x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - MAZAN JIYA 3

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 68212 words

Category: Adventure Stories

Views 187

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
mutu ba takaici da bakin
ciki ne za su kashe ni nan gaba".

Caraf! Sai Imran ya tari numfashinsa ya ce "Ya
kai abokin tafiya ka yi sani cewa in dai da rai da
224

TASKARNOVELS.COM.NG
numfashi akwai sa'a da rabo. Ina tabbatar maka
da cewa ko a bakin Kura nake ban fid da rai da
samun kuɓuta. Kawai ka tsaya mu ZAGE
DANTSE mu yaki wadannan aljanu da iyakar
dukkan karfinmu koda kuwa ba zamu yi nasara
ba."

Koda jin haka sai Haiman ya yi yaken takaici
sannan ya kwance matarsa Lumaira daga
bayansa ya ajiye ta a kas ya dube ta sa'ad da
hawaye ya zubo masa ya ce, "Ki yafe ni yake
matata, yau ne ranar farlo da na gaza akan
tafarkin kare ki da kulawa da ke domin ina
ganin cewa mutuwa a gare mu ni da ke tafi
komai sauki."

Kafin Haiman ya gama rufe bakinsa tuni
Lumaira ta zabga masa mari sannan sai ta fashe
da kuka tana mai cewa, "Ban taɓa sanin cewa
kai rago ba ne sai yau. Tabbas zuciyarka mai
rauni ce kuma ba ka cika jarumi ba, Imran shi ne
JARUMIN KWARAI. Dukkan namijin kwarai
baya mika wuya ga abokan gaba bare har yana ji
yana ganin za a hallaka masoyiyarsa ya kasa
225

TASKARNOVELS.COM.NG
komai. Ashe duk soyayyar da muka yi a baya ta
zama ta banza in dai ka mika wuya ga
wadannan aljanu suka hallaka mu ba tare da ka
yi kokarin komai ba ka yanke duk kaunar da ke
tsakaninmu."

Kafin Lumaira ta gama rufe bakinta tuni Haiman
ya kwarara uban ihu cikin bakin zafin nama ya
zare takobinsa da lafiyayyen hannunsa ya
afkawa wadannan Dakaru da sara tun gabannin
su Dakarun su karɓi izinin yin yakin.

Koda ganin haka sai farin ciki ya lulluɓe Imran
shi ma ya afkawa Dakarun aka ruguntsume da
azababben yaki. In ba don su Haiman suna da
karfin sihirin tsafi daidai nasu ba da tuni
Dakarun sun yi musu kisan farat daya. Babba
abin da ya dugunzuma hankalinsu Imran shi ne,
SARA DA SUKA ba ya tasiri a jikin wadannan
Dakarun sai dai ka ga tartsatsin wuta na tashi
kuma ko kwarzanar jikinsu ba ya yi, sannan
kuma ko kadan babu alamar za su gaji.

226

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda aka sami rabin sa'a ana wannan murzu sai
Haiman da Imran suka raina dukkan
jarumtakarsu da karfin sihirinsu domin ta kai
da kyar suke kare harin da aljanun ke kawo
musu bare ma su mai da martani. Kai da aljanun
ma suka ga cewa wankin hula zai kai su dare sai
suka rikide izuwa ainahin mummunar siffarsu
ta aljanu suka ci gaba da gumurzu a haka.

Koda mahaifiyar Imran tayi arba da aljanun a
cikin siffofinsu na zahiri sai ta sume. A daidai
wannan lokacin ne karfin aljanun ya ninka na da
suka fara kai su Imran kas har ma suka fara yi
musu rauni ya zamana cewa an sari Imran sau
uku, shi kuwa Haiman sau biyu aka sare shi ya
zamana cewa jiri ya debe shi har ya kife kasa da
rubda ciki

Koda Dakarun suka ga Haiman ya kife a kas shi
da natarsa sai suka yi caa! A kansu da nufin su
daddatsa su. Da dai Imran ya ga abin da ke
shirin faruwa sai ya fusata ainun bai san sa'adda
ya daka wawan tsalle sama ya dirga akan
kafadar daya daga cikinsu ya dankara masa
227

TASKARNOVELS.COM.NG
naushi a wuyansa a take wannan badakare ya
sandare ya koma gunki haka su ma yan uwansa
babu wanda ya kara yin motsi.

Duk abin da yake faruwa RAUHUDUL MAUZUL
yana tsaye yana gani, cikin wata mummunar
siffa abar tsoro. A daidai wannan lokacin ne
sadaukin Haima ya farfado, cikin sauri ya dauko
magani ya shafa a rauninsa sannan ya shafawa
jarumi Imran shi ma. Wannan sarkin mayu ya
ce, idan kun tsira daga sharrin dakarun masifa
ai ba za ku iya tsira daga sharrin masifar ba, ga
maza nan bisa kanku.

Haiman ya dubi Imran cikin tsananin fusata ya
ce, maza mu afka masa kafin ya afko mana.
Kafin Rauhudul Mauzul ya yi wani yunkuri tuni
su Imran sun afka masa suka kacame da wani
azababben yaki, duk da su Haiman suna yin
yakin ne da dukkan karfi da iyawarsu sai da
suka zama ababen tausayi a hannun wannan
hatsabibin aljani.

228

TASKARNOVELS.COM.NG
Sai da wannan aljani ya sumar da kowanensu
sau bakwai, yayin da ya sumar da wancan sai
wannan ya farfaďo. Hakika shi kansa ya yi
mamakin bakin naci na waďannan jarumai
domin a tarihinsa bai taba haďuwa da masu
taurin rai kamarsu ba. Suna cikin wannan
gumurzu ne ya samu nasarar fesa musu wata
shuďiyar iska daga bakinsa bakinsa a take suka
zube kasa sumammu

Wannan shi ne abin da ya faru da su sadauki
Haiman a cikin kogon Darul Iksina

Al'amarin su sarki lafaru kuwa bayan boka
Muzaffar ya shige cikin ďaki na farko ya basr su
a tsaye, sai Laffaru ya dubi Rahila ya ce, "Shin
kina tare da ni?" Rahila ta yi murmushi ta ce
"Ina tare da kai". Laffaru ya ce, "Tabbas na yi
imani cewa Aljani Maruful Dauwaz yana cikin
ɗaya daga cikin waďannan gidaje guda bakwai
kuma ko shakka bana yi ba ya cikin gida na
farko wanda Muzaffar ya shiga cikinsa, kuma ba
ya cikin gida na uku wanda su Haiman suka
shiga, haka kuma baya cikin gida na biyu wanda
229

TASKARNOVELS.COM.NG
Muzaffar ya ce mu shiga mu debo dukiya.
Tabbas yana cikin gida na hudu ko na biyar ko
na shida zuwa na bakwai. Ya ke matata ta nan
gaba, a cikin wadannan ragowar gidaje guda
hudu wanne ne kike ganin zamu iya riskar
Aljani Maruful Dauwaz a ciki?"

Koda jin wannan tambaya sai Rahila tayi
murmushi ba ta ce komai ba, kawai sai ta zura
hannu a cikin jakar guzurinta ta dauko wata 'yar
gajeriyar SANDAR TSAFI ta tofa wadansu
dalasiman tsafi a jikinta ta saki sandar.
Maimakon sandar ta fadi kasa sai ta tsaya cak a
sama cikin iska sannan ta nufi inda wadannan
gidaje hudu suke ta fara dungurar kofar farko,
sai ta matsa gaba ta dunguri kofa ta biyu nan ma
ta wuce gaba har sai da taje kofar gida na
bakwan. Koda ta dunguri kofar gidan sai ta
tsaya cak a jikin kofar ta manne.

Koda ganin haka sai Rahila da Laffaru suka dubi
juna suka yi murmushi. Nan take suka buɗe
wannan kofar gida na bakwai salin-alin ba tare
da sun fuskanci wata matsala ba, suka kunna kai
230

TASKARNOVELS.COM.NG
ciki, suna shiga sai kofar gidan ta rufe kanta.
Nan fa ya rage saura Zarina, Shadira da
Shaharan a tsaye suna

kallon junansu aka rasa wanda zai ce kala. Daga
can sai Zarina ta dubi Shadira ta ce, "Ya ke
abokiyar tafiya yanzu ke me kika yanke shawara
akan rayuwarki?"

Sa'adda Shadira ta ji wannan tambaya sai ta yi
ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ai ni yanzu bani da
wani zaɓi wanda ya fi ni ma na shiga cikin gidan
da su masoyina Imran suka shiga. Idan na iske
su a raye shi ke nan, idan kuma sun mutu sai ni
ma na mika wuya ga abin da ya kashe su ya
hallaka ni tunda ban ga amfanin rayuwata ba a
doron kasa domin rayuwa idan babu masoyi ba
ta da dadi. Sa'adda Zarina da Shaharan suka ji
wannan batu sai duk su biyun jikinsu ya yi sanyi
suka ji sun kamu da tsananin tausayin Shadira,
nan take suka tuno da irin wahalar da suka sha
a cikin wannan tafiya wacce ta zame musu asara
kuma abin takaici da bakin ciki, kawai sai suka
kama kuka.
231

TASKARNOVELS.COM.NG

Itama Shadira sai zuciyarta ta karya ta taya su
kukan. Sai da suka dan jima suna kukan sannan
Shaharan ya goge hawayen idanunsa da
lafiyayyen hannunsa sannan ya dubi Shadira ya
ce, "Ya ke abokiyar tafiya ni da masoyiyata
Zarina za mu yi miki rakiya izuva cikin wannan
gida na uku domin mu kaiwa su Imran dauki
idan har suna raye dukkan mugun halin da suke
ciki. Idan kuma ba sa a raye lallai mun zaбi mu
mutu a cikin gidan da dai mu fito a raye".

Koda gama fadin hakan sai Shaharan ya wuce
kan gaba ya nufi kofar wannan gida na bakwai
cikin hanzari Shadira da Zarina suka bi shi.

Nan take suka bude kofar gidan suka kunna kai
ciki, kofar ta kulle kanta.

Al'amarin Sarki Laffaru da Gimbiya Rahila
kuwa, lokacin da suka shiga cikin wannan gida
na bakwai sai suka tsinci kansu tsamo-tsamo a
232

TASKARNOVELS.COM.NG
cikin wani makeken kogi. A can karshen kogin
wata matattakalar bene ce guda goma sha biyu
wadda karshenta wani gini ne mai fadi da tudu.

Kwatsam! Sai suka ga wata shirgegiyar hakitta
kwance akan wannan faffadan gini. Ba komai ba
ne wannan halitta face Aljani MARUFUL
DAUWAZ. Idanunsa na kallon rufin gidan, kuma
suna ta dalalo da hawaye, ruwan hawayen na ta
kwarara ta kan wannan matattakala guda goma
sha biyu tamkar idaniyar ruwa ce ta ɓalle. Nan
take Laffaru da Rahila suka gane cewa tabbas
wannan Aljani da ke ta kuka hawayensa na
kwarara shi ne Aljani Maruful Dauwaz kuma
ruwan kogin da suka tsinci kansu a ciki shi ne
ruwan albarka wanda Boka Muzaffar ya yi musu
karyar cewa zai warkar da marasa lafiya!
(Na sha wahala a wannan posting ďin na yau
sakamakon babu shafi guda biyu kuma
shafukan da aka rasa suna da matukar
muhimmanci. Na yi amfani da salon marubucin
na shigar da fahimtata a madadin shafin da aka
rasa. Na yi shisshigi)

233

TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'adda Aljani Maruful Dauwaz ya ji motsi a
cikin wannan ruwan hawayen nasa sai ya cika
da tsananin mamaki domin shi a saninsa tun da
ya shigo cikin wannan kogo tsawon shekaru
dubu biyu bai sake jin motsin wata halitta ba a
cikin wannan gida da yake ba sai yau.

Cikin firgici ya mike zumbur! Ya dubi cikin
hawayen nasa, kawai sai ya yi arba da su Sarki
Laffaru da kuma Gimbiya Rahila. Nan take ya
Kurawa Rahila idanu, idanunsa suka kafe akanta
ko kiftawa ba sa yi. Amma da ya dube ta sama
da kasa ya ga mutum ce ba aljana ba sai ya
girgiza kai ya koma ya kwanta kamar yadda
yake da farko ba tare da ya sake duban
fuskokinsu ba ya ce, "Ya ku wadannan
hatsabiban bil'adama yaya aka yi kuka zo har
nan tsibirin kuma kuka shigo cikin wannan
kogo na Darul Iksina? Mene ne dalilin
zuwanku?"

Har Sarki Laffaru ya bude baki zai yi magana sai
Rahila tayi wuf ta tari numfashinsa ta ce, "Ya kai
NAMIJIN DUNIYA, BABBAN JARUMI na
234

TASKARNOVELS.COM.NG
Sarauniyar Matan duniya GIMBIYA RASHMIN ka
yi sani cewa mu bakinka ne na musamma kuma
muna dauke da gagarumin sako wanda
masoyiyarka marigayiya Gimbiya Rashmin ta
bayar da shi a ba ka tun kafin rasuwarta."Koda
jin wannan batu sai Aljani Maruful Dauwaz ya
mike zumbur ya fuskanci Rahila kuma ya dube
ta cikin zakuwa ya ce, "Wane sako ne
masoyiyata ta bari wanda har yanzu bai riske ni
ba sai yau bayan gushewarta da shekaru dubu
biyu da doriya?"

Rahila ta yi ajiyar numfashi sannan ta ce, "Ka
kwantar da hankalinka ya kai DODON MAZA, ka
yi sani cewa wannan sako da masoyiyarka ta ba
ka ba komai ba ne face rubutacciyar wasiyya
akan wani burinta guda daya da take son ka cika
mata shi a duniya kafin cikar ajalinka.

Duk duniya babu wanda ya san inda wannan
wasiyya take a ɓoye sai ni, kuma babu mai iya
daukota sai ni din. Idan za ka iya tunawa lokacin
da kake aikin bauta a gidan sarautar Sarkin
aljanu mahaifin Gimbiya Rashmin akwai wani
235

TASKARNOVELS.COM.NG
bawa wanda ya kasance abokinka wanda ake
kira da suna TALMARA IBINI SAUMUR wanda
shi ne mai kula da shimfidar Sarki, haka ne ko
ba haka ba?"

Koda jin wannan tambaya sai Aljani Maruful
Dauwaz ya cika da tsananin mamaki bisa yadda
ya ji Rahila ta san abokinsa Talmara alhalin
rayuwarsa da shi tuni ta gushe sama da shekaru
dubu biyu da suka shude.

Maruful Dauwaz ya gyara zama, nan take ya ji ya
fara aminta da Rahila akan cewa ba ta zo masa
da zancen karya ba, don haka sai ya dube ta ya
ce, "Ya ke wannan bil'adama ma'abociyar
kyawu da kamanni irin na masoyiyata wace ce
ke, kuma ya aka yi kika san abokina Talmara
ibini Saumur?"

Koda jin wannan tambaya sai Rahila ta nutsu
sannan ta ce, "Da farko dai ni sunana Rahila,
kuma mahaifina shi ne mai mulkin Birnin
236

TASKARNOVELS.COM.NG
SHAUFIL wanda ke can yamma da kasar
DAMASKA.

Yadda aka yi na san abokinka Talmara kuwa shi
ne, na sami tarihin rayuwarsa ne a cikin
KUNDIN TARIHI na masarautarmu. Ya taɓa yin
bauta ga Kakana na dari bakwai da sittin da tara
kimanin shekaru adadin zamanka anan cikin
kogon Darul Iksina.

Tun a sannan ne Talmara ya kawo wasiyyar da
masoyiyarka ta rubuta kafin ta mutu ta ba shi
amana shi kuma sai ya damka ta amana ga
wannan Kaka nawa ya ce, ya yi ta ajiyarta har
sai a shekarar da aka gano inda kake a cikin
duniya a damka maka ita.

Bisa wannan dalili ne wannan kaka nawa na
dari bakwai da sittin da tara ya 6oye wannan
wasiyyar a inda babu wanda ya sani sannan ya
rubuta tasa wasiyyar cewa duk ranar da aka

237

TASKARNOVELS.COM.NG
gano inda Aljani Maruful Dauwaz yake aje a
dauko wannan wasiyya a ba shi.

A cikin wasiyyar ne ya bayar da labarin
bawansa Talmara da kuma labarin soyayyarka
da Gimbiya Rashmin da yadda aka yi aka raba
ku da karfin tsiya har bakin ciki ya zamo
sanadin ajalinta.

Ya kai Maruful Dauwaz ka yi sani cewa ko
mahaifina yanzu bai san inda wannan wasiyya
take ba domin na sauya ma ta maɓoya. Idan ka
amince za ka biya mini tawa bukatar ni ma zan
kai ka inda na бoye wasiyyar masoyiyarka na
damka ta a gare ka, amma sai ka yi rantsuwa da
darajar soyayyarka akan Rashmin cewar za ka
zamo mai cika alkawari a gare ni, kuma sai
bayan ka biya mini tawa bukatar sannan zan ba
ka wasiyyar masoyiyarka".

Lokacin da Gimbiya Rahila ta zo nan a jawabinta
sai Aljani Maruful Dauwaz yai shiru kuma ya
238

TASKARNOVELS.COM.NG
fada kogin tunani mai zurfi yana juya al'amarin
a cikin zuciyarsa. Daga can sai ya dago kai ya
dubi Rahila ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki, ki yi
sani cewa a iya rayuwata ta duniya babu abinda
na tsana sama da yaudara da cin amana da
kuma butulci. Bisa wannan dalili nake so ki rike
amanata ni ma zan rike taki. Tun wuri idan kin
san cewa wannan labari na wasiyyar
masoyiyata da
kika zo mini da shi idan karya ne ki kau da shi,
domin idan na gane karya ne sai na hallaka ki
kuma na hallaka duk zuri'arki. Ke Birninku ma
gaba dayansa sai na shafe shi daga doron kasa.
Yanzu sai ki ci gaba da ba ni labarinki da yadda
aka yi kika zo har nan kika riske ni sannan a
karshe ki gaya mini bukatarki wacce kike son na
biya miki. Ki sani cewa na yi alkawari ba zan
sake shiga duniya ba har sai ajalina ya riske ni a
nan cikin kogon Darul Iksina amma yanzu zan
janye wannan alkawari albarkacin wannan
wasiyya ta masoyiyata wacce ban san da ita ba
sai yanzu.

239

TASKARNOVELS.COM.NG
Gargadina na karshe a gare ki shi ne, ina son ki
sani cewa na san kalar rubutun masoyiyata,
kuma gaba dayan matan aljanu na duniya babu
mai irin rubutun Rashmin. Lallai idan na ga
rubutun ba nata ba ne hukuncin kisa ya tabbata
akanki. Ke ba ma rubutun ba, hatta tauwadar da
aka yi rubutun da ita na san irin kalar ta gidan
su masoyiyata Rashmin, idan ba da ita aka yi
rubutun ba na san karya ne ba wasiyyarta ba
ce.'

Sa'adda Rahila ta ji haka sai ta yi murmushi ta
ce, "Duk na yarda da wannan sharadin naka."

Nan take Rahila ta kwashe labarin haduwarta
da su Boka Muzaffar da kuma yadda aka yi suka
je suka dauko sauran abokan tafiya a kasashe
daban-daban, aka ratsa wadannan manyan
dazuzzuka aka iso nan kogon Darul Iksina har
da irin bakar wabalar da suka sha da kuma
rayukan da aka rasa.

240

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Rahila ta gama bayar da wannan labari sai
Aljani Maruful Dauwaz ya jamu da tsananin
tausayi har ya fashe da kuka, sai ga shi Rahila da
Laffaru suna rarrashinsa. Da kyar ya daina
kukan sannan ya nutsu ya dubi Laffaru da
Rahila ya ce, hakika Boka Muzaffar ya cuce ku
kuma ya cika azzalumi. Tabbas kun yi babban
kuskure da har kuka bar shi ya sami nasarar
shiga wannan gida na farko da ke cikin wannan
kogon na Darul Iksina, domin babu makawa sai
ya mallaki Mashin Galilul Haras. Idan kuwa ya
mallaki mashin Galilul Haras tamkar ya mallaki
duniya ne.

Abu daya za mu iya yi mu tsayar da sihirin da ke
jikin Mashin Galilul Haras. Ba komai bane face
mu je mu nemo yawun barci na bakin SARKI
NASHMIR BN HAYAT na Birnin HINDU, Sarkin
da a halin yanzu babu wani matsafi da ya kai shi
karfin sihirin tsafi a duniya, kuma shi ma babu
yanda bai yi ba akan yazo nan kogon Darul
Iksina don ya mallaki mashin Galilul Haras
amma abu ya gagara. Idan har muka samo
yawun barcin Sarki Nashmir muka kai shi can
gidan tarihi na Sarautar Birnin KISRA, muka
241

TASKARNOVELS.COM.NG
binne shi a cikin gidan to duk inda mashin
Galilul Haras yake zai kai kansa can ya adana
kansa babu wanda zai iya sake mallakarsa face
wanda ya tono inda aka binne wannan yawu ya
jika kasar ya sha."

Sa'adda aljani Maruful Dauwaz ya zo nan a
jawabinsa sai Rahila da Sarki Laffaru suka dubi
junansu cikin alamun tsananin mamaki.

Rahila ta dubi Aljani Maruful Dauwaz ta ce,
"Ashe faduwa tazo daidai da zama, ai bukatar da
muke so ka biya mana ba komai bace face ka je
har fadar Sarki Nashmir ka sato mana 'yarsa
Gimbiya Ramlatul Siyam domin Laffaru ya aure
ta sannan ni ma na aure shi, saboda haka me zai
hana a jefi tsuntsu biyu da hoge daya Ma'ana,
idan ka je sato Gimbiya Ramlatul Siyam sai
kuma ka samo yawun barcin mahaifin nata?"

Koda Aljani Maruful Dauwaz yaji wannan batu
sai ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa
242

TASKARNOVELS.COM.NG
wanda ya sa gaba daya kogon ya kama girgiza
har sai da ya tsuke bakinsa sannan komai ya
dawo daidai.

Cikin tsananin fushi Aljani Maruful Dauwaz ya
dubi Rahila da Laffaru ya ce, "Hakika kun cika
wawaye masu tarar aradu da ka. Idan da kun
san irin tsananin tsaron da ke cikin fadar Sarki
Nashmir ba za ku ce na je na sato 'yarsa ba bare
kuma har na samo yawun barcinsa ba. Ina
tabbatar muku da cewa komai jarumtakar Aljani
ko mutum muddin ya kuskura ya yi gaba da
gaba da Sarki Nashmir sai dai uwarsa ta haifi
wani. Ta yaya kuke zaton cewa zan iya shiga
fadar Sarki Nashmir har na iya yi muku wannan
aiki guda biyu?"

Yayin da Rahila ta ji wannan batu sai ta kamo
hannun Sarki Laffaru ta ja shi suka juya don su
fita daga cikn gidan.

243

TASKARNOVELS.COM.NG
A dimauce Aljani Maruful Dauwaz ya kira
sunanta ya ce, "Ya ke Rahila, yaya kuma za ki
tafi ba mu gama magana ba?"

Rahila ta juyo ranta a ɓace ta ce, "Me kuma za
mu tsaya mu yi maka tun da ba ka da wani
amfani a gare mu, kuma ba ka bukatar wasiyyar
masoyiyarka, shi kenan, sai ka ci gaba da zaman
jiran ranar ajalinka a nan cikin kogon Darul
Iksina. Amma ka sani cewa idan har ka mutu ba
ka biya bukatar masoyiyarka Rashmin ba wacce
ke rubuce a cikin wasiyyarta lallai ka ci amanar
soyayyaku".

Gama fadin hakan ke da wuya sai Rahila da
Laffaru suka sake juyawa da sauri suke, nufi
bakin kofar gidan.

Tsulum! Sai suka ga Aljani Maruful Dauwaz ya
baiyana a gabansu hawaye na zuba a idanunsa,
Kawai sai ya dube su ya ce, "Raina fansa ne ga
bukatar masoyiyata gimbiya RASHMIN. Na
244

TASKARNOVELS.COM.NG
amince zan biya muku bukatarku koda kuwa
zan hallaka. Ma za ku hau kaina mu bar wannan
kogo yanzu-yanzu domin mu je mu fara shiryeshilyen zuwa fadar Sarki Nashmir da Birnin
Hindu".

(Ni Maiboko na zabi aljani Maruful Dauwaz a
matsayin madubina a cikin abin da ya shafi
soyayya. Ina koyi da halayensa ďari bisa ďari)

Lokacin da Rahila da Laffaru suka ji wannan
jawabi na Aljani Maruful Dauwaz sai suka cika
da tsananin farin ciki. Nan take suka hau kansa
suka zauna, shi kuma sai
End Ads