x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 21 - MAZAN JIYA 3

  • 60001 words
  • 63000 words
  • Out of 68212 words

Category: Adventure Stories

Views 190

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
wani ba ne ke rike da wannan mashi ba face
abokin tafiyarku wanda ya yaudare ku ya jefa
rayuwarku a cikin TSAKA MAI WUYA, Kunci da
bakin ciki mara tukewa, wato Boka Muzuffar.

Ku yi duba izuwa jikin wancan bango yanzu zan
nuna muku abin da ya wakana."Koda gama
fadin haka sai Ramlatul Siyam ta yi nuni da
hannunta izuwa ga jikin bangon Falon wanda ke
Kudu. Nan take suka ga Boka Muzaffar a cikin
dakin Halwar tsafinsa ya dukufa yana ta nazari.
428

TASKARNOVELS.COM.NG

Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka ga Sarki
Nashmir ya diro cikin dakin daga sama
kamar haske. Kai tsaye Nashmir ya durfafi inda
Boka Muzaffar ya jingine mashin GALILUL
HARAS da nufin ya dauka. Har ya kai hannunsa i
zuwa kan mashin zai dauka ke nan sai ya ji an
doki fuskarsa. Yai tsalle sama ya gwaru da
bangon dakin ya fado kasa.

Cikin hanzari ya mike tsaye zumbur! Yana mai
zare takobinsa sai yai arba da Boka Muzaffar
tsaye a gabansa shi ma ya zare tasa takobin.

Muzaffar ya dubi Nashmir a fusace sannan ya
daka masa tsawa ya ce, Kai tsohon azzalumi ka
yi sani cewa yau shekara talatin da biyar ke nan
ina gwagwarmaya akan na mallaki wannan
mashin ban same shi ba sai yanzu. Kai ma kuma
ka dade kana nemansa kuma ka kasa zuwa
kogon Darul Iksina ka dauko shi. Yanzu da na
gama shan wahalata shi ne kai kuma kake son
429

TASKARNOVELS.COM.NG
ka same shi a banza? To ka sani cewa Karyarka
ta sha karya ya kai Nashmir. Ina tabbatar maka
da cewa, ka kawo kanka GIDAN AJALI, sai dai
gawarka ta fita daga nan".

Sa'adda Muzaffar ya zo nan a zanensa sai Sarki
Nashmir ya takarkare ya bushe da
mahaukaciyar dariya sannan ya murtuke
fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa
ya ce, "Ai kuwa idan har ban sami nasarar raba
ka da wannan mashi ba sai dai a dauki gawa
guda biyu, ni da kai babu wanda zai fita daga
cikin wannan daki a raye."

Kafin Nashmir ya gama rufe bakinsa tuni Boka
Muzaffar ya afka masa sun kacame da
azababben yaki, suka wanzu suna masu kai wa
junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama,
juriya da bajinta.

Sai da Muzaffar da Nashmir suka shafe kwana
uku suna wannan masifaffen yaki, ya zamana
430

TASKARNOVELS.COM.NG
cewa kowannensu ya yi amfani da dukkan
karfin sihirinsa da karfin damtsensa amma aka
rasa wanda zai samu nasarar kashe wani.

A karshe suka yiwa juna fata-fata, har ya
zamana cewa ko ina a jikinsu raunika n. Lokaci
guda suka yanke jiki suka fadi kasa matattu,
dayansu bai sake shurawa ba.

Faruwar hakan ke dawuya sai ga wani haske ya
baiyana a cikin dakin. Nan take hasken ya rikiďe
ya zama Sharlis.

Sharlis ta je inda aka jingine Mashin Galilul
Haras ta dauki mashin ta daga shi sama sai ta
kyalkyale da dariyar farin ciki ta ce, "Na tsinci
dami akala! Tabbas yanzu na zama Sarauniyar
sadaukai ta duniya.

431

TASKARNOVELS.COM.NG
Da sannu zan dauki gagarumar fansa akan
babban makiyina Sarki Laffaru sannan na
mallaki wannan duniya gaba dayanta.

Da wannan mashi a hannuna, babu wani
sadauki ko matsafi da zai gagare ni. Babu wani
wuri da zai yi mini wuyar zuwa. Komai yawan
rundunar mayaka sai na tarwatsa su, komai
nisan tafiya sai na ketata. Gama fadin hakan ke
da wuya sai ta shafi wani ɓangare na jikin
mashin na Galilul Haras.

Nan take ita da mashin suka zama wani irin
gagarumin haske suka cilla sama ta cikin rufin
dakin. Kafin kiftawar ido sun kule a cikin
gajimare sun ɓace ɓat.

Koda gama ganin wannan al'amari sai Gimbiya
Ramlatul Siyam ta fashe da matsanaicin kuka,
tana mai duban su Aljani Maruful Dauwaz ta ce,
"Kun ga yadda karshen mahaifina ya kasance,

432

TASKARNOVELS.COM.NG
shi ya sa na gaya muku cewa ba zan sake
saduwa da shi ba.

Lokacin da Sarki Laffaru ya ga wannanal'amari
sai hankalinsa ya dugunzuma ainun ya dubi
Ramlatul Siyam cikin tsananin tsoro ya ce
"Yanzu ta yaya zan tsira daga sharrin Sharlis
tunda ga shi ta mallaki mashin Galilul Haras,
wannan yana nufin ke nan za mu iya fadawa
hannunta a ko yaushe ta ci gaba da tsarona har
izuwa lokacin da za ta cika burinta a kaina, koda
kuwa na aure ki mun haifi 'yar da za ta kare ni?

Koda jin wannan batu sai Ramlatul Siyam ta yi
murmushi ta ce, "Ba haka ba ne, akwai inda za
mu je mu yi rayuwa babu abin da zai same mu
daga yanzu har izuwa tsawon shekara goma sha
takwas, a sannan ne Shaddadu dan Sharlis ya
cika shekara ashirin da daya a duniya, kuma
mahaifiyarsa ta mallaka masa mashin Galilul
Haras a sannan ne zai bazama farautata cikin
duniya.

433

TASKARNOVELS.COM.NG
A sannan ne kuma 'yarmu za ta cika shekara
goma sha takwas a duniya ta zama gagarumar
BASADAUKIYA kuma MAYAKIYA, wacce za ta
kare ka daga sharrin Shaddadu.

Amma fa ka sani cewa duk ranar da Shaddadu
ya yi arba da kai babu 'yarmu a kusa taka ta
kare, don sai Shaddadu ya kama ka ya tafi da kai
izuwa ga mahaifiyarsa. Ma'ana sai ya kai ka har
can Birnin Kufa ya wulakanta ka sannan ya yi
maka kisan gilla.

Ya yin da Ramlatul Siyam ta zo nan a zancenta
sai hankalin Sarki laffaru ya kara dugunzuma
ainun fiye da ko yaushe, ya dubi Gimbiya cikin
tsananin damuwa ya ce, "Ashe dai tashin
hankali da rashin kwanciyar hankali bai kare
mini ba? Yanzu ta yaya zan magance wannan
fargaba?"

Koda jin wannan tambaya sai Ramlatul Siyam ta
yi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Hanya daya ce
434

TASKARNOVELS.COM.NG
maganin wannan fargaba, sai dai ita ma 'yar
tamu ta fita farautar Shaddadu kamar yadda shi
ma zai fito farautarka, ta raba shi da mashin
Galilul Haras ta hanyar yaudara ba ta hanyar
karfi ba.

Da zarar ta raba shi da wannan mashi shi ke nan
ta karya lagonsa ba zai taba samun damar kama
ka ba bare ya iya hallaka ka."

Lokacin da Ramlatul Siyam ta zo daidai nan a
zancenta sai suka ji Rahila ta turnuke da tari har
tana aman jini.

Al'amarin da ya kara dugunzuma hankalin
Aljani Maruful Dauwaz ke nan, ya zo kanta ya
ciccibe ta ya tashe ta zaune yana mai zub da
hawaye, bai san sa'adda ya kama sambatu ba
yana cewa, "Ya ke Rahila shin kin manta da
alkawarın da ke tsakaninmu ne?Ga shi na
taimake ki na biya miki bukatarki, idan kika
mutu yanzu ba ki yi mini adalci ba. Ki gaya mini
435

TASKARNOVELS.COM.NG
inda kika boye wasiyyar masoyiyata kafin ki
tafi!"

Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ga Rahila
ta bude idanunta da kyar a hankali sannan ta
bude bakinta yana karkarwa domin ta yi
magana, amma sai ta kasa.

Koda ganin haka sai Ramlatul Siyam ta kwalawa
wani Likitanta kira ya rugo ya zo ya bai wa
Rahila wani magani.

Tana gama hadiye ruwan maganin sai barci ya
dauke ta. A sannan ne Likitan yai ajiyar zuciya
ya mikawa Ramlatul Siyam kwalbar maganin ya
ce, "Dole ne a rinka bai wa Rahila wannan
magani bayan kowacce sa'a uku idan ba haka ba
kuwa za ta ci gaba da aman jini wanda zai iya
zama sanadin ajalinta, kuma digo daya na
maganin za a dinga disawa a cikin bakinta. Idan
aka bata sama da digo daya shi ma zai iya yi
mata illah."
436

TASKARNOVELS.COM.NG

Nan take Ramlatul Siyam ta dubi Sarki Laffaru
da Maruful Dauwaz ta ce, "Yanzu sai ku tashi mu
yi shiri mu bar wannan Birni na Hindu domin
idan muka ci gaba da zama a nan, nan da tsawon
kwana daya rak Sharlis za ta gano inda muke ta
zo a cikin dakiku kadan ta hallaka mu ta kama
Laffaru ta tafi da shi.

Koda gama fadin hakan sai Maruful Dauwaz ya
ce, "To yanzu ina ne inda za mu je mu yi jinyar
Rahila har ta warke ta cika mini alkawarina
kuma ke da Laffaru ku yi aurenku".

Ramlatul Siyam ta ce, "Babu inda za mu je mu
tsira face wani daji da ake kira Rauful Mausur.

Shi dai wannan daji na Rauful Mausur yana
tsakanin Birnin Kisra da Birnin Istanbul.
In dai akwai sihirin tsafi a jikin mutum bai isa ya
shiga cikin dajin Rauful Masnur ba face ya zama
437

TASKARNOVELS.COM.NG
gawa saboda haka a nan ne kadai za mu iya
zama mu yi rayuwarmu a cikin kwanciyar
hankali.

Fatana shi ne Rahila ta sami lafiyar da za ta iya
budar baki ta gaya mini inda wasiyyar
masoyiyarka take kafin rai ya yi halinsa".

Koda gama fadin hakan sai Ramlatul Siyam ta
mike tsaye ta sa aka debo musu kayayyaki da
guzuri ana dorawa akan Aljani Maruful Dauwaz.

A wannan lokaci ne Maruful Dauwaz ya fada
cikin kogon tunani yana mai cewa a ransa, "Inda
ina da tabbacin cewa Rahila ba za ta sami lafiyar
da za ta iya yi min magana ba da tabbas yanzu
zan kashe kaina na huta da bakin cikin rayuwar
duniya domin ban ga amfanin rayuwar tawa ba.
Yana cikin wannan tunani ne aka gama shiryeshiryen tafiya.

438

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Ramlatul Siyam ta zo yin bankwana da
jama'arta sai ta fashe da kuka, suma suka fashe
da kukan saboda shakuwa.

A lokacin ne Ramlatul Siyam ta tuno da
mahaifinta Sarki Nashmir kuma ta tuno da irin
tsananin kaunar da ya nuna mata gami da gata,
sai ta je gaban wani gunkinsa da aka sassaka
mai matukar kama da shi wanda ke tsaye a
tsakiyar falonta ta rungume gunkin ta sake
fashewa da matsanaicin kuka.

Da kyar da sidin goshi Sarki Laffaru ya ɓanɓare
Ramlatul Siyam daga jikin gunkin sannan ya ja
ta suka je suka hau kan Maruful Dauwaz suka
zauna.

Dama an shimfide Rahila a kan Maruful Dauwaz
a gefe daya kuma an lulluɓe jikinta duka da
mayafi fuskarta ce kadai a bude. Nan take Aljani
Maruful Dauwaz ya bude fuka-fukansa ya tashi
sama a hankali. Ramlatul Siyam tana dagawa
439

TASKARNOVELS.COM.NG
jama'arta hannu, su ma suna daga mata kowa na
zub da hawaye har Maruful Dauwaz ya kule a
cikin sararin samaniya.....

Aljani Maruful Dauwaz ya wanzu yana mai tsala
gudu a cikin sararin samaniya babu sassauci har
sai da ya shafe tafiyar sa'a biyu da rabi cif
sannan ya iso dajin Rauful Masnur ya sauka a
tsakiyar dajin.

Daji ne mai dauke da ni'ima sosai akwai
kyawawan bishiyoyi, duwatsu da dabbobin daji
iri-iri, babu kalar da babu masu hadari da
marasa hadari.

Koda saukar Maruful Dauwaz a cikin wannan
daji sai shi da Ramlatul Siyam suka kamu da
tsananin sha'awar dajin shi kuwa Sarki Laffaru
sai ya ji ya kamu da tsananin tsoro musamman
da ya jiyo kukan manyan namun daji daga nesa
suna gurnani. Koda Ramlatul Siyam ta fahimci
440

TASKARNOVELS.COM.NG
halin da Sarki Laffaru ke ciki sai ta bushe da
dariya, al'amarin da ya bai wa Maruful Dauwaz
da Laffaru mamaki ke nan.

Maruful Dauwaz ya dube ta ya ce, "Ya ke
wannan Sarauniyar kyawawan matan duniya
ina dalilin wannan dariya taki?".

Ramlatul Siyam ta yi shiru ga barin dariya
sannan ta ce, "Gani na yi mijin da zan aura rago
ne kuma matsoraci ga shi ba zan taba yarda ya
kusance ni ba face ya kawo mini kan rikakken
Zaki a matsayin sadakina".

Koda jin wannan batu sai hankalin Laffaru ya
dugunzuma ainun ya ce, "Haba dai! yaya ni da
na rasa dukkan karfin dantsena za ki ce sai na je
na kashe zaki na yanko kansa?"

Da jin haka sai Ramlatul Siyam ta murtuke fuska
ta ce, "Ai kuwa ashe ba za ka taɓa zama mijina
441

TASKARNOVELS.COM.NG
ba. Ai mu a kasarmu wannan ita ce al'adarmu ta
aure. Kafin namiji ya kusanci matarsa sai ta zabi
irin jarumtakar da take son ya yi, ya yi ta.

Inda za mu tsufa a haka a matsayinka na mijina
ba zan taɓa yarda da kai ba sai ka zo mini da kan
zakin da ka kashe da hannunka saboda haka, ka
shirya daga gobe da safe za ka fara shiga cikin
wannan daji domin farautar rikakken Zaki.

Ka sani cewa idan ka kawo mini kan yaron Zaki
ka yi wahalar banza."

Koda gama fadar hakan sai Ramlatul Siyam ta
dauki tanti daga kan Aljani Maruful Dauwaz ta
fara kokarin kafa shi.

Shi kuwa Sarki Laffaru sai ya koma gefe daya ya
yi tagumi yana tunanin wannan sabon al'amarin
da Ramlatul Siyam ta zo masa da shi.

442

TASKARNOVELS.COM.NG

Nan take ya ji ya tsani kansa kuma nadama ta zo
masa ya ce a zuciyarsa, "In da ya san cewa zai
shiga cikin wannan tsananin tashin hankali da
tun farko bai yarda ya baro kasarsa ba ya sha
wannan bakar wahala da fuskantar tashin
hankali, da gwara ma ya kashe kansa ya huta da
takaici da bakin ciki.

Har Ramlatul Siyam ta gama kafa tantin ta
dauko Rahila ta shigar da ita cikin tantin ta
kwantar da ita, sannan ta debi kayayyakinta ta
kai ciki ta zube, Laffaru bai daina tunani ba.

Yana cikin tunanin ne Ramlatul Siyam ta fito
daga cikin tantinta ta dube shi ta ce, "Ai sai ka
tashi ka yi kokarin kafa naka tantin domin ba zai
yiyu ba na kwanta a waje daya tare da kai ba
face ka kawo mini sadakina".

Tana gama fadin hake ta juya ta koma cikin
tantinta. Shi kuwa Sarki Laffaru sai hankalinsa
443

TASKARNOVELS.COM.NG
ya kara dugunzuma ainun ya rasa abin da ke
masa dadi a duniya.

Kawai sai ya ji Maruful Dauwaz ya bushe da
dariya. Al'amarin da ya fusata shi ke nan ya
dakawa Maruful Dauwaz harara ya ce, "Kai
kuma mene ne ya ba ka dariya?"

Maruful Dauwaz ya ce, "Gani na yi za ka ba mu
kunya a matsayinka na ďa namiji.

Ka tuna cewa Ramlatul Siyam yarinya ce
kankanuwa a kanka, tunda shekarunka sun
ninka nata.

Ka tuna cewa manyan mazajen duniya sun mutu
da bakin cikin rashin mallakar Gimbiya
Ramlatul Siyam, amma kai ga shi yanzu za ka
mallake ta a karon banza saboda kawai ta ce ka
kawo kan rikakken Zaki a matsayin sadakinta
shi ne za ka karaya?
444

TASKARNOVELS.COM.NG

To ka sani cewa ba ka da wani zabi wanda ya fi
ka kawo wannan sadakin in ba haka ba kuwa,
har abada ka rasa ta, kuma sai makiyanka sun
sami nasarar hallaka ka a cikin kankanin lokaci.

Ina tabbatar maka da cewa ni ma ba zan
taimaka maka da komai ba akan samo wannan
sadakin domin idan har ka kasa samo sadakin
da kanka 'yar da za ku haifa ba za ta zamo
gagarumar jaruma ba saboda ba a samu sadauki
sai daga tsatson sadaukai.

Duk da cewar kai GWARZON SADAUKI ne ada,
ai a yanzu ka zama rago, kuma sadaukantakarka
ba za ta dawo ba sai bayan ka haifi wannan 'ya
taka har ta girma".

Koda gama fadin hakan sai Aljani Maruful
dauwaz ya ɓace ɓat, ya sake baiyana a bakin
tantin Gimbiya Ramlatul Siyam ya yi gyaran
murya. Nan take Ramlatul Siyam ta fito daga
445

TASKARNOVELS.COM.NG
cikin tantin ta dubi Maruful Dauwaz ta ce, "Me
kake da bukata?"

Maruful Dauwaz ya risina cikin biyayya ya ce,
"Ina son na ji lafiyar Gimbiya Rahila ne domin
na san matsayin da nake ciki".

Koda jin wannan batu sai Ramlatul Siyam ta yi
ajiyar zuciya sannan ta ce, "Rahila ta farka daga
barci har ma na ba ta ruwa ta sha, amma fa har
yanzu ba ta iya bude bakinta ba bare ma ta yi
magana, kuma idanunta ma da kyar take iya
bude su. Yanzu dai na sake ba ta wannan digon
magani ta sha ta koma barci. Ka kara hakuri
wata kila nan da kwana uku ta sami sauki sosai
har ta iya magana".

Koda Maruful Dauwaz ya ji haka sai hankalinsa
ya dan kwanta ya yi godiya ga Ramlatul Siyam
kuma ya roke ta akan ta ci gaba da kula da
Rahila har izuwa sa'adda za ta sami lafiya.
Gimbiya Ramlatul Siyam tayi masa alkawari
446

TASKARNOVELS.COM.NG
cewar lallai za ta bata kyakkyawar kulawa
iyakar yadda ya kamata.

****

Ba tare da ɓata lokaci ba Sarki Laffaru ya mike
tsaye ya fara kafa nasa tantin. Bisa mamaki sai
ya ji ya sami dan kwarin jikinsa amma bai ji
rabin karfin dantsensa ba irin na da ba.vNan
take farin ciki ya lullube shi har ya fara tunanin
cewa zai iya shiga dajin ya yi farautar rikakken
Zaki.

Haka dai ya ci gaba da aikin kafa tantin nasa
cikin murna har ya kammala sannan ya shiga
ciki ya yi kwanciyarsa ya ci gaba da tunanin zuci
har barci ya sace shi bai sani ba.

Ya yin da dare ya soma yi sosai sai mugayen
dabbobin daji suka fara zarya a kusa da inda
tantin su Ramlatul Siyam yake.
447

TASKARNOVELS.COM.NG

Amma duk dabbar da ta yi arba da Aljani
Maruful Dauwaz sai ka ga ta firgita ta koma da
baya guje izuwa cikin daji tana koke-koke. Wato
dai sai Aljani Maruful Dauwaz ya bayar da
cikakken tsaro a a gare su.

****
Kashe gari da safe Sarki Laffaru ya farka daga
barci sai ya mike zumbur! Ya fito daga cikin
tantinsa domin ya ga lafiyar abokan tafiyar tasa
yana fitowa sai ya iske Ramlatul Siyam a zaune
tana buda baki. Aljani Maruful Dauwaz na zaune
a gefe daya kusa da ita cikin nishadi suna ta hira
har da dariya. Nan take Laffaru ya gangara
izuwa cikin wata korama da ke bayan inda suka
kafa tantunansu ya tube kayansa ya fada cikin
koramar domin ya yi wanka.

Kash! Rashin sani yafi dare duhu. Ashe akwai
wata katuwar Kada a cikin wannan korama bai
sani ba. Ai kuwa yana cikin wanka sai ya ga
448

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan Kada ta taso masa. Ya yunkura domin
ya ruga waje daga cikin koramar sai ya ga ai ba
zai iya gujewa Kadar ba.

Cikin tsananin tsoro Sarki Laffaru ya kurma
uban ihu. Ai kuwa sai Ramlatul Siyam da Aljani
Maruful Dauwaz suka rugo izuwa bakin
koramar. Da isowarsu suka iske katuwar Kadar
ta wangame bakinta za ta hadiye Sarki Laffaru.

Cikin zafin nama Laffaru ya goce bai san sa'adda
ya rungumi Kadar ba suka fara kokawa a cikin
ruwan tana danna shi kasa, shi ma yana kokarin
tasowa sama, kuma yana ci gaba da ihu gami da
kiran taimako.

Har Maruful Dauwaz ya yunkura zai kai masa
dauki sai Ramlatul Siyam ta hana shi ta ce, "A
haka ne zai iya samo sadakina? Wannan fa kada
ce ba rikakken Zaki ba.Mu kyale shi kawai ya
fara bai wa kansa horo tun kafin ya yi arba da
rikakken Zaki.
449

TASKARNOVELS.COM.NG

Nan fa aka ci gaba da gumurzu tsakanin wannan
kada da Sarki Laffaru a cikin wannan ruwa.
Sarki Laffaru ya ci gaba da rukunkume Kadar
iya karfinsa ya ki yarda ya sake ta.

Da yake Kadar ta ruku sosai sai kuwa ta kasa
kwacewa amma sai ta yi amfani da jelarata ta
rinka dukan jikin Laffaru.

Duk sa'adda ta maka masa jelarta sai ka ga
kamar da takobi aka yanke shi, take jikinsa ke
darewa jini ya yi tsartuwa ko feshi yana mai
fwalla ihu, amma duk da haka ya ki yarda ya
saki Kadan duk da cewa wani lokaci tana danna
shi izuwa karkashin ruwan numfashinsa na
daukewa.

Da zarar kadan ya taso sama sai ka ga sun ci
gaba da gumurzu.

450

TASKARNOVELS.COM.NG
Kafin a jima jikin Laffaru ya yi kaca-kaca da
raunika. Ita kuwa Kadan sai ta ji ta fara gajiya
don haka sai tayi nutso kasa taki dagowa sama.

Koda Laffaru ya ga numfashinsa na neman
daukewa gaba daya sai ya saki Kadan babu shiri
ya fara iyo da sauri don ya kaj bakin gaɓar
koramar.

Ai kuwa sai kadan ya juyo da sauri suka kasa
sabon tsere.

Yayin da Sarki Laffaru ya auna ya ga cewa kafin
ya isa bakin gabar koramar sai kadan ya cim
masa sai kawai ya juya ya tare shi.Wannan
karon sai Kadan ya kai wa kafarsa hari. Laffaru
ya goce cikin zafin nama, amma duk da haka sai
da Kadan ya wawuri tsokar nama mai kauri a
cinyar Laffaru.

451

TASKARNOVELS.COM.NG
Laffaru ya kurma uban ihu a lokacin da yai wuf
ya sake rungumar Kadan suka ci gaba da
kokawa a kan ruwan.

Da kyar da sidin goshi Laffaru ya samu ya zare
wata siririyar wuka a jikinsa ya daga sama ya
kirɓawa Kadan. Bisa sa'a sai ya soke ido guda na
Kadan.

Take idon ya fashe, sai ga jini yana bulbula.
Laffaru ya sake daga wukar ya luma ta a kan
daya idon na Kadan.

Ai kuwa sai Kadan ya yi wata irin gagarumar
kara yai kasa ya lume izuwa karkashin koramar
bai sake tasowa sama ba.

Nan fa Laffaru ya fara iyo da kyar har ya samu
ya fito bakin gaɓar koramar. Yana fitowa ya baje
a kas sumamme.

452

TASKARNOVELS.COM.NG

Koda
End Ads