ya bar wajen
kafar maridin ta take tasa kafar, fit sai babban
dan yatsansa ya fice ya tsandara ihu, amma
saboda juriya bai yarda ya fadi ba sai ya
sungumi Zarina ya goya ta a bayansa ya ci gaba
da gudu a tsakankanin maridan. Sai da aka shafe
sa'a guda cur ana wannan bakin gumurzu ya
zamana cewa babu wanda maridin ba su yi wa
rauni biyu zuwa uku ba face Sarki Laffaru da
kuma 'yan uwan jaruman wadanda dama
tuntuni su tsoro ya sumar da su. Shi kuwa
Laffaru don ya бuya ne a kasan boka Muzaffar
wanda shi ma tunda ya suma bai farfado ba. A
37
TASKARNOVELS.COM.NG
wannan lokaci ita kanta Rahila ta gaji ainun har
ta fara sarewa ta sallama cewa lallai duk hallaka
za su yi.
Sadauki Haiman ma ya karaya, domin ta kai
cewa da kyar yake iya ci gaba da tarwatsa
maridan kuma ga shi tunda maridan suka
kewaye su a waje daya ake ta gumurzun
sakamakon ihu da maridan suke ta yi ba su fasa
ba. A wannan lokaci aljani Marhabul Zaurus ne
kadai bai gaji ba, amma shi ma ya san cewa in
dai aka kara 'yan dakiku a haka shi ma ba zai kai
labari ba Lokacin da aljani Marhabul Zaurus ya
ga mutuwa muraran na shirin afko masa sai ya
tuna cewa shi aljani ne yana da fuka-fukai da zai
iya tashi sama ya dunga dukan kan maridan,
kawai sai yai kundunbala yai sama yana mai
surar sadauki Haiman da gimbiya Rahila suka
kama shawagi akan maridan suna saran
kawunansu.
Ai kuwa sai ga shi maridan na zubewa kasa
matattu kamar ana sassabe a gona. Damar da
suka samu ke nan suka sauko kasa cikin zafin
38
TASKARNOVELS.COM.NG
nama suka kwashe, dukkan abokan tafiyar tasu
sannan suka ci gaba da ragargazar maridan.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin maridan
kenan domin su kansu ba su taɓa shiga bala'i ba
irin na wannan rana domin ba su taɓa haduwa
da shaidanun da har suka sami damar iya
hallaka koda daya daga cikinsu ba. Ya yin da
maridan suka ga mummunar 6arnar da aka yi
musu kuma ana daďa ci gaba da yi musu sai
suka fara guduwa suna shigewa cikin ramukan
da suka firfito. Kafin a jima wajen ya zama babu
irinsu face matattunsu. Koda ganin hanya ta
samu sai farin ciki ya kama su Rahila, nan take
Rahila ta umarci aljani Marhabul Zauwas da ya
yi sauri ya kai su karshen iyakar wannan daji
inda za su iya tsayawa su yi jinyar raunikansu
ba tare da fargabar kada maridan su sake kawo
musu farmakin sumame ba.
Nan take kuwa aljani Marhabul Zauwas ya cika
wannan umarni bai sauka a ko ina ba sai a
gaban wata korama da ke karshen dajin
Maridai!
39
TASKARNOVELS.COM.NG
A wannan lokaci ne Sarki Lafaru ya tsugunna a
gaban boka Muzaffar ya kara kunnensa a dai-dai
hancinsa sai ya ji yana numfashi, cikin tsananin
farin ciki Sarki Laffaru ya ruga cikin wannan
korama ya debo ruwa ya watsa wa Muzaffar nan
take Muzaffar ya farfado daga dogon suman da
ya yi yana mai ajiyar numfashi. Nan dai aka
watsawa duk wadanda suka suma ruwa suka
farfado.
Koda Zarina ta dawo haiyacinta sai ta je gun
Shaharan ta durkusa a gabansa ta dube shi cikin
tsananin mamaki ta ce, "Me ya sa ka sallama
rayuwarka domin ceton tawa?". Da jin wannan
tambaya sai Shaharan ya yi murmushi ya ce,
"Zuciyar da ta kamu da soyayyar gaskiya ba ta
shakkar mika rai da jikinta ga abin kaunarta?".
Koda jin wannan batu sai Zarina ta turbune
fuska ta ce, "Kaiconka ya kai wannan
jarumi...Ina mai shawartarka da ka yi kokari ka
goge wannan kauna daga cikin zuciyarka har sai
izuwa lokacin da bukatarmu ta biya muka sami
abin da muka je nema akogon Darul Iksina,
amma daga yanzu har izuwa wannan lokaci ba
40
TASKARNOVELS.COM.NG
za ka sami amincewar abin da kake so ba. Na yi
matukar bakin ciki da ka rasa babban dan
yatsanka na kafa guda daya, amma idan har ba
ka sami muradin zuciyarka ba ina yi maka fatan
samun madadinta. Koda gama fadin haka sai
Zarina ta mike tsaye ta koma inda take.
Shi kuwa sadauki Imran lokacin da ya dawo
cikin haiyacinsa sai suka kama kallon-kallo
tsakaninsa da Shadira. Ga shi dai ya san cewa ta
ceci rayuwarsa kuma yana son ya yi ma ta
godiya, amma sai ya kasa.
Ba tare da ɓata lokaci ba aka shiga yi wa masu
rauni magani. Mahaifiyar Imran da kanta ta
sawa Imran magani. Koda ta ga yadda ya samu
manyan raunika sai ta fashe da kuka. Al'amarin
da ya matukar dungunzuma hankalin Imran ke
nan ya rike kafadunta suka fuskanci juna
sannan ya ce, "Ya ke Ummina ina dalilin wannan
kuka naki?"
Koda jin wannan tambaya sai mahaifiyar tasa ta
yi ajiyar zuciya gami da goge hawayenta sannan
ta ce, "Ya kai ďana, ka yi sani cewa ba wani abu
ba ne ya sa ni wnanan kuka ba face ganin yadda
41
TASKARNOVELS.COM.NG
ka sami wadannan raunika saboda kawai ka
cika mini burina. Hakika wannan tsautsayi da ya
same ka ya sa na yi nadama bisa neman
maganin nan. In da na san cewa wannan
tsautsayi zai same ka da na hakura da wannan
bukata tunda dai ni na tsufa, ba lallai ba ne na
kara shekaru masu yawa a duniya".
Koda jin wannan batu sai kwalla ta ciko a
idanunsa ya rungume mahaifiyar tasa yana mai
cewa, "Ya ke Ummina ki yi sani cewa raina da
lafiyata ba a bakin komai suke ba muddin zan
sami damar faranta miki rai. A duk sa'adda na
tuno irin tsananin wahalar da kika sha a kokarin
ganin na rayu sai na ga cewa har abada babu
abin da zan yi miki na saka miki da shi. Ya za a
yi na kasa yin wannan tafiya alhalin na san cewa
ba ki da burin da ya fi ki ga kin mike da kanki
kin taka kafafunki? Sa'adda Imran ya zo nan a
zancensa sai mahaifiyarsa ta sake kankame shi a
jikinta, a lokaci guda duk su biyun suka fashe da
kuka.
42
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ganin wannan al'amari sai gaba dayan
abokan tafiya suka kamu da tsananin
tausayinsu. Wasu suka yi kwallah, wasu kuwa
sai da suka zubar da hawaye.
A wnanan loakci Sarkin Farisa na sa wa gimbiya
Zarina magani, lokacin da shi ma ya ga raunikan
da ke jikin 'yar uwar tasa sai ya kasa ci gaba da
sa ma ta maganin ya kama zubar da hawaye. Da
ganin haka sai Zarina ta yi murmushi ta ce
"Haba ya kai dan uwana akan wane dalili
zuciyarka za ta karaya bisa abinda ya samevni?
Ka sani cewa farin cikinka farin cikina ne, haka
ma bakin cikinka nawa ne. Har abada ba zan
taɓa samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba
face na ga ka yi aure har ka haihu, sannan ne ni
fa zan fara tunanin yin auren.
Ka tuna cewa tun muna yara da muka taso tare
komai a lokaci guda muke yi, wani ba ya riga
wani, don haka har abada ina kan wannan baka
ba zan sauya ba.
Lokacin da gimbiya Zarina ta zo nan a zancenta
sa sai Sarkin Farisa ya kara kamuwa da tsananin
tausayinta ya ce, "Ya ke 'yar uwata rabin jikina
43
TASKARNOVELS.COM.NG
ki ya sani cewa idan har kina son na yi aure to fa
sai dai mu yi a rana daya Ina nufin a ranar da na
sami lafiya. Idan kuwa ba ki amince da hakan ba
to har abada ba zan yi aure ba. Koda jin haka sai
hankalin Zarina ya dugunzuma ta yi shiru tana
tunani, daga can sai ta lok daga kai ta dubi
Sarkin Farisa ta ce, "Haba ya kai dan uwana
saboda me za ka fadi haka? Sarkin Farisa ya ce,
"Saboda na fuskanci cewa ko soyayyar ma ba
kya so ki yi. Idan har za mu yi aure a rana guda
dole ne ki nemi masoyi da wuri tun yanzu kafin
lokaci ya yi domin hankalinki da shi ki tabbatar
da soyayyarsa ta gaskiya yake yi miki ko saboda
matsayinki yake yi miki ita ba. Tun a yanzu na
fuskanci cewa kin sami wannan masoyi."
Cikin matukar mamaki Zarina ta dubi dan
uwanta Sarkin Farisa ta ce, "Wa kake nufi?"
Sarkin Farisa ya ce, "Wanda ya ceci rayuwarki
dazu a can inda muka fafata da maridai, wato
sadauki Shaharan. Tabbas sadauki Shaharan ya
kamu da matukar kaunarki, kuma ta kauna ta
gaskiya, domin inda da akwai algus a cikin son
da yake yi miki da ba zai iya sallama rayuwarsa
ba da ceton taki. Koda jin wannan batu sai jikin
gimbiya Zarina ya yi sanyi, ta sunkui da kanta
kas kuma ta yi shiru tana tunani. Daga can sai ta
44
TASKARNOVELS.COM.NG
dago kai ta dubi Sarkin Farisa ta ce, "Ya kai dan
uwana ka sani cewa na yi alkawari cewa ba zan
taɓa yin soyayya ba face na ga ka sami lafiya
Tabbas har yanzu ina nan akan wannan batu ba
zan sauya ba, saboda haka zai fi kyau ka daina yi
mini batun soyayya daga yanzu har izuwa
lokacin da bukatarmu za ta biya.'
Da jin haka sai Sarkin Farisa ya ci gaba da sawa
Zarina magani akan ciwonta, yai shiru bai kara
cewa uffan ba.
A ɓangaren Lumaira da mijinta sadauki Haiman
kuwa, lokacin da ta farfado daga dogon suman
da tayi sai ta ji ta a jikin mijinta. Cikin dimauta
ta rungume shi ta kama shafa jikinsa, ai kuwa
sai taji ta tabo jini a wuri biyu.
Nan take hankalinta ya dugunzuma ta rasa abin
da ke ma ta dadi. Kawai sai ta janye jikinta daga
cikin nasa ta fashe da kuka. Cikin matukar
tausayi Haiman ya ruko hannayenta ya danka
mata garin magani ya ce, "Ya ke matata kukan
me za ki yi kuma alhalin muna daf da samun
biyan bukata? Kawai ki shafa mini wannan
magani akan raunin da navji, domin ba komai
45
TASKARNOVELS.COM.NG
ba ne face alamun masu tabbatar da cewa zamu
sami nasarar samun abinda muka fito nema".
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa
Lumaira ta ce, "Ya kai mijina ka yi sani cewa zan
iya zama da kai babu idanu har izuwa karshen
rayuwata muddin zan rinka jin numfashinka a
kusa da ni gami da koshin lafiyarka, duk da
cewa ina matsayin makauniya. Ka yi sani cewa
ba don komai na damu na warke daga cutar
makanta ba sai dan kawai na ga irin fuskarka
kafin ajálina ya riske ni, duk da cewa ina ayyana
fuskarka a zuciyata. Da jin haka sai Haiman ya ji
ya kara kamuwa da tsananin tausayinta. Kawai
sai ya rungume ta ya kama zubar da hawaye.
Duk wannan abu da ke faruwa Shadira da
Masnur sun nutsu suna kallon Lumaira da
Haiman. Koda yaro Musnur ya ga abin da ya faru
tsakanin Lumaira da mijinta sai shi ma ya dauki
garin magani ya kama sa wa 'yar uwarsa
Shadira a jikin raunikanta, yana yi yana zubar
da hawaye. Ga shi dai akwai alamun cewa akwai
maganganu a bakinsa amma saboda ba shi da
46
TASKARNOVELS.COM.NG
bakin maganar sai yai shiru kawai. Lokacin da
Shadira ta fuskanci halin da dan uwanta ke ciki
sai ta fashe da kuka kuma ta rungume shi a
kirjinta ta kamu da tsananin tausayinsa tana
mai cewa, "Ya kai dan uwana kada ka damu da
wannan matsayi da ka gan ni a ciki, domin ina ji
a jikina cewar bukatarmu na daf da biya. Tabbas
akwai alamun cewa zamu iya shan tsananin
wuya a cikin wannan tafiya, wata kila ma
wasunmu su rasa rayuwarsu, amma ni dai
fatana shi ne ka sami lafiya, koda zan rasa
rayuwa ta. Da jin haka sai yaro Masnur ya janye
jikinsa daga cikin na Shadira suka fuskanci juna
ya fara bayani a gare ta cikin yaren bebaye,
wato amfani da hannu ya ce, "Ya ke 'yar uwata
kin sani cewa tun da iyayenmu suka mutu kika
ci gaba da kula da rayuwa ta ya zamana cewa ke
ce uwata, kuma ke ce ubana. Babu wani mutum
wanda na shaku da shi a duniya sama da ke.
Yaya kike zaton zan kasance idan babu ke?
Lallai idan kika rasa rayuwarki a cikin wnanan
tafiya ni ma tawa ba ta da amfani, domin ba zan
taɓa samun sukuni da kwanciyar hankali ba.
Duk abincin da zan sa a bakina komai dadinsa
ďaci zai yi mini. Yadda na ga rana haka zan ga
dare, domin bazan iya rintsawa ba. A takaice dai
47
TASKARNOVELS.COM.NG
komai na duniya zai dagule mini har bakin ciki
ya haddasa mini cutar ajali. Da jin wannan
bayani na hannu da Masnur ya yi mata, sai
Shadira ta yi sauri ta janye jikinta daga cikin
nasa suka fuskanci juna. Bisa mamaki sai ya ga
ta yi masa murmushi sannan tasa hannu ta
share masa hawaye ta ce, "Kwantar da
hankalinka ya kai dan uwana, albarkacin kaunar
da ke tsakanina da kai ba zan mutu ba a cikin
wannan tafiya har bukatarmu ta biya mu koma
gida lafiya. Sa'adda Masnur ya ji haka sai ya cika
da farin ciki, fuskarsa ta cika da murmushi.
Ba shakka soyayya tana cikin litattafan yaki.
*********************
Al'amarin Shaharan kuwa, lokacin da ya ga
Zarina ta ki yarda ma su yi wata magana duk da
cewar ya ceci rayuwarta, sai hankalinsa
dugunzuma ya rasa abin da ke masa dadi, domin
shi hankalinsa dai ya san cewa ya kamu da
tsananin kaunarta kuma ba zai iya sarrafa
zuciyarsa ba ga barin abin da take so, amma da
ya dubi dokinsa ya gan shi a raye sai zuciyarsa
ta yi sanyi, ya ji, dadi a ransa, saboda ko ba
48
TASKARNOVELS.COM.NG
komai dai har yanzu ya san cewa yana sa ran
cewa ba tafiyar bazan yake ba yana kan tafarkin
cika burinsa na duniya, wato zai ci gasar tseren
doki ta duniya, zai mallaki dukiya irin wacce bai
taɓa mallaka ba, kuma zai mallaki gimbiya
Shalirat 'yar Sarkin birnin Hairil Salas. Koda ya
zo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta ce da shi, "To
wai shin me yasa yanzu kake son Zarina wacce a
wannan tafiya ka hadu da ita, alhalin ga Shalirat
can wacce ka shafe shekara da shekaru kana
begenta da burin son aurenta?"
Koda Shaharan ya zo nan a zancen zucinsa sai
ya kasa bai wa kansa amsa, kuma hankalinsa ya
kara dugunzuma.
Sai da aka yi kwana hudu a bakin wannan
korama ana jinya sannan kowa ya ji kwarin
jikinsa aka yi shiri domin a shiga wannan daji na
biyu.
A wannan lokaci ne jikin boka Muzaffar ya yi
sanyi ainun ya kasa cewa a tashi da sauri a tafi.
Shi da ya kasance jagoran tafiya sai ga shi ya
kasa mikewa tsaye ma bare ya wuce kan gaba a
ci gaba da tafiyar.
49
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ganin haka sai Sarki Laffaru ya je gaban
boka Muzaffar ya tsugunna suka fuskanci juna
ya ce, "Ya kai wannan boka, ka yi sani cewa
gabadayanmu nan jikinmu ya yi sanyi bisa ganin
yadda kai ma jikinka ya yi sanyi a cikin wannan
tafiya. Shin ka fitar da tsammani ne bisa samun
nasararmu?"
Sa'adda boka Muzaffar ya ji wannan tambaya sai
ya sunkui da kansa kas yai ajiyar zuciya, kuma
yai shiru kamar ba zai ce komai ba.
Daga can kuma sai ya dago kai ya dubi Sarki
Laffaru cikin alamun tausayawa, kuma cikin
sauke murya yadda babu wanda zai ji abin da
yake fadi face Laffarun, ya ce, "Ya kai abokina ka
yi sani cewa tun a baya sa'adda muka keta ta
cikin wannan daji mai mugayen aljanu rukuni
na uku zuciyata ta karaya ga samun nasararmu.
Ka tuna da irin tsananin wahalar da muka sha
sa'adda muka riski rukuni na biyu da na ukun
50
TASKARNOVELS.COM.NG
wanda in ba don jaruma Rahila ba da tuni gaba
dayanmu mun hallaka. Yanzu kuma da muka
shigo cikin daji na farko daga cikin guda biyar
waɗanda daga su sai kogon Darul Iksina, na ga
wannan masifa da muka shiga sai na tabbatar
da cewa babu mai isa kogon Darul Iksina face
mai tsananin NISAN KWANA.
Ka sani cewa bala'in da ke cikin ragowar
dazuzzukan hudu yafi na wannan daji na farko.
Ni kam na yi matukar nadama bisa yi muku
jagora a cikin wannan tafiya, domin a yanzu na
tabbatar da cewa kunya zan ji domin na dora ku
akan hanyar da ba za ta bulle ba. Koda boka
Muzaffar ya zo nan zancensa sai Sarki Laffaru ya
bushe da dariya. Al'amarin da ya matukar bai
wa boka Muzaffar mamaki ke nan.
Lokaci daya sai Sarki Laffaru ya murtuke fuska
ya ce, "Ya kai wannan boka, ka yi sani cewa shi
bala'i kafin ya zo ne ake tsoronsa ko kuma ake
nadamar tunkararsa, amma idan ka riga ka
shige shi sai a rungumi duk abin da ya zo da shi.
Ina tabbatar maka da cewa har a yanzu ba na jin
51
TASKARNOVELS.COM.NG
tsoro ko fargabar komai, duk da cewa ban yi
kokarin komai ba a cikin wannan tafiya. In da
ace karfin damtsena zai dawo jikina a yanzu ina
tabbatar maka da cewa jarumtakar da zan yi ko
jaruma Rahila ba za ta lya irinta ba. Ina mai
shawartarka da ka daina nuna karayar
zuciyarka ga abokan tafiya, domin kada suma su
karaya su janye ci gaba da wannan tafiya. Ni
kam gwara na rasa rayuwata da dai na koma
gida babu biyan wannan bukata, tunda dai ni da
gawar babu bambanci tunda zan rasa komai
nawa, kuma dan cikina yavzo ya zama ajalina.
Kai ma idan ka yi tunani rayuwarka a cikin
mugun hadari take, idan har ba mu sami nasara
ba bisa wannan bukata da ke gabanmu, domin
ka kulla gaba da matata Sharlis, tunda kai ne ka
kubutar da ni daga sharrinta. Ka fi ni sanin
iyakar karfin Sharlis, don haka kai ne ka san
abin da zai biyo baya fiye da ni".
Sa'adda Sarki Laffaru ya zo nan a zancensa sai
kwalla ta cika idanun boka Muzaffar ya ce, "Ya
kai abókina hakika duk abin da ka fadi gaskiya
ne, kuma a yanzu ma inda ka san irin
mummunar 6arnar da Sharlis ta yi mana ni da
52
TASKARNOVELS.COM.NG
kai da ka dada tabbatar da cewa ba mu da wani
kwanciyar hankali wanda ya fi mu sami nasarar
abin da muka fito nema. Cikin firgici Sarki
Laffaru ya dubi boka Muzaffar ya ce "Wane irin
mugun abu Sharlis ta yi mini a yanzu bayan na
baro kasata?".
Muzaffar ya girgiza kai sannan ya ce, A halin
yanzu Sharlis ta yi yaki da mayakan Sarki
Nurbas ita kadai ta tarwatsa su, kuma ta kashe
Sarki Nurbas. Aljani Shalbasha ibini Rauhuba
kuwa, wanda muka baro a matsayin halifanka ta
gano ko wane ne shi, har ta tura shi izuwa
birnin Zaruf yana wakilcin Shugabancin birnin.
Akan karagarka kuwa ta mulki, ta dora danta
Shaddad yana mulkin jama'arka cikin adalci da
kyautatawa talakawa, saɓanin na ka mulkin. Ina
tabbatar maka da cewa danka Shaddad ya sami
farin jini ainun a wajen jama'ar Kasarka, basa
fatan ka komo gare su. Dubi tafin hannuna
domin ka ga zahiri".
Koda gama fadin haka sai boka Muzaffar ya
bude tafin hannunsa. Nan take hoton fadar Sarki
53
TASKARNOVELS.COM.NG
Laffaru ya baiyana, sai ga Shaddad yaro dan
shekara uku akan karagar mulki, mahaifiyarsa
Sharlis na zaune a gefensa, kuma ga fadawa sun
kewaye Shaddad ana tafiyar da harkokin mulki,
talakawa sai shigowa suke cikin fadar suna
zubewa kasa suna kwasar gaisuwa, yaro
Shaddad na sawa ana basu kyautar suturu,
dukiya da kayayyakin abinci.
Koda ganin wannan al'amari sai bakin ciki ya
sake turnuke Sarki Laffaru fiye da ko yaushe,
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar za ta kone,
bai sansa'adda idanunsa suka ciko da kwallah
ba suka fara zubar da hawaye.
Lokacin da boka Muzaffar ya ga halin da Sarki
Laffaru ya shiga sai ya yi sauri ya shafi tafin
hannunsa, hoton komai ya ɓace, sannan ya dafa
kafadar Sarki Laffaru ya ce "Kada ka damu ya
kai abokina, ita rayuwa dama haka take, wata
rana kai ne a sama, wata ran kuma ka zamo a
kasa. Shin ka manta sa'adda kake kan
sharafinka ne lokacin da ka buwayi gaba dayan
kasashen da ke nahiyarka gaba daya?
54
TASKARNOVELS.COM.NG
Ina mai kara maka karfin guiwa akan wannan
gagarumin aiki da ke gabanmu domin ba mu da
wani zaɓi wanda ya fi mu tabbatar da cewa mun
sami nasarar abin da muka fito nema. Koda
gama faɗin haka sai boka Muzaffar ya yi shiru
yana mai sunkui da kansa kas cikin halin
tsananin damuwa. Sarki Laffaru ya dube shi ya
ce,