a
wannan lokacin ma sai karfinsa gami da zafin
namansa ya ninku fiye da na baya duk kuw da
cewar har wannan lokacin jini na zuba a
hakarkarinsa inda wannan reshe ya sokeshi.
Wohoho! Nan fa kasuwar daukar rai ta bude,
duk inda jarumi Hasnalu yasa gabansa sai dai
kaga birirrikan na zubewa kasa matattu, lokacin
da wuya tai wuya sai birirrikan suka ga cewar
Hasnalu ya kusa karar da su saboda haka sai
suka fara ja da baya dan su tsira da rayukansu
amman sai jarumi Hasnalu ya rinka kure masu
gudu yana rafkesu, sai ga shi girman birirrikan
256
TASKARNOVELS.COM.NG
gami da karfinsu duk si ya zama na banza,
daman ance in kaji ana ki gudu to fa sa gudu ne
bai zo ba. Nan dai Hasnalu ya cigaba da saran
birirrikan sun masu ihu gami da kururuwa suna
kum faduwa kasa mattatu a haka dai sai da ya
karar da su gaba dayansu, ya zamana cewa ko
daya bai tsira da rayuwarsa ba. A sannan ne jiri
ya kashe shi ya fadi kasa sumamme, ai kuwa sai
gimbiya Hursiyya ta yi wuf ta fito daga inda take
boye ta ruga da gudu izuwa kan Hasnalu, shima
aljani Radiyan sai ya fito daga maboyarsu yana
waige-waige cikin alamun tsananin tsoro dan
gani yake kamar akwai sauran wadannan
birirrikan a boye a wajen. A lokacin ne kuma
jarumi Hasnalu ya farfado daga dogon suman
da yayi, ko da ya farfado sai ya tsinci kansa bisa
cinyar Hursiyya idanunta cike da kwalla, a
firgice ya mike zaune zumbur yana mak kallonta
cikin mamaki sannan ya dubi raunin dake
hakarkarinsa, yaga an samasa magani kuma an
daure wajen da kyallen rigarta. Koda Hursiyya
taga Hasnalu ya mike tsaye sai ta kamu da
tsananin farin ciki ta dubeshi cikin murmushi
mai taushi ta ce godiya ta tabbata ga
ubangijinka wanda ya baka nasara da sa'a akan
257
TASKARNOVELS.COM.NG
wadannan mugayen burirrika. Kada jin wannan
batu sai jarumi Hasnalu yaji gabadaya tsigar
jikinsa ta tashi, nan take a karon farko ya ji a
rayuwarsa wata ya mace ta burgeshi saboda
dalilai guda biyu; dalili na farko kuwa shine
ganin kwalla a cikin idanun Hursiyya a lokacin
daya farfado daga dogon sumar d yayi wanda
hakan ya tabbatar masa da cewa tana cikin
tsananin damuwa bisa halin d ya shiga, dalili na
biyu shine tunda ya shigo wannan nahiyoyi
tsawon shekara guda da rabi ya ratsa ta cikin
birane da garuruwa amman bai taba haduwa da
wanda yayi yabo ga ubangijinsa ba face gimbiya
Hursiyya kawai sai Hasnalu yaji kaunar Hursiyya
ta shigeshi farat daya, abinda ko a mafarki bai
taba faruwa a kansa ba. Cikin murmushi
Hasnalu ya dubi Hursiyya ya ce madalla da
wannan yar sarki wacce ta ceto rayuwata,
hakika bna an irin godiyar da zanyi maki ba,
domin n lura da irin jinin d ya zuba a jikina mai
yawa ne, kuma inba dan kin tsaidashi ba da
wata kila yanzu na dade da mutuwa. Koda jin
haka sai itama ta maida mashi da martanin
murmushi ta ce ai asarar irinka guda daya a
cikin al'umma gwara ayi asarar gari guda. Da
258
TASKARNOVELS.COM.NG
farko dai kaga kai kyakkyawa ne irin wanda sai
an tara kyawawa dubu ba'a samu kamarka ba,
kai gwarzo ne a cikin jarumai mai jarumtakar da
sai an tona, domin na fahimci cewar ko dan
uwana sarki dujalu iyakar jarumtakar da zai iya
kenan, ga dukkan alamu ma sai k fishi tunda kai
ka dogara ne da zallar karfinka baka tsafi. Ya kai
wannan jarumi kayi sani cewa kaine saurayi na
farko daya taba burgeni a rayuwata, kuma in
banda dan uwana sarkk Dujalu babu wani
namiji da jikina ya hadu da nasa, ni kaina nayi
matukar mamaki bis yadda aka yi har naji na
aminta da kai tamkar ka kasance dan uwana na
jini. Duk wannan hira da su Hasnalu ke yi aljani
Radiyan na zaune a gefe daya a bayansu, yana
mai kallonsu da sauraronsu amman zuciyarsa
sai faman tafarfasa take tamkar zata kone,
saboda ya fahimci cewar da sannu jarumi
Hasnalu zai ja ra'ayin gimbiya ta karbi
addininsa, kuma akwai alamun cewa zasu iya
fadawa cikin tarkon soyayya. Nan fa hankalin
aljani Radiyan ya dugunzuma ainun ya fara
tunanin hanyar da zai bi ya lalata wannan alaka
tasu, ko kuma ya dauke Hursiyya su bace wa
jarumi Hasnalu. Hasnalu ya dubi gimbiya
259
TASKARNOVELS.COM.NG
Hursiyya ya ce yake wannan yar sarki kiyi sani
cewa nima kece mace ta farko da jikinta ya taba
haduwa da nawa, wanda yin hakan haramun ne
a addinina kasancewarki ba muharramata ba,
babu wani dan adam ko aljan daya taba ceton
rayuwata sai ke, a gaba daya nahiyoyin dake
nan kece mutum ta farko da tayi yabo ga
ubangijina. Yanzu dai abinda nake so ki sani
shine duk wannan gagarumar jarumtaka da
kikaga nayi har na samu nasarar kashe
wadannan birirrikan ba wai tsagwaron karfin
damtsena bane ko dabarata ba face taimako
daga ubangijina. Shin yanzu kin gamsu cewa
ubangijina shine na gaskiya ko kuwa har sai na
cika sharadi nayi abubuwa al'ajabi guda uku
kamar yadda kika bukata a baya? Sa'ad da
gimbiya Hursiyya ta ji wannan tambaya sai ta
juya da baya ta dubi aljani Radiyan shi kuma sai
yayi mata nuni da idanunsa kar ta ce ta gamsu.
Hursiyya ta juyo ta fusknaci Hasnalu cikin
murmushi tace da shi mu bi dai a sannu a
hankali har ka cika ragowar sharadin. Koda jin
haka sai Hasnalu yayi murmushi sannan yace
yake gimbiya ki kasance mai ra'ayin kanki ba
wai ra'ayin wani ba, kuma ki tabbatr kinyi aiki da
260
TASKARNOVELS.COM.NG
gaskiya ba da son zuciya ba, yanzu sai ki tashi
mu cigaba da tafiya. Koda jin haka sai Hursiyya
ta dubi Hasnalu cikin yanayin tsoro ta ce da shi
ai abune mai hadari mu cigaba da wannan
tafiya a haka, kana tare da danyen ciwo a
jikinka, akwai bukatar ka yi jinya koda na tsawon
sa'a goma sha biyar ne. Koda jin haka sai
Hasnalu yayi murmushi sannan ya ce yanzu
kina nufin kice idan na cigaba da tafiya da
wannan ciwon a haka wani abu zai taba lafiyata
kenan? Hursiyya tace ai bama abinda zai taba
lafiyarka ba ma, idan har ka cigaba da tafiya a
haka zaka ma iya rasa rayuwarka gabadaya.
Koda jin haka sai Hasnalu ya sake yin murmushi
a karo na biyu sannan ya karanta wata addu'a
ya tofa akan raunin nasa sannan ya mike ya
dubi Hursiyya da aljani Radiyan ya ce to ni dai
zan cigaba da tafiya, ko dai ku tashi mu tafi tare
ko kuma ku sameni a gaba, yana gama fadar
hakan sai ya kama hanya ya nausa cikin
wannan kogon dutsen mai duhu wnada
wadannan birirrikan suka fito daga ciki. Koda
ganin haka sai aljani Radiyan da Hursiyya suma
suka tashi da sauri suka bi bayanshi. Sai da
suka shafe rabin sa'a suna tfiya a cikin wannan
261
TASKARNOVELS.COM.NG
kogon dutsen amman basu hadu da komai ba
face kwarangaloli na sassan jikin biladama
wanda wadannan birirrika suka kashe, a sannan
ne suk gane cewa ashe wannan kogon dutsen
gari ne guda na birirrikan. Suna fitowa daga
cikin kogon sai kuma suka tsinci kansu a wani
dajin daban ba wancan ba, kawai sai suka
hango cibiyar tekun bahar sufiya ruwana nata
fanjam-fanjam kamar zai zo inda suke ya
shafesu. Nan take kuma suka rinka jiyo ihu
gami da kururuwar mazaje acan kasa-kasa
alamar cewar har yanzu fa ana kafsa wannan
azababben yakin acan bakin tekun. Koda iyo
wannan sauti sai Hasnalu ya waigo da sauri ya
dubi Hursiyya kawai sai yaga ta tsugunna a kasa
tana haki saboda gajiya, shi kuwa aljani Radiyan
ya koma gefe daya ya zauna harma ya fada cikin
kogin tunani. Hasnalu ya matsa kusa da
Hursiyya ya dubeta y ce ga dukkan alamu dai
muna daf da riskar inda ake yin wannan yaki,
dan haka sai kuzo mu karasa da sauri. Koda jin
haka sai Hursiyya ta dubeshi cikin alamun
tsananin mamaki tace wai kai wane irin mutum
ne wanda baya gajiya, ni abinda ma yake bani
mamaki game da kai shine yadda ka kasa
262
TASKARNOVELS.COM.NG
sarewa alhalin cewa kana dauke da rauni a
jikinka, koda ta zo nan a zancenta sai ta dubi
raunin nasa take kuwa ta sha mamaki, domin
kuwa raunin ya kame harma ya bushe kai kace
dama ya dade a jikinsa ba sabo bane. Al'amarin
da yayi matukar girgiza Hursiyya kenan, ta dubi
jarumi Hasnalu ta ce yaya aka yi wannan raunin
naka ya warke da gaggawa haka, tamkar ma ba
yau ka same shi ba? Koda ya ji wannan
tambaya sai Hasnalu yayi murmushi ya ce
wannan shine iko irin na ubangijina, dan haka
yanzu na cika sharadi na biyu da ke tsakaninmu
saura sharadi na uku wanda daga shi sai ki karbi
addinina kamar yadda muka yi alkawari.
Hursiyya ta maida mashi da martanin
murmushi tace tabbas zancenka dutse ne.
Lokacin da aljani Radiyan ya ji wannan batu sai
hankalinsa ya kara dugunzuma ya tabbatar da
cewa lallai dan bai dauki matakin gaggawa ba
akan jarumi Hasnalu to fa duk shirinsa sai ya
tarwatse. Hasnalu ya zauna daf da Hursiyya ya
dubeta ya ce ina ganin dai cewa yanzu tafiyar da
ta rage mana mu riski bakin tekun nan da ake
wannan yaki baya wuce ta rabin sa'a ba, tunda
daga inda muka baro zuwa kin tekun kunce
263
TASKARNOVELS.COM.NG
mani tafiyar sa'a guda ce kuma gashi mun shafe
kusan rabin sa'a a iya tafiyar da muka yi. Jin
hakan ne yasa Hursiyya ta yi murmushi sannan
tace tabbas gama babbar alama na muna iya
jiyo sautin ihun mazaje daga can filin dagar
gami da karafkiyar karafa, sai dai fa abinda ya
bani mamaki shine ban ji karaji gami da rurin
aljanu ba wanda shine ya kamata yafi amsa
kuwwa da cika kunne. Koda jin wannan batu sai
Hasnalu ya jinjina kai sannan ya ce aikuwa indai
akwai aljanu a wannan yaki kuma ya zamana
cewar bama jiyo rurinsu gami da karajinsu to
babu mamaki an kashesu gabadayansu.
Hursiyya ta jinjina kai ta ce kwarai kuwa na
yarda da zancenka, idan kuwa haka ne kaga
kenan yakin yazo da sauki tunda yanzu ya rage
tsakanin mutane kawai, kuma lallai ana daf da
kareshi don haka zaifi mana kyau mu tashi mu
karsa can din da sauri. Koda jin wannan batu
sai aljani Radiyan ya takarkare ya bushe da
wata mahaukaciyar dariya, al'amarin da yasa
Hasnalu da Hursiyya suka juyo da sauri kenan
suna masu kallonshi cike da mamaki, Hursiyya
ta ce da shi ya kai Radiyan ina dalilin wannan
dariya taka ? Maimakon Radiyan ya bata amsar
264
TASKARNOVELS.COM.NG
tambayarta sai ya sake bushewa da dariya a
karo na biyu, lokacin guda kuma ya murtuke
fuska ya ce yanzun nan nima nayi bincike a cikin
madubin tsafina naga cewa lallai an kashe gaba
daya aljanun da suke a wannan tsibiri na kogin
bahar sufiya, a halin yanzu babu sauran aljani a
wannan daji gabadaya face ni da kuma Aljani
Raugatul Agwanu, yanzu kuma gashi zan riga
Raugatul Agwanu zuwa bakin wannan teku,
tunda shi yana can yana bacci bai farka ba,
tunda a halin yanzu sihirin tsafi ya daina aiki
acan filin yakin babu wanda ya isa ya ganni,
kunga kenan zan iya zuwa na shiga cikin takun
salin alin ba tare da wani ya ganni ba na lalubo
inda takobin take, da zarar na daukota shikenan
na zama sarkin duniya kuma yanzu zan bace
maku da gani babu yadda zaku yi da ni. Babban
burina na biyi shine na mallakeki ki zama abar
debe mani kewa kamar yadda shalbirat ta debe
wa aljani Raugatul Agwanu kewa tsawon
shekaru gom sha bakwai, kinga idan na
mallakeki babu mai iya rabamu har abada sai
dai ajali tunda na mallaki takobin Saiful Lujara
na zama sarkin duniya. Sa'ad da aljani Radiyan
yazo nan a zancensa sai takaici ya lullube
265
TASKARNOVELS.COM.NG
gimbiya Hursiyya har idanunta suka ciko da
kwalla, ta dubeshi tace ashe daman yaudarata
ka yi kenan, wannan shine burinka a cikin
wannan tafiya ban sani ba, hakika ka cika maci
amana shugaban azzaluman duniya. Koda jin
haka sai aljani Radiyan ya cigaba da kyalkkyala
dariyar mugunta. Ita kuma gimbiya Hursiyya sai
ta kama kukan bakin ciki, kawai sai ta ji jarumi
Hasnalu ya kira sunan aljani Radiyan yana mai
daka masa tsawa gamk da cewa ya kai Radiyan
kayi dukkan abinda kaga dama amman ka sani
cewa da izinin ubangijina ba zaka samu nasara
ba. Koda gama fadin haka sai Hasnalu ya zauna
a kasa dirshan gaban gimbiya Hursiyya kuma ya
lankwashe kafafunsa sannan ya runtse
idanunsa ya kama karanta wata addu'a ta
neman taimakon Allah a cikin zuciyarsa. Shiko
aljani Radiyan sai ya cigaba da kyalkkyala
dariyarsa ta mugunta, a lokacin ne kuma
hankalin gimbiya Hursiyya ya dugunzuma
ainun, tsoro ya baibayeta kuma jikinta ya kama
rawa, haka dai aljani Radiyan ya cigaba da
kyalkkyala wannan dariya har izuwa tsawon yan
dakiku, katsam kuma sai yayi girgiza ya zama
guguwa, take guguwar tayi kan gimbiya Hursiyya
266
TASKARNOVELS.COM.NG
zata sureta cikin zafin nama jarumi Hasnalu ya
zare takobinsa ya kai wa wannan guguwa
wawan sara ba tare da ya bude idon nasa ba,
kawai sai suka ji aljani Radiyan ya rusa uban ihu
daga can kuma sai suka ji karar faduwarshi
kasa. Hasnalu ya bude idanunsa yaga gawar
aljani Radiyan a kasa gangar jikinsa ta rabu gida
biyu. Koda gimbiya Hursiyya tayi arba da gawar
aljani Radiyan ya kwance sai ta rungume
Hasnalu ta kuma fashe da kukan murna hadi da
yi masa godiya bisa ceton rayuwarta da yayi
daga sharrin aljani Radiyan. Cikin sauri
Hasnalu ya janye jikinsa daga nata ya ce ai ba ni
bane abin godiya face ubangijina, wai shin kin
manta ne cewa a baya kema kin ceci rayuwata,
ai babu bukatar kiyi mani godiya. Hursiyya ta yi
murmushi sannan ta ce saboda me ba zanyi
godiya ba ga abin kaunata ba, ya kai Hasnalu
kayi sani cewa a rayuwata na fidda tsammanin
cewa zan iya samun masoyi a duniya bbanda
dan uwana sarki Dujalu, amman dana sadu da
ki sai na gane ba haka bane, ina mai tabbatar
maka da cewa a lokacin dana fara kyallara ido
na ganka a take naji wani abu ya soki kahon
zuciyata ban gane ko mene ne wannan abu
267
TASKARNOVELS.COM.NG
daya soki zuciyar tawa ba sai bayan munci gaba
da tafiya sannan na gane ashe so ne gami da
haduwar jini, kaine namijin farko daya taba
burgeni a rayuwata har naji na daina burin na
bar duniya. Koda jin wannan batu sai jarumi
Hasnalu yayi murmushi sannan ya ce yake
wannan yar sarki kiyi sani cewa tundaga lokacin
da kika ceci rayuwata kika tsaida jinin dake
zuba a cikina, kuma naga kina hawaye saboda
damuwa bisa halin dana shiga, kuma kika gode
wa Ubangijina sakamakon farfadowata, sai naji
nan take nim sonki ya shigeni, tabbas nayi
matukar mamaki da har na kamu da sonki
saboda acan garinmu naki yarda na baiwa
kowacce ya mace soyayyata saboda na kudira a
raina cewa sai na cika burin da mahaifina ya
kasa cikawa na jaddada addini musulunci a
wannan nahiyoyi naku, sannan zanyi aure kuma
har sai bayan naga inda kabarin mahaifin nawa
yake, ko kuma na samu labarin yadda aka yi ya
mutu, ina ji a jikina cewa a sanadiyyarki zan cika
burin nawa, kuma da izinin ubangijina sai kin
zama matar aure bisa ka'idar addinina. Sa'ad
da Hasnalu ya zo nan a zancensa sai gimbiya
Hursiyya ta cika da tsananin farin ciki, ta
268
TASKARNOVELS.COM.NG
dubeshi cikin murmushi ta ce ya kai abin
kaunata ka yi sani cewa a halin yanzu ka cika
sharadin dake tsakaninmu na ukun, tunda kayi
gagarumin abin al'ajabi na kashe munafiki aljani
Radiyan da taimakon ubangijinka, ni din nan
ganauce na jiyau ba dan haka na bada gaskiya
ga addinin musulunci, yanzu ba tare da wani
bata lokaci ba in so ka shigar da ni cikin wannan
addini naka na Musulunci. Koda jin wannan
batu sai shima jarumi Hasnalu ya cika da
tsantsar farin ciki, ba tare da wani jinkiri ba
kuwa Hasnalu ya karanta mata kalmar shahada
ta maimaita. Faruwar hakan keda wuya sai
Hasnalu ya mike tsaye yana mai mayar da
takobinsa daya kashe aljani Radiyan cikin
kufenta suka nausa izuwa cikin daji da sauri
kuma gudu-gudu tare da barin gawar aljani
Radiyan anan. *********** Acan sansanin
yaki kuwa lokacin da ttsanani yai tsanani sai
labari ya sha bamban domin kowacce rundun
dimaucewa ta yi, hankalinsu ya gushe banda
kashe junansu babu abinda suke yi, kuma ragas
ake yi a wannan aki dan ido bai isa ya tantance
bangaren dake samun nasara ba. Acan
bngaren sarki Maharaz da sadauki Himalu kuwa
269
TASKARNOVELS.COM.NG
abin abu kyan gani domin kowanne ya sari
abokin gwaminsa sau akalla bakwai bakwai,
kowannensu jini ne ke zuba daga jikinsa, tun
suna iya kaiwa juna hari har sai da takai cewa
sun kasa, dan haka da kansu suka zubar da
makamansu tare da sulalewa kasa cikin wani
irin mugun yanayi wanda babu tabbacin zasu
kai labari. A bangaren manyan zakuna kuwa
wato sarki Dujalu da kuma jarumi Imnal abin ya
kazanta fiye da na kowa saboda sai da suka
shafe fiye da sa'a uku suna kaiwa juna sara da
suka cikin matukar zafin nama juriya gami da
bajinta ba tare da dayansu ya samu nasarar
koda lakutar jikin daya ba, take a lokacin ajiya ta
riskesu dan haka sai suka j da baya suna masu
yin haki kamar zakaru, babban abin mamaki
shine babu wanda yake iya kawo masu hari
acikin mayan, kai ba wanda ma ya yarda ya rabi
inda suke saboda kura ta san gidan mai babbar
sanda. Bayan sarki Dujalu da Imnal sunyi
kallon-kallo a tsakaninsu cike da harar juna
gami da mugun nufi a cikin zukatansu har izuwa
tsawon yan dakiku, sai suka sake rugowa da
gudu suka kacame da sabon azababben yaki
cikin sabon salo, a wannan karon kowannensu
270
TASKARNOVELS.COM.NG
yana kai sara da suka cikin tsalle-tsalle gami da
kwance-kwance, kuma suka dinga hadawa da
kai naushi hannu da kafa. Faruwar hakan keda
wuya sai rawa ta sauya tunda kidama ya sauya,
nan take suka fara samun damar cuttar da
junasu, a duk sa'ad da sarki Dujalu ya samu
nasarar naushin Imnal a fuska, kafin ya sake
kaima masa wani naushin shima imnal ya rama
wannan naushi, nan da nan kuwa suka hada wa
junansu jini da majina, suka fara luguiguita
juna, ana cikin haka ne sarki Dujalu ya sammaci
Imnal ya soka masa takobinsa a gefen saman
kirjinsa, wanda har sai da takobin ta bullutso ta
gadon bayansa. Imnal ya kwarara uban ihu
saboda tsananin zafi da yaji, Dujalu yasa
kafarsa ya doki kirjin Imnal jini yayi tsartuwa
kuma Imnal yayi sama tare da fadowa kasa
cikin tsananin galabaita yana numfashi gami da
shure-shure kamar wanda ranshi zai fita. Cikin
tsananin murna sarki Dujalu ya bushe da wata
mahaukaciyar dariya ta mugunta ya taho izuwa
kan Imnal tarw da raba kafafunsa biyu akan
Imnal din yana mai daga takobinsa sama da
nufin ya cakata a cikin Imnal. Ba zato ba
tsammani sai kawai yaga imnal ya tashi zaune,
271
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin zafin nama na gaban kwatance shima ya
sokawa Dujalu tasa takobin a kirji a daidai inda
shima ya sokeshi ya bullutso har gadon
bayansa. Nan fa Imnal ya daddage iya karfinsa
tare da naushin sarki Dujalu da daya hannun
nasa, a take dujalu yayi sama a lokacin da
Imnal ya zare takoninsa daga cikin kirjin sarki
Dujalu aikuwa sai jini ya kama bulbulowa daga
cikin kirjin, Dujalu ya fadi kasa magashiyan yana
kakarin mutuwa. Imnal ya sake mikewa da
nufin ya mike taaye amman sai jiri ya debeshi ya
sake faduwa a kasa ya baje, nan fa aka rasa
wanda zai iya sake tashi tsaye daga cikinsu,
gashi dai suna cikin wani irin mugun hali na daf
da mutuwa amman saboda naci gami da taurin
rai kowanne a cikinsu burinshi shine ya tashi
tsaye domin yaje ya kasara kashe abokin
gabarsa amman sai gashi abu ya gagara. Ganin
sun kasa mikewa tsaye ne yasa suka fara tafiya
da jan ciki suna masu tunkarar junasu, sai da ya
rage saura baifi taku uku ba a tsakaninsu sai
duk su biyun suka sume a lokaci guda. A
wannan lokacin gaba-daya dakarun dake a
wannan filin yakin sun mutu babu sauran
mutum daya daga cikin rundunonin wanda ya
272
TASKARNOVELS.COM.NG
tsira da rayuwarsa. Adaidai wannan lokacin ne
kuma jarumi Hasnalu da gimbiya Hursiyya suka
karaso filin yakin a guje,tun daga nesa gimbiya
Hursiyya ta ga babu mutum ko daya a filin yakin,
duk inda ta hanga sai dai taga gawarwaki fululu
dan haka sai ta ringa