sami wuri suka kishingida
domin su huta sosai kasancewar har a sannan
raunikan jikinsu na damunsu da zogi.
Koda kishingiɗar ta su sai Rahila ta kurawa
Sarki Laffaru idanu tana murmushi kawai,
al'amarin da ya matukar ba shi mamaki ke nan
ya dube ta ya ce, "Ya ke matata ta gobe ina
dalilin wannan murmushi da kike yi a gare ni?"
Koda jin wannan tambaya sai Rahila ta sake yin
murmushi ta ce, "Ba komai ne ya sa ka ga ina yi
maka murmushi ba face ina aiyanawa a raina
cewa ga shi mun yi aure har mun sami
kwanciyar hankali".
335
TASKARNOVELS.COM.NG
Da jin haka sai Laffaru ya gyada kai cikin
alamun karayar zuciya, ya budi baki don ya ce
wani abu sai kawai suka ji wani abu mai
tsananin nauyi ya fado kan tsaunin da suke ciki
take saman tsaunin ya rugurguje ya rufto ciki.
Aljani Maruful Dauwaz ya farka cikin tsananin
razana, amma kafin ya yi wani yunkuri sai ya ji
an yi masa muguwar damka an bankare
hannayensa da kafafunsa ta baya da karfin tsiya,
ya ji kamar za a kakkarya shi. don haka sai ya
kwarara uban ihu sakamakon tsananin zafi da
zogin da yake ji. Ya yi iya kokarinsa ya kufce
amma sai ya kasa.
Ba wani bane ya yiwa Marutul Dauwas wannan
muguwar damka ba face Aljani Barukul Masnur,
hadimin jarumi Najwar.
Hakika masu iya magana sun yi gaskiya da suke
cewa, 'Gaba da gabanta, Aljani ya taka wuta. Duk
irin gagarumin karfin da Aljani Maruful Dauwaz
336
TASKARNOVELS.COM.NG
ke da shi sai ya zamo na banza sakamakon
Barukul Masnur ya ninka shi sau uku a karfin
dantse.
Koda Rahila ta ga abin da ya faru da Maruful
Dauwaz sai ta mike zumbur ta zare takobinta,
shi kuwa Sarki Laffaru ko motsawa ya kasa
saboda tsananin firgita da ya yi bare ya yi
yunkurin zare makami.
Kawai sai suka ga sadauki Najwar ya fado
gabansu ta cikin saman tsaunin inda Aljani
Barukul Masnur ya faso.
Najwar ya dira a gaban Rahila yana murmushin
mugunta a lokacin da ita kuma jikinta ya kama
karkarwa.
Sadauki Najwar ya dube ta ya bushe da
mahaukaciyar dariya, bayan ya kare mata kallo
sama da kasa sai ya ce, "Yanzu ke a haka kike
337
TASKARNOVELS.COM.NG
tunanin za ki iya yakata? Ki dubi jikinki fa ki
gani kina da manyan raunika har guda uku
kuma danyu. Ke ni abin kunya ne ma a ce na yi
fada da ke domin sai dai na ci zalinki kawai.
Duba fa ki ga halin da abokin tafiyar taku ke ciki.
A haka kuke sa ran za ku iya shiga har fadar
maigidanmu ku sace 'yarsa ku samo yawun
barcinsa. Shi kansa Maruful Dauwaz din da kuka
dogara da shi dubi yadda ya zamo tamkar dan
tsako a hannun Shirwa, Ina tabbatar miki da
cewa wannan Aljani da ya bankare Maruful
dauwaz yanzu akwai irinsa sama da guda dubu
dari a cikin fadar shugabana. Ya ya za ku yi da
su?"
Koda jin wannan batu sai Rahila ta dubi sadauki
Najwar cikin karfin hali da taurin zuciya ta ce,
"Wannan kuma matsalarmu ce ba taka ba. Ka
bai wa Aljaninka umarnin ya saki Maruful
Dauwaz ko na afka muku na kawar da ku".
Da jin haka sai sadauki Najwar ya sake bushewa
da dariyar mugunta a karo na biyu ya ce, "Ai sai
ki jarraba mu gani".Kafin ya gama rufe bakinsa
338
TASKARNOVELS.COM.NG
tuni Rahila ta dako tsalle sama daga inda take
tsaye ta kai masa wawan sara a wuya. Ko
gocewa bai yi ba ya tsaya cak a inda yake. Koda
takobin Rahila ta sari wuyan sadauki Najwar,
sai nan take ta narke ta zama ruwa kuma ruwan
ya dige a kasa ya zamana cewa kotar takobin ce
kadai ta yi saura a hannunta. Kawai sai Rahila
tayi jifa da kotar takobin sannan ta gyara
tsayuwarta tana mai dunkule hannayenta biyu,
alamar tana son su gwada 'yar kashi.
Sadauki Najwar ya yi murmushi ya yafito da
hannu. Nan take Rahila ta afka wa Najwar ta hau
bugunsa da naushinsa da hannu da kafa.
Wannan karon ma Najwar bai kaucewa harin
nata ba. Duk sa'adda Rahila ta naushi jikin
Najwar sai ta ji kamar karfe ta nausa, ba shiri ta
ja da baya tana yarfe hanhayenta domin ji ta yi
kamar yatsunta sun kakkarye. Kafin ta sake yin
wani yunkuri sai ta ga Najwar tsulum a gabanta
ya gabza ma ta naushi a fuska.
Nan take ta sulale kasa sumammiya. Koda
Laffaru ya ga abin da ya faru ga Rahila sai ya
339
TASKARNOVELS.COM.NG
razana ainun gaba daya jikinsa ya kama
karkarwa bai san sa'adda ya sakin guntun fitsari
ba a wando saboda tsananin razana. Har izuwa
wannan lokaci Aljani Maruful Dauwaz ya kasa
kwatar kansa daga hannun Aljani Barukul
Masnur sai wutsil-wutsil yake kamar Bera a
bakin Mage.
Sadauki Najwar ya sake tuntsurewa da dariya a
karo na uku sannan ya dubi Barukul Masnur ya
ce, Saki Maruful Dauwaz na fafata da shi domin
ina son na ga iyakar jarumtakarsa".
Da jin wannan umarni sai Barukul Masnur ya yi
jifa da Maruful Dauwaz a kas tamkar an yar da
jikakken tsumma. Cikin taurin rai Maruful
Dauwaz ya mike tsaye zumbur! Ya zare
sihirtacciyar takobinsa ya ce, "Tabbas zan nuna
maka cewa ni jarumi ne wanda ba ya gudu
kuma ba ya shakkar abokin gaba komai
jarumtakarsa da karfin sihirinsa."
340
TASKARNOVELS.COM.NG
Najwar ya yi murmushi ya ce, "Da kyau, haka
nake son na ji kalamin yarda da kai daga bakin
jarumin kwarai".
Gama fadin hakan ke da wuya sai shi ma Najwar
ya zare tasa sihirtacciyar takobin ya fuskanci
Maruful Dauwaz suka tsaya suna kallon kallo, a
lokacin da takobin Maruful Dauwaz ke fitar da
wani irin farin haske ita kuma takobin Najwar
tana fitar da jan haske.
Kwatsam! Sai suka ruguntsume da azababben
yaki, Aljani Barukul Masnur da Sarki Laffaru
suka zama 'yan kallo, ita kuwa Rahila har a
sa'anan ba ta farfado ba. Najwar da Maruful
Dauwaz suka rinka kai wa juna sara da suka
cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta Duk
sa'adda takubban nasu suka hadu sai ka jí an
tsala tsawa mai firgitarwa kuma tartsatsin wuta
da hayaki na tashi. Ai kuwa suna fara gumurzu
Maruful Dauwaz ya raina kansa domin da kyar
yake iya kare harin Najwar saboda ji yake
341
TASKARNOVELS.COM.NG
kamar dutse mai nauyi ake maka masa akan
takobinsa.
Da suka kara nutsawa a cikin gumurzun sai ya
zamana cewa sun tashi hankalin tsaunin gaba
daya domin duk wanda aka kai wa hari ya goce
da zarar an sari dutsen kogon sai ka ga dutsen
ya zabtare yana rugujewa.
Babban abin da ya fi dugunzuma hankali Aljani
Maruful Dauwaz shi ne, KAIFI DA TSINI ba sa
tasiri a jikin sadauki Najwar amma tuni Najwar
ya yi ma Maruful Dauwaz kyawawan yanka
guda biyu, ďaya a kirjinsa, daya kuma a kan
kaurin kafarsa ta hagu. Raunin kafar ya yi zurfi
jini na ta zuba har ta kai cewa yana ďingishi da
jan Kafar amma saboda naci da juriya bai fasa ci
gaba da yakin ba a haka.
Lokacin da Aljani Marufu! Dauwaz ya fahimci
cewa idan har suka ci gaba da yakin a haka
tabbas Najwar zai sami nasarar hallaka shi a
342
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin kankanin lokaci, sai ya fara turanin
dabarar da ya kamata ya yi. Nan take kuwa
dabara ta fado masa ya sauya yanayin fadan ya
fara guje-guje.
Nan fa suka kasa tsere suna ratswa ta cikin
ramukan da ke kan tsaunin da azababben gudu.
Al'amarin da ya matukar bai wa Aljani Maruful
Dauwaz mamaki ke nan bisa ganin yadda
bil'adama ke da tsananin karfin gudu kamar
yadda shi ma yake da azababben gudu a
matsayinsa na Aljani, Aljanin ma wanda babu
mai karfin gudunsa a cikin dukkanin al'ummar
aljanun duniya. Amma da ya tuna cewa aikin
sihiri ne sai hankalinsa ya dawo jikinsa ya kara
zage dantse a cikin tseren gudun da suke yi.
Wani lokacin idan ya ɓace wa Najwar sai kuma
ya dawo masa cikin shammace yana mai kai
masa wawan sara amma duk da hakan ya kasa
samun nasarar koda lakutar jikinsa.
Haka dai suka ci gaba da yakin бuya har izuwa
tsawon lokaci ba su kara yin gaba da gaba ba.
Koda sadauki Najwar ya ga Aljani Maruful
343
TASKARNOVELS.COM.NG
Dauwaz ya fara wahalar da shi har ma yana haki
sai ya fusata ya tsaya cak! a waje daya kuma ya
mayar da takobinsa cikin kufe ya zauna a kasa
dirshan ya harde kafafunsa yana mai runtse
idanunsa.
Ashe Maruful Dauwaz ya makale a saman jikin
rufin tsaunin yana ganin duk abin da yake yi.
Cikin shammace Maruful Dauwaz ya baiyana
tsulum a gaban sadauki Najwar ya kai masa
wawan sara da nufin ya raba kansa gida biyu.
Caraf! Sai sadauki Najwar ya rike takobin
Maruful Dauwaz da hannu daya amma sai
takobin ta sari hannun nasa jini yai tsartuwa
yana mai kwarara uban ihu sakamakon mugun
zafi da ya ji amma duk da hakan bai saki takobin
ba sai yai wuf ya shaki wuyan Aljani Maruful
Dauwaz ya jijjiga shi a sama sannan ya fyada shi
da kasa ya kuma take wuyansa da kafa daya sai
ga shi Aljani Maruful Dauwaz ya soma kakarin
mutuwa.
344
TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'adda sadauki Najwar ya ga Maruful Dauwaz
ya kusan mutuwa sai ya dauke kafarsa daga kan
wuyansa sannan ya nuna shi da hannun hagu,
take wata irin sarkar tsafi mai dauke da wuta ta
kanannade Maruful Dauwaz tana kona shi yana
rusa ihu kamar ransa zai fita.
A lokacin ne Aljani Barukul Masnur ya fashe da
dariyar mugunta saboda jin dadin ganin azabar
da ake yi wa Maruful Dauwaz.
Ba zato ba tsammani sai Najwar ya sake nuna
Maruful Dauwaz da hannu sarkar sihirin da take
kona shi ta ɓace ɓat. Koda ganin haka sai Aljani
Barukul Masnur ya dubi sadauki Najwar cikin
mamaki da fishi ya ce, "Saboda me za ka ki
karasa kashe shi alhalin abin da yakawo mu ke
nan?"
Ya yin da sadauki Najwar ya ji wannan tambaya
sai ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya
345
TASKARNOVELS.COM.NG
murtuke fuska ya ce, "Ba zan kashe shi ba
saboda zai yi mini gagarumin amfani".
Koda jin haka sai Barukul Masnur ya fusata
ainun ya ce, "Idan ba za ka kashe shi ba ni ka ba
ni wuri na kashe shi don kada ka sa fishin Sarki
ya tabbata a kanmu".
Kafin Barukul Masnur ya gama rufe bakinsa tuni
Najwar ya daka masa tsawa sanan ya ce, "Ya kai
Barukul Masnur ka yi sani cewa daga yanzu ka
daina bin umarnin Sarki Nashmir sai dai ka bi
umarnina a matsayina na wanda zai hau
karagar Sarki Nashmir nan da cikar kankanin
lokaci". Ya yin da Aljani Barukul Masnur yaji
wannan batu sai ya cika da tsananin mamaki ya
sake buɗar baki zai ce wani abu sai Najwar ya
tari numfashinsa ya ce, "Ka bi umarnina ko
kuma kai ma yanzun nan na kashe ka. Ka sani
cewa yau shekara talatin da biyar ke nan ina
jiran zuwan wannan rana ga shi kuma ta zo don
haka, babu wani mahaluki da ya isa ya hana ni
amfanarta.
346
TASKARNOVELS.COM.NG
A dai-dai wannan lokaci ne Rahila ta
farfadodaga dogon suman da ta yi. Koda ta bude
idanu ta ga Aljani Maruful Dauwaz kwance
magashiyan a gefe daya duk jikinsa ya cika da
kunar wuta sai zuciyarta ta karaya da tabbatar
da cewa dukkan burinsu ya yanke, kawai sai ta
kurawa sadauki Najwar idanu tana jira kawai ya
zo ya karasa kashe ta.
Ba zato ba tsammani sai ta ga sadauki Najwar ya
dube ta ya yi murmushi sannan ya dubi Aljani
Maruful Dauwaz wanda ke numfashi sama-sama
ya ce da shi, "Ya kai jarumin jarumai, ka yi sani
cewa akan hanyata ta zuwa nan inda kuke na yi
bincike na gano cewa kana da sa'a kuma duk
bala'in da za a yi ba za ka mutu ba kuma kai
kadai ne za ka iya samun nasarar sace Gimbiya
Ramlatul Siyam daga cikin fadar maigidana
Sarki Nashmir.
Bisa wannan dalili ne na yanke shawarar ba zan
kashe ka ba. Ina so ku sani cewa a duniya ba ni
347
TASKARNOVELS.COM.NG
da wani buri wanda ya fi na mallaki karagar
Sarki Nashmir saboda haka yanzu ina son ni da
ku mu hada KARFI DA KARFE mu yaki Sarki
Nashmir mu kawar da shi kun ga ni zan sami
karagata ku kuma za ku sami Ramlatul Siyam.
Batun yawun barcin Sarki Nashmir kuwa,
tuntuni na dade da mallakarsa bari na nuna
muku zahiri".
Nan take sadauki Najwar ya zura hannu a cikin
aljihun wandonsa ya dauko wata 'yar
mitsitsiyar kwalba ya nunawa Maruful Dauwaz
da Rahila.
Koda ganin wannan kwalba sai Aljani Maruful
Dauwaz ya ce, "Ya za a yi mu tabbatar da cewa
abin da ke cikin wannan kwalba yawun barcin
maigidanka ne?"
348
TASKARNOVELS.COM.NG
Najwar ya bushe da dariya ya ce, "Babu yadda
za a yi ku iya tabbatar da hakan face kun je da
kwalbar izuwa gidan tarihi na Birnin Kisra kun
tona kasa kun binne ta kuna yin hakan za ku ga
mashin Galilul Haras ya baiyana a cikin gidan
tarihin. Idan kun amince da bukatata sai mu
zauna anan cikin wannan tsauni har ku gama
jinyar jikinku tsawon kwanakin da ya dace
sannan mu yi shiri mu je a yi yakin karshe
tsakaninmu da Sarki Nashmir domin burina da
naku ya cika."
Lokacin da sadauki Najwar ya zo nan a zancensa
sai Maruful Dauwaz, Rahila da Sarki Laffaru
suka hau kallon junansu suka kasa cewa komai.
Daga can sai Maruful Dauwaz ya yafito Rahila da
Laffaru suka zo wajensa suka yi kus-kus sannan
Laffaru ya dubi sadauki Najwar ya ce, "Mun
amince za mu hada kai domin bukatarmu da
taka ta biya."
Da jin haka sai sadauki Najwar ya bushe da
dariyar farin ciki ya ce, "Tabbas kun yi dabara
mai kyau domin sai da dan gari akan ci gari.
349
TASKARNOVELS.COM.NG
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin sadauki
Najwar da su Aljani Maruful Dauwaz bayan sun
kece raini kowa ya san matsayinsa a fagen
jarumtaka da karfin sihiri.
***
A can kogon Darul Iksina kuwa, lokacin da iskar
bakin wannan karamin yaro ta sumar da Imran
ya baje a kas wanwar kamar ya zama gawa sai
yaron ya cika da tsananin farin ciki. Nan take shi
ma ya rikide izuwa ainahin siffarsa ta aljanu mai
matukar muni da ban tsoro. Kawai sai ya durfafi
kan su Haiman da ke kwance da nufin ya dasa
musu wawa ya cinye su.
A daidai wannan lokaci ne Lumaira da
mahaifiyar Imran suka farfado daga suman da
suka yi. Ai kuwa mahaifiyar Imran tana yin arba
da wannan mummunan Aljani sai ta dimauce
suka kama kwallah ihu. Saura bai fi taku biyu ba
tsakaninsu da Aljanin suka ga an doki Aljanin
350
TASKARNOVELS.COM.NG
yai sama ya maku da jikin bango ya fado kasa.
Suna ďaga kawunansu sama, sai suka ga ashe
Shaharan, Zarina da Shadira ne suka kawo musu
dauki. Mummunan Aljanin na ganin su Shabaran
sai ya mike tsaye ya kwarara uban ihu mai
tsananin firgitarwa ya afka musu aka guntsume
da azababben yaki mai tsanani a tsakaninsa su.
Sai da aka shafe sa'a tara ana bakin gumurzu
tsakanin mummunan Aljanin da su Shaharan ya
Zamana cewa duk su ukun Aljanin yai fata-fata
da jikinsu sun sami raunika da yawa har jiri na
dibarsu suna faduwa. Da kyar da sidin goshi
daya daga a cikinsu ya sami nasarar saran
Aljanin a tsakiyar kansa, bisa tsautsayi.
Nan take Aljanin ya yanke jiki ya fadi kasa
matacce. Faduwarsa ke da wuya sai suma su
Shaharan suka yanke jiki suka baje a kasa ciki
mugun hali kamar ba za su yi rai ba. A sannan
ne Lumaira makauniya ta fara rarrafe tana
shasshafa mutanen da ke kwance a kas tana
neman mijinta Haiman.
351
TASKARNOVELS.COM.NG
Ita kuwa mahaifiyar Imran da ta kasance
gurguwa sai ita ma ta tafi izuwa inda Imran ke
kwance cikin rarrafe tana kuka. Koda ta iso gare
shi ta dube shi ta ga ko motsi ba ya yi sai
hankalinta ya dugunzuma ta rinka jijjiga shi
tana mai cewa, Tashi zaune ya kai dana, ai ba ka
gaya mini cewa za ka mutu ba. Ya za a yi ka tafi
ka bar ni a cikin wannan duniya?"
Haka dai ta yi ta sambatu irin na wadanda suka
sami matsala a cikin kwakwalwarsu.
A wannan lokaci ne Lumaira ta iso kan mijinta
Haiman, ai kuwa tana shafa fuskarsa ta shaida
shi don haka sai ta dago shi zaune ta rungume
shi ta fashe da kuka, ita ma ta kama sambatu.
Haka dai Lumaira da mahaifiyar Imran suka
kasance a cikin halin kuka da bakin ciki har
tsawon rabin sa'a amma su Shaharan ba su
farfado ba.
352
TASKARNOVELS.COM.NG
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai mahaifiyar
Imran ta ji danta ya ja dogon numfashi. Nan take
ta cika da tsananin farin ciki ta daďa kankame
shi a kirjinta ta fara sabon kuka na murna.
Ita kuwa Lumaira da ta tabbatar da cewa
mijinta Haiman ya mutu sai ta saki gawarsa ta
lalubi wuka a jikinsa ta daga sama za ta caka a
cikinta sai ta ji wuf an rike hannunta.
Ba wani ba þne ya rike hannunta face Gimbiya
Zarina. Zarina da Lumaira suka sake fashewa da
kuka tare, Zarina na cewa, "Idan babu ke babu
mijinki wane ne zai bayar da labarin wannan
bakar wuya da muka sha a kasarku?"
Nan dai kowa ya farfado daga suman da ya yi
aka shiga dinke raunika da sa magani.
Ita kuwa Lumaira sai ta sake rungume gawar
mijinta Haiman ta ci gaba da kuka. Al'amarin da
353
TASKARNOVELS.COM.NG
ya dugunzuma hankalin kowa ke nan aka kamu
da tsananin tausayin Lumaira.
Lokacin da Imran ya dawo cikin haiyacinsa
sosai ya yi arba da mahaifiyarsa zaune a
gabansa ta kura masa idanu tana zubar da
hawayen farin ciki sai ya rungume ta ya bushe
da dariyar murna yana mai cewa, "Ya ke
Ummina ki yi sani cewa babu wani bala'i ko
wata masifa da ta isa ta raba ďa da
mahaifiyarsa.
Tun a baya na gaya miki cewa na ji a jikina ba
zan mutu ba kuma ke ma ba za ki mutu ba.
Komai daɗewa sai mun koma gida a raye sai dai
mun yi tafiyar banza mun sha wahalar banza
tun da babu biyan bukata".
Koda Imran yazo nan a zancensa sai ya fashe da
kukan bakin ciki, gabadayan sauran abokan
354
TASKARNOVELS.COM.NG
tafiyar ma sai suka fashe da matsanaicin kuka
aka rasa wanda zai rarrashi wani.
Sai da suka jima a cikin wannan gida suna kuka
da bakin ciki sannan suka fita daga cikinsa.
Anan aka bar gawar jarumi Haiman kuma da
kyar aka banɓare Lumaira daga kan gawar tana
ta ihu da kuka. Komai rashin imanin mutum
idan ya ga yadda Lumaira ta rinka wannan kuka
bisa rabuwa a mijinta dole ne tausayinta ya
kama shi, shi ma ya yi kuka.
Bayan su Shaharan sun fito daga cikin wannan
gida sai suka zazzauna a gaban gidajen bakwai
kowa yai shiru da tagumi har izuwa tsawon
rabin sa'a dayansu bai ce uffan ba.
Daga can sai Shaharan ya dubi Shadira, Zarina,
Lumaira da mahaiflyar Imran ya ce, "Ya ku
abokan tafiya ku tuna cewa da can mu goma sha
daya ne a cikin wannan tafiya, dokina shi ne
cikon na sha biyu, amma yanzu ga shi saura mu
355
TASKARNOVELS.COM.NG
shida kacal a cikin wannan kogo na Darul Iksina.
Ban taɓa zaton zan rayu ba na kawo i yanzu.
Ni kadai ne namijin da ya rage mai sauran
kuzari tunda ga Imran ma ya sami manyan
raunika a jikinsa wadanda sai ya daɗe yana
jinyarsu kafin ya warke ya samu karfin da zai
iya ci gaba da gwagwarmaya.
Yanzu mece ce shawararku? Shin za mu ci gaba
da neman ruwan albarka ne a cikin wannan
kogo ko kuwa za mu zauna nan mu ci gaba da
rayuwa har izuwa sa'adda wata masifar za ta
afko mana ta hallakamu?"
Lokacin da Shaharan ya zo nan a zancensa sai
Shadira ta dago kai ta dube shi ta ce, "Yanzu
mene ne amfanin ruwan albarka a wajena da
wajeu Lumaira?
356
TASKARNOVELS.COM.NG
Na rasa dan uwana Masnur wanda ruwan
albarka zai yi wa magani. Lumaira ta rasa
mijinta wanda take da burin ta ga kalar fuskarsa
bayan ta warke daga cutar makanta. Yanzu ma
idan ta warke ďin ai babu wanda idonta za su
gani ta ji dadi sama masoyinta Haiman."
Koda jin wannan batu sai tausayi ya sake
turnuke kowa aka ci gaba da zubar da hawaye,
kowa ya sake yin shiru har izuwa lokaci mai dan
tsawo sannan Imran ya ce, "Ni ina ganin cewa
mu ci gaba da zama a nan wajen kawai har
izuwa sa'adda za mu gama