ba a so ba zai
bari Gimbiya Ramlatul Siyam ta hau ba.
A bangaren karfin sihirin tsafi kuwa, Rajwan da
Sarki Nashmir sun yi kunnen doki kuma kowa
na shakkar kowa.
290
TASKARNOVELS.COM.NG
Sarkin yaki Rajwan bai taɓa yin aure ba kuma a
duniya babu macen da yake mutuwar so sama
da Gimbiya Ramlatul Siyam, amma sai ya bar
abin a cikin zuciyarsa saboda ya san cewa
Wutsiyar Rakumi ta yi nesa da kasa.
A kullum Rajwan ba shi da wani buri a cikin
zuciyarsa wanda ya fi ya ga Sarki Nashmir ya
mutu domin ya sami damar haye karagarsa,
kuma ya aure 'yarsa Gimbiya Ramlatul Siyam.
Bisa wannan dalili ne Sarkin yaki Najwar ya
kasance mai tsananin biyayya ga Sarki Nashmir
don kada ya gane abin da ke zuciyarsa kuma bai
taɓa yarda ya nunawa Gimbiya Ramlatul Siyam
alamun soyayya ba.
Haka ya danne abin a zuciyarsa ya zamana cewa
yana fama da tsananin begenta dare da rana.
291
TASKARNOVELS.COM.NG
Saboda kwarjinin Gimbiya Ramlatul Siyam da
kuma tsoron mahaifinta ba a taba samun wani
dan Sarki ko dan Boka da ya taɓa fitowa ya nuna
yana sonta da aure ba saboda a dalilin hakan ma
an kashe sama da samari dubu wadanda suka yi
gangancin nuna soyayya a gare ta.
Dangane da ita kanta Gimbiya Ramlatul Siyam
kuwa, ba ta taɓa son wani da namiji ba, kuma
babu namijin da ya taɓa koda yin hira da ita
tsawon dakiku sittin face mahaifinta.
Tsakaninta da maza sai kallo da marmari daga
nesa, amma babu wanda ya isa ya kusance ta.
Hadimanta ma gabadaya mata ne. Kai idan ta
dauro Gimbiya Ramlatul Siyam tana shekara ba
ta ga da namiji ba face a cikin fadar mahaifinta.
Wannan al'amari yana matukar daurewa
mutanen Birnin Hindu kai domin suna wasiwasi
a cikin zuciyarsu bisa tunanin cewa Gimbiya
Ramlatul Siyam ba ta da cikakkiyar lafiya.
292
TASKARNOVELS.COM.NG
Domin a matsayinta na baligar mace ya kamata
a ce ta bukaci namiji.'
Abin da ba su sani ba shi ne; Mahaifinta ya yi
amfani da karfin sihirin tsafi wajen cire mata
sha'awa, kuma an rasa wanda zai iya karya
wannan sihiri
Lokacin da su Sharmal suka ci gaba da tafiya
bisa kan Aljani Sharkamuza a sararin samaniya
sai suka kagu ainun akan su riski su Aljani
Maruful Dauwaz domin sun dade basu yi kan
mai uwa da wabi ba. Bisa wannan dalili ne
Sharmal ya dakawa aljani ysawa Sharkamuza ya
ce, "Wai shin wacce irin tafiya ce wannan kake
yi ne har yanzu mun kasa cim ma abokan gabar
ta mu?"
Koda Aljani Sharkamuza ya ji wannan batu sai
numfasa ya ce, "Ka yi mini uzuri ya shugabana.
ya Shin kun manta ne cewa ku uku ne a zaune
bisa kaina. Nauyin kowanne daya daga cikinku
293
TASKARNOVELS.COM.NG
ya kai na giwa fa. Dole ne karfin guduna ya ragu
ainun, amma ina tabbatar muku da cewa nan da
sa'a biyu kacal lallai za mu riski su Aljani
Maruful Dauwaz a kusa da wani daji da ake kira
HIRZUL ASWAD."
Koda jin wannan batu sai Sharmal ya ce, "Ni
kuwa na taɓa ganin siffar wannan Aljani
Maruful Dauwaz a cikin madubin tsafina a wani
lokaci can baya da na yi nazari akan kogon
Darul Iksina. Wai shin ya ya karfin jarumtakarsa
da karfin sihirinsa yake ne?".
Sa'adda Aljani Sharkamuza ya ji wannan
tambaya sai ya bushe da dariya ya ce, Tabbas
Maruful Dauwaz ya cika gawurtaccen jarumi
kuma ya yi suna sosai a cikin jaruman aljanu na
duniya amma fa na fi shi komai, abin da ya ya fi
ni shi ne daukaka. A halin yanzu babu wani
Aljani mai tsananin karfin gudunsa a sararin
samaniya. Sannan yana da matukar juriya da
naci a filin yaki da shanye wuya komai
tsananinta.
294
TASKARNOVELS.COM.NG
Haka kuma yana da matukar sa'a bisa duk abin
da ya sa a gabansa. Saboda haka ina yin arba da
shi zan yi kokari na yi masa kwaf daya cikin
shammata yadda zan hallaka shi da wuri, in ba
haka ba kuwa zai iya wahalar da ni matuka ko
kuma idan na yi wasa mu yi RAGAS!"
Koda jin wannan batu sai Sharmal, Zarhuf da
Hazwan suka bushe da dariya. Hazwan ya ce,
"Yaya ma za a yi mu bari har Maruful Dauwaz ya
sami nasara akanka? Ai tuni za mu gama da shi.
Rahila da Sarki Laffaru kuwa ta farat daya za mu
gama da su, babu abin da Laffaru zai iya
tsinanawa".
Gabadayansu sai suka bushe da dariyar
mugunta, sautin dariyar tasu ya cika sararin
samaniya gaba ldaya har yana amsa kuwwa.
*
295
TASKARNOVELS.COM.NG
AL'AMARIN Aljani Maruful Dauwaz kuwa
lokacin da suka iso tsakiyar dajin Hirzul Aswad
za su gifta sai Rahila ta yi gyaran murya ta ce
"Bukata ta kama ta don haka tana son a sauka
kasa domin ta kawar da bukatar"
Koda Aljani Maruful Dauwaz yaji haka sai ransa
ya baci, ya yi tsaki ya ce, "Ai ka ji irinta! Shi ya sa
bana son tafiya ta hada ni da mace, saboda ku ba
kwa iya jure bukata. Inda za ki yi hakuri nan da
rabin sa'a za mu isa daf da Birnin Hindu, in yaso
sai nа sauka a bayan gari ki biya bukatar taki".
Rahila ta ce, "In ban da abinka ai cikin dakiku
kadan na hattama. Bawali kaɗai zan yi'.
Koda jin haka sai Aljani Maruful Dauwaz ya saki
fuka-fukansa ya yi kasa. Nan da nan ya dira akan
turba cikin dajin Hirzul Aswad.
Daji ne mai matukar kwarjini da ban tsoro,
domin yana dauke da manya-manyan bishiyoyi
296
TASKARNOVELS.COM.NG
masu yawan ganyaye a samansu, sannan akwai
makeken fili wanda sama da mutum miliyan
dubu za su iya yin yaki a cikinsa. Akwai manyamanyan duwatsu da tsaunika.
Da saukar Aljani Maruful Dauwaz sai Rahila a yi
wuf ta dirga kasa sannan ta ruga izuwa bayan
Wata bishiya. Sai da ta dubi gabas da yamma,
kudu da arewa ta yi nazarin wajen sosai sannan
ta sugunna domin tayi bawalin.
A daidai wannan lokaci ne wata irin gagarumar
iska ta taso daga sararin sama ta dugunzuma
hankalin su Aljani Maruful Dauwaz, domin ji
suka yi kamar iskar za ta sure su ta yi sama da
su, har ma sai da Sarki Laffaru ya fado kasa daga
kan Aljani Maruful Dauwaz.
Cikin firgici Maruful Dauwaz da Sarki Laffaru
suka daga kawunansu sama. Itama Rahila ba
shiri ta mike tsaye zumbur! tana mai daga kanta
sama.
297
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda duk su ukun suka yi arba da abin da ke
shirin faruwa sai suka firgice suka ji kamar su
ruga da gudu. Ba komai suka gani ba face
jaruman nan uku, wato su Sharmal bisa Aljani
Sharkamuza.
Aljani Sharkamuza na dira bisa turba sai dajin
gaba daya ya yi girgiza da tambal-tambal kamar
kasa za ta koma sama saboda tsananin
nauyinsa. Sharlisa ta ruga da gudu ta dane kan
Maruful Dauwaz shi ma Sarki Laffaru ya yi sauri
ya koma kan Maruful Dawaz, du su biyun suka
zare makamansu a lokacin da jikinsu ya kama
karkarwa kai ka ce daga cikin ruwan kankara
aka tsamo su. Tabbas su Rahila sun firgita ainun
bisa ganin
yanayin surar su Sharmal da kuma mugayen
kayan yakin da suke dauke da şu.
A bangaren Aljani Marufu! Dauwaz kuwa, shi
ma ya razana matuka da ganin Aljani
298
TASKARNOVELS.COM.NG
Sharkamuza, domin ko ba a gwada ba linzami ya
Karfin bakin kaza. Tabbas ya san cewa
Sharkamuza ya fi shi karfi, girma da duk abin da
yake takama da shi, amma saboda taurin rai irin
na Maruful Dauwaz firgitar da ya yi ba ta sa
jikinsa ya kama karkarwa ba.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su Aljani
Maruful dauwaz da su Aljani Sharkamuza. Ana
cikin haka ne Maruful Dauwaz ya ce da su
Rahila, "Duk irin bala'in da za a yi kada ku yarda
ku sauka daga kaina. Kai Laffaru ka maida
takobinka ka dauki kwari da baka domin babu
abind a za ka iya yi a wannan gumurzu face
harbi. Ni kam zan yi iya kokarina na ga cewa ba
su tarfa mu ba a waje daya domin idan har suka
tarfa mu kashinmu ya bushe sai sun hallaka mu.
Koda gama fadin hakan sai Aljani Maruful
Dauwaz ya bude fuka-fukansa ya tashi sama
kadan ya tsaya cak a cikin iska sannan ya dubi
Aljani Sharkamuza ya daka masa tsawa ya ce,
"Ya kai wannan ma'abocin karfi da kwarji mene
ne dalilinka na zuwa gare mu?"
299
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin aljani Sharkamuza ya ji wannan
tambaya sai ya bushe da dariya, lokaci guda
kuma ya murtuke fuska ya ce, "Sunana
Sharkamuza ibini Zarlala na kasance daya daga
cikin manyan hadiman Serki Nashmir na Birnin
Hindu. Waďannan jaruman da ke tare da ni
kuwa Sharmal, Zarhuf da Hazwan kenan,
manyan Dakarun yaki na Sarki Nashmir.
Sarkinmu ya aiko mu ne a gare ku domin mu
ragargaza ku mu yi filla-filla da sassan jikinku
domin kun kasance manyan abokan gabarsa
masu son raba shi da 'yarsa da kuma wani sirrin
tsafinsa. Idan kuna da wasiyya ta karshe ga
iyalanku sai ku furtata yanzu kafin mu zare
muku ruhin numfashi. Lallai za mu isar da
wasiyarku. Wannan shi ne iyakar alfarmar da za
mu iya yi muku."
Kafin Aljani Sharkamuza ya gama rufe bakinsa
sai Aljani Maruful Dauwaz ya tari numfashinsa
yana mai kara daka masa tsawa a karo na biyu
ya ce, "Ya kai tsohon azzalumi ka yi sani cewa
karyarku ta sha karya ba ku isa ku ida nufinku
300
TASKARNOVELS.COM.NG
ba akanmu. Ina tabbatar maka da cewa da cewa
sai mun yi fata-fata da ku mun maishe ku gawa
sannan mun dangana da fadar Sarkin naku mun
kawar da shi kuma mu dauke 'yar tasa gami da
sihirin tsafin nasa."
Koda jin wannan batu sai Aljani Sharkamuza da
su jarumi Sharmal suka fusata ainun jikinsu ya
kama tsuma. Cikin bakin zafin anma
Sharkamuza yai sama ya kawowa Maruful
Dauwaz wawan naushi da zabgegen hannunsa.
Maruful Dauwaz yai wuf ya sunkuya hannun
Sharkamuza ya naushi iska amma sai iskar
hannun nasa ta yi fatali da Maruful Dauwaz ta
dauke shi ta makashi a jikin wani tsauni ya
sulale kasa a matukar galabaice.
A zaton Sharkamuza kasusuwan bayan Maruful
Dauwaz sun kakkarye amma bisa mamaki sai ya
ga ya mike tsaye zumbur kamar babu abin da ya
same shi sannan ya zare takobinsa yana mai
gyara tsayuwa.
301
TASKARNOVELS.COM.NG
Duk wannan abu da ke faruwa Rahila da Sarki
Laffaru na rike da gashin wuyan aljanu Maruful
Dauwaz suna reto ba su yarda sun fado kasa ba.
Koda ganin abin da ya faru sai Aljani
Sharkamuza da su jarumi Sharmal su ma suka
zare takubbansu suka sake rugawa izuwa kansa
aka ruguntsume da sabon azababben yaki ya
zamana cewa suna kai wa junansu sara da suka
cikin zafin nama, juriya da bajinta.
Shi kuwa Sarki Laffaru wanda ya fara kokarin
kai harbi da kibiya sai Sharmal ya daka wawan
tsalle sama daga kan Sharkamuza ya doki
kirjinsa da kafa daya. Kamar ya daki tamaula
haka Laffaru ya lula can baya ya gwara kai a
jikin wani dutse. Nan take kan nasa ya dare jini
tsa jini yai tsartuwa ya fado kasa sumamme ko
motsin kirki bai yi ba. Nan fa gumurzu ya dawo
tsakanin rai biyu da rai hudu.
302
TASKARNOVELS.COM.NG
Wohoho! Hakika idan mutum ya ga mutuwa
muraran a sannan ne yake iya yin abin da shi
kansa bai taɓa tsammanin zai iya ba. Nan take
Rahila da Maruful Dauwaz suka fusata ainun
sakamakon ganin abin da ya faru ga Laffaru ya
zamana cewa sun kara ZAGE DANTSE iya
karfinsu aka cigaba da bakin artabu.
Duk sa'adda takubba suka haɗu sai dai ka ga
tartsatsin wuta da hayaki na tashi.
Da yake su Sharmal sun kasance sadaukai masu
karfin Allah Ya isa, nan da nan suka fara jigita
Rahila da Maruful Dauwaz har ta kai cewa ba sa
iya mai da martani sai dai kokarin kare kai.
Koda aka sake dan jimawa a haka sai su Sharmal
suka sami nasarar buge takobin Rahila ta fadi
can gefe daya kafin ta yi wani yunkuri tuni
Sharmal, Zarhuf da Hazwan sun kai ma ta hari a
lokaci guda.
303
TASKARNOVELS.COM.NG
Sharmal ya dankara ma ta sara a gadon bayanta,
Zarhuf ya sare ta a cinyarta, shi kuma Hazwan
ya soke ta a gefen kirjinta 6angaren hagu Take
Rahila ta kwarara uban ihu a lokacin da jini yai
feshi da tsartuwa daga jikinta sannan ta subuto
daga kan Maruful Dauwaz ta baje a kas wanwar
babu alamar rai a jikinta.
Koda Maruful Dauwaz ya ga abin da ya faru da
Rahila sai ya fusata ainun irin fusatar da bai
taɓa yi ba a rayuwarsa, kawai sai ya kurma
wawan ihu ya sake afkawa su Aljani
Sharkamuza su duka hudun ya hau su da SARA
DA SUKA ba ji ba gaji.
Duk da cewa su hudun suka tarar masa sai ga
shi ya zame musu alakakai domin sun kasa koda
kwarzanar jikinsa.
Abin da ya tayar wa da Mauruful Dauwaz
hankali shi ne shi ma ya kasa yivwa koda
304
TASKARNOVELS.COM.NG
dayansu rauni. In ba don ma yana da matukar
naci da juriya ba da tuni sun hallaka shi.
Ana cikin wannan gumurzu ne Aljani
Sharkamuza ya shammaci Maruful Dauwaz ya
durma masa wawan dundu a gadon baya.
Saboda tsananin zafi da zogin da Maruful
Dauwaz ya ji bai san sa'adda ya saki takobinsa
ba ta fadi kasa kuma ya durkushe bisa
guiwoyinsa ya kama amai da gudan jini.
Har Sharmal, Zarhu da Hazwan sun daga
takubbansu na sihiri sama za su gididdiba Aljani
Maruful Dauwaz sai Sharkamuza ya yi musu
nuni da su tsaya, sai suka saurara. Sharkamuza
ya dubi su Sharmal ya ce, "Haba! ai abin kunya
ne a ce mun kashe wannan Aljanin da makami,
da karfin dantsena zan kashe shi. Gama fadin
hakan ke da wuya sai aljani Sharkamuza ya cafi
makoshin Maruful Dauwaz da hannun hagu
sannan ya shiga gabza masa naushi da
hannunsa na dama a fuska. Karar naushin ta
cika dajin gaba daya tamkar ana dukan dutse da
katuwar guduma. Nan da nan cikin kankanin
305
TASKARNOVELS.COM.NG
lokaci ya kumbura fuskara Maruful Dauwaz ko
ina ya duri jini, tun Maruful Dauwaz na iya ihu
har sai da muryarsa ta dashe, jikinsa gaba daya
ya saki kamar an jika tsumma a ruwa ya zamana
ccwa ko motsa dan yatsan hannunsa ba ya iya yi
a lokacin da jini ke ta kwarara daga fuskar tasa.
Sai da Aljani Sharkamuza ya ga ko kadan babu
alamar numfashi a tare da Maruful Dauwaz
sannan ya daina naushinsa, sannan ya bushe da
mahaukaciyar dariyar mugunta, kuma ya shiga
yi wa kansa kirari yana koda kansa.
A daidai wannan lokaci ne Sarki Laffaru ya
farfado daga dogon suman da ya yi, kawai sai ya
ji kansa ya yi masa nauyi ainun har ma ya fi
sauran gangan jikin nasa don haka sai ya kasa
mikewa.
Koda ya bude idanunsa a hankali sai ya hango
Aljani Maruful Dauwaz a hannun Aljani
Sharkamuza ya shake wuyansa, kafafun Mauful
Dauwaz na reto babu alamar rai a tare da shi.
Nan take hawaye ya zubowa Sarki Laffaru
306
TASKARNOVELS.COM.NG
domin ya sa cewa yau dai karshen rayuwarsa ce
ta zo.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai Aljani
Sharkamuza ya ji Maruful Dauwaz ya gabza
masa wawan naushi a ido. Saboda karfin
naushin sai da hannun Maruful Dauwaz ya shige
cikin kwarmin idonsa ya fito ta keyarsa. Maruful
Dauwaz na zare hannunsa daga cikin kokon kan
sai Sharkamuza ya yanke jiki ya fadi kasa
matacce.
Koda Shamral, Zarhuf da Hazwan suka ga
wannan gagarumar jarumtaka da Maruful
Dauwaz ya yi alhalin a zaton su ma ya mutu ba
shi da rai sai suka firgaita ainun, jikinsu ya kama
karkarwa suka kasa sake afkawa Maruful
Dauwaz.
Maruful Dauwaz ya dube su a fusace sannan ya
takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin
firgitarwa. Ai kuwa sai su Shamral suka dada
307
TASKARNOVELS.COM.NG
dimaucewa suka falfala da gudu izuwa cikin
dajin Hizurul Aswad ba tare da sanin inda suka
dosa ba.
Maruful Dauwaz ya ruga inda Gimbiya Rahila ke
kwance ya rungume ta a jikinsa ya fashe da
kukan bakin ciki. Ba zato ba tsammani sai ya ji
ta kawo gwauron numfashi. Nan take Maruful
Dauwaz ya cika da tsananin farin ciki da ya ga
ba ta mutu ba dama tuni ya ga Sarki Laffaru
yana numfashi ya san cewa yana raye.
Cikin gaggawa Maruful Dauwaz ya shiga dinke
raunika ukun da ke jikin Rahila. Bayan ya gama
dinke mata raunikan sai ya shafa mata magani
jini ya daina zuba sannan ya sa mata battar
ruwa a bakinta ta sha. Daga nan sai ya koma kan
Sarki Laffaru shi ma ya dinke masa wannan
rauni da ke kansa ya sa masa magani.
Lokacin da Rahila ta farfaɗo sosai ta dawo cikin
haiyacinta ta ga yadda fuskar Maruful Dauwaz
308
TASKARNOVELS.COM.NG
ta kumbura kuma ta yi kaca-kaca da jini har ya
zamana cewa ba a shaida kamanninsa sai ta
fashe da kuka kuma ta dube shi cikin matukar
alamun tausayawa ta ce, "Ya kai jarumin
jarumai, ka gafarce ni, hakika ni ce na janyo
maka wannan masifa kuma yanzu ne na gane
irin wahalar da ka hango mana za mu shiga
bayan ka yi halwar nan ta kwana uku".
Koda jin wannan batu sai Aljani Maruful
Dauwaz ya budi baki da kyar a lokacin da yake
numfashi sama-sama kamar ba zai rayu ba ya
ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki ki yi sani cewa
wannan wahalar da muka sha yanzu ba komai
bace fac somin taɓi daga cikin irin wahalar da za
mu sha nan gaba. Bai kamata ki ba ni hakuri ba
ko ki nemi gafarata ba tunda ban fito wannan
gwagwarmaya don ke ba sai domin na cika
burin masoyiyata marigayiya Rashmin. Abin da
nake so da ke kawai shi ne idan har mun sami
nasara bisa abin da muka fito nema ki kasance
mai cika alkawari a gare ni". Koda jin wannan
batu sai hawaye ya zubowa Gimbiya Rahila ta yi
shiru ba ta ce komai ba.
309
TASKARNOVELS.COM.NG
A wannan lokaci ne Sarki Laffaru ya mike da
kyar daga inda yake kwance ya dawo wajen su
Maruful Dauwaz ya zauna sannan ya dubi
Maruful Dauwaz cikin alamun karayar zuciya ya
ce, "Zai fi kyau mu hakura da wannan bukata da
ke gabanmu domin babu yadda za a yi mu kai ga
samun nasara.
Ku duba fa ku gani, wadannan Dakarun Sarki
Nashmir ne su hudu kacal suka jefa mu a cikin
wannan hali, idan kuma muka isa fadarsa ya za
mu yi da miliyoyin Dakarun nasa?"
Kafin Sarki Laffaru ya gama rufe bakinsa tuni
Maruful Dauwaz ya tari numfashinsa yana mai
cewa, "A kul! Ka kara yi mana irin wannan
furuci. A iya rayuwata duk abin da na sa a
gabana sai na yi nasara.
Duk wuya duk rintsi ba na gudu kuma ba na ja
da baya. Babu abin da zai sa mu janye akan
310
TASKARNOVELS.COM.NG
wannan al'amari face ba na numfashi a doron
kasa.
Lallai yanzu za mu zauna anan mu yi jinyar
raunikan jikinmu har izuwa tswon kwana goma
sha hudu sannan mu ci gaba da tafiya, saboda
kasusuwan fuskata guda bakwai ne suka karye.
Hakika a iya rayuwata ban taɓa yin karo da
sadauki mai tsananin karfin naushi ba kamar
Aljani Sharkamuza. Tabbas na jinjina masa
domin ya cika gwarzo, ba zan taɓa mantawa da
shi ba.
Koda jin haka sai Rahila ta yi ajiyar numfashi ta
çe, ai komai gwarzontakarsa da karfin
naushinsa bai kai naka ba, tunda kai ka iya
shanye naushinsa da yawa amma da ka yi masa
naka guda daya sai ga shi ka burma masa kai ya
zama gawa".
311
TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin mamaki Maruful Dauwz ya dubi Rahila ya
ce, "Yaya aka yi kika san da faruwar hakan
alhalin sa'adda abin ya faru kina kwance a
sume?"
Rahila ta yi murmushi cikin karfin hali ta ce,
"ban gan sa'ad da abin ya faru ba amma lokacin
da na farfado na ga gawar Sharkamuza kuma na
ga kansa a 6ule alamar shatar hannu ce ta bula
shi, shi ne na aiyana faruwar al'amarin a cikin
zuciyata".
Koda jin haka wannan batu sai Maruful Dauwaz
ya kwanta a kas ya baje sosai don ya huta yana
mai cewa, "tabbas kina da hikima da basira Idan
kun huta ke da Laffaru za ku taru ku gyare
karayar kasusuwan fuskata.
Wannan shi ne abin da ya faru ga su Aljani
Maruful Dauwaz bayan sun yi MUGUN GAMO da
su Aljani Sharkamuza sun fafata kazamin yaki.
312
TASKARNOVELS.COM.NG
*****
A can Birnin Hindu kuwa cikin fadar Sarki
Nashmir, duk abin da ya faru tsakanin su
jaruma Rahila da su Aljani Sharkamuza a dajin
Hizurul Aswad Sarki Nashmir da dukkan
fadawansa sun gani a cikin madubin tsafinsa.
Koda gama ganin wannan al'amari sai Sarki
Nashmir ya kamu da tsananin bakin ciki. Cikin
tsananin fishi ya mike tsaye ya kwarara uban
ihu