x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - MAZAN JIYA 3

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 68212 words

Category: Adventure Stories

Views 189

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
na gano masifu da
tashin hankali iri-iri. Tarzoma za ta yawaita a
doron kasa, kuma za a yi asarar miliyoyin
rayuka da dukiya. Kun riske ni a cikin bakin ciki
267

TASKARNOVELS.COM.NG
kuma gashi kun sake jefa ni a cikin wani sabon
baki cikin wanda ban san ranar karewarsa ba."

Koda Aljani Maruful Dauwaz yazo nanjawabinsa
sai ya sake fashewa da matsanaicin kaka,
Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalin su
Rahila ke nan suka rasa abin da ke musu dadi a
duniya.

Tsawon dakiku masu yawa dayansu bai ce affan
ba. Daga can sai Rahila ta dago kai ta dubi Aljani
Maruful Dauwaz ta ce, "Haba ya koai GWARZON
MAYAKI mai DAKAKKIYAR ZUCIYA! Shin ka
manta ne cewa in dai akwai rai, akwai buri,
kuma akwai nasara da sa'a? Karfin dantse da
karfin sihiri ba su ne kadai suke tabbatar da
nasara ba, akwai tsananin rabo da tsananin sa'a.
Ina son ka tattaro hankalinka a waje daya, ka
sani cewa idan bala'i ya kunno kai babu wata
hanya da za a iya kawar da shi face a rungume
shi.'

268

TASKARNOVELS.COM.NG
Ka tuna cewa idan ma ba ka fito ba daga cikin
kogon Darul Iksina sai wannan masifa ta faru,
gwara ma da ka fito din wata kila ka iya
taбlbuka wani abu wajen kokarin kawar da ita.

Ka tuna da alkawarin soyayyar da ke tsakaninka
da masoyiyarka marigayiya Rashmin. Shin idan
ka ki karanta wasiyyar da ta bar maka ka yi ma
ta adalci ke nan? Ta mutu da bakin cikin rashin
mallakarka kuma ta mutu da bakin cikin rashin
cika burinta guda daya jal a duniya. Me zai sa ba
za ka sallama rayuwarka ba wajen ganin ka cika
wannan buri nata bayan ranta, domin ka bar
abin tarihi wanda babu wani masoyi da ya taba
yiwa masoyiyarsa a doron kasa".

Lokacin da Rahila ta zo nan a dogon jawabinta
sai jikin Aljani Maruful Dauwaz ya yi sanyi
gabadaya, yai shiru ga barin kuka kuma ya sake
shiga sabon kogin tunani. Daga can sai ya dago
kai ya dubi Rahila ya yi murmushi mai taushi a
gare ta ya ce, "Madallah da jaruma mai dumbin
hikima da hangen nesa.
269

TASKARNOVELS.COM.NG

Ki yi sani cewa wannan jawabi da kika yi mini
na karshe ya zare mini dukkan tsoro daga cikin
zuciyata domin kin tuno mini da wata kalma
wacce mahaifina ya taɓa gaya mini tun ina yaro
karami ban fi shekara bakwai ba.

Kalmar ita ce; "Ya kai dana, duk wuya, duk rintsi
kada ka goyi bayan rashin gaskiya. Ka rike
amana, ka zamo mai cika alkawari. Idan ka yi
haka za ka yi tsawon rai a duniya, kuma
makiyanka ba za su sami nasara akanka ba."

Har yau, har gobe ina amfani da wadannan
kalmomi ba zan taɓa watsi da su ba. Tabbas
yanzu na sami kwarin guiwa kuma ina ji a jikina
kamar ni kadai zan iya tunkarar duk mayakan
duniya muddin ban saɓawa wannan nasiha ta
mahaifina ba

Abinda nake so da ku shi ne, daga yanzu ku je ku
fara shiri, ni kam na gama nawa. Lallai gobe da
270

TASKARNOVELS.COM.NG
sassafe za mu tashi mu durfafi Birnin Hindu
domin aikata wannan gagarumin aiki da ke
gabanmu!!"

Sa'adda Aljani Maruful Dauwaz ya zo nan a
zancensa sai Rahila, Sarki Laffaru da mahaifin
Rahila suka sake cika da tsananin farin ciki.

Nan take suka yi wa Maruful Dauwaz godiya
sannan suka yi masa sallama akan cewa za su
koma cikin gari domin su fara shirye-shiryen
wannan gagarumar tafiya.
Maruful Dauwaz ya yi murmushi ya ce,. "Ma za
ku aikata hakan lallai zaku dawo da safe ku
riske ni cikin jiranku kawai".

Nan take suka mike tsaye suka kama
Dawakansu suka hau suka zabure su da gudu
izuwa cikin gari.

271

TASKARNOVELS.COM.NG
A wannan rana sai da Rahila da Sarki Laffaru
suka kwana suna tanadin kayan yaki iri-iri, kai
ka ce miliyoyin Dakarun yaki za su diba su tafi
da su. Har sai da gari ya fara wayewa ba su
rintsa ba Bayan sun gama tara kayan yakin a
waje guda, sai Sarki Laffaru ya kurawa kayan
yakin idanu. Nan take idanunsa suka ciko da
kwalla. Kafin ya ankara tuni hawaye ya fara
sartu akan kumatunsa. Yayin da Rahila ta gan
shi a cikin wannan hali sai ta cika da tsananin
mamaki kuma hankalinta ya tashi don haka sai
ta mike tsaye ta zo gabansa ta tsugunna tana
mai rike hannunsa ta ce "Ya kai mijina na gobe,
ina dalilin zubar wannan hawaye naka?"

Koda jin wannan tambaya sai Sarki Laffaru ya yi
ajiyar zuciya gami da share hawayensa sannan
ya ce, "Ya ke matata ta gobe, ki yi sani cewa yau
ne ranar farko a rayuwata da na ji na yi nadama
bisa abubuwan da na aikata a baya.

Ki sani cewa da can ni gawurtaccen jarumi ne
kuma SADAUKI, sannan GWARZON MAYAKI
wanda gabadayan Sarakunan da ke nahiyata
272

TASKARNOVELS.COM.NG
suke tsorona kuma suke yi min biyayyar dole,
amma yau ga shi an wayi gari ko Kura ba zan iya
kashewa ba a daji da hannuna.

Ba ni da sauran karfin dantse a jikina kuma ba
ni da sauran karfin sihiri, Sharlis ta raba ni da
duk wadannan abubuwa kuma mugun halina ne
ya jefa ni a cikin wannan yanayi.

Lokacin neman gafara a wajen Sharlis ya wuce a
gare ni, ba ni da sukuni ko sauran kwanciyar
hankali face na auri Gimbiya Ramlatul Siyam
'yar Sarki Nashmir na Birnin Hindu. A sannan ne
karfin damtsena da na sihirina zai dawo amma
duk da haka ba zan iya kare kaina ba daga
sharrin dana SHADDADU face na haifi 'yar da za
ta zamo mashahuriyar BASADAUKIYA.

Yaushe ne wannan rana za ta zo? Yanzu fa
shekaruna sun haura arba'in. Yaushe ne zan
sami kwanciyar hankali da nutsuwa a
rayuwata? Tabbas yanzu ne na gane cewa
273

TASKARNOVELS.COM.NG
zalunci da son zuciya ba sa haifar da komai a
rayuwa face asara da nadama. Yau ga shi na rasa
mulkina, dukiyata da kimata a duniya, kuma na
yi hijirar dole na bar mahaifata ina garari a cikin
duniya ba tare da na san makomata ba."

Koda Sarki Laffaru yazo nan a zancensa sai ya
fashe da matsanaicin kuka. Nan take Rahila ta
kamu da tsananin tausayinsa har itama hawaye
ya zubo ma ta, kawai sai ta rungume shi a karon
farko tun haduwarsu tana mai shafar gashin
kansa kuma tana rarrashinsa. Al'amarin da yasa
Sarki Laffaru jin wani gagarumin farin ciki ya
baibaye shi domin bai taɓa zaton zai sake
samun wani mutum da zai tausaya masa ba a
rayuwarsa.

Bayan gari ya waye sosai sai Rahila da Sarki
Laffaru suka yi gagarumar shigar yaki. Idan
mutum ya dubi Sarki Laffaru a wannan lokaci ya
ga irin shigar da ya yi da kuma irin kirar da
Allah Ya yi masa ta sadaukantaka sai ya dauka
cewa shi kadai zai iya yakar kasa guda. Amma
ga wanda ya san sirrin al'amarin sai dai ya yi
274

TASKARNOVELS.COM.NG
masa dariya, domin huhun-ma'ahun ne, da
wanzuwarsa a filin yaki gwara ma a ajiye dutse
wanda ba shi da rai, wata kila abokin gaba ya yi
tuntuɓe da shi.

Lokacin da su Rahila suka gama kintsawa sai
mahaifinta ya zo gare su domin su yi bankwana.
Tun kafin mahaifin nata ya karaso daf da ita, ita
da shi suka fara zubar da hawaye.

Rahila ta karasa gare shi a guje ta rungume shi
kuma ta fashe da kuka tana mai cewa, "Ya kai
Abbana an zo an raba ni da kai a karo na farko
bisa niyyar cewa zan tafi don cika burin
rayuwata amma ga shi har yanzu burin bai cika
ba. Yanzu ga shi zan sake rabuwa da kai a karo
na biyu. Tabbas wannan ita ce rabuwarmu ta
karshe domin idan na dawo na dwo ke nan ba
za mu sake rabuwa ba. Ka kasance mai yi min
fatan samun sa'a da nasara."

275

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai shi ma ya fashe da
kuka ya ce, "Ya ke 'yata, tabbas zan kasance a
cikin yi miki fatan samun nasara dare da rana
har ki dawo daga wannan gagarumar tafiya. Ki
tuna cewa ni ma dukkan burina ya dogara akan
samun nasararki saboda ke ce kadai 'yata a
duniya. Ba ni da burin da ya fi na ga aurenki
kafin cikar ajalina domin na sami jikoki
wadanda za su yada zuri'ata a doron kasa bayan
rayuwata. Yanzu ga shi ba za ki yi aure ba face
kun sami nasara a wannan gagarumin yaki da za
ku tafi. Babu wanda yake da tabbacin za ku sami
wannan nasara amma in dai da rai, akwai rabo."

Koda jin wannan batu sai Rahila ta sake
kankame mahaifinta a jikinta tana mai daďa
rushewa da kuka kuma ta ji kamar ta fasa
wannan tafiya.

Da kyar Sarki Laffaru ya janye Rahila daga jikin
mahaifinta ya dora ta a kan doki shi ma ya hau
wani dokin sannan wasu Dakaru suka kwashi
dukkan kayan yakinsu suka yi musu rakiya
izuwa bayan gari inda Aljani Maruful Dauwaz ke
276

TASKARNOVELS.COM.NG
jiransu. Da zuwansu kuwa suka iske Aljani
Maruful Dauwa a tsaye cikin wata irin
gagarumar shigar yaki irin wacce ba su taɓa
gani ba a rayuwarsu.

Maruful Dauwaz na sanye cikin waɗansu
bakaken kayan karfe na riga da wando. Hatta
fuka- fukansa ya lulluɓe su da bakin karfen,
sannan a kugunsa akwai wata zabgegiyar takobi
mai tsananin tsawo, fadi da tsinin tsiya, gami da
kaifin gayawa jini na wuce. Ita kadai takobin sai
sheki da walwali take yi tana dallare idanun
wanda duk yai arba da ita.

Sannan a wuyansa ya rataya wata garkuwa
wacce aka yi ta da zallar karfe Lu'u-lu'u fari tas,
ita ma sai sheki da walwali take yi.

Sa'adda Rahila da Sarki Laffaru suka ga Aljani
Maruful Dauwaz a cikin wannan gagarumar
shigar yaki sai suka cika da tsananin mamaki
domin a duk tsawon tafiyar da suka yi tun daga
277

TASKARNOVELS.COM.NG
kogon Darul Iksina ba su ganshi da wadannan
kaya ba.

Abin tambaya anan shi ne, a ina Maruful
Dauwaz ya samo wadannan kayan yaki? Amsar
da suka kasa bai wa kansu ke nan, amma sai
suka kudurce a ransu cewa lallai nan gaba idan
an sami sukuni sai sun yi masa wannan
tambaya.

Ba tare da ɓata wani lokaci ba aka zuba gaba
dayan wadannan kayan yakin akan Aljani
Maruful Dauwaz, sannan Rahila da Sarki Laffaru
suka hau kan Maruful Dauwaz din suma suka
zauna.

Nan take Maruful Dauwaz ya bude fuka- fukansa
ya tashi sama. Kafin kiftawar ido ya luluka a
cikin iska ya fara tsala azababben gudu yana
mai tunkarar hanyar da za ta kai shi Birnin
Hindu.

278

TASKARNOVELS.COM.NG
Duk wannan abu da ya faru tsakanin su Rahila
da Aljani Maruful Dauwaz, Sarki Nashmir na
Birnin Hindu ya gani a cikin madubin TSAFINSA
a lokacin da yake zaune a kasaitacciyar fadarsa
tare da 'yarsa Gimbiya Ramlatul Siyam,
tauraruwar taurarin matan duniya na wannan
zamani.

Gimbiya Ramlatul Siyam ta kasance kyakkyawar
mace ta gaban misali, domin babu wani mutum
da zai iya fasalta ainihin kyawun fuskarta da
kyan dirin jikinta daidai da Yadda Allah Ya ba ta,
sai dai Ya kwatanta daidai iyawarsa. A takaice
dai akan batun kyau sai dai a kira Gimbiya
Ramlatul Siyam Kurun-kus!

Masu bincike da masana tarihi sun tabbatar da
cewa a wannan lokaci babu wata fada daga cikin
dukkan fadodin duniya wacce ta fi ta Sarki
Nashmir girma, ginuwa da katuwa. Domin
komai arzikin BASARAKE da bunkasarsa in dai
ya shiga cikin fadar sai ya zama cikakken dan
kauye wanda bai taɓa shiga Birni ba. Kai! irin
wannan daula da aka tanada a cikin gidan
279

TASKARNOVELS.COM.NG
sarautar kuwa, sai dai a kirashi da "ALJANNAR
DUNIYA.

Lokacin da Sarki Nashmir ya ga su Aljani
Maruful Dauwaz sun taho izuwa fadarsa domin
raba shi da 'yarsa Gimbiya Ramlatul Siyam
kuma su debi yawun barcinsa, sai ya bushe da
mahaukaciyar dariya,gabaďaya daya
Fadawansa ma da ke zaune a fadar sai suka taya
shi dariyar domin sun san cewa abu ne wanda
ba zai taɓa yiwuwa ba.

Ita kuwa Gimbiya Ramlatul Siyam sai hankalinta
ya dugunzuma har kwalla ta ciko a idanunta. Ba
komai ne ya jaza ma ta hakan ba face ta dade
tana yin wani mugun mafarki, kuma a cikin
mafarkin ana nuna ma ta cewar an raba ta da
mahaifinta

Ramlatul Siyam ba ta taɓa gayawa Sarki
Nashmir labarin wannan mafarki nata ba,

280

TASKARNOVELS.COM.NG
domin a rayuwarta idan akwai abin da ta tsana
bai wuce ta ga tashin hankalin mahaifinta ba.

Lokacin da Sarki Nashmir ya ga alamun
tsananin damuwa a fuskar Gimbiya Ramlatul
Siyam sai ya cika da tsananin mamaki ya dube
ta ya ce, "Ya ke 'yata, ina dalilin wannan
damuwa taki bisa wannan al'amari da muke
gani a madubin tsafina? Shin kin manta ne cewa
duk duniya babu wani matsafi kama ta, kuma
babu wani cikin gwarzon mayaki da ya fi ni
shuhura? Na rantse da darajar tsafina da kuma
kaunar da nake yi miki, inda duk mutanen
duniya da aljanun duniya za su yi shirin yaki su
zo nan fadata ba za su iya raba ni da ke ba!"

Ya yin da Gimbiya Ramlatul Siyam ta ji wannan
batu daga bakin mahaifinta sai ta yi ajiyar à
sannan ta ce, "Ya kai Abbana ka sani cewa ba ni
da shakkar komai bisa al'amuranka. Amma ka
sani cewa, masu iya magana sun ce, "Dan Hakin
da ka raina, shi ke tsone maka idanu". Ni dai
abin da nake so da kai shi ne ka dauki matakin
gaggawa akan wadannan makiya namu da suka
281

TASKARNOVELS.COM.NG
taho. Kada ka bari su iso nan. Lallai ka tura
Dakaru su tare su tun akan hanyarsu su
ragargaza su".

Koda jin wannan batu sai Sarki Nashmir ya sake
bushewa da dariya a karo na biyu sannan ya
murtuke fuska ya ce, "Ya ke 'yata ki yi sani cewa
yau shekarata hamsin da hudu ke nan akan
karagar mulki, kuma duk shekara sai na yi yaki
da babbar kasa wacce gagarumin matsafi ke
mulka, amma ba a taɓa ci na da yaki ba. Ban
taba zuwa filin yaki da kaina ba sai sau daya,
sa'adda gaba dayan Sarakaunan duniya suka
hada KARFI DA KARFE domin su kawar da ni.
Ina zuwa filin dagar na ci su da yaki a ciikin sa'a
uku kacal.

A wannan lokaci kina yarinya karama ba ki fi
shekara hudu ba a duniya. Ki yi duba izuwa ga
Madubin tsafina domin ki ga abin da ya faru a
filin yakin a wancan lokaci".

282

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda gama fadin hakan sai Sarki Nashmir ya yi
nuni da hannunsa izuwa ga wani katon farin
Allo na zinare da ke fadar.

Nan take filin yaki ya baiyana cike da abokan
gaba kimanin Dakaru miliyan dubu daya. A gefe
daya kuma Dakarun Sarki Nashmir ne basu fi su
miliyan goma ba.

Koda Dakarun Sarki Nashmir suka ga tsananin
yawan abokan gabarsu sai suka firgice suka juya
da baya suka zaburi dawakansu domin su gudu,
amma sai abokan gabar suka taso su a gaba a
kan dawakai suna kure musu gudu suna rafke
su.

Wohoho! Nan fa aka fara cinikin daukar rai,
ihun mazaje ya cika dodon kunne, sannan jikin
bil'adama ya rinka shawagi a sararin sama, jini
kuwa ya dinga feshi da fantsama yana malala a
kas kai ka ce kogin jini ne ya ɓalle.

283

TASKARNOVELS.COM.NG
Kafin cikar sa'a guda an kashe sama da kaso
biyu cikin kaso uku na Dakarun Sarki Nashmir.

Ana tsaka da wannan masifaffen yaki ne aka ga
wata dunkulalliyar guguwa ta fado daga can
kololuwar sama. Nan take ta tarwatsa dukkan
wadannan abokan gaba. Duk wanda yake bisa
kan doki sai da ya fado kasa, wanda ke kasa
kuwa sai da ya baje.Nan take wannan
dunkulalliyar guguwa ta rikide ta zama Sarki
Nashmir, sai ga shi ya baiyana a cikin
gagarumar shigar yaki ta farin sulke sama da
kasa yana rike da wadansu tagwayen takubba
sihirtattu masu matukar kwarjini da ban tsoro.

Sarki Nashmir ya kasance gabjejen katon
mutum, ga tsawo kuma ga kauri tamkar
Basamude. Gabadayan jikinsa a murde yake
kamar curin nakiya, kuma cike yake da jijiyoyi
da kwanji.

284

TASKARNOVELS.COM.NG
Kaico! Kallo daya mutum zai yi masa ya san
cewa yana da karfin Allah Ya isa!

Koda baiyanar Sarki Nashmir sai gabadayan
wadannan Dakarun abokan gaba kimanin su
miliyan dubu daya suka yi dauki kansa shi
kadai.

Kaico! Tsautsayi ba a sa masa rana. Ita kuwa
masifa idan ta taho babu hijabin da ya isa ya
tare ta. Koda Sarki Nashmir ya ga wadannan
miliyoyin Dakaru sun rugo izuwa kansa sai shi
ma ya falfala da azababben gudu na gaban
kwatance izuwa kansu ya ratsa ta cikinsu da
karfin tsiya ya hau saransu da sukarsu. Sai dai
ka ga yana tsarga gangar jikin bil'adama tamkar
takardu yake kekketawa. Duk inda ya sa
gabansa maza faduwa suke tamkar ana sassabe
a gona. Kafin cikar sa'a uku cif gabadayan filin
yakin ya cika da gawarwakin abokan gabar
babu dayansu a raye.Kai ba ma su ba hatta
dawakansu sun zama gawarwaki domin Sarki
Nashmir ya daddatsa su kai ka ce mahauta ce.
285

TASKARNOVELS.COM.NG

Filin yakin ya yi tsit! Tamkar wani mahaluki bai
taɓa wanzuwa ba a wajen, in ban da sautin iska
da ke kadawa babu abin da kunne ke iya ji.

A dai-dai wannan lokaci ne ragowar Dakarun
Sarki Nashmir da suka tsere suka fara dawowa
filin yakin. Koda suka ga gagarumin aikin da
Sarki Nashmir ya yi sai dukkaninsu suka zube
kasa a gabansa suna masu yi masa sujjada.

Nan take Sarki Nashmir ya rikide ya zama
wannan gagarumar guguwar, Guguwar ta yi
sama ta ɓace ɓat a cikin gajimare.

Lokacin da Gimbiya Ramlatul Siyam ta gama
ganin wannan al'amari a cikin madubin tsafin
mahaifinta sai ta ji hankalinta ya kwanta
matuka, ba ta san sa'adda murmushi ya kwace
ma ta ba.

286

TASKARNOVELS.COM.NG
Ta dubi Sarki Nashmir ta ce, "Tabbas yanzu na
gamsu cewa babu wani mahaluki da zai iya
cinka da yaki. Amma dai duk da haka ina son ka
tura Dakaru su tari wadannan abokan gaba
namu tun kafin su iso domin mu ga irin
jarumtakarsu da karfin sihirinsu".

Ya yin da Sarki Nashmir ya ji wannan batu sai ya
yi murmushi ya ce, "Ya ke 'yata ki yi sani cewa,
babu wata alfarma da za ki nema awajena na ki
yi miki ita. Saboda haka lallai zan yi yadda kika
bukata.

Nan take Sarki Nashmir ya kirawo waɗansu
zakwakuran mayakansa su uku wadanda ya
yarda da jarumtakarsu, kuma shi da kansa ya
tsuma su da tsumin tsafinsa ya umarce su da su
hau kan daya daga cikin manyan hadiman
aljanunsa su je su tari su Aljani Maruful Dauwaz
tun gabannin su iso Birnin Hindu. kuma su
tabbatar da cewa sun yanko kan Aljani Maruful
Dauwaz da na abokan tafiyarsa sun zo da su".

287

TASKARNOVELS.COM.NG
Nan take mayakan uku suka yi shiri suka hau
kan wani Aljani wai shi SHARKAMUZA ya tashi
da su sama ya luluka a cikin gajimare.

Aljani SHARKAMUZA ya kasance narkeken kato
wanda girmansa ya ninka na Aljani Maruful
Dauwaz sau uku.

A bangaren kwarjini da kira ta sadaukantaka
kuwa, Aljani Maruful Dauwaz jariri ne akansa.

Su kuwa wadannan zakwakuran mayaka guda
uku da aka tura su kashe su Aljani Maruful
Dauwaz sun kasance tagwayen sadaukai, domin
uwarsu daya ubansu daya, kuma rana daya aka
haife su.

Tsawonsu da kaurinsu yazo daidai da na Sarki
Nashmir, kawai abin da ya fi su shi ne
sadaukantaka da karfin sihiri. ,

288

TASKARNOVELS.COM.NG

Ana kiran wadannan tagwayen sadaukai da
suna, SHARMAL, ZARHUF da HAZWAN.
Shi kansa Sarki Nashmir akwai wata rana da ya
umarci su Sharmal da su hada karfi su ukun su
yake shi domin ya jarraba iyakar jarumtakarsu.

Ai kuwa da ya fafata da su sai da ya sha bakar
wuya, kuma sai da suka yi masa rauni sau biyu.
Da kyar ya sami nasarar bazar da su kas ya
sumar da su

Tun daga wannan ranar ya kara musu matsayi
babba a cikin Dakarunsa babu wanda ya fi su
face Sarkin yakinsa wanda ake kira RAJWAN
BIN SAMMAR.

Sarkin yaki Rajwan ya kasance barden jarumi,
FASA TARO mai TARWATSA MAZA.

289

TASKARNOVELS.COM.NG
Ya kasance gawurtaccen Sadauki wanda
jarumtakarsa kiris ya rage ta zo dai-dai da ta
Sarki Nashmir. Domin kuwa a ranar da suka
gwada 'yar kashi sai da suka kusan yin RAGAS.

Da kyar da sidin goshi Sarki Nashmir ya sami
rinjaye akan Rajwan. In ba don ma ya nuna
masa kwarewa da sanin makama ba da ba zai yi
nasara a kan shi ba.
Gabadaya mutane Birnin Hindu babu mutumin
da suke tsoro sama da Sarkin yaki
Rajwan domin ya fi Sarki Nashmir rashin imani
da zalunci, sannan kuma shi ne wazirin Sarki
Nashmir don haka ana tsoron kada Sarki
Nashmir ya riga Rajwan mutuwa, muddin hakan
ta faru sai Rajwan ya dora kansa akan karagar
mulki da karfin tsiya, ko ana so ko
End Ads