Gimbiya Ramlatul Siyam da Maruful
Dauwaz suka ga irin raunikan da wannan Kada
ya yi wa Sarki Laffaru sai suka kamu da
tsananin tausayinsa.
Nan take Ramlatul Siyam ta ruga da gudu izuwa
bakin koramar ta dauko Laffaru ta kai shi cikin
tantinsa. Da kanta ta shiga yi masa magani ta
dinke raunikan da suke bukatar dinki.
Wannan rauni da ke kan cinyarsa kuwa sai
magani ta zuba masa sannan ta nannade shi da
kyalle mai kyau saboda wajen ba shi da kyan
gani.
A sannan ne Sarki Laffaru ya farfado daga dogon
suman da ya yi. Yana bude idanunsa ya yi arba
da Gimbiya Ramlatul Siyam tsugune a kansa
tana yi murmushi kawai sai ta dube shi ta ce,
"Tabbas ka yi Namijin kokari, Akwai alamun
453
TASKARNOVELS.COM.NG
cewa za ka iya kawo sadakina amma fa sai ka yi
matukar jajircewa."
Koda gama fadin haka sai ta mike tsaye ta ce,
"Ga abincin kalacinka nan na ajiye maka, lallai
sai ka yi jinyar kwana bakwai sannan za ka sami
kwarin jikinka har ka iya fita faratar sadakina.
Nan take Ramlatul Siyam ta juya ta fice daga
cikin tantin tana waigen Sarki Laffaru tana yi
masa wani irin murmushi mai kama da na
mugunta.
Al'amarin da ya fusata shi ke nan ya ji kamar ma
ya hakura da aurenta, amma da ya tuna cewa
idan bai aure ta ba duk wahalar nan da ya sha a
baya ta zamo ta banza sai ya ga batun hakura
bai taso ba, koda zai rasa rayuwarsa, don haka
sai ya ji ya karfafi zuciyarsa akan cewa lallai sai
ya kawo sadakin auren Gimbiya Ramlatul Siyam
ta kowane hali ko da kuwa shi ne sanadin
ajalinsa.
454
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da Ramlatul Siyam ta fito daga cikin
tantin Laffaru sai ta hango Aljani Maruful
Dauwaz zaune a can gefe daya ya yi tagumi,
hawaye na zuba daga cikin idanunsa. Cikin
tsananin mamaki Ramlatul Siyam ta karasa gare
shi ta zauna daf da shi ta dube shi ta ce, "Ya kai
Sarkin sadaukan aljanu me ya faru kake tunani
mai zurfi haka har da zubar da hawaye?"
Koda jin wannan tambaya sai Maruful Dauwaz
ya yi ajiyar zuciya sannan ya share hawayensa
ya ce, "Ya ke tauraruwar taurarin mata ta
duniya, ki yi sani cewa, ba komai ne ya sa ni
wannan zubar da hawaye ba face tsananin
takaici bisa halin da muke ciki a rayuwarmu ni
da ku.
Zaman da na yi anan yanzu na tuno da irin
labarin su Lafaru bisa tsananin wahalar da suka
sha a cikin wadannan dazuzzuka guda biyar
kafin su iso kogon Darul Iksina, da yadda
wasunsu suka rasa masoyansu, ga shi kuma shi
455
TASKARNOVELS.COM.NG
kansa wanda ya yaudare su ya jefa su a cikin
wannan bala'i ya tashi a tutar babu, karshe ma
ya rasa rayuwarsa a banza bai cika burinsa ba.
Hakika abin da na fahimta a rayuwa shi ne,
kowane mahaluki ya kan mutu da burinsa ne,
domin buri ba ya yankewa face ajali ya riske shi.
Babu mamaki mu ma nan da burinmu duk za
mu mutu.
Sa'adda Maruful Dauwa ya zo nan a zancensa sai
Gimbiya Ramlatul Siyam ta yi ajiyar zuciya, a
lokacin da idanunta suka ciko da kwallah
sannan ta ce, "Ya kai sadaukin aljanu na duniya
ka yi sani cewa, ita wannan rayuwar babu wani
abu madawwame a cikinta, walau farin ciki ko
bakin ciki. Yanzu dai ka dauki misali a kaina.
Tun da na taso ina karama ban san wata
wahalar duniya ba, kuma ban san kowa ba sai
mahaifina tunda sa'adda uwata ta mutu ban fi
shekara uku ba.
456
TASKARNOVELS.COM.NG
Babu mahalukin da na shaku da shi sama da
ubana amma yau ga shi mutuwa ta raba mu.
Na rasa daular da nake ciki, yau ni ce a cikin daji
ina rayuwa shigen irin ta dabbobi wacce ba ni
da tabbacin tsaro na lafiyata kuma abin da zan
ci ma sai na nema, Komai ni zan yi wa kaina.
Koda jin haka sai Aljani Maruful dauwaz ya
kamu da tsananin tausayin Gimbiya Ramlatul
Siyam har hawaye ya sake zubo masa. Koda
ganin haka sai ita ma Ramlatul Siyam ta fada
kan kirjinsa ta rungume shi kuma ta fashe da
matsanaicin kuka yana mai rarrashinta.
Kamar yadda Ramlatul Siyam ta fadi haka
al'amarin ya kasance, wato sai da Sarki Laffaru
ya kwana bakwai yana jinyar jikinsa sannan ya
samu lafiya gami da kwarin jikinsa.
457
TASKARNOVELS.COM.NG
A ranar kwana na bakwai ne da hantsi Ramlatul
Siyam ta kawo wa Sarki Laffaru takobinta gami
da garkuwarta ta yaki ta mika masa ta ce, "Ga
shi ya kai mijina na gobe, ka yi sani cewa lokaci
ya yi da za ka tafi neman sadakina saboda haka,
daga nan zuwa faduwar rana ina sauraron
dawowarka tare da sadakin nawa sai ka kama
hanya ka nausa cikin daji".
Sa'adda Ramlatul Siyam ta zo nan a zancenta sai
Sarki Laffaru ya ji tsoro ya baibaye shi kuma ya
ji kamar ya ce ya fasa auren nata amma sai ya
daure bai ce kala ba.
Cikin sanyin jiki da alamun karayar zuciya ya
karbi takobin da garkuwar sannan ya ce, "Shin
za ki iya ba ni aron Maruful Dauwaz ya yi mini
rakiya?".
Ramlatul Siyam ta yi murmushi irin na mugunta
ta ce, "Babu mai yi maka rakiya face takobinka
da garkuwarka. Idan har rana ta fadi gari yai
458
TASKARNOVELS.COM.NG
duhu muka ga ba ka dawo ba mun san ka mutu
sai mu jira izuwa ranar da Rahila za ta gaya wa
Maruful Dauwaz inda wasiyyar masoyiyarsa
take sannan mu tashi mu bar wanan daji. Koda
gama wannan jawabi sai Ramlatul Siyam ta juya
ta tafi izuwa cikin tantinta.
Cikin fushi da kunan rai Sarki Laffaru ya juya ya
durfafi cikin daji yana tafe yana huci kai ka ce
zai iya tarwatsa rundunar mayaka guda saboda
kwarjininsa da kirarsa irin ta sadaukai amma ga
wanda ya sani, banza ce ta kori wofi, domin ba
zai iya tsinana komai ba, abu ne ma mawuyaci
ya iya tsira da rayuwarsa.
Sarki Laffaru ya ci gaba da tafiya har ya yi nisa a
cikin daji, duk da cewa ya san cewa ba shi da
wata jarumtaka a jikinsa wacce zai iya kashe
rikakken Zaki har ya ciro kansa amma sai ya ji
dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarsa ko
mutuwa ce ta tare shi ba zai gudu ba saboda ya
fusata ainun kuma zuciyarsa ta kekashe.
459
TASKARNOVELS.COM.NG
Sau tari a rayuwa dakewar zuciya shi ke haifar
da samun nasara ba wai karfin jarumtaka ba.
Sai da Sarki Laffaru ya yini a daji yana farautar
rikakken Zaki amma bai gan shi ba.
Wani abu da ya daure masa kai shi ne, ko daga
nesa idan wadansu mugayen dabbobin suka
hango Laffaru kamar su Damisa, Kura da
sauransu sai ka ga suna komawa da baya ko su
sauya hanya. Abin da bai sani ba shi ne, tsananin
kwarjinin sa ne ya sa dabbobin suke tsorata da
shi.
Lokacin da Laffaru ya gaji da yawo a cikin dajin
har ya ji kishirwa ta kama shi sai ya je karkashin
wata doguwar bishiya ya zauna sannan ya fidda
dan guzurin abincinsa ya fara ci. Abin da bai
sani ba shi ne, ashe akwai abin da ya fito nema
akan wannan bishiya da ya zauna a karkashinta.
460
TASKARNOVELS.COM.NG
Wani murtukeken rikakken Zaki ne kwance
akan bishiyar yana barci. Zakin bai dade da
cinye wata barewa ba da ya make.
Bayan ya ci ya koshi kuma ya je ya sha ruwa sai
ya zo ya hau can saman bishiyar ya kwanta.
Yana kwanciya kuwa sai barci ya sace shi. Da
yake barcin nasa bai yi nisa ba ko munshari bai
fara ba.
Koda Laffaru ya fara cin abincin sai sautin
taunarsa ya sa Zakin ya farka. Ai kuwa yana
lekawa kasa ya yi arba da Laffaru sai ya kwarara
uban gurnani mai tsananin firgitarwa.
Gurnanin nasa ya cika dajin gaba daya da amsa
kuwwa. Hatta Maruful Dauwaz da Ramlatul
Siyam da ke can tsakiyar dajin sai da suka jiyo
wannan ruri na Zaki.
461
TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin tsananin farin ciki Ramlatul Siyam ta daka
tsalle ta fada kan Aljani Maruful Dauwaz tana
mai cewa, "Na sami miji!"
Bisa mamaki sai ta ga Maruful Dauwaz ya
sunkui da kansa kas cikin alamun karayar
zuciya sannan ya ce, "Wannan rurin Zakin da
kika jiyo ba na fitar rai ba ne, ruri ne na
tsoratarwa.
Tabbas Laffaru ya yi MUGUN GAMO da murjejen
Zaki kuma rikakken gaske domin sai zakin da ya
haura shekaru talatin a duniya shi ne yake irin
wannan ruri".
Koda jin wannan batu sai hankalin
Ramlatu!Siyam ya dugunzuma ainun ta ji kamar
ta ruga da gudu izuwa cikin dajin domin ta kai
wa Laffaru dauki amma sai ta dake.
462
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da wannan Zaki ya yi wannan ruri sai
Laffaru ya mike zumbur a matukar tsorace
domin ya gudu, ai kuwa sai Zakin ya duro a
kansa ya turmusheshi a kas suka kama kokawa
suna mirgine- mirgine.
Zakin ya fara kokarin ya kafa hakoransa akan
makoshin Laffaru shi kuwa sai ya dage iya
karfinsa yana gabzawa Zakin naushi suka ci
gaba da turmutsutsu da birgima a kas.
Nan da nan Zakin ya karkarce jikin Laffaru da
faratan hannayensa da na kafafunsa. Albarkacin
mirginawar da suke yi ne shi ma Zakin fuskarsa
ta rinka gwaruwa a jikin duwatsu da bishiyoyi
har ya sami raunika, jini ya cika fuskar tasa.
Ai kuwa suna cikin birgima a kasan ne da
mirginawa suka fado izuwa asan wani rami
wanda ruwan kogi ne ke azababben gudu a
cikinsa. Suna fadowa cikin ruwan sai
kowannensu kansa ya bugu akan duwatsu duk
463
TASKARNOVELS.COM.NG
suka suma. Igiyar ruwa ta tafi da su izuwa can
gaɓar kogi tayi watsi da su.
Sai da iska ta bugesu sannan Laffaru ya fara
farfadowa. Koda ya yunkura domin ya mike
tsaye sai ya ji ya kasa saboda ji ya yi kamar ba
shi da kafar dama.
Koda ya dubi kafar tasa sai ya ga ta karkarce
kuma ta kumbura suntum! Nan take ya gane
cewa karyewa ya yi. Al'amarin da ya matukar
dugunzuma hankalinsa ke nan.
Kwatsam! Sai wannan Zaki ya farfado daga
dogon suman da ya yi. Ai kuwa yana bude
idanunsa ya yi arba da Laffaru zaune a gabansa
sai ya daka tsalle gami da wangame bakinsa zai
afka masa.
Cikin tsananin zafin nama Laffaru ya cisgo wata
'yar karamar bishiya da ke daf da shi yai sama
464
TASKARNOVELS.COM.NG
ya tari Zakin. Bisa sa'a kuwa sai tsinin reshen
bishiyar ya shige cikin hancin Zakin ya bullutso
ta wuyansa.
Suna fadowa kasa shi da Zakin sai Zakin ya
kama matagungun da shure-shuren mutuwa. Sai
da Zakin ya dade yana shure-shure sannan ya
mutu.
Nan fa tashi ya gagari Laffaru. Dole ya ci gaba da
zama a bakin wannan koramar da wanan
karamar bishiya wacce ya kashe Zakin da ita ya
samu ya kakkarya rassanta ya gyara karayar
tasa ya daure kafar a jikin rassan da taimakon
tsumman rigar jikinsa da ya yayyage. Sai da ya
kwana uku yana jinyar kafar tasa a bakin
wannan kogi ya zamanacewa, ba shi da abincin
ci sai danyen naman wannan Zaki da ya kashe,
har ma Zakin ya rube ya fara tsutsa amma a
haka yake cin naman nasa don kada yunwa ta
kashe shi, tunda babup kyastu a wajen wanda
zai kunna wuta ya gasa naman. Ruwan wannan
kogi kuwa shi ne ya zamo ruwan shan sa.
465
TASKARNOVELS.COM.NG
Al'amarin Ramlatul Siyam da Aljani Maruful
Dauwaz kuwa, koda suka ga rana tafadi dare ya
yi Laffaru bai dawo ba sai hankalinsu ya
dugunzuma ainun suka aiyana a ransu cewa ya
mutu.
Koda kwana uku suka shude sai suka kara
sallamawa.
Abin da ya kara dugunzuma hankalinsu shi ne a
wannan rana ne Rahila ta ci gaba da aman jini
ba kakkautawa, ga shi sun diga mata wannan
maganin barci amma ta kasa yin barcin sai
numfashinta ne ke ci gaba da sarkewa.
Koda ganin halin da Rahila ta shiga sai Maruful
Dauwaz ya fara kuka domin ya san cewa
karshen burinsa ya zo.
466
TASKARNOVELS.COM.NG
Kwatsam! ba zato ba tsammani sai suka ga
mutum ya tunkaro su yana dogara ice da
hannunsa na dama, hannunsa na hagu kuwa na
rike da wani katon kan Zaki.
Koda mutumin ya matso kusa sai suka shaida
shi. Ba wani ba ne face Sarki Laffaru.Cikin
tsananin farin ciki Ramlatul Siyam ta mike
zumbur! ta ruga wajen Laffaru ta rungume shi
tana cewa, "Ka zama mijina na zama matarka".
A daidai wannan lokaci ne suka ji Maruful
Dauwaz ya fashe da matsanaicin kuka.
A firgice suka juyo suka dube shi sai suka ga
ashe Rahila ce ta mutu akan hannayensa.
Ai kuwa sai su ma suka durkushe kasa suka
fashe da matsanaicin kuka. Sai da Laffaru,
Ramlatul Siyam da Aljani Maruful Dauwaz suka
467
TASKARNOVELS.COM.NG
shafe sa'a biyar suna kuka da bakin ciki sannan
suka haka kabari suka binne Rahila.
A sannan ne Aljani Maruful Dauwaz ya dago kai
ya dubi Sarki Laffaru da Ramlatul Siyam a
lokacin da hawaye ke zubowa kan kumatunsa
daki- daki ya ce, "Ya ku abokan tafiya, ku yi sani
cewa lokacin rabuwa ta da ku ya yi, tabbas in ba
don ina da sauran alkawari guda daya ba da
yanzu take a gabanku zan kashe kaina.
Alkawarin da ya rage mini kuwa shi ne na
komawa kofar kogon Darul Iksina domin na
gani idan sauran abokan tafiyarku na nan a
raye.
Alfarma daya zan iya yi musu na karanta
wadannan dalasimai na tsafi na bude kofar
kogon.
468
TASKARNOVELS.COM.NG
Lallai idan akwai wanda yai rai a cikinsu a
sannan ne zai iya fitowa ni kuma sai na dauke
shi na maida shi kasarsa".
Koda jin wannan batu sai Laffaru da Ramlatul
Siyam suka kara kamuwa da tsananin tausayin
Aljani Maruful Dauwaz. Ramlatul Siyam ta dube
shi ta ce, "Ya kai Sarkin sadaukai na duniya, ka
yi sani cewa har abada duniya ba za ta manta da
kai ba domin ka yi jarumtakar da babu wanda
ya taɓa irinta.
Kai ne ka fara shiga wajen da ya gagari kowa a
duniya, kuma kai ne ka dauko ni daga cikin
fadar mahaifina wajen da ya fi ko ina karfin
tsaro a duniya. Bai kamata a ce gwarzon mayaki
kamarka ya yi mutuwar banza ba.
Na sani cewa bayan ka je kogon Darul Iksina
babu abin da za ka sake yi face ka kashe kanka.
Ina mai rokonka alfarma guda daya.
469
TASKARNOVELS.COM.NG
Ina son a ranar da na haihu ka zo ka ga 'yata ka
dauke ta da hannayenka masu albarka ka sa
mata albarka domin ina son anan gaba ta yi
alfahari da cewa Sarkin sadaukan duniya ya
dauke ta da hannayensa.
Ina tabbatar maka da cewa sai na sassaka
gunkinka a lokacin da kake dauke da jaririyata
domin ya zamo abin tunawa da kai a gare mu
har abada. Kuma lallai za mu bar tarihinka a
rubuce yadda jama'ar kowanne zamani za su
riske shi kamar yadda aka samu kadan daga
cikin tarihin naka a kundin tarihi na Birnin
Lairuf wato garin su Gimbiya Rahila. Sa'adda
Ramlatul Siyam ta zo nan a zancenta sai hawaye
ya kara zubowa Aljani Maruful Dauwaz ya ce,
"Hakika babu wata alfarma da za ki nema a
wajena na ki yi miki don haka na yi miki
alkawari lallai zan dawo gare ku a ranar da kika
haihu."
Koda gama fadin hakan sai Aljani Maruful
Dauwaz ya buɗe fuka-fukansa ya tashi sama a
hankali yana kallon su Ramlatul Siyam su ma
470
TASKARNOVELS.COM.NG
suna kallonsa suna hawaye shi ma yana hawaye
har ya luluka a cikin gajimare ya ɓace musu da
gani.
Maruful Dauwaz ya ci gaba da tsala gudu a
sararin samaniya ba sassauci yana mai tunkarar
tsibirin da kogon Darul Iksina yake. Ai kuwa a
cikin sa'a biyu da rabi jal ya iso bakin wannan
kogi wanda kogon na Darul Iksina ke kansa.
Aljani Maruful Dauwaz na sauka a bakin gabar
kogin sai ya dubi gabas da yamma, kudu da
arewa ya ga wayam babu wata halitta mai
numfashi a wajen, koda kuwa tsuntsu guda daya
ko kwari, kuma ba a jin sautin komai face na
iskar da ke kadawa a cikin dajin.
Nan take Aljani Maruful Dauwaz ya tuna tsawon
shekarun da ya yi a cikin kogon Darul Iksina
saboda bakin cikin mutuwar masoyiyarsa, ya
tuna cewa shiga yanzu ba shi da kowa a duniya
domin duk zuri'arsa ma sun kare.
471
TASKARNOVELS.COM.NG
Abin da yai masa saura kawai shi ne wannan
wasiyya wacce masoyiyarsa ta bar masa kuma
ga shi wadda ta san inda wasiyyar take ta mutu
sai ya fashe da matsanaicin kuka.
Sai da Aljani Maruful Dauwaz ya shafe rabin sa'a
yana wannan kuka sannan ya dubi kogon Darul
Iksina ya bude bakinsa ya karanta wadannan
dalasimai na tsafi. Faruwar hakan ke da wuya
sai kofar kogon ta bude da kanta.
Aljani Maruful Dauwaz ya kura idanu izuwa
cikin kofar amma sai ya ji shiru bai ji motsin
tafiya ba kuma bai hango kowa ba.
Tsawon kusan wata rabin sa'ar bai ga wani ya
fito ba sai ya fid da rai ya aiyana a ransa cewa
gabadayan abokan tafiyar su Laffaru sun mutu a
cikin kogon na Darul Iksina.
472
TASKARNOVELS.COM.NG
Aljani Maruful Dauwaz ya yunkura domin ya
tashi sama sai kawai ya jiyo sautin tafiya daga
can cikin kogon Darul Iksina.
Cikin tsananin murna ya dakata ya sake zuba
idanu izuwa cikin kogon. Sannu a hankali sautin
tafiyar ya rinka karuwa har ya yi arba da masu
fitowar.
Ba wasu ba ne face Shaharan, Zarina, Shadira,
Imran, Lumaira da mahaifiyar Haiman.
Dukkaninsu da kyar suke tafiya. Zarina ta goyo
mahaifiyar Imran a bayanta, ita kuma Shadira
tana rike da hannun makauniya Lumaira. Imran
da Shaharan kuwa sun rike kafadun junansu
suna dingishi.
Koda su Imran suka hango Aljani
MarufulDauwaz a can bakin gaɓar kogin sai
473
TASKARNOVELS.COM.NG
suka firgita ainun suka ji kamar su koma cikin
kogon na Darul Iksina domin ba su taɓa ganin
Aljani mai matukar kwarjini da ban tsoro ba
kamarsa.
Amma da suka tuna cewa ba su san wanda ya
bude musu kofar kogon ba har suka fito sai suka
aiyana a ransu cewa lallai wannan Aljani ne ya
bude kofar kogon.
Yayin da Aljani Maruful Dauwaz ya fahimci
cewar sun tsorata da shi sai ya dube su cikin
murmushi ya ce, "Ya ku wadannan ZARATAN
JARUMAI ababan alfahari ku yi sani cewa ni ba
wani bane face Aljani Maruful Dauwaz."
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lulluɓe su
Imran suka yafuto Aljani Maruful Dauwaz da
hannayensu suna masu yi masa nuni da ya zo ya
dauke su. Nan take kuwa Aljani Maruful Dauwaz
ya ketare kogin ya sauka a gabansu.
474
TASKARNOVELS.COM.NG
Ba tare da fargabar komai ba su duka suka hau
kan Aljani Maruful Dauwaz suka zauna shi kuma
sai ya bude fuka-fukansa ya tashi da su sama
yana mai tsala gudu a cikin gajimare.
Suna cikin tafiyar ne ya ba su labarin duk abin
da ya faru tsakaninsa da su Laffaru tun daga
lokacin da suka riske shi a cikin a cikin kogon
Darul Iksina kawo izuwa sa'adda ya dauke su
suka tafi izuwa fadar Sarki Nashmir suka yi
wannan yake-yake, har daga karshe Rahila ta
mutu ba tare da ta sanar da shi inda
wasiyyarmasoyiyarsa take ba, da kuma dajin da
ya baro Ramlatul Siyam da Sarki Laffaru inda za
su ci gaba da rayuwarsu ta zaman aure."
Koda Aljani Maruful Dauwaz ya gama bai wa su
Imran labari, sai suka cika da tsananin bakin
ciki da tausayi suka fashe da kuka gabadayansu.
A sannan ne kuma ya yi musu albishir da cewa,
Boka Muzaffar da Sarki Nashmir sun kashe
475
TASKARNOVELS.COM.NG
junansu amma mashin Galilul Haras ya koma
hannun Sharlis. Haka kuma ya tabbatar musu da
cewa daya bayan daya sai ya mayar da
kowannensu kasarsa.
Koda jin wannan labari sai suka kamu da
tsananin farin ciki. Amma da suka tuna cewa
lokacin rabuwarsu ya zo gaba daya sai suka ci
gaba da kuka saboda sabo da shakuwar da suka
yi.
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin Aljani
Maruful Dauwaz, da su jarumi Imran, jaruman
da su ne kadai suka tsira da rayuwersu a cikin
kogon Darul Iksina bayan sun fid da rai ga tsira
da rayuwa.
*****
476
TASKARNOVELS.COM.NG
AL'AMARIN Sharlis kuwa, lokacin da ta ga ta
mallaki mashin Gul Haras sai ta cika da tsananin
farin ciki ta koma Birnin Kufa.
Tana isa gida ta iske danta Sarki Shaddadu a
zaune cikin matukar damuwa saboda rashin
ganinta. Koda ta baiyana a gabansa rike da
mashin Galilul Haras sai ya mike zumbur! Ya
ruga gare ta suka rungume juna cikin tsananin
farin ciki.
Nan take ta ba shi labarin darajar mashin Galilul
Haras ta tabbatar masa da cewa, za ta koya
masa yadda ake sarrafa Mashin amma sai bayan
ya girma ya mallaki hankalin kansa don kada
kuruciya tasa ya je ya