x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - MAZAN JIYA 4

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 68055 words

Category: Adventure Stories

Views 179

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
kowa ya fice daga
cikin tanti aka bar sarki dujalu shi kadai har a
sanna bai farfado daga dogon suman da yayi ba
amma akwai alamar fitar numfashinsa kadan
kadan: sarki dujalu bai farfado ba sai bayan saa
biyu sa rabi : koda ya bude idanunsa ya tsinci
kansa a cikin tantinsa a kwance sai ya cika da
tsananin mamaki domin shi a zatonsa ya mutu
a filin yaki: sarki dujalu ya yunkura domin ya
yaye mayafinsa da aka lullbeshi da hannunsa
na dama kawai sai yaji kamar bashi da hannun
gaba daya: cikin tsananin firgici ya sa daya
hannun nasa na hagu ya yaye mayafin take yayi
arba da hannunsa na dama ya ga yazama
gungulmi: sarki dujalu ya takarkare ya kwarara
mugun ihu mai tsananin karfi gami da amsa
kuwwa izuwa cikin dajin gaba daya: kai hataa
dabbobi da aljanun dake rayuwa a cikin
35

TASKARNOVELS.COM.NG
karkashin teku bahar Sufuya sai da wannan ihu
na sarki dujalu ya eazansu: bayan yayi ihu
kuma sai ya fashe dd matsanaici kukan vakin
ciki domin wanan shine karo na farko da Taba yi
masa rauni a filin yaki a iya tsawon rayuwarsa
duk da cewar ya halarci yakukuwa sama da
guda dari a rayuwarsa

: kuma tunda uwarsa ta haifeshi bai taba zubar
da hawayen takaici ba sai yau: cikin wannan
hali ne shugaban Dakarunsa na jinsin Aljanu
wanda ake kira BARUZUL MADWAN yashigo
cikin tantin ya zube kasa ya kwashi gaisuwa
yace Ya shugabana yanzu mene ne abin yi
tsakaninmu da su waye zai sami damar shiga
cikin wannan kogi na Bahar Sufiya don dauko
Takobin saiful Lujara tsakanin mu da su; tunda
anyi yarjejeniya bisa cewar wadanda suka yi
nasara a yakin mutum uku uku sune zasu
dauko takobin kuma gashi yanzu kamar RAGAS
akayi tunda kai suma kayi a filin yakin shi kuma
Hibru mutuwa yayi: Page 33 Koda jin wannan
batu sai farin ciki ya lulube sarki dujalu bisa jin
cewar yasamin nasarar kashe Hibru amma
36

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma da ya dubi gundulmi hannunsa sai ya
sake kamuwa da tsananin bakin ciki: Tsawon
tan dakiku sarki dujalu yana tunani bai baiwa
aljani barzul madwan amsar tambayarsa ba sai
daga can ya dago kai ya dubeshi yace ya kai
shugaban dakarun aljanu kayi sani cewa a halin
yanzu yarjejeniyar da ke tsakaninmu da su sarki
maharaz ta rushe wannan yaki ya zama danye
don haka za ayi hutu na tsawon kwna uku
domin na baiwa avkan gabamu damar da zasu
sami saukin dacin rashin da suka yina babban
masoyinsu: dalilina anan shine abin kunya ne a
gareni na yakesu a lokacin da zukatansu ke
cike da rauni: lallai na fi son na yakesu a
lokacin da suke cikin nutsuwarsu sbda haka
yanzu kaje ka sa a rubuta takarda a kaiwa
abkan gaba bisa wannan hukuci da nayanke.
Aljani barzul madwan ya risina yace angama ya
shugabana: kawwai sai ya bace bat! Daga cikin
tanti tamkar bai taba wanzuwa ba a ciki

* * *
* bayan su sarki Maharaz sun
kwashe gawarwakin dakarunsu mutum biyu da
aka kashe; wato gawar sarki yaki Hibru data
37

TASKARNOVELS.COM.NG
Barde Kursham sun koma cikin sansaninsu sai
aka shiga gidimar binne gawar: nan fa kowa da
kowa ya kama kuka kamar ba za a daina ba:
babu wanda zai fi baka tausayi ma sama da
sarki Maharaz domin har birgima ya kama ya a
kasa sai da aka rirrikrshi aka shiga bashi baki
sbda jiya yiya tsani kansa gwara ma ace shima
ya mutu ya huta da bakin ciki: Lokacin da aka
sanya Hibru a cikin kabarinsa aka rufeshi sai
inmal da sarki maharaz suka kwana akan
kabarin suja cigaba da kuka ba sassauci: akan
kabarin suka kwna suna kukan har sai da alfirjir
ya keto sannan aka zo aka kwashesi sumammu
aka kaisu cikin tanti aka kwantar: da kyar da
sindin goshi gimbiya Mulaifa ta ceto rayuwarsu:
bayan sun dawo hayyancisu ne aka kawo
musu abin kalaci dama a jiya da daddare ma
basu ci komai ba: nan fa gardama ta karke a
tsakaninsu da mulaifa suka ce ba zasu ciba:
Gimbiya Mulaifa ta zare wata karaar wuka mai
tsananin kaifi da tsini ta saita cikintana kuka
tace idan har baza ku cin abinci ba lallai zata
kashe kanta: nan fa suka kama cin abinci bisa
dole har sai da suka koshi: gama cin abinci
nasu ke da wuya sai ga wani badakare Mai
38

TASKARNOVELS.COM.NG
suna GAIYABU ya shigo cikin tanti rike da
wasika a hannunsa: Gaiyabu ya zube kasa
gaban sarki maharaz ya kwashe gaisuwa
sannan ya mika masa wasikar: nan take sarki
maharaz ya warware wasikar ya karanta a fili
kamar haka; SAKO DAGA SARKI DUJALU:
ZUWA GA SARKI MAHARAZ BABBAN ABOKIN
GABATA: YAKAI WANNAN SARKI KAYI SANI
CEWA ABINDA YA FARU TSAKANINMU DA KU
BA KOMAI BANE FACE SHARAR FAGE: NA
SANCEWA NA KUNSA MUKU GAGARUMIN
BAKIN CIKI BISA NASARAR DA NA SAMU TA
KASHE SARKI YAKINKA; KUMA BABBAN
MASOYINKA HIBRU TO AMMA NIMA HIBRU YA
TAFI YA BARNI DA TABON BAKIN CIKI DA HAR
ABADA BA ZAN MANTA DASHI BA TUNDA
YARABANI DA HANNUNA GUDA DAYA: TABBAS
NAYI JINJINA GA MAMACI HIBRU DOMIN SHI
NE JARUMI NA FARKO WANDA YA TABA
SAMUN DAMAR YI MIN RAUNI A FILIN DAGA
KUMA NA YI ALKWARI KODA BAYAN WANNA
YAKI NE ZAN ZIRYACI KABARIN HIBRU NA YI
MASA JINJINA: INA MAI SANAR DAKAI CEWA
BISA GUMURZUN DA AKA YI A JIYA MU DAKU
BABU WANI SAKAMAKO FACE RAGAS SABODA
39

TASKARNOVELS.COM.NG
HAKA ZAMU CI GABA DA WANNAN YAKI NAN
DA CIKAR KWANA UKU SBDA NAFI SON NAYI
YAKIN DA KU A LOKACIN DA KUKE DA
NATSUWA BA YANZU BA DA KUKE CIKIN
DAMUWA DA ALHINI: INA FATAN ZA KU KARBI
WANNAN SHAWARA TAWA HANNU BIYU

Koda sarki maharaz ya zo nan a karatun
wasikar sai yamike tsaye zumbur a fusace ya
yayyaga wasikar sannan ya yunkura da nufin
yafita waje ya sa a fara shirye shiryen yaki
cikin hanzari inmal ya sha gabansa yace ya
shugabana ka tausasa zuciyarka ka dau hkr sau
tari yanke hukunci a lokacin da rai ya fusata
baya haifar da komai face nadama da asara:
muyi amfani da shawarar wanan abokin ga
namu mujira izuw tsawon kwna ukun: koda jin
wanna batu sai sarki maharaz ya duci inmal
cikin alamun tsananin damuwa yace yakai
magajin sarkin yaki shin baka da tunanin cewa
sarki dujalu so yake ya yaudaremu ya yi amfani
dawann dama ya kawi mana harin sumamea
cikin kwana ukun nan yadda zai iya murkusheu
40

TASKARNOVELS.COM.NG
a cikin kankanin lokaci? Inmal ya numfasa yace
haba ya shugabana ai babu wani motsi wanda
sarki da dakarunsa za suyi ba tare da mun gani
ba tunda daga nan sasaninmu muna hangensu
suna hangenmu, dare da ranan masu gadi suna
lura: ka kara hakuri ya shugabana har ixuwa
lokacin da wadannan kwanki zasu ciki
ni ina ji a jikina cewar mune zamu sami nasarar
dauko takobin Saiful Lujara a cikin wannan
kogi: koda inmal yazo nan a zancensa sai
Gimbiya mulaifa mata dubeshi tace kayi
amfani da shwarar inmla ya kai abbana domin
ina gainin cewa itace zata fiye mana alheri:
koda gama fadin hakan mulaifa ta kama
hannun inmal taja shi suka fice daga cikin
tantin suka bar sarki maharaz a tsaye cikin
tsananin da muwada takaici
WANNAN SHINE ABINDA YAFARU A CAN
BAKIN KOGIN BAHAR SUFIYA BAYAN ANCI
GABADA FAFATA YAKKI TSAKANIN RUDUNAR
SARKI MAHARAZ DA RUNDUNAR SARKI
DUJALU A KARO NA BIYU

41

TASKARNOVELS.COM.NG
* * * * * AL:AMARIN Gimbiya Hursiya Kuwa;
lokacin da aljani burzaru ya nufi can birnin da
ira ta tabbatar da cewa an rabata Da sarki
kenan sai ta fashe da matsaininci kukana bakin
ciki: Bata gushe ba tana kukan hat aljni Barzaru
ya sauketa a tsakiyar gidan sarautar tasu

Koda bayi kunyangi barori da dakarun tsaro na
gidan suka ganta sai duk suka zube kasa a
gabnta suna kwasar gaisuwa ko kallomsu ba
tayi ba sai ta juya a fusace tashige izuwaa can
cikin gidan sarautar da sauri: duk sa adda ta
waigo bayanta sai ta ga aljani Barzaru nabiye da
ita: Al'amarin da yai matukar ba ta mamaki da
tsoro kenan. nan take ta gane cewa lallai sarki
ne ya umarci barzaru da ya sa ido akanta don
kada ta sulale ta koma can sansani yaki: Nan
fa Hursiya taji hankalinta ya dugunzuma ainun
kuma ta kudurce a ranta cewar takowanne hali
sai ta san yadda tayi ta subecewa barzaru
takoma can sansanin yaki sbda gwara itama ta
mutu a can da dai azo mata da labarin
mutuwar sarki tunda bata da kowa a duniya sai
shi. kai tsaye Gimbiya Hursiyya ta wuce izuwa
42

TASKARNOVELS.COM.NG
cikin turakarta. tana shiga ciki ta mai da kofa
tarufe bam da karfi cikin fishi sannan ta fada
kam gadonta ta kwanta ruf da ciki ta fashe da
sabon kuka: Shi kuwa aljani barzaru a kofar
turakar yaja ya tsaya kuma ya kame kamar
gunki yana muzurai ko yaushe idanunsa na
kallon gabas da yamma kudu da arewa don
hada gimbiya Hursiya ta Shamaceshi ta fice ba
tare da sani ba: su kuwa fadawan sarki dujalu
wadanda aka barwa jiran gari koda suka ji
cewar gimbiya Hursiya ta dawo daga sansanin
yaki ita kadai? Sai suka cika da tsananin
mamaki suka dugungumo gaba daynasu syka
zo ganin gimbiya. koda suka aika da manzo a
gareta bisa zuwansu sai ta aiko a gay musu
cewa baza ta gana dakowa ba sai gobe da safe
a fada: Al:amarin da yai matukar dugunzuma
hakalinsu kenan suka rasa abinda ke musu
dadi sabo sa su kawai so suke suji matsayin da
ake ciki a can sansanin yaki: Shin sarki Dujalu
yana nan a raye ko kuwa ya mutu? MASU IYA
MAGANA SUN CE IDAN KAGA KARE YANA
SHINSHINA TAKALMI TO SO YAKE ZAI DAUKA.
tunda gimbiya Hursiyya taji cewa yan majalisar
sarki sun kagu da su yi magana da ita sai jikinta
43

TASKARNOVELS.COM.NG
ya bata cewar so suke suci amanar sarki,
ma'ana idan suka ji sarki ya mutu sai su yi sauri
su nada wanda suke son ya gajeshi acikinsu
batare da sun bata sarautar bakamar yadda
yake aka ida: Koda aiyana hakan sai hankalin
Hursiya ya sake dugunzuma ainun domin ta
fahimci cewar lallai tana ciki hadari domin idan
ta fadawa yan majalisar gaskiya al amari cewar
bata san abinda ya faru a filin yakin ba tunda
bata gani da idanunta zasu zata karya take su
dauka cewa lallai itama da kyar ta tsira kuma
an kashe sarki da mukarrabansa: ama da
Hursiya ta tuna cewa ai tana tare da aljani
Barzaru babban jarumi kuma sadauki mai
watsa maza babbn hadimi sarki dujalu mai
amana sai hankalinta ya dan kwanta sbda ta
san cewa zai kareta daga dukkan wani mugun
abu amma kuma sai ta fara tunasnin hanyar da
zata bita koma can sansanin yakin domin
zamanta a can zai fiye mata kwnciyar hankali.
Kashe gari da safe bayan Gimbiya Hursiya ta
gama kintsawa tayi kalaci sai ta caba ado
sanna ta nufi fada fuskarta cike da annuri tana
takawa dai dai tamkar taron dawisu ta rinka
tafiya cikin izza da jin kamshi: da shigarta cikin
44

TASKARNOVELS.COM.NG
fadar sai ta iske gaba dayan yan majalisar a
zaune sun yi tsuru tsuru suna jira isowarta:
koda suka ga gimbiya a cikin fara ada nishadi
sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka fara
tunanin cewa lallai sarki dujalu ne yake samun
nasara acan filin yakin: Dama bayan tafiyar
sarki dujalu da rundunarsa ta yaki sai yan
majalisar suja yi taro na sirri a tsakaninsu inda
suka gaiyato wani amintaccen bokansu mai
suna IRMAS BINI KAIBUR suka umarceshi daya
yi musu bincike akan abinda zai faru a can
bakin kogin Bahar sufiya: Koda boka Irmas ya
dauko madubin tsafinsa ya shafeshi da hannun
hagu domin yaga abinsa zai faru sai nan take
madubin tsafin yayi bindiga ya farfashe:
Al:amarin da yai matukar razana boka irmas da
yan majalisar kenan suka firgita ainun: Har yan
majalisar sun yunkura zasu mike tsaye su fice
da gudu dga cikin dakin tsaro sai boka irmas ya
daka musu tsawa yace kowa ya zauna a inda
yake in bahaka ba kuwa babu wanda zai koma
gidansa a raye: Koda jin hakan sai kowa ya koa
inda yake ya zauna: boka irmas yai gyaran
murya sannan ya dubi gaba dayan yan
majalisar yace yaku shuganbanina kuyi sani
45

TASKARNOVELS.COM.NG
cewa babu wani matsafi a wannan nahiya mai
karfin sihiri dayakai na sarki dujalu sbda haka
ya boye duk abinda ke faruwa a cam bakin
tekun bahar sufiya ga dukkan wani mahaluki
dake cikin wannan nahiya: bisa wannan dalili
ne kuka ga madubin tsafina yai bindiga; yanzu
hanya daya ce zamu bi my iya ganewa idan
sarki dujalu yana samun nasara a filin yaki ko
baya samu: Nan gaba a lokacin da yakin ya fara
tsauri lallai akwai mutumin da zai dawo daga
can filin yakin wandas ya kasance makusanci
na sarki ya hau kan karagar sarki ya zauna: to
tabbas rudunarmu basu da saa kuma baza su
dawo ba a raye, idan kuwa yaki zama akan
karagr sarki to tabbas sarki dujalu zai dawo
gida a raye: Kofa gimbiya Hursiya taga yan
majalissar sun kura mata idanu sai hankalinta
ya dugunzuma ta dada tabbatar da cewa lalai
akwai wani mugun abu da ke ransu. Awannan
Lokaci aljani barzaru na biye da ita yana take
mata bayan don tabbatar da tsaro amma babu
mai ganinsa face gimbiy Harsiya kadai, har
Gimbiya hursiya ta nufi inda karagar sarki take
da nufin ta zauna sai aljani barzaru yi sauri ta
sha gabanta yayi mata nuni da jada taje ta
46

TASKARNOVELS.COM.NG
zauna akan karagar. Batare da gardamar komai
ba kuwa ta sauya wuri taje ta zauna akan
kujerar da ta saba zama ko da yaushe a fadar
kamar kullum: koda ganin haka sai jikin yan
majalisar ya yi sanyi gaba dayansu sai murna
takoma ciki kuma hankain su ya dugunzuma
sabo da burin da suke son cikawa tsawon
shekara da shekaru ya rushe alhalin wannan ce
kadai damar da suke da ita da zasu kawr da
bakin zalunci da aka dade ana yi musu a
nahiyar: a wanna lok Icin fadar tacika makil da
mutanen gari da duk inda mutum ya duba sai
dai yaga kawunnan bil adama rututu ako ina
babu masakar sinke. ba komai ne ya janyo
wannan cikowa ba face mutane sun ji cewar
gimbiya hursiya ce kadai ta dawo daga can baki
kogin bahar safiya don haka kowa yana son yaji
halin da yan uwansa ke ciki wadanda suka tafi
yaki. Bayan Gimbiya Hursiya ta zauna akan
wannan kujera wadda ta saba zama akai sai
aka buga mata tamburan sarauta gami da
bushin algaita don girmamawa a gareta bisa
matsayinta na kanwar sarki. Ana gama buga
tamburan ne gimbiya hursiya ta mike ta
fuskacin jamaar gari tace ua ku jamaata ina
47

TASKARNOVELS.COM.NG
mai sanar da ku cewar wannan yaki da muka
fita mun fita akan saa da nasara domin kuwa
na baro jamaarmu suna ragargazar jama ar
sarki maharaz doin haka akwai cikakakiyar
alama tacewar mune zamu ci wannan yaki.
Koda gimbiya Hursiya tazo nan a zncenta sai
fadar ta rude da shewar mutane jama a su cika
da dumbin farin ciki kuma suka sami kwanciyar
hankali ba komai ne ke damub mutne ba facw
tunanin yan uwansu wadanda aka tafi da su
yakin suna ga nin cewa ba lallai bane su dawo
ba amma jin cewar sune kesamu nasara a
yakin sai suka sami nutsuwa sun san cewa da
yawan jama'arsu za su dawo a raye. haka
gimbiya Hursiya ta cigaba da kwantar musu da
hakalin jama a cikin kalami na kara kwarin
guiwar har suka sami cikakkiyar nutuswa da
fahimta: a sannan ne ta sallami kowa a fadar ta
watse kowa ya kama gabansa. * * * * lokacin
da yan majalisar suka fice daga cikin fadar sai
suka kewaye daya bayan daya a sirrince suka
hadu acan gidan waziri sarki dujalu wanda ake
kira MAZARUB IBINI HALSHAM kuma basu taru
ba sai da dare ya raba saada gari yayi tsit ba a

48

TASKARNOVELS.COM.NG
jin sauti komai face kukan tsuntsaye da
nakarnuka. Zan ci gaba.
MAZAN JIYA
Littafi na Hudu 4
Part E
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey

A cin wani babban falo na waxiri mazarub suka
hadu, hatta barori da bayi na gidan a wannna
rana tsaresu aka yi a wani daki dabam don kada
su gazuwan yan majalisar ko su ji abinda zasu
tatauna, dakarun dake tsaron gidan ne kawai
suke kai kawo wadanda suka kasance
aminatattun waziri mazarub

: Bayan kowa ya gama hallara a cikin wannan
falo sai aka janyo kofofi da tagogin falon aka
rufee sannan wziri maharab yai gyaran murya
ya kalli yan majalisar mutu tara shine cikon na
49

TASKARNOVELS.COM.NG
goman wadanda gaba dayansu sun kasance
dattijai babu dan kasa da shekara hamsin da
biyar a cikinsu: waziri marzub yace yaku yan
majalisa kun sani cewa shekara da shekaru tun
zamanin mahaifin sarki dujalu muke fama da
kunci bakin ciki gami da takaici bisa irin mulkin
zalunci da ake yi mana

babu sasauci ga basarke attajiri ko talakan
gari: Gaba daya kasashen dake wannan nahiya
a karkashin ikon sarki dujalu suke sai abinda
yace shi akeyi: Yafi kowa dukiya karfi tsafi da
karfin dantse amma dik da haka ya raina wanan
baiwa daya samu kuma so yake ya mallaki
duniya nan gaba danyata;; Shin haka za mu
cigaba da zuba ido muyi ta zama a matsayin
bayinsa yayanmu da jikokinmu ma su cigaba da
yi masa bauta har abadan abidina, kuyi sani
cewa mune makasantansa amma bai san
darajarmu da kimanmuba, to ko mutuwa yayi
haka yar uwarsa gimbiya Hursiya zata ci gaba
da azabtar damu. Tunda yanzu sarki dujalu
yana can sassann yakin da yafi kowanne yaki

50

TASKARNOVELS.COM.NG
hadari a rayuwarsa mun sami dsmar da zamu
kawo karshen bakin cikinmu

Yanzu gashi yar uwarsa ta dawo tace wai
mune muke samun nasara a wanna yaki ta
yaya zamu iya tabbatar da cewa abin data fadi
gaskiya ne: kumas ta ya ya zamu iya cimma
burinmu mu yar da kwallon mangwaro mu huta
da kuda? Sa adda waziri mazarub yazo nan a
zancensa sai falon yayi tsit Tamkar mutuwa ce
ta gifta gaba dayan suka kama muzurai suna
kallon junansu aka rasa wanda zai ce kala
daga can sai wani tsohon mafi shekaru a
cikinsu wanda ya kasancve dan wada wanda
tsawonsa bai wucce kamu shida ba mai suna
SADUSA ya mike tsaye yana mai gyaran murya:
Nan fa kowa ya Uba masa idanu: sadusa yai
murmushi sannan ya shafi dogon gemunsa
wanda ya sauko har kasan cikinsa yace yaku
yan uwana yan majalisa ku yi sani cewa ga
dade ina jiran zuwan wannan rana har mana
fidda tsammanin zuwanta ama sai gashi tazo

51

TASKARNOVELS.COM.NG
ina so ku sani cewa a duk fadin kasar nan da
nahiyar nan bani da wani makiyi wanda yafi
sarki dujalu

domin a sanadinsa ne na rasa iyayena iyalina
da dukkan dangina: A yanzu haka ni kadai ne na
rage daga cikoin zuri armu hakam ya samo
asali ne akan wani laifi da zuri armu tayi masa
yasa aka rinka kamosu daya bayan daya ana yi
musu yankan rago

: A wannan lokaci ni bana wannan nahiyar na
bazama cikin duniya neman ilmin tsafi: Ban
dawo ba sai bayan sarki dujalu ya gama kashe
gaba dayan zuri ar tamu gidamu mana iskeshi a
kone kurmus ko tsinke guda daya ban samu ba,
a bakin wani makofcinmu na sami lbrin abinda
ya faru ga zuri ata gaba daya: Nan take zuciyata
ta kama tafarfasa kamar zata kone sbda fishi

52

TASKARNOVELS.COM.NG
Nan fa wannan makoci nawa ya shiga
rarrashina yana mai bani shawarar na hanzarta
na bar garin nan domin idan sarki dujalu ya
sami lbr cewa ina dsga cikin zuri ar da suka yi
masa wannan laifi tabbas kashe ni zai yi. A
wannan lokaci ina ta faman rusa kukane na
bakin ciki amma ko danaji wananan makofci
nawa yace wai sarki zai sa a kasheni: Sai na
bushe da dariyar takama na ce ai na wuce
wannan matsayi: Kai dai kawai ka zuba ido ka
sha kallo: Ba komai ne yasana yarda da kaina
ba sai bisa tarin dumbin ilimin da na samo na
tsafi don haka ina ganin cewa zan iya kare
kaina daga dukkan masifa: Nan take na mike
tsaye na yiwa makobcin nawa sallama sannan
na bude jakata na debo dukkan gurayena da
layu na tsafi na daddaurasu a jikina: Bayan na
kammala shiri sai na durfafi fadae sarki dujalu
kai tsaye ba tare da fargabar komai ba: Lokacin
da na isa fadar sarki dujalu sai na isketa a cike
makil da fadawansa da ;mutanen gari ana
tafiyar da harkokin mulki, duk da cewar fadar
cike take da dajaru a
End Ads