gaban nasayin
farauta bai mai da sihirin tsaron ba a dajin na
darul Hushushul maut. Tun da boka sadusa
yazo duniya bai taba ganin aljanin mai girma
kirar karfi kutuciyar samartaka da tsananin
muni ba kamar Raugatul Aguwanu don haka a
cikin tsananin firgice yake da shi sbda ya san
cewa ko yaya yayi wani dan kuskure wanda
Raugatul Aguwanu ya gano cewa ya fishi karfin
sihitin take zai halaka Su shi da halyal: Bayan
sun fuskanci juna sai sadusa yace ya kai
wannan sarki jaruan aljanu na duniya ka yi sani
cewa musaman nazo wannan daji na darul
Hushushul maut domin na gana dakai
114
TASKARNOVELS.COM.NG
Tabas na san wani gagarumin al amari wanna
kai baka sani ba
Koda jin wannan batu sai aljani Raugatul
Aguwanu ya gyara zama ya tattara hankalinsa a
waje daya kuma ya nutsu sosai yana mai
sauraron boka sadusa. Sadusa yai gyaran
murya sannan yace shin kana da lbrin
gagarumin yakin da ake fafatawa yanzu hakan a
can bakon kogin Bahar Sufiya? Koda jin wanna
batu sai aljani Raugatul Aguwanu yasake gyara
zama yace kwarai kuwa na san da batun
wannan yaki wanda ake yi tsakan Sarki dujalu
da sarki maharaz, In banda abinka waye yake
shiga fadan manya? Ai dujalu da maharaz sun
fi kowa karin sihirin tsafi a wanna duniya kaf:
Shi ya sa kagani na rabe a waje daya na dawo
nan cikin daji na hakura da rayuwa acikin
mutane da yan uwana aljanu
Koda jin haka sai boka Sadusa ya kyalkyle da
dariya al amarin da yai matukar baiwa aljani
Raugatul Aguwanu mamaki kenan
115
TASKARNOVELS.COM.NG
Awannan lokaci Halyal da kyakkyawar yarinya
ta cikin keji kuwa a ckin matukar tsoro suke
domin gani suke cewar idan tusa ta karewa
bodari hallaka zaiyi
Su kansu sun fahimci cewar sadusa dai yan
dabaru yake yi domin su kubuta: Cikin alamun
dadin mamaki Raugatul Aguwanuyace yakai
wannna hatsabibin bola ina dalilin wannan
dariya taka? Sadusa ya murtuke fuska tamkar
an aiko masa da sakon mutuwa sannan yace ai
nan dajin da ka kadawo tamakar kayi gudun
gara ne ka tarar da zago: to tsaya kaji idan aka
gama wannan yaki duk wanda yasami nasara
tsakanin sarki dujalu da sarki maharaz shine zai
mallaki kayan yakin MAZAN JIYA wannan duk
kuwa ya mallaki Takobin SAIFUL LUJARA
MASHIN GALILUL HARAS da HULAR LAMSARA
sai ya mallaki kowa da komai na cikin wannan
duniya kaga kenan kai kanka sai kazama
bawansa wannan daji naka na darul Hushushul
maut sai ya zama wajen shan iskasa
116
TASKARNOVELS.COM.NG
Kai kuwa nasani cewa a dunia babu abinda ka
tsana sama da kayi bauta a karkashin wani ka fi
son rayuwarka ta kare acikin cin gashin kanka
ko ba haka bane? Koda boka sadusa yazo nan a
zancesa sai hankalin aljani Raugatul Aguwanu
ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe a
rayuwarsa sbda ko kada bai taba tunanin
faruwar wannan al amari ba: nan take halyal da
kyakkyawar ta cije keji suka ji sun sami
nutsuwa da kwanciyar hankali bisa jin wanna
bayani da sadusa ya yiwa aljani Raugatul
Aguwanu musamman da suka gayadda jinkisa
yai sanyi kuma hankalinsa ya tsahi. Tsawon
yan dakiku Raugatul Aguwanu yana nazari
tunani har maya mike tsaye yakama kai kawo
yana ciza ya tsa. daga bisani sai ya koma kan
kujerarsa ya zauna kusa da sadusa ya dubeshi
ya ce yakai wannan takadarin boka kayi sani
cewa hakika kazo mini da babban al amari
wanda yafi gaban tunaniba da hangena don
haka sai nayi bincike na tabbatar da gaskiyarsa
117
TASKARNOVELS.COM.NG
To wai shin idan har abindaka fada min
gaskiyane to yaya zan iya kubuta kena Ni dai
kam da dai na zauna a karkashin wani mulkeni
gwara na kashe kaina domin ban ga anfani
wannan tsananin karfin dantsen nawa gai da
karfin sihirina wanda na shafe sama da shekaru
arba in ina yawon nemansa a cikin duniya
Sadusa ya gyada kai yace tabbas kayi gaskiya:
Amma ina mai tabbatar maka dacewa ni ina da
mafita a gareka amma sai bayan ka gama
bincikenka kaga gaskiyar wannan al amari
sannan zan gaya maka mafitar kuma bisa wani
sharadi
Koda jin haka sai aljani Raugatul Aguwanu ya
kyalkyale da dariya sanna yace hakika yai na
gamu da sarkin wayo: Ti amma fa kasani ramin
karya kurarre ne idan har duk abinda kazo mini
dashi ba gaskiya bane asirinka zai tonu
118
TASKARNOVELS.COM.NG
idan kuwa asirinka ya tonu da kai da wancan
kyakkyawan dan naka sai nayi muku mugun
kisan gilla irin wanda ba taba yiwa wani
mahaluki ba a doron kasa
: kafin Aljani Raugatul Aguwanu ya gaa rufe
bakinsa tuni boka sadusa ya dakamasa tsawa
yana mai cewa kai matsoracin aljani wanda
yakasa fita filin daga inda manya mazaje ke
fafatawaa: ina mai horonka da ka iya bakinka
ka saisaita lafazinka a gareni in ba haka ba
kuwa yanzu nan zan fusata na koneka kua na
kone gaba dayan wannan daji dakake matukar
kauna kamar yadda uwa keson danta
Dajin wannan jawabi sai Raugatul Aguwanu ya
dan tsorata don haka sao ya sunkui da kansa
kas cikin alamun girmamawa yace kayi mini
uzuri ya kai takadarin boka ka sani fa ni haka
halina yake bana son raini. Yanzu dai ni a koshe
nake zan sha giya domin na kwanta na yi barci
sosai sai dare ya tsala sannan zan tashi nayi
119
TASKARNOVELS.COM.NG
bincike a Hallarar tsafina bisa wannna sabon al
amarin daka zo mini da shi
Abinda nake bukata da ku shine ya yin dana
fara barci bana bukatar naji matsin komai ko
yaya yakee domin idan har na farka bana iya
komawa barci
Kai idan da hali ma ku fita daga waje kuje ku
yawata a cikin dajin nan har izuwa lokacin da
zan tashi daga barcina
ina mai tabbatar muku da cewa akwai
abbuwan al ajabi da yawa a cikin daji nan
wadanda zasu debe muku kewa izuwa lokacin
tashina daga barci: Koda jin wannan batu sai
sadusa yayi murmushi sannan yace ka san
ance da dan gari akan ci gari: Me zai hana fito
da wannan kyakyawar yarinya daga cikin keji
domin tayi mana jagora a cikin wannan daji
tunda ta fimu saninsa? Sa adda aljani Raugatul
120
TASKARNOVELS.COM.NG
Aguwanu yaji wannan bukata ta sadusa sai yai
shiru ya juya al amarin a cikin zuciyarsa kuma
ya kurawa sadusa idanun cikin alamun Rashin
Yarda daga can sai yace Menene tabbacin
cewa ba yaudarata za kuyi ba ku gudu da
Gimbiya SHALBIRAT? Kai sani cewa da raina
babu wani abu na biyu da nakeso sama da ita.
Sadusa yai murmushi yace Ai inda don ita na zo
wannan daji da baza kazo ka riskemu ba a cikin
kogonka tunda ina da karfin sihirin da zan iya
saceta: Raugatul Aguwanu ya gyada kai cikin
alamun nuna gamsuwa amma a can karkashin
zuciyarsa Dari dari yake yi
: Kawai sai yayi kuru ya sa danyatsansa guda ya
bude kejin da gimbiya Shalbirat ke ciki:
Shabiyat ta taka dan yatsan Raugatul Aguwanu
cikin tsananin farin ciki mara misaltuwa sbd
tsawon shekaru goma sha bakwan da ta yi a
wannan daji na Darul Hushushul maut a cikin
kejin ta yisu bata taba fitowa ba waje
121
TASKARNOVELS.COM.NG
: A sannan ne Raugatul Aguwanu ya sauke tafin
hannunsa kasa ta dir: Sai gata yar motsitsiya a
gaban sadusa tamkar dan karamin bera
Duk wannan abu dake faruwa Halyal na tsaye a
can gefe daya ya kurawa Shalbiyat idanu yana
mai matukar al Ajabi bisa ganin tsananin
kyawunta wanda yake ganin cewa ko Gimbiya
Hursiya kanwar sarki dujalu Albarka
Lokacin da Shalbirat ta duro kasa daga kan
tafin hannun Raugatul Aguwanu sai ta kaa
raawa da tsalle doin murna kuma ta fasge da
kukan farin ciki: A sannan ne aljani Raugatul
Aguwanu ya dubi sadusa yace Ga masoyiyata
Gimbiya Shalbirat na fito da ita kua na damkata
amana a hannunka: ka tafi da ita izuwa cikin
daji ku yawata daga nan har izuwa wayewar
gari: Koda gama fadin hakan sai aljanin
Raugatul Aguwanu ya nufi inda aka ajiye wani
katon tulu wanda sbd girmansa da nauyinsa
kato arba in bazasu iya rabashi da kasa ba ama
shi da yan yatsu biyu ya daga tulun: Ashe tulun
122
TASKARNOVELS.COM.NG
cike yake da ruwan gida kawai sa i ya kafa bakin
tulun a bakinsa ya kama sha kwal kwal karar
tafiyar ruwan giyar a cikin cikinsa tamkar ruwan
tekune ya balle yana shatata izuwa cikin teku
Raugatul Aguwanu bai sauke tulun giyar
kasaba sai da yaji babu sauran digo daya na
ruwan giya sannan ya ajiyeshi a kas ya tafi
izuwa kan wannan katon gado nasa na alfarma
yana layi yakife kasa: ko dakika goma bayi ba ya
kama wani irin gagarumin Munshari
: koda ganin faruwar hakan sai gimbiya
shalbirat ta yunkura a fusace ta zare wata
wukar sihiri ta aljani Raugatul Aguwanu dake
kugunsa daga sama da nufin ta caka masa ita a
kirjinsa sai boka sadusa yai wuf ya rike
hannunta sanan ya karbe wukar ya mai da ira
cikin kufenta da ke jikin Raugatul Aguwanu
Sadusa yayiwa Shalbirat da Halyal nuni da suyi
shiru kuma kada suyi wani kyakkyawar motsi:
Nan take yajasu suka fice daga cikin kogon
gaba daya: Sai da suka yi nisa da inda kogon
123
TASKARNOVELS.COM.NG
dutsen yake inda basa iya hangoshi sannan
suka zauna domin su dan huta: za;ansu ke da
wuya sai Shalbirat ta fashe da matsanincin
kuka
Al amarin da yai matukar dugunzuma hankalin
su Halyat kenan suka shiga rarrashinta suna
tamyarta dalilin kukan nata: Da kyar suka
shawo kanta ta daina kukan sannan tace ba
komai ne yasa kuka ga ina wannan kuka ba
face tsananin bakin cikin kun hanani kashe
aljani Raugatul Aguwanu domin ya salwantar
da rayuwata kuma ya kunsa min bakin cikin da
Har na mutu babu wata fansa da za ta
kankareshi: Kuyi sani cewa ni ce ya guda daya a
wajen mahaina sarki sharyalu na Birnin taukib:
babu irin kalar gatan da ban gani ba a duniya
kuma a nahiyar damuke babu wani sarki mai
karfin mulki da tarin dukiya irin ta mahaifina:
Mahaifin nawa bashi da kowa a duniya face
wata kanwaesa mai suna JUZAIRAT ta ri ga
mahaifina yin aure da shekara shida amma
bata taba samun haihuwa ba har mahaifina
yazo ya yi auren ka haifeni: Al amarin da yajefa
124
TASKARNOVELS.COM.NG
juzairat cikin tsananin bakin ciki kenan sbda
bata da wani buri wanda ya fi ta haifi dan da zai
gaje sarauta. babu irin asirin da juzairat ba
tayiwa mahaifiyata ba akan kada tasamu ciki
gami da kulle kulle da makirce makirce na
zahiri amma duk butaka bata biya ba
Kai sai da takai ta kawo juzairat tana nuna
kiyayyerta ga samun juna biyun mahaifiyata a
filin har maifina ya fahimta amma bai taba
nuna mata damuwarsa ba sbd tsananin son da
yake mata: Lokacin da na isa shekara ba kwai a
duniya lavarin tsananin kyawuna ya bazi ko ina
a nahiyar ya zamana cewa tun a sannan ya yan
sarakai da yan mayan attajirai sun fara zuwa
neman aurena sai hankalin juzairat ya
dugunzuma ainun kuma ta tsaneni fiye da
komai: A wannan lokaci tsufa ya fara riskar
mahaifina kuma gashi kullum yana cikin fama
da lalura ta rashin lafiya iri iri: gaba daya
likitocin mahaifina sun kasa gane abinda ke
damunsa don haka suka daina bashi magani
aka rinka kiran bokaye kowa yana yin iya bakin
kokarinsa amma babu sauki
125
TASKARNOVELS.COM.NG
A wannan lokacin na shaku da mahaifina ainun
fiye da yadda na shaku da mahaiyata domin
dare. Da rana bana yarda na nisanra dashi sau
tari sai bayan nayi barci akan kirjinsa sannan
mahaifiyata take zuwa ta daukeni ta tafi dani
izuwa kan gadonta ta shimfideni
Wani dare wanda shine daren mummunan
bakin ciki a Tarihin rayuwata wato daren da ba
zan taba mancewa dashi ba: Ina kwance akan
gado MAHaifina muna ta wasa dariya sai ciwo
ya taso asa har ya mike zaune da kyar ya zama
tari har da aman jini
Al amarin da ya dugunzuma hankalina kenan
na fara kuka kuma na yunkura da nufin naje na
kirawo mahaifiyata amma sai mahaifina ya yi
wuf ya riko hannuna a lokacin da shima ya
kama zubar da hawaye
126
TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin karfin hali yadubeni yace yake yata kiyi
sani cewa bakin alkalami ya riga ya bushe
mutuwa zanyi kuma yanzu nan ba dadewa ba:
Koda jin wanna batu sai na cika da tsananin
mamaki na kasa tambayarsa dalilin da yasa ya
fadi haka: Mahaifi nawa ya kankameni a
kirjinsa ya fashe da matsananincin kuka har
izuwa lokaci mai tsawo
Daga can sai ya janyeni daga jikinsa muka
fuskacin juna yace yake yata ki saurara da kyau
kiji abinda zan gaya miki
Kinga wannan rashin lapiya da na dade a
kwance ina fama da ita ba wani bane yasa mini
ita ba face yar uwata juzairat
koda jin wanna batu sai idanuna suka zazzaro
jikina ya kama tsuma sbd tsananin mamaki da
tsoro, mahaifina yacigaba da cewa juzairat tayi
127
TASKARNOVELS.COM.NG
mini asiri ne ta hanyar amfani da wani azzaluin
aljani wai shi Raugatul Aguwanu
Duk mutumin da wannan aljani ya shafa har
abada ba zai warke ba daga cuta sai dai ajali
aljani Raugatul Aguwanu bai amince zai yi
wannan mummunan aiki ba sai bisa sharadin
cewa za a mallaka masa ke kyauta domin
kyawunki: ina tabbatar miki da cewa nan da
cikar sa a uku zan mutum kuma junaizar da
aljani Raugatul Aguwanu suna nan suna jiran
cikar wannan lokaci domin juzairat ta sami
damar hawa karagata ta mulki shi kuma aljani
Raugatul Aguwanu ya sami damar daukeki ya
tafi dake izuwa can wani sihirtaccen daji wanda
baya shiguwa inda zai tsareki: Na san zakiyi
mamaki bisa yadda akayi nasan duk wannan al
amari to na sani ne ta hanyar wanin
shahararren bokon boka wanda yazo ya dubani
128
TASKARNOVELS.COM.NG
Hatta lokacin da juzairat ta gana da aljani
Raugatul Aguwanu sai da yanuna mini a cikin
madubin tsafinsa kuma ya tabbatar mini da
cewar bakin alkalami ya bushe babu wani
magani da zai iya bani na sha na warke daga
wannan ciwo
Koda na ji haka sai na fashe da kuka na dubi
bokan nace yakai wannan boka kayi sani cewa
ina yin wannan kuka ne ba don zan mutum ba
ko don bakin cikin abinda yar uwata taui mini
kawai inayi ne sbda zan mutu na bar yata
gimbiya shalbirat. Ina mai rokanka da ka bani
taimkon da zan iya kunbutar da rayuwar yata da
mahaifiyata a bayan raina koda kuwa zasu
gudu sukama wata nahiyar su cigaba da
sabuwar rayuwa
koda nazo nan a zancena sai boka yakamu da
tsananin tausayina Har hawaye ya zubo masa
sannan ya dora hannunsa a cikin aljihu ya
dauko wani lailayayen dutse ya miko mini na
karba sannan yace ka boye wannan dutse sai
129
TASKARNOVELS.COM.NG
nan da Kwanaki casa in: a daren kwana na
casa in dinne zaka mutu a lokacin dare ya raba
tsakiya: Lallai kafin cikar wannan lokaci ka
damkawa yarka wannan dutse dana baka
yanzu sannan ka umarceta da taje ta janye
mahaifuarta a cikin wannan dare su sulale
daga cikin birnin nana: idan har wannan dutse
yana hannin yarka shalbirat kuwa tana tare da
mahairyarta babu wani tsautsayi da zai samesu
har sun fice daga wannan nahiya: koda bokan
yazo nan a jawaabinsa sai na kamu da tsananin
farinciki: duk da cewar a kwance nake cikin jin
radadin ciwo sai dana yunkura na mike zaune
da kyar na kama yi masa gdya: kafin na kirawo
hadimina nasa a baiwa bokan lada tuni ya bace
bat: Ya nanemeshi sama da kasa ya rasa: Nan
take na boye wannan farin dutse a cikin aljihun
wandona bantaba yarda ani ya ganshi ba duk
dacewar ina cikin halim cuta, daga wannan
rana kullum sai yar uwata Juzairat tazo turakata
ta zauna sai ta sani a gaba ta na ta kuka tana
nuna matukar bakin cikina bisa lalura da nake
ciki
130
TASKARNOVELS.COM.NG
: daga wannan rana kullum sai yar uwata
Juzairat tazo turakata ta zauna sai ta sani a
gaba ta na ta kuka tana nuna matukar bakin
cikina bisa lalura da nake ciki.
: Dai dai rana daya ban taba nuna mata cewa
nasan kaidin data kulla mini ba: Sai dai kawai
idan na kalleta na zubar da hawaye takaici: ba
komai ne yasa nake zubar da hawayen takaici
ba face nayi matukar mamaki bisa yadda
wacce nake kauna fiye da komai a duniya ita ce
take son ganin mutuwata: Har izuwa wannan
lokacin da nasan cewa ita ce ta samini wannan
ciwo ban ji na tsaneta cikin zuciyata ba sbda
tun muna yara kanana na taso da tsananin
sonta: A dalilinta nayi yake yake ba adadi: Na
bata da abkaina sarakai wadanda suka
kasance aminena sbda sun nemi aurenta basu
samuba: hakan ta faru ne sbda na bata damar
tazabawa kanta miji: Muna yara juzairat ta taba
taka dan aljani suka shafeta: A kokarin samo
mata magani sai dana bar gida na shekara
hudu a cikn daji har na kusan rasa rayuwata
131
TASKARNOVELS.COM.NG
domin da na dawo gida sai da na shekara guda
akwance ina jinya
kuma an bata maganin da nakawo take ta
warke daga cutar mutuwarrabin jiki
Yau gashi an wayi gari Juzairat suk ta manta da
wannan wahalar da na sha a dalilinta wai ita ce
ma take neman rayuwata sbda kawai kwadayin
mulki kuma har takeson ta sabauta iyalina.
yake yata yanzu zan baki wanan fari dutsen
wanda boka ya bani: Da zarar kin karbeshi sai ki
ruga izuwa dakin mahaifiyarki ki labarta ma duk
abinda na gaya miki yanzu domin ku gudu:
Koda gama fadin hakan sai sarki ya zura
hannunsa acikin aljihun wando ya dauko
wannan farin dutsen ya miko mini:
HANNUNAna karkarwa kuma ina kuka na karbi
dutsen sannan na fada kan kirjinsa na
kankameshi ina mai sake fashe wa da
matsaicin kuka ina cewa ba zan iya rabuwa da
kai ba ya kai abbana gwara na tsaya aljani ya
kamani ya kaini inda bazan sake ganin komai
132
TASKARNOVELS.COM.NG
da kowa ba har izuwa ranar ajalina tunda dai
kaima mutuwa zakayi
koda jin haka sai hankalina ya dungunzuma ya
shiga rarrashina yana bani baki: sai da na shafe
sa a biyu ina kankame da shi ina kuka da kyar
ya shawo kaina na amince na sauka daga kan
kadon rike da wannan farun dutsen na sihiri a
hannuna ina waugensa ina zubar da hawaye
shima yana daga mini hannun hawaye na
kwararowa daga cikin idanunsa. . Nima nan
take idona ya ciko taf da hawaye dan haka sai
na tsaya cak da yin typing din ayi hak'uri jin
MAZAN JIYA Littafi na Hudu (4) Part L Na
Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh
AlQuyraemey Haka dai na daure na fice daga
cikin turakar na ruga izuwa turakar mahaifiyata
a cikin wannan dare. Duk inda na gifta a cikin
gidan sai naga dakaru suna bina da kallo cikin
mamaki. Haka dai na cigaba da gudu har na isa
cikin turkar mahaifiyata na kunnan kai izuwa
cikin turakarta: Ina shiga sai na iske mahaifiyar
tawa zaune a gefen gado idanunta cike da
hawaye kuma ko kadan babu alamar tayi barci
133
TASKARNOVELS.COM.NG
a kwayar idanunta: Al amarin da yai matukar
bani mamaki kenan na karasa gareta jikina a
sanyaye: HAR NA BUDI baki zan yi mata
bayanin abinda ke tafe dani sai ta rigani tace
duk abin da ya faru yanzu tsakaninki da m
Amahaiki naji kua na ganin domin ina labe a
kofar dakin ina kallonku baku sani ba
Yake yata kiyi sani cewa zuciyarta ta karaya
domin nasan cewa abi ne mawuyaci mu tsira
daga sharrin Juzairat: Ni kam na zabi na mutu
tare da mijina yau a cikin wannan dare nan da
cikar sa a guda inyaso ke ki tserar da kanki
koda jin wannan batu sai na fada kan kirjin
mahaifiyata na fashe da sabon kuka ina mai
cewa ai kuwa sai dai nima na tsaya na mutu
tare da ku din da dai na tafi wata nahiyar daban
na zauna inda ban ssan kowa ba ba a sannani
ba inda babu uwa kuma babu uba: Hakika
rayuwar da babu masoyi ai ba ta da wani
amfani a doron kasa Koda mahaifiyata taji
wannan batu sai ta mike tsaye zumbur cikin
134
TASKARNOVELS.COM.NG
firgici ta sureni da gudu muka fito daga cikin
turkarta: Nan fa ta direni kasa ta kamo hannuna
ta jani muka cigaba da gudu muka nudi kofar
fita daga cikin gidan sarautar gaba daya: Har a
sannan ina rike da wannan farin mulmullen
dutse na sihiri wanda mahaifina ya bani: muka
cikin gudun ne muka jiyo alamar wata irin
gagarumar iska ta biyomu a baya tana kokarin
cafkomu amma ta kasa: Sai da ya rage saura
bai fi taku biyar ba tsakaninmu da bakin kofar
wacce tuni masu gadi sun firgice sun budeta
suma sun cika wandunansu da iska sun yi
waje: Kawai sai