x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - MAZAN JIYA 3

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 68212 words

Category: Adventure Stories

Views 186

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
iya magana
sun ce, 'Ruwa baya tsami banza' Tabbas akwai
abinda ke damunka shi ya sa ka baro cikinmu ka
dawo nan ka zauna kana tunani. Idan har son da
kake yi mini na gaskiya ne kada ka ɓoye mini
komai. Ka tuna cewa na rasa dan uwana Sarkin
Farisa yanzu bani da sauran kowa a duniya. Kai
ma ka rasa dokinka wanda da shi ne kaɗai za ka
cika babban burinka na duniya, ba ka da wani
abu da yai saura wanda ya fi ni daraja. Lallai ya
zama wajibi a gare mu mu hada kai mu taimaki
juna tunda muna bukatar junan namu". Sa'adda
Gimbiya Zarina ta zo nan a cikin zancenta sai
jarumi Shaharan ya yi ajiyar zuciya sannan ya
202

TASKARNOVELS.COM.NG
kwashe labarin duk abinda ya faru tsakaninsa
da Aljani Marhabul Zaurus ya zaiyane ma ta.

Koda jin wannan labari sai hankalin Zarina ya

dugunzuma ainun, ta yi shiru tana mai tunani.
Daga can sai ta kawo gwauron numfashi ta ajiye
sannan ta ce, "Hakika Biri ya yi kama da Mutum.
Inda Boka Muzaffar ya kasance adali kuma mai
gaskiya da ya nuna matukar damuwarsa bisa
duk irin abubuwan da suka rinka faruwa a gare
mu mu duka. Ni na rasa dan uwana amma ko
jaje bai yi mini ba. Shadira ta rasa dan uwanta
bai tausaya mata ba. Kai ma ka rasa dokinka bai
ce da kai komai ba. Haiman da kai kun rasa
hannayenku dai dai amma duk bai nuna
tausayinsa ba. Wannan yana yi mana nuni da
cewa Boka Muzaffar bai damu da rayuwarmu ba
alhalin kuma shi ne ya dora mu akan wannan
TAFARKI zuwa kogon Darul Iksina kuma mun
dade muna jiransa akan yin wannan tafiya. Ko
shakka babu Muzaffar yana da wata manufa a
Karkashin zuciyarsa kuma yana da wani buri na
musamman akan shiga cikin kogon Darul Iksina.
203

TASKARNOVELS.COM.NG
Lallai ya yi amfani da mu ne kawai a matsayin
Karukan farautarsa. Ya kai masoyina shawarar
da zan ba mu ita ce duk irin umarmin da Boka
Muzaffar zai ba mu a cikin kogon Darul Iksina
kada mu yi amfani da shi kuma idan da hali mu
hana sauran abokan tafiya aiki da wannan
umarni nasa." Lokacin da Zarina ta zo nan a
zancenta sai Shaharan yai ajiyar zuciya sannan
ya ce, "Ya ke masoyiyata ki yi sani cewa abokan
tafiyarmu sun yarda da Boka Muzaffar dari bisa
dari, koda za mu ba su labarin wasiyyar da
Aljani Marhabul Zaurus ya bayar ba za su
aminta ba. Idan kuma muka sanar da su a yanzu
za su yi mana tawaye, wata kila ma su hada kai
su yake mu. Abin da zai fiye mana alheri shi ne
kawai mu bar wannan al'amari a cikin
zuciyarmu. Wanda duk yake da rabon fitowa a
raye daga cikin kogon Darul Iksina lallai zai fito.
Yanzu ki tashi mu koma can wajen abokan
tafiya domin idan muka ci gaba da hira anan
Boka Muzaffar zai iya zarginmu har ma ya yi
tunanin daukar mataki a kanmu".

Gama fadin hakan ke da wuya sai duk su biyun
suka mike tsaye suka koma can wajen sauran
204

TASKARNOVELS.COM.NG
abokan tafiya. Nan take aka shiga kafa tantuna
gami da shirya abincin da za a ci.

Kamar yadda Boka Muzaffar ya shirya haka
al'amura suka kasance, wato sai da su Shaharan
suka shafe kwana uku cur suna jinyar raunikan
jikinsu a nan bakin kogin tudun tsira sannan
suka kintsa aka kama hanya aka durfafi kogon
Darul Iksina.
Haka dai suka wanzu suna tafiya, ba sa ya da
zango face idan dare ya yi sannan su tsaya a
kafa tantuna a kwanta ayi barci.

Wani abin mamaki da ya faru shi ne, a iya
tsawon kwana ukun da suka yi wannan tafiya ko
maciji ba su kara gani ba akan hanyarsu bare ya
kawo wa dayansu hari.

Da la'asar sakaliya suka iso bakin kogon Darul
Iksina. Kogon na Darul Iksina ya kasance abin
al'ajabi ga dukkan wanda ya yi arba da shi,
domin ya wanzu ne tamkar ginin gida akan wani
205

TASKARNOVELS.COM.NG
dan karamin tsuburi, wanda ruwa ya kewaye
shi kuma ruwan ba shi da zurfi domin komai
gajartar mutum bai fi ya kawo masa iya kaurin
kafarsa ba.

Kogon na Darul Iksina an yi shi ne cikin siffar
gida na ginin jan dutse na Murjani, wanda tun
daga nesa mutum zai ga yana ta kyalkyali da
daukar ido sannan haskensa ya haskake dajin
gaba daya.

Girman gidan ya kai na dan karamin gari yana
da fadi da tsawo sosai domin idan aka fuskance
shi ba a iya hango karshen katangarsa. Idan
mutum ya daga kai ya dubi saman ginin kogon
sai ya ga kamar bashi da karshe kwai dai ya
lmtokare da sararin samaniya ya kule a cikin
gajimare. Ko kadan babu alamar kofa ko taga a
jikin gidan kuma ko ina a mulmule yake a shafe
tamkar wani abu bai taɓa shiga cikinsa ba.

206

TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da su jarumi Shaharan suka iso daf da
kogon Darul Iksina sai gabadayansu suka ja
suka yi cirko-cirko suna kallon kogon cikin
tsananin al'ajabi. Shi kansa Boka Muzaffar an
batar da tunaninsa domin yadda duk yake
tsammani zai ga kogon ba haka ya gan shi ba.

Bayan sun dan ɓata dakiku masu yawa suna
kallon kogon sai Boka Muzaffar ya wuce kan
gaba ya shiga cikin wannan ruwa ya durfafi
tsuburin da kogon Darul Iksina ke kai ba tare da
fargabar komai ba yana ta kyalkyala dariyar
farin ciki kuma yana yafito sauran abokan tafiya
da hannu.

Koda ganin haka sai Haiman ya bi bayansa yana
goye da matarsa Lumaira, sannan Imran dauke
da mahaifiyarsa, Shadira na binsu daf da daf
Shaharan da Zarina na biye sannan Gimbiya
Rahila, Sarki Laffaru ne na karshe.

207

TASKARNOVELS.COM.NG
Kamar yadda Shaharan da Zarina ke da shakku
akan Boka Muzaffar, haka Sarki Laffaru ya
kasance domin shi ma ya lura da take-takensa
tun daga farkon tafiyar tasu har izuwa sa'adda
suka iso bakin tekun tudun tsira don haka sai ya
aiyana a ransa cewa duk irin umarnin da Boka
Muzaffar ya bayar a cikin kogon Darul Iksina ba
zai yi aiki da shi ba koda kuwa zai rasa
rayuwarsa.

Bayan kowa ya haye wannan ruwan sai aka hau
kan tsuburin aka iso daf da kogon Darul Iksina
aka tsaya aka yi cirko-cirko kowa ya zubawa
Boka Muzaffar idanu.

Yayin da Muzaffar ya ga shi kaɗai ake sauraro
sai farin ciki ya lulluɓe shi nan take ya shiga yi
wa kansa kirari yana mai cewa;

"Ni ne Bokan zamani wanda ya gagari dukkan
Bokaye.

208

TASKARNOVELS.COM.NG
Ni ne murucin kan dutse ban fito ba sai da na
shirya.

Ina matsafa da jaruman duniya, yau ga Bokan
farko da zai zamo sanadin da za a shiga kogon
Darul Iksina.

Na bata hankali Dare na sami suna da daukaka,
kuma na samu.

In banda Aljani Maruful Dauwaz babu wanda zai
riga ni shiga kogon Darul Iksina, lallai na bar wa
duniya abin tarihi.

Ko yanzu na mutu na kasaita kuma na gawurta,
lallai duniya ba za ta manta da ni ba." (OH ni
Maiboko! Ka ji ďan egiya mayaudari macuci)

Gama fadin hakan ke da wuya sai Muzaffar ya
fiddo wata 'yar karamar wuka daga jikinsa ya
209

TASKARNOVELS.COM.NG
kama suturar jikinsa dai-dai ciayarsa ya kwaye
ta, sai ga wadansu dalasiman tsafi rubuce akan
ciyar

Nan take ya fara karanto dalasiman tsafin cikin
daga murya. Faruwar hakan ke da wuya sai
wata irin iska mai karfi ta fara kadawa tana
zagaye gaba dayan kogon na Darul Iksina, gaba
daya yanayin sararin samaniya ya sauya daga
fari fat ya koma kore shatar.

Al'amarin da ya firgita gaba dayan abokan
tafiyar ke nan, dukkaninsu suka ji tsigar jikinsu
ta tashi, kuma tsoro ya baibaye su.

Boka Muzaffar na gama karanto wadannan
dalasiman tsafi sai wannan iska ta dauke dif,
yanayin sararin samaniyar ya dawo dai-dai
yadda yake a da.

210

TASKARNOVELS.COM.NG
Ba zato ba tsammani sai suka ga wata katuwar
kofa ta bakin mulmulallen karfe ta baiyana akan
ginin kogon Darul Iksina, sannan sai suka ji
karar zare sakatu a jikin kofar har guda casa'in
da tara. Daya bayan daya sakatun suka rinka
zare kansu. Ta casa'in da taran na gama fita sai
kofa ta bude wanwar.

Koda suka yi arba da cikin kogon sai gaba
dayansu suka cika da tsananin al'ajabi. Ba komai
ne ya haddasa hakan ba face ganin abin da ke
cikin kogon.

Wadansu gidaje ne kala-kala a cikin kogon har
guda bakwai. Kowanne gida guda daya ya kai
girman unguwa guda, kuma dukkan gidajen
anginasu ne daga dangin su Zinare, Lu'u-lu'u,
Jauhar, Murjani da sauransu. Duk wanda ka
kalla sai ka ga kamar ya fi wanda ke kusa da shi
kyau da ginuwa

211

TASKARNOVELS.COM.NG
Ba tare da fargabar komai ba Boka Muzaffar ya
kuna kai izuwa cikin kogon suma sauran abokan
tafiyar sai suka bivshi da sauri duu! Da yake
Sarki Laffaru ne na karshe yana shiga sai kofar
gidan ta rufe kanta wadansu sakatu guda casa'in
da tara suka mayar da kansu cikin ramukansu,
sanann kofar ta sake rufe kanta.

Faruwar hakan ke da wuya sai Boka Muzaffar ya
bushe da dariyar mugunta. Lokaci guda kuma ya
hade rai ya ce, "Ni ne kadai zan iya sake bude
muku kofar wannan gida ku fito in ba haka ba
kuwa sai dai ku mutu a cikinsa".

Gama fadin hakan ke da wuya sai Boka Muzaffar
ya sanya hannunsa a cikin aljihunsa ya fiddo
wata 'yar karamar jemammiyar fata. Babu.
komai a jikin fatar face taswirar gidajen da ke
cikin wannan kogo gaba dayansu guda casa'in
da taran. A jikin kowanne gida akwai rubutun
wadansu kalmomin tsafi.

212

TASKARNOVELS.COM.NG
Nan take Boka Muzaffar ya ajiye wannan
jemammiyar fata a kasa, gaba dayan abokan
tafiyar suka kewaye ta suna kallonta cikin
mamaki.

Muzaffar dube su daya bayan daya ya ce, Shin a
cikinku akwai wanda zai iya karanta mini kalma
daya daga cikin kalmomin da aka rubuta a jikin
wannan fata?"

Koda jin wannan tambaya sai kowa ya duruduru aka rasa wanda zai ce kala. Da ganin haka
sai Boka Muzaffar ya sake bushewa da dariya
sannan ya ci gaba da kuri yana mai cewa, "Ku
duka a yanzu rayukanku a hannuna suke.
Wanda duk ya bi umarnina zai kuɓuta ya sami
cikar burinsa. Wanda kuma duk ya bijire mini
kuwa zai hallaka anan cikin kogon Darul Iksina.

Koda gama fadin hakan sai Boka Muzaffar ya
Kurawa wannan fata idanu sannan ya dago kai
ya dubi Haiman da Imran ya ce, "Ku je ku bude
213

TASKARNOVELS.COM.NG
kofar wancan gida na uku ku shiga cikinsa kai
tsaye. Lallai a cikinsa ne za ku riski ruwan
albarka da za ku yiwa masoyanku magani da shi
su warke".

Ba tare da gardamar komai ba kuwa Haiman da
ke goye da matarsa Lumaira ya nufi kofar
wannan gida. Imran goye da mahaifiyarsa ya
mara masa baya.

Nan take suka bude kofar wannan gida na uku
suka kunna kai ciki. Suna shiga sai kofar gidan
ta rufe kanta. (Allah wadaran mai hali irin na
boka Muzaffar)

Daga nan sai Boka Muzaffar ya dubi Zarina da
Shadira ya ce, "Ku kuma kun rasa masoyanku
don haka ba ku da sauran bukatar ruwan
albarka. Kai ma jarumi Shaharan baka da
bukatar wannan ruwa, saboda haka ka bi Zarina
da Shadira ku shiga cikin gida na biyu. Duk abin
da kuke so na duniya wanda ya dunganci dukiya
214

TASKARNOVELS.COM.NG
za ku samu a cikin wannan gida, ku shiga ku
debo iya muradinku akwai hadiman da za su yi
muku dako har izuwa kasashenku."

Koda jin wannan batu sai Shadira ta nufi
wannan gida na biyu, amma sai Shaharan da
Zarina suka toge. Al'amarin da ya matukar bai
wa Boka Muzaffar mamaki ke nan ya dube su ya
ce, 'Me kuka tsaya jira? Ko kuwa kuna so ku
bijirewa umarnina ne?"

Sa'adda Shaharan ya ji wannan tambaya daga
bakin Boka Muzaffar sai ya yi murmushi ya ce,
"Ya kai wannan Boka ka yi sani cewa ni yanzu
tsakanina da kai babu sauran yarda da amana,
saboda jikina ya ba ni cewa so kake ka yaudare
mu ka cutar da mu. Ina tabbatar maka da cewa
duk inda ka shiga ni ma nan zan shiga tunda na
san cewa ba za ka kai kanka inda za ka hallaka
ba".

215

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai Boka Muzaffar ya
bushe da dariya ya ce, "Tabbas ka yi dabara ya
kai wannan jarumi, b." amma ka kama hanyar
da ba za bulle ba

Boka Muzaffar ya dubi Sarki Laffaru ya ce, ya kai
abokina, maza ka ruga izuwa cikin daki na hudu
domin anan ne za ka sadu da Aljani Maruful
Dauwaz wanda zai cika maka burin rayuwarka.
Sarki Laffaru ya toge ya ce, "Kai ba zai yiwu ba.
Haba abokina! Ai ilimin tsafi ka fi ni amma ba
wayo ba ko sanin tuggun duniya. Ina tabbatar
maka da cewa kafarka-kafata. Duk inda ka shiga
nan zan shiga. Idan har ma gaskiya ne cewar zan
sadu da Aljani Maruful Dauwaz a cikin gida na
hudu ta ya ya zan iya sarrafa shi ya aminta da ni
har ya biya mini bukatata?"

Koda jin wannan tambaya sai Boka Muzaffar ya
ce, "Ai ga Gimbiya Rahila nan amfanin tahowa
da ita kenan a cikin wannan tafiya muddin
Aljani Maruful Dauwaz zai yi arba da ita duk
abin da kake so zai yi muku tunda kamanninta
216

TASKARNOVELS.COM.NG
iri daya ne sak da na masoyiyarsa wadda ya
rasa."

Kafin Muzaffar ya gama rufe brakinsa tuni
Gimbiya Rahila ta tari numfashinsa ta ce, "Kai!
dakata tsohon banza! Mayaudari, ai kama da
wane ba ta wane. Ni mutum ce, masoyiyar Aljani
Mauruful Dauwaz kuwa aljana ce, kuma ta
mutu. Wanda duk ya mutu ba zai dawo ba,
Mauruful Dauwaz ya san da haka. Abin da na ke
so da kai kawai ka kai mu inda Maruful Dauwaz
yake mu gana da shi ni na san abin da zan gaya
masa ya aminta da bukatarmu, idan kuma ba za
ka yi haka ba sai dai KAIFIN TAKOBI ya raba mu
da kai yanzu".

Koda jin wannan batu sai Boka Muzaffar ya
bushe da mahaukaciyar dariya wacce ta cika
kogon gabadaya da amsa kuwwa sannan ya ce,
"Ai ni yanzu na gama dahuwa bana tsoron
konewa. Ina mai sanar da ku cewa yanzu karfin
sihirin tsafina zai yi aiki don haka idan ma za ku
taru ku duka ba za ku iya hallaka ni ba har sai na
cika burina. Ku sani cewa gabadayanku
217

TASKARNOVELS.COM.NG
yaudararku na yi babu wanda na kawo shi nan
domin samun biyan bukatarsa sai don biyan
tawa bukatar. Tuni na yi bincike a cikin hallarar
tsafina na gane cewa dole sai da ku zan iya ratsa
wadannan dazuzzuka guda biyar domin sihirin
tsafi ba zai iya kuɓutar da mutum daga sharrin
da ke cikinsu ba. Batun ruwan albarka da na
gaya muku cewa idan ku ka yi amfani da shi
masoyanku za su warke, duk karya ce na shirya
muku kawai na yi amfani da ku a matsayin
Karnukan Farauta na.

(Boka Muzaffar da yan siyasa ba su da maraba a
gurin dadin baki da bakar yaudara. Allah ya
kyauta)

Ya kai Laffaru, kai ne kadai za ka iya cika
burinka idan ka sadu da Aljani Maruful Dauwaz
idan har ya amince da kai. Ni kam abu daya ne
ya kawo ni cikin wannan kogo, ba komai bane
face wani MASHI wanda ake kira GALILUL
HARAS. Yau shekara arba'in ke nan ina ta
bincike akan yadda zan zo na mallake shi sai
yau na sami wannan dama. Da zarar na dauki
218

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan mashi na Galilul Haras na fita da shi
daga cikin kogon nan na mallaki duniya gaba
dayanta.

Idan duk mutanen dunuiyar nan da dukkan
aljanun duniya za su taru ba su isa su hana ni
shiga wannan gida na farko ba don dauko
wannan mashi.

Da wannan furuci nake yi muku bankwana sai
mun sake saduwa nan gaba a lokacin da
kasashenku da Sarakunanku suka dawo
karkashin mulkina".

Koda gama wannan bayani sai Boka Muzaffar ya
ɓace bat! yana mai kyalkyala dariyar farin ciki.
Nan take kofar wannan gida na farko ta bude
sannan ta kulle kanta.

219

TASKARNOVELS.COM.NG
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin su Sarki
Laffaru da Boka Muzaffar a farkon shigarsu
cikin kogon Darul Iksina.

Al'amarin Haiman da Imran kuwa wadanda ke
goye da masoyansu lokacin da suka shiga cikin
wannan gida na uku sai suka tsinci kansu a cikin
wata makekiyar fada wacce ta kasance akwai
komai a cikinta na sarauta sannan ga Dakaru
nan kimanin su dubu a tsaitsaye rike da
makaman yaki amma dukkaninsu sun kasance
gumaka masu kirar mutanen farko wato manyamanya. Sun kasance masu tsawo da kaurin
gaske domin kuwa kowane dayansu tsawonsa
ya ninka na su Imran sau uku.

Akan karagar mulkin fadar kuwa gunkin wani
dan karamin yaro ne kafafuwansa a tankwashe
a kansa akwai dan gajeren rawani kuma
fuskarsa cike take da annuri kamar ace kyat ya
yi magana.

220

TASKARNOVELS.COM.NG

Lokacin da Imran da Haiman suka ga yanayin
tsarin wannan fada sai suka cika da mamaki.
Haiman ya dubi Imran cikin alamun damuwa ya
ce, "Anya kuwa Boka Muzzafar ba yaudararmu
ya yi ba. Yaya mu da muka zo neman ruwan
albarka zai shigar da mu nan, ga shi ko alamar
danshi babu a wajen bare a sami ruwa sai
gumakan banza kawai".

Da jin wannan batu sai Imran ya yi ajiyar zuciya
sannan ya kwance mahaifiyarsa daga bayansa
ya ajiye ta a kas gefe daya shi ma ya zauna ya
dubi Haiman ya ce, "Tabbas biri ya yi kama da
tutum, akwai alamun yaudara da cin amana a
cikin wannan al'amarin, yanzu kenan duk
wahalar nan da muka sha a baya ta zama a
banza. Wasun mu sun rasa masoyansu, wasu
sun rasa wani sashi na wani bangare na jikinsu,
a karshe mun tashi a tutar babu, ba mu ga
tsuntsu, ba mu ga tarko. Lallai Boka Muzzafar ya
yi mana zaluncin da har abada ba zamu yafe
masa ba face mun dauki fansa."

221

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Imran ya zo nan a zancensa sai duk su
hudun kwallar bakin ciki ta cika musu idanu, su
duka suka yi shiru har izuwa tsawon 'yan
dakiku. Daga can sai Haiman ya dubi Imran ya
ce, "Ya kai abokin tafiya ka yi sani cewa zama
bai kama mu ba, ka duaki mahaifiyarka ka goya
ta mu juya da baya mu koma inda muka baro su
Boka Muzaffar wata kila mu riske su in ya so ayi
duk wadda za a yi."

Imran ya ce, "Kwarai kuwa ka zo da shawara
mai kyau". Cikin hanzari ya mike tsaye ya dauki
mahaifiyarsa ya goyata sannan suka juya da
nufin su fice daga cikin fadar.

Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka ga gaba
dayan gumakan wadannan Dakaru sun motsa
suna masu buga kafafuwansu da gyara
makaman yakinsu.

222

TASKARNOVELS.COM.NG
A firgice su Imran suka juyo da sauri, ai kuwa
sai suka ga ashe ruhi ne ya shiga cikin gangar
jikin gumakan duk sun zama rayayyu.
Kafin su Imran su yi wani yunkuri tuni dakarun
sun yi musu kawanya babu ta inda sa su iya
gudu Kawai sai suka ji an kyalkyale ja dariya
dagacan kan karagar mulki. Wannan karamin
yaro mai rawani a kansa shi ne ya yi dariyar a
lokacin da yake saukowa daga kan karagar
mulkin.

Ta ke Dakarun suka buďewa yaron hanya ya
tako a hankali cikin tafiyar kasaita ya iso har
inda su Imran ke tsaye ya dube su a wulakance
ya ce, "Yau shekara dubu daya ke nan rabon da
wani mahaluki ya shigo cikin wannan kogo na
Darul Iksina. Sunana RAUHUDUL MAUZUL, ni
ne Sarkin MAYU na aljanun duniya. Lallai muna
cikin tsananin kishirwar bil'adama, kuma mun
daďe rabonmu da mu tauna nama da kashi.
Yanzun nan za mu gididdiba ku gutsun-gutsun
yadda za a sarrafaku izuwa nau'i-nau'in girki
wanda zan kwana biyu ina walima."

223

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda gama wannan jawabi sai wannan yaro ya
juya ya nufi inda karagar mulkinsa take. Nan
take Imran da Haiman suka fahimci cewa lallai
yaron na isa kan karagarsa yana zama za a far
musu a gama da su. Kawai sai Imran ya yunkura
ya zare sandarsa a lokacin da mahaifiyarsa da
ke goye a bayansa ta fara kuka. Itama Lumaira
da ke goye a bayan Haiman sai zuciyarta ta
karaya ta fara kuka.

Haiman ya dubi Imran cikin tsananin karayar
zuciya ya ce, "Ya kai abokin tafiya mene ne
amfani ka 6ata lokacinka kayi yaki yanzu? Shin
ka manta ne da duk irin gwagwarmayar da
muka yi a baya da irin tsananin wuyar da muka
sha? Mece ce ribarmu idan ma mun sami
hasarar hallaka wadannan aljanu? abin da muka
rayu ma dominsa ba zamu samu ba. Ni kam
yanzu na hakura da rayuwa na zaɓi mutuwa
domin idan ma ban
End Ads