x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - MAZAN JIYA 3

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 68212 words

Category: Adventure Stories

Views 183

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
so din ya ki karɓar soyayyar
tasa.

Me zai hana ki yi wa sadauki Shaharan
murmushi koda sau daya ne rak domin ya sau
nutsuwa da saukin radadi da zogi na begenki a
cikin zuciyarsa? Tabbas ya kamu da tsananin
sonki, kuma so ba na wasa ba. Koda jin wannan
batu sai Zarina ta haɗa fuska ta ce, "Haba ya kai
dan uwana, ka sani cewa na yi alkawarin cewar
bá zan yi aure ko soyayya ba face na ga kai ma
ka warke, kuma ka sami masoyiya wadda za ka
aura.

Lallai ina nan a kan wnanan alkawari nawa,
babu abin da zai sa na karya shi face mutuwa.
Ka yi hakuri ya kai dan uwana, ba zan iya yin
wannan abu da ka umarce ni da yi ba".
96

TASKARNOVELS.COM.NG

Boka Muzaffar da Sarki Laffaru kuwa, a wannan
lokaci suna zaune a can gefe daya kusa da
gimbiya Rahila suma suna tasu hirar dabam.
Duk sa'adda Rahila ta dago kai sai ta ga Sarki
Laffaru ya kura ma ta idanu ko kiftawa baya yi.
Abin da ya ba ta haushi ke nan, kuma ya ba ta
mamaki.

Ta ce a cikin zuciyarta, "Wai shin me Sarki
Laffaru yake ci ne na baka na zuba? Kuma mene
ne ya burge shi a tare da ni, shi da yake kan
tafarkin auren gimbiya Ramlatul Siyam 'yar
Sarkin birnin Hindu wacce ban fi ta kyau ba,
kuma mahaifinta yafi mahaifina arziki da
daukaka a duniya?

Koda yake, ai shi mutum ne mai son mata da
yawa. Ni kam babu ruwana da duk matsalarsa,
burina kawai shi ne na biya tawa
bukatar".Rahila na cikin wannan tunanin ne ta ji
boka Muzaffar ya ce, "A tashi a ci gaba da tafiya".

97

TASKARNOVELS.COM.NG

Nan take kuwa aka mike aka durfafi cikin daji na
uku. Imran ne akan gaba goye da mahaifiyarsa,
Shadira na biye da shi daf da daf, sannan jarumi
Haiman goye da matarsa Lumaira, sai Zarina
goye da Sarkin Farisa, sai Raliila, sannan boka
Muzaffar da Sarki Laffaru. Al'ajani Marhabul
Zaurus ne na karshe.

Al'amarin da ya ke fusata boka Muzaffar ke nan,
saboda yana mamakin yadda aljani Marhabul
Zaurus yafi dukkan sauran abokan tafiyar tsoro,
a matsayinsa na ljani mai shirgegiyar halitta,
amma duk ta zama ta banza.

Koda shigar su Imran cikin wannan daji na uku
sai suka fara daga kawunansu sama suna kallekalle don su ga ta inda wadannan mugayen
tsuntsaye za su kawo musu farmaki, da ma
kowa ya zare makaminsa yana dube-dube da
waige-waige gami da kallon sama ta kowanne
ɓangare.

98

TASKARNOVELS.COM.NG

Sai da suka yi doguwar tafiya a cikin dajin,
amma ko motsin Tsuntsayen ba su ji ba.
Al'amarin da ya matukar basu mamaki ke nan,
har sarki Laffaru ya dubi boka Muzaffar ya ce,
"Anya kuwa mun shigo cikin dajin da mugayen
Tsuntsayen nan suke?"

Kafin boka Muzaffar ya budi baki ya ce wani abu
sai kwatsam! Suka ji kasar dajin gaba daya ta
kama girgirza tana darewa. Al'amarin da ya
firgita su ke nan. Nan take ramuka suka rinka
budewa, sai ga wadannan mugayen Tsuntsayen
suna bullutsowa sama daga cikin ramukan
tamkar an tashi matattu a makabarta.

Kafin su Imran su yi wani yunkuri sama da
Tsuntsaye dubu dari sun yi musu kawanya babu
ta inda za su iya ratsawa su wuce.

99

TASKARNOVELS.COM.NG
Daga can kololuwar sama kuma sai ga wata
runduna guda ta wadannan tsuntsaye suna tsala
gudu sun durfafo su.

Nan fa cikin kowa ya duri ruwa, hankalin kowa
ya dugunzuma ainun, domin sun san cewa suna
cikin bakin hadari. Tabbas rayuwarsu tana a
tsakanin MUTUWA DA RAYUWA.

(Zuwa ga makaranta. Ina so mu sani cewa, salon
da Madakin Gini ya bi wajen wahalar da
jaruman yana da alaka da kwarjinin kogon
DARUL IKSINA ne. Ana so a tabbatar mana da
cewa, hakika waďannan dazuka sun cika
gagarabadau ababan misali)

Kafin tsuntsayen saman su iso sai na kasan suka
fara marmatsowa domin su afka musu. Koda
ganin abin da ke shirin afkuwa sai Imran ya
buɗe muryarsa da karfin tsiya ya ce, Ku biyo ni a
baya, duk inda ku ka ga na yi ku bi ni.

100

TASKARNOVELS.COM.NG
Ai kuwa yana gama fadin haka sai ya falfala da
azababben gudu ya tunkari tsuntsayen da ke
gabansa ya ratsa ta cikinsu da karfin tsiya ya
rufe su da duka da sandarsa, sai ga shi ya
tarwatsa su da karfin tsiya ya sama musu hanya,
suka ci gaba da gudu. Amma sai Tsuntsayen
suka biyo su a guje aka ruguntsume da
masifaffen yaki. Su Imran suna gudu suna
juyowa suna kare harin tsuntsayen da
makamansu. Duk sa'adda makamansu suka
hadu da kafafun Tsuntsayen sai dai ka ga
tartsatsin wuta ya tashi kamar karfe da karfe ne
suka haďu.

A daidai wannan lokacin ne wadancan
Tsuntsayen da ke tahowa daga sama suka iso
suka lullube saman su Imran, yakin ya kara
tsamari ainun. Duk da cewa su Imran suna tsala
gudu suna ketawa ta cikin bishiyoyi amma
Tsuntsayen ba su fasa bin su ta sama da kasa ba.
Ko bishiya Tsuntsayen suka yi karo da ita,
komai kaurin bishiyar sai dai ka ga ta karye ta
fadi kasa sun wuce abinsu. Duk sa'adda
tsuntsayen suka karci kayan karfen da ke jikin

101

TASKARNOVELS.COM.NG
su Imran kuwa, sai dai ka ga kayan na darcwa
tamkar takarda aka yanka da zabira.

Wani lokacin ma faratan Tsuntsayen na kartar
jikin jaruman bayan sun keta kayan jikin nasu.
Sai dai ka ji suna ihu, jini na tsartuwa a jikinsu.

Imran ne kawai Tsuntsayen ba su yiwa rauni ba,
sai kuma gimbiya Rahila. Lokacin da jarumi
Imran ya lura da halin da sauran abokan
tafiyarsa ke ciki, wato waďannan tsuntsayen
sun yi musu rauni, kuma suna kokarin surarsu,
in ba don ma sun kasance jarumai ba masu
juriya da naci da tuni tsuntsayen sun yi sama da
su. Abin da ya fi dugunzuma hankalin su Imran
shi ne, ganin yadda KAIFI DA TSINI ba ya tasiri a
jikin tsuntsayen, har ta kai cewa ma takubbansu
sun fara dakushewa.

Nan take Imran ya fusata ainun, ya ci gaba da
dukan tsuntsayen da sandarsa kuma a kai ya fi
dukansu, sai dai ka ga sun fado kasa, amma
102

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma sai su sake mikewa zumbur! Su yi sama su
ci gaba da kawo hari.

Imran sai ya sauya salon yaki, ya rinka dawowa
da baya yana kade tsuntsayen da sandarsa, don
kubutar da sauran abokan tafiyarsa. Wato sai
yai gaba kuma yai baya, amma duk da haka dai
bai hana tsuntsayen ci gaba da kawo mugayen
hare-hare ba. Duk wannan gumurzu da ake yi a
cikin gudu ake yinsa.

Sau tari idan Tsuntsayen suka kawo farmaki sai
ka ga jaruman na faduwa kasa saboda karfin
iskar fuka-fukan Tsuntsayen da kuma karfin
harin nasu. Amma kuma sai ka ga jaruman sun
yi wuf sun mike sun ci gaba da gudu kafin
Tsuntsayen su cafke su duk da cewa kuwa sun
yi musu rauni. Haka dai aka ci gaba da wannan
dauki ba dadi har tsawon sa'a daya da rabi, a
sannan ne suka iso tsakiyar dajin.
Koda Tsuntsayen suka ga su Imran na neman
tsira daga sharrinsu, sai suka taru gaba dayansu
suka yi musu kawanya kuma suka yi musu
103

TASKARNOVELS.COM.NG
rubdugu aka ruguntsume da sabon azababben
yaki mai tsananin firgitarwa da tashin hankali,
domin kuwa, su tsuntsayen suna yakin ne da
dukkan karfinsu don ayi ta, ta kare, su ma su
Imran sun jajirce iyakar iyawarsu don kare
kansu.

Koda aka dan jima ana wannan bakin artabu sai
al'amura suka sauya, saboda jaruman sun fara
gajiya. Hatta gimbiya Rahila ma ta gaji ainun har
wani tsuntsu ya cafi kugunta da 'yan yatsunsa
biyu ya yunkura zai yi sama da ita ke nan sai
sadauki Imran ya do ki tsakiyar kansa da sanda.
Tsuntsun ya rikirkice, kuma ya yi wani uban
ruri sakamakon tsananin zafi da zogin da ya ji,
babu shiri ya saki Rahila ta fado kasa a matukar
galabaice, saboda kugun na ta ma da ya danka
da yatsun kafarsa ya yi ma ta rauni har ta kasa
mikewa ta ci gaba da gudu. Koda ganin halin da
Rahila ta shiga sai boka Muzaffar yai wuf ya
sure ta ya goya ta a bayansa ya ci gaba da gudu,
kuma aka ci gaba da gumurzun a haka.

104

TASKARNOVELS.COM.NG
Kaico! Tsautsayi ba a sa masa rana. Ita kuwa
masifa, idan ta zo babu makawa sai ta afku, sai
dai a dauki dakon hakuri dole.

Lokacin da aka sake dan jimawa a cikin wannan
hali sai ya zamana cewa kayan karfen da ke jikin
kowa wanda ke dan ba su kariya duka ya
kekkece babu mai sauran amfani, kowa sai ya
fara gajiya, ya Zamana cewa mugayen
tsuntsayen sun rutsa jaruman a waje daya sun
kasa ci gaba da gudu, don haka sai suka ci gaba
da kai musu mugayen hare-hare. Tun suna
karewa da mai da martani har ya zamana cewa
sun kasa mai da martanin, sai dai kare kai.
Tafiya gaba-gaba dai sai kare kai din ma ya
gagara.

Wayyo! A wannan lokaci ne fa Tsuntsayen suka
fara yiwa jaruman mugayen rauni. Sarki Laffaru
ne ya fara kifewa kasa yana mai kwarara uban
ihu sa'adda wadansu tsuntsaye biyu suka yi
masa rubdugun sara da faratan kafafunsu a
lokaci guda.
105

TASKARNOVELS.COM.NG

Saran farko a kirjinsa aka lafta masa har jini yai
feshi, sara na biyu kuwa a gadon bayansa ne
lafcece. Jarumi Shaharan da ke ta guje-guje da
zulle- zulle a tsakankanin Tsuntsayen sai shi ma
wani tsuntsu ya fake shi ya make shi a fuska.
Saboda karfin makuwar sai da yai katantanwa a
sama sau uku sannan ya baje a kasa sumamme.

Gimbiya Rahila da Zarina kuwa, wani tsuntsu ne
yai musu kwaf daya da fuka-fukansa, su ma dai
suka yi ďaiďai a kasa ko kyakkyawan motsi ba
su kara yi ba. Haiman, Shadira da boka Muzaffar
kuwa, a kafafunsu aka laf-lafta musu sara, suka
yi tsugunnon dole suna kwarara ihu sakamakon
tsananin zogi da radadin da suka ji.

Nan take jini ya rinka zuba a jikinsu, kuma jiri
ya debe su suka kwanta a kas bisa dole suka
rungumi Raddara kawai suna jiran su ji
mutuwarsu domin babu abinda za su iya
tsinanawa don kare kansu.

106

TASKARNOVELS.COM.NG

Lumaira mahaifiyar Imran da Sarkin Farisa
kuwa, tuni duk sun suma, ba don samun rauni
ba, sai saboda tsananin firgita bisa ganin
wannan gagarumar masifa da suka tsinci kansu
a ciki wacce tafi karfin jaruman da ke kokarin
kare lafiyarsu.

Nan dai ya zamana cewa babu sauran jarumi
guda daya da ke tsaye a cikinsu face sadauki
Imran, shi ma albarkacin iya sarrafa wannan
sanda da ke hannunsa ne yasa ya kai labari.

Koda Tsuntsayen suka ga saura jarumi Imran
shi kadai a tsaye yana fafatawa da su, sai suka ja
da baya gaba dayansu suka tsaitsaya a sama
cak! Cikin iska kamar hadin baki, kai kace
hutawa suke. A lokacin ne shi ma jarumi Imran
ya tsaya cak! Ya gyara tsayuwa rike da sandarsa
gamgam da hannu biyu, yayin da jini ke
satatowa ta kan gefen hannunsa na hagu
sakamakon wani lafcecen yanka da ke kan
kafadarsa.
107

TASKARNOVELS.COM.NG

Imran ya dudi gabadayan jarumai abokan
tafiyarsa ya gansu gabadaya a kwance a kas
cikin mugu hali kamar ma wasunsu sun mutu,
domin babu alamar rai a jikinsu.

A sannan ne ya tuno da mahaifiyarsa, wacce ke
goye a bayansa, kawai sai ya kira sunanta, ai
kuwasai ya ji shiru. Cikin firgici! Ya taɓo kanta
da hannunsa guda, sai yaji kan ya langabe
alamar babu rai a tare da ita.

Cikin gagarumin fushi Imran ya takarkare ya
kwarara uban ihu ya falfala da matsanaicin
gudu izuwa kan wadannan Tsuntsayen da
dukkan fushinsa da karfinsa da nufin a yi ta, ta
kare ko shi ko su!

Ai kuwa su ma Tsuntsayen sai suka taso masa
gaba dayansu suna yin wannan ruri mai iya
kurmantar da bil'Adama, amma shi bai ma san
suna yi ba.
108

TASKARNOVELS.COM.NG

Kafin ya hade da Tsuntsayen tuni ya daka
wawan tsalle sama tamkar an cilla shi daga cikin
baka ya tari Tsuntsayen ya hau dukansu da
sandarsa a cikin bakin zafin nama da dukkan
iyakar karfin dantsensa.

Bisa tsautsayi kuwa sai ya sami daya daga
cikinsu Tsuntsayen a ido. Nan take idon
tsuntsun ya fashe, ya sulalo kasa. Ji ka ke tim!
kamar giwa ta fadi, don har sai sa dakasa ta yi
girgiza. Tsuntsun ya baje matacce a kas ko
shurawa bai yi ba.

Koda Imran ya ga ya sami wannan nasa ta gano
lagon Tsuntsayen sai ya ci gaba da dukan
idanun Tsuntsayen da sandarsa. Ai kuwa sai ga
shi yana karkaɗosu kasa suna mutuwa.

Babu abin da zai yi matukar burge mutum a
wannan gumurzu face yadda Imran yake daka
tsalle sama tamkar fuka-fukai ne a jikinsa, wato
109

TASKARNOVELS.COM.NG
a sama yaci gaba da gumurzun da Tsuntsayen.
Wani lokacin ma sai dai ka ga yana tattaka
Tsuntsayen tamkar yana taka matattakalar
bene. Abinka da Sarkin yawa ya fi Sarkin karfi, a
hakan ne wasu Tsuntsayen suka rinka kai masa
sara da suka.

Wani loakcin ka ga sun same shi jini na tsartuwa
da feshi a jikinsa yana kwarara uban ihu, amma
saboda bakin naci da dakewar zuciya da juriya
shi ma bai fasa ragargazar su ba.

Abin da ya ayyana a ransa shi ne, koda
wadannan Tsuntsayen za su kashe shi sai ya
tabbatar da cewa shi ma ya yi musu muguwar
бarna da yawansu tun da dai ya gano lagonsu.

Haka dai aka ci gaba da wannan mummunan
artabu tsakanin jarumi Imran da mugayen
tsuntsayen har izuwa tsawon sa'a guda, ya
zamana cewa ya kashe fiye da kaso biyu cikin

110

TASKARNOVELS.COM.NG
ukunsu, amma fa a wannan lokaci ya gaji ainun,
har ba ya iya yin tsalle sama a kasa yake yakin.

Wani lokacin ma idan suka make shi sai ya baje
a kasa kamar ya mutu, amma da zarra sun yi
caa! a kansa za su yagalgala shi sai su ga ya mike
zumbur! Ya ci gaba da ragargazar su tamkar ma
a sannan ya fara yakin. Kai wani lokacin ma har
lambo yake yi wa tsuntsayen ya yi kamar ya
mutu, sai dai kawai su ga ya sake mikewa ya ci
gaba da kashe su.

Su kansu wadannan mugayen Tsuntsayen a iya
wanzuwarsu a cikin wannan daji ba su taɓa
haduwa da takadarin bil'Adama mai taurin rai
ba kamar Imran.

Koda Tsuntsayen suka ga Imran ya yi musu
gagarumár ɓarna, kuma ga shi sun kasa kashe
shi sai suka karaya, suka dauka cewa ba za su
iya kashe shi ba, don haka ba shiri su duka suka

111

TASKARNOVELS.COM.NG
yi sama suka luluka izuwa can kololuwar sama,
suka bar nahiyar dajin gaba daya.

A dai-dai wannan lokaci ne Imran ya kama layi
da tangadi kamar wanda ya sha giya ya bugu,
sakamakon jinin da ke zuba a cikin sassan
jikinsa. Bai ma san sa'adda sandarsa ta suбuce
daga hannunsa ba.

Tabbas a wannan lokaci inda Tsuntsayen na
kusa da salin-alin za su sa masa wawa su cinye
shi, ko ruburbushin jikinsa ma ba za su rage ba,
domin ba zai iya kare kansa da komai ba,
saboda dukkan karfinsa ya kare.

Inda Tsuntsayen sun san cewa haka za ta faru
da tabbas basu gudu ba! Nan take Imran ya kife
kasa sumamme. In da ace akwai mutum tsaye a
filin da aka yi wannan bakin gumurzu da dole ya
ce kowa ya mutu, domin babu wanda yake
numfashi daga cikin su Imran.

112

TASKARNOVELS.COM.NG
Wajen gaba daya ya yi kaca-kaca da jini da kuma
gawarwakin wadannan tauntsaye abin ba kyan
gani. Sai bayan kusan sa'a biyu lokacin da wata
irin iska mai tsananin sanyin gaske ta fara
kadawa sannan jaruna Shadira ta farfado ita
kadai.

Tana bude idanunta ta ji gaba daya jikinta yai
ma ta nauyi tamkar an danne ta da katon dutse,
don haka sai ta kasa mikewa tsaye. Koda ta dubi
filin yakin ta ga gabadayan abokan tafiyarta a
kwance babu mai numfashi, sai ta fashe da kuka,
domin a zatonta kowa ya mutu babu sauran mai
rai.

Nan fa ta fara jan jiki tana tafiya a hankali da
kyar har ta isa inda jarumi Imran ke kwance.
Shadira ta dago da kan Imran ta ga baya motsi,
kuma babu alamar numfashi a jikinsa, sai kawai
ta rungume kansa a kirjinta ta dada fashewa da
matsanaicin kuka na bakin ciki.

113

TASKARNOVELS.COM.NG
Ruwan hawayenta da ke zuba akan fuskara ne
ye zamo sanadin farfadowarsa daga dogon
suman da yayi. Nan take Shadira ta ji Imran ya
rike kafadarta da hannunsa guda.
Koda ta ji haka ta gane cewa bai mutu ba sal ta
bushe da dariya ta sake rungume shi a kirjinta
cikin tsananin farin ciki. Shi ma sai ya kama
dariyar murna. Sai da suka daďe a kankame da
juna suna ta dariya kamar ba za su saki juna ba.
Bayan sun dawo cikin haiyacinsu ne duk su
biyun suka dubi sauran abokan tafiyarsu, suka
ga cewa har yanzu fa su biyu ne rak! Suka mike,
sai hankalinsu ya dugunzuma ainun.

Imran ya dubi Shadira a lokacin da hawaye ya
subuto masa, ya ce, "Yanzu mu biyu ne rak ke
nan muka tsira da rayuwarmu a wannan daji?"
Koda jin wannan tambaya sai ita ma hawaye ya
zubo ma ta ta ce, "Haka dai yanayi ya nuna,
amma zai fi kyau mu tashi mu duba kowa, babu
mamaki akwai sauran mai rai, domin kaicma na
fitar da rai da kai, amma kuma sai ga shi ka
mike".

114

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai Imran yaji ya sami
kwarin zuciya gami da farin ciki. Kawai sai ya
yunkura ya mike tsaye da kyar yana tangadi
kamar ba zai iya taku daya ba. A haka ya nufi
inda sauran abokan tafiyar ke kwance yana
harde kafafu kamar zai fadi, domin har a sannan
bai daina jin jiri ba.

Ita kuwa Shadira sai ta sake yunkurawa domin
ta mike tsaye amma sai ta kasa.
Imran ya je kan kowa daya bayan daya ya
girgizavsu amma har ya gama duba su duka bai
ga mai alamar rai ba.

Koda ganin haka sai ya durkushe kasa bisa
guiwoyinsa ya fashe da kukan bakin ciki. Koda
Shadira ta hango halin da yake ciki sai ta ci gaba
da jan ciki har ta riske shi sannan ta kwanta
akan kirjinsa ta ci gaba da tayavshi kukan.

Da ma Imran mahaifiyarsa ce wadda ya duba
daga karshe don haka, yana kankame da ita
115

TASKARNOVELS.COM.NG
yana ta kuka, a lokacin da ya ji ya tsani kansa,
kuma ya tsani duniyar gaba daya. Bayan sun yi
kuka har sun gaji sai Shadira ta dago da kanta
daga kan kirjinsa ta dube shi ta ce, "Ya kai
masoyina, wai shin yanzu mene ne amfanin
rayuwarmu a doron kasa? Na rasa dan uwana
Masnur, kai skuma ka rasa mahaifiyarka.
Dukkan burinmu na duniya ya yanke. Yanzu ga
shi abokan tafiyarmu kaf ďinsu sun mutu. Mene
ne amfanin zuwanmu kogon Darul Iksina tunda
wadanda za mu je dominisu babu su?

Sa'adda Shadira ta zo nan a jawabinta sai Imran
ya sake fashewa da matsanaicin kuka, ya ce,
"Hakika rayuwarmu ba ta da wani amfani,
gwara ma ace mu ma duk mun mutu" Koda jin
wannan batu sai Shadira ta yi murmushi ta ce
"Ai kuwa ni yanzu farin cikin da ya rage mini a
nan duniya kawai shi ne, na mutu akan kirjinka,
ko ba komai na mutu tare da masoyina na biyu
wanda na so shi fiye da komai. Ka sani cewa in
ban da dan uwana Masnur da na rasa babu
wanda zuciyata ta aminta da shi kuma take
kauna da gaskiya sama da kai! Koda jin haka sai
hawayen farin ciki ya zubowa Imran daga can
116

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma sai ya ce, ba shakka kin zo da shawara to
amma ta yaya za mu mutu a tare ba tare da
ďaya ya riga ďaya mutuwa ba?

Shadira ta, mu nausa cikin daji watakila mu
haďu da wata muguwar dabbar, sai mu sallama
mata kanmu ta cinye mu ko kuma mu nemi
katon tsauni mu hau karshensa sai mu
rukunkume juna mu sallamo kasa bisa duwatsu
mu hallaka. Koda jin haka sai Imran ya ce,
"Tabbas kin zo da shawara mafi kyau".

Nan take Imran ya ajiye mahaifiyarsa a gefe
daya ya kura mata idanu sa'adda hawaye ya ci
gaba da shatata bisa kan kumatunsa har izuwa
tsawon 'yan dakiku, sannan ya ce, "Ya ke
Ummina ki gafarce ni, hakika zan mutu da
tsananin bakin ciki bisa rashin samun nasarar
cika burin zuciyata.

Na so a ce na mutu akan hannunki domin na
nemi gafararki bisa abin da na kasa cikawa,
117

TASKARNOVELS.COM.NG
amma idan har akwai wata rayuwar bayan
wannan na yi miki alkawari sai na cika miki
burinki.. Haka dai Imran ya ci gaba da surutai
barkatai
End Ads