wanda ya zamo sanadiyyar girgizar fadar
gaba daya, duk mutanen da ke cikin fadar suka
dimauce sannan kuma sai ya naushi katon
madubin tsafin nasa wanda ke manne a jikin
bango.
Nan take mdubin ya rugurguje ya tarwatse yai
gutsun-gutsun. Sarki Nashmir ya sake dakawa
fadawansa tsawa ya ce, "Kowa ya bar su su biyu
rak daga shi sai Sarkin yakinsa sadauki Najwar.
313
TASKARNOVELS.COM.NG
Nan da nan kuwa kowa ya fice ya bar su fadar
tayi tsit tamkar babu wani mahaluki mai
numfashi a cikinta. Tsawon 'yan dakiku Sarki
Nashmir da Najwar na kallon juna dayansu bai
ce uffan ba. Daga can sai Sarki Nashmir ya
kyalkyale da dariya, lokaci guda kuma ya
murtuke fuska ya dubi Najwar ya ce. "Ya kai
Sarkin yakina abin alfahari a gare ni, ina son ka
yi shiri yanzu ka tafi izuwa dajin Hizurul Aswad
ka hallaka Aljani Maruful Dauwaz da abokan
tafiyarsa tunda su Aljani Sharkamuza sun kasa
kawar da su."
Sa'adda sadauki Najwar ya ji wannan umami sai
ya dubi Sarki Nashmir cikin alamun tsoro da
matukar damuwa ya ce, "Ya shugabana ka yi
sani cewa Aljani Maruful Dauwaz ba karamin
hatsabibi ba ne don haka ina matukar shakkar
tararsa da yaki duk da cewa kuwa na san na fi
karfinsa. Ina mai baka shawarar ka yi shiri da
kanka ka je ka gama da shi tun gabannin ya iso
nan ya yi maka muguwar ɓarna".
314
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda sadauki Najwar yazo nan a zancensa sai
Sarki Nashmir ya sake bushewa da dariya a karo
na biyu daga bisani kuma sai ya murtuke
fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa
ya nuna Najwar da yatsa cikin fishi ya ce, "Ya kai
Najwar ka yi sani cewa duk wani motsi da za ka
yi akan tafin hannuna kake. Na san sirrin
zuciyarka fiye da yadda kake tsammani. Karya
kake yi ka ce da ni kana shakkar yin karo da
Aljani Maruful Dauwaz domin ka fi karfinsa
nesa ba kusa ba. Na sani cewa ka daɗe kana da
burin ka ga na mutu ka haye kan karagata
sannan ka auri 'yata Gimbiya Ramlatul Siyam da
karfin tsiya, amma baka sami damar hakan ba.
In da za ka iya hallaka ni da tuntuni ka kawar da
ni. Bisa dole ne ka hakura ka ci gaba da jira.
Yanzu zan ba ka zabi guda biyu. Ko dai mu yi
yakı yanzu take anan cikin fadata idan ka kashe
ni ka sami karagata da 'yata. Idan kuma ni ne na
kashe ka shi ke nan sai na je na tari su Aljani
Maruful Dauwaz. Idan. kuwa ba za ka iya yakata
ba sai ka shirya ka tafi izuwa dajin Hizurul
Aswad. Maza ka yankewa kanka shawara yanzuyanzu"
315
TASKARNOVELS.COM.NG
Sa'adda Najwar ya ji wannan zaɓi da Sarki
Nashmir ya ba shi sai hankalinsa ya dugunzuma
ainun yai shiru yana tunanin abin da ya kamata
ya yi. Kawai sai Sarki Nashmir ya mike tsaye ya
zare takobinsa ya ce, "Tunda ka kasa bai wa
kanka zabi sai mu yi yakin.
Da jin haka sai sadauki Najwar ya yi murmushi
sannan ya risina cikin biyayya ya ce, "Haba ya
shugabana, wane ni na ce zan yi yaki da kai
alhalin tuntuni na jarraba na gani cewa kana
gaba da ni. Na amince zan tafi na tari su Aljani
Maruful Dauwaz kuma na rantse da darajar
karagarka ba zan dawo nan gare ka ba sai da
kan Maruful Dauwaz da na abokan tafiyarsa".
Koda gama fadin hakan sai sadauki Najwar ya
juya ya fice daga cikin fadar da sauri. Cikin
kankanin lokaci ya isa gidansa ya shiga
kimtsawa. Cikin hanzari ya yi gagarumar shigar
yaki, ya debo dukkan gurayensa da layunsa na
tsafi ya daurasu a jikinsa sannan ya fito ya hau
316
TASKARNOVELS.COM.NG
kan wani basamuden Aljani wai shi BARUKUL
MASNUR wanda ya ninka Sharkamuza sau uku a
girma da karfin dantse da na sihiri.
Nan take Barukul Masnur ya bude fuka- fukansa
ya tashi sama dauke da sadauki Najwar suka
luluka a cikin gajimare.
Lokacin da Sarki Nashmir ya fito daga cikin
fadarsa bayan ya gama ganawa da sadauki
Najwar sai ya wuce kai tsaye izuwa cikin gidan
sarautar ya nufi bangaren da turakar Gimbiya
Ramlatul Siyam. Duk inda Sarki Nashmir ya
ratsa sai ka ga wadannan Dakaru na aljanu da
na bil'adama suna sujjada a gare shi kuma suna
buɗa masa hanya yana wucewa.
Koda Sarki Nashmir ya dubi miliyoyin Dakarun
aljanun da ke shawagi a kan saman rufin
turakar Gimbiya don tabbatar da tsaro sannan
ya dubi miliyoyin Dakarun bil'adama da suka
kewaye harabar turakar gaba daya sai ya cika
317
TASKARNOVELS.COM.NG
da farin ciki ya kama zancen zuci yana mai cewa
a ransa, ya ma su Aljani Maruful Dauwaz za su
iya shigowa har cikin wannan fada su kashe
gabadayan wadannan Dakaru sannan su sace
Gimbiya Ramlatul Siyam? To wai shin ma shi
yana ina har hakan za ta faru?
Abu na biyu kuma, ta yaya su Maruful Dauwaz
za su sami yawun barcin bakinsa alhalin shi ba
ya barci sai sau daya a cikin kwanakin mako?"
Koda Sarki Nashmir ya zo nan a zancen zucinsa
sai ya kyalkyale da dariya a fili bai sani ba har
Dakaru, barori da kuyangin gida sarautar suka
bi shi da kallo suna mamakin dalilin dariyar
tasa.
A daidai wannan lokaci ne ya iso daf da kofar
turakar Gimbiya Ramlatul Siyam, Dakarun da ke
tsaron kofar turakar suka bude masa ya kunna
kai ciki. Sai da ya yi doguwar tafiya a cikin
turakar sannan ya iso cikin dakin barcin
318
TASKARNOVELS.COM.NG
Gimbiya Ramlatul Siyam, ko ina ya duba sai dai
ya ga kuyangin na ta hidima iri-iri.
Da shigar Sarki Nashmir cikin dakin barcin sai
ya iske Gimbiya Ramlatul Siyam ita kadai
kwacen akan gado ta yi rub da ciki tana ta
faman rusa kuka.
Cikin tsananin mamaki da tashin hankali Sarki
Nashmir ya karasa gare ta ya zauna a gefen
gadon ya tashe ta zaune a lokacin da idanunta
suka cika sharkaf da hawaye ya dube ta a cikin
matukar damuwa ya ce, "Ya ke 'yata, mene ne ya
faru gare ki wanda har ya sa ki zubar da
hawaye? Kin sani cewa ban taɓa ganinki ba a
cikin wannan hali".
Sa'adda Ramlatul Siyam ta ji wannan tambaya
sai ta yi shiru tana mai sunkui da kanta kas ta ki
cewa komai. Kawai sai Sarki Nashmir ya zare
wata wuka a jikinsa ya yanki kansa a damtsen
hannun hagu, jini yai tsartuwa akan fuskar
319
TASKARNOVELS.COM.NG
Ramlatul Siyam ya sake daga wukar zai daďa yi
wa kansa rauni sai Ramlatul Siyam ta yi wuf ta
rike hannunsa kuma ta fashe da kuka tana mai
cewa, "Saboda me za ka cutar da kanka?
Nashmir ya dube ta a lokacin da idanunsa suka
cika da kwallah ya ce, "Ina amafanin rayuwata
idan har ba zan iya yi miki maganin matsalar da
ta same ki ba? Lallai akwai wani babban
al'amari wanda kika daɗe kina ɓoye min shi,
lallai sai kin sanar da ni shi a yau kuma a yanzu.
Idan kuwa kika ki sai dai a fitar da gawata daga
cikin wannan ďaki naki.
Koda jin wannan batu sai Gimbiya Ramlatul
Siyam ta rungume Sarki Nashmir ta fashe da
wani sabon kuka sannan ta ce, "Ya kai Abbana
ka yi sani cewa na dade ina yin wani mugun
mafarki amma ban taba sanar da kai ba.
Wannan Aljani da ka nuna mini a madubin
tsafinka shi nake gani a cikin mafarkina kuma
320
TASKARNOVELS.COM.NG
ana nuna mini cewa ya zo har cikin gidan
sarautarmu ya yaki Dakarunka an yi kazamin
yaki wanda ya zamo sanadin asarar miliyoyin
rayuka da dumbin dukiya har sai da dukkan
ginin gidan nan ya fadi kasa kuma gagarumar
gobara ta kama ko ina. Ina ji ina gani wannan
Aljani ya shiga tsakanina da kai ya raba mu ya
dauke ni yai sama da ni a lokacin da kai kuma
kake cikin wani mugun hali ka kasa koda
mikewa tsaye".
Koda Gimbiya Ramlatul Siyam ta zo nan a
zancenta sai Sarki Nashmir ya takarkare ya
kwarara uban ihu. Al'amarin da ya firgita
gabadayan jama'ar da ke cikin gidan sarautar ke
nan. Dakaru suka rugo da gudu izuwa cikin
turakar rike da makamai tsirara.
Da shigowar Dakarun suka ga rauni a hannun
Sarki amma kuma babu kowa a cikin turakar sai
su biyu jal shi da 'yarsa sai suka cika da dumbin
mamaki.
321
TASKARNOVELS.COM.NG
Nan take Sarki Nashmir ya yi wa Dakarun inkiya
suka juya da baya suka fice suka kullo kofar.
Sarki Nashmir ya dubi Gimbiya Ramlatul Siyam
cikin tsananin takaici ya ce, "Ya ke 'yata hakika
kin yi babban kuskure da kika boye min wannan
al'amari. Inda ace kin sanar da ni tun a ranar da
kika fara yin mafarkin da tuni na dauki matakin
gaggawa na kawar da waďannan abokan gaba
nawa.
Yanzu dole ne na zuba ido na ga abin da zai faru
tsakaninsu da Sarkin yakina Najwar. Idan har
bai sami nasarar hallaka su ba dole ne na zauna
na jira karasowarsu sannan ayi ta ta kare amma
kafin sannan yanzu zan shiga cikin dakin halwar
tsafina domin na binciko mafita. Duk abin da
ake ciki kada ki kuskura ki fito daga cikin
wannan daki face ni da kaina na zo na ce ki fito.
Ina tabbatar miki da cewa in dai kina cikin
wannan daki babu wata masifa ko wani
tsautsayi da ya isa ya same ki."
Koda gama fadin haka sai Sarki Nashmir ya
mike tsaye ya juya ya fice daga cikin dakin da
322
TASKARNOVELS.COM.NG
sauri ya nufi inda dakin tsafinsa yake, ya bar
Gimbiya Ramlatul Siyam a zaune cikin tsananin
tashin hankali da rudewa.
Wannan shi ne abinda ya faru a Birmin HINDU
bayan Sarki Nashmir ya tura Dakarunsa na
farko izuwa dajin Hiuzurl Aswad domin su
kashe su Aljani Maruful Dauwaz.
Al'amarin su Aljani Maruful Dauwaz kuwa,
bayan sun shafe rabin sa'a a kwance suna
hutawa sai Aljani Maruful Dauwaz ya karanta
waďansu dalasiman tsafi. Nan take wata irin
murtukekiyar sarkar tsafi ta fito daga cikin
karkashin kasa ta nannaďe hannayensa,
kafafunsa da fuka-fukansa sannan ta daure su
tamau yadda ko motsa su ba zai iya ba. A sannan
ne ya dubi Rahila da Sarki Laffaru ya ce, "Ku zo
ku gyara mini karayar kasusuwan fuskata".
Koda jin haka sai Rahila ta dubi Sarki Laffaru ta
ce, "Je ka ka karyo mini dogayen itatuwa kamar
guda bakwai masu dan kwari."
323
TASKARNOVELS.COM.NG
Nan take Laffaru ya tafi domin cika umarnin.
Koda ya hau kan wata bishiya ya fara karyo
itatuwan sai takaici ya kama shi saboda ya tuna
cewa shi fa Sarki ne mai cikakken iko wanda
duniya take tsoro amma yau ga shi mace tana sa
shi aiki, tana ba shi umarni yana bin umarnin
cikin rawar jiki.
Nan dai ya hanzarta ya je ya kai wa Rahila
wadannan itatuwan. Tana karɓar itatuwan sai
ta hau kan kirjin Aljani Maruful Dauwaz ta
zauna kai ka ce akan wani katon tsauni take.
Take ta umarci Maruful Dauwaz da ya bude
bakinsa.
Ba tare da gardamar komai ba kuwa
yawangame bakin nasa mai fadi tamkar rijiyar
mutanen da. Rahila ta zura hannayenuta a cikin
bakin.
324
TASKARNOVELS.COM.NG
Kodata kamo kasusuwan fuskar tasa wadanda
suka kakkarye ta fara gyarawa tana daure su da
itatuwa sai Maruful Dauwaz ya fara kwarara
uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogi. Ihun
nasa ya haddasa wanzuwar iska mai karfi a
cikin dajin wacce ta rinka zubar da bishiyoyi
kasa.
Hakan bai sa ta tausayawa Maruful Dauwaz ba
sai ta ci gaba da aikinta har ta kammala. Saboda
tsananin azabar da Maruful Dauwaz yaji sai da
hawayen wuya ya zubo masa.
Bayan Rahila ta gana gyara wa Maruful Dauwaz
karayar kasusuwan fuskarsa ne suka bude jakar
guzurinsu ita da Sarki Laffaru suka fiddo da
abinci suka ci.
Shi kuwa Maruful Dauwaz sai ya gangara izuwa
cikin wata katuwar korama ya kafa bakinsa ya
kama shan ruwa, sai da ya sha ruwan mai
yawan gaske wanda adadinsa ya kai duro
325
TASKARNOVELS.COM.NG
ashirin da biyar sannan ya fito daga cikin
koramar ya koma wajen su Rahila ya kishingida
suka fara hira, inda Maruful Dauwaz ya dubi
Rahila ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki me ya sa
na ga kamar kina cikin damuwa ne kin kasa
sakin jikinki ki ci abinci sosai?"
Koda jin zuciya wannan batu sai Rahila ta yi
ajiyar sannan ta ce, "Ya kai jarumin jarumai, ka
yi sani cewa ba komai ba ne ya sa ka ga ina cikin
wannan hali ba face abubuwa biyu da suka
dame ni.
Abu na farko shi ne, hankalina a tashe yake bisa
ganin irin mummunan yakin da muka yi da
Dakarun Sarki Nashmir wanda da kyar muka
tsira da rayuwarmu. Tabbas na san cewa har a
yanzu fa ba tsira muka yi ba kuma a ko yaushe
za mu iya ganin waɗansu mugayen Dakarun
nasa.
326
TASKARNOVELS.COM.NG
Saboda haka ni yanzu ina ganin cewa zamanmu
ma a nan yana da hadarin gaske. Ko dai mu
nemi wajen buya ko kuma mu tashi mu ci gaba
da tafiyarmu in ya so mu yi jinyar jikin namu
akan hanya.
Abu na biyu da yake damuna shi ne, yawan
tunowa da sauran abokan tafiyarmu waɗanda
muka baro a can kogon Darul Iksina.
Hakika ina matukar tausaya musu musamman
idan na tuno da irin tsananin wuyar da muka
sha tare da su da yadda wasunsu suka rasa
masoyansu. Yanzu ga shi mun baro su a cikin
kogon na Darul Iksina kuma babu yadda za su
iya fitowa.
Yanzu shi ke nan duk burinsu ya yanke ke nan,
sun hallaka bisa wannan tafarki?".Koda Rahila
ta zo nan a zancenta sai ta fashe da matsanaicin
kuka. Al'amarin da ya karya zuciyar Aljani
Maruful Dauwaz da Sarki Laffaru ke nan su ma
327
TASKARNOVELS.COM.NG
suka kama zubar da hawaye saboda tausayi!
Tsawon 'yan dakiku dayansu bai ce uffan ba.
daga can sai Maruful Dauwaz ya dubi Rahila ya
ce, 'Ya ke wannan 'yar Sarki, hakika kin zo da
shawara mai kyau bai kamata mu ci gaba da
zama anan ba domin masu iya magana sun ce,
'Zama waje daya tsautsayi ne in ji kifi'. Yana da
kyau mu nemi maboya inda za mu yi jinyar
jikinmu domin ina tabbatar muku da cewa ni
kaina ba zan iya ci gaba da tafiya ba mai tsawon
koda rabin sa'a a cikin wannan hali da nake.
Batun abokan tafiyarku kuwa da muka baro su a
can kogon Darul Iksina ni kaina na yi matukar
bakin ciki bisa halin da suka kasance kuma zan
so ace sun kubuta sun fito daga kogon a raye
amma maganar gaskiya abu ne mai matukar
wuya. Na yı muku alkawari idan har mun sami
nasarar shiga fadar Sarki Nashmir mun dauko
Gimbiya Ramlatul Siyam lallai sai mun biya ta
tsibirin Darul Iksina mu gani ko abokan tafiyar
taku sun fito."
328
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Rahila da Laffaru suka ji wannan batu sai
farin ciki ya lulluɓe su suka ji kaunar Aljani
Maruful dauwaz ta karu ainun a cikin zuciyarsu.
Duk su biyun sai suka fada kansa suka rungume
shi suna masu yi masa godiya.
Maruful Dauwaz ya ce, "Yanzu sai mu tashi mu
tafi neman inda zamu buya a cikin dajin nan
domin mu ya jinyar kanmu.
Za mu yi wasu tambayoyi kafin mu sako kashi
na Hamsin da uku. Zan yi farin ciki idan na samu
gamsassun bayanai daga gare ku wanda shi ne
zai kara mini kwarin guiwa har mu samu mu
shiga littafi na Huďu. Na gode!
Kafin daya daga cikin su Rahila ya ce wani abu
sai Maruful Dauwaz ya sure su su biyun ya aza
su a gadon bayansa sannan ya yunkura da kyar
cikin matukar karfin hali ya tashi sama ya kama
yawo a cikin dajin yana neman inda za su бuya.
329
TASKARNOVELS.COM.NG
Bai daďe da fara shawagi a sama ba kuwa sai ya
hango wani katon tsauni mai yawan kofofin
kogo. Kai tsaye Maruful Dauwaz ya durfafi
wannan tsauni ya dira a cikin kofar kogon.
Dirarsa ke da wuya sai ya yi tsafi wutar ice ta
baiyana a kan hannayensa. A sannan ne Rahila
da Laffaru suka sauko daga kansa suka tsaitsaya
suna kallonsa kawai. Maruful Dauwaz ya dube
su ya ce, "Ku zo mu duba ko ina a cikin dukkan
kogon da ke kan wanna tsauni domin mu
tabbatar da lafiyar tsaunin.
Ba tare da gardamar komai ba kuwa su Rahila
suka amince da wannan shawara. Sai da ska
shafe sa'a uku cur suna ta shige da fice a cikin
ramukan da ke kan tsaunin amma ba su ga
halitta guda daya ba a ciki, koda kuwa kwaro ko
tsuntsu.
Abin da ya fi daure musu kai shi nc, duk ramin
da suka shiga sai su ga ya bulle zuwa cikin wani,
sannan sun ga wadansu irin manya-manyan
tukwane irin na mutanen farko a cikin kogon
gami da gidajen itatuwa da shimfidu na fatun
dabbobi iri-iri, wata fatar ma ba su taɓa ganin
330
TASKARNOVELS.COM.NG
irin ta ba kuma dukkan wadannan abubuwa sun
yi kura matuka kuma yana ta lullube su alamar
cewa an shafe shekaru masu yawa ba a yi
amfani da su ba.
Koda ganin wannan al'amari sai Aljani Maruful
Dauwaz yai ajiyar zuciya ya ce, "Tabbas akwai
maridan da suka yi rayuwa a cikin wannan kogo
shekaru aru-aru da suka shude".
Koda jin wannan batu sai Sarki Laffaru yai sauri
ya goge yanar da ke kan wani gadon ice sannan
ya yaye shimfidar da ke kansa sai suka yi arba
da wani katon kwarangwal na wani maridi.
Hatta Aljani Maruful Dauwaz sai da ya firgita da
ya ga wannan kwarangwal domin iya tsawon
rayuwarsa a duniya bai taba ganin halitta mai
girma kamarsa ba, don shi kansa ya fi shi tsawo
a tsaye sau hudu.
Sarki Laffaru ya zare takobinsa ya kwankwashi
kashin kwarangwal din, kawai sai ya jinjina kai
331
TASKARNOVELS.COM.NG
ya ce, "Wannan kwarangwal din ya fi shekaru
dubu uku da mutuwa a cikin wannakogo".
Cikin mamaki Rahila ta dubi Sarki Laffaru ta ce,
Kai kuwa yaya aka yi ka san wannan ilimi?".
Laffaru ya yi murmushi ya ce, "Ai lokacin da
nake da karfin sihirin tsafina na yi bincike
matuka akan wannan fanni na sanin dadewar
abu a duniya, don haka na sami ilimi mai yawa
akan hakan".
Gama fadin hakan ke da wuya sai Aljani Maruful
Dauwaz ya dauki gawar wannan kwarangwal
daga kan gadon icen yai jifa da ita izuwa jikin
kogon dutse ta rugurguje sannan ya sake kade
kurar da ke jikin fatar buzun da aka shimfida.
Akan buzun ya kwanta akan gadon yana mai
cewa, "Ni kam na sami wajen kwanciyata ku ma
sai ku nemi naku. Lallai a cikin wannan kogo za
mu yi jinyarmu tsawon mako biyu. Hankalina ya
kwanta da wannan kogo domin ko wani mugun
332
TASKARNOVELS.COM.NG
abun ne ya zo mana in dai muna cikin nan zai yi
wuya ya iya hallaka mu cikin sauri".
Gama fadin hakan ke da wuya sai Maruful
Dauwa ya rufe idanunsa, nan take barci ya
dauke shi sakamakon tsananin wahalar da ya
sha a bakin gumurzun da ya yi da Aljani
Sharkamuza.
Kash! Rashin sani ya fi dare duhu! Inda Aljani
Maruful Dauwaz ya san abin da zai faru da bai
kwanta akan wannan gadon ice har bacci ya
dauke shi ba.
Domin kuwa, yin barcinsa ke da wuya Aljani
Barukul Masrur ya sauka a dajin dauke da
sadauki Najwar suka duro a daida inda aka yi
wannan bakin gumurzu tsakanin su Aljani
Sharkamuza da su Aljani Maruful Dauwaz.
Ai kuwa suna dira suka yi arba da gawar Aljani
Sharkamua. Koda suka ga irin kisan da aka yi
masa, wato suka ga zururun rami ta cikin idonsa
333
TASKARNOVELS.COM.NG
guda har bayan keyarsa sai suka cika da
mamaki kuma zuciyarsu ta kama tafarfasa
kamar za ta kone.
Nan take Aljani Barukul Masnur ya shaki
numfashi sannan ya dubi sadauki Najwar ya ce,
"Ya shugabana na ji kamshin bil'adama guda
biyu a cikin wannan daji da kuma kanshin Aljani
dan uwana guda daya".
Koda jin haka sai sadauki Najwar yai
murmushin mugunta ya ce, "Abin da nake so da
kai shi ka tashi sama ba can kololuwa ba ka
dinga kaďa fuka-fukanka a hankali yadda ba za
a ji motsinka ba har mu gano inda su Maruful
Dauwaz suke. Sai dai kawai mu yi musu
MAMAYAR BAZATO! Aljani Barukul Masnur ya
yi dariya ya ce "Hakika ka zo da shawara mai
kyau ya shugabana".
Gama fadin hakan ke da wuya Barukul Masnur
ya bude fuka-fukansa ya yi sama yana mai daďa
334
TASKARNOVELS.COM.NG
bude kofofin hancinsa domin ya jiyo kamshin su
Maruful Dauwaz ya gano a inda suke.
A cikin kogon dutse kuwa, lokacin da Rahila da
Sarki Laffaru suka ga Aljani Maruful Dauwaz ya
kama barci har da yin munshari mai nauyi sai su
ma su Rahila suka