Al'amarin da ya dugunzuma hankalin jaruman
kenan musamman Haiman da Shaharan
wadanda suka kasance miskinai masu hannu
dai dai. Imran da Gimbiya Rahila, Shadira da
Zarina ne kawai suke gagarumin kokari sai
kuma Boka Muzaffar da ke taimaka musu amma
Sarki Laffaru buya yake yi kawai a bayansu yana
gudu.
Sai da aka shafe sa'a daya da rabi ana wannan
bakin gumurzu, ya zamana cewa kurar rairayin
ta tashi ta bulbule dajin gaba daya har ma basa
iya ganin junansu sosai kuma duk da cewa suna
ja dabaya cikin gudu suna yakin amma ba su isa
kogin Tudun Tsira ba.
A daidai wannan lokaci ne jaruman suka fara
gajiya ya zamana cewa da kyar suke iya kare
harin Kunamar, kuma a sannan ne Kunamar ta
181
TASKARNOVELS.COM.NG
fara kawo musu suka da tsinin faratan
hannayenta. Da zarar sun kare sukar da
garkuwa sai ka ga farcen Kunamar ya burma
garkuwar tamkar an buda ganga da wuka.
Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalinsu ke
nan. In ba don ma jaruman sun kasance masu
matukar juriya da na ci ba da tuni Kunamar ta
gama yin fata-fata da sassan jikinsu tun a farkon
fara gumurzun.
Ya yin da Kunamar ta ga an jima ana wannan
dauki ba dadi amma ba ta sami nasarar suka
koda jikin daya daga cikinsu ba sai ta fusata
ainun, ta kara kaimi, ta mai da hankalinta akan
kai musu munanan sara. Ai kuwa nan da nan ta
lalata dukkan garkuwoyinsu suka yi ta jifa da su,
bisa dole suka ci gaba da yakarta da takubba.
Kaico! Tashin hankali ba a sa masa rana. A
wannan lokaci ne Kunamar ta sami lagon
jaruman ta fara samun nasarar saran jikinsu. A
182
TASKARNOVELS.COM.NG
lokaci guda ta sari Shadira da Zarina a damtsen
hannayensu wurin ya yi rami mai zurfi jini yai
feshi suka kwalla ihu suka fadi can gefe daya a
matukar
galabaice. Haiman, Imran da Zarina, Rahila da
Shaharan kuwa a kafafunsu ta sassaresu ta yi
watsi da su can gabanta.
Boka Muzaffar da Sarki Laffaru gami da Aljani
Marhabul Zaurus kuwa wani irin wawan
mangari tayi musu suka yi sama kamar an cilla
su daga cikin Baka sannan suka fado a kasa a
sume kuma a warwatse. Nan take Kunamar ta
ruga izuwa inda su Shaharan ke zube a kas
domin ta karasa hallaka su. Suna ji suna gani
aka rasa wanda ai iya mikewa tsaye ya kare
kansa. Tuni a wannan lokaci mahaifiyar Imran,
Lumaira da dokin Shahara sun dade da suma
sakamakon mummunar buguwar suka yi a kas.
183
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ya rage bai fi saura taku goma ba tsakanin
Kunamar da su Imran, Shaharan ya ga mutuwa
muraran ta taho gare su sai ya kwarara uban
ihu, duk da cewa akwai Raton rauni a kafarsa
wanda naman wajen ya zabtare yana reto har
ana ganin kashin Kafar sai ya daka wawan tsalle
sama kamar kibiya aka harba ya dira akan
tsakiyar Kunamar yana rike da takobi da hannu
daya. Daya dungulmin hannun nasa kuwa ya
naushi idon kunamar da shi. Saboda karfin
naushin sai da dungulmin hannun nasa ya nutse
a cikin idon Kunamar. Yana zaro hannun nasa
sai ga jini yana feshi.
Duk da haka Kunamar ba ta daina kawo masa
sara da suka ba da dukkan sauran hannayenta,
shi kuwa ya wanzu yana mai kade hannayen na
ta da takobinsa cikin bakin zafin nama wanda
ko a mafarki bai taɓa zaton zai iya yin hakan ba.
A hakan Kunamar ta ci gaba da matsawa tana
kokarin isa inda su Haiman ke kwance sun kasa
tashi domin ta turmushe su.
184
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Shaharan ya gane nufin Kunamar sai ya
sake dankara ma ta wawan naushi a daya idon
nata. Take shi ma idon ya burme, jini ya kama
ɓulbulowa ta zama makauniya.
Wohoho! Nan fa Kunamar ta haukace ta yi wata
uwar girgiza ta jeho Shaharan kasa daga kanta.
Dai-dai inda ya fadin ta kai wawan suka da
dukkan hannayenta, cikin matsanancin bakin
zafin nama ya goce, kafafuwan na ta suka cake a
cikin kasa suka lume can kasa. Kafin ta zaro
kafafun na ta Shaharan ya mike zumbur ya
falfala da masifaffen gudu. Duk da cewar
Kunamar ta makance, sai ta yi amfani da sautin
takun sawayensa ta bi shi a guje, suka kasa uban
tsere.
Tabbas in ba don Shaharan ya yi wannan dabara
ba ya dauke hankalin Kunamar daga wajen
abokan tafiyar tasa da sai ta hallaka dukkan
abokantafiyar a lokaci guda.
185
TASKARNOVELS.COM.NG
Sai da aka shafe rabin sa'a ana wannan tseren
gudu tsakanin Shaharan da wannan Kunama,
duk sa'adda ya waiga bayansa sai ya ga tazarar
da ke tsakaninsa da ita bai wuce kamu biyar ba,
don haka a ko yaushe za ta iya luma masa
faratanta.
Da zarar ya yi yunkurin sauya wurin da ya nufa
sai ya ga itama Kunamar ta sauya ta bi shi.
Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalinsa ke
nan musamman da ya ga cewar har a sannan ba
su iso kogin tudun tsira ba.
Baya ga wannan tashin hankali da yake ciki abin
da yai ta fado masa a rai shi ne, rashin sanin
halin da su Zarina ke ciki a yanzu. Shi dai ya san
cewa gabadayansu suna cikin mugun hali, babu
mamaki ma wasunsu sun mutu bai sani ba, don
haka, kokarinsa shi ne yai sauri ya kai kunamar
cikin wannan kogi domin ta hallaka sannan ya
dawo baya a guje domin ya kaiwa su Zarina
agajin gaggawa. Haka dai Shaharan ya ci gaba da
gudu iyakar karfinsa.
186
TASKARNOVELS.COM.NG
Hakika idan masifa ta kai masifa mutum na iya
mantawa da wani bala'in. Saboda tsananin
tsoron wannan Kunama wacce ke biye da
Shaharan, ya manta da lafcecen raunin da ke
kafarsa har ma gudan tsokar da ya zabtaro a
jikin kafar ya gutsure da kansa ya fadı kasa
amma bai sani ba.
Da kyar da siďin goshi Shaharan ya riga wannan
Kunama isa cikin wannan kogi na tudun na
tsira, amma kafin ya faɗa cikin kogin sai da ta
sare shi da kaifin faratanta sau uku a gadon
bayansa. Duk sa'adda ta sare shi sai ya tsandara
ihu ya gantsare kamar zai fadi kuma sai jini ya yi
feshi daga jikinsa.
Yana fadawa cikin kogin ne ita ma Kunamar
kafafunta suka tsunduma a cikin ruwan kogin.
Nan take jikin Kunamar ya kama narkewa, kafin
cikar dakika sittin gaba dayan jikin nata ya
narke ya zama ruwa. A sanann ne jarumi
187
TASKARNOVELS.COM.NG
Shaharan ya fito daga cikin ruwan da kyar yana
dingishi da mai da numfashi kamar zai mutu.
A dai-dai wannan lokaci ne ya ji raunin kafarsa
ya dame shi da tsananin zogi. Koda ya dubi
raunin ya ga yadda tsokar naman kafarsa ya
zabtare sai ya kwarara uban ihu ya fadi kas.
Yana faduwa ya tuno da halin da ya baro abokan
tafiyarsa, sai ya sake mikewa zumbur! Ya falfala
da irin wannan azababben gudun nasa ya koma
da baya tamkar babu wannan rauni a jikinsa.
Da isar Shaharan inda ya baro su Haiman sai ya
iskesu a cikin wani irin mugun hali. Duk
wuraren da wannan Kunama ta sara a jikinsu
har ya rube ya fara tsutsa kuma wajen dada
girma yake yana dada zabtarewa, su duka suna
ihu.
Ya Koda ganin wannan bala'i sai hankalinsa ya
dugunzuma ainun kuma ya cika da tsananin
188
TASKARNOVELS.COM.NG
mamaki bisa yadda aka yi shi nasa raunin bai
rube ba ya kama tsutsa.
Abinda ya fara fado masa a rai shi ne, watakila
saboda ya shiga cikin wannan kogi ne na tudun
tsira shi ya sa nasa raunikan ba su yi tsutsar ba.
Cikin firgici da hanzari ya cicciɓi Zarina da
Shadira ya saɓa su a kafadunsa ya sake
falfalawa da gudu ya nufi inda kogin tudun tsira
yake. Wannan karo shi kansa ya yi matukar
mamaki bisa ganin irin masifaffen gudun da
yake yi don ya ninka wanda ya yi da farko.
Kafin rabin-rabin sa'a ya iso bakin kogin. Da
zuwa sai ya jefa Zarina da Shadira a ciki, suna
fadawa cikin kogin sai raunikan nasu suka daina
tsutsa kuma suka dawo kamar yadda suke da
farko. Koda ganin haka sai farin ciki ya lullube
Shaharan ya juya da sauri ya sake falfalawa da
gudu ya koma can wajen sauran abokan tafiya.
189
TASKARNOVELS.COM.NG
Haka ya rinka dauko su da bibbiyu akan
kafadunsa yana gudu yana kawo su cikin kogin
tudun tsira yana watsa su ciki har ya gama debo
su gabadaya ya zamana cewa saura dokinsa da
Aljani Marhabul Zaurus kadai.
wannan lokaci shi ma dokin Kunamar ta sare shi
a waje biyu kuma raunin ya zama tsutsa har ya
cinye rabin jikinsa, dokin ya baje a kas har ya
fara kokarin mutuwa.
Koda Shaharan ya ga halin da dokinsa ke ciki
kuma ya ga shi ma Aljani Marhabul Zaurus yana
cikin irin wannan hali sai hankalinsa ya
dugunzuma ainun tunda shi ma Marhabul
Zaurus din ba zai iya koda mikewa zaune ba
bare ya dauki dokin ya kai shi can bakin kogin
tudun tsira.
Shaharan ya sunkuya ya cicciɓi dokinsa da
dukkan karfinsa amma sai ya kasa koda raba
dokin da kasa ne saboda nauyinsa. Sai da
190
TASKARNOVELS.COM.NG
Shaharan ya jarraba daukar dokin nasa har sau
uku amma yana kasawa, kawai sai ya zauna a
gefe daya yana kallon dokin yana kuka, sa'adda
dokin ya fara kakarin mutuwa.
Yana ji, kuma yana gani tsutsa ta baibaye
gabadaya jikin dokin, wannan tsutsar ta zamo
sanadin ajalinsa. Nan fa Shaharan ya kurma
uban ihu sannan ya sake fashewa da matsancin
kuka.
Shi kuwa Aljani Marhabul Zaurus lokacin da
azabar tsutsar jikinsa ta addabe shi sai ya fara
ihu yana kuka yana mai cewa, "Ya kai wannan
jarumi ka sani cewa ni ma mutuwa zan yi yanzu,
ina mai yi maka gargadi da ka yi hankali da
Boka Muzaffar domin gaba dayanku yaudararku
yake yi, so yake da zarar kun isa kogon Darul
Iksina ya hallaka ku, ku duka saboda shi kadai
yake son ya mallaki wannan ruwan sihiri da
kuma Aljani Maruful Dauwaz.
191
TASKARNOVELS.COM.NG
Tabbas idan ya mallaki wadannan abubuwa
biyu babu abin da zai gagare shi a cikin wannan
duniya. Ni kaina sai yanzu ne na gane cewa ya
yaudare ni ya cutar da ni.
Tabbas wannan duniya makaranta ce kullum
ana samun kima a cikinta. Ka yi hattara ya kai
Shaharan, lallai ka yi iya kokarinka wajen ceton
rayuwar sauran abokan tafiya. Ni kam tawa ta
kare, sai dai nan gaba ku bayar da labarina idan
kun tsira da rayuwarku!".
Gama fadin hakan ke da wuya sai Aljani
Marhabul Zaurus ya ɓingire kasa ya zama gawa.
Shi kuwa jarumi Shaharan sai ya ci gaba da
matsanaicin kuka sakamakon mutuwar dokinsa.
Bai gushe ba yana wannan kuka har izuwa
tsawon sa'a guda sannan ya mike tsaye ya juya
ya nufi hanyar da za ta kai shi can bakin kogin
tudun tsira. Yana tafe yana waigen dokinsa yana
zub da hawaye har ya daina hango dokin nasa.
192
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da Shaharan ya iso bakin kogin tudun
tsira sai ya iske kowa ya dawo cikin haiyacinsa,
ana ta yi wa juna magani a jikin raunika.Tun
daga nesa Zarina ta hango shi sai ta mike tsaye
ta ruga gare shi, suna haduwa suka rungume
juna cikin tsananin farin ciki.
A wannan lokaci Haiman da matarsa Lumaira na
zaune a gefe daya suna ta duba lafiyar junansu
kuma suna murna da ganin junansu a raye.
Shadira Imran da mahaifiyarsa ma suna gefe a
tare. Boka Muzaffar, Sarki Laffaru da Gimbiya
Rahila na zaune a tare su ma suna ta murna da
ganin kansu a raye
Lokacin da Boka Muzaffar ya ga jarumi
Shaharan ya dawo shi kadai babu dokinsa kuma
babu Aljani Marhabul Zaurus sai ya ji a jikinsa
cewa lallai Aljani Marhabul Zaurus da dokin
Shaharan rai ya yi halinsa.
193
TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin hanzari Zarina ta janye jikinta daga cikin
na Shaharan ta shiga duba lafiyarsa. Koda tayi
arba da wannan katon rauni da ke kafarsa sai ta
dimauce kuma ta fashe da kuka. Nan take ta
zaunar da shi ta shiga sa masa magani akan
raunin sannan ta je ta nemo tsumma mai tsafta
ta nannade raunin duka ta ɗaure shi.
Gama hakan ke da wuya sai ta kwantar da
Shaharan a kas tana mai dora kansa akan
cinyarta ta shiga tunani mai zurfi. Daga can sai
ta fara rera waka cikin sanyaya kalamai masu
dimauta maza alokacin da hawayenta ke diga
bisa kan fuskar Shaharan. A cikin wakar tana
bayani kamar haka;
"Mazaje sun fadi a yayin da gumu ya kai gumu"
"Ranar wuya ita ce ranar da daci ke yanke zaki"
"Ranar masoya ke rasa masoyansu"
194
TASKARNOVELS.COM.NG
"Daji biyar na masifa yau mazan Kwarai sun
ratsaka mma basu sha da dadi ba"
"Ga ďa da uwa a cikin bala'i, amma ba su iya
tseratar da juna ba"
"Miji da mata sun ga gararin da ba su taɓa" gani
ba. "Jini da jini na hade amma bakin takobi ya
raba su" "Yau fa ga ranar cika buri amma
amfaninta ya gushe tunda babu masoyi" "In ban
da akwai sauran masoya a doron kasa da
mazaje sun zabi mutuwa akan rayuwa!" Lokacin
da Shadira ta fara rera waďannan baitoci sai
jikin kowa ya yi sanyi aka yi ta kuka kamar ba za
a daina ba. Kuma aka yi tsit ana saurarenta har
izuwa dogon lokaci.
Ita kanta sai da ta ji ta gaji da yin wakar sannan
ta yi shiru ta kifa kanta akan kirjin Shaharan har
barci ya sace su su biyun ba su sani ba.
Gaba dayan abokan tafiyar sai da suka yi baccin
wuya, baccin dole saboda tsananin gajiyar da ke
jikinsu. Dayansu bai farfado ba sai bayan sa'a
biyu da rabi.
195
TASKARNOVELS.COM.NG
Mahaifiyar Imran ce ta fara farfadowa tana bude
idonta ta hangi danta Imran da Shadira kwance
a waje daya sai ta ji ta cika da tsananin farin ciki
da ta rayu ta kawo izuwa wannan lokaci da take
daf da warkewa daga cutar da ta addabi
rayuwarta tsawon shekara da shekaru kuma
take daf da ganin auren danta.
Bayan ta jima tana kallon Imran da Shadira tana
ta murmushi sai kuma ta juya ta kalli inda
Haiman da matarsa Lumaira ke kwance, nan
take taji suma ta tayasu farin ciki ainun tunda
suna daf da cika burinsu na warkewar. Lumaira
daga cutar makanta.
Koda ta tuno da yaro Masnur dan uwan Shadira,
Sarki Farisa dan uwan Zarina da kuma dokin
Shaharan ai ta fashe da matsanaicin kuka
saboda ko ba komai ta shaku da su a cikin
wannan doguwar tafiya da aka yi kuma ta
tausayawa masoyansu matuka bisa rashin su da
suka yi.
196
TASKARNOVELS.COM.NG
Sautin kukan mahaifiyar Imran ne ya sa kowa
ya farka daga barci.Koda Imran ya ga
mahaifiyarsa na kuka sai ya mike tsaye zumbur
daga jikin Shadira ya ruga "Ya ke izuwa wajen
mahaifiyar tasa ya durkusa a gabanta suka
rungume juna yana mai cewa, Ummina ina
dalilin wannan kuka naki?"
Ki yi sani cewa yanzu lokaci ne na farin ciki ba
na kuka ba tunda muna daf da cika burin zuciya.
Koda jin wannan batu sai mahaifiyar tasa ta
janye jikinta daga cikin nasa suk fuskanci juna
sosai sannan ta ce, "Ya kai dana ka yi sani cewa
ba komai ne ya sani wannan kuka ba face
tsananin tausayinmu gaba daya nan. Tabbas ko
nan gaba idan ana bayar da labarinmu sai an yi
kuka a duniya kuma labari ne irin wanda baya
shafewa kuma ba za a taɓa mantawa da shi ba.
Ko a iya nan labarinmu ya tsaya mun aje tarihin
abin al'ajabi kuma abin alfahari".
197
TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'adda mahaifiyar Imran ta zo nan a jawabinta
sai Imran ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya ke
Ummina ki yi sani cewa a cikin matafiyan nan
gaba daya ba masu sa'a sama da mu ni da ke.
Duk tsananin masifun da muka hadu da su a
baya ni da ke babu wanda ya rasa wani bangare
na jikinsa, amma sauran abokan tafiya kuwa
daga wanda ya sami manyan raunika a jikinsa
sai wanda ya rasa masoyi da wanda ya rasa
wani бangare na jikinsa.Ina ji a jikina cewa har
mu shiga cikin kogon Darul Iksina babu abin da
zai same mu kuma sai bukatarmu ta biya."
Koda jin wannan batu sai mahaifiyar tasa ta
dube shi cikin firgici ta ce, "Haba ya kai dana kai
kuwa mene ne tabbacinka cewa za mu sami
wannan nasara alhalin har yanzu akwai sauran
tashin hankali a gabanmu na shiga cikin kogon
Darul Iksina?"
Ya yin da Imran yaji wannan batu sai ya yi
murmushi ya ce, "Ba komai ne ya sa nake da
wannan yakinin ba face na san cewa a duniya
babu wata soyayya mai karfi sama da soyayyar
198
TASKARNOVELS.COM.NG
da ke tsakanin da da mahaifi. Ya ke Umkina ki
tuna cewa tun ina cikin cikinki kike dawainiya
da ni kike shan wuya har kika haife ni sannan
kika shiga rainona. Sa'adda na fara zama mutum
kuwa sai ya zamana cewa soyayyarki a gare ni
kullum tana karuwa kuma ya zamana cewa ko
kuda ba kya son ya taɓa dafiyar jikina. Ba zan
taɓa mantawa ba da irin dawainiya da wahalar
da muka sha ta rayuwar talauci, rashin
makwanci da tsananin yunwa gami da yawo
kwararo-kwararo har ta kai mu ga zaman dole a
cikin daji. Na yi imani a zuciyata cewa wannan
wahala da muka sha ba za ta zamo a banza ba,
lallai sai mun ji dadi kafin cikar ajalinmu".
Ya yin da Imran ya zo nan a zancensa sai
mahaifiyarsa ta cika da dumbin farin ciki ta sake
rungume shi a kirjinta tana mai bushewa da
dariyar murna shi ma ya tayata dariyar.
A dai-dai wannan lokaci ne Boka Muzaffar ya
mike tsaye ya dubi gaba dayan abokan tafiyar
daya bayan daya ya ce, "Ya ku 'yan uwana ku yi
sani cewa yau ne muka kawo karshen wuya a
199
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin wannan tafiya tamu kuma daga nan zuwa
kogon Darul Iksina tafiya ce ta kwana uku kacal.
Ina mai tabbatar muku da cewa babu wani
mugun abu da za mu sake haduwa da shi akan
hanya har mu isa kogon Darul Iksina amma ku
sani cewa a cikin kogon Darul Iksina akwai
masifu iri-iri har kala dari tara da casa'in da
tara. Gaba dayanku nan babu wanda ya san
yadda za a iya tsallake masifun da ke cikin
wannan kogo face ni saboda haka da zarar mun
shiga cikin kogon ku kasance masu biyayya a
gare ni da bin umarnina. Duk abinda na ce ku yi
kawai ku yi shi cikin gaggawa kada ku yi mini
gardama ko jayayya. Idan kunne ya ji, gangar
jiki ta tsira. Yanzu zamu zauna anan har tsawon
kwana uku domin mu yi jinyar raunikan jikinmu
sannan mu ci gaba da tafiya".
Koda gama wannan jawabi sai Boka Muzaffar ya
koma inda yake ya zauna. Zamansa ke da wuya
sai jarumi Shaharan ya dube shi ya ce, "Ya kai
jagoran wannan tafiya ina da tambaya guda
daya a gare ka. Wai shin me ya sa tun da muka
fara wannan tafiya ba ka ceci rayuwar mutum
daya ba daga cikinmu da karfin sihirinka? Ka
200
TASKARNOVELS.COM.NG
tuna fa cewa ka shafe shekaru masu yawa kana
bincike da hidima akan wannan tafiya tamu, ai
ya ci ace ka san duk irin bala'in da za mu
fuskanta a cikinta ka tanadar mana rigakafinta."
Koda jin wannan batu sai Boka Muzaffar ya
kyalkyale da dariya sannan ya hade fuska kamar
an aiko masa da sakon mutuwa ya ce, "Ya kai
Shaharan ka yi sani cewa babu wani sihirin tsafi
da ya isa ya yi tasiri a cikin wadannan
dazuzzuka biyar da muka ratsa fiye da shekaru
dubu da suka gabata haka wannan al'amari yake
amma idan muka shiga cikin kogon Darul Iksina
kowannenmu sihirin tsafinsa zai iya tasiri".
Koda Boka Muzaffar ya zo nan a zancensa sai
Shaharan ya mike tsaye ya yi 'yar tafiya nesa
kaɗan da inda sauran abokan tafiya suke ya
zauna ya shiga sabon tunani. Abinda ya fara
fado masa a rai shi ne, tunowa da wasiyar da
Aljani Marhabul Zaurus ya yi masa kafin ya
mutu cewar ya yi hankali da Boka Muzaffar
lallai mayaudari ne shi kuma
201
TASKARNOVELS.COM.NG
azzalumi".Shaharan na cikin wannan tunani ne
yaji an dafa kafadarsa ta baya. Cikin firgici ya
waigo da sauri sai ya ga ashe Zarina ce don haka
sai ya yi murmushi a gare ta itama ta maida
masa da martanin murmushin sannan ta zauna
daf da shi suna masu fuskantar inda sauran
abokan tafiya ke kwance, wato can bakin kogin
tundun tsira.
Tsawon 'yan dakiku dayansu bai ce uffan ba
daga can sai Zarina ta yi gyaran murya ta ce, 'Ya
kai masoyina, ka yi sani cewa masu