ce, "Ya kai
Marhabul Zaurus ina son ka sauke wannan doki
da ke bayanka ka tafi izuwa can inda Zarina ta
fada rami ka dauko ta tare da gawar dan uwanta
ka kawo su nan gare mu.
160
TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'adda Aljani Marhabul Zaurus ya ji wannan
umarni sai fuskarsa ta yamutse kamar zai fashe
da kuka sannan ya dubi Muzaffar cikin tsananin
damuwa ya ce, "Ya shugabana shin ka dubi halin
da nake ciki kuwa yanzu? Na rasa rabin fukafukina guda, daya fuka-fukin kuma ya tsage. Ina
tabbatar maka da cewa yanzu ba zan iya
daukarku ba ku duka har ma na yi doguwar
tafiya da ku a sararin samaniya."
Koda jin haka sai Boka Muzaffar ya sake dakawa
Aljani Marhabul Zaurus tsawa a karo na biyu ya
ce, "Ai ba cewa na yi ka dauke mu yanzu mu ci
gaba da tafiya ba, cewa na yi ka je ka dauko
Gimbiya Zarina da gawar dan uwanta kawai ka
dawo da su nan."
Da jin haka sai Aljani Marhabul Zaurus y mika
hannunsa guda ya dauke dokin Shaharan daga
kansa ya sauke shi a kas sannan ya bude fuka.
fukansa da kyar ya yunkura ya tashi sama yana
tambal-tambal kamar zai fado kasa. Kai da gani
161
TASKARNOVELS.COM.NG
ka san cewa ba karamin namijin kokari ya yi ba
har da ma ya iya tashi sama.
A haka dai ya luluka izuwa can sama yana tsala
matsanaicin gudu har ya ɓace da gani. Bayan
kamar dakika dari da ashirin kacal sai ga Aljani
Marhabul Zaurus ya dawo dauke da Zarina da
kuma gawar dan uwanta rungume akan kirjinta
ta kankame gawar tana ta kuka.
Al'amarin da ya kara karya zukatansu ke nan, su
duka kowa ya kamu da tsananin tausayin
Gimbiya Zarina aka kama kuka.
Sai a wannan lokaci ne Zarina ta lura cewa
Shaharan da Haiman sun rasa hannayensu ďai
ďai. Nan fa bakin ciki ya sake lulluɓe ta, ta fashe
da sabon kuka, ya zamana cewa babu wanda ba
ya zubar da hawaye a wajen.
162
TASKARNOVELS.COM.NG
Nan dai masu sauran kuzari a jikinsu suka haka
rami aka binne Sarkin Farisa sannan aka yanke
shawarar a zauna a wajen har tsawon mako uku
sannan a ci gaba da tafiya.
Boka Muzaffar ne ya kawo wannan shawara
Koda jin haka sai jaruma Rahila ta ce, "Wai shin
mene ne ma amfanin ci gaba da wannan tafiya
tamu?
Shin har yanzu kuna sa rai ne cewa za mu isa
kogon DARUL IKSINA a raye ne? Ku dubi fa
halin da muke ciki a yanzu, wasunmu sun
nakasa, nakasar da har abada babu warkewa
don haka fiye da rabin karfinmu babu shi. Dajin
da ya rage a gabanmu shi ne dajin da ya fi
kowanne daji haɗari, inda wannan katuwar
Kunama take mai tsananin gudun tsiya wacce
babu wanda muke sa ran zai iya tsere mata a
cikinmu face jarumi Shaharan, kuma ga shi shi
ma ya sami nakasa ya rasa hannunsa guda. Ta
yaya kuke tsammanin zai iya gudun da zai iya
tserewa wannan Kunama a haka har ya ja ta
izuwa cikin wannan kogi inda za ta hallaka?"
163
TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'adda Rahila ta zo nan a zancenta sai kowa ya
yi shiru aka rasa wanda zai ce kala. Daga can sai
Boka Muzaffar ya dubi jarumi Shaharan ya ce,
"Ya kai abin dogaronmu a cikin daji na biyar, ka
ji abinda Rahila ta ce, shin gaskiya ne ba za ka
iya yin gudu ba kamar yua ya kamata
sakamakon wannan nakasa da ka samu?"
Koda jin wannan tambaya sai Shaharan yai
ajiyar zuciya ya ce, "Ko shakka babu rashin
Wannan hannu nawa sai ya rage mini karfin
guduna Sosai, to amma ai mai rai ba ya fid da
tsammanin sa'a da rabo. Wannan lalura da ta
same ni ba za ta sa mu karaya ba. Ina son mu
kasance masu juriya da karfafar juna duk da
cewa masifun da suka same mu a cikin wannan
tafiya sun karya mana zuciya. Yanzu ga Shadira
ta rasa dan uwanta Masnur, Zarina ma ta rasa
dan uwanta Sarkin Farisa. Duk da hakan yanzu
mu shida muka rage masu son cika burinsu a
kogon Darul Iksina. Ni ina son dokina ya warke
daga cutar da ke addabar kafafunsa. Haiman
yana son matarsa ta warke daga cutar makanta,
164
TASKARNOVELS.COM.NG
Imran yana son mahaifiyarsa ta warke daga
gurguntaka. Sarkin Laffaru da Boka Muzaffar
suna son su mallaki Aljani Maruful Dauwaz, ita
kuma Gimbiya Rahila tana son ta auri Sarki
Laffaru bayan ya mallaki Maruful Dauwaz. Ku
duba fa ku gani a halin yanzu Shadira da Zarina
ba su da sauran buri a cikin wannan tafiya tamu
amma hakan bai sa sun ki ci gaba da yin tafiyar
ba, saboda me mu kuma za mu karaya akan ci
gaba da tafiyar?"
Lokacin da Shaharan yazo nan a zancensa sai
kowa ya ji dukkan tsoro ya kau daga zuciyarsa,
suka ji ba su ki ba ma a cigaba da tafiyar nan
take in ba don akwai bukatar su yi jinyar
jikkunansu ba. Haka dai aka zauna ana jinyar
juna ya zamana cewa Lumaira tana matukar
kula da mijinta, ba ta barinsa ya yi komai da
kansa, ita ke yi masa saboda rashin hannu guda.
Shi ma Shaharan Zarina ce ke dawainiya da shi.
A lokacin ne soyayya mai karfi ta kara kulluwa
tsakanin Shaharan da Zarina har suka ji ba za su
iya rabuwa ba daidai da sa'a daya.
165
TASKARNOVELS.COM.NG
Imran da Shadira ma sai suka sake shakuwa da
juna ainun, ya zamana cewa dare da rana ba sa
rabuwa. Mahaifiyar Imran ce kadai take shiga
tsakaninsu a wasu lokutan tana yi masa hidima.
A kullum sai Zarina ta shafe sama da sa'a biyar
zaune a gaban kabarin dan uwanta Sarkin
Farisa tana kuka da begensa. Shaharan ne kadai
ke iya rarrashinta ya tashe ta daga gaban
kabarin ya kai ta cikin tantinta ya zaunar da ita
sannan ya ba ta abinci da hannunsa ta ci har sai
ya ga ta koshi sannan shi ma yake cin abincin.
A ɓangaren Gimbiya Rahila da Sarki Laffaru
kuwa, suma soyayya ce ta rinka haɓaka kai kace
bai girme ta ba a shekaru nesa ba kusa ba. Kuma
ganin yadda take matukar kula da shi ne gami
da ganin tsananin kyawunta ya sa ya dulmiye a
cikin kogin kaunarta. (Laffaru tsohon ďn duniya
kenan)
166
TASKARNOVELS.COM.NG
Ita kuwa Rahila ba komai ne yasa sonsa ya
mamaye zuciyarta ba sai don sanin cewa shi ne
kadai namijin da za ta aura ta cika babban
burinta na duniya, burin da babu wanda ya san
shi face ita kadai.
Kamar yadda aka yanke shawarar zama a cikin
wannan daji na hudu har izuwa tsawon mako
uku, haka al'amarin ya kasance. A ranar da
mako ukun ya cika ne kowa ya sami kwarin
jikinsa ya zamana babu sauran mai jinya a cikin
matafiyan kuma ba sa jin ciwon komai a jikinsu
sai dai tabubbuka.
Da sassafe kowa ya kimtsa aka hau kan Aljani
Marhabul Zaurus aka zazzauna sannan ya bude
fuka-fukansa wadanda suka kasance daya da
rabi ya tashi da su sama ya luluka a cikin
gajimare.
Marhabul Zaurus ya wanzu yana ta tsala gaudu
a cikin gajimare har tsawon kwana guda da yini
167
TASKARNOVELS.COM.NG
daya. Kwatsam! Sai yaji wata irin iska mai karfin
tsiya ta zuko shi ta damfara shi da kasa a cikin
abinda bai wuce dakika goma ba.
Gaba dayan matafiyan da ke kansa suka gangaro
kasa ba shiri. Al'amarin da ya fusata su jarumi
Imran ke nan. Cikin fishi Imran ya dubi Aljani
Marhabul Zaurus ya ce, "Wane ne ya ba ka izinin
ka yi irin wannan wawar sauka ďauke da mu?
Inda da tsautsayi ai da wasunmu sun karya
wuya sun hallaka a yanzu".
Koda jin wannan batu sai Boka Muzaffar ya yi
caraf ya tari numfashin Imran ya ce, "Ka yi wa
bawana uzuri domin kuwa ba laifinsa ba ne. Ina
son ku sani cewa babu wata halitta da ta isa ta
ratsa ta saman wadannan mugayen dazuzzuka
guda biyar, shi ya sa ma tun da farko duk dajin
da muka iso farkonsa sai Marhabul Zaurus ya
sauko da kansa kas saboda ya san cewa bai isa
ya ketare lafiya ba. Yanzu mun iso farkon daji na
biyar wanda shi ne daji na karshe. Muna fita
daga cikinsa za mu yi arba da kogon Darul
Iksina Idan har muka ratsa ta cikin wannan daji
168
TASKARNOVELS.COM.NG
lafiya lau a raye mun gama shan wuya. Daman
an ce bayan wuya sai dadi".
Ya yin da Boka Muzaffar ya zo nan a jawabinsa
sai kowa ya shiga gyara damararsa da kayan
yakinsa. A lokacin ne sadauki Haiman ya dubi
hannunsa na dama wanda da shi ne yake sarrafa
takobi ya ga babu hannun kuma dole sai dai ya
yi amfani da hannun hagu, kawai sai ya fashe da
kuka.
Al'amarin da ya sa kowa ya kamu da tsananin
tausayinsa kenan. Take matarsa Lumaira ta
bude hannayenta ya fada kan kirjinta suka
kankame juna suna masu kuka ta shiga
rarrashinsa ta ce, Ya kai mijina ka kwantar da
hankalinka, ka daina tunowa da abin da ka rasa.
Ka sani cewa " kaddara ta riga fata, kowanne
bil'adama baya sanin yadda karshen halittar
jikinsa za ta kasance face ya mutu. Ka sani cewa
wannan hannu naka da kar ba zai sa ka rasa
dukiya ko soyayyata ba, ko kuma mulki da
dukkan matsayi a wannan duniya. Zan kasance
mai matukar alfahari da kai idan har ka sami
169
TASKARNOVELS.COM.NG
nasarar shiga kogon Darul Iksina kuma ka debo
wannan ruwan sihiri na cikinsa, koda kuwa ni
ban rayu ba na kai izuwa lokacin, domin ka ajiye
babban abin tarihi na sadaukantaka da
jarumtaka wadda waninka bai ajiye a baya ba.
Babban bakin cikina shi ne, ace mutuwa ta raba
mu a wannan lokaci wanda ba mu sami haihuwa
ba bare mu bar abin tunawa da juna. Bana son
ka mutu ka bar ni, gwara ni na tafi na barka
domin idan kai ne ka tafi, raunin zuciyata ba zai
bar ni na iya ci gaba da rayuwa ba." Lokacin da
Haiman ya ji wannan batu sai ya sake kankame
Lumaira a kirjinsa ya ci gaba da kuka.
A bangaren Shaharan da Gimbiya Zarina kuwa,
lokacin da suka tsaya suna tattaunawa kamar
masu yin bankwana sai Zarina ta ga Shaharan
ya kura ma ta idanu har hawaye na zubowa
daga cikin idanunsa. Cikin yanayin mamaki ta sa
hannunta guda ta share masa hawayen sannan
ta ce, "Ya kai masoyina, a ina dalilin zubar
wannan hawaye naka? Ka tuna cewa saboda kai
fa na ci gaba da rayuwa na kawo i yanzu. Babu
abin da nake son gani face farin cikinka, kuma
170
TASKARNOVELS.COM.NG
babu abin da zubar da hawayenka zai haddasa
mini face tsananin bakin ciki mara tukewa."
(Oh ni Maiboko! Wato ana tafka gagarumar
soyayya a cikin litattafan yaki)
Ya yin da Zarina ta zo nan a zancenta sai hawaye
ya sake zebowa akan kumatun Shabaran ya
dube ta ya ce, "Ya ke masoyiyata ki yi sani cewa
ba komai ne ya sa ni zubar da wanan hawayen
ba face tsananin tausayinki.
Abu na farko, ga shi kin rasa dan uwanki wanda
kike so fiye da komai a cikin wannan duniya. Ni
kuma da muka fara soyayya yanzu ga shi na
zama nakasasshe. Ta ya ya kina matsayin 'yar
Sarki za ki auri nakasasshe mai hannu daya?
Shin ba kya tananin cewa wannan abin gori ne
kuma abin zuzutawa a cikin duniya?" Sa'adda
Zarina ta ji wannan batu sai ta yi murmushi
sannan ta ce, "Ya kai abin begena dare da rana
ina mai tabbatar maka da cewa wannan nakasa
171
TASKARNOVELS.COM.NG
da ta same ka ba ta kara komai ba a tsakanina
da kai face ɗumbin soyayya mara adadi. Ina so
ka sani cewa babu ruwan so da kyau, matsayi ko
yanayi. Shi So wani tsuro ne wanda idan ya fito
a cikin zuciya baya mutuwa sai dai kullum ya ci
gaba da girma har ya mamaye filin zuciyar
gabdaya saboda yana samun taki da ruwa daga
tafkin bege da kauna
Sauyin siffar jikinka ba zai iya kankare kaunar
da ta gama mamaye zuciyata ba. Inda za a yi
gutsun gutsun da sassan jikinka muddin zan
ganka a raye zan so na ci gaba da zama da kai a
hakan har izuwa Karshen rayuwata, koda kuwa
ba za ka iya tsinana mini komai ba."
Koda jin wannan batu sai Shaharan ya ji ya daďa
kamuwa da tsananin kaunar Gimbiya Zarina
fiye da ko yaushe don haka sai ya sake
rungumeta a kin kirjinsa ya kama kukan farin
ciki a cikin zuciyarsa
172
TASKARNOVELS.COM.NG
Kamar yadda Zarina da Shaharan da kuma
Haiman da matarsa suka yi wannan tattaunawa
haka ma Sarki Laffaru da Gimbiya Rahila suka
yi. Shi kuwa Boka Muzaffar da aljanui Marhabul
Zaurus sun yi wannan tattaunawar, sai dai su ba
maganganu na alamun bankwana suka yi ba,
kuma keɓewa suka yi gefe daya yadda babu mai
jinsu.
Boka Muzaffar ya dubi Aljani Marhabul Zaurus
ya ce, "Abin da nake so da kai shi ne, da zarar
mun sami nasarar shiga cikin kogon Daru!
Iksina kai sauri ka hallaka gaba dayan abokan
tafiyar nan tamu domin idan muka kuskura
dayansu ya mallaki wannan ruwan sihiri to
tamkar ya mallaki duniya ne gabadayanta
domin yana shan ruwan zai iya sarrafa Aljani
Maruful Dauwaz. Da ma karya nayi musu na ce
ba zamu iya sarrafa Maruful Dauwaz ba face
mun je masa da Gimbiya Rahila. Alkawarin da
ke tsakaninmu ni da kai yana nan, tabbas sai na
yi maka sarautar Sarkin aljanu na duniya
173
TASKARNOVELS.COM.NG
muddin ka cika wannan umarni nawa ba tare da
ka yi kuskure ba."
Lokacin da Aljani Marhabul Zaurus yaji wannan
batu sai ya cika da tsananin mamaki kuma ya
shiga rudani da wasi-wasi don haka sai ya dubi
Boka Muzaffar cikin yanayin rashin fahimta ya
ce, "Ya shugabana lallai zan kasance mai cika
umarninka, amma ina tsoron abu biyu. Abu na
farko shi ne, ta yaya zan iya kawar da wadannan
abokan tafiya tamu alhalin duk sun fi ni karfin
sihirin tsafi, Sarki Laffaru ne kadai ba shi da
sihirin komai a yanzu. Abu na biyu ina shakkar
Gimbiya Rahila domin tun a farkon wannan
tafiya tamu na lura da cewa kai kanka ta fi ka
karfin sihiri da jarumtaka, shin ba ka tunanin
cewa ita kadai za ta iya wargatsa dukkan
shirinmu?"
Tambayar ta biyu da nake son na yi a gare ka ita
ce, tun a farko ka gaya mini cewa kana son ka
mallaki rabin kasar Sarki Laffaru da rabin
dukiyarsa bayan ka taimake shi ya auri Gimbiya
Ramlatul Siyam, to shin yanzu ba ka bukatar
174
TASKARNOVELS.COM.NG
komai daga gare shi ne shi ya sa ka ba ni
umamin na hallaka shi?"
Sa'adda Aljani Marhabul Zaurus ya zo nan a
zancensa sai Boka Muzaffar ya tuntsure da
dariya har sauran abokan tafiyar suka tsargu da
jin dariyar amma sai ya wayance ya dubi Aljani
Marhabul Zaurus cikin murmushi da kara
kaskantar da murya ya ce, "Kai dai kawai ka
zuba ido ka sha kallo kuma ka bi umarnina zan
warware maka duk abin da ya shige maka duhu
anan gaba".
Ba tare da ɓata lokaci ba Shaharana ya wuce
kan gaba, sadauki Haiman na biye da shi goye
da matarsa Lumaira, sannan Imran da Shadira,
Imran na goye da mahaifiyarsa, Zarina na take
musu baya, sai kuma Gimbiya Rahila, Boka
Muzaffar da Sarki Laffaru.
Aljani Marhabul Zaurus ne na karshe yana tafe
yana waige-waife cikin alamun tsoro kamar ace
kyat ya fita da gudu.
175
TASKARNOVELS.COM.NG
Sai da aka shafe sa'a guda cif-cif ana tafiya a
cikin wannan daji na biyar ba su ga koda
giftawar dan karamin kwaro ba, kuma ba su ji
motsin komai ba. Gashi a wannan lokaci rana ta
kwalle kuma guzurin nasu na ruwa da abinci
duk ya kare don haka yunwa da kishirwa sun
fara addabarsu
Wani abin takaici kuma shi ne, gaba daya
wannan daji a cike yake da rairayin sahara babu
bishiyoyi ma bare a sami inuwar da za a fake,
kuma babu kogo ko korama inda za a sha ruwa,
dole sai an isa karshen dajin anan ne akwai
kogin da ake kira TUDUN TSIRA yake'.
Lokacin da Boka Muzaffar ya ga sun shafe
wannan doguwar tafiya amma ba su hadu da
wannan katuwar Kunama ba sai hankalinsa ya
dugunzuma ya aiyana a ransa cewa lallai a ko
yaushe Kunamar za ta iya baiyaną a gare su ta
kawo musu MAMAYAR BAZATO.
176
TASKARNOVELS.COM.NG
Ana cikin tafiyar sai Muzaffar ya bude muryarsa
da karfi ya ba da umarnin a tsaya. Da yake
Shaharan ne akan gaba sai ya tsaya cak! A inda
yake. Ai kuwa sai kowa ma ya tsaya. Boka
Muzaffar ya dubi gaba dayan abokan tafiyar
daya bayan daya ya ce, 'Ya ku abokan tafiya ku
yi sani cewa rayuwarmu tana cikin mugun
hadari tunda har yanzu wannan muguwar
Kunamar ba ta baiyana a gare mu ba kuma ba
mu ci rabin tafiya ba izuwa karshen wannan
daji. Idan muka ce zamu ci gaba da tafiya ko
kuma mu koma da baya inda zamu nemi ruwa
da abincin da zamu ci ba zamu kai ba, yanwa da
kishirwa za su kashe mu.
Haka kuma idan ma muka ce za mu ci gaba da
tafiyar a haka a ko yaushe Kunamar za ta iya
baiyana a gare mu ta hallakavmu gaba daya,
saboda haka yanzu meye abin yi? Tabbas muna
cikin TSAKA MAI WUYA kuma GABANMU TSINI
NE, BAYANMU SIYAKI.
177
TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'adda Boka Muzaffar ya zo nan a jawabinsa
sai hankalin kowa ya dugunzuma aka yi tsit aka
rasa wanda zai ce kala. Daga can sai Rahila ta ce,
"Ni a tawa shawarar mu tsaya anan mu huta
sosai domin mu sami kwarin jikinmu koda
kuwa ba mu sami ruwa mun sha ba. Idan muka
huta din sai mu ci gaba da tafiya in ya so da
zarar mun ga Kunamar ta fito sai jarumi
Shaharan ya janye ta da gudu ya kai ta har can
kogin Tudun Tsira inda za ta hallaka sannan mu
bi bayansa hankali kwance. Nan take aka taru
waje daya aka zazzauna ana hutawa duk da
cewa zafin rairayi ya addabi kowa.
Kash! Inda su Haiman sun san abin da zai biyo
baya da ba su yi gangancin zama domin su huta
ba.
Ashe ita wannan Kunama ta ga shigowar su
Haiman cikin dajin tun a farkon zuwansu, kawai
sai ta kama haka rami ta shige izuwa can
karkasin kasa, rairayi ya rufeta ruf, ta ci gaba da
tafiya a can karkashin rairayin ba tare da ana jin
motsinta be har ta sha kansu taje wannan wuri
178
TASKARNOVELS.COM.NG
daidai inda suka zazzauna suna hutawa. Abin da
ba su sani ba shi ne akan Kunamar suka
zazauna.
Ba zato ba tsammani sai suka ji wani katon abu
ya yi sama da su gaba dayansu suka rikito kasa.
Koda suka yi arba da abin da yai watsi da su sai
suka dimauce ce har sun yi yunkurin guduwa,
sai Shaharan ya daka musu tsawa ya ce, "Su
tsaya, duk wanda kuwa ya gudu tamkar ya sayi
ajalinsa ne".
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jaruman
da wannan shirgegiyar Kunama wacce idan
daga nesa mutun ya hangota sai ya yi zaton ko
tsauni ne saboda girmanta kuma ta kasance
baka wuluk har shekin baki take yi ba kyan gani.
Kafafuwanta gasu nan birjik zankala-zankala
masu dauke da muggan yatsu masu farata
ma'abota TSINI DA KAIFI.
179
TASKARNOVELS.COM.NG
Shaharan ya dubi sauran abokan tafiya a lokacin
da kowa jikinsa ya kama kyarma ya ce, "Babu
batun guduwa a yanzu tunda wannan Kunama
ta shammace mu ta baiyana tsulum! a gabanmu.
Na tabbata idan ma muka ce zamu yi gudun da
yawanmu ba za su tsira ba Kunamar za ta riske
su ta hallakasu. Ni kaina ba ni da tabbacin zan
iya tsere ma ta tunda babu tazara a tsakanina da
ita. Ku sani cewa ba mu da wani zabi wanda
yabfi mu tunkare ta da yaki muna yakarta muna
karawa gaba da gudu. Ina mai gargadinmu da
kada dayanmu ya yi sakaki har Kunamar ta soke
shi da farcenta domin da zarar hakan ta faru za
ta sa masa dafi wanda zai narkar da shi nan
take".
Kafin Shabaran ya gama rufe bakinsa tuni
Kunamar ta afko musu su duka tana mai kawo
musu SARA DA SUKA da dukkan kafafunta su
kuwa sai suka wanzu suna masu kare harin da
garkuwoyi kuma suna mai da martani da saran
takubba gami da ja da baya cikin gudu. Kunamar
ta ci gaba da binsu tana kuntata su. Duk sadda
takubbansu ya haďu da jikin Kunamar sai ka ga
180
TASKARNOVELS.COM.NG
tartsatsin wuta gami da hayaki