Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka ji wani
irin gagarumin gurnani wanda ba su taɓa jin
irinsa ba a rayuwarsu. Gurnanin ya cika dajin
gaba daya kuma suka rasa ta inda gurnanin ya
fito. Lokaci guda su duka suka dimauce babu
wanda jikinsa bai kama kyarma ba, hatta Zarina
kuwa wacce ke kan gaba tana yi musu jagora.
Nan fa suka ji kamar su juya da baya su ranta
ana kare. Har sarki Laffaru da boka Muzaffar
sun yunkura za su juya da baya sai Zarina ta
daka masu tsawa ta ce, "Duk wanda yake son ya
juya da baya sai ya yake ni ya kawar da ni
tukunna. Ai mun yi sharadi da ku kafin mu shigo
wannan dajin, saboda haka babu gudu kuma
babu ja da baya, ko mutuwa ce sai dai mu
tunkare ta".
139
TASKARNOVELS.COM.NG
Gama fadin hakan ke da wuya sai Zarina ta daga
takobinta sama ta ci gaba da tafiya izuwa gaba.
Babu shiri kowa ya bi bayanta cikin alamun
tsananin tsoro.
Lokacin da Zarina tayi taku bakwai kacal sai
tsulum! Suka ga wani murjejen Zaki ya dako
tsalle daga can nesa bisa wani tsauni ya duro
kasa daf da su. Saboda nauyin Zakin yana dira
sai kasa ta yi girgiza, gaba daya dajin ya yi
tambal-tambal kamar zai rufta kasa.
Ko a tarihi ko a labarai su boka Muzaffar ba su
taɓa jin zaki mai girma ba kamar wannan,
domin sai an cure manyan giwaye guda uku a
waje guda sannan za su kai girman wannan
Zaki.
Da ni Maiboko da ku makaranta, bari mu jira
zuwa gobe domin mu ga wane ne zai rasa
rayuwarsa a cikin wannan dajin domin kuwa
140
TASKARNOVELS.COM.NG
tabbas! Kwarjinin wannan dajin ya ci a ce an
rasa rayuka a cikinsa.
Zakin ya wangame bakinsa mai kama da bakin
rijiya ya yi wani sabon gurnani Karfin gurnanin
ya sa bishiyoyi suka dinga kakkaryewa suna
zubewa kasa. Duwatsu suka kama mirginowa
suna karo da junansu suna farfashewa. Ba shiri
kowa ya tsugunna ya toshe kunnuwansa biyu
don gudun kada su kurmance.
Sai da gurnanin ya lafa sannan su Zarina suka
ďago da kawunansu. Bisa mamaki, sai suka
nemi wannan Zaki sama ko kasa suka rasa
kamar an yi ruwan sama an dauke dif.
Al'amarin da ya matukar dugunzuma
hankalinsu kenan, suka rasa abin da ke musu
dadi duniya, don sun tabbatar da cewa Zakin
buya ya yi domin ya kawo musu MAMAYAR
BAZATO. Cikin hanzari gabadayansu suka taru a
waje daya kowannensu ya daga makaminsa
sama yana kalle-kalle da waige-waige kawai jira
suke yi su ga ta inda Zakin zai 6ullo musu.
141
TASKARNOVELS.COM.NG
A wannan lokaci ne Zarina ta ga cewa ashe
Lumaira mahaifiyar Imran da sarkin Farisa
wanda ke goye a bayanta tuni sun suma saboda
tsananin firgitar da suka yi bisa ganin wannan
katon Zaki. Suna cikin wannan hali ne Zakin ya
yi fitar burgu daga cikin karkashin kasa ya dako
tsalle a sama izuwa kansu kai ka ce cillo shi aka
yi daga cikin baka. Cikin bakin zafin nama
gabadaya jaruman suka daka tsalle sama domin
su tare shi da nufin su sassara shi.
Kash! Rashin sani ya fi dare duhu. Inda
wadannan jaurmai sun san abin da zai biyo baya
da ba su yi wannan ganganci ba.
Koda Zakin ya hadu da su a sama sai ya kai wa
dukkaninsu hari da kafafunsa na gaba da na
baya, da kuma bakinsa a wangame. Cikin sa'a
kauwa ya cisge hannun Haiman na dama da
hannun Shaharan na Thagu. Jarumi Imran kuwa
akan cinyarsa ya lafta masa wawan sara sai ga
142
TASKARNOVELS.COM.NG
naman cinyar ya bude yana lage- lage kamar an
farke cikin dabba.
Sarki Laffaru kuwa a gadon bayansa ya tsira
masa farcen, wajen ya yi rami. Boka Muzaffar
kuwa a gefen cikinsa ya soke shi, jini yai
tsartuwa. Shadira kuwa kanta ne yai karo da
kan Zakin jini yai tsartuwa daga cikin hancinta
da bakinta, tun a saman ta suma. Zarina ce kadai
Zakin bai yiwa rauni ba amma takobinta ta rabe
gida buyu sa'adda ta dankarawa Zakin sara a
kuiɓin cikinsa. Lokaci guda jaruman duka suka
rikito kasa suka baje a kas sumammu.
Zarina ce kadai a tsaye bisa kafafunta jikinta na
kyarma saboda tsananin razana bisa ganin abin
da ya faru ga sauran abokan tafiyarta. Ita kuwa
gimbiya Rahila Zakin ya mangare ta ta je ta buga
kanta akan wani dutse, kan nata ya dare jini na
kwarara ko motsi ba ta yi ba babu alamar akwai
rai a jikinta.
143
TASKARNOVELS.COM.NG
Nan fa Zarina da ke goye da dan uwanta Sarkin
Farisa ta fara ja da baya-baya a lokacin da Zakin
ya tsaya a gabanta suna kallon-kallo.
Shi dai Zakin tsananin mamaki ne ya sa shi ya
kasa afka mata, domin a iya tsawon
wanzuwarsa a cikin wannan daji komai yawan
rudnunar mayaka in dai ya dako wannan tsalle
ya dira akansu to fa babu wanda zai tsira da
rayuwarsa. Amma yau ga shi wata hatsabibiyar
bil'adama guda daya ta tsallake wannan mugun
hari nasa.
Zarinata ci gaba da ja da baya yana tunanin
dabarar da za ta yi ta tsira daga sharri wannan
Zaki don tabbas kwaf daya zai yi mata ta mutu.
Abu na biyu kuma da ya kara dugunzuma
hankalinta shi no, ta san ba za ta taɓa iya tsere
masa ba da karfin gudu sai dai ta yi ta 'yan zillezille da guje-guje. Kuma a hakan da zarar ta gaji
zai banke ta kuma kasancewar tana dauke da
144
TASKARNOVELS.COM.NG
goyon dan uwanta ta san cewa da wuri za ta gaji
kuma ba za ta iya yin gudu mai yawa ba.
Kawai sai ta yanke shawarra ta fara guje-gujen.
ta cikin bishiyoyi tana zulle-zulle wata kila ta
shiga wani sakon inda Zakin ba zai iya shiga ba.
Gama aiyana hakan ke da wuya sai ta juya da
sauri cikin zafin nama ta falfala da azababben
gudun tsiya. Ai kuwa sai suka kasa tsere ita da
Zakin. Kafin ta yi taku uku sai ta ga Zakin ya
daka tsalle ya dira a gabanta, amma kafin shi ma
ya juyo ya fuskance ta tuni ta juya ta sauya
hanya tana mai ratsawa ta cikin bishiyoyi, shi
ma ya tuso ta a baya. Sai dai ka ga Zakin yana
banke bishiyoyin suna ratattakewa tamkar daka
su aka yi a cikin Turmi. Kai ba ma bishiyoyi
kadai ba, duk dutsen da Zakin ya bangaza da
kirjinsa take yake tarwatsewa.
Nan fa aka ci gaba da tsere tsakanin Zakin da
Zarina ta dage iya karfinta tana gudun ceton
145
TASKARNOVELS.COM.NG
ranta dana dan uwanta wanda ke goye a
bayanta. In ba don Zarina ta kasance tana da
zafin nama ba gami da juriya da kuma sanin daji
ba da tuni Zakin ya gama da ita.
Wani lokacin idan ta hango kwazazzaɓo sai ka
ga ta bi ta cikinsu da gaiya saboda shi ma Zakin
yana shiga cikinsu sai ka ga karfin gudunsa na
raguwa. Babu abin da ke daga mata hankali face
ganin duk sa'adda ta waiga bayanta sai ta ga
ashe Zakin yana daf da ita kamar ma a ko
yaushe zai iya wangame bakinsa ya hadiye ta.
Haka dai Zarina ta ci gaba da masifaffen gudu
irin wanda ba ta taɓa yi ba a rayuwarta. Shi
kuwa Zakin ya a ci gaba da binta babu alamar
zai gaji.
Sakamakon shiga ko ina da take yi ne jikinta ya
rinka buguwa da duwatsu da bishiyoyi ta rinka
samun raunika a jikinta wani lokacin ma sai dai
ta ji ice ya soke ta ta kwala uban ihu. Wani icen
146
TASKARNOVELS.COM.NG
ma idan ya soke ta karyewa yake yi a jikinta sai
dai tana cikin gudun ta zare shi, kana ganin jini
na fita a jikinta amma ba ta fasa gudun ba. Sai da
aka shafe sa'a daya da rabi ana wannan yseren
gudu tsakanin Zakin da gimbiya Zarina, shi bai
cim mata ba ita kuma ba ta tsere masa ba. A
sannan ne jiri ya fara dibarta ta kama tangadi,
amma saboda naci da tsaurin rai ba ta daina
gudun ba.
Tana cikin wannan hali ta je ta gwaru da wata
bishiya ta fadi kasa ta dinga mirginawa a kasa.
Ai kuwa sai Zakin ya dako wawan tsalle da nufin
ya diura akanta.
Abin da zakin bai sani ba shi ne, ashe sun iso daf
da wani katon rami mai tsananin fadi da zurfin
tsiya.
Zakin na dira akan Zarina sai santsi ya
kwashesu duk su biyun suka gangara cikin
wannan rami. Zarina ta kurma uban ihu a
147
TASKARNOVELS.COM.NG
lokacin da ta ga ta fada cikin wannan rami. Shi
ma Zakin sai ya wangame bakinsa ya kwarara
uban gurnani domin ya tabbatar da cewa shi ma
halakarsa ce ta zo, domin komai zai iya faruwa
idan suka isa karshen wannan rami da nisan
kasansa ya wuce a misalta shi.
Sai da suka shafe. lokaci mai dan tsawo suna
fadawa can kasan ramin. Tun kafin su isa iskar
da ke kadawa mai karfi ta sa duk suka sume ita
da Zakin.
Bisa rashin sa'a sai Zakin ya fado akan wani
dogon kahon dabba wacce ta dade da mutuwa a
cikin ramin. Take kahon ya fasa gadon bayan
Zakin ya bullutso ta cikinsa. Zakin ya kwarara
uban ihu na karshe a rayuwarsa sannan ya ama
gawa.
Ita kuwa Zarina akan wata ruɓaɓɓiyar gawar
dabbar daji ta fado da rub da ciki.
148
TASKARNOVELS.COM.NG
Sai bayan sama da sa'a biyu sannan Zarina ta
farfado daga dogon suman da ta yi tun sa'adda
take fadawa kasan ramin. Idanunta ne suka fara
budewa a hankali, ta yi arba da gawar wannan
Zaki a gabanta. Nan take farin ciki ya lullube ta.
Jin nauyi a bayanta ne ya sa ta tuna cewa duk
wannan gumurzu fa da tayi tana dauke da dan
uwanta sarkin Farisa ne a bayanta.
Cikin hanzari ta kwanto sarkin Farisa daga
bayan nata, ta shimfideshi a kas a lokacin da
kansa ya langabe idanunsa suka kafe kuma gaba
daya jikinsa ya sandare.
A zaton Zarina dogon suma ya yi, don haka sai
ta mike zumbur ta rufa izuwa cikin wani
kwazazzaɓo dake cikin ramin inda ruwan sama
ya dan taru. Zarina ta kwarfo ruwa a cikin tafin
hannunta ta zo ta watsa ruwan a fuskar sarkin
Farisa amma sai ta ga ko motsi bai yi ba.
Al'amarin da ya firgita ta kenan. Ta shiga girgiza
149
TASKARNOVELS.COM.NG
shi tana yi masa fifita har izuwa tsawon lokaci
amma shiru babu labari.
Cikin dimaucewa ta sa bakinta cikin nasa ta
hura masa iska, duk dai a banza. A wannan
lokaci ne ta tabbatar da cewa rai ya yi halinsa.
Kawai sai Zarina ta takarkare ta kwarara uban
ihu wanda ya cika dajin gaba daya da amsa
kuwa sannan ta kama gawar ta rungume a
kirjinta ta sake fashewa da matsanaicin kuka.
Allah Sarki, rayuwa ba ta da tabbas!
Duk wanda ya ga Zarina a wannan hali da ta
shiga dole ne ya tausaya mata matuka
musamman idan ya yi la'akari da tsananin
wuyar da ta sha ta tserar da rayuwar abokan
tafitarta daga sharrin wannan Zaki, amma sai
duk abin ya zamo ma ta a banza tun da ga shi ita
ta rasa dan uwanuta wanda a dalilinsa ne kadai
take son ta je kogon Darul Iksina.
Wannan shi ne abin da ya faru ga gimbiya
Zarina bayan Zakin da ya far musu ya hallaka
150
TASKARNOVELS.COM.NG
tare dan uwanta Sarkin Farisa a cikin wannan
rami ma matukar zurfi.
*********************
A can inda Zarina ta baro sauran abokan tafiya
kuwa, al'amarin ba kyan gani, domin su duka
sun yi fata-fata a cikin jini, kuma dayansu bai
farfado ba sai bayan shudewar sa'a daya da rabi.
Jarumi Imran ne ya fara farfadowa. Koda ya ga
naman ciyarsa ya fafe yana lage-lage sai yai
sauri ya kamoshi ya hade sannan ya dauko jakar
guzurinsa da ke zagaye a kugunsa ya fiddo zare
da allura ya shiga dinke raunin. Yana dinkin
yana ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da
yake ji.
Ko kadan hankalinsa bai kai kan sauran abokan
tafiya ba saboda ta kansa yake. Sai da ya gama
151
TASKARNOVELS.COM.NG
dinke raunin tsaf ya shafa magani akai sannan
jini ya daina zuba.
A wannan lokaci ne ya dawo cikin haiyacinsa.
Koda ya dago da kansa ya dubi sauran abokan
tafiya ya ga halin da suka shiga sai ya kamu da
tsananin bakin ciki kuma ya fashe da
matsanaicin kuka. Babu abin da ya fi
dugunzuma hankalinsa face ganin yadda
Haiman da Shaharan suka rasa hannayensu daidai.
Har izuwa wannan lokaci babu wanda ya sake
farfadowa daga dogon suman da suka yi. Imran
ya sake daga kansa ya dubi can inda Shadira
take ya hango ta baje a kas jini a hancinta da
bakinta ko motsi ba ta yi, sai ya zata ta mutu.
Cikin firgici ya yunkura don ya mike tsaye yaje
wajenta amma sai ya kasa domin cinyarsa tai
masa nauyi ko motsa ta bai son yi. Kawai sai ya
kama jan jikinsa a kas, a haka ya je har inda
Shadira ke kwance ya dago ta ya rungume ta a
kirjinsa ya sake fashewa da matsanaicin kuka.
152
TASKARNOVELS.COM.NG
Yana cikin wannan hali ne ya ji Shadira ta
numfasa. Cikin tsananin farin ciki ya janye ta
daga cikin kirjinsa ya dubi fuskarta sai ya ga ta
bude idanunta har tana yi masa murmushi.
Imran ya sake rungume ta, duk su biyun suka
fashe da kukan farin ciki. A dai-dai wannan
lokacin ne mahaifiyar Imran da Lumaira matar
Sarki Haiman suka farfado. Koda mahaifiyar
Imran ta ga danta a raye kuma rungume da
masoyiyarsa Shadira, sai ta cika da dumbin farin
ciki ta kama kyalkyala dariya.
Ita kuwa Lumaira matar Haiman ya yin da ta ga
mijinta da dungulmin hannu kwance a cikin jini
face-face sai ta dafe kai ta runtuma uban ihu
sannan ta cicciɓe shi ta rungume tana mai tsala
kuka domin zatonta ya dade da mutuwa. Ba zato
ba tsammani sai ta ji ya kawo numfashi. Cikin
murna ta kwantar da shi a kas tayi sauri ta cire
mayafin jikinta ta naɗe dungulmin hannun nasa
domin har a sannan bai daina zubar da jini ba.
153
TASKARNOVELS.COM.NG
Sai duk suka kurawa junansu idanu suna masu
zubar da hawaye. Duk da yake ba ganinsa take
ba.
Daga can sai ta dube shi ta ce, "Ya kai mijina
hakika in da na san za ka rasa hannunka a
wannan tafarki da na kashe kaina domin kada
ma ka yi wannan tafiya domin lafiyarka ta fiye
mini rayuwata."
Koda jin wannan batu sai Haiman ya sake
fashewa da kuka kamar ba zai daina ba, daga
bisani ya dube ta ya ce, "Ya ke masoyiyata ki
tuna cewa kin yi mini komai a rayuwa kuma ba
dan ke ba, da ban rayu ba na kawo i yanzu.
Sai da muka shafe shekara da shekaru muna
jinya sakamakon kaunarki da kulawar da kike
ba ni. Ashe kuwa raina da lafiyata ba su da wani
amfani muddin ban faranta miki rai ba.
Na rantse da darajar kaunar da ke tsakanina da
ke, lafiyarki tafi rayuwar dukkanin mutanen
154
TASKARNOVELS.COM.NG
duniya a wajena kuma ina tabbatar miki da
cewa, koda zan rasa daya hannun nawa sannan
na rasa duka kafafuna biyu muddin ina
numfashi a doron kasa zan iya tafiya da jan ciki,
to fa ba zan janye ba bisa wannan tafarki na
nema miki lafiya har sai idan babu ruhi a jikina.
Koda jin wannan batu sai Lumaira ta sake
rungume shi suka kankame juna suna masu ci
gaba da kuka.
A dai-dai wannan lokaci ne Shaharan da abokan
tafiya kowa ya farfado. Koda Shaharan ya ga ya
rasa hannunsa guda kuma ya ga bai ga Zarina da
dan uwanta Sarkin Farisa ba sai ya kamu da
tsananin bakin ciki ya rushe da kuka.
Cikin hanzari ya yage rigar jikinsa ya nannade
dungulmin hannunsa don tsaida jini sannan ya
ruga izuwa cikin dajin yana kwallawa Zarina
kira.
155
TASKARNOVELS.COM.NG
Da kyar da siɗin goshi sauran abokan tafiya
suka mimmike zaune sannan masu kwarin
cikinsu suka shiga yiwa sauran magani.
Shi kansa Boka Muzaffar sai da aka yi masa
dinki a cikinsa. Shi kuwa Sarki Laffaru a gadon
bayansa aka yi masa dinki.
Gaba dayansu dai ba su dawo cikin hayyacinsu
ba sai bayan shudewar sa'a uku. A wannan
lokaci ne kowa ya ji nadama bisa baro kasarsa
don zuwa kogon Darul Iksina domin zukatansu
duk sun karaya sun san cewa abu ne mawuyaci
dayansu ya isa kogon Darul Iksina a raye duk da
cewa saura daji daya kacal a gabansu.
Al'amarin jarumi Shaharan kuwa, lokacin da ya
nausa cikin daji yana kwala wa Zarina kira, sai
ya ji shiru kamar maye ya ci shirwa.
Bisa sa'a kuwa sai ya bi wannan hanya wacce
Zarina da wannan Zaki suka bi suna masu kasa
tsere kuma sai ya yi ta bin sawunsu.
156
TASKARNOVELS.COM.NG
Duk da haka sai da ya shafe sa'a biyu da rabi
yana ta bilinbituwa a cikin daji yana dada ci
gaba da kwala wa Zarina kira amma bai ganta
ba kuma bai ji ta amsa kiran ba.
Kwatsam! Sai ya iso gaban wannan raini mai
zurfi wanda Zarina ta fada. Yana lekawa cikin
ramin kuwa ya hango ta zaune dirshan rungume
da gawar dan uwanta Sarkin Farisa tana kuka.
Shaharan ya sake kwala ma ta kira har sau uku
amma ko dago kai ba ta yi ba bare ta kalle shi.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke nan
ya rasa abin da zai yi.
Bayan Zarina ta sha kuka ta gaji har hawayenta
ya kafe sai ta dago kai ta dubi Shaharan wanda
ke can saman ramin ta yi masa wani irin kallo
mai nuna alamun bankwana har tana daga masa
hannu. Kawai sai ta zare wata zabgegiyar wuka
a kugunta ta daga sama za ta cakawa kanta a
157
TASKARNOVELS.COM.NG
ciki. Tsawar da Shaharan ya daka mata ne ya sa
ta kasa lumawa kanta wukar ta dago kai ta dube
shi a lokacin da hawaye ya zubo ya masa.
Shaharan ya bude muryarsa da karfi ya ce, "Ya
ke masoyiyata kiyi sani cewa, kina kashe kanki
nima zan fado cikin wannan ramin na kashe
kaina, domin ban ga amfanin rayuwata ba
muddin babu ke. Haka dai Shaharan ya ci gaba
da gayawa Zarina kalmomi masu taushi irin
wadanda ke kwantar da zuciya amma da kyar
da sidin goshi ya shawo kanta ta fasa kashe
kanta.
A sannan ne fa ya fara tunanin hanyar da zai bi
ya iya fito da ita daga cikin wannan mugun rami
mai zurfi, amma sai dabara ta kwace masa.
Koda ya ga ya rasa yadda zai yi sai ya ce da ita ta
zauna ta jira zai koma inda ya baro sauran
abokan tafiya domi su taru su hada tunani da
158
TASKARNOVELS.COM.NG
basirarsu waje daya a sami yadda za a iya fito da
ita a cikin ramin".
Zarina ta ce, "Shi ke nan za ta jira ya je ya dawo".
Shaharan ya ce shi ba zai tafi ba har sai ta yi
masa alkawarin cewar ba za ta kashe kanta ba
bayan tafiyarsa ba. Nan take Zarina ta yi
rantsuwa da darajar kaunar da take yiwa dan
uwanta marigayi cewar ba za ta kashe kanta ba.
Sannan Shaharan ya juya ya falfala da gudu
izuwa inda ya baro su Muzaffar.
Da isarsa gare su kuwa ya tarar kowa ya dawo
cikin baiyacinsa amma duk sun yi zugum-zugun
kamar suna zaman makoki. Nan take ya shaida
musu duk abin da ya faru ga jaruma Zarina
cewar ita ce sanadin mutuwar wannan katon
Zaki wanda yai musu wannan mugun lahani
kuma dan uwanta Sarkin Farisa ya mutu.
Da jin haka sai dukkaninsu suka kamu da
tsananin tausayin Zarina, wasu kuma suka kama
159
TASKARNOVELS.COM.NG
kuka, wasu kuma suka kama zubar da kwalla.
Jim kadan sai Boka Muzaffar ya dubi can gefe
daya inda Aljani Marhabul Zaurus ke kwance
dauke da dokin Shaharan kawai sai ya ga ashe
shima ya rasa rabin fuka-fukinsa guda, shi kuma
dayan fuka-fukin ya tsage a tsakiyarsa tamkar
an sa Zabira an yanka tsakiyar takarda. Koda
ganin wannan al'amari sai Boka Muzaffar ya yi
ajiyar zuciya sannan ya dubi Shaharan ya ce,
"Babu wanda zai iya fito da Zarina daga wannan
rami face Aljani Marhabul Zaurus kuma ga shi
shi ma yana da nakasa amma ban sani ba ko zai
iya a hakan ba, mu je gare shi mu ji".
Nan take Boka Muzaffar ya yunkura ya mike
tsaye da kyar, shi ma Shaharan ya kama
kugunsa da hannun nasa daya jal da ya rage
suka durfafi inda Aljani Marhabul Zaurus ke
kwance. Da isarsu garshi sai Boka Muzaffar ya
dube shi ya daka masa tsawa ya