x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 22 - MAZAN JIYA 4

  • 63001 words
  • 66000 words
  • Out of 68055 words

Category: Adventure Stories

Views 193

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
abinda bai fi
dakika biyu ba rak yaga har ya iso dajinsa na
darul hushushul maut, dan haka cikin tsananin
farin cikk ya sakko kasa ya kunna kai izuwa cikin
wannan kogon dutsen nasa, koda ya shiga cikin
kogon kawai sai ya kama kyalkkyala dariya jar
da faduwa kasa kamar wanda ya zautu, haka
dai aljani Raugatul Agwanu ya cigaba da
wannan dariyar tamkar ba zai daina ba, haka
dai ya rude kuma ya kidime yama rasa abinda
zai yi daga can wata zuciyar ta ce da shi; kaje ka
fara yakar manyan kasashen duniya da babu
kamarsu, ka cisu da yaki su dawo karkashin
mulkinka. Wata zuciyar kuma sai ta ce da shi
A'a kamata yayi ka tara aljanun duniya kaf su
durkusa a gabanka suyi maka sujjada domin ka
371

TASKARNOVELS.COM.NG
zama ubanjinsu sannan kasa a gina maka
masarauta irin wadda ba a taba gina kamarta
ba tun daga wanzuwar duniya kawo iyanzu. A
cikinta kasa a gina maka aljannar duniya a
kuma kawata ta kyawawan mata na jinsin
mutane da aljanu guda miliyan dubu ɗay-ɗay
kuma a zuba kayan kawa na dangin su dinare,
lu'u lu'u, jauhar, zubar daji da dai sauransu irin
wanda ba a taba tara mai yawansu ba. Haka
dai aljani Raugatul Agwanu ya cigaba da sakesake iri-iri a cikin zuciyarsa yana mai cike da
mamakin yadda aka yi yayi wannan babbar
tsuntuwar a sama alhalin shekara da shekaru
manyan sarakunan aljanu da Sadauku, Bokaye
na aljan dana mutane sunyi iya yinsu su mallaki
kayan yakin mazan jiya amman sun kasa. Sai
da aljani Raugatul Agwanu ya shafe sama sa'a
guda yana tunani gami da sakar zuciya sannan
ya yanke shawarar ya fara ziyartar kaaashen
aljanu ya tara sarakunansu kaf sannan ya basu
umarnin bisa bukatarsa ta fara gina masa fada
wacce babu kamarta. Nan take aljani Raugatul
Agwanu ya juya da nufin ya fice daga cikin
wannan kogo nasa, amman bisa mamaki sai ya
ji yana jin yunwa, al'amarin da ya fusata shi
372

TASKARNOVELS.COM.NG
kenan ya ce a cikin zuciyarsa ai ya kamata ace
yanzu na daina jin yunwa da kishin ruwa a
rayuwata tunda na mallaki wadannan kayan
yakin na mazan jiya wadanda ke dauke da
sihirin da babu kamarsu a duniya. Kawai sai ya
kama cin yayan itatuwa dake cikin kogon nasa
har sai da yaji ya koshi gami da yin gyatsa. Sai a
sannan ne ya sake juyawa a karo na biyu ya fice
daga cikin kogon da nufin ya bude fuka-fukansa
ya tashi sama, amman sai yayi arba da abinda
ya bashi mamaki fiye da tunnainsa gami da
hankalinsa, ba wani abu bane aljani Raugatul
Agwanu yayi arba da shi ba face jarumi
Hasnalu, su duka tsaye a bakin kogon
dutsenasa tamakar dama sun dade a wajen.
Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin jarumi
Hasnalu da aljani Raugatul Agwanu, alokacin
da su Imnal suka rakube gefe daya sakamakon
ganin kayana yakin mazan jiya fa suka yi a jikin
aljani Raugatul Agwanu. A wannan lokaci
girman aljani Raugatul Agwanu da kwarjinsa ya
kinka nada sau goma tamkar hurashi akayi ya
kumbura, tsananin karfin sihirin kayan yakin
mazan jiya ne yasa suffar tasa ta sauya gaba
daya, shi kansa jarumi Hasnalu in banda yana
373

TASKARNOVELS.COM.NG
da dakakkiyar zuciya irin ta manyan jarumai
kuma yayai imani da Allah da ja zai yi da baya,
domin sai fa xuciyrsa ta darsu ya tabbatar da
cewa karo da wannan aljani ba karamin aiki
bane, domin karfi ko kwarewar yaki ba zata ceci
mutum ba. Aljani Raugatul Agwanu ya dubi su
jarumi Hasnalu ya daka masu tsawa yana mai
cewa, yaku wadannan kananun kwarin maza
kuyi sujjada a gareni kafin gushina ya tabbata a
gareku, kuyi sani cewa ni yanzu na zama
ubangijin mutane da aljanu,wanda duk bai
bauta mani ba to zai zama gawa, ko kuma ya
gamu da azabata mara yankewa... Kafin aljani
Raugatul Agwanu ya gama rufe bakinsa jarumi
Hasnalu ya tari numfashinsa yana mai daka
mashi tsawa ya ce kai tsohon mushriki kuma
batacce ka sani cewa babu abun bautawa da
gaskiya face ubangijin musulunci, ina mai kira a
gareka daka zubar da wannan kayan yakin dake
jikinka na mazan jiya, kuma ka tuba ga Allah ka
karbi addinin gaskiya runda kaga yadda gaskiyar
ta rinjayi karya a bakin tekun bahar suffiya,
kuma kaga wannan al'amari kuru-kuru da
idanunka, idan kuwa ka bujere wa wannan
umarni nawa zan yankeka da taimakon
374

TASKARNOVELS.COM.NG
ubangijina na halakaka take yanzu. Koda jarumi
Hasnalu yqzo nan a zancensa sai aljani
Raugatul Agwanu ya bushe da wata
mahaukaciyar dariya, wacce ta haifar da wata
irin guguwa mai karfin gaske, wadda tasa
bishiyoyi suka kama kakkaryewa suna zubewa
kasa, ruwan korama ya kama fanjam-fanjam,
iskar ta tashi su jarumi Imnal kamar zata tashi
da su sama, har saida aljani Raugatul Agwanu
ya tsuke bakinsa sannan komai ya lafa. Cikin
tsananin fushi aljani Raugatul Agwanu ya zare
takobin Saiful Lujara tana mai yin wani irin
haske gami da walwali na sihiri mai ban tsoro ya
dubi jarumi Hasnalu yace yaro maza bisa
kanka, sai ubangijin naka ya kareka na gani.
Kafin Jarumi Hasnalu ya zare tasa takobin tuni
aljani Raugatul Agwanu ya kawo masa wawan
sara fa nufin ya tsargeshi gida biyu, cikin zafin
nama ya goce wa takobin Saiful Lujara, takobin
ta dira akan wani katon dutse na wuta, take
dutsen ya ragargaje kuma ya nike ya zama gari,
fallutsuwar da ruburbushin da dutsen yayi ne
gami da tsananin zafin ruburbushin da karfin
karar bindigar dutsen ya zubo akan su jarumi
Imnal take gaba dayansu suka zube sumammu.
375

TASKARNOVELS.COM.NG
Alokacin ne fa aka fara azababben yaki tsakanin
aljani Raugatul Agwanu ya jarumi Hasnalu ya
zama cewa sun himmatu suna kaiwa junansu
sara cikin bakin zafin nama juriya da bajinta, a
duk sa'ad da aljani Raugatul Agwanu ya kawo
wa jarumi Hasnalu sara ko suka ya kauce tofa
duk abinda ya samu walau dutse, bishiya ko
kasa take abin yake narkewa kuma ya kamada
wuta, babban abinda ya daure wa Raugatul
Agwanu kai shine ganin yadda takobin Hasnalu
bata karyeba sakamakon haduwar da tayi da
takobin Saiful Lujara, alhalin dutse d bishiya ma
narkewa suke yi idan takobin ta shafesu bama
ta saresu ba, abinda aljani Raugatul Agwanu bai
sani ba shine karfin addu'a ne yasa takobin
jarumi Hasnalu ta tsira. Shi kuwa jarumi
Hasnalu duk sa'ar da takobinsa ta sari jikin
aljani Agwanu sai dai yaga tartsatsin wuta yana
tashi tamkar karfe ya sara, idan kuwa takobin ta
sari hular lamsara sai dai kaga tsawa fa walkiya
na tashi gami da wani irin mugun hayaki da yake
turnuke dajin gabadaya. Sai da suk shafe
tsawon sa'a guda suna wannan bakin artabun
amman babu wanda ya samu wata nasara a
tsakaninsu, al'amarin daya fusata aljani
376

TASKARNOVELS.COM.NG
Raugatul Agwanu kenan kuma yayi matukar
bashi mamaki, dan haka sai ya ja da baya ya
sakar wa Hasnalu mashin galilur haras, aikuwa
sai mashin ya tafi da tsananin gudu yana shirin
cake idonsa na hagu, koda Hasnalu ya goce sai
mashin ya wuce ta saman fuskarsa ya je ya
shige ta vikin wani katon dutse ya fice fit, kuma
ya dawo da baya da gudu ya yo kan Hasnalu.
Nan fa Hasnalu ya cigaba da yaki da wannan
mashi na galilur haras, shi kuwa aljani Raugatul
Agwanu sai ya tsaya cak yana kallon bakin
gumurzun da ake yi tsakanin mashin galilur
haras da kuma karumi Hasnalu ma'ana ya zama
dan kallo babu abinda Aljani Raugatul Agwanu
yake face kyalkkyala dariyar mugunta
musamman da yaga cewa mashin ya kuntata
Hasnalu. A daidai wannan lokaci ne su Imnal
suka farfado daga dogon suman da suka yi,
koda sukaga irin azababben yakin da ake yi
tsakanin mashin galilur haras da jarumi
Hasnalu sai suka cika da tsananin mamaki gami
da tsoro, domin basu taba ganin makami kamar
galilur haras wanda yake muguwar barna kamar
haka, barnar data ragargaza dajin gabadaya, ta
haddasa famtsamuwar narkakken dutse, b shiri
377

TASKARNOVELS.COM.NG
su jarumi Imnal suka mike suka ruga da gudu
izuwa can nesa kadan suka tsaya suna kallon
ikon Allah, domin idan suka tsaya inda ake
gumurzun narkakken ruwan dutsen ne zai dafar
da su. Sai da aka kara shafe wata sa'a guda ana
gumurzu tsakanin mashin galilur haras d jarumi
Hasnalu har takai cewa Hasnalu ya fara gajiya,
a lokacin ne kuma mashin ya kawo wa Hasnalu
mugun suka a ciki ya goce cikin matukar zafin
nama, amman duk da haka sai da mashin ya
huda rigarsa ya fice fit, take kuwa rigar ta kama
da wuta, cikin hanzari Hasnalu ya yaga rigar
tasa ya jefar fa ita, a lokacin ne kuma mashin ya
kara dawowa da baya ya saito kirjinsa zai
tsireshi, kawai sai su Imnal suka ga Hasnalu ya
mayar da takobinsa cikin kufe kuma ya runtse
idanunsa yana mai karanta wata addu'a.
Al'amarin da ya firgitasu kenan, gimbiya
Hursiyya ta kama kwala wa Hasnalu kira daga
inda suke labe cikin dimauta tana mai ce mashi
ya kauce kada mashin ya soke shi. Ko juyowa
ya dubeta Hasnalu baiyi ba, kuma sam babu
alamar tsoron wannan mashin a tare da shi.
Shiko aljani Raugatul Agwanu sai ya kama
kyalkyala dariyar mugunta saboda yana ganin
378

TASKARNOVELS.COM.NG
cewa tabbas wannan karon ajalin Hasnalu ya
zo, koda ya rage saura baifi kamu daya ba jal
tsakanin kirjin Hasnalu da mashin galilur haras
sai akaga mashin ya tsaya cak a sama, shi bai
gado kasa ba kum shi bai wuce ba, a sannan ne
jarumi Hasnalu ya bude idanunsa kawai sai ya
dafa mashin da hannunsa na dama take mashin
ya dagargaje kuma ya tarwatse yayi gutsugutsun kamar kwayar zarra. Koda ganin abinda
ya faru sai aljani Raugatul Agwanu ya kwarara
uban ihu cikin tsananin bakin ciki har kwallar
takaici ta zubo daga cikin idanunsa. Su kuwa su
sarki Maharaz koda ganin wannan nasara da
Hasnalu ya samu akan mashin galilur haras sai
suka kama kabbara gami da yiwa Allah godiya.
Nan fa aljani Raugatul Agwanu ya sake kwarara
uban ihu a karo na biyu, sannan cikin tsananin
fushi ya zare takobin Saiful Lujara ya afka wa
jarumi Hasnalu da dukkan karfinsa suka sake
kacamewa da azababben yaki. Wohoho!
Hakika wuya ba a sa mata rana, maza sune
maganin maza, kuma tabbas karfi yana da
ranarsa, haka ma kwarewa da sanin makama a
yaki tana da rana. Tabbas inba dan jarumi
Hasnalu ya kasance gwarzon mayaki ba wnda
379

TASKARNOVELS.COM.NG
ya saba gwagwarmaya tare da fafatawa a cikin
maza ba, kuma yana hadawa da neman tsari a
wajen Allah da tuni aljani Raugatul Agwanu yayi
masa kwab daya a wannan fafatawar da suka
fara, amman duk da haka sai da kai cewa aljani
Raugatul Agwanu ya zame masa alakakai, ya
rasa ta inda zai bullo masa, shima kuma Aljani
Raugatul Agwanu ya rasa hanyar da zai bi ya
samu nasara a kansa, sai gashi takobin tasa ta
Saiful Lujara da hular lamsara sun kasa tsinana
masa komai, a haka sai da suka shafe sa'a guda
suna wannan gumurzu. Kaico! Ance gobara
daga kogi maganinta sai Allah, ba shiri aljani
Raugatul Agwanu ya ja da baya ya tsaya yana
haki yana kum kallln jarumi Hasnalu cikin
tsananin al'ajabi, domin shi a rayuwarsa ma bai
taba gajiya a filin yaki ba dan yana iya kwana
arba'in yana yaki a filin daga cikin tsakiyar
miliyoyin abokan gaba, amman yau gashi
mutum daya jal ya gagareshi kuma ya gajiyar da
shi a cikin sa'a daya da rabi. Bayan anyi kallon
kallo tsakanin jarumi Hasnalu da aljani
Raugatul Agwanu na taawon dakika dari uku da
sittin, sai nan take hadari ya gangamo aka fara
wata Irin iska mai karfi amman hakan bata sa su
380

TASKARNOVELS.COM.NG
Imnal sun bar wanen da suke labe ba, saima
suka nemi mafaka suka labe, babban burinsu
kawai shine suga yadda karshen wannan fada
zai kasance. Nan take kuwa aka fara yayyafi
kadan-kadan yana mai sakkowa kasa, kawai sai
ljani Raugatul Agwanu ya cire hular lamsara ya
ajiyeta gefe guda, sannan kuma ya ajiye takobin
Saiful Lujara a kusa da hular, ya tada kwanjinsa
yayin da jijiyoyin jikinsa suka tashi suka yi
burdin-burdin nan fa kirarsa ta sadaukantaka ta
fito ainun, aiko sai ya takarkare ya kwarara uban
ihu mai tsananin firgitarwa, duk da irin
jarumtaka tasu Imnal sai da suka ji kamar su
arce da gudu, domin babu wanda bai motsa ba
harma da jan baya ba a cikinsu, duk da cewa
suna can baya nesa a matsayin yan kallo.
Shikuwa Jarumi Hasnalu ko gezau bai yi ba,
kawai shima sai ya gyara tsayuwa yana mai
dunkule hannunsa. Su zukatan su Imnal kuwa
cike suke da mamaki har suna tambayar
zukatansu cewa wai shin wacce irin dakakkiyar
zuciya jarumi Hasnalu ke da ita ne, ta yaya zai
tari wannan gansamemen sadaukin aljani yana
matsayin biladama. Aljani Raugatul Agwanu ya
dubi jarumi Hasnalu yace na ajiye dukkan
381

TASKARNOVELS.COM.NG
ababan dogaron nawa da dukkan tsafina, zan
yakeka da tsagwaron karfin damtsena, idan ka
sa kaima ka yakeni da tsagwaron karfin
damtsenka, kada kayi amfani da karfin
sihirinka. Sa'ad da jarumi Hasnalu yaji wannan
batu sai yayi murmushi sannan ya ce na yarda
xan yakeka da tsagwaron karfin damtsen da
ubangijin ya bani, kuma ina ka sani cewa ni bani
da wani sihiri face karfin ubangijina da yake
bani kariya daga dukkan sharrinku na aljanu...
Kafin jarumi Hasnalu ya gama rufe bakinsa tuni
aljani Raugatul Agwanu ya shammaceshi ya
daka tsalle sama yayi masa rotse fa gwiywar
hannunsa a ka, nan take Hasnalu ya sulale kasa
magashiyan mugun yananyi mai kama da suma
ko gushewar tunani. Nan fa hankalin su Imnal
ya dugunzuma ainun, kuma suka kamu da
tsananin tsoro, abinda ya basu mamaki shine
kamata yayi ace kan jarumi Hasnalu ya dgargaje
domin ko dutse aljani Raugatul Agwanu ya doka
da wannan gwiywar hannuntasa sai dutsen ya
farfashe, amman sai gashi babu abinda ya
samu Hasnalu, sai dai jini da yayi fitar burgu
daga cikin hancinsa gami da bakinsa. Nan take
Imnal ya yunkura zai falfala da gudu domin ya
382

TASKARNOVELS.COM.NG
kaiwa jarumi Hasnalu dauki, amman sai sarki
Maharaz yai caraf ya rikeshi tare da cewa ai
kada mage ba yanka bane tsaya dai muga
abinda zai faru. A wannan lokaci aljani Raugatul
Agwanu sai faman ihu yake gami da kuri da cika
baki, bisa ganin yayi wa jarumi Hasnalu kaf daya
ya baje a kasa yana neman shekawa barzahu,
koda yaga cewa Hasnalu ba zai iya tashi ba, sai
ya juya ya dauko takobin Saiful Lujara da nufin
ya dawo ya daddatsa Hasnalu yayi gutsugutsun da sassan jikinsa. Aiko yana daukar
takobin kafin ma ya juyo tuni jarumi Hasnalu ya
mike tsaye zumbur tamkar an ja zaren baka,
kawai sai ya dako tsalle sama daga inda yake ya
daki bayan aljani Raugatul Agwanu, kamar daga
cikin baka aka harba aljani Raugatul Agwanu
aka yayi tsalle sama yaje ya gwaru da wani
katon dutse, karar haduwar kirjinsa da dutsen
ta cika dajin gabadaya, dutsen ya farfashe
kuma ya fado kasa a matukar galabaice yana
mai yin aman jini ta baki da hanci kai harma ta
kunnesa ma jini ne ke bulbulowa, anan ya kama
shure-shuren mutuwa sakamakon cakudewar
jini da ƙwaƙwalwarsa. Cikin tsananin mamaki
da farin ciki su Imnal suka rugo da gudu izuwa
383

TASKARNOVELS.COM.NG
ga jarumi Hasnalu suka rungumeshi sun masu
yi masa jinjina bisa Wannan gagarumar
jarumtaka da ya nuna, shi kuwa Aljani Raugatul
Agwanu bai shafe dakika talatin ba yana
wannan shure-shuren ya zama gawa. Farin ciki
a wajen gimbiya Hursiyya da su sarki Maharaz
ba sai an fada ba,nan dai suka zauna
gabadayansu jarumi Hasnalu ya shiga koyar da
su yadda ake yin ibada kamar su; tsarki, wanka,
alwala da sallah, koma ya fara koya masu
karatun Alkur'ani mai girma, ya biya masu
suratul fatiha da falaki da nasi, bayan nan ne
yayi masu limanci suka gabatar da sallar
la'asar, da aka idar da sallar akayi addu'a sai
jarumi Hasnalu ya dubesu gabadayansu tare da
cewa to yanzu duk wanda yake jin yunwa sai
yaje ya ci, wanda kuma duk yke da bukata ya
kawar da ita, domin zamu cigaba da tafiya ne,
da izinin Allah zan cika alkawarina na kai
kowannenku zuwa kasarsa. Cikin matukar farin
ciki kowa ya bude jakar guzurinsa ya dauko
abinci ya kamaci, shiko jarumi Hasnalu sai ya
dauko tasbaha ya kama lazimi. Jarumi imnal,
sarkk Maharaz da gimbiya Mulaifa suka ware
waje guda suna cin abincinsu tare, Sadusa tare
384

TASKARNOVELS.COM.NG
da dansa Halyal da gimbiya Shalbirat suma
suka taru akan abinci guda. Ita kuwa Hursiyya
sai ta kasa cin nata abincin, sakamakon cewa
jarumi Hasnalu yaki yaci abincin kuma ya kama
lazimi, kawai sai ta dauki nata abincin taje ta
zauna gefen jarumi Hasnalu ba tare da ya lura
da ita ba. Koda Hursiyya ta danyi motsi sai
Hasnalu ya juyo ya dubeta, da dai yaga ta ajiye
abincin taki ci sai ya cika da mamaki ya dubeta
ya ce me yasa baki ci naki abincin ba? Da jin
wannan tambaya sai gimbiya Hursiyya tayi
murmushi tace ta yaya masoyi zai ji yunwa
alhalin masoyinsa baya ji, ina mai tabbatar
maka da cewa jina da ganina duk sun zama
naka, koda kaya ce idan ta sokeka a halin yanzu
nima sai naji zafin sukar a jikina, idan kaga naci
wani abu yanzu to sai dai idan yare da kai ne.
Sa'ad da jarumi Hasnalu yaji wannan bato sai
nan take yaji kaunar Hursiyya ta baibaye ilahirin
zuciyarsa kai da ransa ma gabadaya har bai san
sa'ad da ya maida mata da martanin murmushi
ba, kawai sai ya juyo ya fusknaceta sosai tare
da tsoma hannunsa cikin abincin dake gabanta
ya fara ci ya ce sa hannu muci tare, domin dai
dana barki da yunwa gwara na kawar da kunya
385

TASKARNOVELS.COM.NG
na saka hannu muci tare tunda a gaban mutane
ne, inda dai mun kadaita ne ba zan yadda na
kusanceki haka ba. Cikin tsananin murna gami
da farin ciki Hursiyya ta sanya hannunta a cikin
abincin ssuka fara ci tare suna masu yi wa
junansu murmushi mai nuna tsantsar so da
kauna. Bayan kowa ya gama kimtsawa ne sai
jarumi Hasnalu ya dubi gabadaya abokan
tafiyyar ya ce yanzu ina so kuyi mani affuwa mu
fara zuwa birnin su gimbiya shalbirat, domin ita
ce wacce aka raba da mahaifarta da iyayenta
tun tana da shekara bakwai, kuma ita ce take
da burin sake saduwa da mahaifiyarta idan har
tana raye. Koda jin haka sai kowa yayi kabbara
aka kuma aminci da wannan magana ta jarumi
Hasnalu, nan take kowa ya mike tsaye aka hau
kimtsawa, bayan kowa ya gama ne jarumi
Hasnalu ya shige gaba tare da falfalawa da
gudu yana mai karanta wasu Addu'o'i na
musamman a cikin zuciyarsa. Hakika Allah
shine mai yin yadda ya so, kuma shine mai
kunfa yakun, da yace kasance sai kawai abu ya
kasance take. A cikin rabin sa'a su jarumi
Hasnalu suka shafe tafiyar watanni tara, sai
gasu a kofar gidan sarautar gimbiya shalbirat,
386

TASKARNOVELS.COM.NG
duk da cewa an sauya tsarin fasalin gidan kama
daga katanga, da sauransu, kuma an kawata
gidan ainun ba kamar yadda yake a da ba
tsawon shekaru shekaru goma sha tara baya,
sai da gimbiya Shalbirat ta shaida gidan
sarautar, ta tabbatar da cewa nan gidansu ne.
Koda masu tsaron kofar gidan sarautar suka ga
su jarumi Hasnalu tsulum a gabansu kamar
aljanu, kuma basu ga ta inda suka taho ba,
sannan basuga durarsu daga sama ba, sai suka
kamu da tsananin tsoro jikinsu ya kama tsuma,
kafin su jarumi Hasnalu suyi magana an bude
masu kofa sun kunna kai ciki. Shalbirat ce ta yi
masu jagora wato ta wuce gaba su kuma suna
biye da ita a baya haka suka nufi fada kai tsaye.
Duk inda suk wuce sai dai kaga dakaru,bayi,
barori da kuyangin gidan sarautar suna ratsawa
gami da basu hanya, a haka har suka isa cikin
fadar inda suka iske Sarauniya Juzairat bisa
karagar mulki, koda Shalbirat ta kura mata
idanu sai ta shaidata, domin ita ce ta ci amanar
mahaifinta ta kawar dashi daga kan mulki, ta sa
masa cutar ajali, kuma itace tasa aljani
Raugatul Agwanu ya saceta ya kaita can dajin
darul hushushul maut. A wannan lokaci fadar
387

TASKARNOVELS.COM.NG
ta cika makil da fadawa da mutanen gari,
amman koda aka hango su jarumi Hasnalu sun
durfafi karagar mulki, sai fadawa da dakaru
suka kama mikewa tsaye suna masu ja da baya
cikin matukar tsoro da razana, ya zamana cewa
wannan sarauniya dake kan kujerar mulki
idanunta sun zazzaro, kuma ita jikinta na tsuma
kamar ace kyet ta fida da gudu. Gimbiya
shalbirat ta cigaba da tunkarar sarauniya, su
jarumi Hasnalu na take mata baya, a haka har
sai da suka iso daf da ita, yadda ita da Shalbirat
suna iya jin numfashin
End Ads