x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - MAZAN JIYA 3

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 68212 words

Category: Adventure Stories

Views 137

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

TASKARNOVELS.COM.NG

1

TASKARNOVELS.COM.NG

MAZAN JIYA
3
MAZAN JIYA
Littafi na biyu 3
Part C
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
MAZAN JIYA! (3)

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai!
****************************************
LOKACIN da Sharlis ta gama wannan zancen
zuci sai kawai ta juya ta fice daga cikin turakar
Sarki Laffaru ta nufi inda bargar dawakai take.
2

TASKARNOVELS.COM.NG
Da zuwa sai ta shiga cikin bargar ta kamo wani
farin ingarman doki ta fito da shi. Koda bawan
da ke kula da dawakai ya hango Sharlis ta fito da
doki sai ya rugo da gudu ya dauko mata siddi ya
daura mata.

Cikin hanzari Sharlis ta daka tsalle ta haye kan
dokinta tana goye da danta Shaddad, sannan ta
zaburi dokin da gudu ta fice daga cikin gidan
sarautar gabadaya ta nufi kofar gari kai tsaye. A
wannan lokaci ne Sarki Laffaru ya fito daga cikin
turakarsa ya iso babbar harabar gidan sarautar
inda ya iske Dakarun yakin kasar kimanin
mutum dubu dari uku da hamsin suna ta shiryeshiryen fita wannan yaki, sai fito da makamai
suke. Masu daurawa dawakai siddi na daurawa,
masu tanadar guzuri na yi. Haka ma masu
gyaran Baka da Kibiyoyi.

Koda ganin haka sai Sarki Laffaru ya daka musu
tsawa ya ce, A yi sauri a kammala shiri domin ga
abokan gaba can har sun iso kusa da kofar gari.
Koda jin wannan batu sai gabadayan Dakarun
suka cika da mamakin yadda aka yi Sarki ya san
3

TASKARNOVELS.COM.NG
cewa abokan gaba sun iso kusa da kofar gari
alhalin yana can cikin gidan sarauta kuma daga
can nesa ake jiyo tambarin yaki na abokan
gabar. Ai kuwa nan take sai ga Sarkin kofa ya
rugo da gudu a firgice! Da zuwansa sai ya zube
kasa gaban Sarki Laffaru ya ce, "Ya shugabana,
ga abokan gaba can sun iso kofar gari kunia
baou Kowa a waje face matarka Sharlis ita kadai
akan doki ta fuskancesu".

Koda jin wannan batu sai Sarki Laffaru ya ce, a
yi maza a kawo masa doki. Nan da nan kuwa aka
kawo dokin ya hau ya zabure shi da gudu ya yi
waje. Ai kuwa sai gabadayan dakarun suka bi
bayansa duu!! kamar tururuwa da iyalanta sun
fito daga rami.
A can kofar gari kuwa, lokacin da Dakarun su
Sarki Nurbas suka iso kusa da kofar birnin Kufa,
Sarki Nurbas na kan gaba sai ya ja linzamin
dokinsa ya tsaya. Lokaci guda gaba dayan
miliyoyin Dakarun nasa waɗanda adadinsu ya
kai miliyan uku da tsirari sai suka tsaitsaya.

4

TASKARNOVELS.COM.NG
Sarki Nurbas ya waiga baya ya dubi wadannan
dakaru nasa ya ga yawansu sai ya ji wani irin
dadi a ransa domin ya san a yau dai ko sama da
kasa za ta hade sai ya murkushe birnin Kufa ya
kama Sarki Laffaru ya yi masa kisan gilla,
sannan ya kwashe duk dukiyarsa ya dora
wakilinsa akan karagar mulkin. Gama aiyana
hakan ke da wuya a cikin zuciyarsa sai ya waigo
ya dubi kofar birnin Kufa domin ya ba da
umarnin a afkawa garin a fasa kofa da karfin
tsiya a shiga.
Yana waigowa haka sai ya ga wata jaruma guda
daya jal bisa doki sanye da farin sulke ta rufe
fuskarta da hular karfe kuma ta zare takobi tana
kallonsu. Al'amarin da ya matukar bai wa Sarki
Nurbas mamaki kenan, kawai sai ya bushe da
mahaukaciyar dariya, ya juya ya dubi
Dakarunsa ya ce, "Hakika Sarki Laffaru ya
haukace. In ban da wanda ya sami tabin
kwakwalwa waye zai turo jaruma guda daya jal
ta zo ta yaki wannan runduna tamu?"

Koda gama fadin hakan sai Sarki Nurbas ya sake
bushewa da dariya sannan ya dubi waɗansu
5

TASKARNOVELS.COM.NG
zakwakuran mayakansa guda uku wadanda ya
yarda da jarumtarsu ya ce, "Maza ku je ku kama
waccan jarumar ku yi mata tsirara sannan ku ja
ta a kas bayan kun daure hannayenta da igiya
ku kawo ta nan gabana tana mai wulakanta.
Koda jin wannan batu sai wadannan Dakaru
uku suka zaburi dawakansu suka nufi bakin
kofar birnin Kufa in da Shalis ke tsaye. A daidai
wannan lokaci ne Sarki Laffaru da Dakarunsa
suka fito daga cikin birnin. Koda Sharis ta gan su
sai ta daga musu hannu tana mai yi musu nuni
da kada su karaso inda take. Nan take kuwe
Sarki Laffaru ya ja tunga suma gabadayan
Dakarunnasa sai suka yi koyi da shi. Ya yin da
Sharlis ta ga wadannan Dakaru uku na Sarki
Nurbas sun durfafo ta a sukwane bisa dawakai
sai ta mayar da takobinta cikin kufe sannan ta
zaburi dokinta a guje domin ta tare su tun kafin
su zo su riske ta. Lokacin da ya rage sauira bai fi
taku biyar ba su hadu ita da Dakarun uku sai ta
daka tsalle daga kan dokinta ta yi sama kamar
tsuntsuwa tasa kafarta ta gabza musu naushi a
fuskokinsu duk su ukun suka tuntsuro daga kan
dawakansu suka zube a kas. Ita kuwa akan
dokinta ta duro ta zauna dirshsan. Koda ganin
wannan bajinta da Sharlis ta yi sai
6

TASKARNOVELS.COM.NG
gaba dayan Dakarun Sarki Laffaru suka hau
rafka tafi.

Cikin tsananin fishi Dakarun uku suka mike
tsaye zumbur suka zare takubbansu suka ruga
kanta cikin kunan rai da mugun nufi, domin su
huce kunyar da ta ba su. Da isowarsu sai daya
daga cikinsu ya sokawa dokinta takobi a ciki,
take dokin ya durkushe kasa zai kayar da ita
amma sai ta yi sama ta ci gaba da gabzar
Dakarun da kafarta su kuwa suka yi ta kai mata
sara tana gocewa suna samun iska. Nan fa duk
jama'ar da ke filin yakin suka cika da matukar
al'ajabin irin wannan jarumtaka ta Sharlis
domin sai da ta shafe kusan dakika dari uku da
sittin a sama kafarta ba ta taɓa kasa ba tana yi
wa wadannan Dakaru uku luguden duka da
kafafunta har katantanwa take yi a saman ta
juya gabas da yamma, kudu da arewa cikin
tsafin nama. Har tsawon wannan lokaci dayansu
bai sami nasarar taɓa jikinta ba da takobinsa
kuma duk ta farfasa musu baki da hanci jini na
zuba.

7

TASKARNOVELS.COM.NG
Ya yin da duka ya kai duka duk sai ta galabaitar
da su suka zube kasa magashiyan. A sannan ne
ta diro a gabansu ta yi nuni da hannunta na
hagu a gare su sai ga rigunansu da wandunansu
a hannunta ya zamana cewa kowannensu babu
komai a jikinsa face dan kamfai. Nan fa Dakarun
uku suka kamu da tsananin kunya suka manne
da junansu suna бoye fuskokinsu. Al'amarin da
ya sa Sarki Laffaru da Dakarunsa suka bushe da
dariya ke nan. Nan take Sharlis ta jefa wata igiya
izuwa kan Dakarun su ukun ta sarkalo wuyansu
a tare sannan tayi tsalle ta sake hawa dokinta
tana rike da wannan igiya ta ja Dakarun uku a
kas ta durfafi inda abokan gaba suke.

A wannan lokaci ne zuciyar Sarki Nurbas ta
kama tafarfasa kamar za ta kone saboda fusata
bisa ganin yadda Sharlis ta wulakanta
Dakarunsa da yake ji da su. Lokacin da ya rage
saura bai fi taku uku ba Sharlis ta hadu da su
Sarki Nurbas sai ta ja linzamin dokinta ya yi
turjiya, har kura ta tashi sannan ta dubi Sarki
Nurbas a fusace ta ce, "Ya kai wannan Sarki ka
yi kuskure har da ka ke tsamanin za ka iya
wulakanta ni, domin ni murucin kan dutse ce
8

TASKARNOVELS.COM.NG
ban fito ba sai da na shirya, kuma ni ce mace
mai kamar maza, daya tamkar da dubu. Ni ce
tarwatsa maza (Ni Maiboko har na tuna da
littafinTARWATSA MAZA labarin DODO
GURMAZU), kuma guguwar annoba. Ina mai ba
ka shawara da ka janye Dakarunka ka hakura da
wannan yaki domin babu nasara a gare ka. Idan
kuwa ka ki, ina tabbatar maka da cewa ni kadai
zan iya da ku domin duk yawan nan naku taron
yayo ne baku isa ku yi mini komai ba. Wanne ka
zaɓa?"

Kafin Sharlis ta gama rufe bakinta sai Sarki
Nurbas ya tofa mata yawu ya sami goshin hular
karfenta ya ce, "Kaiconki ya ke wannan
takadiriyar mace. Kina zaton ban san ko ke
wace ce ba? Ke ce Sharlis 'yar boka Narwas
wacce ke shirin daukar fansa akan Sarki Laffaru
bayan yaron da ke bayanki ya girma ya zama
gawurtaccen sadaukin da babu kamarsa. Ina
tabbatar miki da cewa kin yi babban sakaki a
yanzu domin abu ne mawuyaci ki cika burinka
saboda tuni Sarki Laffaru ya bi tafarkin da zai
iya tsira daga tarkonki.

9

TASKARNOVELS.COM.NG

Ina mai sanar da ke cewa wancan Sarki Laffaru
da ke tsaye a kofar birnin Kuffa ba Sarki Laffaru
na gaskiya ba ne, wani takadarin aljani ne mai
suna SHALBASHA BIN RAUHUB. A yanzu haka
Laffaru na gaskiya ya tunkari kogon Darul
Iksina tare da boka Muzaffar bokan da ya zo ya
gaya masa hanyar da zai bi ya kuбutar da shi
daga sharrinki. Ba don komai suke son zuwa
kogon Darul Iksina ba sai domin su riski wani
aljani wai shi Maruful Dauwaz wanda suke son
ya amince yaje ya sato musu gimbiya Ramlatul
Siyam 'yar Sarki Nashmir na birnin Hindu
budurwar da babu mai kyanta a duk fadin
duniya face gimbiya Rahila 'yar Sarki Huzaika
na birnin Sabbar.

Ki sani cewa idan har aljani Maruful Dauwaz ya
sami nasarar sato gimbiya Ramlatul Siyam Sarki
Laffaru ya aure ta za su haifi wata kyakkyawar
'ya wacce za ta zamo basadaukiya mai karfin
dantse irin na Shaddad, kuma ita ce za ta kare
Laffaru daga sharrin dan uwanta Shaddad.
Shawara da zan baki ita ce, ki fita daga cikin
10

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan yaki ki ba ni dama na ragargaza
Dakarun Sarki Laffaru sannan na kashe aljani
SHALBASHA IBNI RAHUBA sannan na dora
wakilina akan karagar Laffaru koda ya dawo
daga kogin Darul Ikisina bai isa ya shiga
birninsa ba in yaso a sannan sai mu hada karfi
ni da ke mu hallaka shi. Idan kin amince da
hakan zan bar miki duk dukiyar Sarki Laffaru
bana bukatar koda tsinke daya daga cikinta!

Sa'adda Sarki Nurbas ya zo nan a zancensa sai
Sharlis ta yi shiru tana tunani tsawon dakiku
sittin saboda maganganun nasa sun ratsa ta
ainun kuma taji a jikinta cewa duk abinda ya
fada gaskiya ne domin biri ya yi kama da
mutum. Amma da ta yi wani tunanin daban sai
ta ga cewa idan ta yi amfani da wannan shawara
ta Sarki Nurbas ba za ta dauki fansa ba akan
Laffaru kamar yadda take so.

Koda gama wannan tunani sai Sharlis ta dubi
Sarki Nurbas a fusace ta ce, "Na ji duk abinda ka
faɗa kuma na gamsu gaskiya ne, amma ba zan
iya amfani da shawararka ba. Da jin haka sai
11

TASKARNOVELS.COM.NG
Sarki Nurbas ya zare takobinsa ya ce, Ai kuwa
sai dai mu yi yaki domin ni duk abinda na sa a
gabana sai na yi shi ba na ja da baya saboda
haka ka'idar sihirin tsafina yake! Tun kafin na
baro gida na yi bincike na tabbatar da cewa ni
ne da nasara a wannan yaki, don haka ba gudu
ba ja da baya!"

Lokacin da Sharlis ta ji haka sai ta zaburi
dokinta ta je can karshen kusurwar arewa ta sa
tsinin takobinta ta karto layi tun daga farkon
kusurwar har izuwa karshen kudu, sannan ta
dawo tsakiyar fili ta dubi Sarki Nurbas ta ce,
"Idan ka ga dayanku ya hauro layin nan da na
karta sai idan ba na numfashi".

Cikin tsananin fishi Sarki Nurbas ya ce, Ai kuwa
yanzun nan za ki daina numfashin!
Kawai sai ya zaburi dokinsa da nufin ya ketara
wannan layi da Sharlis ta shata. Koda dokin yaje
daf da layin sai ya yi tirjiya ya dinga daga
kafafuwansa sama yana haniniya domin ji ya yi
kamar ana tsikarinsa da karfen da aka gasa a
12

TASKARNOVELS.COM.NG
cikin wuta" Sarki Nurbas ya yi ta kokarin tilasta
dokin ya haure layin amma dokin sai ya ki ya
juya da baya. Cikin fishi Sarki Nurbas ya sauka
daga kan ya gabza wa dokin dokin naushi a
wuya. Ta ke dokin ya fadi kasa. Sarki Nurbas ya
dubi Dakarunsa gaba dayansu ya daka musu
tsawa ya ce, Me kuke jira ne da ita ku afka mata
mana! Gaba dayan miliyoyin Dakarun sai suka
zaburi dawakansu da nufin su haura wannan
layi. Ai kuwa sai dawakansu suka rinka turjiya
kamar yadda dokin Sarki Nurbas ya yi.
Saboda turmutsutsu sai dawakan suka rinka
karo da junansu suna zubar da mahayansu kasa
suna tattake su.

Nan take wasu daga cikin Dakarun suka rinka
mutuwa. Koda ganin wannan al'amari sai Sarki
Nurbas ya sake fusata ainun kawai sai ya yi nuni
da hannunsa na hagu ga Sharllis.

Nan take wata iska mai karfin tsiya ta zuko
Sharlis ta direta a gabansa suka kaure da
azababben yaki shi da ita.Nan fa Dakarun nasa
13

TASKARNOVELS.COM.NG
ma suka yi caa! a kanta suka yanyame ta suna
masu kai ma ta sara da suka. Koda Sharlis ta yi
wata irin katantanwa da takobinta sai ta
tarwatsa su sai dai ka ga mutane a sama kamar
janyesu ake da kugiya.
Wohoho! Hakika gwani ya ji daɗinsa, domin
idan ka iya ka huta da takaici. Inda Sharlis ba ta
kasance jarumar kwarai ba da tuni wadannan
Dakaru sun yagalgalacta sun yi filla-filla da
sassan jikinta, amma sai ga shi ta zame musu
alakakai, sannan kuma ta rinka girbar
kawunansu. Nan fa sama ta cika da kasuwar
kawuna, jini ya rinka tsartuwa da feshi yana
tsiri izuwa sama yana zubowa kasa. Babu
abinda zai bai wa mutum mamaki face yadda
Sharlis ke yaki biyu a lokaci guda, wato tana
fama da harin Sarki Nurbas wanda shi kadai ne
ma yake iya kai mata munana harin kuma tana
fama da harin Dakarunsa.

Su Sarki Laffaru da ke tsaye a can baya suna
kallon wannan bakin gurmurzun yaki da ake
fafatawa sai suka cika da matukar al'ajabi suna
mamakin yadda akayi Sharlis ta sami irin
14

TASKARNOVELS.COM.NG
wannan gagarumar jarumtaka. Nan take aljani
Sharbasha ibini Rauhuba ya ji zuciyarsa ta buga
da karfi ya ce a ransa, Tabbas jaruma Sharlis ba
karamar shaidaniya bace, lallai tana da karfin
sihirin tsafi da kuma karfin dantse, idan na yi
wasa ma za ta iya gano sirrina." Haka dai su
aljani Shalbasha suka ci gaba dazuba ido suna
kallon ikon Allah.
Lokacin da Sarki Nurbas ya ga irin mummunar
ɓarnar da Sharlis ke yi musu, sai zuciyarsa ta
kara harzuka fiye da ko yaushe kawai sai ya
dakawa Dakarunsa tsawa ya umarce su da su ja
da baya gabadayansu, su bar shi da Sharlis shi
kadai.

Ba tare da ɓata lokaci ba kuwa Dakarun suka ja
da baya, kuma suka yi wa Sharlis da Sarki
Nurbas kawanya suka zuba ido su ga abinda zai
faru. Sharlis da Nurbas suka fara zagaya juna
kowannensu na tunanin hanyar da zai shigi
kowa.
Daga can sai suka kaure da sabon azababben
yaki, suka rinka kai wa juna sara da suka cikin
tsananin zafin nama, juriya da bajinta. Sai da
15

TASKARNOVELS.COM.NG
suka shafe sa'a guda suna gumurzu amma
dayansu bai sami nasarar koda taɓa jikin daya
ba. Al'amarin da ya sa Sharlis ta cika da tsananin
mamaki kenan domin tun daga lokacin da ta
koyi yaki kawo i yanzu ba ta taɓa haduwa da
jarumin da ta kasa kai shi kas ba a cikin dakiku
dari da ashirin ba, amma yanzu ga shi Sarki
Nurbas ya gagare ta a tsawon sa'a guda. Lokacin
da suka gaji sai suka ja da baya suka yi cirkocirko suna haki. Nan fa suka kurawa juna idanu
kawai suna nazarin irin salon fadan da ya
kamata su sauya. Jim kadan suka sake kaurewa
da sabon fada, amma wannan karon sai
kowannensu ya sauya sabon salon fada, suka
rinka tsalle-tsalle suna alkafira sama kuma suna
katantanwa a kasa suna dada kai wa juna
mugun hare-hare.

A haka ne kowannensu ya sami nasarar yankar
kowa. A kafada Sharlis ta yanki Nurbas, shi
kuma a damtsen hannunta na dama amma nasa
raunin yafi nata zurfi da tsawo, ita nata raunin
ma dan karami ne.

16

TASKARNOVELS.COM.NG
Koda Sharlis ta ji zogi a hannunta ta shafa
hannun ta ga jini sai ranta ya ɓaci ta afkawa
Sarki Nurbas da dukkan karfinta ya zamana
cewa ta hada abu uku a lokaci guda, yana kai
masa sara da takobi, tana kai masa naushi da
bugu da hannu da kafa, kuma tana yin tsalletsalle a samansa. Nan da nan kuwa ta ruda shi
don haka sai ya fara amfani da karfin sihirinsa,
amma sai sihirin ya ki ya yi tasirin komai domin
bai iya kare hare-hare na ta ba kuma bai iya
cutar da ita ba. Ana cikin haka ne duk su biyun
ska daka tsalle sama na ban al'ajabi domin gani
aka yi sun luluka a can kololuwar sama kamar
an zurou igiya an janye su.

A can saman ne suka kai wa juna mugayen sara.
Nurbas ya kai ma ta sara a ciki, sai ta goce ta
mikar da jikinta baya, takobintasa ta sari iska.
Kafin ya sake kawo ma ta wani saran ta dunkule
ta zama 'yar mitsitsiya ta fice fit ta tsakankanin
kafafunsa. Nurbas ya waiga da sauri domin ya
kai ma ta wani mugun harin, amma sai ya ji
kaifinu takobinta ya tsarge wuyansa gida biyu.
Caraf sai Sharlis ta ruko gashin kansa, nan take
kan ya rabu da wuyan sai ga jini na 6ul6ulowa
17

TASKARNOVELS.COM.NG
daga gangar jikin nasa ta subuto kasa ta fado a
tsakiyar Dakarunsa a lokacin da Sharlis ke
saukowa kasa a hankali tamkar tsuntsuwa mai
fuka-fuki.

Koda Dakarun Sarki Nurbas suka ga gangar jikin
Sharlis ta fado babu kai
End Ads