Ramlatul Siyam ta
dako wawan tsalle ta dira a gabansa. Nan take
suka ruguntsume da azababben yaki, suka rinka
kai wa juna SARA DA SUKA cikin tsananin zafin
nama, juriya, naci da jarumtaka.
Karar haduwar takubbansu da ihunsu ne ya sa
Dakarun tsaron Gimbiya suka rugo izuwa cikin
turakar da suke fafatawa.
Koda suka ga ana tafka matsanaicin yaki
tsakanin Gimbiya da Najwar sai suka yunkura
404
TASKARNOVELS.COM.NG
za su kai wa Gimbiya Ramlatul Siyam dauki, sai
ta daka musu tsawa ta hanacsu.
Bisa dole suka tsaya suka yi cirko-cirko suka
zama 'yan kallo.
AL'AMARIN su Aljani Maruful Dauwaz kuwa, sai
da suka daɗe suna yawo da bilinbituwa a cikin
gidan sarautar sannan suka hango gidan
Gimbiya Ramlatul Siyam.
Tun daga nesa suka fahimci cewar ba lafiya ba,
domin Dakarun aljanun da ke shawagi a saman
gidan sun yi kaimi a wajen kewaya gidan kamar
za su afka cikin gidan. Haka ya sa su ma dakarun
bil'adaman da ke zagaye da gidan suka kasance.
Kash! Rashin sani ya fi dare duhu! Aljani
Maruful Dauwaz bai san cewa sihirin tsafi ba ya
405
TASKARNOVELS.COM.NG
tasiri a wajen dakarun da ke tsaron gidan
Gimbiya Ramlatul Siyam ba, saboda haka
lokacin da ya durfafi gidan a cikin siffarsa ta
ainahi, wato ta Aljani, ai kuwa sai suka yi caa! A
kansa suka kawo masa miyagun hare-hare masu
gaggawar tsinke numfashi.
In ba don Maruful Dauwaz yana da tsananin
bakin zafin nama ba da tuni sun daddatsa shi
gunduwa-gunduwa. Cikin tsananin zafin nama
ya daka tsalle ya bar inda yake, makaman
Dakarun suka karci kasa, kasar wajen ta
daddare.
Nan fa Aljani Maruful Dauwaz ya zare takobinsa
ya fada cikin miliyoyin Dakarun aka
ruguntsume da azababben matsanaicin yaki.
Ita ma Rahila sai ta zare takobinta ta taya Aljani
Maruful Dauwaz yakin, amma da ta ga yakin ya
fi karfinta, wato yawan Dakarun ya wuce misali,
kuma sihirin tsafi ba ya tasiri a kansu ba ta isa
406
TASKARNOVELS.COM.NG
ta ci gaba da yakar Dakarun ba sai ta yi wuf ta
suri Sarki Laffaru suka daka tsalle suka shige
cikin kunnen Aljani Maruful Dauwaz suka yi
lamo kamar babu su a wajen.
Shi kuwa Aljani Maruful Dauwaz sai ya zama
kamar shaidani a tsakiyar Dakarun. In yai sama
sai Dakarun aljanu su yanyame shi ya kasa
tsinana komai. Idan ya sako kasa kuwa sai
Dakarun bil'adama su yi masa rubdugu.
Nan fa hankalinsa ya dugunzuma ainun
musamman da ya fahimci cewar wadannan
Dakarun yaki masu tsaron Gimbiya Ramlatul
Siyam sun sami horon yaki na musamman kuma
su sihirin tsafinsu yana tasiri, amma duk wanda
ya zo gare su nasa sihirin tsafin ba zai yi tasiri a
kansu ba.
Aljani Maruful Dauwaz ya ji ya yi nadama
matuka da ya kawo kansa wannan wuri domin
bai ga ta yadda zai iya guduwa ba bare ya iya ci
407
TASKARNOVELS.COM.NG
gaba da yakin har ya sami nasarar hallakar da
Dakarun ya shiga cikin gidan Gimbiya Ramlatul
Siyam. Ko shakka ba ya yi idan aka ci gaba da
wannan bakin gumurzu a haka har izuwa wani
lokaci mai dan tsawo tabbas zai gaji, kuma da
zarar ya gajin za a sami nasarar hallaka shi.
Koda Maruful Dauwaz ya zo nan a zancen
zucinsa sai ya tuno da Rahila da Sarki Laffaru da
ke kan kafadarsa. Bisa mamaki sai ya ji ko
motsinsu ba ya ji akansa. Al'amarin da ya kara
dugunzuma hankalinsa ke nan, ya zata ko tun
sa'adda aka fara wannan gumurzu suka faɗo
kasa daga kansa aka mutsittsike su.
Nan fa ya raba hankalinsa biyu, wato ya ci gaba
da yakin kuma yana dira a kasa yana dube-dube
ko zai ga su Rahila, saboda idan har tabbatar da
cewa an kashe su bai ga amfanin wannan yaki
da yake yi ba tunda da ma saboda su yake yakin
domin idan anyi nasara su cika masa alkawarin
da ke tsakaninsu.
408
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda ya fara hakan sai Dakarun na sama da na
kasa suka sake yi masa rubdugu suka rinka kai
masa SARA DA SUKA gami da naushi da bugu ta
ko ina. Kaico! Idan aka yanka Kazar wuya to ba
makawa sai an fige ta.
Lokacin da Dakarun suka kara ZAGE DANTSE
akan Aljani Maruful Dauwaz sai ya zamana cewa
da kyar yake iya kare sara da sukan da suke
kawo masa, sai dai yana iya kare naushi da
bugu, su ma ba duka ba, domin akwai lokacin da
wani basamuden Aljani ya gabza masa wawan
naushi a baki. Ta ke hakorinsa guda yai fitar
burgu tare da wani gudan jini.
Nan take Aljani Maruful Dauwaz ya ga taurarin
wuya a idanunsa ya fara gani dishi-dishi, ya
shiga cikin wani irin mugun hali mai kama da
fitar haiyaci.
A sannan ne wani katon jarumin Aljani mai
nacin tsiya ya sami nasarar dankara masa sara a
409
TASKARNOVELS.COM.NG
gadon bayansa. Take gadon bayan ya dare,
Aljani Maruful Dauwaz ya kwarara uban ihu yai
katantanwa a sama har sau uku ya rikito kasa ya
baje a bisa turba cikin halin suma.
A daidai wannan lokaci ne Rahila da Sarki
Laffaru suka gangaro daga cikin kunnensa za su
fado kasa, sai Rahila tayi wuf ta kamo jelar wani
Aljani ta wurkila sama sau biyar kuma ta cafo
Sarki Laffaru da hannu daya ta dada jefa shi a
cikin kunnen Aljani Maruful Dauwaz ya kule a
ciki.
Ita kuma sai ta ci gaba da yakar Dakarun
aljanun na sama da na kasa tana shawagi akan
Maruful Dauwaz tana hana sauran Dakarun
samun nasarar karasa kashe Maruful Dauwaz.
Rahila tana wannan yaki ne da dukkan karfinta
cikin tsananin fusata domin ta san cewa idan ta
bari aka hallaka Aljani Maruful Dauwaz, to fa
410
TASKARNOVELS.COM.NG
komai ya dagule domin dayansu ba zai tsira da
rayuwarsa ba, kuma dukkan burinsu ya rushe.
Ita kanta Rahila ta yi matukar mamakin irin
wannan bajinta da take yi a cikin miliyoyin
Dakarun na aljanu da mutané.
To amma fa ta san cewa karshen tikatiki, tik! A
kodayaushe komai zai iya faruwa a gare ta
tunda dai ta kasa koda kashe Badakkare daya
daga cikin Dakarun. kuma ga shi Dakarun ba sa
gajiya kamar ma kara samun karfi da kuzari
suke. Ai kuwa ana dada kara samun wani dan
lokaci sai ita ma Rahila ta fara gajiya, Dakarun
bil'adaman da ke kasa suka fara yin tamaula da
ita.
Kafin a jima sun kumbura ma ta fuska kuma sun
hada ma ta jini da majina., in ba don ma tana da
tsananin karfin dantse ba da matukar juriya da
tuni sun daddatsa ta gunduwa-gunduwa.
411
TASKARNOVELS.COM.NG
Ai kuwa ba ta ankara ba sai ji ta yi an dankara
mata sara sau uku a lokaci guda. Saran farko a
bayan kafarta ta hagu. Na biyu a kafadarta ta
dama. Na ukun kuwa a gefen cikinta. Ko ina sai
da jini yai feshi. Rahila ta kurma uban ihu ta fadi
kasa rikica ko shurawa ba ta yi ba.
A daidai fuskar Aljani Maruful dauwaz ta fado.
Iskar da ta haifar ce ta sa Maruful Dauwaz ya
farfado daga dogon suman da ya yi. Yana bude
idanunsa ya yi arba da Rahila kwance a gabansa
kamar gawa. A daidai wannan lokaci ne Dakaru
suka sake tasowa za su afkawa Maruful Dauwaz
su yi gutsin-gutsin da sassan jikinsa.
Cikin bakin zafin nama mara misaltuwa Maruful
Dauwaz yai wuf! ya sure Rahila ya jefa ta cikin
kunnenesa ta kule a ciki tamkar an jefe guga
cikin rijiya, sannan ya daka wawan tsalle a ya ci
gaba da saran Dakarun yana naushi da bugunsu
duk a lokaci guda, kuma yana kwarara ihu mai
tsananin firgitarwa.
412
TASKARNOVELS.COM.NG
Tsananin karfin ihun nasa ne ya sa Dakarun
suka fara firgita, bisa dole suka rinka buďa masa
hanya yana durfafar kofar gidan. Babu abin da
zai bai wa mutum mamaki face yadda Maruful
Dauwaz ke wannan yaki cikin tsananin fushi,
juriya da naci duk da cewar jini na zuba a gadon
bayansa, kuma jiri na dibarsa. Kokarinsa shi ne
ya dangana da jikin kofar gidan ya ɓalla ta da
karfin tsiya.
Koda Dakarun suka gane nufin Maruful Dauwaz
sai su ma suka kara zage dantse suna kara yi
masa rubdugu amma sai suka kasa kai shi kasa
domin fatali yake yi da su da karfin tsiya yana
yin gaba.
Su kansu Dakarun sun yi matukar mamaki
domin ba su taɓa ganin sadauki mai bakin naci
irin nasa ba, domin dan karamin yanka ko sara
ma baya sa shi ya je kas, sai dai kawai ka ji yana
ihu sakamakon zafi da zogin da yake ji.
413
TASKARNOVELS.COM.NG
(SANNU MAURUFUL DAUWAZ,NSADAUKIN
SADAUKAI BABBAN MASOYI GA MARIGAYIYA
RASHMIN)
************
A can cikin turakar Gimbiya Ramlatul Siyam
kuwa, fadan da ake yi tsakanin sadauki Najwar
da Gimbiya Ramlatul Siyam ya yi tsamari ainun,
domin kowannensu ya gane kurensa. Duk da
cewar sun kasa koda lakutar jikin juna amma
kowanensu ya gabzawa kowa naushi da bugu.
Najwar ya yi matukar mamakin yadda aka yi
Ramlatul Siyam ta kasance gagarumar jaruma
Amma da ya tuna sadaukantakar mahaifiyarta
sai ya daina mamaki.
Lokacin da suka shafe sa'a uku suna
kwarmazuwa babu wanda ya sami nasarar kai
wani kasa sai duk suka ja da baya bisa dole suka
tsaya suna haki kamar Zakaru. A sannan ne
wadannan Dakaru da suka shigo turakar suka
414
TASKARNOVELS.COM.NG
sake yunkurawa za su afkawa Najwar amma sai
Ramlatul Siyam ta sake hana su suka ja da baya.
Koda ganin haka sai sadauki Najwar ya bushe
da dariya sannan ya maida takobinsa cikin kufe
sannan ya gyara tsayuwarsa yana mai dunkule
hannayensa biyu ya ce, "Tunda dai mun kasa
cutar da juna da makami ai sai mu fid da raini
da karfin dantse kawai".
Koda jin wannan batu sai jikin Ramlatul Siyam
ya yi sanyi kamar ba za ta amince ba. Daga can
kuma sai ta kwalla ihu ta rugo gare shi suka
kacame da sabon masifaffen yaki.
Tabbas Ramlatul Siyam ta yi ganganci domin
kwarewarta da sanin makama ba ta kai rabin ta
Najwar ba tunda shi ya saba da karo da mazaje
iri-iri hatta mahaifin nata ma da kyar yake
samunnasara a kansa bare ita da jarumtakar ta
ma ba ta kai ta mahaifin na ta ba.
415
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda suka fara kai wa juna naushi da bugu sai
Najwar yai wuf ya kama hannayen Ramlatul
Siyam ya murde su izuwa bayanta ya daure
hannayen da wata igiyar tsafi cikin zafin nama
sannan yai sauri ya dora wata wuka akan
wuyanta ya dakawa Dakarun da ke cikin turakar
tsawa ya ce, Su dare su ba shi hanya ko kuma ya
yanka ta!
Ba shiri Dakarun suka dare suka ba shi hanya ya
nufi kofar fita yana waige-waige da kallon
Dakarun don kada wani daga cikinsu ya
shammacecshi, yana mai ingiza Ramlatul Siyam
yana kuma daɗa rike hannayenta da karfi yana
harde kafafunta don kada ita ma ta
shammacecshi da kafar tata.
Koda suka iso daf da kofar fita sai kawai suka ga
an doko kofar da karfin tsiya. Take kofar ta fado
ciki ta fadi kasa rikica, sai ga Aljani Maruful
Dauwaz ya baiyana dauke da jaruma Rahila. Shi
da Rahilan duk jikinsu ya yi kaca-kaca da jini
har suna layi kamar za su fadi kasa.
416
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Najwar ya yi arba da su sai ya cika da
tsananin mamaki domin bai taɓa ganin
mahalukin da aka kulle a cikin wannan kurkuku
har ya samu damar fita sai su.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin Sadauki
Najwar da kuma Aljani Maruful Dauwaz. Daga
can sai Najwar ya tuntsure da dariya ya dubi
Maruful Dauwaz ya ce, "Ku ba ni hanya na wuce
ko kuma na sa a karasa hallaka ku. Kun san dai
na fi karfinku tunda na kara da ku kun gani."
Koda jin wannan batu sai Rahila ta dakawa
Najwar tsawa ta ce, "Ai tsakaninmu da kai yanzu
babu yarda ko bin umarni tunda mun gane cewa
kai mayaudari ne kuma maci amana. Tunda har
ka ci amanar Sarkinka to babu wanda ba za ka ci
amanarsa ba.
Ka sani cewa mun baro kasashenmu da komai
namu domin mu mallaki Gimbiya Ramlatul
417
TASKARNOVELS.COM.NG
Siyam, kuma mun sha bakar wahala har mun
kusa rasa rayuwarmu. Babu irin bala'in da ba
mu haɗu da shi ba bisa wannan TAFARKI. Shin
kana zaton cewa akwai wani abu da zai iya
firgita a yanzu?
Bama kai ba, ko Sarkinka ne muka yi fito-na-fito
da shi a wannan lokaci ba za mu gudu ba bare
mu janye bisa abin da ke gabanmu. Kawai ka ba
mu Gimbiya Ramlatul Siyam idan ba haka ba
kuwa sai dai mu ci gaba da yaki mai rabo ka
dauka."
Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ga an
watso Dakaru daga cikin turakar sun baje a kasa
matattu kimanin su dubi dari da doriya, sannan
kuma suka ji an ci gaba da mummunan yaki a
can wajen gidan.
Ihun mazaje da karar haduwar makamai sun
cika dodon kunne.
418
TASKARNOVELS.COM.NG
Ashe zuri'ar su Aljani Barukul Masnur ne suka
kawo wa sadauki Najwar dauki domin sun gaji
da zaman jiransa a can fada.
Wohoho! Nan fa gidan Gimbiya Ramlatul Siyam
ya daďa hargitsewa, cikinsa da wajensa aka ci
gaba da azababben yaki.
Maruful Dauwaz da Rahila suka afkawa Najwar
suna kokarin kwatar Gimbiya Ramlatul Siyam
daga hannunsa, amma sai suka kasa.
Su Aljani Barukul Masnur kuwa, sai suka rabu
zuwa kaso biyu, kaso daya suka tari Dakarun da
ke kofar gidan Gimbiya, kaso daya kuma suka
tari Dakarun da ke ciki aka ci gaba da BAKIN
ARTABU. Nan fa aka rinka ragargaza maza,
kasuwar cinikin daukar rayuka ta baje kolinta.
Sassan jiki na aljan da na bil'adama ya dinga
yawo a sararin samaniya.
419
TASKARNOVELS.COM.NG
Jini kuwa ya rinka feshi da fantsama ya wanke
gaba dayan ginin gidan ciki da waje kai kace
sabon shafe aka yi da shi.
Sai da Najwar ya sumar da Maruful Dauwaz da
Rahila sau bakwai-bakwai, amma saboda naci
da zarar sun farfado sai ka ga sun tashi an ci
gaba da yaki da su.
Babu yadda Najwar bai yi ba akan ya fice da
Gimbiya daga cikin wannan gida nata amma abu
ya gagara domin koda ya bazar da su Maruful
Dauwaz sun zube kasa sumammu da ya tunkari
bakin kofar fita sai ka ga Dakarun da ke tsaronta
sun sake yi masa rubdugu sun hana shi sakat.
Hakika a wannan lokaci sai da Rahila da Maruful
Dauwaz suka gane kurensu kuma suka jiyo
kamshin mutuwa. Duk su biyun babu wanda bai
sami raunika a jikinsa ba sana da guda arba'in.
420
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da su Merful Dauwaz suka yi suma na
bakwai ne, Najwar ya zare wadansu gajerun
wukake biyu daga jikinsa da nufin ya fafe
cikinsu Maruful Dauwaz.
Koda Gimbiya Ramlatul Siyam ta ga abin da te
shirin faruwa sai ta daga kafarta ta gaban
fuskarta ta doki fuskar Najwar.
Cikin gigicewa yai tsalle sama da baya. Kafin ya
duro kasa sai ita ma ta daka tsalle sama ta tare
shi ta zare wata wukar a jikinta ta soka masa ita
a makoshinsa. Najwar ya kurma uban ihu a
lokacin da jini yai tsartuwa daga cikin
makoshinsa, suka rikito kasa tare.
Najwar ya baje a kasa yana kakarin mutuwa.
A dai-dai wannan lokaci ne Dakarun da ke
tsaron Gimbiya suka gama kashe gaba dayan
zuri'ar su Aljani Barukul Masnur. Sai ga shi
babban cikin Dakarun gidan ya shigo rike da
kan Aljani Barukul Masnur a hannunsa jini na
421
TASKARNOVELS.COM.NG
ďiga a jikin kan, yai nuni da kan izuwa ga
Gimbiya Ramlatul Siyam kuma ya risina ya ce,
"Ya shugabata mun gama da dukkan maciya
amanar mahaifinki".
Gimbiya Ramlatul Siyam ta yi murmushi ta ce,
Ni ma na gama da shugabansu ga shi a kwance
zai mutu".
Ramlatul Siyam ta yi nuni da sadauki Najwar
wanda ke kwance a kas male-male a cikin jini
har a sannan bai daina kakarin mutuwa ba.
Ramlatul Siyam ta tofa wa Najwar yawu a fuska
ta ce, "Wannan shi ne sakamakon maci amana
irinka!"
A dai-dai waunan lokacie Rahila da Aljani
Maruful Dauwaz suka furtado suna numfashi
sama-sama kuma suna gani dishi-dishi. Koda
422
TASKARNOVELS.COM.NG
ganin haka sai shugaban Dakarun gidan ya
yunkura zai karasa kashe su Maruful Dauwaz
amma sai Ramlatul Siyam ta daka masa tswa ya
dakata.
Shugaban Dakarun ya dubi Ramlatul Siyam
cikin tsananin mamaki ya ce, "Haba ya
shugabata, saboda me za ki hana ni hallaka su
alhalin sun kasance manyan abokan gaba
waɗanda suka zo domin su sace ki su raba ki da
mahaifinki kuma su raba ki da wannan daula da
kike ciki wacce babu inda za ki sami irinta a
wannan duniya?"
Sa'adda shugaban Dakarun ya zo nan a
zancensa sai ya ga Gimbiya Ramlatul Siyam ta
sunkui da kanta kas ta yi shiru. Nan take
idanunta suka ciko da kwalla har hawaye ya
zubo mata sannan ta dago da kanta ta ce, "Ai
tuni na rabu da mahaifina domin ba zai taɓa
dawowa ba, tun ranar da ya bar gida na san
cewa mun yi bankwanan karshe ba za mu sake
saduwa ba har abada.
423
TASKARNOVELS.COM.NG
Hakika lokaci ya yi da zan bar ku domin na je na
fuskanci rayuwata ta gaba domin ita ce
kaddarata, tabbataccen al'amarin da ba zai
shafu ba.
Daga yau gabadayan Hadiman da ke cikin
Wannan gida kun sami 'yancin kanku,
kowannenku yana da damar tafiya inda yake so
a cikin wannan duniya domin ya fara sabuwar
rayuwa. tabbas wannan masarauta sai dai a
tuna da ita a tarihi amma ta ruguje ke nan. Idan
kun so za ku iya nada sabon Sarki daga cikinku
wanda zai ci gaba da jagorantarku".
Koda gama fadin haka sai Ramlatul Siyam ta sa
aka shiga yi wa Rahila da Aljani Maruful Dauwaz
magani domin a ceto rayuwarsu.
A daidai wannan lokaci ne Sarki Laffaru ya fito
daga cikin kunnen Aljani Maruful Dauwaz. Koda
yai arba da miliyoyin gawarwakin da ke cikin
424
TASKARNOVELS.COM.NG
falon kuma ya ga Gimbiya Ramlatul Siyam tsaye
a gabansa ga su Maruful Dauwaz a kwance ikin
mugun yanayi mai kama da suma ko Imutuwa
sai ya firgita ainun ya yunkura zai koma cikin
kunnen Aljani Maruful Dauwaz.
Caraf! Sai Gimbiya Ramlatul Siyam ta cafo
hannunsa tana mai yi masa murmushi ta ce,
"Haba ya kai mijina na gobe tsoron me kuma za
ka ji alhalin komai ya zo karshe, burinka na daf
da cika".
Koda jin wannan batu sai Sarki Laffaru ya yanke
jiki ya gangaro daga kan Aljani Maruful Dauwaz
a sume saboda tsananin mamaki da farin ciki.
Bai farfado ba sai bayan sa'a uku.
(
yasin Laffaru ya cika ďan sa'a)
Yana farfaɗowa ya ga Aljani Maruful Dauwaz
zaune daf da shi yana ta faman shara kuka.Ba
komai ne ya sa Maruful Dauwaz yin wannan
kuka ba face ganin Rahila a cikin mugun yanayi
425
TASKARNOVELS.COM.NG
saboda Likitoci sun taru a kanta suna iya yinsu
amma har a sannan tana numfashi sama- sama.
Su kansu Likitocin guiwoyinsu sun yi sanyi sun
sallama cewar abu ne mawuyaci ta yi nisan
kwana ko kuwa ta rayu.
Maruful Dauwaz ya ci gaba da rusa kuka kamar
ba zai daina ba saboda ya san cewa idan Rahila
ta mutu shi ke nan ba zai ga wasiyyar
masoyiyarsa ba marigayiya Gimbiya Rashmin.
Babban abin bakin cikin ma shi ne, Rahila ba ta
iya koda bude bakinta ma bare ta yi magana ta
gaya masa inda ta ɓoye wannan wasiyya ta
masoyiyarsa
Bayan Maruful Dauwaz ya dade yana kuka, sai
Gimbiya Ramlatul Siyam da Sarki Laffaru suka
kamu da tsananin tausayinsa suka shiga
rarrashinsa har Ramlatul Siyam ta kwantar
masa da hankali. tana cewa, ya yi hakuri babu
mamaki nan da wani lokaci ta iya bude bakinta
har ta yi magana".
426
TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin alamun karayar zuci Aljani Maruful
Dauwaz ya share hawayen idanunsa ya dubi
Gimbiya Ramlatul Siyam ya ce, "Ya ke wannan
yar Sarki, ki yi sani cewa ni kam na cire rai da
rayuwar Rahila, don haka rayuwata ba ta da
wani sauran amfani a doron kasa.Ki sani cewa
na yi matukar mamaki da kika hana a kashe mu.
Shin za ki iya gaya mana dalilin da yasa kika
hana a kashe mu har kika sa aka ceto
rayuwarmu? Wannan ita ce kadai alfarmar da
nake nema a wajenki kafin na yi sallama da
wannan duniya".
Lokacin da Gimbiya Ramlatul Siyam ta ji
wannan tambaya daga bakin Aljani Maruful
Dauwaz sai hawaye ya zubo ma ta ta ce, "Ya kai
Sarkin sadaukan aljanu, ka yi sani cewa ni a
rayuwata tun ina yarinya karama duk abin da
zai same ni sai an nuna min shi a mafarkina.
427
TASKARNOVELS.COM.NG
Kuma duk mafarkin da na yi sai ya tabbata a
gaske. Fiye da shekaru biyar baya da suka shude
na gani a cikin mafarkina cewar Daular Mulkin
Mahaifina za ta rushe kuma zai bar gida don
tafiya neman wani mashi da ake kira Galilu
Harus.
Idan ya tafi neman wannan mashi ba zai dawo
ba, a can zai mutu wajen fafatawa da wanda ke
rike da mashin.