x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - MAZAN JIYA 3

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 68212 words

Category: Adventure Stories

Views 193

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
gajiyawa a cikin
yakin alhalin kwanansu goma sha hudu ke nan
suna wannan masifaffen yaki a waje ďaya har ta
kai cewa sun rugurguza gaba dayan ginin gidan
na Boka Muzaffar tamkar ginin bai taɓa
wanzuwa ba Komai dake cikin gidan ya kone ya
zama toka, Mashin Galilul Haras ne kadai ko
kwarzanewa bai yi ba.

Sadauki Najwar ya ci gaba da bincike domin ya
gano wanda zai sami nasarar daukar mashin na
Galilul Haras a tsakanin matsafan uku, amma sai
abu ya gagara.

Ya sake yin bincike akan sa'adda yakin nasu zai
zo karshe amma abu dai ya gagara. Al'amarin da
ya dugunzuma hankalin sadauki Najwar ke nan
ainun fiye da ko yaushe ya fusata har ya maka
madubin tsafin nasa a kas ya tarwatse.

381

TASKARNOVELS.COM.NG
Nan fa ya zauna ya yi tagumi yana tunanin abin
da ya kamata ya yi. Sai da ya daɗe a zaune cikin
wannan hali sannan ya yanke shawarar cewa
duk yadda zai yi dole ne a cikin wannan dare ya
mallaki Gimbiya Ramlatul Siyam kuma ya
mallaki karagar mulkin Sarki Nashmir.

Ko a yau din ne kadai ya sadu da Gimbiya
Ramlatul Siyam kuma ya zauna akan karagar
mulki ai ya gama cika burinsa na duniya bai ki
ba ma Ajalinsa ya riske shi tun da ya yi abin da
babu wani mahaluki da ya isa ya yi shi a doron
kasa. Ko ba komai ba zai yi mutuwar banza ba
wacce za a manta da shi.

Dole ne a rinka tunawa da shi a cikin tarihin
MAZAN JIYA wadanda suka yi gagarumar
bajintar da ba za a taɓa mantawa ba.

Koda sadauki Najwar ya gama aiyana hakan sai
ya mike zumbur! ya fita daga cikin gidansa, bai

382

TASKARNOVELS.COM.NG
zame a ko ina ba sai inda Aljani Barukul Masnur
yake a cikin gidan sarautar.

Irin su Aljani Barukul Masnur sun kai su miliyan
daya da rabi a cikin Dakarun da ke tsaron fadar
Sarki Nashmir kuma dukkaninsu sun fito ne da
ga wata zuri'a ta aljanu a Birnin Hindu.

Tunda zuri'ar tasu ta wanzu a doron kasa, suka
kasance bayi, ba su taɓa samun 'yancin kansu ba
a wajen 'yan uwansu ajlanu da manyan Bokayen
duniya na jinsin Bil'adama.

Wani babban abin takaici a gare su shi ne, sun
kasance 'yan tsiraru a cikin al'ummar aljanu na
Birnin Hindu, kuma an kafa musu karan-tsana,
shi ya sa ake karar da dukkan rayuwarsu a cikin
bauta.

Iyaye da Kakanninsu da wannan bakin ciki suka
tsufa suka mutu, domin sun san cewa har abada
383

TASKARNOVELS.COM.NG
ba za su iya yin tawaye ba don su kwaci 'yancin
kansu. Lokacin da sadauki Najwar ya riski Aljani
Barukul Masnur sai ya ja shi izuwa cikin wani
daki suka kadaita a inda babu wanda zai ji abin
da za su tattauna.

Najwar ya dubi Barukul Masnur ya ce, "Na ji
dadi da ka rufa mini asiri ba ka gayawa kowa
sirrina ba, bisa wannan dalili yanzu zan yi wa
zuri'arku gabadayanta gatan da ba a taɓa yi
muku ba. Ka sani cewa a cikin shekara guda sau
daya jal ake ba ku hutun aikin bauta.

To ni yanzu na ba ku hutu na tsawon wata uku,
kuma a yau na shirya muku walima ta
musamman a cikin fadar maigirma sarki
Nashmir".

Koda jin wannan batu sai idanun Barukul
Masnur suka zazzaro ya cika da tsananin tsoro
ya ce, "Haba ya shugabana, ai idan ka yi haka
Sarki ya dawo sai ya sa a hallaka mu gaba
384

TASKARNOVELS.COM.NG
dayanmu. Kai kanka ba za ka tsira ba daga
sharrinsa".

Koda jin wannan batu sai Najwar ya bushe da
dariya ya ce, "Ka san dai idan Sarki ba ya nan
babu mai ba da umarni a gidan nan sai ni ko ba
haka ba ne?"

Barukul Masnur ya ce, Haka yake". Najwar ya ce,
Maza ka je ka sami ragowar yan uwanka su
duka ka gaya musu cewa ina nemansu yanzuyanzu a fada. Koda gama fadin hakan sai Najwar
ya 6ace fat. Bai baiyana a ko ina ba sai a fadar
Sarki Nashmir inda karagar mulki take.

Baiyanarsa ke da wuya ya bai wa Barori da
Kuyangi umarnin su je su kawo abinci da abin
sha iri-iri wanda za a yi walima da shi.
Nan take kuwa Barorin da kuyangin suka cika
wannan umarni cikin 'yan dakiku kadan.
Faruwar hakan ke da wuya sai ga gabadayan
385

TASKARNOVELS.COM.NG
zuri'ar su Aljani Barukul Masnur sun baiyan a
fadar.

Al'amarin da ya matuka bai wa gabadayan
Dakarun tsaro na gidan maraki ke nan, domin
hakan ba ta taɓa faruwa ba tunda Sarki Nashmir
ya hau karagar mulki.

Bayan zuri'ar su Aljani Barukul Masnur sun
gama hallara gaba dayansu kimanin su miliyan
daya da rabi sai sadauki Najwar ya daka tsawa
ga sauran Dakaru, barori da bayi da ke cikin
fadar ya ce kowa ya fita ya bar su da zuri'ar su
Barukul Masnur. Nan take kuwa aka bi wannan
umarni.

Bayan kowa ya gama fita ne sai Najwar ya sa
aka kulle dukkan kofofi da tagogin fadar don
kada ma wani ma ya ji abin da za su tattauna.

386

TASKARNOVELS.COM.NG
Ba tare da 6ata wani lokaci ba Najwar ya bai wa
su Aljani Barukul Masnur umarni suka fara
walima.

Saboda tsananin fari ciki da mamaki ba su san
sa'adda suka kama bushasha ba har ma wasu
suka rinka kade-kade da raye-raye, wasu ma
suka yi ta shan ruwan barasa kai ka ce a cikin
gidajensu suke ba a fadar mai girma Sarki
Nashmir ba. Shi kansa Najwar sai ya shagala ya
yi ta rawa a cikinsu yana nishadi.

Bayan kowa ya ci ya gyatse sai sadauki Najwar
ya tafi kai tsaye izuwa kan karagar Sarki
Nashmir ya zauna akanta ya harde kafafuwansa.
Koda ganin haka sai gaba dayan aljanun suka
firgice suka kama kuka suna rokon Najwar da ya
ba su umarnin su fice daga fadar don kada Sarki
Nashmir ya dawo a yanzu ya ga abin da ke
faruwa ya sa a hallaka su su duka.

387

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda jin wannan batu sai Najwar ya bushe da
dariya, lokaci guda kuma ya murtuke fuska ya
ce, 'Ya ku wannan zuri'a ta aljanu da ba su da
gata a wannan kasa tamu, shin kun yi imani
cewa ni ne Wazirin Sarki Nashmir?"

Su duka suka amsa da "Na'am". Najwar ya
cigaba da bayani yana cewa. "Fiye da shekaru
dubu arba'in ba ku taɓa samun 'yancin kanku
ba, Iyayenku da Kakanninku duk a cikin kangin
bauta suka mutu. Yau ni Najwar zan kwato
muku 'yancinku. Koda jin haka sai gabadayan
aljanun suka rude da shewa cikin tsananin
murna har sai da Najwar ya daga hannunsa
sama sannan suka yi tsit tamar mutuwa ta gifta.

Najwar ya ci gaba da cewa, "Ku sani cewa da
kadan Sarki Nashmir ya fi ni jarumtaka da
karfin shirin tsafi. To ni ma na gaji da yi masa
bauta babu ci gaba. Yau ne ranar da na sami
damar da zan yi masa tawaye, amma sai idan
kun ba ni hadin kai sannan ni da ku za mu samu
'yancinmu.
388

TASKARNOVELS.COM.NG

Ina tabbatar muku da cewa Sarki Nashmir ya
tafi wani gagarumin yaki shi kadai yakin da ba
zai taba tsira da rayuwarsa ba. Yanzu zan nuna
muku zahiri ku gani da idanunku".

Koda gama fadin hakan sai ya yi nuni da
hannunsa izuwa ga jikin bangon fadar. Nan take
suka ga taswirar hoton gumurzun da ake yi
tsakanin Sarki Nashmir da su Boka Muzaffar.
Al'amarin da ya matukar ba su mamaki ke nan.

Najwar ya sake nuna bangon da hannunsa
hoton komai ya dauke sannan ya ce, na yi
bincike a cikin tsafina na gano cewa za a kashe
Sarki a wannan yaki, saboda haka a daren yau
ina son ku ba ni hadin kai mu yi juyin mulki
cikin shammace domin idan muka bari har
dakakarun gidan nan suka san cewa Sarki
mutuwa zai yi, to kuwa za su dora 'yarsa ne
akan karagarsa. Idan kuwa hakan ta faru
'yancinku da nake son na karɓo muku ya suбuce
ke nan har abada, domin da zarar Ramlatul
389

TASKARNOVELS.COM.NG
Siyam ta zauna akan karagar mulki za ta sami
dukkan karfin sihirin tsafi irin na mahaifinta,
kun ga kenan ba zan taɓa iya yi mata juyin
mulki ba.

Lallai da zafi-zafi akan bugi karfe, idan kuwa aka
bari ya huce shi ke nan ba zai lankwasu ba.
Sa'adda Najwar ya zo na nan a jawabinsa sai
gaba dayan aljanun suka rude da shewa suna
masu cewa sun ba shi hadin kai dari bisa dari.

Nan take farin ciki ya lulluɓe Najwar ya sallame
su akan cewa, da zarar dare ya raba su dawo
nan fadar yana nemansu. Nan take aljanun gaba
daya suka tafi suka bar shi shi kadai tare da
Aljani Barakul Masnur.

Aljani Barakul Masnur ya dubi Najwar cikin
murmushi ya ce, "Tabbas yanzu na gamsu cewa
duk abin da ka tsara zai tabbata. Amma muna da
matsala guda daya. Yaya za mu yi da su Aljani
Maruful Dauwaz wadanda su ma sun zo ne
390

TASKARNOVELS.COM.NG
domin su mallaki Gimbiya, kuma ta yaya za ka
iya fito da Gimbiya daga cikin gidanta alhalin
kasan cewa ba za mu iya kawar da Dakarun da
ke tsaronta ba?

KAKA-KARA-KAKA!

Lokacin da sadauki Najwar ya ji wannan batu
sai ya bushe da dariya har da faɗowa kasa daga
kan karagar mulkin, ya yi ta dariyar kamar ba
zai daina ba. Daga can sai ya tsagaita da dariyar
tare da nutsuwa ya dubi Aljani Barakul Masnur
ya ce, Ai ni ba na yin Kwaina sai da Zakara.

Tuni na yi bincike akan yadda zan sami wannan
nasara, kuma na ga mafita don haka ka zuba ido
za ka sha mamaki. Nan da cikar sa'a daya jal zan
zo maka da Gimbiya Ramlatul Siyam kuma a
cikin gidanka za mu ɓoye ta har sai mun sami
nasarar juyin mulki sannan za a fito da ita a
daura aurena da ita."
391

TASKARNOVELS.COM.NG

Gama fadin hakan ke da wuya sai Najwar ya
6ace ɓat. Koda ganin haka sai shi ma Aljani
Barukul Masnur yai sauri ya bar cikin fadar.

Al'amarin sauran Dakaru, Bayi da Barori da
Kuyangin da ke hidima a cikin gidan sarautar
Sarki da Nashmir kuwa, lokacin da suka ga
Najwar ya zo da Sababbin al'amura a gidan
sarautar sai suka cika da tsananin mamaki,
amma da yake sun san cewa yana matukar
shakkar Sarki kuma yana matukar biyayya a
gare shi sai suka za ta cewa abin da yake da
sanin Sarki yake yi.

A can kurkuku kuwa, hankali Rahila da na Sarki
Laffaru ya dugunzuma ainun sun kasa zaune
sun kasa tsaye, sai kai kawo suke yi a cikin
kurkukun domin gani suke kamar shi ke nan
sun shiga inda ba za su taɓa fita ba, sai dai a fitar
da gawarsu.

392

TASKARNOVELS.COM.NG
Shi kuwa Aljani Maruful Dauwaz ko a jikinsa
wai an mintsini kakkausa. Da ma ya ga su Rahila
sun damu ainun sai kawai ya kishingida ya
kama rara wata waka. Koda yai nisa a cikin
wakar sai ya fashe da kuka saboda ya tuno da
masoyiyarsa marigayiya Rashmin.

Koda Rahila da Laffaru suka ga Aljani Maruful
Dauwaz ya kama kuka sai su ma suka fara
kukan domin a zatonsu zuciyarsa ce ta karaya
bisa samun kuбutarsu.

Suna cikin wannan hali ne wani Badakkare ya
durfafo dakin da suke ciki dauke da abincin su
Rahila. An kawo musu abincin ne saboda sanin
cewa su mutane ne idan ba a ba su abinci ba za
su iya shiga mugun hali ko ma su rasa
rayuwarsu gabaki daya.

Da isowar Badakkaren sai ya buɗe wata 'yar
karamar taga ya zuro kwanon abincin. Kafin ya
janye hannunsa tuni Aljani Maruful Dauwaz ya
393

TASKARNOVELS.COM.NG
rike shi. Nan take Badakkaren ya zama dan
minini ya shige cikin kurkukun.

Faruwar hakan ke da wuya sai Maruful Dauwaz
ya rikide siffarsa gabadaya ta koma irin ta
wannan Badakkare. Yana dafa Rahila da Laffaru
sai suka zama 'yan mini-mini. Nan take ya dauke
su ya dora su akan kafadarsa sannan ya fice
daga cikin kurkukun kamar yadda danshi ke
ratsa kasa suka bar wannan Badakkare kulle a
cikin kurkukun yana kwance ya kasa koda
motsawa.

Maruful Dauwaz ya ci gaba da tafiya a cikin
kurkukun a siffar wannan Badakkare duk inda
ya je sai ka ga an bude masa kofa ya wuce.

Rahila da Laffaru kuwa sai tsalle-tsalle suke
akan kafadarsa suna tsananin murna bisa ganin
sun fito daga cikin wannan kurkuku.

394

TASKARNOVELS.COM.NG
Saboda kankantar Rahila da Laffaru girmansu
bai wuce na tsayin babban dan yatsa ba babu
wanda ya gan su akan kafadar Maruful Dauwaz
har suka fice gabadaya daga cikin kurkukun,
sannan suka isa wani sako inda babu kowa.

A sannan ne Maruful Dauwaz ya ďaga tafin
hannunsa dai kafadarsa, Rahila da Laffaru suka
dirgo kan tafin hannunsa, sannan ya sauko da su
Kasa daidai fuskarsa ya ce da su, "Kun gasgata
maganata cewar zan iya kubutar da mu?".

Rahila da Laffaru suka gyada kai a tare cikin
murmushi. Rahila ta ce, "Tabbas mun gamsu,
Yanzu kuma mene ne abin yi na gaba?" Maruful
Dauwaz ya ce, "Na ji a jikina cewar Najwar
yaudararmu zai yi ba zai yarda mu mallaki
Gimbiya Ramlatul Siyam ba. Dole ne yanzu mu
nemi inda gidan Gimbiya Ramlatul Siyam yake
domin mu je mu sace ta mu gudu gabadaya, da
jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Rahila
da Laffaru suka ce, "Kawai a tafi".

395

TASKARNOVELS.COM.NG
Har Aljani Maruful Dauwaz ya yunkura zai fita
daga cikin sakon da suka бuya sai ya dawo da
baya ya tsaya. Al'amarin da ya bai wa su Rahila
mamaki ke nan. Rahila ta dubevshi cikin firgici
ta ce m, ya kai Sarkin sadaukan aljanu, mene ne
dalilin da ya sa ka dawo da baya?" Cikin alamun
tsananin damuwa Aljani Maruful Dauwaz ya
dubi Rahila kamar zai yi kuka ya ce, "Ya ke
wannan 'yar Sarki ki yi sani cewa yanzu ne
zamu tunkari masifar da tafi duk wacce ta same
mu a baya don haka zan iya rasa rayuwata ku
ma za ku iya rasa taku. Kafin mu je zan yi miki
tambaya ta karshe ina so ki fada mini iyakar
gaskiyarki, Shin idan na gama biya muku
bukatarku za ku cika alkawarinki a gare ni? Shin
da gaske ne za ki kai ni inda kika boye wasikar
masoyiyata?"

Lokacin da Rahila ta ji wadannan tambayoyi sai
idanunta suka ciko da kwalla har hawaye ya
zubo mata sannan ta ce, "Na rantse da darajar
gemun mahaifina zan zamo mai cika alkawari a
gare ka kuma lallai zan kai ka inda wasiyyar
masoyiyarka Rashmin take."

396

TASKARNOVELS.COM.NG

Da jin haka sai farin ciki ya lulluɓe Aljani
Maruful Dauwaz ya mayar da su Rahila izuwa
kan kafadarsa sannan ya fito daga cikin sakon
da suka buya ya ci gaba da tafiya yana neman
ɓangaren da gidan Gimbiya Ramlatul Siyam
yake.

Duk inda yake wucewa Dakaru ne tsibi-tsibi, da
zarar ya ga ana kallonsa sai hankalinsa ya tashi
don gudun kada a gano cewa shi ba Hadimin
gidan ba ne.

*****

Al'amarin sadauki Najwar kuwa, lokacin da ya
bace daga fadar Sarki Nashmir bai bayyana a ko
ina ba sai kofar gidan Gimbiya Ramlatul Siyam.

397

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda masu gadin gidan suka gan shi sai suka
bude masa kofar gidan da sauri ya kunna kai
ciki. Najwar bai isa inda turakar Gimbiya take
ba sai bayan ya yi tafiyar rabin sa'a. Ya so ace ya
isa turakar da wuri ta hanyar amfani da karfin
sihirinsa amma da yake sihirin tsafi ba ya tasiri
a gidan Gimbiya Ramlatul Siyam dole ya hakura
ya yi wannan doguwar tafiya.

Shi kansa ya san cewa bai isa ya je ya dauko
Gimbiya ba da karfin sihiri ko da karfin dantse,
sai dai idan Gimbiyar ce da kanta ta amince ta
biyo shi.

Ko ina a cikin gidan Dakaru ne na tsaro, manyamanyan sadaukan aljanu da bil'dama masu
yawan gaske, yadda komai jarumtakar mutum
ko aljan idan suka yi masa rubdugu dole ne
suami nasara a kansa.

Lokacin da Najwar ya iso tsakiyar turakar
Gimbiya Ramlatul Siyam sai aka tsayar da shi
398

TASKARNOVELS.COM.NG
anan domin anan ne iyakarsa bai isa ya matsa
gaba ba.

Babu wanda yake wuce wannan wuri ya isa har
cikin turakar Gimbiya face Sarki Nashmir da
kansa.

Koda aka tsaida Najwar sai kuwa ya tsaya cak
batare da wata gardama ba sannan ya ce, aje a
gaya wa Gimbiya cewa Sárki ne ya ba shi sako
ya kawo mata.

Nan da nan aka je aka sanar da ita. Sai ta ce a
komo a gaya masa cewar ya bayar da sakon a
kai mata. Ya yin da Najwar ya ji haka sai ya ce
aje a gaya mata cewa sako ne na sirri kuma
Sarki ya ce lallai kada kowa ya ji wannan sako.

Koda Gimbiya ta ji haka sai ta mike zumbur!

399

TASKARNOVELS.COM.NG
Cikin tashin hankali ta taho izuwa inda Najwar
yake. Tana isowa kuwa ta iske Najwar a tsaye
yana tsumayenta.

A wannan lokaci Gimbiya ta tsala ado na gaban
kwatance har kyawunta ya ninka na kullum.
Koda Najwar ya ga Gimbiya a cikin wannan ado
ai ya rude ya dimauce, bai san sa'adda ya kama
dalalar da yawu daga bakinsa ba (Ka ji maye).
Ita kanta Gimbiya sai da ta gane halin da ya
shiga har ta kyalkyale da dariya.

Daga can sai ta hade fuska ta dubi gaba dayan
Dakarun da hadiman da ke falon ta ce su kauce
su ba su wuri. Nan take kuwa aka watse aka bar
su su biyu rak.

A sannan ne ta yi masa nuni da wata kujera ya
zauna, ita ma sai ta zauna bisa wata
luntsumemiyar kujera da ke fuskantar tasa.

400

TASKARNOVELS.COM.NG
Ta dube shi cikin wani irin murmushi mai
taushi wanda ya sake dimauta shi sannan ta ce,
Ya kai Sarkin yaki ina mai sanar da kai cewa fiye
da hekaru goma baya na sani cewa kana
matukar so na kuma kana begena dare da rana.
Kai kuwa kan wanne dalili ka dorawa kanka
jarabar sona alhalin ka san cewa wutsiyar
Rakumi ta yi nesa da kasa?"

Koda jin wannan batu sai hankalin Najwar ya
gunzuma ya cika da tsananin mamaki ya dubi
Gimbiya a firgice ya ce, "Ke kuwa ya a ka yi kika
san wannan al'amari alhalin ban taɓa nuna miki
so ba kuma ban taɓa furtawa wani ba?"

Sa'adda Ramlatul Siyam ta ji wannan tambaya
sai ta bushe da dariya sannan ta ce, mahaifina
ne ya sanar da ni hakan. Ina tabbatar maka da
cewa ya san duk halin da kake ciki kuma ya
sanar da ni akan na yi hankali da kai.

401

TASKARNOVELS.COM.NG
Yanzu wane sako ne tafe da kai, kuma yaya aka
yi ka sami wannan sako daga mahaifina alhalin
sa'adda ya bar gida kai ma ba ka nan ya tura ka
yaki?"

Koda jin wannan tambaya sai hankalin Najwar
ya kara dugunzuma domin ya san cewa ba shi
da wata gamsasshiyar amsa wacce zai iya kare
kansa.

Can kawai sai ya bushe da dariya ya "Babu wani
sako daga mahaifinki, yanzu na zo ne na fitar da
ke daga cikin gidan nan naki domin naj na
aureki da karfin tsiya kuma a daren yau zan yi
wa mahaifinki juyin mulki na hau kan
karagarsa.

Koda jin wannan batu sai Gimbiya Ramlatul
Siyam ta bushe da dariya, ta yi ta dariyar kamar
za ta daina ba. Daga can kuma sai ta murtuke
fuska ta ce, Kifi na ganinka mai Jar Koma! Ka yi
ban kuskure da kake tunanin za ka iya fitar da ni
402

TASKARNOVELS.COM.NG
daga cikin wannan gida nawa. Ina tabbatar
maka da cewa, koda babu wadannan miliyoyin
Dakaru da ke kare ni ,ni kadai na ishe ka, domin
Barewa ba ta gudu danta ya yi rarrafe ba, Idan
kuma kana shakka jarraba ka gani.........."

Kafin Ramlatul Siyam ta gama rufe bakinta tuni
sadauki Najwar ya tunkaro ta kai tsaye. Ita uwa
ko gezau ba ta yi ba har ya iso gare ta.

Koda ya kai mata cafka da hannunsa sai ta goce
ya cafki iska. Kafin ya yi wani yunkuri ta tama
hannun nasa ta murde, kuma ta sa kafarta guda
ta do ki bayansa, Saboda karfin dukan sai da ya
yi sama ya gwara fuskarsa a jikin bango sannan
ya fado kasa.

Najwar ya mike tsaye zumbur cikin tsananin
mamaki! Kawai sai ya ji danshi akan hancinsa
da bakinsa, yana shafarsu sai ya ga jini.
Al'amarin da ya matukar fusatashi ke nan ya

403

TASKARNOVELS.COM.NG
gyara tsayuwarsa yana mai dunkule
hannayensa.

Koda ganin hakan sai ita ma Ramlatul Siyam
ta mike tsaye ta gyara tata tsayuwar gami da
dunkule hannunta ta ce, "Yau zan nuna maka
cewa, na sha Jarumtaka a nonon uwata, kuma
na gaji SADAUKANTAKA a jinin mahaifina. Kafin
Najwar ya ce wani abu tuni
End Ads