x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - MAZAN JIYA 4

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 68055 words

Category: Adventure Stories

Views 185

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
gabadayan Nahiyar.
Al'amarin Jarumi Shaddadu kuwa, lokacin da
wannan ma'aikaciyar gidan abinci ta ja shi suka
shiga cikin wannan lungu, sai suka yi ta wuce
gidaje har sai da suka je karshen lungun sannan
ta shige da shi izuwa cikin wani gida. Sai da ta
sa mukulli sannan ta bude gidan, suna shiga, ta
mai da kofar ta rufe. A cikin wani dan karamin
falo Shaddadu ya tsinci kansa mai dauke da
daki guda daya jal, sai kuma bandaki. Saboda
rashin yarda sai da Shadaddu ya leka cikin
dakin da bandakin ya tabbatar da babu kowa a
ciki sannan ya dawo ya zauna a falon. A
sannan ne matar wadda shekarunta ba za su
haura talatin da biyar ba, mai kyan diri da fuska
ta dube shi ta yi dariya ta ce. "Kana zaton za a
hada baki ne da ni a cuce ka? To ka sani cewa ni
karuwa ce, kudi ne kawai a gabana. In dai za ka
biya ni zan ci gaba da rufa maka asiri har izuwa
lokacin da za ka bar garin nan". Kafin
Shaddadu ya budi baki ya ce wani abu sai suka
jiyo an shigo lungun da gudu kuma alamar
mutane ne da yawa suka shigo.Cikin sauri
192

TASKARNOVELS.COM.NG
matar ta mike tsaye ta ruga izuwa bakin taga ta
yaye labule ta leka. Da sauri ta saki labulen
kofar la ruga izuwa wajen Shaddadu a gigice ta
ce, "Zo mu je na boye ka, Sarauniya ce da kanta
ta fito nemanka". Shaddadu ya dubi matar
cikin alamun matukar mamaki ya ce, "Akan me
za ki бoye ni an gaya miki ni ina shakkar wani
ne? Ki bari Sarauniyar taku ta shigo har nan ki
ga yadda za mu wanye." Matar ta dubi
Shaddadu kamar za ta yi kuka ta ce, "Ni dai ka
rufa mini asiri idan Sarauniya ta zo ta ganka
anan gidana kashe ni za ta yi". Koda jin haka
sai jikin Shaddadu yai sanyi. Ba tare da gardama
ba kuwa ya bi ta suka shige cikin wannan dakin
barci nata da sauri. Suna shiga sai ya ga ta
yaye dardumar dakin, ta daga wata kofar katako
sai ga matattakala izuwa cikin gidan kasa.
Matar ta dubi Shaddadu ta ce, "Shiga nan ka yi
zamanka". Cikin sauri Shaddadu ya shige cikin
gidan kasan, sannan ta mai da kofar ta rufe
sanna dardumar. Faruwar hakan ke da wuya
sai ta ji ana, bubbuga ma ta kofar gida. A guje ta
je ta bude, Sarauniya Zubaina ta gani tsaye a
gabanta cikin gagarumar shigar Yaki, ga wasu
manyan Dakarunta su goma suna take mata
193

TASKARNOVELS.COM.NG
baya. Zubaina ta dubi matar da kyau a cikin
nutsuwa ta ce, "Ya ke YALDISA ina wannan
bakon saurayi?" Yaldiṣa ta risina cikin
girmamawa ta ce, "Ya Shugabata, rabo na da
bakon saurayi tun da muka fito tare daga gidan
abinci ya tambaye ni hanyar kasuwa na nuna
masa anan muka rabu". Koda jin wannan batu
sai Sarauniya Zubaina ta yi murmushi mai nuna
alamun rashin yarda sannan ta hankade Yaldisa
ta fadi gefe guda. Kai tsaye Zubaina da
Dakarunta suka kunna kai izuwa cikin falon.
Sarauniya Zubaina ta zauna akan kujera sannan
ta umarci Dakarunta da su caje ko ina na gidan.
Lokacin da Yaldisa ta taso ta zo gaban Zubaina
ta durkusa tana mai sunkui da kanta kas ba tare
da ta nuna wata alama ta tsoro ba ko rashin
gaskiya. Zubaina ta sake duban Yaldisa ta yi
murmushi a karo na biyu sannan ta ce, "Ya ke
Yaldisa yau shekara bakwai ke nan kina aiki a
karkashina. Na san dukkan halayenki, ke
karuwa ce wadda in dai za ta sami kudi babu
abin da ba za ta iya yi ba. Ki gaya mini gaskiya
tun kafin lokaci ya kure miki. Idan na gano cewa
kina da hannu akan ɓoye wannan bako daga
baya, kin san halina, ba sani ba sabo. Ban san
194

TASKARNOVELS.COM.NG
tausayi ba kuma ban san hakuri ba, kashe ki zan
yi kawai". Yaldisa ta dago kai ta dubi Zubaina
ta ce, Ya Shugabata tsawon shekaru bakwan da
nake aiki a tare da ke ban taba yi miki karya ba,
wannan ya isa ki aminta da ni. Zubaina ta
jinjina kai gami da ajiyar zuciya ta ce, tabbas
abin da kika fada gaskiya ne, amma ai a wajenki
kudi su ne gaba da komai. Ni na abbatar da
cewa za ki iya siyar da iyayenki ma muddin za ki
sami kudi. Gama fadin hakan ke da wuya sai
ga Dakarun Zubaina sun dawo gabanta.
Shugabansu wanda ake kira SADAR ya risina ce,
"Ranki ya daɗe, babu kowa a cikin gidan nan".
Koda jin haka sai Zubaina ta mike tsaye ta nufi
bakin kofa, Dakarun nata na biye da ita. Har ta
sa kafarta guda a waje sai ta juyo ta dubi Yaldisa
ta ce. "A ko yaushe za mu iya kawo ziyarar
bazato, Kar ki manta hukuncin kisa ne a kanki
idan na kama ki da laifin boye mai laifi". Gama
fadin hakan ke da wuya sai Sarauniya Zubaina
da Dakarunta suka fice daga cikin gidan.
Yaldisa ta mai da Rofar ta rufe sannan ta jingina
bayanta a jikin kofar tana mai yin doguwar ajiyar
numfashi cikin tsananin tsoro. Ba ta matsa
daga inda take tsaye a jikin Rofar ba sai bayan
195

TASKARNOVELS.COM.NG
lokaci mai tsawo bayan ta tabbar da cewa su
Sarauniya Zubaina ba sa kusa sannan ta nufi
dakin barcin nata. Tana shiga sai ta iske
Shaddadu a kwance akan gadonta har ma ya
kama barci abinsa tamkar ba shi aka zo nema
ba. Cikin fushi ta girgiza gadon, Shaddadu ya
mike zaune ya dube ta cikin mamaki ya ce,
"Lafiya za ki katse mini barcina alhalin a cikin
gajiyar tafiya nake?" Koda jin haka sai Yaldisa
ta sake fusata ta ce, "Au! Kai ta barci ma kake
ba ta raina ba? To tsaya ka ji, ga kudinka da ka
ba ni, ba zan iya siyar da rayuwata ba a kan
dirhami ashirin kacal da ka ba ni". Koda jin
haka sai Shaddadu ya yi murmushi, nan take ya
janyo jakar guzurinsa ya bude ya sake debo
dirhami ashirin ya mikawa Yaldisa ya ce, ga
wannan ki kara. Ni dai ki kyale ni na yi barcina.
Yaldisa ta tankwaɓe hannun Shaddadu dinaren
ya zube kasa ta yı masa tsawa ta ce, "Ran nawa
zan siyar maka akan dinare arba'in? Ka ga ni ba
na bukatar kudinka kawai ka tashi ka bar mini
gida don ba za ka janyo mini hukuncin kisa ba a
banza". Maimakon Shaddadu ya yi fishi sai ya
yi dariya kuma ya dauko kullin dinarensa
gabadaya ya cilla wa Yaldisa ta cafe ya ce.
196

TASKARNOVELS.COM.NG
"Gashi nan gabadayan abin da na mallaka ke
nan in kin so ki kyale ni na kwana. Na yi miki
alkawarin babu abin da zai taɓa lafiyarki koda
asirinki ya tonu, kuma gobe da safe zan bar miki
gidanki". Koda gama fadin hakan sai
Shaddadu ya koma ya kwanta akan gadon yana
mai juya mata baya. Kafin cikar dakika dari da
ashirin ya fara munshari. Al'amarin da yai
matukar bai wa Yaldisa mamaki ke nan kuma ya
ba ta dariya. Nan dai ta sunkuya ta tsince
ragowar wannan dinaren da ya zube kasa ta
zuba a cikin kullin wanda aka ba ta ta boye,
sannan ta je ta ci gaba da dan aiyukanta na
gida. Har dare ya yi Shaddadu bai farka daga
barci ba. Lokacin da Yaldisa ta ji ta soma jin
barci har ma tana gyangyadi daga zaune sai
hankalinta ya tashi domin dama can tsoro ne ya
hanata zuwa ta kwanta, saboda tana ganin
cewa a kodayaushe Dakarun Sarauniya Zubaina
za su iya kawo ziyarar bazato. Da dai ta ga tana
jin barcin sosai sai ta mike tsaye ta nufi cikin
dakin barcin. Tana shiga ta ga har a sannan
Shaddadu barci yake yi. Koda ta kura masa
idanu ta dube shi sama da kasa ta ga irin
tsananin kyawun fuskarsa da kyawun surar
197

TASKARNOVELS.COM.NG
jikinsa, sai nan take ta ji ta kamu da tsananin
sha'awarsa. Sai a sannan ne ta gane cewa
ashe da can tsoro ne ya sa ta kasa yi masa
kallon nutsuwa bare ta san cewa kyakkyawa ne.
Nan dai Yaldisa ta kautar da tsoro ta cire tufafin
jikinta ta sanya na barci sannan ta kwanta a
bayan Shaddadu. Koda ta kai hannu ta tabo
Shaddadu sai ya mike zumbur! A fusace ya
dube ta ya daka mata tsawa da karfi. Yaldisa
ta razana ainun har sai da hantar cikinta ta
kada. Shaddadu ya ce. "Na gaya miki ba na
bukatar mace a kusa da ni. Ki sauka daga kan
gadon nan tunda dai biyanki na yi kudin komai a
gidan nan". Cikin alamun tsananin mamaki
Yaldisa ta sauka daga kan gadon ta dauki
matashin kai guda daya ta dawo falo ta kwanta
a kasa. Nan fa Yaldisa ta ci gaba da mamakin
wannan bakon saurayi har barci ya sace ta ba ta
sani ba. SHADDADU FA YANA DA GASKIYA.
DOMIN KOMAI TUMBATSAR SADAUKI MATUKAR
YA HADA SHAGALA DA MACE SAI AN YI
NASARA A KANSA. SADAUKI HANTARU IZINA A
GARE MU. Lokacin da gari ya waye sai Yaldisa
ta ji ana tashinta daga barci. Koda ta farka ta
bude idanuntasai ta yi arba da wata mace
198

TASKARNOVELS.COM.NG
tsohuwa tukuf! Zaune gabanta. Cikin alamun
tsananin tsoro ta mike zumbur! Ta koma jikin
bango ta takure jikinta tana mai kallon tsohuwar
a firgice ta ce, "Wace ce ke kuma yaya aka yi
kika shigo gidan nan? Shin kin samu wani ban
da ni a cikin gidan nan ne?" Koda jin wannan
tambaya sai tsohuwar ta bushe da dariya, nan
take ta rikide ta zama Shaddadu. Mamaki ya
sake kama Yaldisa ta ce, "Ashe ma kai ne?
Mene ne dalilin da ya sa ka rikide izuwa siffar
wannan tsohuwa". Shaddadu ya yi ďan guntun
murmushi a gare ta sannan ya ce, "Ai jiya bayan
kin yi barci ya yin dà dare ya raba sai na tashi na
rikide izuwa siffar wannan tsohuwa na ci gaba
da barcina. Faruwar hakan ke da wuya kuwa sai
ga wadansu hadimai na Sarauniyarku sun shigo
cikin gidan nan da karfin sihirin tsafi, suka kama
bincike. Koda suka shigo cikin dakin barcinki
sai suka ga tsohuwa akan gadonki tana shara
barci har da munshari, sai suka juya suka fice
daga gidan gabadaya. Wannan shi ne dalilin
da ya sa na sauya kamannina don kada a zo a
gan ni na shafa miki kashin kaji. Sa'adda
Shaddadu ya zo nan a zancensa sai Yaldisa ta
cika da tsananin mamaki da murna. Shaddadu
199

TASKARNOVELS.COM.NG
ya dube ta ya ce, to ni yanzu nan zan tafi neman
abin da ya kawo ni garin nan don haka sai dai na
yi miki bankwana. Yana gama fadin hakan sai
ya koma cikin dakin da yai barci ya dauko
Mashinsa na GALILUL HARAS wanda ya rataye
shi a jikin bango sannan ya dauko karamin
Tsuntsun nan nasa na tsafi ya dora shi akan
kafadarsa. Koda ya fito falo Yaldisa ta yi arba
da Mashin da kuma wannan Tsuntsu sai ta dube
shi cikin mamaki ta ce, "Yaushe kuma ka sami
wanna Mashin da wannan Tsuntsun? Ni dai a
sanina jiya ba ka tare da su". Koda jin wannan
tambaya sai Shaddadu ya yi murmushi ya ce,
"Ai babu mai ikon ganin wadannan abubuwa
nawa face da amincewata." Yana gama fadin
hakan sai ya sake rikidewa ya zama wannan
tsohuwa wacce saboda tsananin tsufa sai da ta
rankwafa ta yi doro. Shi ma Mashin Galilul
Haras sai ya rikide ya zama sanda. Tsohuwar ta
dogara sandar ta nufi bakin kofa za ta fita, sai
Yaldisa ta ruga ta sha gabanta ta ce, "Haba ya
kai bako, yaya za ka kwana a gidana na ba ka
abinci kuma na ba ka makwanci duk da dai siya
ka yi amma za ka tafi ban san koda sunanka ba?
Ka yi sani cewa ina da wadansu 'yan tambayoyi
200

TASKARNOVELS.COM.NG
guda uku rak a gare ka wadanda na ke son
amsarsu kafin mu rabu.Tambayata ta farko ita
ce, Mene ne dalilin da ya sa kake neman wata
Jaruma mai suna ZIYA'UL HAK? Tambaya ta
biyu, ina son na sani idan kai namiji ne cikakke,
ko kuwa ba ka da lafiya? Tun da na fara
karuwanci ban taba haduwa da namijin da bai yi
sha'awata ba sai kai saboda kyawuna da
kyawun surata. Tambaya ta uku ita ce, Yaushe
za ka bar wannan garin namu?" Sa'adda
Shaddadu ya ji wadannan tambayoyi sai ya yi
murmushi mai taushi ga Yaldisa ya ce, Game da
tambayarki ta farko, amsarta ita ce, ina neman
Jaruma Ziya'ul Hak ne saboda ta kásance
babbar abokiyar gabata a duniya, muddin zan yi
arba da ita sai na hallaka ta. Amsar
tambayarki ta biyu kuwa, ni namiji ne cikakke
mai lafiya, amma mahaifiyata ta cire mini
sha'awar 'ya mace da karfin sihiri, kuma ta hore
ni da kaidinku tun ina karami don haka, a
rayuwata babu abinda na tsana kuma nake
tsoro sama da mata. Game da amsar
tambayarki ta karshe ita ce ba zan bar wannan
gari naku ba har sai na tabbatar da cewa
abokiyar gabata Jaruma Ziya'ul Hak ba ta
201

TASKARNOVELS.COM.NG
cikinsa. Na barki lafiya sai watarana idan da
rabon mu sake saduwa. Koda gama fadin
hakan sai tsohuwar ta je ta bude kofa ta fice
daga cikin gidan. Ita kuwa Yaldisa sai ta ji ta
kamu da tsananin damuwa da bakin ciki tamkar
wacce ta rabu da wani dan uwata shakikinta
kuma rabuwa ta har abada wacce ba za a sake
saduwa ba. Kawai sai Yaldisa ta ji idanunta
sun ciko da kwalla har hawaye ya subuto ma ta.
A sannan ne ta gane cewa lallai ta kamu da son
Shaddadu ne, kuma a sannan ne ta tuna cewa
ai bai gaya mata sunansa ba. Nan take Yaldisa
ta ruga da gudu izuwa kofar gida. Tana fita ta
dubi gabas da yamma, kudu da arewa amma ba
tá ga alamar Shaddadu ba, ya 6ace ɓat! Tamkar
daukewar ruwan sama, kawai sai ta yi ajiyar
zuciya ta juyo ta koma cikin gidants zuciyarta na
cike da damuwa da takaici. (KE YALDISA. AI
WUTSIYAR RAKUMI TA YI NESA DA KASA) ****
Lokacin da Shaddadu ya fito daga cikin gidan
karuwa Yaldisa a cikin siffar wannan tsohuwa
yana dogara sanda sai yai tsafi wani dan koko
ya bayyana a hannunsa. Nan take ya kunna kai
izuwa cikin gari yana bara tamkar tsohuwa ce
mai neman abin da za ta ci. Sai da ya shafe sa'a
202

TASKARNOVELS.COM.NG
guda yana yawon bara bai hadu da wanda ya ba
shi koda ruwan sha ba bare abinci ko durhami
guda. Al'amarın da ya ba shi mamaki ke nan,
duk da cewar shi rayuwarsa a can Birnin Kufa
bai taba yin bara ba asali ma a gidan Sarauta ya
taso cikin gata amma ai ya san cewa mutanen
gari suna taimakon Almajirai. Abin da bai sani
ba shi ne, game da al'adar mutanen wannan
gari ba a yin bara a ko ina sai dai Almajiri ya je ya
sami wuri a bakin hanya ya zauna ya yi bararsa
in yaso masu wucewa mai niya ya ba shi.
Shaddadu na cikin yawon barar tasa ne ya
hango Almajirai a gefen hanya kimanin su goma
maza da mata a zaune sun yi layi mutane masu
wucewa suna ta ba su sadaka. Cikin murna
Shaddadu ya karasa inda Almajiran suke a cikin
siffarsa ta tsohuwa tukuf gami da dogara sanda
da kyar. Yana isa gare su sai ya tsaya ya fara
kokarin zama kusa da wani tsoho wanda ya fi
shi tsufa nesa ba kusa ba. Amma bisa mamaki
sai ya ga tsohon ya mike da sauri cikin
kuzarinsa tamkar ba tsohon ba ya taimaka
masa ya zaunar da shi kuma ya mika masa
sandarsa ya rike. A sannan ne suka dubi juna
cikin murmushi sai tsohon ya dubi tsohuwar ya
203

TASKARNOVELS.COM.NG
ce, "Ya ke wannan almajira in ce ko ke bakuwa
ce a garin nan? Na ga kina bara akan hanya
alhalin ba haka dabi'ar g garin nan take ba?"
Koda jin wannan tambaya sai Shaddadu ya ji bai
amince da wannan tsoho ba don haka sai ya
ɓoye masa gaskiyar al'amari ya ce, "A'a ni ba
bakuwa ba ce a wannan gari amma dai daga
kauye na zo nan. Wannan ne dai karon farko da
na fara yin bara anan. Koda jin haka sai tsohon
ya sake yin murmushi ya ce, "To ai a nan ba a
yin bara a ko ina sai a gefen hanya don haka sai
ki kula saboda gaba". Da jin haka sai tsohuwar
ta maidawa tsohon martanin murmushi kuma
ta yi masa godiya. A daidai wannan lokaci ne
suka hango Sarauniya Zubaina ta tunkaro su
bisa doki tare da Dakarunta su ma bisa dawakai
kimanin su dari biyu. Da isowar Sarauniya
Zubaina gaban Almajiran sai ta sauko daga kan
dokinta ta shiga rabawa Almajiran sadakar
dirhami guda-guda. Duk wanda ta zo kansa sai
ta kura masa idanu ta yi wani surkullenta na
tsafi domin ta gano akwai bakon saurayin nan a
cikinsu wanda ya karya dokarta ya shigo gari ba
izini ya ɓalla kofar garin kuma ya yi wa Dakaru
duka. Haka dai Sarauniya Zubaina ta ci gaba da
204

TASKARNOVELS.COM.NG
bai wa almajiran sadaka har ta zo kan wannan
tsoho wanda ya taimaki tsohuwa. Da zuwanta
kan tsohon sai ta tsaya cak! Ta dade tana
kallonsa kuma tana surkullenta a kansa har sai
da gumi ya tsattsafo mata amma ba ta gano
komai ba. A sannan ne ta yi ajiyar numfashi ta
dubi tsohon ta ce, "Ya kai wannan almajiri shin
ba ka ga wani bakon saurayi ba a cikin garin nan
wanda ya shigo mini gari ba izini kuma ya balla
mini kofa?" Dattijon ya gyada kai ya ce, "Ban
gan shi ba amma dai na ji ana zanċensa a cikin
nan kuma da zarar na gan shi zan gaggauta
zuwa fada na sanar". Koda jin haka sai
Sarauniya ta yi murmushi sannan ta matsa gaba
wajen tsohuwar ta ba ta sadaka tana mai kura
mata idanu gami da yin Wannan surkulle. Ai
kuwa sai da ta ɓata lokaci fiye da sa'adda ta
tsaya a gaban wannan tsoho har ya zamana
cewa ta jike sharkaf da gumi. Sarauniya
Zubaina ta sa hannu ta share guminta tana mai
ajiyar zuciya sannan ta dubi tsohuwar ta ce. "Ya
ke wannan almajirila yaushe ki ka zo garin nan?
Tabbas ban taba ganinki a cikin wannan birnin
ba. Koda jin wannan tambaya sai tsohon
almajirin ya tari numfashin tsohuwar almajirar
205

TASKARNOVELS.COM.NG
ya ce, "Ai wannan Almajirar bakuwa ce daga
kauyen LAIRUF, ba ta ma saba yin bara a nan
ba. Dazun nan muka hango ta tana yin bara a
cikin gari sai da ta zo nan muka yi mata bayanin
al'adar garin nan". Sa'adda Sarauniya Zubaina
ta ji wannan batu sai ta sake yin ajiyar zuciya
sannan ta mike ta dubi Almajiran da ke zaune a
wajen gaba dayansu ta ce "Duk sa'adda
dayanku ya ga wani bakon Jarumi saurayi ya
hanzarta zuwa fada ya sanar da ni, zan ba shi
lada na adadin dukiyar da har ya mutu ba zai iya
cinyewa ba". Koda jin wannan batu sai
gabadayan Almajiran suka kama shewa suna yi
wa kansu fatan su dace da samun wannan lada.
Nan dai Sarauniya Zubaina ta je ta kama
dokinta ta hau ta wuce gaba Dakarunta na take
mata baya. A lokacin ne wata rundunar daban
ta Dakarun Sarauniya Zubaina suka shigo cikin
garin suka barbazu a ko ina lungu-lungu, sakosako suna neman bakon Jarumi. Koda wannan
tsohon Almajirin ya hango abin da ke faruwa sai
ya dubi tsohuwar Almajirar ya ce, "Kai al'amarin
nan da ban mamaki yake. To wai shin shi
wannan bakon Jarumi wane irin hatsabibi ne
haka? Tun jiya ake nemansa a garin nan amma
206

TASKARNOVELS.COM.NG
an rasa inda yake. Anya kuwa shi ma bai
kasance hatsabibin matsafi ba?" Koda jin haka
sai tsohuwar ta ce, "Ai kai ma ka san ruwa ba ya
tsami banza. Duk yadda aka yi wannan bakon
Jarumi shi ma ya taka babban matsayi a tsafi da
jarumtaka, in ba don haka ba da tuni Sarauniyar
garin nan ta kamo shi tunda na ji an ce ita ma
shahararriyar matsafiya ce kuma Jaruma".
Tsohon Almajirin ya gyada kai sannan ya ce.
"Tabbas zancenki dutse ne. Yanzu dai ga shi
mun sami babbar dama bisa tayin da Sarauniya
ta yi mana. Ya
End Ads