x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - MAZAN JIYA 3

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 68212 words

Category: Adventure Stories

Views 179

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
tsaye da
74

TASKARNOVELS.COM.NG
kyar ya zo kan yaro Masnur ya daga hannunsa
guda sannan ya kara hancinsa a dai-dai nasa ya
ji babu alamar numfashi, ya dora kunnensa a
kirjin Masnur, nan ma ya ji babu alamar
numfashi, sai ya dago kai ya dubi abokan tafiya
daya bayan daya cikin yanayin karayar zuciya
yana mai musu nuni da yaro Masnur ya mutu.
Nan take kowa ya fara kuka, masu kwalla na yi,
masu zubar da hawaye na zubarwa..

Ana cikin wannan hali ne jaruma Shadira ta
farfado sosai, ai kuwa sai ta mike zaune
zumbur! ta shafa bayanta, koda ta ji babu yaro
Masnur sai ta mike tsaye zumbur! tana waigewaige tana neman dan uwanta Masnur ta fara
kwala masa kira.

A wannan lokaci MAsnur na kwance a bayan
boka Muzaffar ba ta ganshi ba. Ganin zubar
hawaye ne akan fuskokin abokan tafiyar ta ta
yasa jikinta yai sanyi. Kawai sai ta dubi boka
Muzaffar ta ce, "Ina dan uwana?" Muzaffar ya
kasa ba ta amsa, kawai sai ya share hawayen
idanunsa ya koma gefe daya, Shadira ta yi arba
75

TASKARNOVELS.COM.NG
da gawar Masnur a kwance idanunsa a bude
kamar zai yi ma ta magana, har a sannan jini na
kwarara daga kan tsakiyar kansa.
Shadira ta tunkaro inda gawar ke kwance çikin
tsananin tsoro, har jikinta na makyarkyata.
Koda ta iso daf da gawar ta dubi tsakiyar kan
Masnur sai ta ga ashe kan ya kusan darewa ma
gida biyu har tana ganin kwakwalwarsa. Nan
take Shadira ta kwarara uban ihu sannan ta
durkushe-kasa bisa guiwoyinta ta ciccibi gawar
Masnur ta rungume ta a kirjinta ta fashe da
matsanancin kuka tana mai kurma ihu.
Al'amarin da ya jefa kowa cikin tsananin tausayi
da bakin ciki kenan aka ci gaba da kuka kamar
ba za a daina ba.

Komai rashin imanin mutum idan ya ga yadda
Shadira ke wannan uban kuka da bakin ciki bisa
rashin dan uwanta dole ne ya kamu da tsananin
tausayinta.

Bayan Shadira ta dade a kankame da gawar dan
uwanta yaro Masnur tana kuka sai kuma ta
76

TASKARNOVELS.COM.NG
shiga sambatu cikin rera waka mai dauke da
kalmomin ban tausayi masu karya zuciya tana
mai cewa:
"Ina amfanin rayuwa idan babu masoyi? Duniya
ki rike jin dadinki Kuma ki rike kayan kawar da
ke cikinki.

"Domin ba ki da abin da zai kawar mini da bakin
cikin zuciyata"

"Ke mutuwa ashe ke matsoraciya ce? Ki fito fili
ki tare ni idan kin isa, yau sai na ga bayanki!"

Lokacin da su sadauki Haiman suka ji irin
wannan sambatu da Shadira ke yi sai suka daďa
kamuwa da tsananin tausayinta. Nan take
Lumaira ta saki Haiman ta je wajen Shadira ta
rungume ta ta baya ta shiga rarrashinta, amma a
banza, kamar ma daďa zuga ta ta yi, sai Shadira
ta sake fashewa da matsanaicin kuka tana mai
dada kankame gawar ďan'uwanta Masnur,
kuma ta ci gaba da sambatu.
77

TASKARNOVELS.COM.NG

Har aka gama sa wa kowa magani a rauninsa
Shadira ba ta saki gawar Masnur ba, kuma ba ta
daina kuka da sambatu ba.

Al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa ke
nan a wajen. Koda ganin haka sai boka Muzaffar
ya kira dukkanin jaruman, wato Haiman, Imran,
Zarina da Shaharan suka koma gefe daya domin
su tattauna akan al'amarin jaruma Shadira

Boka Muzaffar ya dubi jaruman a nutse, ya ce,
"Ya ku abokan tafiya, ku yi sani cewa na kira ku
ne izuwa nan domin mu yi shawara bisa halin
da abokiyar tafiyarmu ta shiga. Idan muka kyale
ta ba mu raba ta da gawar dan uwanta ba ta ci
gaba da wannan sambatu za ta iya haukacewa.
Ma'ana ta rasa hankalinta gabadaya, idan kuma
muka ce za mu rabu da ita anan tabbas za ta iya
kashe kanta tunda ba ta da sauran buri da farin
ciki a rayuwarta. Haka kuma ba za ta yarda ta bi
mu ba mu ci gaba da wannan tafiya tare da ita
tunda burinta ya yanke. Yanzu mene ne
78

TASKARNOVELS.COM.NG
shawararku bisa abin da ya kamata mu yi a
kanta?" Sa'adda boka Muzaffar ya zo nan a
zancensa sai hankalin kowa ya kara dugunzuma
aka rasa wanda zai ce kala, kuma suka kara
kamuwa da tsananin tausayin Shadira.

Bayan shudewar 'yan dakiku masu tsawo, sai
sarki Laffaru yai gyaran murya ya ce, "Ni ina
ganin cewa ba mu da wani zabi wanda ya fi
kawai mu tafi mu bar ta a nan ita da gawar dan
uwanta, domin idan ma muka tafi da ita matsala
za ta zame mana, ba za ta iya taɓuka komai a
cikin tafiyar ba, sai dai ma ta daďa karya mana
zuciya".

Koda jin wannan batu sai gimbiya Zarina ta
fusata, ta daka wa Sarki Laffaru tsawa ta ce, "Ai
dama kai tsohon azzalumi ne, ba ka san irin
ciwon da masoyi yake ji ba yayin da ya rasa
masoyinsa, shi ya sa ka raba Sharlis da iyayenta,
ka lalata rayuwarta, gavshi kuma kaicma yanzu
rayuwarka ta shiga mugun hadarin da ba ka da
tabbacin kubuta. Wato yanzu mun gama cin
moriyar ganga kenan kana son mu yar da
79

TASKARNOVELS.COM.NG
kwauranta? Sai da Shadira ta gama sallama
rayuwarta ta ceto tamu sannan kake son mu yi
mata butulci mu tafi mu bar ta a lokacin da
bacta da kowa, ba ta da sauran buri."

Zarina ta dubi boka Muzaffar ta ce, "Ba za mu
bar Shadira a nan ba. Yanzu sai mu lallaɓa ta mu
karbe gawar daga hannunta mu binne shi
sannan mu ci gaba da wannan tafiya bayan mun
yi jinyar jikku nan mu ta a kallah kwanaki
bakwai.

Koda jin wannan batu sai kowa ya aminta. Nan
take Zarina da Lumaira suka je wajen Shadira
suka shiga rarrashinta a kan ta ba su gawar yaro
Masnur domin a binne shi amma sai taki.

Koda ta ga sun matsa ma ta sai tacyi wuf ta goya
gawar a bayanta ta daure ta tamau sannan ta
dana kibiyoyi akan bakanta ta tsira su ta ce,
"Duk wanda ya ce, "Zai raba ni da dan uwana a
cikinku sai na kashe shi!"
80

TASKARNOVELS.COM.NG

Cikin alamun tsoro Zarina da Lumaira suka bar
wajenta suka koma can inda su boka Muzaffar
ke zaune. Nan fa aka rasa wanda zai je ya karbi
gawar a hannunta. Da ma tunda aka fara
wannan rikici sadauki Imran bai ce uffan ba.

Kawai sai ya dubi mahaifiyarsa ya ce, "Zan je na
karbi gawar wannan yaro daga hannun 'yar
uwarsa na binne shi".

Koda jin haka, sai mahaifiyar Imran ta firgita
ainun ta rike hannayensa ta ce, "Kada ka je gare
ta ta kashe ka a banza". Imran ya yi murmushi
ya ce, "Koda ta rasa hankalinta ba za ta kashe ni
ba. Ki zuba ido kawai ki ga abin da zai faru".

Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya nufi
inda Shadira ke tsaye goye da gawar yaro
Masnur ya durfafe ta kai tsaye ba tare da
shakkar komai ba, amma ya kura mata idanu
81

TASKARNOVELS.COM.NG
cikin alamun tausayawa, har kwalla ta ciko a
idanunsa.

Lokacin da Shadira ta ga Imran ya durfafo ta
kuma ta tabbatar da cewa so yake ya karɓe
gawar Masnur daga gare ta sai ta ritsa shi da
bakanta ta saita shi, kuma ta tabe bakan, amma
sai hannunta ya kama karkarwa ta kasa
harbinsa, ita ma ta kura masa idanu kawai ba
tare da ta sauke bakan nata kasa ba. Imran ya ci
gaba da tunkararta ba tare da jin tsoron komai
ba. Al'amarin da ya bai wa kowa mamaki kenan
aka ci gaba da kallonsu kawai domin a ga abin
da zai faru.

Yayin da ya rage saura bai fi taku uku ba kacal
tsakanin jaruma Shadira da Imran sai ta dan
sauke bakanta ta saki harbi daf da kafarsa ta
daka masa tsawa ta ce, "Kada ka kara kusanto
ni. Wannan shi ne kashedin karshe a gare ka!"
Imran ya yi murmushi kawai ya ci gaba da
tunkaro ta, ita kuma ta dada daga kwarinta ta
saita shi kuma ta taɓe kwarin iya karfinta. A
82

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan lokaci ne mahaifiyar Imran ta fashe da
kuka saboda ganin za a kashe danta a banza.

Har Imran ya zo daf da Shadira yadda baka ce
kawai a tsakaninsu amma ta kasa harbinsa
kawai sai ya sa hannunsa ya ture Bakan nata
sannan ya buďe hannayensa a lokacin da
hawayen tausayi ya zubo masa. Nan take
Shadira ta yi jifa da bakanta ta rungume shi tana
mai sake fashewa da kuka, ta kankameshi a
jikinta.

Imran ya janye jikinsa daga cikin nata suka
fuskanci juna sosai ya ce, "Ya ke abar bege da
tunanina tun farkon haduwarmu, ki yi sani cewa
tsananin tausayinki bisa wannan babban rashi
da kika yi yanzu ya sa na karya alkawarin da na
yi wa mahaifiyata a baya cewar ba zan yi
soyayya ba sai bayan ta sami lafiya. Hakika na
kamu da tsananin tausayinki da na ga kin rasa
dan uwanki wanda kike so fiye da komai a
duniya, sannan sai na kwatanta rashin a kaina
na ce inda ni ne na rasa mahaifiyata lallai zan
ďimauce fiye da yadda kika ďimauce. Daga yau
83

TASKARNOVELS.COM.NG
na yi alkawarin zan ba ki soyayya ta gaskiya
gami da kulawa irin wacce kika bai wa dan
uwanki Masnur domin na debe miki kewar
rashinsa. Ina son ki rungumi kaddara. Ki sani
cewa gabadayanmu nan babu wanda ya fi karfin
ya tsinci kansa a cikin irin halin da kika shiga.
Yanzu sai ki bani gawar Masnur domin mu
binneshi".

Sa'adda Imran ya zo nan a zancensa sai Shadira
ta sake rungume shi ta fashe da sabon kuka na
murna da bakin ciki.

Lokacin da mahaifiyar Imran ta ji abin da danta
Imran ya fada wa Shadira sai farin ciki ya
lulluɓe ta ta ji kamar an ba ta kyautar mulkin
duniya, domin ďanta ya samu soyayyar gaskiya.
Haka dai suka taru suka haka kabari suka sanya
yaro Masnur a ciki suka bizne koda Shadira
lallai da gaske ta rasa ďan uwanta har abada sai
ta kara fashewa da kuka ta rungume Imran.
Haka dai Imran ya cigaba da rarrashinta har
gari ya waye ba tare da sun runtsa ba. Bayan
cikar kwanaki bakwai sai kowa ya kimtsa ya yi
84

TASKARNOVELS.COM.NG
shiri domin a cigaba da tafiya. Lokacin da
jaruma Shadira ta ga za ta bar kabarin dan
uwanta Masnur kuma abu ne mawuyaci ta sake
ganin kabarin sai ta fashe da kuka ta fada kan
kabarin tana sumbatarsa.

Al'amarin da ya karya zuciyar gabaďayan
abokan tafiyar kenan, saboda kowa ya san cewa
shi ma zai iya rasa masoyinsa nan gaba a cikin
tafiyar. Su duka sai suka kama kuka. Hatta
gimbiya Rahila, boka Muzaffar da Sarki Laffaru
wadanda ba su da 'yan uwa ko masoya a cikin
wannan tafiya, ba su san sa'adda suka fara kuka
ba. Da kyar Imran ya samu ya bambare Shadira
daga kan kabarin dan uwanta Masnur, ya ja ta
suka je suka hau kan aljani Marhabul Zaurus
suka zauna.

Cikin gaggawa sauran abokan tafiyar ma suka
hawo suka zazzauna sannan Marhabul Zaurus
ya bude fuka-fukansa ya tashi sama ya luluka
izuwa cikin gajimare yana mai tsala gudu suka
durfafi dajin na uku
85

TASKARNOVELS.COM.NG
Bayan an sami kamar sa'a uku ana tafiya a sama
ba tare da kowa ya ce kala ba, sakamakon
alhinin mutuwar da aka yi, sai aljani Marhabul
Zaurus yai gyaran murya sannan ya juyo da
kansa ya dubi boka Muzaffar cikin alamun tsoro
ya ce, "Ya shugabana ka yi sani cewa tun yanzu
zuciyata ta fara bugawa da karfi saboda tsoro,
domin nan da cikar sa'a biyu rak za mu riski
wannan daji na uku mai dauke da miyagun
manya-manyan tsuntsaye.

Ka sani cewa aljanu ma komai girmansu da
karfinsu suna shakkar waďannan tsuntsaye
saboda karfin sihiri ba ya tasiri a kansu, kuma
suna da gagarumin karfi na gaban kwatance
domin da yatsu biyu kacal suke surar giwa su yi
sama da ita komai girmanta. Kuma duk abin da
suka karta da faratan kafafunsu to fa ko dutse
ne sai ya farfashe.

Daya daga cikinsu yana iya cinye rabin giwa ya
baiwa 'ya'yansa rabin su cinye Suna da tsananin
yawan gaske yadda ko a birni guda suka yiwa
rubdugu za su iya hallaka komai da kowa a cikin
86

TASKARNOVELS.COM.NG
kankanin lokaci. Anya kuwa za mu iya tsallake
sharrin wadannan tsuntsaye?"

Koda jin wannan tambaya sai boka Muzaffar ya
sunkui da kansa kas yai shiru bai ce komai ba,
saboda ba shi da wani bayani mai gamasarwa.
Daga can sai yai ajiyar zuciya ya kira sunan
aljani Marhabul Zaurus ya ce, babu abin da zan
iya cewa akan wannan tambaya da ka yi mini,
abin da na sani kawai shi ne muna sa rai da
samun nasara. Gama fadin haka sai boka
Muzaffar ya tsuke bakinsa yai shiru bai kara
cewa uffan ba.

Haka dai aka ci gaba da tafiyar amma duk
wanda ka duba sai ka ga akwai alamun tsoro a
yanayin fuskarsa. Hakika gaba dayan wadannan
matafiya a gigice suke da shiga wannan daji na
uku inda za a yi karo da wadannan masifaffun
tsuntsaye .
Babban abin da ya fara karya musu zuciya shi
ne, ganin yadda jaruma Shadira ta rasa dan
uwanta a daji na biyu don haka kowa ya san
87

TASKARNOVELS.COM.NG
cewa komai zai iya faruwa gare shi a cikin
wannan tafiya babu mai tabbacin zai gama
lafiya. Bayan shudewar sa'a biyu cif, Sai suka iso
wannan daji na uku.

Tun daga baya-baya aljani Marhabul Zaurus ya
saki fuka-fukansa ya sauko lasa ba tare da ya
karbi izinin saukowa ba.

Al'amarin da ya fusata boka Muzaffar ke nan ya
dube shi ya ce, Waye ya ba ka izinin ka sauko da
mu kasa tun gabannin mu iso farkon daji na
ukun?

Koda jin wannan tambaya sai aljani Marhabul
Zaurus ya risina cikin biyayya ya ce, "Ya
shugabana ka yafe ni kuma ka sani cewa, na yi
haka ne domin mu sake yin cikakken shiri na
shiga wannan daji na uku, saboda idan muka
shige shi kai tsaye, wadannan mugayen
tsuntsaye za su iya yi mana rubdugu a lokaci
guda su gama da mu.
88

TASKARNOVELS.COM.NG

Ina tabbatar muku da cewa karfinmu da
makaman mu ba za su cece mu ba daga harin
tsuntsayen sai dai sa'a da jajircewa!

Lokacin da aljani Marhabul Zaurus ya zo nan a
jawabinsa sai jikin kowa yai sanyi, kuma
hankalin kowa ya kara dugunzuma, ban da na
Shadira, domin ko kadan babu alamar tsoro a
tare da ita, mutuwar ma nemanta take. Kai in ba
don son Imran da ke yawo a zuciyarta ba da tuni
ta kashe kanta ma, domin ba ta ga amfanin
rayuwarta ba a doron kasa.

Nan take kowa ya sauko kasa daga kan aljani
Marhabul Zaurus. Shaharan da dokinsa ne suka
sauka daga karshe.

Shaharan ya ja dokinsa a hankali izuwa cikin
wadansu ciyayi, ya sake shi ya kama kiwo
abinsa a lokacin da ya kurawa dokin idanu yana
89

TASKARNOVELS.COM.NG
kallon mugayen raunikan da ke jikin dokin, ga
shi dama ba shi da lafiya, ko tafiya baya yi.

Nan take kwallah ta zovwa Shaharan domin a
duniya babu abin da yake so sama da wannan
doki, ko kuda ba ya son ya taɓacshi, amma
yanzu gacshi duk ďinki ne kaca-kaca a jikinsa.

Bayan kowa ya zauna an dan huta, sai aka shiga
tattaunawa bisa irin shirin da ya kamata a yi,
don shiga cikin wannan daji.

Boka Muzaffar ya ce, "Abu na farko dai, kun ga
su wadannan tsuntsaye ba sa jin sara da suka,
kuma komai nauyin abu suna iya surarsa da
'yan yatsun kafafunsu su yi sama da shi, kuma
duk abin da suka sura bai isa ya iya kubcewa
daga hannunsu ba, saboda haka duk yadda za
mu yi ka da mu kuskura mu bar tsuntsayen nan
su dauki daya daga cikinmu ta kowane
hali".Sa'adda boka Muzaffar yaczo nan a
jawabinsa sai kowa yai shiru yana tunani. Daga
90

TASKARNOVELS.COM.NG
can sai jarumi Haiman yai gyaran murya ya ce,
"To shin su wadannan tsuntsaye a gaba dayan
jikinsu babu inda KAIFI DA TSINI zai yi tasiri?"

Da jin wannan tambaya sai boka Muzaffar ya yi
shiru yana tunani, daga can sai ya ce, "Fiye da
shekaru dari bakwai baya ba a taɓa samun
mahalukin da ya ratsa ta cikin wadannan
dazuzzuka biyar ba, ya koma gida a raye bare aji
daga bakinsa cewa wadannan tsuntsaye suna da
lago.

A duniya babu abun da za a ce ba zai yiwu ba,
saboda haka babu mamaki mu ne waɗanda za
su gano lagon wadannan tsuntsaye. Ni dai a
yanzu shawarar da zan bayar ita ce, mu rufe
jikinmu da kayan yaki na karfe yadda koda
tsuntsayen sun kawo mana sara da suka da
faratan kafafunsu sai dai su sami karafunan ba
dai jikinmu ba".

91

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai sarki Lafaru ya dubi
boka Muzaffar a fusace ya ce, "Me ya sa tun
kafin mu baro garuruwanmu ba ka sanar damu
wannan al'amari mun yi tanadi ba?
Yanzu a ina za mu sami kayan yaki na karfe
wadanda za mu rufe jikinmu da su?'

Koda jin wannan batu sai boka Muzaffarya ya
bushe da dariya, lokaci guda kuma ya murtuke
fuska sannan ya ce, "To ai in ban da abinka
mene ne amfanin sihirin tsafin da muka
mallaka?"

Kafin wani daga cikinsu ya kara cewa wani abu
tuni boka Muzaffar ya rintse idanunsa ya fara
karanta dalasiman tsafi. Sai da ya shafe dakiku
dari biyu da ashirin yana karanta dalasiman
tsafin a fili, yana gamawa kuwa sai kowa ya
tsinci kansa a cikin kayan yaki na karfe. Hatta
mahaifiyar Imran, Sarkin Farisa, Lumaira da
dokin Shaharan kuwa. Sai ya zamana gaba
dayan jikinsa a rufe yake da sulken karfe.

92

TASKARNOVELS.COM.NG

Kai bama dokin Shaharan ba, hatta aljani
Marhabul Zaurus jikinsa ya lullube da kayan
yaki, hatta katon kansa kuwa, idanunsa, bakinsa
da kunnuwansa ne kadai a waje.

Koda kowa ya tsinci kansa a cikin wannan
kayan yaki sai suka cika da murna saboda a
tunaninsu sun tsira daga sharrin wadannan
mugayen tsuntsayce. Abin da bacsu sani ba shi
ne, wannan kariya ba zavta hana tsuntsayen
cutar da su ba.

A wannan lokaci jaruma Shadira na zaune ita
kadai a gefe daya bisa kan wani dutse ta daga
kanta sama tana tunani. Ba komai take tunani
ba face irin abubuwan da suka faru a baya
tsakaninta da dan uwanta marigayi yaro
Masnur. Musamman a irin lokutan da suke
wasan 'yar birin-birin, da sa'adda suke cin
abinci tare da kuma lokacin da take yi masa
wanka ta yi masa ado. Kai hatta kwanciyar barci

93

TASKARNOVELS.COM.NG
kullum akan kirjinta Masnur ke bacci, ba ya
yarda ya gusa daga kusa da ita.

Sa'adda Shadira ta zo dai-dai nan a tunaninta sai
zuciyarta ta karye, ta fashe da kuka. Al'amarin
da ya dugunzuma hankalin kowa ke nan. Cikin
sauri jarumi Imran ya je gare ta ya zauna daf da
ita, sannan ya sa hannunsa ya share hawayen da
ke zuba a fuskarta ya ce, "Ya ke abar kaunata, na
sani cewa kin yi babban rashi wanda har abada
ba za ki taba mantawa da shi ba, amma saboda
me ni ba zan maye miki gurbin dan uwanki ba?

Daga yau ina son ki daukeni a matsayin dan
uwa, uwa, uba, uwa, kuma babban masoyi
wanda babu kamarsa. Na rantse da darajar
kaunar da nake yi wa mahaifiyata zan soki
kamar yadda kowacce uwa ke son danta, kuma
kamar yadda dan uwa ke son dan uwansa na
jini. Sannan zan sallama rayuwata don kare
taki".

94

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jaruma Shadiara ta ji wannan batu sai ta
rungume Imran tana mai cewa, "Ina yi maka
fatan cika wannan alkawari.Tabbas idan
alkawarinka ya cika za ka maye mini gurbin dan
uwana da na rasa".

A can gefe daya kuwa, Shaharan na satar kallon
gimbiya Zarina, amma bai san cewa tana
kallonsa ba da wutsiyar idonta, kuma dan
uwanta ma Sarkin Farisa yana lura da abin da
ke faruwa a tsakanin nasu. Nan take Sarkin
Farisa yai murmushi a lokacin da ya dubi 'yar
uwar tasa ya ce, "Ya ke 'yar uwata, ni kuwa ina
son na nemi wata alfarma guda daya rak a
wajenki".

Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama
Zarina ta ce, "Yanzu dama ashe akwai wata
bukata da kake da ita amma tuntuni baka furta
mini ita ba? Sarkin Farisa ya numfasa, "A'a a
yanzu ne bukatar ta zo mini".

95

TASKARNOVELS.COM.NG
Zarina ta ce, "Ina sauraronka, in dai abu ne mai
yiwuwa a duniyar nan, kuma ina da ikon yi sai
na yi maka shi. Sarkin Farisa yai shiru kamar ba
zai ce komai ba, daga can kuma sai ya dubi
Zarina ya ce, "A duniya babu mutumin da nake
tausayawa face wanda ya jarabtu da son wani,
amma wanda yake
End Ads