duba gawarwakin tana
neman gawar dan uwanta sarki Dujalu kuma
tana mai fashewa da kuka, shima jarumi
Hasnalu sai ya shiga duba gawarwakin dake a
filin yakin ko zai ga wanda yake da sauran rai,
sai da suka shafe rabin sa'a suna dube-dube
sannan a lokaci guda suka zo kan Dujalu da
Imnal, cikin gaggawa suka shiga kokarin ceto
rayukansu, inda d farko suka fara tsayar da jinin
dake zuba a jikinsu, sannan suka shiga dinke
raunikan dake jikinsu tare da sa masu magani,
kafin daga nan suka yayyafa masu ruwa suka
farfado suna masu dawowa cikin hayyacinsu. A
sannan nan ne Dujalu da Imnal sukaga jarumi
Hasnalu da Hursiyya tsaye a gabansu kawai sai
suka cika da tsananin mamaki kuma suka kmaa
kalle kalle da hange-hange sukaga gabadaya
filin gawarwaki ne babu sauran wani mai rai a
cikinsa. Koda Hursiyya taga dan uwanta sarki
Dujalu ya tsira da rayuwarsa sai ta rungumeshi
273
TASKARNOVELS.COM.NG
ta fashe da kukan farin ciki, shi kuwa Jarumi
Imnal a sannan ne hankalinsa ya dugunzuma
ainun, ya fara kuka saboda ya hanga ko ina
amman baiga gimbiya Mulaifa ba, kuma baiga
sarki Maharaz ba, nan take ya takarkare ya
kwarara uban ihu tare da fashewa da
matsanancin kuka, haka yayita yin kukan yana
mai dunkule kansa a kasa kamar ba zai daina
ba. Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka
hango wani mutum daga can nesa ya mike cikin
gawarwakin yana mai tunkaro inda suke yana
tangadi. Su duka sai suka zuba masa idanu sai
da ya kara matsowa kusa da su sosai sai sukaga
ashe sarki Maharaz ne, a wannan gabadaya ya
rine da jini, koda Imnal ya shaida cewa sarki
Maharaz ne sai ya mike tsaye da kyar ya tafi
zuwa gareshi, suna haduwa suka rungume juna
tare da durkuwa a kasa. Cikin matukar karfin
hali sarki Maharaz ya bude baki ya ce yayi
magana a cikin kunne Imnal ya ce masoyiyyarka
na can baya gawarwaki sun danneta, bani da
tabbacin tana raye ko ta mutu. Koda jin haka
sai Imnal ya saki Maharaz ya sake mikewa da
kyar ya kara gaba. A lokacin ne sarki Maharaz ya
yanke jiki zai fadi, kawai sai ga jarumi Hasnalu
274
TASKARNOVELS.COM.NG
ya karaso gareshi a guje ya tallaboshi sannan
nan take ya shiga ƙoƙarin ceto rayuwarsa.
Imnal ya cigaba da tafiya yana tangadi sannan
yana dube-duben inda gawarwaki suka danne
gimbiya Mulaifa. A wannan lokacin gimbiya
Hursiyya tana ta kokarin danne sarki Dujalu
domin so yake ya mike tsaye ya je ya cigaba da
yakar jarumi imnal, koda taga ya dage lallaı sai
ya je ya kashe imnal din sai ta daka masa tsawa
a karon farko a rayuwarta da shi. Cikin tsananin
mamaki da takaici sarki Dujalu ya koma ya
zauna a kasa dirshan sannan ya dubeta sa'ad
da hawaye ya zubo masa ya ce yake yar uwata,
yanzu yau kece da kanki kike daka mani tsawa
akan ina son na kashe makiyinmu, ashe kin
manta da duk irin halaccin da nayi maki kenan a
baya, kuma kin manta da duk irin kaunar da na
nuna maki, shin bakya kishin birninmu gami da
jama'armu kenan, ko kuma kin makance ne
baki ganin miliyoyin rayukan da muka yi asara
da kuma dunbin duniyarmu data salwanta a filin
yakin nan, yanzu kina nufin shikenan sai dai
burina nason mallakar wannan duniya ya rushe,
tabbas d dai haka ta faru gareni gwara ku
kyaleni na mutu dan banga amfanin ceto
275
TASKARNOVELS.COM.NG
rayuwata da kuka yi ba, wane ne wancan bakon
jarumin dana ganshi a tare da ke, kuma ya aka
yi kika dawo wannan filin alhalin nasa aljani
Balzaru ya shammaceki ya daukeki ya tafi dake
can birninmu? Hursiyya ta dubi sarki Dujalu a
lokacin data share hawayen dake kan fuskarta
ta ce ya kai dan uwana kayi sani cewa kayi mani
tambayoyi masu yawa, amman kayi hakuri duk
zan baka amsoshinsu nan bada jimawa ba,
abinda yasa nayi maka tsawa a yau shine, a yau
ne na gane da kai sarki Maharaz duk kuna kan
tafarkin bata ne mabayyani, kuma kuna wannan
yaki ne bisa zalunci da son zuciyarku kawai,
gashi kun janyo anyi asarar miliyoyin rayuka ba
tare da dayanku ya samu nasara ba, a yau kai
da Maharaz zaku gasgata zancena cewar duk
kuma kan hanyar bata domin a gaban idanunku
wancan bakon jarumin zai yi abinda kuka kasa
aikatawa da taimakon ubangijin gaskiya, koda
ta zo nan a zancenta sai suka jiyo Imnal yana
kwalla masu kira yana neman taimako.
Hursiyya ta mike tsaye zumbur kawai sai ta
hango Imnal yana ta kokarin ture wasu
gawarwaki domin ya zaro gimbiya Mulaifa
amman sai ya kasa, shi kuma a wannan lokaci
276
TASKARNOVELS.COM.NG
jarumi Hasnalu nata kokarin ceto rayuwar sarki
Maharaz. Koda ganin haka sai Hursiyya ta ruga
da gudu izuwa inda Imnal yake, ta taimaka
masa suka ture gawarwaki dake kan Mulaifa
suka zarota, aikuwa sai suka isketa a raye tana
numfashi kadan-kadan, cikin hanzari Hursiyya
ta shiga ƙoƙarin ceto rayuwar Mulaifa ta fara
tsayar da jinin dake zuba a jikinta ta hanyar saka
masa magani, sa'ar m da aka yi shine babu
manyan raunika a jikinta masu zurfi da yawa.
Koda Imnal yaga Hursiyya ta dage tana kokarin
ceto rayuwar masoyiyarsa gimbiya Mulaifa sai
ya cika da tsananin mamaki bisa ganin kanwar
babban abokin gabarsa ce take kokarin ceto
masoyiyarsa. A wannan lokacin ne Imnal ya
gama dawowa cikin hayyacinsa, ya juya baya ya
hango sarki Maharaz a raye tare a jarumi
Hasnalu kuma ya hango sarki Dujalu gefe daya
zaune yana kallonsu, bayan kamar sa'a guda
lokacin an gama yi wa kowa magani, aka samu
nutsuwa sai gaba dayansu su shidan suka taru
a waje guda, a lokacin ne Hursiyya ta kwashe
labarinta ta zayyana masu, tun daga lokacin da
ta hada baki da kuyangarta lazimat taje ta samo
mata aljani Radiyan ya fito da ita daga gidan
277
TASKARNOVELS.COM.NG
sarauta, kawo izuwa sa'ar da suka shiga cikin
kunnen Aljani Raugatul Agwanu ya cigaba da
tafiya da su har yazo dajin da suka hadu da
jarumi Hasnalu, da dukkan abubuwan mamakin
da jarumi Hasnalu yayi akan hanyarsa ta zuwa
bisa taimakon Ubangijin musulunci, kawo
izuwa lokacin da itama ta karbi addinin
musulunci a hannun Jarumi Hasnalu har suka
karaso bakin tekun. Lokacin da Hursiyya ta
gama bada wannan labari sai jikin Mulaifa,
Imnal da sarki Maharaz yayi sanyi, zukatansu
suka yi sanyi suka fara ayyanawa cewa lallai
wannan addini na Hasnalu shine addinina
gaskiya. Shikuwa sarki Dujalu sai ya fashe da
kukan bakin ciki, kuma cikin tsananin takaici ya
ce yake yarbuwata hakika kin tarwatsa mani
dukkanin shirina, yanzu duk irin tsananin
wahalar dana sha ta tsawon shekara da
shekaru ina shirye-shiryen mallakar duniya ina
kuma mai yin tanadi ya zama na banza kenan?
To bari in fada maki ni ban yarda cewa wannan
addini shine n gaskiya ba, dan haka ina nan a
kan bakana na cigaba da wannan yaki har sai na
kashe abokan gabata na shiga cikin wannan
teku na dauko takobin Saiful Lujara. Kafin
278
TASKARNOVELS.COM.NG
Hursiyya ta kara budar baki ta ce wani abu sai
sarki Maharaz ya tari numfashinsa ya dubi
Dujalu ya ce ya kai wannan sarkin abokin
gabata, ka sani cewa komai da yarjejeniya muke
yinsa, mu yanzu mun janye maka wannan yaki
mun hakura mun bar mka takobin Saiful Lujara,
idn har zaka iya daukota to ga fili nan ga mai
doki sai ka jaraba daukota mu gani, amman
bisa sharadi guda Sharadin kuwa shine idan har
ka kasa daukota kuma jarumi Hasnalu ya shiga
ya daukota zaka bada gaskiya ga addininsa
kamar yadda zamu bada gaskiya ga addininsa
yanzun nan. Sa'ad da sarki Dujalu yaji wannan
batu sai yayi shiru ya fada cikin kogin tunani,
daga can kuma ya dubi sarki Maharaz ya ce na
amince da wannan sharadi. Yana gama fadin
haka sai ya mike tsaye ya dauke takobinsa
sannan ya dubi sarki Maharaz ya ce kafin na
karbi addinin wannan bakon jarumin inason ka
taimakeni na dawo da dukkan sihirin tsafina
domin da shine zan iya shiga cikin wannan teku
na yaki ljanun dake karkashinta masu gadin
takobin na daukota. B tare da gardamar komai
ba sarki maharaz yayi murmushi ya ce nasan
cewa inba da taimakona ba babu yadda za'a yi
279
TASKARNOVELS.COM.NG
sihirinka tsafinka ya dawo, lallai zan taimakeka
b tare da naji shakka ko tsoron komai ba domin
ni yanzu nayi imani cewa addinin Musulunci
shine addinin gaskiya, kuma na yarda cewa kai
ba zaka iya dauko wannan takobiba sai dai
jarumi Hasnalu ya daukota. Koda jin haka sai
Sarki Dujalu ya bushe da dariyar mugunta yana
mai cewa aikuwa sai ka yi nadama kuma ka
gane cewa kayi babban kuskure tunda har
zuciyaka ta yarda da hakan, ina mai tabbatar
maka da cewa indai sihirin tsafina ya dawo
jikina to sai na samu nasarar dauko takobin
Saiful Lujara, kuma kaine mutum na farko da
zan kasheshi da ita. Sarki Maharaz yayi
murmushi sannan ya ce na amince d hakan.
Gama fadar hakan kedawuya sai sarki Maharaz
ya mike tsaye shima sarki Dujalu sai ya mike
tsaye suka tunkari juna, saura bai fi taku daya
ba su hadu sai cikin sauri Hursiyya ta shiga
tsakaninsu ta dubi sarki Dujalu idanunta na
zubar da hawaye ta ce ya kai dan uwana na
rantse da girman iyayenmu ko tsafinka ya dawo
ba zaka iya dauko wannan takobiba... Kafin
Hursiyya ta gama rufe bakinta tuni sarki Dujalu
ya hankadeta ta fadi can gefe guda, kawai sai ya
280
TASKARNOVELS.COM.NG
dubeta a fusace yana mai cewa kin bani kunya
d har kika zabi abokin gabarmu kika gujeni, to
kisani cewa har abada bazan yada Addinin
iyayye da kakanni ba domin shine abin kunya na
karshe da zanyi a rayuwata. Yana gama fadin
hakan ne sai ya karasa jikin sarki Maharaz suka
manne da juna, faruwar hakan keda wuya sai
wani irin haske mai karfi ya lullubesu, aka fara
wata irin gagarumar iska mai karfi gami da
taawa da walkiya a sararin samaniya, kawai sai
sarki Maharaz ya janye jikinsa daga jikin na
Dujalu tare da komawa gefe daya. Take wani irin
jan haske ya taho daga sararin samaniya ya
rinka shiga jikin sarki Dujalu har saida ya gama
shigewa kaf, a sannan ne sarki Dujalu ya ji wani
irin azababben karfi ya shigeshi, irin wanda bai
taba jin irinsa a duniya ba, dan ji yake tamkar
idan aka yi masa gammo zai iya daukar wannan
duniyar a ka ya kuma yi tafiya da ita. Nan take
sarki Dujalu ya kwarara uban ihu kuma y
sunkuya kasa ya dauki takobinsa ya nufi bakin
tekun bahar sufiya kai tsaye ba tare da shakkar
komai ba, har ma yana ji a cikin ransa cewa
cikin kankanin lokaci zai iya karar da duk aljanin
da suke cikin wannan teku kuma ya dauko
281
TASKARNOVELS.COM.NG
takobin Saiful Lujara. Nan dai y shiga cikin
tekun ya nutse can cikin karkashinta. Faruwar
hakan keda wuya sai Sarki Maharaz ya dubi
jarumi Hasnalu cikin murmushi ya cw da shi ya
kai wannan babban jarumi mai daraja, wanda
ya fitar damu daga cikin duhu izuwa haske,
maza ka shigar damu 2annan addini naka mai
daraja, kamar yadda ka shigar da Hursiyya.
Kafin jarumi Hasnalu ya bude bakinsa sai kawai
suka ji wata irin iska mai karfi ta taso masu har
tana neman wujijjigasu, sai da takai cewa sun
rike hannayen juna dan kada iskar tayi sama da
su, katsam kuma sai guguwar ta rikide ta zama
wani gwabjejen aljani wanda girmansa ya ninka
na aljani Raugatul Agwanu sau bakwai, gangar
jikinsa ta rufe gabas gabadaya. Koda sarki
Maharaz yayi arba da wannan aljani sai ya kamu
da tsananin tsoro ya durkusa a kasa bisa
gwiywoyin, ba wani bane wannan aljani face
aljani darbuza, gunkin da ake bauta mawa acan
birnin sarki Maharaz. Darzuba ya dubi sarki
Maharaz a fusace ya daka masa tsawa ya ce
ashe yanzu duk taimakon da muka dade muna
yi maka tsawon shekara da shekaru ya zama na
banza, mune muka doraka akan karagar mulki,
282
TASKARNOVELS.COM.NG
muka baka arziki mai yawa, kuma muka
daukaka amman kuma shine yanzu zaka yi
mana butulci kadaina bauta mana ka koma
bautar wani...? Kafin aljani darzuba ya karasa
kalmar dake bakinsa tuni jarumk Hasnalu ya
tari numfashinsa ya daka masa tsawa yana mai
cewa kai tsohon kafiri, babban matsafi kuma
mayaudari kayi sani cewa kai ba komai bane
face bawan ubangijin musulunci domin shime
ya halicceka, shekara da shekaru kana yaudarar
sarki Maharaz da jama'arsa kana shiga cikin
gunkin da suke bauta mawa kana magana da su
a matsayin ubangijinsu, to ka sani cewa yau
dubunka ta cika, kuma asirinka ya tonu, ina mai
kiranka daka tuba ka daina kiran kanka a
matsayin ubangiji ka mika wuya ga ubangijin
musulunci wanda shine ubangijin komai da
kowa. Koda jin wannan batu sai aljani Darzuba
ya bushe da wata mahaukaciyar dariya wacce
ta cika dajin gaba daha da amsa kuwwa, dan
haka dole kowa ya rinka toshe kunnuwansa.
Lokaci guda kuma darzuba ya tsuke fuskarsa
yana mai daka wa jarumi Hasnalu tsawa yana
mai cewa kai karanin kwaro, karyarka tasha
karya, fiye da shekaru dubu ina fafawa da ire283
TASKARNOVELS.COM.NG
irenka amma basu taba samun nasara akaina
ba, saboda haka kalma yanzu zanyi maka kisan
gilla a gaban wadannan mutane, domin su
zama sheda akan cewa nine abin bauta mafi
cancanta. Gama fadin hakan keda wuya sai
aljani Darzuba ya wangame katon bakinsa ya
frsa wa jarumi Hasnalu wata irin gagarumar
wuta. Cikin bakin zafin nama Hasnalu ya daka
wawan tsalle ya bar inda yake yana mai neman
taimakon Allah, aikuwa sai wannan wuta ta
zuba akan wata katuwar bishiya, wacce
kaurinta ya kai kamu arba'in, tsayinta kuwa ya
kai zira'i saba'in. Nan take bishiyar ta nake ta
zagwanye kamar an tsom alumin a cikin ruwa,
sai tiririn hayaki kawai aka gani na ruburbushin
bishiyar. Koda aljani Darzuba yaga jarumi
Hasnalu ya tsallake annan mugun hari nashi,
sai ya taso masa a fusace da dukkan karfinsa,
aikuwa shima Hasnalu sai ya tare shi rike da
takobinsa suka kacame da azababben yaki mai
tsananin ban tsoro, a duk sa'ad da takobin
Hasnalu ta hadu da takobin aljani Darzuba sai
kaji kara kal! Kal!! Tamkar karfe da karfe ne suka
hadu, kuma tartsatsin wuta ya tashi, nan fa
Imnal, Hursiyya, Maharaz da Mulaifa suka cika
284
TASKARNOVELS.COM.NG
da tsananin mamaki bisa ganin irin jarumtakar
Hasnalu, domin kwanjin aljani darbuza guda
daya ma ya kai kaurin bishiyar katuwar kuka
guda uku, amman duk sa'adda ya kai wa jarumi
Hasnalu naushi ya kauce tofa duk abinda ya
samu walau dutse ko bishiya take suke
ragargaje, haka idan ya kai mashi sara ko suka
da mugayen faratan hannayensa masu
tsananin karfi da tsini kamar zabira to kome
suka samu sai dai kaga abin ya dare gida biyu
kamar an yanka tsakiyar tuffa, ko kuma kaga
abin ya huje tamkar an hujeshi da mashi. Nan
fa suka tayar da hankalin dajin gabadaya, kasa
ta kama girgiza wuta ta dinga fallatsa tana dira a
wurare da dama tana haddasa gobara, su
kansu su Imnal sai da suka gama guje-guje
suna neman wajen buya, saboda masifar takai
masifa, amman duk da haka basu fasa leken su
aljani Darzuba ba domin suga abinda ke
wakana. Haka dai aka cigaba da wannan bakin
artabu tsakanin jarumi Hasnalu da aljani
Darzuba, har dare ya raba sosai amman daya
daga cikinsu bai samu nasarar koda lakutar jikin
dya ba, da kansu suka ja da baya suk yi cirkocirko suna haki gami da harar juna. Shi dai aljani
285
TASKARNOVELS.COM.NG
Darzuba mamaki ne ya kamashi ainun yadda
har aka yi yau ya hadu da shu'umin biladama
alhalin tsawon shekara da shekaru yana cin
karensa ba babbaka, duk mahalukin da suka yi
gaba da gaba da shi walau mutum ko aljan, tofa
a cikin abinda bai fi dakika goma ba yake
gamawa da shi komai karfin damtsensa dana
sihirinsa kuwa, amman yau gashi dan tatsitsin
biladama ya gagareshi a kusan sa'a bakwai
suna gumurzu. Shikuwa jarumi Hasnalu tunda
suk fara wannan gumurzu addu'a yake yi a
zuciyarsa ta neman tsari, dan haka a yanzu sai
ya fra karanta addu'ar neman sa'a akan abokin
gaba, a daidai wannan lokacin ne aljani
Raugatul Agwanu ya iso bakin tekun dauke da
boka Sadusa, Halyal da Gimbiya Shalbirat ya
dauka a bayan wani katon dutse inda su Imnal
suka buya, su duka sai suka fara leke suna
hango inda ake wannan gumurzu, abinda suka
iya hangowa kawai shine aljani Darzuba da
jarumi Hasnalu a tsaye sun fuskanci juna suna
kokarin sake kacamewa dda wani sabon fada.
Su jarumi Imnal kuwa sun buyan wasu fogyen
bishiyu dake nesa kadan da inda ake wannan
fafatawar, suna masu kallon abinda zai faru.
286
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda su aljani Raugatul Agwanu suka hango
aljani Darzuba da Jarumi Hasnalu su biyu kacal
a bakin kogin bahar sufiya sai suka cika da
tsananin mamaki, aljani Raugatul Agwanu ya
jinjina kai cikin alamun tsoro ya dubi su Sadusa
ya ce Tabdijan lallai yau abin babbane, tunda
har takai cewa saura manyan mazaje kafai a
filin dagar, shin ko kunsan wancan wane aljani
ne a tsaye kuwa? Boka Sadusa ya dubeshi cikin
ashin sani yace wane ne? Kuma wane ne
biladaman dake fuskantarsa? Raugatul
Agwanu yayi ajiyar zuciya sannan yace ai
wancan aljanin shine sarkin sadaukai na
dukkan aljanun duniya, kuma shine ubangijin
da mutanen sarki Maharaz suke bauta mawa,
kimanin shekaru dubu ashirin baya an taba yin
yakin duniya na aljanu, wannan sarki na aljanu
shine kadai ya baro filin daga a raye, amman sai
da gabadaya mayakan sama da aljanu dubu
dari tara suka mutu, a tarihin sadaukai da
mayaka na duniya ba'a taba samun jarumi
kamarsa ba, shi kuma wancan bil'adaman ban
taba ganinsa ba, kuma ban taba jin labarinsa,
ku duba da kyau gabadaya filin yakin can
ciccike yake da gawarwaki, daga nan ma ina iya
287
TASKARNOVELS.COM.NG
hango ruburbushin sassan jikin aljanu
dukkaninsu sun kone, ai kawai ina ganin cewa
mu tsaya anan mu cigaba da kallo domin muga
yadda wannan fada zai kasance tsakanin
Darzuba da wancan shaidanin biladama, na
tabbata duk akan takobin Saiful Lujara suke
fadan, babu mamaki suyi ragas mu kuma mu
tsinci dami a kala. Koda jin wannan batu sai
tunanin boka Sadusa ya sauya, shi dai burinsa
kawai yazo yaga sarki Dujalu ya mutu ya koma
can kasarsa ya sanar wa da yan majalisarsa a
bashi babban mukami a masarautar, amman
kuma yanzu da yaji batun samun takobin Saiful
Lujara a saukake sai ya fara tunanin ya za'ayi ya
mallaketa shi kadai, ya shammaci aljani
Raugatul Agwanu ya halakashi tunda ya fahimci
cewar shi sokone, nan dai ya kudurce a ransa
cewa ya saurara yaga yadda karshen wannan
gumurzu zai kasance tsakanin aljani Darzuba
da bakon jarumin da baisan ko wane ne ba.
Acan karkashin tekun bahar sufiya kuwa lokacin
da sarki Dujalu yayi nutso zuwa cikinta yana mai
jin tsananin karfi a jikinsa, yana ji tamkar zai iya
yakar duniya kaf sai y kama lalube, nan fa ya
dinga tafiya irin ta kifi a cikin tekun, da yayi
288
TASKARNOVELS.COM.NG
tafiyar tsawon rabin sa'a yaga baiga alamar
takobin Saiful Lujara ba, sai ya dawo da baya
yayi yamma, haka dai ya cigaba da lalube har ya
nufi bnagaren karshe na arewa, aiko yana cikin
wannan gudu ne ya hango dandazon wadannan
aljanu masu gadin Takobin Saiful Lujara a
gaban wata katuwar akwatu ta zinare sunyi
mata kawanya a sama da kasa. Koda sarki
Dujalu ya hango ttsananin yawan aljanun nan
da kuma kirarsu ta girma da sadaukantaka gami
da irin mugayen makaman da suke dauke d shi
sai zuciyarsa ta buga karfin gaske yaji tsoro ya
darsu a cikin zuciyarsa, amman daya tuna irin
shekarun daya bata yana shirye-shirye akan
mallakar annan takobi ta Saiful Lujara da kuma
tsananin wahalar da ya sha a wannan yakin har
yakai ga wannan nasara ta matakin karshe, sai
yaji dukkan tsoro ya gushe daga cikin zuciyarsa,
yace ai rai ba a bakin komai yake ba muddin
akwai biyan bukata, dan haka sai yayi kukan
kura y ruga izuwa kan mugayen aljanun da nufin
ya tsarwatsasu ya fasa wannan akwatu ta zinare
ya dauko takobin Saiful Lujara daga cikinsa, a
maimakon aljanun su taso masa gaba dayansu,
sai guda daya ne jal ya taso masa suka kaure da
289
TASKARNOVELS.COM.NG
zababben yaki, aikuwa suna fara yakin ne sarki
Dujalu ya gane kuransa domin tsananin zafin
naman ljanin da karfin damtsensa gami da na
sihirinsa ya ninka nasa sau bakwai, sai da takai
cewa sarki Dujalu baya iya kaiwa aljanin hari sai
dai kokarin kare kai kawai d yake yi, gashi dai
duk sa'ad da aljanin ya sari jikin Dujalu
makamin baya tasiri amman fa jikin nasa yan
tsami dan yana shan bugun tsiya. Koda wannan
aljanin yaga Dujalu