x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - MAZAN JIYA 4

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 68055 words

Category: Adventure Stories

Views 184

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
LUJARA: Page 141 zidane kd:
page 142
173

TASKARNOVELS.COM.NG

Acan dajin darul Hushushul maut kuwa aljani
Raugatul Aguwanu Ya shafe sama da sa a tara
yana bincike a cikin madubin tsafinsa domin ya
tabbatar da gaskiyar al amarin da su boka
sadusa suka zo masa da shi amma sai ya kasa
ganin komai. A karshe ma daya matsa bincike
sai madubin tsafin nasa yayi bindiga ya
tarwatse. Al amarin da matukar firgitashi ke
nan ya sake sallamawa boka sadusa. Da
sassafe su boka sadusa suka farka daga barci a
cikin wannan kogo na aljani Raugatul Aguwanu,
suna bude idanuwansu suka ga aljani Raugatul
Aguwanu a zaune yagama shirin tafiya yana
sanye da bakin sulke na yaki irin nasu na aljanu
sannan yana rike da wani dogon mashi gami da
garkuwa. A wannan lokaci idan mutum ya kalli
ajani Raugatul Aguwanu sai yayi zaton cewa shi
kadai zai iya yakar duniyar gaba dayanta sbda
tsananin girmansa da kwarjinsa: Nan take
Raugatul Aguwanu ya dubi boka sadusa yace
na gama dukkan binciken da zan yi kuma na
gamsu da duk abinda kazo mini da shi sbda
174

TASKARNOVELS.COM.NG
haka yanzu ni nagama shirin wannan tafiya ku
kawai nake jira. Page 144: Tabbas da na zauna
yaki yazo yacini har gida gwara naje na tari
yakin. Koda jin wannan batu sai boka sadusa ya
kyalkyale da dariya mugunta sannan yace ai
kuwa kayi wa kanka riga kafi domin da cin dare
daya kumburin ciki gwara dayawa tunda a dade
anayi sai gaskiya. Batare da bata wani lokaci ba
su boka sadusa suka shiga harhada
kayayyakinsu: Suna cikwannan hali ne aljani
Raugatul Aguwanu ya kyalara ido ya kalli
Gimbiya Shalbirat ya ganta a cikin ainahin
siffarta ta mutum nan take yaji ya kamu da
tsananin sonta fiye da ko yaushe, sannan sai
takaici ya rufeshi ya fara tunani zuci, yana mai
aiyanawa aransa cewa idan fa yayyi wasa
wannan karon shi kenan an rabashi da
shalbirat. Nan take ya dubi boka sadusa a
fusace ya ce yakai wannan takadarin boka shin
mun yi yarjejeniyane da kai akan cewa zaka
fiddo Gimbiya shalbirat daga cikin kejin dana
sata har ka dawo mata da ainahin siffarta?
Sadusa yadakawa Raugatul Aguwanu tsawa
yace tsakanin ni da kai wanene yafi sanin
abinda yadace? Kada kasake yi mini shisshigi a
175

TASKARNOVELS.COM.NG
cikin aikina, ' domin duk abin da kaga nayi shi
ne daidai kuma kauce masa zai janyo
rugujewar dukka shirinmu. Page 145 zidane
kd: koda jin wannan batu sai jikin aljani
Raugatul Aguwanu yai sanyi ya sunkui da kansa
kas sanna yace toni zan fita waje dommin na
sami damar bude fuka fukaina gaba daya zan
kwanta a kasa na rankwafa da zarar kunfito sai
ku hau kaina ku zauna ni kuma na tashi daku
sama mu kama tafiya. Ina mai tabbatar muku
dacewa zan kaimu bakin tekun bahar sufiya a
cikin abinda bai wuce sa a hudu ba amma fa
bisa sharadi guda : Cikin mamaki boka sadusa
yace wannen irin sharadi kenan? Raugatul
Aguwanu yace ai dama tunda farko baku yi dani
cewa cikin sansanin yaki zan kai ku ba: lallai
zan sauka ne a can bayan sansanin nesa da shi
inda ba za a hangomu ba sai dai mu hangosu.
Koda jin wannan batu sai boka sadusa ya bushe
da dariya yace haba ya kai Raugatul Aguwanu
yaya kana matsayin sarkin sadaukai na aljanun
duniya amma ka dinga jin tsoro? Raugatul
Aguwanu yace ai komai isar aljani a wannan
zamani dole ne yaji tsoron sarki dujalu.da sarki
maharaz sbd sun kure sun kai kololuwa a
176

TASKARNOVELS.COM.NG
matakin karfe na sihirin tsafi. Sadusa yace to
shi kenan naji mazza kaje wajen ka jirau gamu
nan fitowa. page 146 Nan take Raugatul
Aguwanu ya fice daga cikin kogo dutsen yana ai
waigen gibiya shalbirat cikin wani irin kallo mai
nuna tsantsar kaunarsa a gareta ita kuwa sai ta
galla masa harara tana ai da masa martanin
kallon na tsananin kiyayya yadda inda za a
danne mata shi zata iya sa wuka ta yankashi,
musamman idan ta tuno da yankan kaunar da
yai mata ya rabata da kasarsu da iyayenta ya
ajiyeta acikin keji kamar tuntsuwar tsawon
shekaru goma sha tara. Da fitowar aljani
Raugatul Aguwanu daga cikin kogon dutsen sai
ya tsaya a tsakiyar babban filin dake gaban
kogon ya rankwafa kasa yana mai bude fuka
ffukansa cikin nishadi. Girman fuka funkansa
guda daya ya isa ya yiwa mutu dubu daya rumfa
su tsira daga zafi rana da saukar uwan sama. A
dai dai wannna lokaci ne aljanin Raugatul
Aguwanu yaji wata irin iska ai dan karen sanyi
da dadi ta busa har izuwa cikin kunnensa nan
take ya lumshe idanu ya kama gyangyandi.
Ashe wannan iska mai dadi da sanyi ba iska
bace daga allah iska ce ta tsafi kuma bawani
177

TASKARNOVELS.COM.NG
bane ya busata face aljani Radiyan wanda ya
dauko Gimbiya Hursiya daga can birnin sarki
dujalu domin ya mayar da ita can sansanin yaki.
A wannan lokacin aljani Radiyan da Gimbiya
Hursiya na can labe a cikin duhuwar bishiyoyi
suna hango abinda ke faruwa ga aljani Raugatul
Aguwanu: Koda suka gaya kama gyangyadi sai
suka fitonda sauri daga maboyarsu suka ruga
da gudu izuwa inda yake: Da zuwa suka daka
tsalle suka hau kan farsa suka cigaba da gudu a
knsa har suka hau kan kafadarsa sannan suka
daka tsalle suka fada cikin kunnensa na hagu:
Nan fa suka ji kamar a cikin RIJIYA GABA DUBU
jefasu

Sai da suka shafe rabin saa suna ta fadwa can
cikin kunnen sannan suka iso karshen mai
tsananin duhu: Page 147 zidane kd

sai da boka Radiyn ya haskake cikin kunnen da
hasken wata sandar tasafi sannan suka iya
ganin junansu
178

TASKARNOVELS.COM.NG

Nan fa Gimbiya Hursiya ta dubi gabas da
yamma kudu da area kuma yadubi sama
dakasa ta gaba kamar a cikin gidan sarautarsu
aka sata sbda tsanani girman cikin kunnen

Raugatul Aguwanuna na cikin yin wanna
gyangyandi ne yaji kuma ana sosa masa
kunnen: sbda tsananin dadi da yaji sai ya dada
rufe idanunwansa yayi lamo kamar bashi da rai
ko kadan ma bai yi tunanin abinda ke sosa
masa kunnen ba

A zotonsa waannan iskar mai busowa da karfi
ce tke shiga cikin kunnen nasa

Page 148 Yana cikin wannan hali ne yaji an
daka masa tsawa: A firgice ya bude idaninsa ya
mike zaune sai yaga she su boka sadusa ne
tsaye a gabansa: sadusa ya dubeshi yace yaya
kai da zamuyi doguwar tafiya tare da kai yanzu
179

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma zaka buge da gyan gyadi? Raugatul
Aguwanu yace ai dole ne na yi barci: Shin baka
jin daddadar iskar da take kadawa bane?
Sadusa yayi tsaki sannan yace kaidai ka cika
shirirta da shirme

To ai sai ka yi shiru gamu mun fito tafiya
zamuyi: nan take aljani Raugatul Aguwanu ya
dada rankwafawa kasa boka sadusa Halyal da
Gimbiya Shalbirat suka hau kan gadon bayansa
suka zauna: Zamansu ke da wuya sau ya bude
fuka fukansa ya luluka da su izuwa can
kololuwar sama ya kama tsala gudu yana keta
giza gizai tamkar gudun taurariwa mai wutsiya

A Dai dai wannan lokaci ne aljani Raugatul
Aguwanu yaji dan motsi a cikin kunnensa har ya
daga dan yatsansa guda zai cusa a cikin
kunnen yaji an fara masa susa

Page 149 zidane kd
180

TASKARNOVELS.COM.NG

Dan karen dadi daya ji ne yasa ya fasa sanya
dan yatsan nasa ya saki jikinsa cikin kwanciyar
hankali ya cigaba da tsala gudu: A Wannna
lokacin gimbiya Shalbirat ta kamu da tsananin
farin ciki takama murmushi: Boka sadusa ya
dubeya cikin mamaki yace ke kuwa mene ne ya
saki farin ciki haka har kike ta murmushi da
yake baki? Shalbirat tace gaba ai dolene na
kasance a cikin farin ciki, tunda rabona da
gannin fili haka ba a cikin keji ba yau shekara
goma sha tara kenan: Da jin haka sai tausayi ya
kama sadusa da Halyal har idanunsu suka ciko
da kwallah: A cikin kunnen aljani Raugatul
Aguwanu kuwa, Boka radiyan ya dubi Gimbiya
Hursiya ya ce bari na karasa miki Labarin da
dan uwanki sarki dujalu bai karasa miki ba
hakan zai debe miki kewa kafin mu karasa bakin
kogin bahar sufiya: Cikin tsananin mamaki
Hursiya ta dubi boka Radiyan ba tare da ta iya
furta masa komai ba: Boka Radinyan yayi
murmushi yace kada ki yi mamaki akan
lamarina domin na wucce dukkan tunaninki na
san abinda baki sani ba zaki gasgata hakan idan
kiyi la akari da abubuwan da suka faru
181

TASKARNOVELS.COM.NG
tsakaninmu tunda haduwarmu kawo izuwa
yanzu da muke cikin kunnen aljani Raugatul
Aguwanu

page 150 Gimbiya Hursiya ta gyada kai kawai
cikin tana sauraron boka Radiyan

Shi kuma ya cigaba da dora mata Labarin
Kamar Haka

: * * * MAZAN JIYA! (4) Kashi na sittin da
biyar (65) ABDUL'AZIZ SANI MADAKINGINI
(King ofAdventure Story) . LOKACIN da jarumi
SHADDADU ya cigaba da tafiya bisa wannan
tsuntsun tsafi, ga Mashin Galilul Haras daure a
gadon bayansa kuma gashi a cikin gagarumar
shigar Yaki, sai tsuntsun ya ci gaba da keta gizagizai a sararin samaniya ba kakkautawa. Sai
182

TASKARNOVELS.COM.NG
da suka shafe sa'a biyar da rabi suna tafiya
sannan tsuntsun ya sauko kasa-kasa da kansa,
ashe wani babban Birni suka tunkaro a
gabansu. Koda ya rage bai fi zira'i goma ba
tsakaninsu da Birnin sai tsuntsun ya sauko
kasa. Shadaddu ya sauko daga kan tsuntsun.
Saukarsa ke da wuya sai tsuntsun ya rikide ya
zama dan karami kuma ya tashi sama ya dira a
kafadar Shaddadu. Faruwar hakan ke da wuya
sai Shadaddu ya kunna kai izuwa kofar wannan
Birni ba tare da shakkar komai ba. Da isarsa
bakin kofar garin ya iske masu gadi wadansu
Dakaru samudawan karti kimanin su arba in a
tsaitsaye cikin shigar Yaki. Ko kallonsu
Shadaddu bai yi ba ya nufi bakin kofar Garin
wacce take a rufe. Su ma Dakarun sai suka yi
kamar ba su ganshi ba, domin ko kallonsa ba su
yi ba. Shi ma sai ya ki ya yi musu magana ya je
ya kwankwasa kofar domin a bude masa duk da
cewa ya ga daya daga cikin masu gadin a zaune
daf da bakin kofar bisa wata kujera rike da
katuwar Kuba. Shadaddu ya kwankwasa kofar
har sau uku, amma shiru ba a bude kofar ba.
Kawai sai ya ji masu gadin sun kama yi masa
dariya. Daya daga cikinsu ya dube shi ya ce,
183

TASKARNOVELS.COM.NG
"Ya kai wannan sakaran bako, shin ba ka da
da'a ne ko kuwa ba a koya maka ladabi ba ne a
gidanku? Idan haka halayyarka take a can
garinku to mu nan ba haka ba ne. Amma idan
kai Kurma ne sai ka gaya mana". Kawai sai
Shadaddu ya kalli mai maganar yai masa
murmushi ba tare da ya maida masa da
martanin maganar ba. Kawai sai ya ja da baya
kadan ya daga ya daki kofar garin wacce ta
kasance mai kauri da nauyin gaske ta zallar
bakin karfe. Nan take kofar ta jijjige ta fada ciki.
Al'amarin da yai matukar firgita Dakarun ke nan
suka zazzare mnakamansu amma kuma suka
kasa afka wa Shadaddu sakamakon ganin
wannan gagarumar jarumtaka da ya yi.
Shadaddu ya waigo ya dubi Dakarun ya yi musu
murmushi a karo na biyu sannan ya juya ya
shige izuwa cikin Birnin. Nan fa Dakarun nan
suka kama duru-duru suka rasa abin da za su yi
tsakanin su bi wannan bakon saurayi su yake
shi ko kuma su kai rahotonsa izuwa ga
Sarauniyarsu? Nan dai suka yanke shawarar
daya daga cikinsu ya ruga izuwa fada ya kai
labari. Nan take kuwa aka bi wannan shawara.
Lokacin da Shadaddu ya kunna kai izuwa cikin
184

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan Birni sai ya zama abin kallo, duk inda ya
ratsa sai ya ga mutane har fitowa suke daga
cikin gidajensu suna binsa a baya, musamman
mata domin dimaucewa suka rinka yi. Abin da
yai matukar bai wa Shadaddu mamaki ke nan,
domin shi bai ga abin kallo ba a tare da shi.
Abin da Shadaddu bai fahimta ba shi ne
tsananin kyawunsa da kwarjinihsa ne ya sa ake
kallonsa. Koda ya ga kallon da ake yi masa ya
yi yawa, kuma jama'a dada karuwa suke ana ta
binsa sai ya juya ya kwarara uban ihu ya yi
kamar zai zare Takobinsa. Nan fa jama'a suka
tarwatse cikin firgita suka kama gudu. Kafin
cikar dakika biyar babu kowa akan hanyar.
Shadaddu yai dariya ya ce, "Ashe ma duk
matsorata ne a garin. Kawai sai ya ci gaba da
tafiya. Burinsa kawai shi ne ya ga kasuwa ko
inda ake siyar da abinci domin yunwa ta fara
damunsa ga shi bai taho da wani abinci ba a
cikin jakar guzurinsa sai tarin Dirhami mai
yawan gaske. Haka dai ya ci gaba da tafiya
yana kutsawa ta cikin lunguna da sako-sako na
Garin, amma kuma bai ga mutane sun daina
kallonsa ba, sai dai ba sa biyo shi a baya
sakamakon ganin rashin annuri akan fuskarsa,
185

TASKARNOVELS.COM.NG
kai da gani ka san cewa mutane suna shakkarsa
saboda ganin irin kirarsa ta manyan sadaukai.
Yana cikin dube-dube ne ya hango wani gida
wanda aka yi rubutu a jikin saman kofarsa
kamar haka. 'GIDAN ABINCI'. Koda ganin
wannan rubutu sai murna ta kama Shadaddu ya
kunna kai izuwa cikin gidan. Yana shiga ya iske
mutane da yawa a zazzaune bisa kujeru a
karkashin tebura suna ta cin abinci kala-kala.
Lokaci guda kowa ya dago kai ya kalle shi
sannan aka kawar da kai aka ci gaba da cin
abincin babu wanda ya sake dubansa.
Al'amarin da ya daurewa Shadaddu kai shi ne
gaba dayan mutanen da ke cikin gidan abincin
maza ne, kuma karti majiya karli, ababan
kwatance. Mace guda daya ce jal a cikin gidan,
kuma ita ce mai bayar da abincin. A can gefe
daya bisa wani dogon tebur mai dauke da
tukwanen abinci kimanin guda goma.
Shadaddu ya sake yin nazarin kartin da ke cikin
gidan ya ga kowannensu yana da siffa irin ta
mayaki duk da cewar babu makamai a jikinsu.
Nan take jikin Shadaddu ya ba shi cewar akwai
tuggun da ake son shirya masa amma sai ya
basar ya nuna ba ya tunanin komai. Kai tsaye
186

TASKARNOVELS.COM.NG
ya nufi inda mai bayar da abincin take. Da zuwa
sai ya bude jakarsa ya dauko Dirhami goma ya
ajiye a gabanta sannan ya nuna mata irin kalar
abincin da yake so. Kawai sai ya ga ta kura
masa idanu ko kiftawa ba ta yi har sai da ya doki
tebur din da ke gabanta sannan ta dawo cikin
hayyacinta. Ashe tsananin kyawunsa ne ya
dimautata ta sandare kamar Gunki. Koda ya
buga teburin ta dawo cikin haiyacintae ta ga ya
ajiye ma ta kudi akan tebur sai ta gan nufinsa.
Hannunta na karkarwa ta dauki cokali da faranti
ta zuba masa abincin. Shadaddu ya karbi
abincin ya je ya zauna akan wani tebur wanda
babu kowa akai ya fara cin sbincia. Yana cikin
cin abincin ne ya ga wadannan mutane da ke
cikin gidan sun fara mimmikewa tsaye suna
zaro makamai a jikin karkashin tebur din da
suke zaune. Ko motsawa Shadaddu bai yi ba,
da ma ta wutsiyar idanu ya kalle su, kawai sai ya
cigaba da cin abincinsa. Koda wannan mace
mai bayar da abinci ta ga an fara zaro makamai
sai tavyi wuf! Ta ruga izuwa cikin wani ɗaki ta
kullo kofa. A sannan ne aka rufo kofar shigowa
gidan gabadaya. Hakan ba ta sa Shadaddu ya ji
ko dar ba! Kawai sai ya ci gaba da cin abincinsa.
187

TASKARNOVELS.COM.NG
Lokaci guda gaba dayan kartin suka afkawa
Shadaddu da nufin su daddatsa shi. Cikin
masifaffen bakin zafin nama Shadaddu ya zare
tasa Takobin, ya yi wata irin katantanwa a
tsakiyarsu ya tarwatsa su da karfin tsiya. Nan
fa aka ruguntsume da Yaki, suka yi masa
rubdugu suka rinka kai masa sara da suka ta ko
ina. Shi kuma ya yi ta kare hare-harensu amma
sai ya dinga mai da martani da bugu da naushi
maimakon da makami. Nan fa ya rinka hada
musu jini da majina, amma saboda naci da
juriya irin na maza masu Jarumta ko sun fadi
kasa sai ka ga sun mike zumbur! Sun ci gaba da
kai masa munanan sara da suka, amma ba a
samu wanda ya sami nasarar koda lakutar
jikinsa ba. Shi kuwa Shadaddu sai ya nuna
tsagwaron sadaukantaka da fifikon yaki, ya ki ya
sari jikin dayansu da makami. Haka dai ya ci
gaba da gabza musu naushi da musu bugu
hannu da kafa har sai da ya bazar da gaba
dayansu a kas, bayan an kakkarya tebura da
kujerun da ke gidan, an lalata komai ya zamana
cewa komai ya ragargaje. á Sai ga shi karti
sama da mutum arba'in kwance kas sun yi lagalaga sun kasa tashi. A sannan ne wannan
188

TASKARNOVELS.COM.NG
mace mai siyar da abincin da ta ji an daina
kwarmazuwa ta bude dakin da ta shiga ta бuya
ta fito da sauri ta ga Shadaddu ya dauki tulun
giya ya kafa a bakinsa yana ta sha. Sai da
ruwan giyar ya kare kaf sannan ya wurgi da tulun
ya fashe. Ko alamar buguwa bai yi ba ya dubi
macen ya ce, "Ina cigiyar wata Jaruma mai suna
ZIYA'UL HAK ko kin santa?" Cikin alamun tsoro
matar ta dubi Shadaddu a lokacin da jikinta
gabadaya ya kama tsuma ta ce "Ba mu taba jin
ma mai irin wannan suna ba a garin nan ya kai
wannan bakon saurayı ma'abocin kyau da
jarumtaka. Wane ne kai, kuma daga ina ka fito?"
Koda jin wannan tambaya sai Shadaddu ya yi
mata wani guntun murmushi sannan ya ce, "Ni
kaina ban san amsar tambayar da kika yi min
ba!" Koda gama fadın haka sai ya sake bude
jakar guzurinsa ya dauko dirhami ashirin ya
mika mata ta karba sannan ya ce, yanzu
Makwanci nake bukata . Matar ta yi murmushi
ta ce, "Samari ka sami makwanci har ma da mai
debe maka kewa. Shaddadu ya yi ma ta wata
irin harara wacce ta sa zuciyarta ta buga da
karfi, ya dube ta a fusace ya ce, "Ba na bukatar
mace a kusa da ni". Cikin rawar jiki ta ja
189

TASKARNOVELS.COM.NG
Shaddadu suka fice daga cikin wannan gida
suka kunna kai izuwa cikin wani lungu. Ai
kuwa suna shigewa wannan lungun sai ga
Dakarun gidan Sarautar garin sama da mutum
dari biyu sun shigo unguwar a guje rike da
makamai suna neman Shaddadu domin tuni
labari ya isa ga Sarauniyar garin cewa ga wani
bakon Sadaukin saurayi can ya ɓalla kofar gari
da karfin tsiya ya shigo kuma har ya fara barna a
cikin gari. Bisa wannan dalili ne Sarauniyar ta
taso Dakaru domin su zo su kamo wannan
bakon Jarumi a mace ko a raye.. Lokacin da
Dakarun Sarauniya suka je wannan gidan abinci
suka iske wadannan karti arba'in a kwakkwance
mashe-mashe sun sha duka kuma suka ga
komai na gidan a ragargaje sai suka cika da
mamakin yadda za a ce wai mutum daya ne ya
yi wannan aiki. Nan dai suka shiga neman
Shaddadu amma ko alamarsa babu. Da suka
ga babu shi sai suka koma can fadar Sarauniyar
tasu suka sanar da ita cewa ba su ga wannan
bakon saurayi ba. Lokacin da Sarauniya
ZUBAINA IBINI LAIYARA ta ji cewar ba a ga
bakon saurayin ba sai ta bushe da dariya.
Al'amarin da yai matukar bai wa kowa mamaki
190

TASKARNOVELS.COM.NG
ke nan a fadar, aka zuba mata idanu kawai.
Daga can kuma sai ta tsuke bakinta ta murtuke
fuska ta ce, "Tabbas BABBAN GORO sai
MAGOGIN KARFE. Hakika babu wanda zai iya
tarar wannan bakon saurayi face ni. Da kai na
zan yi shiri na tafi farautarsa a cikin garin nan.
Na yi bincike a kansa na gano cewa yana da
matukar karfin sihiri da jarumtaka, to amma duk
abin da yake takama da shi ya zo gidansa. Tun
da na hau kan karagar wannan mulki a wannan
Birni namu na HADIYAS ba a taɓa samun wani
tsagera da ya zo mini Birnina babu izini yakarya
mini kofar gari kuma ya je gidan abinci ya yi wa
Dakaruna dukan tsiya. Hakika idan na kama
wannan bako sai na gana masa azaba mai
radadi har izuwa lokaci mai tsawo sannan na
yanke masa hukuncin kisa." Koda gama
wannan jawabi sai Sarauniya Zubaina ta mike
tsaye a fusace ta shige izuwa cikin gidan
Sarautar, a sannan ne fada ta watse kowa ya
tafi yana fadin albarkacin bakinsa. Wasu suna
cewa, "Lallai wannan bako ya tabo tsuliyar
Dodo". Wasu kuma suna cewa, "Ai saukin
wannan bako kawai ya samu ya sulale ya gudu
daga garin saboda kowa ya san cewa Sarauniya
191

TASKARNOVELS.COM.NG
Zubaina ta kasance BASADAUKIYA ta gaban
kwatance, kuma hatsabibiyar Bokanya ce
wadda babu kamarta a
End Ads