x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - MAZAN JIYA 3

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 68212 words

Category: Adventure Stories

Views 177

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
sai suka firgice suka
kama guje-guje suna barin filin yakin.
Sharlis ta dira bisa turba rike da kan Sarki
Nurbas. Ko da su aljani Shalbasha ibini Rauhub
suka ga abin da ya faru sai suka cika da tsananin
mamaki. Aljani Shalbasha bai san sa'adda
jikinsa ya kama kyarma ba musamman da ya ga
jaruma Sharlis ta nufo kansa gadan-gadan. Abin
da ya fado a ransa shi ne, shi ma kashe shi za ta
yi, domin babu mamaki ta gano cewa, shi ba
Lafarun gaskiya ba ne.

Koda Sharlis ta iso gaban aljani Shalbasha ta ga
jikinsa na kyarma sai ta yi murmushi sannan ta
ce da shi, "Ka tafi da wannan kan izuwa birnin
Zaruf ka shiga har cikin fadarsa ka hau kan
karagar mulkinsa ka zauna. Ina son ka yi
18

TASKARNOVELS.COM.NG
zamanka a cikin garin ka zamo halifana ka ci
gaba da mulkin birnin Zaruf tunda na ci su da
yaki. Koda jin wannan batu sai aljani Shalbasha
ya zaro idanu cikin alamun tsananin damuwa ya
ce, "Haba yake matata! Yaya ni da nake mulkin
babbar birni kamar wannan na Kufa za ki ce na
koma birmin Zaruf na mulke su, ai na ci baya".
Sa'adda Sharlis ta ji haka sai ta sake yin
murmushi a karo na biyu sannan ta matso daf
da aljani Shalbasha ta yi masa rada a kunne ta
ce, tunda ba ka son maigidanka Lafaru ya
wulakanta, idan za ka shiga cikin birnin Zaruf
dauke da kan Sarkinsu sai ka juye izuwa wani
kamannin daban kamar yadda yanzu ka juye
izuwa na mijina.

Ya kai Shalbasha ka sani cewa umarni na ba ka a
yanzu, idan kuma ka zo mini da tangarda
yanzun nan takobina za ta sha jininka kamar
yadda ta sha na Sarki Nurbas! Koda jin haka sai
jikin aljani Shalbasha ya ci gaba da karkarwa
fiye da farko, amma don kada jama'a su gane
abinda ke faruwa sai shi ma ya yiwa Sharlis rada
a kunne ya ce, "Tuba na ke ya shugabata na
yarda zan bi umarninki, kuma ina rofonki da ki
19

TASKARNOVELS.COM.NG
yi mini rai kada ki kashe ni. Ki sani cewa ni
bawa ne kawai mai bin umarni, ba ni da laifin
komai". Sharlis ta yi murmushi sannan ta ce,
"Bana cutar da wanda bai cutar da ni ba, in da
dai ban gano ko kai waye ba har aka cutar da ni
da tabbas sai na cutar da kai.

Yanzu ka debi Dakarun nan birnin guda dubu
dari ka tafi da su izuwa can birnin Zaruf, amma
kafin sannan ina son ka juye izuwa kamannin
wazirin Sarki Laffaru domin a halin yanzu
wazirin na kwance agidansa yana jinyar rashin
lafiya. Lallai idan mutanen birnin Zaruf suka
ganka a cikin siffar wazirin Laffan kuma rike da
kan Sarkinsu tare da Dakarun Sarki Laffaru
dubu dari babu wanda zai yi ma ka tawaye, dole
ne su yi biyayya a gare ka ka mulke su. Duk
ranar da Sarki Laffaru ya dawo gida zan sa ya
aika maka ka dawo a tura wani ya karɓi
matsayinka.

Daga wannan lokaci sai ka san inda dare ya yı
maka, idan kuwa na sake ganinka koda a kusa
da birnin nan ne sai dai tsohuwarka ta haifi
20

TASKARNOVELS.COM.NG
wani. Gama fadin hakan ke da wuya sai jaruma
Sharlis ta tafi izuwa cikin birnin Kufa kai tsaye,
ta bar Dakarun yaki a tsaitsaye suka bi ta da
kallo kawai cikin tsananin mamakin yadda
akavyi ita kadai ta tarwatsa dukkan abokan
gaba har kuma ta sami nasarar kashe Sarki
Nurbas

Daga wannan rana Sharlis ta rinka dora ɗanta
yarima Shaddad akan karagar mulkin ubansa
tana koya masa yadda ake tafiyar da mulki yana
wakiltar mahaifinsa.
Al'amarin da ya jefa fadawan Sarki Laffaru cikin
tsananin damuwa da bakin ciki ke nan, akan an
bai wa kankanin yaro dan shekara uku
shugabancinsu. Suna ji suna gani suka hakura
dole da Shugabancin nasa, aka rasa wanda zai ce
an yi ba dai-dai ba saboda tsananin tsoron kada
fushin Sharlis ya tabbata a kansu. Su kuwa
sauran mutanen gari na Kufa kuwa, sai wannan
sabon mulki na ďan Sarki Laffaru ya zame musu
abin alheri, domin gabadaya zaluncin da ake yi a
kasar an daina. An daina kwacewa talakawa
dukiya, yi wa mata fyade da zalunci na ba gaira
21

TASKARNOVELS.COM.NG
ba dalili. Al'amarin da ya matukar kawo
kwanciyar hankali da daukakar kasuwanci da
arziki domin kowa ya saki jiki yana fito da
hajarsa kasuwa ya kasa ta komai yawanta. Nan
da nan fatake suka rinka yi wa birnin Kufa
shigar burtu ya zamana cewa kasuwar garin na
ci har sau uku a sati maimakon sau daya jal da
take ciki. Nan fa birnin Kufa ya bunkasa ainun a
karfin kasuwanci da arziki, mutane suka rinka
yin hijira daga sauran kasashe makwabtaka
suna dawowa birnin Kufa har garin ya cika ya
batse, yawan al'umma ya wuce misali saboda
haka sai Sarki Shaddad ya kafa doką aka hana
baki shigowa su zauna sai dai su yi cinikinsu su
fita.

Babu abinda yake bai wa jama'ar birnin Kufa
mamaki face yadda wannan sabon Sarki nasu
dan shekara uku jal! a duniya ke da basira da
hangen nesa. Idan kuwa yana yi wa mutane
jawabi sai ka rantse dan shekara dari ne yake
zance. Nan da nan labari ya cika duniya cewar
Sarki Laffaru ya ɓata ba a san inda yake ba,
amma dansa Shaddad yaro dan shekara uku ya
gaje shi har ma ya bambanta da ubansa domin
22

TASKARNOVELS.COM.NG
shi adali ne saɓanin mahaifinsa da ya kasance
azzalumi.
Bisa wannan dalili ne mutane suka rinka zuwa
daga kasa-kasa, manyan Sarakai, attajirai da
manyan bokaye domin kawai su ga Sarki
Shaddad da idanunsu su tabbatar da abin
al'ajabin da ake ta fada.

Babu abinda zai burge mutum face yadda ko
yaushe Sarki Shaddad yake zama a fada tare da
mahaifiyarsa Sharlis a kodayaushe tana
damansa. Ga ta kyakkyawar gaske, kuma ga dan
nata shi ma kyakkyawan gaske, duk sun yi shiga
iri daya abin gwanin ban sha'awa.
Duk abinda Sarki Shaddad zai yi sai ya nemi
shawarar mahaifiyarsa Sharlis, sai abinda ta ba
shi umarni shi yake zartarwa, kawai dai sunan
shi ne Sarki, amma Sharlis ce ke tafiyar da
komai na mulki.

Sai da Sarki Shaddad ya sami kwana goma sha
hudu akan karagar mulki sannan Sharlis ta sami
23

TASKARNOVELS.COM.NG
nutsuwa ta shiga halwar tsafi domin ta binciko
halin da Sarki Laffaru ke ciki. Ai kuwa nan take
ta ga duk abinda ya faru tun daga lokacin da
boka Muzaffar ya zo ya dauke Sarki Laffaru
kawo izuwa sa'adda suka je suka dauko gimbiya
Rahila sannan suka je suka dauko sauran
abokan tafiya har suka iso wannan mugun daji
inda suka fafata kazamin yaki da wadannan
mugayen aljanu. Koda gama ganin wannan
al'amari sai Sharlis ta kurma ihu cikin tsananin
bakin ciki, hankalinta ya dugunzuma fiye da ko
yaushe a rayuwarta, ta tabbatar da cewa an
shammace ta
Sharlis ta yi shiru ta shiga tunani mai zurfi.
Babban tashin hankalinat shi ne, ba za ta iya
tafiya ta bar danta Shaddad shi kadai akan
mulki ba, domin ta bi bayan su Sarki Laffaru ta
wargatsa duk shirinsu. Nan fa ta fara tunanin
wata dabarar da za ta yi ta wargatsa shirin nasu
ba tare da ta bi bayansu ba.

Sharlis ta ce a ranta, "Yanzu dai kokarinsu shi ne
su sami damar da za su isa kogon Darul Iksina
su dauko aljani Maruful Dauwaz domin ya je ya
24

TASKARNOVELS.COM.NG
sato musu gimbiya Ramlatul Siyam 'yar Sarki
Nashmir na birnin Hindu. To ai kuwa abu ne
mawuyaci su iya tsallake wadannan masifu da
ke cikin dazuzzukan nan biyar har su isa kogon
Darul Iksina domin fiye da shekaru dubu biyu
baya ba a sami wanda ya keta ta cikin su ba face
shi kansa aljani Maruful Dauwaz aljanin da aka
tabbatar da cewa babu kamarsa a zafin nama,
karfin gudu a sama da kuma tsananin juriyar
wuya kowacce iri ce.

Abu na biyu kuma shi ne, ai koda ma sun ami
nasarar dauko aljani Maruful Dauwaz shiga
fadar Sarki Nashmir har a dauko gimbiya
Ramlatul Siyam daidai yake da tafiya neman jaki
mai kaho. Domin hatta Sarki Bokayen aljanu na
duniya almajirin Sarki Nashmir ne, a wajensa ya
yi karatun tsafi. Tsaron da ke cikin gidan
sarautar Sarki Nashmir da irin abubuwan
masifun da ke cikinsa sun ninka wanda ke cikin
wadannan mugayen dazuzzuka biyar na hanyar
kogon Darul Iksina sau arba'in. Koda Sharlis ta
zo nan a zancen zucinta sai ta bushe da dariyar
murna, ta ce, "Ai babu wata hanya da burin su
Sarki Laffaru zai cika, to amma duk da haka ba
25

TASKARNOVELS.COM.NG
zan saki jiki ba na zuba ido kawai, dole ne na yi
tunanin matakin da ya kamata na dauko, koda
tsautsayi zai sa su sami nasarar daga yanzu
zuwa lokacin da za su sami nasarar dauko aljani
Daruful Dauwaz."

Wannan shi ne abin da ya faru a birnin Kufa
bayan ɓacewar Sarki Laffaru.

*****
AL'AMARIN su boka Muzaffar kuwa, kamar
yadda boka Muzaffar ya bayar da shawara haka
aka yi, wato sai da aka kwana biyu suna jinyar
jikinsu ya zamana cewa dukkanninsu sun ji
kwarin jikinsu sannan suka yi shiri domin su
shiga daji na farko.

Bayan kowa ya gama kintsawa sai sukai cirkocirko gaba dayansu aka rasa wanda zai fara
wucewa kan gaba, har ita kanta kuwa gimbiya
Rahila saboda tsananin fargaba da tunanin
abinda ke cikin dajin.
26

TASKARNOVELS.COM.NG

Koda ganin haka sai boka Muzaffar ya dubi
sadauki Haiman ya ce, Ya kai wannan jarumi
mai jarumtakar ban al'ajabi ka yi sani cewa
yanzu ne zamu shiga dajin Maridai, kai kadai ne
za ka iya tarwatsa wadannan Maridai mu kutsa
ta cikinsu mu wuce. Saboda haka kai ne za ka
wuce gaba sanann gaba dayanmu mu bi ka a
baya. Koda jin wannan batu sai sadauki Haiman
ya zare takobinsa ya wuce gaba. Da ganin haka
sai jaruma Shadira ma ta goya yaro Masnur a
baya, jarumi Imran ya goya mahaifiyarsa,
gimbiya Zarina ta goya dan uwanta sarkin
Farisa.

Al'amarin da ya dugunzuma hankalin sadauki
Shaharan ke nan, domin shi ba zai iya daukar
dokinsa ba.
Koda boka Muzaffar ya ga hankalin Shaharan ya
tashi ainun, sai ya yi dariya, sannan ya dubi
aljani Marhabul Zaurus ya ce, "Dauki dokin
Shaharan ka taho da shi. Cikin matukar firgici
27

TASKARNOVELS.COM.NG
aljani Marhabul Zaurus ya dubi boka Muzaffar
ya ce, haba ya shugabana ya za ka ce na karawa
kaina nauyi alhalin ka san irin bala'in da za mu
shiga a cikin wannan daji.

Cikin fishi boka Muzaffar ya dakawa Marhabul
Zaurus tsawa ya ce, "Ba wai rokonka nake ba
umarni nake ba ka. Bisa dole Marhabul Zaurus
ya dauki dokin sadauki Shaharan ya dora shi a
gadon bayansa,sannan aka ci gaba da tafiya.
Sadauki Haiman na kan gaba, jaruma Shadira na
biye da shi, sai Zarina, Imran da Shaharan. Boka
Muzaffar, Sarki Laffaru, gimbiya da Rahila ne a
karshe sai kuma aljani Marhasul Zaurus wanda
ke goye da dokin Shaharan.

Hakan dai suka ci gaba da tafiya har suka wuce
iyakar dajin da suka baro suka shiga cikin
farkon dajin gaba daya, wato dajin mugayen
Maridai. Da shigarsu cikin wannan daji sai suka
kamu da matukar fargaba. In ka dauke jaruman
guda hudu da gimbiya Rahila da boka Muzaffar
gaba daya sauran abokan tafiyar jikinsu
karkarwa yake kamar wadanda aka tsoma a
28

TASKARNOVELS.COM.NG
cikin ruwan kankara. Ba komai ne ya haddasa
hakan ba face ganin yanayin wannan daji.

Wadansu irin gabza-gabzan bishiyoyi ne a dajin
dogaye masu siffofin mutane kirar mutanen
farko. Babu abinda zai bai wa mutum mamaki
face yadda siffofin bishiyoyin suka zama haka
tunda ba sassakasu aka yi ba, a haka suka tsiro
suka girma. Da zarar mutum ya kalli bishiyoyin
sai ya ji zuciyarsa na dukan uku-uku saboda
munin siffofinsu kuma sai ya ga kamar za su
kawo masa hari a ko yaushe. Dajin ya yi tsit
tamkar wani abu mai rai bai taɓa wanzuwa ba a
cikinsa, amma da zarar su sadauki Haiman sun
taka busassun ganyayyakin wadannan bishiyoyi
sai ka ji karar ruburбushewar ganyayen ta cika
dodon kunne, kuma ta cika dajin gaba daya
harda amsa kuwwa. Ga shi babu inda mutum zai
taka inda babu ganyayen.
Abin da su Haiman basu sani ba shi ne, wannan
kara ta ganyaye ita ce alamar da mugayen
maridan suke ganewa cewa an shigo cikin
mahallinsu.

29

TASKARNOVELS.COM.NG
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai ga
wadannan zabga-zabgan Maridai suna fitowa
daga cikin wadansu ɓoyayyun ramuka a
karkashin kasa tamkar an tashi matattu a
makabartar da ta kunshi gawar da ba ta da dadi.
Koda su Haiman suka yi arba da wadannan
Maridai sai suka firgice ainun, nan take
dukkaninsu suka ji sun yi nadamar baro
kasashensu don cika burin kansu.
Shi kansa sadauki Haiman da aka ce shi ne zai
iya tarwatsa maridan sai da ya tsorata ainun ya
raina kansa, domin ya tabbatarwa kansa cewa
boka Muzaffar karya ya yi da ya ce da shi shi ne
zai iya tarwatsa su, domin ido ba mudu ba ne
amma ya san kima, kuma ko ba a gwada ba
linzami ya fi karfin bakin kaza.

Sadauki Haiman yaji kamar ya yar da takobinsa
ya juya da baya a guje, amma da ya ga cewar
tuni maridan sun yi musu kawanya babu hanyar
gudu sai ya tsaya cak!
Hakika masu iya magana sun yi gaskiya da suka
ce, "Idan mutum ya ga mutuwa ta ritsa shi, to fa
a sannan ne yake zama jaurmin dole, domin ya
30

TASKARNOVELS.COM.NG
ceci rayuwarsa ta kowane hali." Lokacin da
sauran jaruman tafiya suka ga sadauki Haiman
ya tsaya cak bai yi yunkurin komai ba sai kallon
maridan yake kawai sai suma suka gyara
tsayuwa suna wasa da makamansu.

Su kuwa sauran abokan tafiyar tun sa'adda suka
yi arba da halittun suka sume duk da cewa ana
goye da su. Shaharan, Sarki Laffaru ne kawai ba
su suma ba saboda su ma zuciyoyinsu na
sadaukai ne
A iya tsawon rayuwar wadannan Maridai a dajin
shekaru dubu biyu baya ba su taɓa ganin
mutane ko aljanu masu dakakkiyar zuciya ba
kamar su sadauki Haiman, domin duk wanda ya
yi arba da su take yake sumewa ko ya haukace,
amma su ga su daram a gabansu.
Sannu a hankali maridan da ke gabansu suka
fara marmatsowa suna wangame manyan
bakunansú masu kama da bakin rijiya da nufin
su dasawa su Haiman wawaso su cinye su.

31

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Haiman ya ga mutuwa na durfafo shi
gadan-gadan sai ya ďaga takobinsa sama ya
kwarara uban ihu sannan ya ruga da gudu ya
durfafi maridan. Cikin hanzari sauran abokan
tafiyar suka yi koyi da shi.
Koda Haiman ya riski maridan sai ya hau su da
sara da suka cikin tsananin zafin nama ya rinka
tarwatsa su da karfin tsiya a guje yana samar
musu. hanya suna wucewa, amma takobin tasa
ba ta iya datsa jikinsu, sai dai mammake su suna
zubewa kasa, amma da zarar sun fadi sai su
mike zumbur a ci gaba da kasa tsere da su.
Jaruma Shadira, sadauki Imran, gimbiya Zarina,
gimbiya Rahila da boka Muzaffar ne suka rinka
taimakawa Haiman suna sara da dukan maridan
ta gefe da gefe, da kuma bayansu. Babban
abinda ya fi dugunzuma hankalin su Shadira shi
ne, a duk sa'adda maridan suka kawo musu
wafta ko sara da kaifafan faratan hannayensu
idan suka goce suka sami kasa sai ka ga sun
haifar da katon rami, idan kuwa bishiya suka
samu sai ka ga sun datsata gida biyu, in kuwa
dutse ne tarwatsewa yake ya farfashe. Haka
kuma zafin naman maridan ya wuce misali,

32

TASKARNOVELS.COM.NG
domin a cikin dakika biyu suna iya kawo hari
goma.
Nan fa maridan suka ruda su suka rikirkita su.
Idan ba don gimbiya Rahila na da matukar zafin
nama ba da karfin dantse da tuni maridan sun
gama hallaka dukkan abokan tafiyar da ke
bayan sadauki Haiman, domin ita ce take wata
irin gagarumar bajinta tana kare hare-harensu
ta hanyar shawagi a sama, tayi gabas, tayi
yamma, kudu da arewa tana saran maridan da
takobinta tana karkadar da su.Duk wannan
kokarin da Rahila ke yi sai ya
zamo a banza, domin ta kai cewa maridan sun
far make jaruman suna faduwa kasa suna dada
kai wawan taku da nufin mutsittsike su amma
sai ka ga Rahila na janye su daga kasan cikin
zafin nama tana kubutar da rayuwarsu. A haka
aka ci gaba da gudu ana daďa ratsawa ta cikin
maridan. Tunda sadauki Haiman yake gumura a
yaki bai taɓa tsintar kansa a cikin bala'i irin
wannan ba. Hatta bala'in da suka fuskanta a
wadanna dazuzzukan da suka wuce bai kai na
wannan ba. Lokacin da maridan suka ga an
dauki dogon lokaci suna artabu da wadannan
shu'uman mutane sai suka fara wani irin ihu
33

TASKARNOVELS.COM.NG
mai tsananin karfi wanda ka iya sa mutum ya
kurmance. Lokaci guda su Haiman suka kasa ci
gaba da gudu suka toshe kunnuwan da
hannayensu, damar da maridan suka samu ke
nan suka ritsa su a waje daya suka ci gaba da kai
musu sara da suka da faratansu.

Saboda karfin harin maridan da zafin namansu
ya zamana cewa tun jaruman na iya kare kansu
da makamansu har sun fara gajiya. Boka
Muzaffar aka fara cakawa tsinin farce a saman
kafadarsa. Farcen maridin ya faso ta bayansa,
Muzaffar ya kwarara uban ihu sakamakon
mugun zafin da yaji. Maridan na zare farcen
nasa daga cikin kafadar Muzaffar sai jini yai
tsartuwa, Muzaffar ya fadi kasa sumamme. A
sannan ne hankalin sauran jaruman ya
dugunzuma ainun domin sun zata ma boka
Muzaffar ya mutu. Shi kuwa Sarki Laffaru da ya
ga abin da ya faru ga boka Muzaffar abin
dogaronsa sai yai sauri ya kwanta a kasa ya yi
kamar ya mutu saboda sanin cewa ba zai iya
tsinana komai ba a wannan gumurzu.

34

TASKARNOVELS.COM.NG
A dai-dai wannan lokaci sadauki Imran ba
karamin kokari ya yi ba yana ta bubbuge
kawunan maridan da sandarsa kuma yana
samin damar tarwatsa su amma jaruma
Shardira ta fi shi kokari domin a duk sa'adda ta
dana kibiyoyinta ta harba sai dai ka ga kibiyoyin
na cakewa akan maridan suna faduwa kasa
amma saboda taurin ransu da nacinsu sai dai ka
ga sun sa hannu sun zare kibiyar sun mike tsaye
sun ci gaba da kai mugun hari duk da cewa jini
na zuba a jikinsu.

Ita kuwa jaruma Zarina abin da ya taimake ta
kawai shi ne, ta iya zulliya matuka. Duk ta inda
maridan suka kawo ma ta farmaki sai ka ga ta
goce ba sa samunta, amma tashin hankalinta shi
ne ta fara gajiya, don haka a ko yaushe komai
zai iya faruwa. Sadauki Shaharan ma karfin
gudunsa ne ya cece shi domin a tsakiyar
dodannin yake ta tsala gudu yana shiga
karkashinsu, wani lokacin har jikinsu yake hawa
yana gudu suna kawo masa mangari yana
gocewa. Inda matsalar take shi ne, shi ma ya
fara gajiya su kuwa maridan ko alamar gajiya ba
sa yi, kamar ma kara kuzari suke. Ana cikin haka
35

TASKARNOVELS.COM.NG
ne wani maridi mai shegen naci ya shammaci
Imran ya yi masa dundu a take Imran ya baje a
kasa da ruf da ciki a lokacin da ya ji kamar
kasusuwan bayansa sun kakkarye, don haka sai
ya kasa mikewa.

Maridin ya daga hannu zai caka faratansa a
gadon bayan Imran. Koda Shadira ta hango
abinda ke shirin faruwa sai ta daka wawan
tsalle daga inda take ta dira a inda Imran ke
kwance da nufin ta dauke shi, da yake zafin
naman Maridin ya fi nata, sai ya sami nasarar
kartar hannunta a lokacin da ta sami nasarar
janye Imran har ya juyo da fuskarsa ya ga irin
ceton da ta yi masa. Nan take hannun Shadira ya
dare jini ya yi feshi, itama ta kwala ihu kuma ta
fadi kasa a galabaice. Koda Imran ya ga yadda
Shadira ta ceci rayuwarsa kuma ya ga abinda ya
faru gare ta, sai ya fusata ainun ya daka tsalle
sama tamkar an cilla shi daga cikin baka ya
narkawa wannan maridi sanda aka. Take kan
maridin ya tarwatse ya kife a kasa matacce.

36

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ganin haka sai Imran ya buďu baki ya
buɗe muryarsa gaba daya ya yiwa sauran
abokan tafiya bushara da su yi kokarin dukan
kan maridan domin anan lagonsu yake. Kamar
maridan sun fahimci abinda Imran ya fadawa
'yan uwansa sai suka daina sunkuyo da
kawunansu. Nan fa bala'i ya kai bala'i, masifa ta
yi masifa, turnuku ya kara tsanani. Zarina na
cikin yin zilliya a karkashin maridan sai wani
maridi ya tarfa ta ya naushe ta a kirji ta baje a
kasa tana numfashi sama- sama, kuma tana gani
dishi-dishi. Kawai sai maridin ya daga kafarsa
zai tatsileta. Cikin bakin zafin nama Shaharan ya
janyeta daga kasan amma kafin
End Ads