labewa na kara kunnenaa
ina sauraron abin da yake fada amma ban sami
ikon haddace kalmoin ba sai a ranar nan da
kayi laifi aka bankareka a saa aka yi maka
wannan mummunana hukunci
A ranar ne na bude akwatin sarki naga tarihirin
A ranar ne na bude akwatin sarki naga tarihin
alakarsa da mahafinka kuma naga wani babban
sirri wanda bazan iya gaya makashi yanzuba
saidai a bayan wannan yaki idan muna raye
lokacin da Gimbiya mulaifa tazo nan a
zancenta sai jarumi inmal ya cika da tsananin
mamaki yai shuru yana mai kallonta cikin
mamaki
: kada ganin haka sai tayi masa murmushi
sannan ta kwanta yana mai dora kanra akan
cinyanta domin ta dada huta gajiyar yaki
93
TASKARNOVELS.COM.NG
WANNAN SHINE ABIN DA YA FARU A
SANSANIN YAKI NA BAKIN TEKUN BAHAR
SUFIYA BAYAN AN FAFATA KAZAMIN
MASIFAFFEN YAKI A KARO NA UKU
* * ¥ A CaN Birnin sarki dujalu kuwa karshe
gari da sassafe tun kafin alfirjir ya keto boka
sadusa yayi shirin tafiya wata nahiyar dabam
domin neman aljanin da zai aika can bakin
kogin bahar sufiya a matsayin dan leken a sirin
wanda zai gano musu halin da ake ciki
: boka sadusa yanada matar aure guda daya
wata kyakkyawar mace wadda ake kiraa
Hunaisa sai kuma da Guda daya wani karamin
yaro dan kimanin shekara bakwai 7 wanda ya
kasance kyakkyawa kuma allah ya hore masa
basira hikima da sauran fahimtar al amari har
da hasashen abin da ka iya faruwa a gaba.
Allah ya jarrabi boka sadusa da matukar son
wannan da nasu mai suna HALYAL kuma sun
shaku matuka yadda ko kadan basa son
rabuwa da juna dai dai da kwana daya: Wani
94
TASKARNOVELS.COM.NG
abin mamaki shi ne babu yadda boka sadusa
bai yi ba akan ya koyawa halyal ilimin tsafi
amma ko kadan shi Halyal bashi da ra ayin ya
gaji ubansa a wannan bangare
Shi dai Halyal bashi da wani buri a rayuwarsa
wanda yafi ya halarci yaki koda sau daya ne a
rayuwarsa amma sadusa ya hanashi: babu irin
rokin da Halyal bai yiwa Sadusa ba akan ya
kyaleshi ya tafi izuwa bakin kogon bahar sufiya
domin ya gawannan gagarumin yaki wanda yayi
Hasashen akana cewar yaki ne wanda ba a
taba yin kamarsa ba a duniya kuma ba a zaton
za ayi anan babban burin Halyal shine ya ga
jarumtaka a fili yadda maza ke dakawa maza
gumba a hannu kuma shima yana son anan
gaba ya zama gawurtaccen jarumi wanda zai
shahara a duniy ammma da yake ra ayinsa ya
sha bamban da na mahafinsa bai taba samun
damar koyon yaki ba sannan kuma ko kadan
bashi da wata jarumtaka ko sadaukantaka a
jikinsa al aarin da yasan asa bakin ciki da
takaici kenan a cikin zuciyarsa. bayan sadusa
ya gama shiri tsaf Ya sanya tufafinsa kua ya
95
TASKARNOVELS.COM.NG
dauko jakar guzurinsa sai ya shiga cikin turakar
matarsa Hunaisa domin ya yi musu sallaa: ita
kadau a zuane tana kalaci
Cikin mamaki ya dubeta yace ina Halyal yake?
Koda jin wannan tamabaya sai itaa ta dubeshi
cikin mamaki tace ai yau halya ya rigani tashi
ma: Tun dazu yai wanka ya kitsa har ya dauki
jakarsa ta tafiya don ya shaida mini cewa
xakuyi wannan tambaya: Koda jin haka sai boka
sadusa ya murtuke fuska ya ce aa ni bamuyi
haka da shi ba kuma ba zan yarda nayi wannan
tafiyar mai hadari ba da shi: wai shin ma yanzu
ina Halyal din yake?? Hunaisa ta ce yana can
kofar gida ya jiranka: Ni dai ina rokinka da
girman tsofafinka ka amince masa kuyi wannan
tafiya ..... Ni dai ina rokinka da girman
tsofafinka ka amince masa kuyi wannan tafiya
: Tare domin kuwa ya kwallafa ransa gaba daya
akanta sbda yana gani cewa wannan ce kadai
damar da yake da ita da zaije sansanin yaki
yaga yadda ake zubar da jarumtaka tunda ka
96
TASKARNOVELS.COM.NG
gaya mana cewa zaka tafi neman aljanin da
zaka tura bakin tekun bahar sufiya ne. Sa'adda
Hunaisa tazo nan a zancenta sai hankali boka
sadusa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe
kuma yaji ya kamu da tausayin Halyal amma da
ta tuna irin mugun hadarin dake cikin wannan
tafiya sai zuciyarsa ta bushe kuma ta kekashe
ga barin jin tausayin
Sadusa ya dubi Husnaila yace ki yi hkri ya ke
matata ba zan biyawa Halyal bukatarsa ba
domin yin hakan dai dai yake da na turashi
izuwa FARAUTAR AJALINSA sakamakon hadarin
dake cikin wannan tafiya: kin fi kowa sannin
halina idan na yi magana bana sauya ra ayi. Da
wannan furuci nake yi miki sallama sai na
dawo: Ina sa ran zansamu aljanin dazan tafi
nema a cikin kwana uku amma ban sani ba ko
aljanin zai tafi tare dani ne izuwa can kogin
bahar sufiya ko kuma shi kadai zai tafi
Duk dai halin da nake ciki zn aiko miki da
wasika ta hannun tsuntsuna
97
TASKARNOVELS.COM.NG
ko da gama fadin haka sai boka sadusa ya juya
ya fice daga cikin turakar a lokacin da Hunaisa
ta biyo bayansa da sauri idanunta cike da
kwalla wahaye na shirin zubowa sbd tausayin
danta halyal bisa bakin cikin da zai shiga idan
aka ki tafiya dashi
Hayal na zaune a gindin wata bishiya dake
kofar gidansu ga jakarsa ta guzuri rataye a
kafadarsa. Yana wasa da tarin wadansu
tsakuwoyi da ke gabansa sai kawai ya hango
mahaifinsa da mahaifinyarsa sun fito daga cikin
gida sauri
Koda halyal yayi arba da fuskar mahaifinsa ya
ga ko kadan babu annuri a cikinta sai
hankalinsa ya dugunzuma kuma jikinsa ya
bashi cewar lallai mahaifin nasa bazai amince
yayi wannan tafiya ba dashi ba
98
TASKARNOVELS.COM.NG
Ya yin da sadusa ya matso daf da halyal sai
halyal ya mike tsaye cikin sanyin jiki gami da
karayar zuciya
: Koda sadusa ya yi kwallah a cikin idanun
halyal sai nan take shima ya kamu da
tausayinsa halyal ya dubeshi cikin yanayin
damuwa yace ya kai dana na sani cewa a yau
ne ranar da kake da damar cika babban burinka
na duniya amma kada kamanta cewa ni da
mahaifiyarka muna sonka fiye da komai a cikin
wanan duniya, don haka lallai bama son abinda
zai rabau da kai tunda kai kadai ne damu. Taya
yaya kake tsammmanin cewa nida kaina zan
daukeka na tafi da kai izuwa hallaka? Ina so ka
sani cewa a halin yanzu zan yi wannan tafiya ne
izuwa wata nahiyar dabam wacce ban san
sirrin dazukantaba kuma ban san irin mugayen
abubuwn da zan riska ba a cikinta kafin na sami
aljanin da nake nema. Bubu mamaki mana rasa
rayuwata a wanan tafarki ka ga kenan idan na
tafi tare da kai mahaifiyarka zata yi rashi biyu.
Babu miji kuma babu da yaya kake zaton
rayuwarta za ta kasance idan babu mu a doron
99
TASKARNOVELS.COM.NG
kasa?? Lokacin da boka sadusa yazo nan
azancensa jikin halyal yayi sanyi ainun ta
sunkui da kansa kamar ya hakura daga can
kuma sai ya dago kai ya dubeshi ya ce Yakai
abbana shin ka manta ne cewar ka taba
gayamini cewar bisa binciken da kayi a hallarar
tsafinka ajali ba zau taba riskar daya daga
cikinmu ba a wani wuri face a gida?? Ashe
kenan duk irin gararin da zamu shiga zamu
dawo gida a raye? Lokacin da boka sadusa ya
jin wannan batu sai ya sunkuo da kansa kas
cikin alamun kunya yai shiru yace komai ba, har
izuwa tsawon yan dakiku, sai daga can kuma ya
dago kai ya dubi halyal lokacin da kwalla ta ciko
a cikin kwayar idanunsa ya ce ya kai dana
hakika duk abinda ka fadi gaskiya ne, to amma
kuma ai bana son mu dawo gida a cikin mugun
hali rashin lpyar da zata zama sanadin
ajalinmuka hkri bazan iya yin wannan tafiya ba
tare da kai. koda jin haka sai halyal ya durkushe
kasa yana mai fashewa da kuka. al amarin
daya kara jefa sadusa da Hunaisa cikin
tsananin tausayinsa kenan. Nan dai sadusa ya
kama kadadun halyal ya tasoshi tsaye ya
sumbaci goshinsa sannan ya rungumeshi a
100
TASKARNOVELS.COM.NG
kirjinsa duk su biyun suka fashe da kuka a
lokacin guda.
Zan ci gaba.
MAZAN JIYA
Littafi na Hudu 4
Part J
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
Koda ganin haka sai itama hunaisa ta rugo
garesu ta kankamesu su ukun ta tayasu kukan
sadusa ya janye jikinsa daga cikin nasu ya tafi
yana waigensu hawaye na zuba daga
idaanunsa.
Al amarin daya kara dugunzuma hankali halyal
da Hunaisa kenan suka ci gaba da matsanaicin
101
TASKARNOVELS.COM.NG
kuka suna hangen sadusa har sau da ya bace
musu da gani.
Nan fa Halyal da Hunaisa suka cigaba da kuka
suna kankame juna kamar bazasu daina ba har
izuwa tsawon kusan dakika daru biyu da sittin.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka jiyo
takun sawu a yayin da kawunansu ke kallon
kasa, cikin sauri suka dago domin su ga wanda
ke zuwa.
Kawai sau suka ga ashe sadusa ne ya dawo
kuma ya tunkarosu hannanyesa a bude hawaye
yana shatata bisa kumatunsa.
Cikin tsananin farin ciki Halyal ya ruga izuwa
gareshi ya dada kan kirjinsa suka rungume juna
suna masu kyalkyala dariya.
* **
Tun da suka fara tafiya daga cikin gari halyal
yafara ganin abubuwan al ajabi bisa yanayin
102
TASKARNOVELS.COM.NG
tafiyar tasu domin da zarar sun yi tafiya kamar
taku goma sai yaga sun shafe nisan zira'i dari
nan da nan suka fice daga cikin gari suka nausa
cikin daji.
Ai kuwa suna shiga daji yaji sadusa ya kama
hannunsa ya rike nan fa ya jashi da gudu suka
falfala da gudu.
Wannan karo sai halyal ya sako cike da
tsananin mamaki fiye da farko domin yanzu
tafiyar sa a guda ce suke shafewa a cikin dakika
sittin kacal sai dai kawai yaga suna gifta
dazuzzuka a cikin matsananincin gudu tamkar
giftawar tauraruwa mai wutsiya.
Amma da ya tuna cewar duk wannan lamari
alamari ne na tsafi sai kawai yayi murmushi
yace
a zuciyarsa kowa da kiwon da ya karbeshi.
Haka dai sadusa da halyal suka cigaba da gudu
a cikin daji babu sassauci.
Tun safe suka fara wannan gudu amma har sai
da rana ta fadi sannan suka tsaya cak a farkon
103
TASKARNOVELS.COM.NG
wani daji mai yanayi iri dabam da na sauran
dukkan dazuzzukan Da suka wuce a baya.
Adai dai wanna lokacin ne ji tsananin gajiya da
kishirwa ta riskesu, ba shiri suka durkushe kasa
bisa guiwoyinsu suka kama haki sannan
kowannensu ya bude butar ruwansa ya
kwankwada, koda suka dawo cikin hayyacinsu
sosai sai suka kama kallon wannan daji da suka
tsinci kansu a cikinsa.
DAJI NE mai dauke da wandansu irin dogayen
bishiyoyi masu tsananin tsawo da ba a iya ganin
karshensu kuma ganyayen bishiyoyin masu fadi
ne sosai don haka su karawa dajin duhu ya
zama abin tsaro.
Sannan kua akwai wadansu irin duwatsu a dajin
masu wani irin sufofki na ban tsaro, wani
dutsen sai kaga yana kama da mutum wani
kamar aljan wasu kuma da dabbobi suke kama,
kai komai dakewar zuciyar mutum idan ya tsinci
kansa a cikin wannan daji sai ya razana
musaman idan ya ji irin tsananin shirun dak
cikin dajin, mutum baya jin sautin komai hatta
na tsuntsaye kuwa aa da zarar mutum ya taka
104
TASKARNOVELS.COM.NG
ganyeye bishiyoyin dajin wadanda suka fado
kasa suka bushe rumus sai kaji karar ta cika
dajin gaba daya hara da amsa kuwwa.
Nan take halyal yakamu da tsananin tsaro gaba
dayan jikinsa ya kama tsuma bai san sa adda
ya dada kankame jikin sadusa ba.
Koda ganin haka sai sadusa yai murmushi yace
saki jikinka ya kai dana kayi sani cewa indai
kana tare dani babu wani tsautsayi da zai
sameka ka sani cewa tun shigo wata sabuwar
nahiyar ne wacce ba tamu ba.
Yanzu kamata yayi mu nemi wuri mai kariya
inda zamu yadda zango tunda duhu ya soma
sannan sai nayi mana bincike na gano ko akwai
abinda muka zo nema a cikin wannan daji.
Koda gama fadin hakan sai suka mike tsaye
suka kara nausawa cikin suna ketawa ta cikin
surkuki duhuwoyi ciyayi da sako sako. Ai kuwa
sai da suka shafe lokaci mai dan tsawo suna
neman wani kogon dutse da zasu iya shiga
cikinsa su fake sakamakon hadarin da yake
barazanar zubar da ruwa a ko yaushe, tunda har
105
TASKARNOVELS.COM.NG
an fara walkoya gami da tsawa mai. ban tsoro,
wacce duk sa adda aka yita sai dai kaga halyal
na dada kankame hannun sadusa.
Abinda ya dada daure masu kai shine duk
tsawin wannan lokaci da suka shafe suna yawo
a cikin dahi ko kadangare basu gani ba.kuma
basu hadu da wani mugun abu ba, shi kansa
sadusa sai daya tambayi kansa a ckin.zuciyarsa
yace,
TO WAI SHIN MENENE YA HANA DABBOBI DA
KWARI RAYUWA A CIKIN WANNAN DAJI???
suna cikin wannan dube dube ne suka hango
wani katon kogon dutse a gabansu, cikin
hanzari suka ruga izuwa bakin kogon a lokacin
da aka fara yayyafi kua aka ci gbada tsala
wakiya da tsawa, da isarsu bakin kogon dutse
sai suka tsaya sadusa ta yi nuni da hannunsa
izuwa cikin kogon, take wani irin haske na tsafi
ya haskake cikin kogon gaba dayansu kofa suka
yi arba da
aabin da ke cikin kogon sai suka cika da
tsananin mamaki, ba komai suka gani ba face
wata yar karama aljanar duniya.
106
TASKARNOVELS.COM.NG
Kaya ne na alatu a cikin kogin tamkar turakar
wani hamshikin basarake. An shimfida dardua
ta alfarma ai dan karen laushe ta rufe
kasankogon gaba daya mai launin shudi.
A gefe daya nan a zncenta sai ta fashe da kuka
al amarin dayai matukar baiwa su sadusa
mamaki kena har suka ji sun kamu da tsananin
tausayinta daga can sau sadusa ya dubeta ya
daka mata tsawa yace yake wannan ma
abokiyar keji: shin yanzu zaki iya iya gaya mana
ko wane ne ya ajiyayeki a wannan kogon dutse
wanda muka ji kin kirashin da shugaban
azzalumai na duniya.
Koda jin haka sai wannan kyakkyawa ta cikin
keji tayi a jiyar zuciya tace sanin wanda ya
ajiyeni acikin wanna kogo dai dai yake da sanin
ranar ajalin mutum domin yakasance
GUGUWAR ANNOBA kuma GOBARA DAGA
KOGI wacce ba da magani:
Sunan wanda ya ajiyeni anan shine ALJANI
RAUGATUL AGUWANU. Koda jin wannan batu
sai boka sadusa ya mike zubur! Cikin firgici da
107
TASKARNOVELS.COM.NG
tsananin tsoro ya kama hannun halyal domin su
fice daga cikin kogon:
Karar takun sawun aljani raugatul aguwanu tasa
suka koma cikin kogon dutse da sauri suka
shige cikin karkashin wanna makeken gado na
aljanin raugatul aguwanu:
Takun sawun na Raugatul aguwanu tamkar
giwaye neke tserun gudu a cikin dajin har maya
haddasa girgizar kasa. Kai tsaye aljani raugatul
aguwanu yashigo cikin kogon nasa tya zauna
kan gefen wanna gado nasa. Kai tsaye aljani
raugatul aguwanu yashigo cikin kogon nasa tya
zauna kan gefen wanna gado nasa.
Saboda nauyinsa sai da gadon ya lotsa kasa
har su sadusa suka ji kamar wani katon dutse
ne ke shirin dannesu ya kakkarya musu
kasusuwan gadon baya. Koda kyakkyawar
yarinyar nan tacikin keji ta ga haka sai ta dubi
Raugatul Aguwanu ta bushe da dariya tace
haba ya shugabana yau kuma wahalar farautar
ce tasa ka manta ka fara zama akan teburinka
kaci yayan itatuwa? Koda jin haka sai aljani
Raugatul Aguwanu ya bushe da dariyar farin
108
TASKARNOVELS.COM.NG
ciki: Kasancewar kyakkyawar yarinyar bata
taba yi masa magana mai dadi ba a tsawon
shekaru da ya ajiyeta a cikin wanan kogon sai
yau. Cikin hanzari ya mike tsaye ya nufi inda
kujerarsa ta zama take wadda ke karkashin
wannan babban zagayayyen tebur. Kafin ya isa
kan kujerar tuni sadusa da Halyal sun fito daga
karkashin gadon sun ruga izuwa bayan tarin
dukiyar zinare sun buya. A Dai Dai wannan
lokaci ne Raugatul Aguwanu ya zauna akan
kujerar. ai kuwa sai ya shaki kamshi bil adama
a cikin kogon fiye da yadda ya saba shaka a
kullum ya tabbatar da cewa yasami baki. Nan
fa ya kama waige waige da dube dube cikinn
kogon. Koda su sadusa suka ga haka sai suka
binne kansu a cikin wannan duniya ta zinare
tamkar basu taba wanzuwa ba a wajen. Hakan
ta faru ne da taimakon karfin sihirin tsafi
sadusa. Aljani Raugatul Aguwanu ya mike tsaye
ya kama dube dube ya shiga nan ya fita can: ya
bankada ko ina amma bai ga bil adama ba
alhalin kuma yaji kamshinsu. Koda ya dago kai
suka hada ido da wanna kyakkyawar yarinya ta
cikin keji sai ta sunkui dakanta kas, abinka
mara gaskiya ko a ruwa sai ya yi jibi sai jikinta
109
TASKARNOVELS.COM.NG
ya kama tsuma. A fusace Raugatul Aguwanu ya
durfafo kejin da take cikin ya dubeta ya daka
mata tsawa yace ke tsohuwar munafuka
tabbas kin san da shigowar baki wannnan kogo
nawa amma sbda munafunci da cin mana irin
naku na mata shine kika yi shiru baki gaya mini
ba. To ki sani cewa idan har baki gaya ini inda
suka buya ba a cikin wannan kogo yanzu nan
zan fito dake daga cikin kejin nan na yayyagaki
filla filla na watsar. Ai daa na ajiyeki ne anan
kawai don ki debe mini kewa kasancewar babu
wata hallita a cikin wannan daji sai ni kadai.
Koda jin wannan batu sai kyakkyawar ta bushe
d dariya lokaci guda kua ta fashe da kuka
sannan ta kalleshi tace ai daa na dade ina
rokonka akan ka kasheni na huta da takai ci da
bakin cikin rayuwar da ka jefani cikin amma
kaki, ka rabani da iyayena dangina da kasarmu
ka baroni da cikin jinsin mutane yan uwana ka
kawoni nan cikin wannan daji inda ko kwaro
babu bare wani dan tsuntsu wanda zai rinka jin
sautin kukansa ina jin dd cewar akwai mai rai a
kusa dani
110
TASKARNOVELS.COM.NG
Tun inayarinya karaa ka sato ni ka kawoni nan
kuma ka tsafanceni ka sani a cikin wanna keji
na zama kamar ya tsuntsuwa alhalin na
kasance bil adama. Ka cuceni cutar da bani da
halin daukar fansa face na ga ranar da Zakayi
mutuwar wulakanci : Tabbas a duniya ba a taba
samun azzalumai kamar ka ba. Ina mai
rokonka da ka hanzarta kasheni domin na huta
da wnn bakin zalunci naka. Sa adda
kyakkyawar yarinyar ta cikin keji ta zo nan a
zancenta sai aljani Raugatul Aguwanu ya kara
fusata ainun yace aikuwa yanzu nan zan ida
mugun nufina akanki. Kawai sai ya kai hannu ya
suro kejin danufin yabude ya daukota daga
cikin amma sai yaji an ce dakata ya kai
Shugaban azzalumai na duniya. Cikin hanzari
da mamaki Raugatul Aguwanu ya juyo da baya:
take yayi arba da boka sadusa da dansa Halyal
tsaye a bayansa. Raugatul aguwanu ya kurawa
boka sadusa idanu cikin tsananin mamaki har
izuwa tsawon yan dakiku yana nazarinsa sanna
yace ya kai wannan ha tsabibin boka kai kuwa
ya ya aka yi ka shigo cikin wannan daji har ka
iso nan cikin makwanci na batare dani ji motsin
shigowarku ba? Kune bil adama na biyu da
111
TASKARNOVELS.COM.NG
suka taba shigowa cikin wannan daji har suka
rayu a tsawon sama da nisan sa a guda sbda
karfin shirina gami da azababben karfin dantse
na
: wannan daji da kuka shigo shine dajin da ake
yiwa lakabi da DARUL HUSHUSHUL MAUT wato
gidan daba ashiga kuma ba a fita. Tunda nazo
na tare a wannan daji yazama nawa ni kadai
domin na kori dukkan aljanu dabbobi da
tsuntsaye gami da dukkan kwarin dake cikinsa.
Zan ci gaba.
MAZAN JIYA
Littafi na Hudu 4
Part K
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
112
TASKARNOVELS.COM.NG
Fatake da matafiya kuwa hatta na jinsin aljanu
haka suka hkra da giftawa ta saman wanna daji
domin koda tsautsayi suka zo wucewar
kamawa suke da wuta su kone saidai tokarsu
tazubo kasa: kai kuwa wane irin karfin tsafi ne
da kai hka wanda har yafi nawa ka ketare duk
masifun da na zuva a wwannan daji? Lokacin
da boka sadusa yaji wannan tambaya sai yayi
murmushi cikin izza sannan ya durfafo inda
wannan tebur yake ya zauna kuma ya dauku
tuffa guda daya yakama ci tamkar a cikin
turakarsa yake sannan ya yafuto aljani
Raugatul Aguwanu da hannu yana mai kiransa:
Ba tare da gardamar komai ba Raugatul
Aguwanu ya ajiye wannan keji wanda yake
hannunsa sannan ya taho wajen sadusa ya
zauna akan tasa kujerar suka fuskaci juna
: A wannan lokaci zuciyar sadusa ta kama
dukan uku uku domin a cikin matukar tsorace
yake kawai dai banza ce ta kori wofi
113
TASKARNOVELS.COM.NG
A iya tunanin aljani Raugatul Aguwanu boka
sadusa ya fishi karfin sihirin tsafi tunda har ya
iya shigowa wannan daji na darul hushushul
mautt lapiya: Abinda ya manta shine a yau ya
sha afa cewar tunda sassafe ya cire dukkan
tsaron da yasa wa dajin sakamakon wani
dogon nazari da yayi a halwar tsafi don bincike
akan yanayin da duniya kw ciki: Har yagama
binciken nasa ya tafi dajin dake