASKARNOVELS.COM.NG
tunda da idanunka kaga yadda tsafi ya kasa
dauko kayan yaki, sai Ubangijin musulunci ne
ya bada iko aka dauko su. Lokacin da sarki
Dujalu ya zo nan a zancensa sai Sarki Maharaz
ya tsugunna daf da shi tare da kama
hannayensa ya rike ya ce ya kai abokin gaba
kayi sani cewa a halin yanzu na cire dukkan
wata gaba dake cikin zuciyata dangane da kai,
kuma na yafe maka dukkan wani bakin ciki da
ka cusa mani, kaunarka ta shiga cikin zuciyata
tamkar bata taba kinka ba, ina yi maka
kwadayin samun wannan babban rabo wanda
na samu yanzu na karbar addinin gaskiya, kaga
shikenan ka samu dadi da daula anan gidan
duniya, acan daya duniyar ma sai ka samu.
Koda sarki Maharaz ya zo nan a zancensa sai
sarki Dujalu ya dubeshi cikin murmushin karfin
hali, sannan ya daga hannunsa ya dora a saman
kafadarsa da kyar ya ce hakika nima a halin
yanzu naji ina kaunarka tamkar dan uwana na
jini, kuma na yafe maka dukkan wani laifi da
kayi mani, amman k sani cewa bakin alkalami
ya riga ya bushe, kuma zuciyata ta bushe ga
barin sauya manufarta. Hakika bazan iya karbar
addinin Musulunci ba, saboda zan kasance a
361
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin tsananin kunya a ranar da aka tashemu ni
da iyayena da kuma kakanninmu, suna kallona
ina kallonsu za a yi masu azaba ni kuma a
sannan a sakani a cikin Rahama. Koda jarumi
Hasnalu ya ji wannan batu daga bakin sarki
Dujalu sai ya cika da tsananin mamaki ya ce ya
kai wannan sarki yanzu ashe daman kasan
cewa akwai wata rayuwa bayan wannan? Kuma
ka sani cewa wadanda suka bijirewa Allah za a
yi masu azaba, yayin da wadanda suka bishi za
a yi masu sakayya da aljanna mafificiya? Sarki
Dujalu ya kada kai yayin da hawaye ya sake
zubo masa ya ce tabbas nasan duk wannan
al'amari, tun ban fi shekara bakwai a duniya,
kuma mahaifina ne ya sanar da ni, shima
mahaifinsa ne ya sanar da shi, amman da yake
duk an cusa mana kiyayyar addinin Musulunci
tun muna yara, sannan baiyi tasiri a cikin
zukatanmu ba. Ya kai wannan jarumi kayi sani
cewa na taba ji daga bakin mahaifina cewa
kimanin shekaru ashirin baya da suka gabata
akwai wani ma'abocin addinin Musulunci da
yazo nahiyarmu yayi gwagwarmaya da
iyayenmu sai dai mahaifina ya samu nasarar
kasheshi, yanzu haka suturarsa gami da kayan
362
TASKARNOVELS.COM.NG
yakinsa suna nan acikin dakin tarihi dake cikin
gidan sarauta ta, kuma akwai bayanin inda aka
binne gawarsa a cikin wani littafi dake cikin
wani akwati da aka ajiye tufafinsa. Ga yadda
aka yi bayanin wannan mutum kuwa da siffofin
jikinka, a yanzu da kake tsaye a gabana kai da
shi tamkar an tsaga kara ne, babu mamaki ma
kana da nasaba da shi. Koda sarki Dujalu ya zo
nan a zancensa sai hawayen farin ciki ya
zubowa jarumi Hasnalu ya ce hakika ka gajarce
mani wahala, ka sanar da ni abinda nazo nema
wannan nahiya taku, kuma gashi na jefi tsuntsu
biyu da hoge daya, tunda gashi na samu abinda
na zo nema kuma na samu nasarar korar duhun
da kuke ciki na kawo maku haske. Da jin haka
sai Sarki Dujalu yayi murmushi cikin karfin hali a
lokacin da tari ya sake turnukeshi ya zubar da
yawun jini, Hursiyya ta sake kankameshi tana
mai sake fashewa da kuka, da kyar sarki Dujalu
ya sake bude baki ya dubi jarumi Hasnalu ya ce
ya kai gwarzon jarumi ina mai rokonka daka
gaggauta rokon ubangijinka akan ya lalata
tasirin wadannan makamai na mazan jiya
tungabanin aljani Raugatul Agwanu ya fara
amfani da su. Abu na karshe da nake son na
363
TASKARNOVELS.COM.NG
rokeka shine tunda yar uwata Hursiyya ta karbi
addininka kuma kuna son juna kai da ita, to ka
aureta kuma ka dauketa ka tafi da ita can
nahiyarku domin ina son ta manta da ni, kuma
ta manta da kasarta ta haihuwa har abada.
Koda jin haka sai Hursiyya ta sake fashewa da
matsanancin kuka tana mai cewa ya kai dan
uwana kayi sani har abada fan uwa ba zai tana
mancewa da danuwansa ba, har na mutu da
begenka zan kasance gami da zubar da hawaye
dan takaicin rashin karbar addinin gaskiya.
Koda jin wannan batu sai kowa dake wajen ya
kama zubar da kwalla, a sannan ne boka
Sadusa ya durkusa bisa gwiyawunsa gaban
jarumi Hasnalu idanunsa cike da kwalla ya ce
tabbas addininka shime addinin gaskiya, maza
ka shigar da ni wannan addini mai girma da
daraja. Nan take kuwa jarumi Hasnalu ya budi
baki dan ya biya masa kalmar shahada sai yaro
Halyal da gimbiya shalbirat ma suka zo suka
durkusa a gaban jarumi Hasnalu cikin hadin
baki suka ce muma munyi imani da addinin
Musulunci. Cikin matukar farin ciki arumi
Hasnalu ya biya masu kalmar shahada, suka
maimaita. Sarki Maharaz da jarumi Imnal da ke
364
TASKARNOVELS.COM.NG
tsaye gefe daya da gimbiya Mulaifa gami da
Hursiyya duk sai suma suka mu da matukar
farin ciki. Bayan su boka Sadusa sun karbi
addinin Musulunci ne, sai jikin sarki Dujalu ya
kara tsanani, take numfashinsa ya fara sarkewa
kuma idanunsa suk kama rufewa da budewa,
da kyar ya samu ya sake bude bakinsa ya dubi
jarumi Hasnalu ya ce ya kai wannan sadaukin
sadaukai kuma sirikina, kalmata ta karshe a
garek ita ce ina mai rokonka da ka mayar da
gimbiya shalbirat kasarsu domin ta sadu da
mahaifiyarta, kuma ka mayar d su sarki
Maharaz zuwa birninsu tunda dai yanzu babu
sauran aljani anan wanda xai iya mayar da su
can garuruwan nasu har ya karesu daga sharrin
mugayen abubuwan dake kn hanya. Koda jin
wannan batu sai jarumi Hasnalu ya numfasa ya
ce kada ka damu ya kai wannan sarki, da izinin
ubangijina kowannenmu anan zai isa gida
lafiya, kuma daga nan babu inda zamu fara
zuwa ba face dajin darul hishushul maut inda
aljani Raugatul Agwanu yake domin naje na
yakeshi na nuna masa cewa kayan yakin da ya
makllaka na maxan jiya shirme ne tunda na
dogara da ubangijin da yayi wadanda suka
365
TASKARNOVELS.COM.NG
kirkiri kayan yakin mazan jiya. Da izinin
Ubangijina zamu isa dajin darul hushushul
maut acikin kankanin lokaci. Ya kai wannan
sarki ina mai sake rokonka a karo na karshe
daka janye wannan mugun ra'ayi akan
addininka na gado ka karbi addinin gaskiya
kodan saboda yar uwarka ta kasance a cikin
farin ciki na kamutu cikin babban rabo. Koda jin
haka sai sarki Dujalu yayi dariyar karfin hali
sannan ya ce kayi hakuri samari a rayuwata ban
taba yin magana biyu ba, kuma ban taba sa abu
a gabana ba ya gagareni ko kuma naja da baya
sai a wannan karon da na kasa dauko makaman
mazan jiya a karkashin wannan teku bayan nayi
iyakar abinda zanyi amman na kasa, lallai ba
zan juya wa iyayena da kakannin baya ba,
burina shine na sadu da su a cikin irin halin da
zasu kasance. Gama fadar hakan keda wuya
sai sarki Dujalu ya kama kakarin mutuwa, nan
fa Hursiyya ta dada kankameshi a kirjinta tana
mai kara fashewa da kuka. Su kuwa su jarumi
Hasnalu sai tausayin wannan yan uwa ya
turnukesu suka kama zubar da hawaye, haka
dai sarki Dujalu ya cigaba da kakarin mutuwa
gami da shure-shure harda iface-iface har
366
TASKARNOVELS.COM.NG
izuwa wani lokaci kafin daga karshhe aka zare
masa ruhin numfashi, nan fa jikinsa ya sandare
idanunsa suka kafe. Kaico! Kaji muguwar
mutuwa irin ta marasa rabo, hakika wanda
Allah Ya batar bazai taba zama mai shiriya ba,
gashi dai babu yadda su Hursiyya basu yi da
sarki Dujalu ba akan yya karbi addinin gaskiya
domin ya rabauta, amman da yake tuni Allah Ya
hukunta bashi da rabo sai ya kasa karbar
gaskiyar. Bayan sarki Dujalu ya mutu akan
cinyar Hursiyya sai ta dada kankameshi a
kirjinta tana mai dada fashewa da matsanancin
kuka fiye da koyaushe, da kyar da shidin goshi
gimbiya Mulaifa ta bambareta daga jikin gawar
sannan ka tona rami aka gefen tekun bahar
sufiya aka binne sarki Dujalu a ciki. Jarumi
Hasnalu da jarumi Imnal suka je suka kinkimo
wani katon dutse suka ajiyeshi a gaban kabarin
sarki Dujalu, nan take suka zare takubbansu
suka rinka kartar dutsen har sai da suka rubuta
sunan sarki Dujalu a jikin dutsen sannan kuma
suka dinga dora duwatsun wuta a bisa kabarin
har saida suka rufeshi ruf domin kada kabarin
ya baje, komai daran dadewa ya zama abin
tarihi. Aikuwa har yau har gobe idan mutum ya
367
TASKARNOVELS.COM.NG
je bakin kogin bahar sufiya zai ga wannan kabari
na namijin duniya sadaukin sadaukai sarki
Dujalu gami dana marigayi Sarkin yaki Hibru
mahaifin jarumi Imnal, kuma tsakanin
kaburburan bai wuce taku biyu ba. Bayan su
jarumi Hasnalu sun gama gina kabarin sarki
Dujalu sai Imnal da sarki Maharaz suka je suka
durkusa a gaban kabarin Hibru suka kura wa
kabarin idanu sun masu zubar da hawaye, daga
can kuma sai Imnal ya fashe da kuka. Jarumi
Hasnalu ya dafa kafadar Imnal cikin alamar
matukar tausayawa ya ce ya kai abokina ina
dalilin wannan matsanancin kuka naka? Kayi
sani cewa dukkan mai rai mamacine, su da
suka tafi basu yi gaggawa ba, haka mu da muke
nan bamu yi jinkiri ba. Imnal ya juyo ya dubi
jarumi Hasnalu idanunsa sharkaf da hawaye ya
ce ya kai abokina ba wani bane yasa ni zubar da
hawaye ba face tunowa da cewa mahaifina ya
mutu bai karbi addinin Musulunci ba alhalin
kuma a bakinsa na fara jin labarin wannan
addini, kuma a yadda yake yi mani bayani har a
zuciyarsa yayi imani da addinin kuma yana
takaicin akan rashin samun damar karbar
addinin, domin shi bai samu damar hakan ba.
368
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da jarumi Hasnalu yaji wannan batu,
sai yayi murmushi mai taushi ga jarumi Imnal ya
ce ya kai abokina kayi sani cewa Ubangijina mai
hikima ne akan komai, kuma mai Rahama ne ga
bayinsa a duk sa'ad da ya so, tunda har
mahaifinka ya kadaita Allah a cikin zuciyarsa
duk da cewa bai sanshi ba kuma bai samu
damar da zai sanshi ba, to Allah subhanahu
wata'ala zai iya masa Rahama ya sa shi a gidan
aljanna. Koda jin wannan batu sai mamaki da
farin ciki ya lullube su Imnal, sarki Maharaz yayi
ajiyar numfashi ya ce hakika Ubangijin
musulunci shine mafi rahama da jin kai akan
bayinsa, lallai muna roko akan yasa mu
kasance cikin bayinsa masu rabo da dacewa,
gaba dayansu suka amsa da Amin. Nan take
Jarumi Imnal ya tashi ya rungume Hasnalu ya ce
hakika a yau kazo mani da batu mafi dadi dana
taba ji a rayuwata wanda ya jefani acikin farin
cikin da bantaba ji ba a rayuwata. Nan dai suka
dunguma gaba dayansu tare da barin bakin
takun Bahar sufiya suka nausa izuwa cikin daji.
Jarumi Hasnalu nayi masu jagora, Imnal, sarki
Maharaz, da gimbiya Hursiyya suna tafiya suna
kuma waigen kabarin masoyansu suna zubar da
369
TASKARNOVELS.COM.NG
hawaye har ya zamana cewa sun yi nisa da
bakin tekun. A daidai wannan lokacin ne jarumi
Hasnalu ya fara sauri-sauri, gudu-gudu kuma
yana mai karanta wasu Addu'o'i na musamman
a cikin zuciyarsa, daga can sai ya waigo ya dubi
su jarumi Imnal da su gimbiya Hursiyya yace
kuyi koyi dani bisa dukkanin abinda kukaga na
yi. Ai kuwa sun fara yin gudun da yake yi suka ga
abin al'ajabi irin wanda basu taba ganiba a
rayuwarsu, domin gani suke tamkar iska ce ke
daukarsu sama tana tafiya da su, aikuwa nan da
nan suka dinga keta dazuzzuka suna yin
azababben gudu tamkar gudun tauraruwa mai
wutsiya, gashi dai gudu suke amman ko kadan
babu mai alamar gajiyawa a cikinsu, sannan a
kiyasce suna shafe tafiyar sa'a uku cikin dakika
goma kacal. Kai hakika tsananin gudun da suke
yi ya wuce misali kawai Allah ne kadai ya barwa
kansa sanin mizaninsa. Wannan shine abinda
ya faru da su jarumi Imnal acan bakin kogin
bahar sufiya bayan an fafata yakin karshe a
kokarin dauko makaman mazan jiya.
*****************
*****************
Al'amarin aljani Raugatul Agwanu kuwa lokacin
da ya sace wadannan kayan yaki na mazan jiya
370
TASKARNOVELS.COM.NG
guda uku wato; Takobin Saiful Lujara, mashin
galilur haras da kuma hular lamsara sai yayi
sama ya luluka a cikin gajimare, kawai sai ya
rataya wannan takobi ta Saiful Lujara a bayansa
ya sanya hular a kansa kuma ya rike mashin a
hannunsa na hagu, nan take yaji wani irin
gagarumin karfi ya shige shi mara misaltuwa
tamkar zai iya dakon duniyar gabadaya, kai
hatta karfin gudunsa a sararin samaniya sai da
ya ninka na da sau dubu. Cikin