ya bude fuka-fukansa
ya tashi da su sama ya keta ta cikin rufin saman
kogon kamar yadda danshi ke tsattsafowa daga
cikin kasa.
Nan da nan ya luluka a cikin gajimare ya fara
tsala azababben gudu tamkar giftawar
tauraruwa mai wutsiya.
245
TASKARNOVELS.COM.NG
A daidai wannan lokci ne Rahila ta tuno da
sauran abokan tafiyarsu wadanda suka baro a
cikin kogon Darul Iksina. Nan take hankalinta ya
dugunzuma ta dubi Aljani Maruful Dauwaz ta ce,
"Kash! Na manta ban nemi alfarma a wajenka ka
ceto rayuwar sauran abokan tafiyarmu da muka
baro a cikin kogon Darul Iksina".
Koda jin haka sai Aljani Maruful Dauwaz ya
gyada kai cikin alamun takaici da tausayi ya ce,
"Ai kuwa kin yi babban kuskure domin yanzu
bakin Alkalami ya bushe. Babu wani mahaluki
da ya isa ya shiga cikin daya daga cikin gidajen
da ke kogon Darul Iksina face ya zama gawa. Ni
kaina na manta da batun abokan tatiyar taku
kuma ya kamata ki yi mini uzuri saboda mu
aljanu babu halittar da ta fi mu yawan
mantuwa".
Koda jin haka sai hankalin Rahila ya sake
dugunzuma ainun ta ce, "Yanzu kana ganin
kuwa su Imran za su iya fitowa daga cikin kogon
Darul Iksina?"
246
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan tambaya sai Aljani Maruful
Dauwaz yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "Tun
kimanin shekaru dubu uku baya da wanzuwar
kogon Darul Iksina babu wani mahaluki walau
mutum ko aljan da ya taɓa shiga cikinsa ya fito a
raye sai ni din nan yanzu sai kuma ku biyun nan.
Saboda haka ba ni da wata amsa da zan iya ba ki
akan wannan tambaya. Amma dai na san cewa
in ba wanda ya san dalasiman tsafin da ake
karantawa ba kofar kogon ta bude babu wanda
zai iya shiga cikinsa ko kuma ya fito daga
cikinsa. Ina tabbatar miki da cewa duk duniya
babu wanda ya san wadannan dalasiman tsafi
face mutum daya da Aljani daya.
ba wasu ba ne face ni kaina da kuma wannan
hatsabibin Boka naku, wato Boka Muzaffar
wanda a halin yanzu na san tuni ya ďauki mashi
galilul Haras ya tafi da shi izuwa can dakin
halwar tsafinsa.
247
TASKARNOVELS.COM.NG
Ba zai fito ba daga cikin dakin tsafin nasa sai
bayan cikar kwana arba'in. A ranar da ya fito ne
zai mallaki kowa da ke cikin wannan duniya,
kun ga ke nan, gagarumin aikin da ke gabanmu
ba kadan ba ne. Ya zama dole mu yi iya
kokarinmu mu tabbatar da cewa mun sami
nasarar sato Gimbiya Ramlatul Siyam gami da
yawun barcin mahaifinta kafin cikar kwana
arba'in din har mu je mu binne yawun a can
gidan tarihi na Birnin Kisra. Ku sani cewa
samun nasarar wadannan abubuwa biyu dai-dai
yake da tafiya neman Jaki mai kaho!
Lokacin da Aljani Maruful Dauwaz ya zo nan a
jawabinsa sai jikin Rahila da na Sarki Laffaru ya
yi sanyi matuka kuma hankalinsu ya
dugunzuma ainun suka sami karayar zuciya bisa
samun nasara akan wannan gagarumar bukata
tasu don haka duk su biyun sai suka yi shiru
suna tunani.
Sa'adda Aljani Maruful Dauwaz ya ji su Rahila
sun yi shiru sai ya bushe da dariya sannan ya ce,
"Ya ku abokan alkawarina, kada ku dakushe
248
TASKARNOVELS.COM.NG
zuciyoyinku da tunanin rashin samun nasara.
Ku sani cewa tsakanin RASHI DA SAMU taki ne
dan mitsitsi. Tabbas matsoraci ba zai taba zama
gwani ba, kuma sai an gwada akan san na
Kwarai. Lallai za mu siyar da rayuwarmu ko don
mu ceto mutanen duniya daga sharrin Boka
Muzaffar domin idan ya fito daga wannan
halwar tsafi ta kwana arba'in sai ya buwayi
mutane da aljanu. Kai hatta dabbobi ma da ke
cikin daji sai sun shiga uku. Yanzu sai ku fada
mini inda za mu je mu keɓe kanmu domin ina
son ni ma na shiga halwar tsafi ta kwana uku
rak saboda na gano matsalolin da za mu
fuskanta ya yin da muka tafi izuwa Birnin Hindu
don sato Ramlatul Siyam da samo yawun barcin
mahaifinta, na san yadda zan tare su kuma na
gano yiwuwar samun nasararmu da rashinta".
Koda jin haka sai Rahila ta dubi Sarki Laffaru ta
ce, "Ko Birninka za mu je ne? Laffaru ya zazzaro
idanu ya ce, "Shin kin mantane da bala'in da
nake ciki? Yanzu haka Sharlis tana nan a
masarautata ta dora danta Shadaddu akan
karagar mulkina.
249
TASKARNOVELS.COM.NG
Burinta shi ne yanzu ta kama ni ta tsare har sai
danta ya girma sannan ya yi mini KISAN GILLA
bayan ya yi mini mugun wulakanci ya tozarta ni
a kasata gaban talakawana.
Ni a yanzu ma in ban da muna tare da Maruful
Dauwaz da ba zan taba samun kwanciyar
hankali ba. Abin da nake bukata yanzu shi ne,
idan Maruful Dauwaz ya shiga halwar tsafinsa
ya yi mini bincike shin gaskiya ne idan na auri
Gimbiya Ramlatul Siyam zan haifi 'yar da za ta
kare ni daga sharrin dana Shaddadu? Hakika na
tsorata da maganganun Boka Muzaffar babu
mamaki karya ya shirya mini".
Koda jin haka sai Aljani Maruful Dauwaz ya
bushe da dariya sannan ya ce, "Ya kai wannan
Sarki, ka kwantar da hankalinka ka sani cewa na
yi maka alkawari muddin muna tare babu abin
da zai same ka, amma fa sai idan ka tabbatar da
cewa a zamanin da kana kan sarautarka ba ka yi
mulkin Zalinci ba domin ni a rayuwata babu
250
TASKARNOVELS.COM.NG
abin da na tsana sama da zalunci, cin amana da
rashin gaskiya."
Koda Sarki Laffaru ya ji wannan batu sai
hankalinsa ya dugunzuma kuma cikinsa ya duri
ruwa domin ya san cewa a lokacin mulkinsa ne
ya zalunci Sharlis da zuri'arta kuma a dalilin
haka ne mahaifinta ya yi gagarumin tanadi na
daukar fansa akansa.
Nan take Laffaru ya aiyana a zuciyarsa cewar ba
zai taɓa gaya wa Aljani Maruful Dauwaz
gaskiyar labarinsa ba bisa irin mulkin zaluncin
da ya yi a kasarsa da yadda ya cutar da Sharlis
dadanginta.
Haka dai Aljani Maruful Dauwaz ya ci gaba da
tsala gudu a sararin samaniya har izuwa tsawon
sa'a biyar ya zamana cewa Rahila da Laffaru ba
su kara cewa uffan ba har ma suka fara
gyangyadi.
251
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Aljani Maruful Dauwaz ya fahimci halin da
suke ciki sai ya dan kada jikinsa suka farka a
firgice. Aljani Maruful Dauwaz ya ce da su, "Ku
yi hakuri na tashe ku daga barci, hakan ta faru
ne saboda har yanzu ba ku zaɓi inda ya kamata
mu je ba. Muna bukatar inda za a karɓe mu
hannu biyu kuma mu sami damar gudanar da
harkokinmu cikin sirri".
Caraf! Sai Lahir ta ce, "Mu je kasarmu dornin a
can ne nake da yakinin ba za mu fuskanci wata
matsala ba, kuma ina son na sake saduwa da
mahaifinatun gabannin burina ya gama cika
saboda na san cewa na bar mahaifina a cikin
kewata".
Koda jin wannan batu sai Aljani Maruful
Dauwaz ya bushe da dariya ya ce, "Tabbas kin yi
mana zaɓin wuri mafi dacewa kuma ina mai yi
miki albishir da cewa kafin cikar rabin sa'a za
mu isa Birninku na Shauful".
252
TASKARNOVELS.COM.NG
Kamar yadda Aljani Maruful Dauwaz ya fadi
haka al'amura suka kasance, wato a cikin rabin
sa'a cif suka iso kofar Birnin Shaufi.Nan take
Aljani Maruful Dauwaz ya sauko kasa ya dira daf
da Birnin ya zamana tazararsa da bakin kofar
garin bai wuce taku ashirin ba.
Koda masu gadin kofar Birnin suka yi arba da
Aljani Maruful Dauwaz sai suka firgice suka
ruga izuwa cikin gari suna ihu, dayansu bai yi
jarumtakar tsayawa ba duk da cewa yawansu ya
kai dari uku. Saboda tsananin razanar da suka yi
basu ma lura da cewa Aljani Maruful Dauwaz na
dauke da 'yar Sarkinsu ba, wato GIMBIYA
RAHILA.
Nan da nan labari ya riski Sarki cewar ga wani
bakon Aljani wanda babu mai girmansa daga
cikin aljanun duniya ya sauka a kofar gari. Koda
jin wannan batu sai Sarki ya mike tsaye zumbur
ya sa aka busa kahon fita yaki. Nan da nan
Dakaru suka shiga shiri ka rifa debo makaman
yaki. Shi ma Sarkin ya ruga izuwa cikin
turakarsa ya yi damarar yaki ya debo dukkan
253
TASKARNOVELS.COM.NG
gurayensa da layunsa na tsafi ya sanyasu a
jikinsa sannan ya jagoranci Dakarun yakin nasa
kimanin su dubu dari uku suka yi hawa bisa
dawakai rike da muggan makamai suka
sukwane su i zuwa can kofar gari.
Da isar wannan runduna bakin kofar gari sai
gaba dayan dawakan nasu suka firgice suka
kama tirjiya da haniniya, suna daga kafafunsu
sama suna zubar da mahayansu, kuma suna
komawa da baya a guje izuwa cikin gari.
Ba komai ne ya haddasa hakan ba face tsorata
da dawakan suka yi sakamakon yin arba da
Aljani Maruful Dauwaz saboda kwarininsa da
cikar surarsa ta sadaukantaka da girman
halittarsa.
Dokin Sarkin kadai ne bai juya da baya ba amma
shi ma ya tsorata ainun da ganin Aljani Maruful
Dauwaz. Shi kansa Sarkin taurin zuciya da
254
TASKARNOVELS.COM.NG
kishin mulkinsa ne da jama'arsa ya sa ya dake
ya ki ya gudu.
Koda ya dubi mutane biyu da ke kan Aljanin da
kyau sai ya shaida 'yarsa Gimbiya Rahila. Cikin
tsananin farin ciki ya duro daga kan dokin nasa
ya ruga izuwa inda Aljani Maruful Dauwaz yake.
Itama Rahila sai ta duro kasa daga kan Maruful
Dauwaz ta ruga izuwa wajen Sarki.
Suna haduwa suka rungume junansu cikin farin
cikin sake saduwa. Sarki ya yi ta sumbatar
fuskarta da gashinta kamar ba zai daina ba.
Bayan sun nutsu sai ya dube ta ya ce, "Ya ke
'yata ki gayawa abokin tafiyarki Sarki Laffaru
cewa shin ya taba cika alkawari a rayuwarsa
kuwa?"
Koda jin haka sai Laffaru ya bushe da dariya
sannan ya sauko da sauri daga kan Aljani
Maruful Dauwaz ya ruga izuwa wajen mahaifin
Rahila ya mika masa hannu suka gaisa sannan
255
TASKARNOVELS.COM.NG
ya ce, yau ne ranar farko a rayuwata da na taba
cika alkawari dawo maka da 'yarka cikin koshin
lafiya".
Sarki ya yi murmushi ya ce, "Ai dama ba kai ba
ne ka dauki wannan alkawari ba, Boka Muzaffar
ne, ina kuka baro shi?
Koda jin wannan tambaya sai Rahila da Laffaru
suka yi sunkui da kansu kas sukai shiru ba su ce
komai ba. Rahila ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce,
"Labari ne mai tsawo sai mun zauna. Yanzu dai
mu shiga cikin gari domin jama'a su ganmu tare
hankalinsu ya kwanta."
Sarki ya yi murmushi ya ce, "Kin yi gaskiya yake
'yata, amma ku gayawa wancan abokin tafiya
taku ya tsaya anan kadanya biyo mu domin
koda an ganshi tare da mu sai jama'a sun firgice.
Wai shin ma wane ne shi?"
256
TASKARNOVELS.COM.NG
Rahila ta yi murmushi ta ce, "Wannan shi ne
Sadaukin Sadaukan aljanun duniya, jarumi uban
jarumai dodon maza kuma gwarzon mayaki
ma'abocin gaskiya da amana, Aljani Maruful
Dauwaz."
Koda jin wannan batu sai Sarki ya cika da
tsananin farin ciki ya ruga izuwa wajen Aljan
Maruful Dauwaz ya rungurne shi yana mai cewa
"Lale marhaban da babban bako aminin
Talmara ibni Saumur.
Koda jin wannan batu sai jikin Aljani Maruful
Dauwaz ya kara yin sanyi, kuma ya ji ya kara
aminta da Gimbiya Rahila dari bisa dari.
Nan dai Sarki, Rahila da Sarki Laffaru suka
dunguma suka tafi izuwa cikin gari suka bar
Aljani Maruful Dauwaz anan bayan gari yana
mai warwasa kafarsa yana rangadi domin
rabonsa ma da ya wasa kafafunsa bisa turba
shekaru dubu biyu da dari biyu ke nan.
257
TASKARNOVELS.COM.NG
Da shigarsu cikin gari jama'a suka ga Sarki tare
da 'yarsa Rahila sai suka cika da tsananin
murna. Nan fa aka shiga taya shi murna.
Nan da nan gari ya gauraye da kade-kade da
raye-raye. Sarki, Laffaru da Rahila suka shige
izuwa cikin gidan sarauta suka zauna a cikin
dakin cin abinci aka kawo musu nau'in abinci
iri-iri sama da kala dari.
Nan fa Sarki Laffaru ya bude cikinsa ya yi ta zuri
domin rabonsa da cin lafiyayyen abinci haka tun
kafin ya baro Birninsa.
Tuni Sarki yasa aka gyara manyan raguna guda
arba'in gami da ruwa cikin duro arba'in ya ce a
kaiwa Aljani Maruful Dauwaz ya fara taɓawa
kafin a kawo masa nau'in abinci.
258
TASKARNOVELS.COM.NG
Da kyar aka sami wadansu dakakkun Dakaru
masu taurin zuciya suka daure suka mika
wannan sako. Koda Maruful Dauwaz ya ga an
kawo masa wannan abinci sai shi ma ya cika da
tsananin farin ciki domin ya shafe dubunnan
shekaru bai ci irinsa ba, sai ma wanda ya fishi
dadi da ni'ima a cikin kogon Darul Iksina. A
wannan rana dai sai da Rahila da Sarki suka
raba dare suna hira inda ta kwashe labarin duk
abin da ya faru a cikin wannan tafiya tasu ta
zaiyane masa tun daga lokacin da su Boka
Muzaffar suka zo suka dauke ta a gida kawo
izuwa sa'adda suka sami nasarar keta
wadannan dazuzzukan guda biyar har suka isa
kogon Darul Iksina da yadda suka hadu da
Aljani Maruful Dauwaz suka baro su jarumi
Imran a can.
Koda mahaifin Rahila ya ji wannan labari sai ya
kamu da tsananin tausayi, bai san sa'adda ya
kama zubar da hawaye ba kuma ya cika da
tsananin mamaki bisa yadda Boka Muzaffar ya
yaudari sauran abokan tafiyarsa ya jefa su cikin
masifa haka.
259
TASKARNOVELS.COM.NG
Bugu da kari, sai hankalinsa ya dugunzuma
ainun da ya ji cewar Boka Muzaffar ya mallaki
Mashin Galilul Haras domin yana da cikakken
tarihin mashin, ya san cewa duk wanda ya
mallake shi zai iya mallakar duniya gaba
dayanta. Sai da mahaifin Rahila ya shafe lokaci
mai tsawo yana juya al'amarin a cikin zuciyarsa
sannan ya yi ajiyar zuciya ya dubi Rahila ya ce,
"Ya ke 'yata, ki yi sani cewa aikin da ke gabanku
ba karami ba ne domain yaki da Sarki Nashmir
na Birnin Hindu daidai yake da ninkin wahalar
da kuka, sha a dazuzzuka biyar din da kuka
ratsa kuka je kogon Darul Iksina. Kuma tabbas
babu wani Aljani da zai iya kai ku fadar Sarki
Nashmir har ku iya dauko 'yarsa kuma ku samo
yawun barcin bakinsa face Maruful Dauwaz.
Ni babban abin da nake ganin cewa ma ba za ku
iya samowa ba shi ne, yawun barcin Sarki
Nashmir, domin ga yadda na sami labari a wajen
masana, Sarki Nashmir bai taɓa yin barcin dare
ba kuma a duk tsawon mako guda sau daya
yake barcin sa'a shida da rana. Babu
260
TASKARNOVELS.COM.NG
takamaiman ranar da ya ware domin yin barcin
nasa. Ma'ana ranakun Litinin zuwa lahadi bai
ware ranar yin barcin ba a kowacce rana zai iya
yin barcin kuma a kowanne lokaci kin ga ke nan,
ba karamin dace za ku yi ba ku riski lokacin
barcin nasa.
To wai shin ma ta yaya za ku iya shiga Birnin
nasa ma bare har ku shiga gidan sarautarsa
alhalin duk duniya babu wani wuri da ya kai
masarautarsa tsaro? In ba don ba a raba rai da
buri ba, da sai na ce ku hakura da wannan
bukata domin ban ga yiwuwar hakan ba."
Lokacin da mahaifin Rahila yazo nan a zancensa
sai Rahila ta ji zuciyarta ta karaya kuma nan
take hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa
abin da ke mata dadi a duniya, amma da ta tuna
irin bakar wahalar da suka sha a cikin tafiyarsu
ta zuwa kogon Darul Iksina da yadda suka tsira
da rayuwarsu a lokacin da basu taɓa zaton
samun kuɓuta ba sai ta sake samun kwarin
guiwa ta dubi mahaifin na ta ta ce, "Ya kai
Abbana kayi sani cewa babu wani abu da zai
261
TASKARNOVELS.COM.NG
gagara a wannan duniya, don haka ba na fid da
rai ga samun nasara bisa wannan gagarumin
aiki da ke gabanmu face ba ma numfashi a
doron kasa. Lallai za mu ba iwa Aljani Maruful
Dauwaz dama ya shiga halwar tsafinsa ta kwana
uku domin ya binciko mana ta yadda za mu
fuskanci wannan gagarumar tafiya ta neman
ceto rayuwar dukkan mutanen duniya da
aljanun duniya daga sharrin azzalumi bakin
mugu Boka Muzaffar. In da sauran Sarakunan
duniya sun san halin da ake ciki da tabbas sun
ba mu hadin kai an hada KARFI DA KARFE an
tafi wannan gagarumin aiki".
Sa'adda Rahila ta zo nan a jawabinta sai
mahaifinta ya kawo gwauron numfashi da ajiye
sannan ya dube ta ya ce, "Ya ke 'yata ina
tabbatar miki da cewa da yawan manyan
Bokayen duniya sun san halin da ake ciki, kuma
sun sanar da Sarakunansu tsananin tsoron Sarki
Nashmir ne ya sa kowa ba zai iya hada kai da ku
ba.
262
TASKARNOVELS.COM.NG
Duk fadin wannan duniya mutum daya ne
wanda inda zai hada kai da ku da sai kun sami
nasara farat daya akan Sarki Nashmir.
Ba wani bane wannan mutum face Sharlisa
mahaifiyar yaro Shadadd, wanda a nan gaba zai
yi shuhura ya zamo gagarumin jarumin da ba
shi da sa'a.
Ko hauka ne ya sami Sharlisa ba za ta taбa hada
kai da ku ba saboda idan ta yi hakan ba za ta
taɓa cika burinta na son daukar fansa akan
Sarki Laffaru ba.
A yanzu haka Sharlisa tana nan tana shiri da
bincike akan yadda za ta tarwatsa dukkan
shirinku, don haka, ku yanzu bala'i biyu ne a
gabanku, akwai na Sarki Nashmir kuma akwai
na Sharlisa. Shi kansa Sarki Nashmir a halin
yanzu yana kan shirye-shiryen yadda zai kwace
mashin Galilul Haras daga hannun Boka
Muzaffar domin ya san cewa ya dauko mashin
263
TASKARNOVELS.COM.NG
daga kogon Darul Iksina kuma in dai ya
kammala aikin da yake yi a yanzu acikin dakin
halwar tsafinsa na tsawon kwanaki arba'in
tabbas sai burinsa ya cika.
Ita ma Sharlisa yanzu hankalinta ya rabu gida
biyu, domin tana son ta tarwatsa shirinku kuma
tana son ta mallaki wannan sihirtaccen mashi
na Galilul Haras.
Saboda haka, BAKIN ARTABUN da za a yi akan
wannan mashi yafi karfin masifar YAKIN
DUNIYA gaba daya. Ya ke 'yata, ki yi sani cewa
tun kafin ku iso nan na yi bincike a cikin tawa
halwar tsafin na ga dukkan wannan al'amari."
Yayin da mahaifin Rahila ya zo nan a jawabinsa
sai hankalin Rahila ya dugunzuma ainun fiye da
ko yaushe, ta ji kamar ta tashi a sannan ta tafi
izuwa masaukin Sarki Laffaru domin ta sanar da
shi halin da ake ciki su dunguma su je bayan
gari wajen Aljani Maruful dauwaz shi ma su
sanar da shi don su san irin sabon shirin da ya
kamata su yi bisa wannan al'amari.
264
TASKARNOVELS.COM.NG
Daga can kuna sai ta taushi zuciyarta ta ce a
cikin ranta, "Tunda dai Maruful Dauwaz ya ce
zai shiga halwar tsafi ta kwana uku domin ya yi
nasa binciken ya kamata na saurara na ji abin da
binciken nasa zai samo".
Kamar yadda aka tsara haka al'amuran suka
gudana; wato sai da Aljani Maruful Dauwaz ya
kwana uku a cikin halwar tsafi bai sake ganawa
da su Gimbiya Rahila ba.
A ranar kwana na uku da yammaci ya kammala
bincikensa. Koda ya ga sakamakon binciken sai
ya dimauce ya firgita ainun, bai san s'adda ya
kwarara uban ihu ba ya kama gwara kansa da
kasa.
Al'amarin da ya janyo karamar girgizar kasa ke
nan a gaba daya Birnin na Shaufil. Gidaje suka
rinka rugujewa suna danne mutanen da ke
cikinsu, garin ya yamutse aka yi ta guje-guje da
265
TASKARNOVELS.COM.NG
iface-iface kai ka ce duniyar ce za ta tashi. Har
sai da Aljani Maruful Dauwaz ya daina ihu
sannan komai ya lafa.
A wannan lokaci Maruful Dauwaz ya daddauje
fuskarsa bai sani ba, har ta yi kaca-kaca da jini.
Kawai sai ya fashe da kukan bakin ciki.
Yana cikin wannan hali ne Rahila, Sarki Laffaru
da mahaifin Rahila suka zo gare shi a sukwane
bisa dawakai cikin halin firgici domin a zatonsu
yakin bazata ne ya ɓarke tsakaninsa da wakilan
Sarki Nashmir ko wakilan Sharlisa.
Koda isowar su Rahila sai suka iske Maruful
Dauwaz shi kadai a zaune babu alamar ya yi
yaki da wata runduna, amma ga fuskarsa a
daddauje, jini yai masa kaca-kaca, kuma yana ta
rusa kuka. Cikin dimauta duk su ukun suka yi
sauri suka sauko daga kan dawakansu suka
zube kasa gabansa. Rahila ta dube shi cikin
tsananin damuwa ta ce, "Ya kai Sarkin Sadaukan
266
TASKARNOVELS.COM.NG
duniya, mene ne ya faru gare ka muka riske ka a
cikin wannan hali?"
Koda jin wannan tambaya sai Aljani Maruful
Dauwaz ya fusata ya daka musu tsawa. Nan take
suka dimauce, Sarki Laffaru da mahaifin Rahila
basu san sa'adda suka saki fitsari ba a wando.
Ita kanta Rahila gaba daya jikinta ne ya kama
karkarwa tamkar an tsoma ta a cikin ruwan
kankara.
Aljani Maruful Dauwaz ya dube ta a fusace ya ce,
"Ya ke wannan 'yar Sarki, ki yi sani cewa kun
cuce ni da kuka je kuka fito da ni daga cikin
kogon Darul Iksina. Inda na san abin da zai faru
ke nan da na kashe kaina tun a can kogon na
Darul Iksina sa'adda kuka zo mini da bukatarku.