Koda Shadira ta fuskaci alamun yana neman
zautuwa sai ta yunkura da kyar ta kama
hannayensa suka mike tsaye tare ta jan shi suka
kama dingishi suna tafiya har suka yi dan nisa
da wajen.
Ai kuwa nan take suka yi arba da wani rami mai
zurfin gaske a gabansu. Kawai sai suka dubi
juna suka yi murmushi. Ba tare da jiran komai
ba suka durfafi wannan rami ko kallon gabansu
ba sa yi, sai kallon fuskokinsu suna yi wa juna
murmushin karshe.
Saura taku uku kacal tsakaninsu da ramin sai
kawai Imran ya ji an kwala masa kiran. Cikin
dimauta da razani ya juyo baya. Koda ya ga
wanda ya kira sunan nasa sai ya cika da
118
TASKARNOVELS.COM.NG
tsananin mamaki gami da farin ciki mara
misaltuwa. Ba wani ya hango ba face
mahaifiyarsa tana rarrafe ta tunkaro su kuma
hawaye na zuba daga idanunta.
Nan take Imran ya ruga da gudu izuwa gare ta
ya sure ta ya rungumeta a kirjinsa. Shi da ita
suka bushe da dariyar murna, ya kama
sumbatar ko ina a fuskarta yana mai cewa, Ashe
ba ki mutu ba ya Ummana, ashe ba ki mutu ba"
Mahaifiyar tasa ta rike fuskarsa da hannayenta
biyu ta ce, "Ya za a yi na mutu alhalin kana raye
a doron kasa, kuma akwai alkawari a
tsakaninmu?
Ya kai dana, kayi sani cewa na dade ina
mafarkin cewa burinmu ya cika, ina tabbatar
maka da cewa ban taɓa yin mafarki bai tabbata
ba. Lallai ina ji a jikina cewa, komai wuya, komai
rintsi sai na sami lafiya na taka kafafuna ka gani
da idanunka. Koda mahaifiyar Imran ta zo nan a
zancenta sai Imran ya sake rungume ta a
kirjinsa ya fashe da kukan farin ciki, tana mai
tayavshi kukan.
119
TASKARNOVELS.COM.NG
Jaruma Shadira da ke tsaye a can bayansu tana
kallonsu cikin tsananin murna sai ta taho gare
su ita ma ta rungume su ta taya su kukan farin
cikin.
Ba zato ba tsammani sai suka ji motsi yai yawa a
bayansu. Koda suka waigo sai suka ga ashe
sauran abokan tafiyar su ne suka farfado daga
dogon suman da suka yi daya bayan daya. Cikin
tsananin farin ciki suka karaso gare su suna
tashinsu zaune.
Nan fa aka shiga taimakon juna. Masu manyan
raunika a jikinsu aka rinka dinke musu raunin,
raunin da za a sa masa magani aka sa masa
maganin.
Zarina ce ta dinkewa Shaharan manyan raunika
guda biyu da ke jikinsa da hannunta, ita kuma
dan uwanta Sarkin Farisa ya dinke nata raunin
da kansa.
120
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da Zarina ke dinkewa Shaharan
rauninsa ne Sarkin Farisa ya lura da cewa
Zarina da Shaharan suna satar kallon juna suna
murmushi, don haka sai ya gane cewa lallai
akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu.
A iya sanin da Sarkin Farisa ya yi wa Zarina ba
ta taɓa koda taɓa wani da namiji ba face shi,
kuma bai taɓa ganin ta yi wa wani murmushi ba
sai shi, amma yau gavshi ta damu bisa ranin da
ke jikin Shaharan har ta yi masa magani da
hannunta, kuma tana yi masa murmushi.
Koda Zarina ta ga cewa dan uwanta ya fuskanci
tana son Shaharan sai kunya ta kama ta kuma
hankalinta ya dugunzuma, domin ta karya
alkawarin da ta dauka cewa ba za ta yi aure ko
soyayya ba face ta samowa dan uwanta maganin
cutar da ke jikinsabCikin tsananin takaici da
damuwa Zarina ta mike tsaye tsam! daga gaban
jarumi Shaharan ta koma can gefe daya ta yi
tagumi a yayin da idanunta suka ciko da kwalla
tana mai bakin cikin saba alkawarin da ta yi.
121
TASKARNOVELS.COM.NG
A can gefe daya kuwa, gimbiya Rahila ce take sa
wa Sarki Laffaru magani akan raunikan da ke
jikinsa, ita kuma boka Muzaffar na sanya mata.
Shi kuma aljani Marhabul Zaurus ne yake sa
masa maganin. Abin da ya daurewa kowa kai a
wajen shi ne aljani Marhabul Zaurus ya fi kowa
samun yawan raunika a jikinsa a wannan bakin
gumurzu da aka yi a daji na uku, amma kuma
yafi kowa jure raunikan kuma da kansa ya yi wa
kansa magani.
Dokin Shaharan kuwa, shi kadai ne bai sami
rauni ko daya ba sakamakon kariyar da aljani
Marhabul Zaurus ya ba shi, ya lulluɓe shi da
dukkan fuka-fukansa, don haka duk harin da
aka kawowa dokin akan Marhabul Zaurus yake
karewa.
Lokacin da Sarkin Farisa ya ga 'yar uwarsa
Zarina ta koma can gefe daya ta zauna sai ya
dubi jarumi Shaharan ya ce, "Ya kai ma'abocin
122
TASKARNOVELS.COM.NG
gudu, ka yi sani cewa kai ne saurayi na farko da
'yar uwata ta nunawa soyayya a duniya.
A dalilin son da samari ke yi mata, da yawansu
sun hallaka bisa kamuwa da cutar begenta a
zukatansu. A tunanina, har abada babu wani
mahaluki da zai iya bai wa 'yar uwata farin ciki
face ni kaina, amma yanzu na karyata kaina
kuma na yi imani cewa kai za ka iya ba ta
dukkan farin cikin rayuwa.
Na sani cewa ka dade kana begen 'yar Sarkin
garinku a cikin zuciyarka, kuma ka baro kasarku
ne domin ka yi gasar tseren doki ta neman
auren 'yar Sakin naku.
Ina mai tabbatar maka da cewa 'yar uwata tafi
'yar Sarkinku kyau, ta fita karfin mulki da arziki.
Ina ji a jikina cewa abu ne mawuyaci na rayu a
cikin wannan tafiya tamu har burina ya cika,
wato samo mini maganin cutar da ta addabe ni
123
TASKARNOVELS.COM.NG
ta hana ni yin aure. Bisa wannan dalili daga yau
na ba ka amanar 'yar uwata.
Idan har rai ya yi halinsa ina son ka aure ta
domin ka debe mata kewa ta tunda kaivne za ka
iya ba ta farin cikin da take samu daga gare ni.
Ka sota, So na hakika, irin wanda dan uwa ke yi
wa dan uwansa, ba wai So irin wanda saurayi ke
yi wa budurwa ba.
Idan da hali ka So ta kamar yadda na ga
mahaifiyar imran ke son danta Imran." Sa'adda
sarkin Farisa ya zo nan a jawabinsa sai
tausayinsa ya kama jarumi Shaharan har
hawaye ya subuto masa nan take suka rungume
juna. Shaharan ya ce, "Ni kuwa na yi maka
alkawari lallai zan rike 'yar uwarka bisa amana
da soyayya mara misaltuwa. Koda jin haka sai
Sarkin Farisa ya kara Kankame Shaharan a
kirjinsa yana mai yi masa godiya.
124
TASKARNOVELS.COM.NG
Bayan gimbiya Rahila ta gama sa wa Sarki
Lafaru magani sai ya dube ta cikin mamaki ya
ce, "Ya ke wannan ma'abociyar kyawu da
jarumtaka, ke kuwa me ya sa kike nuna kauna
da damuwa a gare ni?" Koda jin wannan
tambaya sai Rahila ta bushe da dariya.
Al'amarin da ya bai wa Lafaru da boka Muzaffar
mamaki ke nan. Rahila ta hade fuskarta sannan
ta ce, "Shin ka manta ne cewa dukkan burina na
duniya ya ta'allaka ne akanka? Kamar ydda naka
ya ta'allaka akan auren gimbiya Ramlatul Siyam.
Dole ne na fara nuna maka kauna tun a yanzu
domin ta kowanne hali sai na aure ka sannan
burina zai cika. Ni yanzu babbar matsalata shi
ne, ba ni da tabbacin za mu isa can kogon Darul
Iksina gabadayanmu nan a raye, domin na
karaya bisa irin yanayin da muka tsinci kanmu a
ciki.
Da farko dai na san cewa gaba dayanmu nan
babu mai jarumtakata amma sai ga shi na kasa
tsinana komai a cikin wannan daji na uku da
muka shigo. Ko shakka ba na yi jarumi Imran ne
125
TASKARNOVELS.COM.NG
ya kashe tsuntsayen nan kuma bai isa ya kashe
su ba gaba daya ina kyautata zaton dai guduwa
suka yi da suka ga barnar de yake musu ta yı
yawa. Ku tuna cewa yanzu fa saura mugayen
dazuzzuka guda biyu a gabanmu kuma masifar
da ke cikinsu ta fi wacce muka wuce a baya."
Koda Lahira ta zo nan a zancenta sai jikin kowa
yai sanyi kuma hankali ya dugunzuma aka yi tsit
ana tunanin zuci. Tsawon 'yan dakiku dayansu
bai ce uffan ba.
Daga can sai sarki Laffaru ya dubi boka
Muzaffar ya ce, "Ya kai abin dogaronmu wai
shin yanzu idan muka ratsa ta cikin wadannan
dazuzzuka biyu muka wuce lafiya, ya ya batun
shiga cikin kogon Darul Iksina ya ke? Shin babu
wata matsala da za mu fuskanta a cikinsa?"
Koda boka Muzaffar ya ji wannan tambaya sai
yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ni kam dukkan
ilimina ya tsaya iya nan ban san ma yadda za mu
iya shiga cikin kogon Darul lksina ba kuma ban
san irin matakan tsaron da ke cikinsa ba".
126
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai ran sarki Laffaru ya
ya dubi boka Muzaffar a fusace ya ce, "Ashe kai
wawa ne ba ka san ciwon kanka ba! Yanzu kai
da ba ka ma san yadda za mu shiga cikin kogon
Darul Iksina ba amma ka debo mu muka sha
wannan bakar wahala?"
Kafin sarki Laffaru ya gama rufe bakinsa boka
Muzaffar ya daka masa tsawa wacce ta firgita
shi ainun ya ji kamar an kaɗa hantar cikinsa.
Boka Muzaffar ya ce, "Ai kaine babban wawa
wanda rashin hangen nesansa ya jefa shi a cikin
bala'i.
Ai wanda yake cikin ruwa ko bakin takobi masa
kamawa zai yi. Shin ka manta da bala'in da kake
ciki ne na abokiyar gabarka Sharlis? Ai da ka
zauna ka jira ranar da ɗanta zai girma ya yi
maka gisan gilla ya haye kan mulkinka da
dukiyarka gwara ka taho neman maganin
wannan barna koda kuwa ba za ka samu ba. Ka
127
TASKARNOVELS.COM.NG
tuna cewa rai ba a bakin komai yake ba muddin
akwai biyan bukata. Sai da Sharlisa ta sai da
rayuwarta ta sha bakar wahala tun tana yarinya
karama har ta girma sannan ta sami nasarar
hawa kan tafarkin daukar fansa a kanka. Saboda
me kai yanzu ba za ka sallama rayuwarka ba
don ganin ka kubuta daga sharrinta?
Gabadayan abokan tafiyar nan tamu sun
sallama rayuwarsu ne don cika burin
zuciyoyinsu, ga shi har daya daga cikinsu ta rasa
dan uwanta, dukkan burinta ya rushe, amma
duk da haka ba ta fasa ci gaba da yin wannan
tafiya ba. Ai ko ba komai mun ajiye abin tarihi
wanda babu wani mahaluki da ya
taba yinsa, koda kuwa a iya nan tafiyarmu ta
yanke. Lokacin da boka Muzaffar ya zo nan a
jawabinsa sai sarki Laffaru ya shiga taitayinsa
har ya bai wa Laffaru hakuri. Al'amarin da ya
janyo jikin kowa ya yi sanyi ke nan.
Boka Laffaru ya ce, "Ya zama wajibi mu zauna
anan har tsawon mako biyu domin mu yi jinyar
128
TASKARNOVELS.COM.NG
jikinmu sosai kafin mu shiga daji na biyar
saboda idan muka yi gangancin ci gaba da tafiya
a haka, cikin kankanin lokaci mu duka zamu
hallaka". Nan take kowa ya aminta da wannan
shawara ta boka Muzaffar. Ba tare da ɓata lokaci
ba suka kafa tantuna sannan aka ci abinci.
Bayan kowa ya huta sai suka shiga janye
gawarwakin wadannan tsuntsaye suna jefa su a
cikin ramin nan mai zurfi don kada su dame su
da doyi, kuma kananan tsuntsaye masu cin
mushe su adabbe su a wajen.
Suna gama watsa tsuntsayen a cikin ramin sai
suka kunna wuta suka jefa a cikin ramin. Nan
take gaba dayan gawar tsuntsayen ta kama ci da
wuta.
Haka dai su Imran suka ci gaba da zama a cikin
wannan daji suna jinyar kansu har tsawon mako
biyu amam kullum a tsorace suke domin gani
129
TASKARNOVELS.COM.NG
suke kamar ko yaushe ragowar wadannan
tsuntsayen za su iya
kawo musu MAMAYAR BAZATO.
Ai kuwa tsuntsayen sun sha zuwa su yi shawagi
a samansu amma wani Iko na Allah ko sau daya
tsuntsayen ba su yi yunkurin kai musu hari ba.
Daga karshe ma sai tsuntsayen suka ɓace ɓat
tamkar ba su taɓa wanzuwa ba a dajin.
A ranar da kwanaki goma sha hudu suka cika ne
kowa ya ji ya sami karfin jikinsa sai dai tabon
raunika kawai a jikinsu. Nan fa suka yi shiri
kowa ya kimtsa sannan aljani Marhabul Zaurus
su duka ya tashi da su sama aka ci gaba da taifya
suka durfafi daji na hudu wanda ke dauke da
muggan dabbobin daji iri-iri masu matukar
hadari
Da isowarsu farkon dajin sai aljani Marhabul
Zaurus ya saki fuka-fukansa ya sauko kas ya
tsaya cak bai motsa ba. Kowa sai ya noke ya ki
130
TASKARNOVELS.COM.NG
saukowa daga kan aljani Marabul Zaurus aka
kama kallon- kallo.
Al'amarin da ya sa boka Muzaffar ya bushe da
dariya ke nan ya ce, "Me kuke tsoro kowa ya
kasa sauka kasa? Ba a sami wanda ya iya amsa
masa wannan tambaya ba. Koda ganin haka sai
boka Muzaffar ya sauka kas sannan ya dubi
gimbiya zarina ya ce, "Gaishe ki ya mai ilimin
daji ki yi sani cewa yau ne ranarki domin muna
bakin daji na huďu da ke dauke da mugayen
dabbobi. Ke kaɗai ce za ki iya kuбutar damu a
cikin wannan daji don haka sai ki sauko ki yi
mana jagora har mu isa karshen dajin".
Koda jin wannan batu sai Zarina ta yunkura za
ta sauko kas. Cikin hanzari sarkin Farisa ya ruko
ta dube ta cikin alamun firgici da tashin hankali
a lokacin da idanunsa suka ciko da kwallah ya
ce, "Ya ke 'yar uwata ki yi sani cewa a halin
yanzu zuciyata tana bugawa da karfi kuma ina ji
a jikina cewa in dai muka shiga cikin wannan
daji karshen zamanmu tare ya zo. Ni kam na
hakura da wannan buri da ke gabanmu saboda
131
TASKARNOVELS.COM.NG
haka mu yanke wannan tafiya tamu daga nan
mu zauna anan mu jira mu ga abin da hali zai yi
ko abokan tafiya za su isa can kogon Darul
Iksina su dawo lafiya. Idan kuma ba su dawo ba
sai mu juya da baya mu koma kasarmu. Gwara
mu koma gida mu ci gaba da rayuwarmu a cikin
mulkinmu muna ganin juna ba tare da mun cika
burinmu ba".
Sa'adda sarkin Farisa ya zo nan a zancensa sai
Zarina ta kamu da tsananin tausayinsa har
hawaye ya zubo ma ta. Nan take ta rungume shi
tana mai cewa, "Ya kai dan uwana ka kwantar
da hankalinka ka sani cewa babu abin da zai
same ka muddin ina tare da kai, duk tsautsayin
da zai taɓa ka sai dai bayan ya taba ni. Ka tuna
cewa yanzu fa saura daji daya jal a gabanmu mu
isa kogon Darul Iksina bayan mun gama da
wannan wanda ke gabanmu. Bai kamata a ce
wannan wahala da muka sha ba a baya ta zama
ta banza ba dama masu magana sun ce 'Idan
aski ya zo gaban goshi ya fi zafi' Amma kuma ai
bayan wuya sai dadi."
132
TASKARNOVELS.COM.NG
Ya yin da Zarina ta zo nan a zancenta sai jikin
sarkin Farisa ya yi sanyi. Haka dai ya sauko daga
kan aljani Marhabul Zaurus ba a son ransa ba.
Yana sauka sai Zarina ta goya shi a bayanta ta
ɗaure shi tamau sannan ta matsa gaba tayi taku
bakwai sai ta waigo ta dubi su Imran ta ce, "A
nan za ku tsaya ne ko kuwa za ku biyo ni?"
Da jin haka sai gaba dayansu suka sauko da
sauri daga kan aljani Marhabul Zaurus sannan
gimbiya Lahira, boka Muzaffar da sarki Laffaru
suka bi su a baya aka nausa cikin wannan daji
na biyar. Zarina na kan gaba tana dube-dube da
waige-waige har suka shafe dan dogon lokaci ba
su gamu da komai ba, kuma ba su ji sautin
komai ba a cikin dajian tamkar babu wani abu
mai rai a cikinsa.
Kwatsam! Sai suka iso wata mararraba wacce ke
dauke da alamar hanyoyi guda bakwai. Da
zuwansu wannan wuri sai Zarina ta tsaya cak ta
zaro takobinta.
133
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ganin haka sai kowa ma ya gyara
makaminsa. Zarina ta dubi kowacce hanya daga
cikin guda bakwan ta yi nazarinsu sosai amma
ba ta ga sawun wata dabba ba a cikinsu. Ta
tsugunna ta dora kunnenta a kan kasa, nan ma
sai ta ji shiru. Kawai sai ta mike tsaye ta dubi
abokan tafiya cikin alamun karayar zuciya ta ce,
"Ya ku abokan tafiya ku yi sani cewa na kasa
gano ainihin halin da wannan daji ke ciki a
yanzu domin babu wata alama ta wata dabba a
cikinsa. Tabbas idan ma akwai dabbobi a cikin
wannan daji sun kasance masu wayon gaske,
kuma ba mamaki sun kasance masu yawo a
sama, wato fuka-fukai ne da su domin babu
alamar sawun kafafunsu akan kasa. Saboda
haka yanzu ba mu da wani zabi wanda yafi mu
yi kundunbala mu afka cikin dajin ta cikin daya
daga cikin wadannan hanyoyi bakwai, in yaso
idan ma mun haɗu da wata dabbar a gaba sai
mu yake ta".
Koda gama fadin haka sai Zarina ta kunna kai
izuwa cikin dajin ta bi hanyar farko daga cikin
bakwan, suma suka rufa ma ta baya.
134
TASKARNOVELS.COM.NG
Nan fa suka yi ta tafiya Zarina ta raba hankalinta
biyu ya zamana cewa tana kallon kasa ko za ta
ga sawun wata dabba, kuma tana kallon saman
bishiyoyi ko za ta ji wani motsi, amma shiru
kamar an aiki bawa garinsu.
Wani babban abin tashin hankali shi ne, suna
fara nisa a cikin dajin suka tsinci kansu a cikin
wadansu irin dogayen bishiyoyi masu yawa har
gaba daya dajin ya yi dan duhu. Tabbas wata
muguwar dabbar za ta iya ɓuya a cikin
wadannan duhuwoyi na saman bishiyoyin.
Haka dai suka ci gaba da tafiya har tsawon rabin
sa'a amma ba su hadu da komai ba. Kwatsam Sai
Zarina ta ga wani katon sawu na Gwaggon Biri.
Saboda girman sawun har wajen rami ya yi
wanda su duka suka shige cikin ramin suka
tsaitsaya. Kowa ya rika kallon sawun cikin
tsananin mamaki.
Cikin firgici boka Muzaffar ya dubi Zarina ya ce,
"Ya ke masaniyar daji, wannan sawun wacce
irin dabba ce haka?".
135
TASKARNOVELS.COM.NG
Zarina ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Ba sawun komai
ba ne face na gwaggon biri".
Koda jin haka sai kowa ya firgita aka zazzaro
idanu ana mamaki. Muzaffar ya ce, "Yanzu dama
akwai biri mai tsananin girma kamar haka?"
Zarina ta ce, "Ai a duniya gaba daya kaf irin
wadannan birirrika guda uku ne kacal. Daya
yana wannan nahiya. Na biyun yana can nahiyar
Bimin Sin. Shi kuma na ukun yana can nahiyar
Birnin Hindu.
Su ne birirrika guda uku wadanda babu
kamarsu a duniya. tabbas idan muka yi gaba da
gaba da wannan biri dayanmu ba zai tsira da
rayuwarsa ba kuma daga yanzu zuwa koda
yaushe za mu iya yin arba da shi. Ni dai a tawa
shawarar zai fi kyau mu koma da baya mu sauya
wata hanyar".
136
TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'adda sauran abokan tafiya suka ji wannan
batu sai hankalin kowa ya dugunzuma aka yi
shiru ana tunani. Daga can sai boka Muzaffar ya
ce, "Ya ku abokan tafiya kun sani cewa a
cikinmu nan gaba daya babu wanda ya san
sirrin daji da sirrin mugayen dabbobin dake
cikinsa sama da jaruma Zarina, saboda haka
dole ne mu yi amfani da dukkan shawarar da ta
ba mu. Ina ganin cewa zai fi kyau mu koma da
baya mu sauya hanya kamar yadda ta shawarce
mu". Da jin haka sai kowa ya aminta, ba a sami
wanda ya yi gardama ba. Nan take suka
dunguma suka juya da baya suka koma izuwa
farkon hanyar inda ta rarraba izuwa kaso
bakwai.
Da zuwa sai suka tsaya suna shawarar hanyar
da ya kamata su bi daga cikin bakwan, aka rasa
wanda zai zaɓi hanyar. Kawai sai boka Muzaffar
ya dubi Zarina ya ce, "Ya ke wannan jaruma ki yi
sani ccwa ke ce shugabarmu a cikin wannan
tafiya don haka ke ce za ki zaɓar mana hanyar
da ya kamata mu bi". Sa'adda Zarina ta ji haka
sai ta yi ajiyar zuciya sannan ta cc, "Zan zaɓi
hanya daya daga cikin ragowar guda shidan da
137
TASKARNOVELS.COM.NG
suka rage mana. Amma fa ku sani cewa duk
hanyar da muka bi babu komawa da baya komai
bala'in da muka gani a cikinta".
Koda jin wannan batu sai kowa yai shiru aka
rasa wanda zai zo da jayayya. Kawai sai sadauki
Haiman ya ce, Mun yarda da wannan sharadi
naki. Koda jin haka sai gimbiya Zarina ta nufi
wata hanya da ke tsakiyar hanyoyi shidan da
suka rage ta durfafi cikinta kai tsaye ko waige
ba ta yi.
Sadauki Haiman wanda ke goye da matarsa
Lumaira shi ne ya fara bin bayanta sannan
Imran goye da mahaifiyarsa, sai Shaharan
sannan gimbiya Rahila, boka Muzaffar, sarki
Laffaru. Aljani Marhabul Zaurus ne a karshe
dauke da dokin Shabaran wanda ko yaushe a
durkushe yake bisa kafafunsa ko mikewa baya
iya yi sakamakon rashin lafiyarsa.
138
TASKARNOVELS.COM.NG
Haka dai waɗannan jarumai suka wanzu suna
tafiya a cikin wannan daji har tsawon sa'a guda
ba