x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - MAZAN JIYA 4

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 68055 words

Category: Adventure Stories

Views 188

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
yi sama suka ci gaba da
306

TASKARNOVELS.COM.NG
kewaya wannan korama suna neman Jarumi
Shaddadu tare da Mashin Galilul Haras amma
sai da suka duba ko ina ba su gansu ba. A
sannan ne Maruful Dauwaz ya sauko kasa bisa
turba, Ziya'ul Hak ta sauko daga kansa ta dube
shi cikin tsananin damuwa ta ce, yanzu ta yaya
za mu iya komawa gidan Sarautar Sarauniya
Zubaina alhalin sihirin tsafinmu ya daina aiki, ba
za mu iya rikiɗewa ba izuwa siffar Mafarauci da
Karensa? Maruful Dauwaz ya jinjina kai ya ce,
"Tabbas zancenki dutse ne, to amma ba mu da
wani zabi face ki je ki gaya wa Zubaina cewa, kin
fito ne farautar wani abokin gabarki mai suna
JARUMI SHADDADU kuma ki siffanta
kamanninsa. Tun da masu gadin kofar sun gan
shi kuma tabbas sun sanar da Zubaina
kamanninsa. Tana jin bayaninki za ta aminta da
ke kuma za ta ba ki hadin kai. Ki sani cewa ita
ma Sarauniya Zubaina gawurtacciyar matsafiya
ce idan na bi ki muka je tare za ta farke mana
laya tunda mu yanzu namu sihirin tsafin ba ya
tasiri, zan ci gaba da zama a nan dajin har zuwa
sa'adda za ku sake fitowa farautar Jarumi
Shaddadu. Fatana kawai shi ne a ce Shaddad
ba ya tare Mashinsa na galilul Haras, in dai ba
307

TASKARNOVELS.COM.NG
ya tare da shi tabbas wannan karon za ki sami
nasarar hallaka shi." Koda jin wannan batu sai
Jaruma Ziya'ul Hak ta kamu da tsananin farin
ciki. Nan take ta yi wa Aljani Maruful Dauwaz
sallama ta tafi i zuwa cikin gari *** Sarauniya
Zubaina na zaune a fadarta ana tafiyar da
harkokin fadar sai ga wadannan Dakaru da suka
tafi farautar Jarumi Shaddadu tare da mafarauci
sun shigo da gudu. Da zuwansu gaban karagar
Zubaina sai suka zube kasa suna haki, aka rasa
wanda zai ce kala. Cikin fushi Zubaina ta daka
musu tsawa ta ce, ina wannan Mafaraucin
yake? Ku ba ni labarin abin da ya faru, shin an
kamo wannan tsageran Jarumin? Koda jin
wannan tambaya sai daya daga cikin Dakarun
ya dubi Sarauniya sannan ya sake risinawa a
gabanta ya ba ta labarin duk abin da ya faru
iyakar abinda suka gani da idanunsu. Koda jin
wannan labari sai hankalin Sarauniya haina ya
dugunzuma ainun ta mike tsaye tana ma kai
kawo cikin tsananin damuwa. Alamarin da yai
matukar bai wa fadawanta mamaki kenan.
Wazirinta ya dube ta ya ce, ya shugabata, wai
shin mene ne dalilin da ya sa kika yi matukar
damuwa ne akan lallai sai kin kama wannan
308

TASKARNOVELS.COM.NG
bakon Jarumi? Ni ina ganin cewa tunda dai an yi
iya kokari akan a kama shi abu ya gagara ya
kamata a hakura haka domin idan aka ci gaba
da matsawa za a iya asarar rayukan Dakarunmu
da dukiyarmu. Koda jin haka sai Zubaina ta
dubi Waziri a fusace ta ce, akwai abin da nake
son na karba a hannunsa wanda ya fi rayukan
Dakarunmu da dukkan dukiyarmu daraja da
amfani. Tuni na yi bincike a cikin hallarar tsafina
na gano cewa wannan bakon Jarumi yana tare
da wani Mashi wanda ake yiwa lakabi da
MASHIN GALILUL HARAS. Duk wanda yake tare
da wannan Mashi zai iya yakar duniya
gabadayanta domin komai yawan mayaka zai
iya hallaka su shi kadai. Koda jin wannan batu
sai gaba dayan mutanen da ke fadar suka cika
da tsananin al'ajabi. Waziri ya ce, yanzu ta yaya
za mu iya zuwa mu kamo wannan bakon Jarumi
alhalin ba mu san inda yake ba, kuma idan har
yana tare da Mashin ai ba za mu iya kama shi
ba. Koda jin wannan batu sai jikin Sarauniya
Zubaina ya yi sanyi ta rasa abin da za ta ce.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka ji an
ce, nii zan iya taimakawa a ga inda wannan
bakon Jarumi yake har a kamo shi! Cikin
309

TASKARNOVELS.COM.NG
kaďuwa kowa ya waiga baya aka dubi bakin
kofar shigowa fadar, sai aka yi arba da Jaruma
Ziya'ul Hak a tsaye. Cikin mamaki Sarauniya
Zubaina ta dubi Ziya'ul Hak ta ce, ke kuwa wace
ce kuma daga ina kika fito? Da jin wannan
tambaya sai Ziya'ul Hak ta risina ta kwashi
gaisuwa sannan ta dago kai ta ce, ni sunana
BADI'ATUL LAUMARA. kuma na fito ne daga can
Nahiyar kasashen da ke gabashin taku. Na baro
gida ne saboda farautar babban abokin gabata
JARUMI SHADDADU wanda a halin yanzu yana
nan a cikin Birnın nan naki ya buya bisa
taimakon daya daga cikin mutanen garın nan.
Ina son mu hada KARFI DA KARFE ni da ke
domin mu sami nasarar kama wannan
azzalumin Jarumi mu yi masa kisan gilla saboda
ina da labarin irin barnar da ya yi a cikin wannan
Birni naki sannan ya karya miki doka. Sa'adda
Ziya'ul Hak ta zo nan a zancenta sai Sarauniya
Zubaina ta bushe da dariya. Al'amarin da la bai
wa kowa mamaki ke nan a fadar har da ita kanta
Ziya'ul Hak. Sarauniya Zubaina ta ce, haba ya ke
Ziya'ul Hak 'ya ga Sarki Laffaru na Birnin Kufa a
da, saboda me za ki boye mini kanki alhalin na
san ko wace ce ke kuma na san abin da ya baro
310

TASKARNOVELS.COM.NG
ki daga gida? Ni da ke zani ce ta tarar da mu je
mu. Na sani cewa ke ba ki da wani buri wanda
ya fi ki kashe Jarumi Shaddadu sannan ki je ki
kamo mahaifiyarsa a raye ki kai ta wajen
mahaifinki ku yi mata kisan wulakanci. Ni
kuma ba ni da burin da ya fi na mallaki Mashın
Galilul Haras da ke hannun Shaddadu, sabo da
haka na amince mu hada KARFI DA KARFE
domin kowannenmu ya cika burinsa. Idan kin
amince yanzu sai ki bi ni izuwa cikin Turakata
domin mu zauna mu tattauna ke ma ki ci abinci
ki huta. Yayin da Sarauniya Zubaina ta zo nan a
zancenta sai Ziya'ul Hak ta yi murmushi ta ce,
na amince. Nan take Sarauniya Zubaina ta ja
Ziya'ul Hak i zuwa cikın gidan Sarautar suka
wuce har i zuwa cikin Turakarta suka Zauna.
Zamansu ke da wuya Kuyangi suka kawo abinci
da abin sha na alfarma suka kama ci da sha
suna hira cikin nishadi da annashuwa tamkar
sun kasance 'yan uwa ko kuma aminan juna
Bayan sun ci sun sha sai aka kawo musu giya.
Koda Zubaina ta zuba giyar a cikin kofuna guda
biyu ta mika wa Ziya'ul Hak domin ta sha, sai ta
ki karba. Ta dubeta ta ce, ya ke wannan
Sarauniya ki yi sani cewa ni a daji aka haife ni
311

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma a cikinsa na girma don haka ban saba da
shan giya ba, amma kuma babu abin da iyayena
ba su koya mini ba dangane da irin rayuwar da
ake a cikin Birni. Koda jin wannan batu sai
Sarauniya Zubaina ta bushe da dariya sannan ta
ce, na yarda da wannan labari naki amma na
tausaya miki kuma na tausayawa iyayenki da
suka yi rayuwar dole a daji sabo da tsoron
sharrin mahaifiyar Shaddadu. Lallai idan har
kina son iyayenki su sami zaman lafiya da
kwanciyar hankali dole ne ki yi iya kokarinki ki
tabbatar da cewa kin samu nasarar kashe
Jarumi Shaddadu. Wai shin ma ke ba kya so ne
ki ga mahaifnkı Sarki Laffaru ya koma birninsa
na Kufa ya karbi karagarsa ta mulki? Hakika a
duniya babu mutumin da ya fi zama abin
tausayi sama da wanda ya rasa dukiya ko mulki
domin ya dandana dadi mara misaltuwa kuma
dadin ya zo ya salwanta. A cikin wanne irin
yanayi kike tsammanın zai tsıncı kansa?
Zıya'ul Hak ta dubi Sarauniya Zubaina ta ce, ina
mai tabbatar miki da cewa ta kowanne hali sai
na ga na tabbatar da na sami nasara akan
Shaddadu da mahaifiyarsa. Yanzu ke ta yaya
kike ganin cewa za mu iya kamo Shaddadu mu
312

TASKARNOVELS.COM.NG
hallaka shi? Koda jin wannan tambaya sai
Sarauniya Zubaina ta yi murmushi sannan ta ce
binciken da na yi a cikin hallarar tsafina na gano
cewa, ba wani ba ne ya taimaki Jarumi
Shaddadu cikin wannan gari nawa ya boye shi a
sa'adda nake matukar nemansa face wata
baiwata kum karuwa mai zaman kanta wacce
ake kira Yaldisa. Akwai wani gidan sai da abinci
nawa wanda Yaldisa ce ke kula da shi, a nan ne
ta fara haduwa da Jarumi Shaddadu. Tun a
wannan gida ne na shirya masa tuggun da za a
kashe shi a dauko mini Mashinsa na Galilul
Haras a kawo mini amma sai ya tsallake
wannan tarko nawa bisa karfin dantsensa da
kuma taimakon Yaldisa inda ta dauke shi ta kai
shi can gidanta ta boye shi a cikin wani ďakı da
ke karkashin kasa. Ni da kaina tare da
Dakaruna mun shiga har cikin gidan Yaldisa
mun duba ko ina ba mu ga Jarumi Shaddadu.
Duk ban gano wannan al'amari ba sai a yau da
na tsananta bincike a cikin madubin tsafina.
Tabbas ko shakka ba na yi a yanzu haka ma duk
inda Jarumi Shaddadu yake yana tare da
Yaldisa. Abin da ya daure mini kai shi ne, na yi
iya bincikena na kasa gano a inda suke a yanzu.
313

TASKARNOVELS.COM.NG
To amma ai idan sun san wata ai ba su san wata
ba. Tun da Jarumi Shaddadu ya yi mana wuyar
gani da kamawa, ai ita Yaldisa ba za ta yi mana
wuya ba. kamata ya yi mu kamo Yaldisa mu zo
mu tsare ta anan fada kuma mu sa a yi cigiyar
cewa idan Jarumi Shaddadu bai kawo kansa
fada a cikin sa'a goma sha hudu ba za a kashe
ta ta hanyar ratayewa. Na tabbalar da cewa ba
zai iya zuba idanu yana gani a kashe ta ba
saboda halaccin da ta yi masa a zuwansa
wannan gari nawa. Lallai zai iya kokarinsa ya
ga ya ceci rayuwarta duk da cewa ba sonta yake
ba, asali ma shi bai san mene ne so ba kuma
bai taba son wata 'ya mace ba ko ya yi
sha'awarta Kin ga, da zarar Jarumi Shaddadu
ya zo fada in yana tare da Mashin Galilul Haras
za mu sa shi ya miko shi gare mu ko mu kashe
Yaldisa. Idan kuma ba ya tare da Mashin sai
mu hada karfinmu ni da ke mu yake shi, tabbas
in muka hada jarumtakarmu ni da ke sai mun
rinjayi tasa mun hallaka shi. Lokacin da Ziya'ul
Hak ta ji wannan jawabi na Sarauniya Yaldisa
sai ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce, to ke mene
ne ribarki idan muka kashe Shaddadu ba ki
sami Mashin Galilul Haras ba? Koda jin
314

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan tambaya sai Sarauniya Zubaina ta
kama in-ina ta rasa me za ta ce, amma sai ta
wayance ta ce, ai kashe Shaddadu abu ne mai
muhimmanci a gare ni ko don saboda kwararan
dalilai guda biyu. Dalili na farko shi ne,
Shaddadu ya shigo birnina ya karya mini doka,
kuma ya nakasta mini dakaruna da yawa ya
karva mini kofar gari. Dalili na biyu kuma shi
ne, koda ba ya tare da Mashin Galilul Haras ai
Mashin yana nan a cikin Birnin nan nawa tunda
a bincikena na gani cewa Mashin ya fada cikin
wannan korama wacce kuka fada cikinta ke da
shi tun farkon fara fadanku sa'adda Mashin
Galilul Haras ya hadu da Takobinki. Ina mai
tabbatar miki da cewa ke ma yanzu gabadayan
sihirin tsafinki ya daina tasiri kamar yadda na
Jarumi Shaddadu ya daina, amma fa ki sani
cewa da zarar Mashin Galilul Haras ya dawo
hannunsa shi ke nan tsafinsa ya dawo. Don
haka, dole ne mu yi iya kokarinmu mu tabbatar
da cewa Mashin bai dawo hannunsa ba, ya
zamana cewa hannunmu ya riga nasa kaiwa kan
Mashin. Lokacin da Sarauniya Zubaina ta zo
nana zancenta sai hankalin Ziya'ul Hak ya
dugunzuma ainun ta fara tunanin cewa hada
315

TASKARNOVELS.COM.NG
kan da take kokarin yi da Sarauniya Zubaina ba
shi da wani amfani domin idan Zubaina ta
mallaki Mashin Galilul Haras tamkar ta mallaki
komai da kowa ne na duniya, don haka
mahaifinta ma da kasarsu ta Birnin Kufa za ta
dawo karkashin Sarauniya Zubaina. Nan take
wani tunani ya fadowa Ziya'ul Hak ta ce a cikin
ranta, Wai shin mene ne ya hana mahaifiyar
Shaddadu kokarin mulkar duniya a lokacin da ta
mallaki Mashin Galilul Haras?Maimakon haka,
sai ta sallama Mashin ga Shaddadu saboda
kawai ya zo ya neme ni ya halaka ni kuma ya
hallaka mahaifina? Tana cikin wannan tunani
ne Sarauniya Zubaina ta katse mata tunanin ta
dafa kafadarta ta ce, yanzu zan sa a kai ki
masauki domin ki kwanta ki huta sai gobe za mu
fita ni da ke mu aiwatar da wannan gagarumin
aiki don cika burinmu. Koda gama fadin hakan
sai Zubaina ta kirawo wata kuyangarta ta hada
ta da Ziya'ul Hak aka tafi da ita izuwa
masaukinta. Kas! Babban kuskuren da Ziya'ul
Hak ta yi shi ne, da ta manta da batun abokin
tafiyarta Aljanı Maruful Dauwaz. Kamata ya yi ta
koma can daji in da suka rabu ta sanar da shi
abın da ya faru tsakaninta da Sarauniya Zubaina
316

TASKARNOVELS.COM.NG
amma sai ta manta da hakan gaba daya. ****
Al'amarin Yaldisa kuwa ashe lokacin da Ziya'ul
Hak ta shigo fadar Sarauniya Zubaina ita ma
tana nan a cikin fadar amma ta batar da
kamanninta babu wanda ya isa ya shaida ta.
Bayan ta gama gani da sauraren duk abın da ya
faru tsakanin Ziya'ul Hak da Sarauniya Zubaina
sai ta sulale ta bar fadar, ta kunna kai izuwa
cikin daji. Idan ta yi 'yar doguwar tafiya sai ta
sami bayan dutse ko bayan bishiya ta labe har
izuwa tsawon lokaci domin ta tabbatar da cewa
babu wani dan leken asiri da ya biyo sawunta.
A haka dai ta samu ta isa har cikin wannan Kogo
wanda ta bar Jarumi Shaddadu a kwance yana
jinyar raunin da ke kansa. Da shigarta cikin
Kogon sai ta ga wayam! Babu Shaddadu babu
alamarsa a cikin Kogon. Al'amarin da yai
matukar dugunzuma hankalinta ke nan ta firgita
kuma ta dimauce. A razane ta juya ta fito daga
cikin Kogon dutsen ta wangame baki da nufin ta
kwalla masa kira, kawai sai ta gan shi tsulum!
Ya duro a gabanta daga kan wata bishiya.
Cikin tsananin farin ciki ta rungume shi, shi
kuwa sai ya kankameta a jikinsa yana mamakin
kansa domin wannan ne karo na farko da ya ji ya
317

TASKARNOVELS.COM.NG
aminta ya hada jikinsa da na 'ya mace.
Alamarin da yai matukar dugunzuma
hankalinsa ke nan ya janye jikinsa daga cikin
nata ya sunkui da kansa kas yana tunani. Ita
kanta Yaldisa ta yi tsananin mamakın yadda ta
ga har ya tsaya ta rungume shi alhalin ya tsani
ya ga mace ta kusance shi Cikin sanyın jıkı
Yaldisa ta dubi Shaddadu ta ce, Mene ne dalilın
da ya sa ka fito daga cikin Kogon dutsen nan da
na boye ka alhalin ka san cewa rayuwarka a
cikin mummunan hadari take tunda makiya
suna farautarka kamar yadda mai yunwa yake
farautar abinci? Koda jin wannan tambaya sai
Jarumi Shaddadu ya yi ajiyar zuciya cikin
alamun karayar zuciya sannan ya ce, ai dole ne
na fito daga cikin wannan Kogo saboda
hankalina ya yi mummunan tashi bisa rashin
ganin Mashina. Ki sani cewa babu inda ban
duba ba a cikin koramar nan amma ban ga
Mashin ba. A lokacin da nake neman Mashin
ne ma na ga wannan mugun Aljani abokin
tafiyar Ziya'ul Hak na buya. Shi ma babu irin
neman da bai yi ba a cikin wannan korama don
ya dauko Mashina. Tabbas inda ya gan ni da tuni
ya hallaka ni tunda ni yanzu ba ni da sauran
318

TASKARNOVELS.COM.NG
karfin sihirin da zan iya yakarsa. Ki yi sani cewa
ni yanzu ina cikin tsaka mai wuya tunda ga shi
makiyana suna farautar rayuwata ni kuma ina
farautar Mashina. Kin ga ke nan, hankalina ya
rabu gida biyu, dole ne na yi iya kokarina na zabi
abin da ya kamata na fara durfafa tsakanin
makiyana ko kuma neman Mashina. Sa'adda
Yaldisa taji wannan batu sai ita ma hankalinta
ya dugunzuma ainun ta rasa abin da ke ma ta
dadi. Nan take ta dubi Shaddadu cikin yanayin
matukar damuwa ta ce, ya kai ma'abocin kyawu
da kwarjini, ka yi sani cewa muddin ina
numfashi a doron kasa babu abin da zan bari ya
taba lafiyarka. A halin yanzu Sarauniyarmu da
abokiyar gabarka Ziya'ul Hak sun hada karfi da
karfe domin su yake ka su hallaka ka, kuma ga
dukkan alamu gobe da safe za su fito
farautarka. Ni kaina yanzu rayuwata a cikin
hadari take domin na san cewa tuni Sarauniya
ta yi bincike ta gano cewa ni ce na ke boye ka
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama
Jarumi Shaddadu ya yi shiru yana tunani. Daga
can sai ya dago kai ya dubi Yaldisa ya ce, wai
shin mene ne dalilin da ya sa kika siyar da
rayuwarki domin ceton tawa? Koda jin wannan
319

TASKARNOVELS.COM.NG
tambaya sai Yaldisa ta sunkui da kanta kas ta yi
shiru ta kasa ba shi amsa, daga can kuma sai ta
dago kai ta dube shi a lokacin da idanunta suka
ciko da kwallah ta ce, ya kai Jarumi abin
kwatance ka yi sani cewa ban taba jin na yi
nadamar karuwancin da nake yi ba sai bayan
haduwa ta da kai. Na yi hulda da mazaje da
yawa amma ban taba haduwa da namijin da na
ji ba na son rabuwa da shi ba face kai duk da
cewar wani abu bai taba shiga tsakanina da kai
ba kuma na girme ka da shekaru a kalla kusan
goma.Tun da na hadu da kai na ji na tsani
wannan muguwar sana'a tawa ta karuwanci
kuma na gane sewa bautar da nake yi wa
Sarauniya Zubaina ba ta da wani amfani tunda
ta kasance azzaluma kuma duk dukiyar da na
ke tara mata ba ta taba ba ni ladan dirhami daya
ba Ni nake rike da kaina ta hanuyar siyar da
jikina a wajen maza. Hatta wannan gida nawa
da na kai ka ka kwana haya nake yi a cikinsa.
lyayena sun mutu tun ban fi shekara bakwai ba
a duniya kuma sun kasance bayın Mahaifin
Sarauniya Zubaina. Tsananin wahalar aikin
bauta ne ya zamo sanadın ajalinsu. Bayan sun
mutu ne Sarauniya Zubaina ta ci gaba da rike ni
320

TASKARNOVELS.COM.NG
a matsayin baiwarta, amma saboda sanın ina
da kyau tun a sannan ta ajiye ni a wannan gidan
abinci nata aka koya mini yadda ake dafa abinci
da siyar da shi. Ba zan taba mantawa ba
sa'adda na cika shekara goma sha biyu, lokacın
da dukkan surar jikina ta 'ya mace ta bayyana
wasu Dakarun Sarauniya Zubaina su biyu suka
yi mini fyade a wannan gidan abıncı. Ko kadan
Sarauniya ba ta hukunta wadannan Dakaru ba
da suka yi mini fyaden duk da cewar sai da na
kwana goma sha biyar a kwance ina jinyar
jikina. Bakin cikin nuna halin ko in kula da
Sarauniya ta yi ne bisa abin da ya same ni ya
zamo sanadın fara karuwancina. Har yau har
gobe idan na tuna da wannan alamari sai na ji
babu abin da na tsana a rayuwala sama da
Sarauniya Zubaina domin ita ce ta salwantar da
rayuwata. Lokacin da Yaldisa ta zo nan a
zancenta sai hawaye ya zubo mata sannan ta ci
gaba da magana tana mai cewa, ya kai
ma'abocin kyawu da kwarjini ka yi sani cewa ni
ba na neman soyayyarka a gare ni saboda in na
ce ka so ni ban yi maka adalci ba tunda ni ba
tsararka ba ce a soyayya, kuma ni mace ce
mara asali da mutunci ban dace da dan Sarauta
321

TASKARNOVELS.COM.NG
ba kamarka a yadda ka ba ni tarihin rayuwarka
amma ina da buri guda daya a rayuwata.
Wannan buri nawa kuwa shi ne, na mutu akan
tafarkın sonka kuma na ceci rayuwarka har
izuwa lokacin da za ka sami nasara akan
makiyanka. kuma ka ga Mashinka. Lokacin da
Yaldisa ta zo nan a jawabinta sai Jarumi
Shaddadu ya ji ya kamu da tsananın tausayinta
har hawaye ya zubo masa Tsawon 'yan dakiku
suna kallon junansu an rasa wanda zai ce Kala.
Ita dai Yaldisa sai farın cıkı da mamaki suka
kama ta a lokacin da ta ga hawaye na zuba daga
cikin idanun Shaddadu. Abin da ta fara
tambayar kanta shi ne, wai shin wannan
hawayen na Shaddadu da ya zubo na tausayinta
ne ko kuwa na kamuwa da sonta ne? Nan ta
kasa bai wa kanta amsa, amma sai
End Ads