x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - MAZAN JIYA 3

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 68212 words

Category: Adventure Stories

Views 192

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
jinyar jikinmu domin
akwai alamun cewa babu abin da zai same mu
anan din face mun shiga daya daga cikin
wadannan gidaje bakwai."

Nan take kowa ya nuna amincewarsa akan
Wannan shawara da Imran ya kawo suka fara
kokarin neman abincin da za su ci tunda ga
komai han na dangin abinci da abin sha iri-iri a
kogon Darul Iksina kuma wani abin mamaki shi
ne babu abun da yake lalacewa daga cikin irin
kayan.
357

TASKARNOVELS.COM.NG

Wannan shi ne abin da ya faru ga su jarumi
Imran a cikin kogon Darul Iksina bayan sun rage
saura su shida kacal a cikin abokan tafiyarsu su
goma sha daya.

***

A CAN Birnin Hindu kuwa, lokacin da Sarki
Nashmir ya shiga dakin halwar tsafinsa sai ya
shiga bincike akan mashin Galilul Haras nan
take ya gano abin da ya yi matukar girgiza masa
hankali.

Ba komai ya gani ba face Boka Muzaffar rike da
mashin Galilul Haras zaune a cikin dakin
tsafinsa yana gabatar da wani aiki na tsawon
kwana arba'in wanda da zarar ya sami nasarar
kammala aikin to fa babu yadda za a yi a iya
raba shi da mashin Galilul Haras har abada,
koda kuwa an je Birnin Kisra an binne yawun
barcin Sarki Nashmir din.
358

TASKARNOVELS.COM.NG

Koda ganin wannan al'amari sai Sarki Nashmir
ya dimauce ya rasa abin da ya kamata ya yi. Shin
zai yi shirin yaki ne ya tafi can inda Boka
Muzaffar yake ya yake shi ya raba shi da mashin
Galilul Haras ko kuwa zai tsaya ne ya ga
dawowar su sadauki Najwar don ya tabbatar da
cewa sun hallaka su Aljani Maruful Dauwaz?"

Nan fa Nashmir ya rasa hukuncin da ya kamata
ya yanke. Nan dai yai shiru ya faɗa kogin tunani
mai zurfi har dabara ta faɗo mas.

Dabarar kuwa ita ce, kawai ya yi shiri ya je ya
tunkari Boka Muzaffar ta kowanne hali ya
hallaka shi ya dauko mashin Galilul Haras tunda
da can ya yi iyakar kokarinsa a kan ya dauko
mashin a kogon Darul Iksina ya kasa tunda
yanzu ga mashin ya samu a banza kawai sai ya
je ya karba.

359

TASKARNOVELS.COM.NG
Ko shakka Sarki Nashmir ba ya yi cewar akwai
wani mahaluki da ya isa ya shigo har cikin
fadarsa ya sace yarsa Gimbiya Ramlatul Siyamu
saboda sanin irin tsananin yawan Dakarun,
tsaron da ya tanada masu tsananin karfin
dantse da karfin sihiri.

Cikin gaggawa Sarki Nashmir ya katse halwar
tsafinsa ya tafi izuwa turakarsa ya yi gagarumar
shigar yaki, ya debi dukkan makamansa na yaki
gami da guraye da layu na tsafi sannan ya hau
kan wani tsuntsun tsafinsa wanda ba rai ne da
shi ba Ma'ana ba tsuntsun gaske ba ne.

Take tsuntsun ya tashi da shi sama ya durfafi,
Birmin Sarki Laffaru inda gidan Boka Muzaffar
yake a tsakiyar wani daji da ke bayan Birnin.

Kash! In ba don mantuwa ba da Nashmir, ya
gama samun nasara!

360

TASKARNOVELS.COM.NG
Ba komai ne ya manta ba face bincika alamarin
Sarkin yakinsa sadauki Najwar

A yanzu sarki Nashmir bai san cewa sadauki
Najwar ya hada kai da su Aljani Maruful Dauwaz
domin a zo a rushe mulkinsa kuma a sace
Gimbiya Ramlatul Siyam. In da ya san da
wannan al'amari da ba zai tafi neman mashin
Galilul Haras ba.

A can Birnin Kufa kuwa, Sarki SHADDADU na
tafiyar da mulki cikin tsari kamar yadda ya
kamata bisa umarnin mahaifiyarsa Sharlis kuma
mutanen gari suna jin dadin mulkin sosai.

Wata rana da safe Sharlis da Shaddad na zaune
a fada, ana tafiyar da harkokin mulki kawai sai
tunanin Sarki Laffaru ya fadowa Sharlisa a rai,
man take hankalinta ya dugunzuma ainun, ta yi
zumbur! Ta mike tsaye ta fice daga fadar cikin
sauri. Al'amarin da ya matukar bai wa kowa
mamaki ke nan domin tun da ta dora Shaddad
361

TASKARNOVELS.COM.NG
akan karagar mulki ba ta taɓa fita ba ta bar shi
shi kadai zaune a fadar sai yau.

Kai tsaye Sharlis ta wuce izuwa cikin ɗakin
halwar tsafinta tana tafe tana mamakin yadda
aka yi ma ta yi sakaki ba ta yi bincike ba bisa
matsayin da su Sarki Laffaru ke ciki ba tun daga
ranar da ta neme shi ta rasa, sai dai ta yi
binciken ta gano inda suka tafi shi da Boka
Muzaffar.

Lokacin da Sharlis ta isa cikin dakin tsafin sai ta
turo kofar ta rufe sannan ta zauna ta dukufa
tana bincike. Nan take ta ga duk abin da ya faru
gà su Sarki Laffaru a cikin wadannan ragowar
dazuzzuka na masifa da suka ratsa har suka isa
cikin kogon Darul Iksina suka sadu da Aljani
Maruful Dauwaz kawo izuwa yakinsu na karshe
da su sadauki Najwar har shi Najwar din ya
hada kai da su bisa cewar zai taimaka musu su
je su yaki maigidansa Sarki Nashmir domin a
sato Gimbiya Ramlatul siyam.

362

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda gama ganin wannan al'amari sai Sharlis ta
kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki a
lokacin da hankalinta ya dugunzuma ainun ta
rasa abin da ke ma ta dadi. daga nan kuma sai ta
sake yin bincike ta ga halin da Sarki Nashmir ke
ciki cewar ya taho izuwa nan Birnin Kufa domin
ya riski Boka Muzaffar a gidansa don ya karbi
mashin Galilul Haras.

Koda ganin wannan sabon al'amari sai Sharlis ta
sake dimaucewa ta rasa abin da ya kamata ta
fara yi. Shin za ta tafi can Birnin Hindu ne ko
kuwa za ta soma zuwa gidan Boka Muzaffar ne
da ke kusa da ita ta yake shi ta karɓe mashin
Galilul Haras tun kafn Sarki Nashmir ya iso?

Ai idan ta mallaki mashin Galilul Haras tafi
karfin kowa, cikin kankanin lokaci za ta iya
hallaka gaba dayan makiyanta har ma ta mallaki
duniyar gabadaya.

363

TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'adda Sharlis ta gama aiyana hakan a
zuciyarta sai ta bushe da dariya sannan ta ce,
"Hakika Boka Muzaffar ba shi da wayo.
Maimakon ya shiga halwar tsafi ta kwana
arba'in don ya yi sihirin da zai hana kowa
samun damar raba shi da mashin, kamata ya yi
ya fara zuwa ya kashe duk mutanen da ya san za
su yi yunkurin raba shi da mashin tukunna.

Nan take Sharlis ta yanke shawarra ta fara zuwa
gidan Boka Muzaffar ta raba shi da wannan
mashi sannan ta je ta hallaka su Aljani Maruful
Dauwaz ta kamo Sarki Laffaru da karfin tsiya ta
zo ta kulle shi a kurkuku har sai danta Shaddad
ya girma ya dauki fansa a kansa.

Koda gama aiyana hakan sai ta fita daga cikin
ɗakin tsafin ta ruga izuwa turakarta.

Cikin kankanin lokaci tayi gagarumar shigar
yaki ta hau doki ta tafi izuwa dajin da gidan

364

TASKARNOVELS.COM.NG
Boka Muzaffar yake tana mai falfala azababben
gudu akan doki.

AL'AMARIN su sadauki Najwar kuwa, sai da
suka taya su Aljani Maruful Dauwaz zaman jinya
a cikin wannan tsauni har tsawon kwana goma
sha hudu sannan su Aljani Maruful Dauwaz suka
warke suka sami kwarin jikinsu. Nan take suka
fara shirin tashi domin su tafi izuwa can fadar
Sarki Nashmir.

Bayan kowa ya gama kimtsawa sai sadauki
Najwar ya dubi Aljani Barukul Masnur ya ce,
"Ina mai gargadinka da kada ka kuskura ka
kaucewa umarnina ko kuma ka ce za ka tona
mini asiri saboda ka ga yanzu za mu koma fada
kana shakkar Sarki, Idan har kunne ya ji to
gangar jiki ta tsira".

Koda gama fadin haka sai Najwar ya dubi Aljani
Maruful Dauwaz ya ce, "Idan muna son mu sami
365

TASKARNOVELS.COM.NG
nasarar rushe mulkin maigidana mu kawar da
shi, dole ne mu yi abu uku. Abu na farko yanzu
zan kama ku na daure ku na kai ku wajensa a
matsayin fursunoni. Na san ba zai yi gaggawar
hallaka ku ba sai dai ya sa a kulle ku a kurkuku.
Mataki na biyu na shi ne, zan shiga tunanin
dabarar da zan yi na sace Gimbiya Ramlatul
Siyam daga turakarta a sirrance ko a dabarance
sannan na shirya matakan hallaka Dakarun
tsaro na fadar, yadda idan aka fara yakin za mu
sami nasarar kawar da su duka a cikin kankanin
lokaci.

Shi kuwa Sarki Nashmir ni ne zan tare shi mu
fafata in ya so muna cikin gumuzun sai ku kawo
mini dauki mu hada KARFI DA KARFE mu
hallaka shi. Da zarar sauran Dakarun nasa sun
ga mun ballaka shi dole ne su yi mubaya'a a
gare mu su dawo karkashin ikonmu."

Sa'adda sadauki Najwar ya zo nan a zancensa
sai Aljani Maruful Dauwaz ya dube shi ya ce, "Ya
kai wannan sadaukin sadaukai, mun ji duk
bayaninka kuma mun gamsu da shi, amma
366

TASKARNOVELS.COM.NG
muna son mu gana a tsakaninmu idan akwai
wani korafi sai mu sanar da kai".

Koda jin haka sai sadauki Najwar yai murmushi
ya ce, 'Ai babu komai ina sauraronku."

Nan take Maruful Dauwaz, Rahila da Sarki
Laffaru suka koma gefe daya suka fara
tattaunawa Inda Aljani Maruful Dauwaz ya
dubes u ya ce, "To kun ji abin da wannan
sadaukin jarumi ya zo mana da shi, anya kuwa
ba kwa tunanin cewa akwai. yaudara a cikin
al'amarin?

Ku tuna fa cewa shi ne Sarkin yakin Sarki
Nashmir tsawon shekaru, ta yaya kuke
tsammanin cewa zai bijire wa Sarkinsa a
yanzu?"

367

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai Rahila da Sarki
Laffaru suka yi shiru kamar ba za su ce komai
ba, kuma hankalinsu ya kara dugunzuma.

Daga can sai Rahila ta yi ajiyar zuciya sannan ta
dubi Maruful Dauwaz ta ce, "Ai yanzu ba mu da
wata huija da za mu ce ba za mu yard jarumi
Najwar ba tunda inda ya so hallaka mu da tuni
ya kawar da mu.

Tunda har ya kyale mu lallai akwai kamshin
gaskiya a cikin zantukansa, sai dai ina shakku
akan batun Gimbiya Ramlatul Siyam da ya ce shi
zai san hikimar da zai yi ya sace ta. Ina ji a jikina
cewar yana da wani shiri na musamman akan
Gimbiya Ramlatul Siyam don haka dole ne mu
sa ido a kansa.

Tabbas yanzu ba mu da wani zaбi wanda fi ya
mu bi umarninsa tunda ya fi mu sanin dukkan
sirrin fadar Sarki Nashmir kuma masu iya

368

TASKARNOVELS.COM.NG
magana sun ce, 'Da dan gari akan ci gari', ko
kuwa a cikinku akwai mai wata sharar daba?"

Da jin haka sai Rahila da Laffaru suka dubi juna
sannan suka yi shiru. Rahila ta ce, "Ba mu da
wata shawara wacce ta fi kawai mu yi
kundunbala mu bi umarnin sadauki Najwar
tunda al'amarin ya zama lalube a çikin duhu, ba
a san inda za a dace ba."

Nan take Maruful Dauwaz ya matsa gaban
sadauki Najwar ya ce, "Mun amince da dukkan
umarninka sai mu tafi kawai".

Koda jin haka sai Najwar ya bushe da dariyar
farin ciki. Nan take yai nuni da hannunsa izuwa
ga Maruful Dauwaz, Rahila da Sarki Laffaru sai
wata murtukekiyar sarkar tsafi ta kanannaɗe su
su duka ta ɗaure su tamau amma wannan karon
babu wuta a jikin sarkar.

369

TASKARNOVELS.COM.NG
Sadauki Najwar ya dubi Aljani Barukul Masnur
ya ce, "Maza ka dauki su Maruful Dauwaz ka
dora su a gadon bayanka sannan mu juya mu
koma izuwa Birnin Hindu".

Nan take kuwa Barukul Masnur ya cika wannan
umarni. Shi ma Najwar sai ya hau kan Barukul
Masnur ya zauna. Nan take Barukul Masnur ya
bude fuka-fukansa ya tashi sama ya kama tsala
azababben gudu yana mai tunkarar Birnin
Hindu.

Hakika inda ace mutum na nan a lokacin da
Aljani Barukul Masnur ya dauki su Aljani
Maruful Dauwaz ya tashi da su sama dole ne ya
cika da tsananin mamaki ya sallamawa Ubangiji
bisa wannan iko nasa, saboda shi kansa Maruful
Dauwaz girman halittar jikinsa ta isa abin
al'ajabi domin in daga nesa mutum ya hange shi
zai yi zaton ko tsauni ne amma sai ga shi Aljani
Barukul Masnur ya ninka shi girma sau uku.

370

TASKARNOVELS.COM.NG
Tabbas! Babu wanda ya san iyakar balittun ke
wannan duniya face Allah. Hakika shi ne abin
tsoro, wanda ya zamo mafi cancanta a bauta
masa tunda shi ne Ya halicci kowa da komai.

Tafiyar rabin sa'a kacal Aljani Barukul Masnur
ya yı ya iso fadar Sarki Nashmir. Koda isowarsa
bakin kofar shiga gidan sarautar sai ya tsaya cak
sakamakon ganin masu gadin kofar sun ki bude
musu kofar su shiga.

Koda ganin haka sai sadauki Najwar ya dubi
masu gadin ya daka musu tsawa ya ce, "Me kuke
jira ne ba ku bude mana kofar mun shiga ba ko
kuwa ba ku shaida mu ba ne?"

Da jin wannan tambaya sai shugaban masu
gadin kofar ya dubi sadauki Najwar cikin
girmamawa ya risina ya ce, 'Ya shugabana ka yi
hakuri muna kan umarnin Sarki ne domin da zai
fita bai gaya mana cewa za ku dawo tare da
fursunoni ba kuma ka san dokar gidan nan babu
371

TASKARNOVELS.COM.NG
wani bako da aka yarjewa shiga face da izinin
Sarki".

Sa'adda sadauki Najwar ya ji cewar Sarki baya
nan ya fita sai ya cika da tsananin mamaki gami
da tsananin farin ciki saboda sanin cewa ya
sami babbar dama da zai iya cika burinsa a
saukake, amma duk da haka dole ne ya bi
al'amarin a sannu.

Najwar ya dubi shugaban masu gadin kofar ya
sake daka masa tsawa a karo na biyu ya ce,
"Shin zan aikata wani abu ne daban ba tare da
izinin Sarki ba? Maza ka sa a bude mana kofa
kada fishin Sarki ya tabbata akanku idan ya
dawo".

Koda jin haka sai shugaban masu gadin ya
sunkui da kansa kas yai shiru kuma ya ki ya
bayar da umarnin a bude kofar saboda ya fada
cikin wasi-wasi da fargaba.

372

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ganin haka sai sadauki Najwar ya fusata
ainun ya zare takobinsa ya dubi shugaban masu
gadin kofar ya ce, "Maza ka bayar da umarnin a
bude mana kofa ko yanzun nan na zare maka
ruhin numfashinka da dukkan jama'ar taka".

Koda jin haka sai jikin shugaban masu gadin ya
kama kyarma, ba shiri ya dubi yaran nasa ya
daka musu tsawa ya ce su yi maza su bude
kofar! Nan take kuwa masu gadin suka fara
kokarin bude kofar.

Ita dai wannan kofa ta shiga fadar Sarki
Nashmir tsawonta ya kai kamu dubu uku, haka
ma fadinta. Idan aka fara bude ta sai an shafe
sa'a uku ana janye ta daga sama tana shigewa
cikin karkashin kasa. Wata murtukekiyar sarkar
karfe ce guda biyu a jikin kofar a dama da
hagunta.

Kowacce sarka guda akwai aljanu dubu goma
wadanda ke rike da ita. Idan za a bude kofar
373

TASKARNOVELS.COM.NG
aljanun da ke dama ne suke jan wannan sarka
har sai sun shafe sa'a uku suna janta sannan za
ta gama budewa ta kule a cikin kasa.

Haka kuma idan za a rufe kofar aljanu dubu
goma da ke hagu ne za su yi ta jan sarkar har
tsawon sa'a ukun sannan kofar take rufewa ta
tokare da saman ginin fadar.

Kaurin wannan kofa ya kai kamu dari uku,
huma an yi ta ne da zallan karfen lu'u-lu'u, babu
wani makami da zai iya yiwa kofar lahani komai
kkarfinsa, tsininsa da nauyinsa.

Sai da su Najwar suka yi jira har tsawon sa'a
uku sannan kofar ta gama budewa suka kunna
kai izuwa cikin gidan sarautar.

Da shigarsu sai Aljani Maruful Dauwaz da Rahila
da Sarki Laffaru suka cika da tsananin mamaki
sakamakon ganin tsananin girman gidan da
374

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma irin gine-ginen da ke cikinsa da kayan
kawar da aka shirya tamkar aljannar duniya.

Babu abin ma da ya fi ba su mamaki face ganin
yadda Aljani Baruk! Masnur ya yi ta tafiya a
cikin gidan sarautar, bai iso inda aka gina
kurkukun gidan ba sai da ya shafe tafiya mai
nisan gaske Wacce suka yi a baya tun daga dajin
Hizurul Aswad.

Nan take Aljani Barukul Masnur ya sauko kasa
ta dira a bakin kofar kurkukun.
Dirarsa ke da wuya sai sadauki Najwar
Ya dubi masu gadin kurkukun ya ce, "Ga
fursunonin Sarki ku shigar da su ciki a kulle su
har sai na dawo karbarsu"

Nan take Wadansu jibga-jibgan aljanu wadanda
sun ninka Aljani Barukul Masnur sau biyu a
girma da Kwarjini suka kama su Maruful
Dauwaz tamkar Shaho ya kama Dan tsako suka
375

TASKARNOVELS.COM.NG
shige da su izuwa cikin kurkukun aka yi ta tafiya
da su har sai da aka yi doguwar tafiya ana wuce
mugayen matakan tsaro, sannan aka jefa su a
cikin wani daki aka kulle su.

Babu abin da ya firgit su Aljani Maruful Dauwa
face ganin tsananin tsaron kurkukun da kuma
irin yanayin ginin da aka yi shi, komai
jarumtakar mahaluki da Karfin sihirinsa bai isa
ya iya guduwa daga cikin wannan kurkukun ba.

Koda suka garkame su Aljani Maruful Dauwaz a
cikin wani kuntataccen ďaki sai hankalinsu ya
dugunzuma domin ji suka yi kamar an jefa su a
cikin rijiya gaba dubu an rufe muffin rijiyar.

Cikin tsananin takaici da nadama Rahila ta dubi
Aljani Maruful Dauwaz ta ce, hakika mun yi
babban kuskure da muka yarda da sadauki
Najwar. Abin da na fahimta yanzu shi ne,
Sadauki Najwar ba ya son ya kashe mu so yake
a kawo mu gare shi a raye, wata kila don ya
376

TASKARNOVELS.COM.NG
ďanďana mana muguwar azaba ne kafin ya
hallaka mu.

ya Koda jin wannan batu sai cikin Sarki Laffaru
duri ruwa ba, ya firgita ainun bai san sa'adda ya
saki fitsari a wando ba. Al'amarin da ya sa Aljani
Maruful Dauwaz ya tuntsure da dariya ke nan,
sannan ya daka wa Laffaru tsawa ya ce, "Kai
tsohon azzalumin Sarki, shin ka manta ne da
irin bakin mulkin da ka yi wa mutane a baya?

Ai bai kamata a ce ka zamo matsoraci mai
gudun azaba tunda babu irin kalar azabar da ba
ka sa an yi wa mutane ba.

Hakika a da can kai Kura ne, amma yanzu
wannan Kurar ta zama Akuya. Abin da nake so
da kai shi ne ka kwantar da hankali ka. Ka sani
cewa mai rai ba ya kasa motsi. Na yi muku
alkawari ba za mu tozarta ba a cikin wannan
kurkuku, ta kowanne hali sai na ceci
rayuwarmu na fitar da mu".
377

TASKARNOVELS.COM.NG

Sa'adda Rahila da Sarki Laffaru suka ji wannan
batu sai suka cika da tsananin mamaki. Rahila ta
dubi Maruful Dauwaz ta ce, Kai kuwa ta yaya za
ka iya fitar da mu daga cikin wannan mugun
kurkuku mai tsananin tsaro haka?"

Da jin wannan tambaya sai Maruful Dauwaz yai
murmushi ya ce, Ku zuba ido kawai ku sha kallo,
nii ne fa jarumi mai sa'a da rabo wanda komai
RINTSI DA TSANANI sai ya fita daga cikin
kowanne bala'i.

Idan kuka yi la'akari da abubuwan da suka faru
a gare mu a baya za ku gane cewa sa'ata ita ce ta
kai mu ga kawowa i yanzu.

Wannan shi ne abin da ya faru ga su Aljani
Maruful Dauwaz bayan an kawo su fadar Sarki
Nashmir a matsayin fursunoni.

378

TASKARNOVELS.COM.NG
Al'amarin su sadauki Najwar kuwa, lokacin da
ya ga an shigar da su Aljani Maruful Dauwaz
cikin kurkuku an je an kulle su sai ya tafi cikin
tsananin farin ciki bisa ganin cewa duk
abubuwan da ya tsara don cika burin rayuwarsa
suna tafiya daidai.

Babu abin ma da ya kara karfafa masa guiwa
face da ya zo ya tarar da cewa Sarki Nashmir ba
ya nan. Abin da ya fado masa a rai shi ne, dole
ne yanzu ya je ya yi bincike domin ya gano inda
sakri Nashmir ya tafi da kuma lokacin da zai
dawo domin ya yi sauri ya gama kammala
dukkan shirye- shiryensa kafin Sarki Nashmir
ya dawo.

Kai tsaye sadauki Najwar ya wuce izuwa
gidansa wanda ke can ɓangare daya a cikin
gidan sarautar. Cikin tsananin farin ciki ya shiga
gidan ya wuce izuwa dakin halwar tsafinsa ya
dukufa. Nan take ya ga abin da ya matukar
girgiza masa hankali ya ga cewa ashe ma idan ya
cika burinsa a yau din ma tsugune ba ta kare ba,
akwai gagarumar masifa a gabansa.
379

TASKARNOVELS.COM.NG

Ba wani abu sadauki Najwar ya gani ba a cikin
madubin tsafinsa face rincaɓewar masifaffen
yaki tsakanin Boka Muzaffar, Sarki Nashmir da
Sharlis a can gidan Boka Muzaffar da ke Birnin
Kufa a dokar daji.

Su ukun suna yakar juna ne akan abu daya. Ba
wani abu bane face MASHIN GALILUL HARAS.

Mashin na jingine a cikin dakin tsafin Boka
Muzaffar amma an rasa wanda zai sami nasarar
daukar mashin a tsakaninsu su ukun domin sun
wanzu a cikin kai wa junansu sara da suka cikin
bakin zafin nama, juriya da jarumtaka ta gaban
kwatance kuma kowannensu yana amfani ne da
dukkan karfin dantsensa da karfin tsafinsa.

Duk sa'adda takubbansu suka hadu sai dai ka ji
tartsatsin wuta na tashi gami da hayaki.

380

TASKARNOVELS.COM.NG
Duk wanda aka sari jikinsa kuwa sai ka ji kamar
karfe aka sara, makamin bay a tasiri haka uma
babu wanda yake da alamar
End Ads